Sponsored Links
Hausa Novels and Love StoriesRubutacciya Hausa Novel

Rubutacciya Hausa Novel

Sponsored Links

��RUBUTACCIYA BOOK 1

         CHAPTER 1

     *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*

*Wannan littafin na kudine idan kina bukata kiyi magana ta wannan number 09068032427 Idan baki shirya siye ba kada kiyiman magana ki bari sai kin shirya*

KADUNA

Da yammacin ranar Alhamis ne, Allah ya yalwata garin na Kaduna da ruwan sama. Hakan ya jawo boyewar jama’a da dama domin fakewa ruwan. Ruwane ake tsugawa mai Karfi kamar zai fasa saman kwanukan jama’a. Cikin hukuncin na Rabbi, wanda ya saukar da ruwan ba tare da wayonmu ko dabararmu ba, ya tsaida abin shi cak! Cikin lokaci Kalilan. Hakan ya sa jama’ar da ke Boye suka fara firfitowa kowa na KoKarin kama gabansa, domin gab ake da kiran Isha’i. A irin wannan yanayin da za ka ci nasarar leKa dakunan jama’a za ka tsinci kowannen su a Kundudune cikin rigar sanyi, ko kuma bargo. Marasa Karfi kuwa, irin almajirai da sauran su, suna Kudundune a lungu ko kuma cikin zannuwa.

Alhaji Lukman ne zaune a mazaunin direba, yana tafiya a natse bisa shimfidaddiyar kwalta, fuskarsa babu alamun gajiya ko kuma Kosawa da irin cinkoson motocin da ya ci karo da su kafin, ya sami daman hawa saman gada. Hakan ya dasa masa tunani kala-kala a cikin

Zuciyarsa. A wannan karon zuciyarsa ta gama karaya, har ya soma jin ya gaji da yadda hanyar ba ta motsawa. Babu abinda yake hange a yanzu kamar gidansa da ke cikin rukunin gidajen na Unguwar Rimi. Yana son watsa ruwa, haka ba . ya son isha’i ta riske su a hanyar.

Duban agogon cikin motarsa ya yi wanda , yake nuna masa Karfe bakwai da rabi. A _ zuciyarsa ya ce, ya makaro. Cunkoson ababen hawan suna ci gaba da yawaita ne daga saman gadan, hakan ya sa ya dan waiwayo ya dubr * dansa Sultan da ke kallon gefen titi hankalinsa kwance.. Ta madubi ya dubi matarsa Hajiya * Salma, ita ma dai idanunta suna kafe a cikin jarida.

Ya sake mayar da hankalinsa a kan kwaltar yana duban yadda kowa ke sauri domin isa ga muhallinsa. Ganin yawan cunkoson ya fi yawa ne daga saman gadar, yasa ya sauya ra’ayinsa, wajen sauka Kasa ya bi ta Kasan gada. Wanda yake hango tarin sauki fiye da tsayuwarsa a inda bai san lokacin isarsa gida ba.

Hajiya Salma da ke hakimce a baya, ta dago daga karatun Jaridar da take yi, idanunta

manne da farin gilashi, tana duban yadda Maigidanta ya sauya hanya, hakan ke tabbatar masu dole sai sun je Mando kafin su yi kwana. Babban dansu mai shekaru goma sha biyar a�? duniya yana ci gaba da watsa idanunsa a bisa titin kamar mai son tuna wani abu. A cikin zuciyarsa kuwa ji yake kamar a dauwama a cikin irin wannan yanayin, kasancewarsa mutum mai tsananin son damina. Yanayin da ke sa shi farin ciki fiye da kowanne irin yanayi.

Tun bayan fitowarsu daga Jaji, gidan. mahaifiyar Abbansa, suka shiga mota, babu wanda ya furta ko da kalma daya. Kowa da irin . sake-saKen da yake yi, kasancewar ita zuctya ba a raba ta da yawan tunane-tunane, duk da shirme yafi yawa a cikin dukkan tunanin. Haka tsarin su yake, ba su damu da dole sai sun yi surutu ba, idan kuwa za su yi sai ya kasance mai ma’ana ne, kasancewarsu ‘yan boko masu ji da kansu. Ko cikin gidan su ka shiga za ka sami gidan su shiru kamar babu kowa a cikinsa. Sau tari idan sun shiga za ka sami gidan shiru kamar babu kowa, shi ya sa da zarar masu surutu sun kawo ziyara gidan, suke tattara surutunsu, su ajiye tsakar gida. Suna fitowa suke nada gammo su dauki abinsu. Domin ko ka yi babu mai ba ka cikakkiyar amsa. Sau tari masu surutun cikin dangi suna fitowa daga gidan suke fara tsinewa bakin hali da son korar bako da Karfi da yaji irin na gidan Alhaji Lukman.

Sultan ya dan dubi mahaifinsa, kamar zai basar, sai kuma ya ce, “Abba idan ka sami wuri ka tsaya kusa da tashar motocin can, zan sha kayan marmari sannan ina jin fitsari, zan je in yi,�? Yana maganar yana yamutsa fuska kamar wanda akai wa dole sai ya yi.

Hajiya Salma ta dago tana duban danta, “Sultan ka bari mu Karasa gida mana. Ba ka san ana daukar ciwuka wajen tsuguno a irin nan wajen ba ne?�? ta yi maganar tana sake zura idanunta a kansa cikin kulawa.

Idanunsa ya sake watsawa a bisa titin, yana nazarin har yaushe cunkoso zai ragu su isa gidan? Girgiza kansa kawai ya yi ba tare da ya ce uffan ba, ya dawo da kallonsa ga mahaifinsa da ya sami wuri ya tsaida motar. Gorar ruwa ya dauka ya fice daga motar. Idanu yake rarrabawa

yana neman inda ya kamata ya yi fitsarin. Wurin

ya jagalgale da yawa, don haka ya dinga jin Kyama ya kasa ajiye Kafafunsa yadda ya kamata. Lalacewar wurin ya darsa masa danasanin fitowarsa, amma kuma yadda yake jin fitsarin ba zai iya haKura ya koma ba. Bayan wata Katuwar mota ya samu ya zaga, sannan ya yi abinda ya kawo shi, ya mike hannunsa riKe da ragowar gorar ruwan yana son fita ya wanke Kafafunsa. Numfarfashin da yake ji sama-sama kamar akwai wani abu a kusa da shi, ya sa ya dan dakata da tafiyar da yake yi, tare da kasa kunnensa sosai Yadda yake jin numfarfashin yana Karuwa, ya sa Kafafunsa suka kama rawa-. Tsananin tsoro ya shige shi. Don haka ya yi tsalle gefe guda yana zare idanu. Ji ya yi kamar an sawa Kafafunsa dabaibayi. Ji ya yi kamar Kafafun sun gaza daukarsa. A hankali yake jiyo sautinta, “A taimake ni! Ruwa! Ruwa! Zan mutu.�? Cikin Karfin hali da son ganin mene ne ya daga kafarsa daya ya sake daga dayar ya nufi wurin da sautin ke ratsa kunnuwansa. Gumi ke. �? tsattsafo masa kamar ba shi ba ne ke jin sanyi. Duk yadda ya so ya yi Karfin halin tunkarar

shiga wurin da yake jin sautin abin ya faskara. Da baya da baya ya koma yana sake waige kamar mai neman wani abu. Wani ya hango daga shi sai singlet da buta a hannu, rudanin da ya shiga ya hana shi mamakin yadda ake kwada sanyi, amma kuma babu riga a jikinsa. Da sauri ya bi bayansa, “Malam! Ina jin Kara a kusa da babbar motar can, don Allah zo ka duba ka gani. : .

Mutumin ya zabga masa harara, “Kai! Me kake yi a nan? Idan ba ka wuce ba, za ka ci mutan gidanku.�? Ya sa kai da nufin tafiya Sultan ya sha gabansa, “Don Allah ka zo ka gani.�? Tsayawa ya yi yana Kare wa Sultan kallo cikin duhun, kafin ya ce, “Mutum ce a wurin sai kuma me kake son ji?�? Mutumin da ya yi shayeshayensa ya baiwa Sultan amsa cikin Kufula a kan bata masa lokaci da yake neman yi.

Sultan ya zazzaro idanu alamun firgici. “Mutum? To me yake yi a wannan wurin? Ku ce ya tashi wani abu zai same shi.�? Sultan ya jero wadannan kalaman cikin kidimewa. Da alamun Sultan ya fara kai mutumin bango idan aka yi la’akari da kallon banzan da yake aika masa.

| Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce, “Kai yaron nan akwai shegen naci, kamar irin kafiran farkon nan. Eh mutum! Mutum din ma mai numfashi. Ba namiji bane mace ce, Saudatu ce, take yaudarar jama’a da Hijabi sai ga cikin shege. Ko da yake arniya ce, ta shigo mana musulunci da masifa. A nan Kasan motar take kwana. Kila ma nakuda take yi, don yau kwananta biyu kenan ban ganta ba. Da a can take kwana aka koro ta.�? Ya nuna wani wuri da hannu, wanda babu komai a gun Sal tayoyin babbar mota.

Tunda yake magana Sultan ya kafe shi da idanu ta hasken motocin da ke wucewa, suna hasko su. Sai dai kafin ya ankare ya sake samo tambayar da zai yi masa har mutumin ya wuce abinsa, yana auna wa Sultan zagi. Numfarfashin da ya sake jin ya Ziyarci kunnuwansa, ya kanainaye zuciyarsa da wani irin tausayl. Damuwa ce manne a zuciyarsa.

Wannan karon da rashin tsoro ya doshi Karkashin motar, wanda ga dukkan alamu motar ta jima da tashi aiki. Kai tsaye ya rankwafa-ya ~ shige. Ruwan saman da aka yi ya sami

makwanci a KarKashin motar,

“Sannu Anti. Anti me kike son in kawo maki? Don Allah Anti kiyi min magana kin ji?�? Wasu hawaye suka sake tsinke masa, wasu suna korar wasu. Cikin hukuncin Allah aka hasko hasken fitila, wanda ya ba Sultan daman kallon fuskarta. Hawaye ne kwance a bisa fuskar. Idanunta a rufe. Bude idanun ta yi , ta zubawa Sultan, tana kallon yadda hawaye suka bata masa gaban riga. idanun ta mayar ta rufe. Ganin yadda take kuka yasa ya sake Kankameta yana kuka sosal.

Tunda yake bai taba ganin babba yana kuka ba, sai a kan Saudat. “Anti ki yi hakuri ki daina kuka. Ki yi addu’a ne Anti don Allah.�?

Cikin sautin muryar marasa lafiya ya ji muryarta tana magana, “Na gode, na gode. Ku taimakeni ku raba ni da nan za a kasheni ne.Ina son ko ban rayu ba, abinda ke cikin cikina ya rayu, domin dasawa wanda ya kawo ni nan, bakin ciki da tabon da ba zai taba gogewa a tarihin zuri’arsu ba. In gaya maka wani abu, da kuma littafi ka tafi da shi ka miKawa wani babba, wanda zai iya taimaka min wajen yada labarin nan? Ka yi alKawarin ko bayan raina za ka taimake ni ka tona asirin wanda ya sa jefa rayuwata a cikin masifa? Kayi alKawarin za ka Kwatowa dan da zan Haifa ‘yancin sa?�?

Kwakwalwar Sultan ta yi karama da sauraren wannan kalaman na Saudat. Kukansa ya Karu ya gyada kansa ba tare da dogon nazari ba, alamun ya amince. Yana son yin magana a lokacin da ta mika hannu take nuna masa wani Boyayyen buhu a sakale, wani mutum ya fizgo shi da Karfin tsiya, kan Saudat din ya koma gefe. A gaban Abbansa suka tsaya a lokacin da yake jin muryarsa yana cewa, “Kada ka ji masa ciwo mana malam!”�?

Sultan ya fizge da Karfin tsiya daga irin rikon da mutumin ya yi masa ya zube a gaban mahaifinsa a bisa guiwowinsa ba tare da ya damu da cabalbalin wurin ba. “Abba ka taimake ni kada ta mutu. Abba ku bar ni in je inji abinda za ta gaya min. Abba za ta mutu idan muka tafi.�?

Abban ya kai kallo ga Hajiya Salma, wanda dukkansu mamakin Sultan din ne ya rufe su. Kafin su yi magana mutumin da ya finciko shi daga gun Saudat ya fara magana, “Alhaji ka kama yaron nan naka ku bar wurin nan. Yarinyar nan cikin shege ta yi, saboda rashin kamun kai

ko da kuwa daki daya kuke kwana. Zai kasance akwai jahilci a cikin jama’a da suke tunanin H.1.V zai shafi makusancinka. Na gode.�? Kallo ya bi shi da shi har ya isa ga matarsa ya ja suka wuce.

Lokaci bayan lokaci yana jin dirar kukan yaronsa har tsakiyar kansa. Amma kuma babu wanda ya iya Kara cewa komai. A haka suka Karasa gidan, ‘yan Kannensa su biyu, Hafsat da Haidar suka taso da gudu daga hannun Mairo mai aikinsu, kai tsaye gurin Sultan suka nufa. Ya shafi kansu kawai ya wuce ciki. Duk: suka bi jikinsa da kallo, sannan suka dubi Abbansu suka ce, “Abba me ya sami Yaya Sultan jikinsa ya lalace? Ya fadi a kwata ne?�?

A nan ma babu wanda ya ce masu komai. Shi kuwa yana shiga ya fada bandaki ya yi wanka da alwala ya fito ya shimfida darduma ya gabatar da Sallarsa, a nan kan daddumar ya yi barci, tare da sa hannunsa a matsayin matashin kai.

“Umma! Umma!! Abba!!! Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Me ta yi maku? A’a don Allah ku bar min Antina kada ku kashe ta.�?

A guje suka shigo dakin suna girgiza shi. Cikin tashin hankali da gigicewa ya tashi da Karfinsa ya ture su ya yi hanyar waje da gudun gaske. Cikin sa’a mahaifin ya kamo shi ya rungume shi a Kirjinsa yana shafar bayansa, “Ka natsu Sultan ni ne mahaifinka. Ka natsu ka ji? Mene ne?�?

Cikin hawaye masu yawa da ke sauka daga kwarmin idanunsa, “Abb�? Abba..�?

Ajiyar zuciya ya saki da Karfi, kamar wenda zai hadiyi zuciya. “Abba idan bamu je mun taimaki Anti Saudat ba, nima zan tafi can da nisa inda ba zaku ganni ba.�? Cikin jin zafin kalaman yaron kamar ya watsa mata ruwan zafi, ta Karaso har gaban Alhaji Lukman ta finciko yaron ta dauke shi da mari har sau biyu, kafin ta kai hannu ta buge masa baki tana huci. “Dan ubanka zo ka kwashe kayanka ka bar min gida shashashan yaro. Har kayi girman da Za ka fara�? sa min ciwon kai Sultan? Duk cikin mutane ka rasa wacce za ka ce a taimaketa sai karuwa? Mazinaciya? Tubabbiya? Wacce iyayenta suka guje ta? Bare mu haduwar Kaddarar fitsari? Uwa uba mai dauke da cutar da kaf zuri’arku sai tabi  ta kashe daya bayan daya. Na ji a jikina matsala ce ke shirin tunkarar mu shi ya sa na hanaka zuwa fitsarin nan, kayi min kunnen shegu.�?

Ran Alhaji Lukman ya kai matuKa a baci, ya dinga dubanta kamar bai taba ganinta ba. “Akan matsalar nan zaki dukar min yaro? Ke kin fi Karfin Allah ya jarabceki ne? Ko kuwa har kin gama tsara abubuwan da za su faru da ke a gidan duniya ne? Har kin gama tsara komawarki gare shi? Kina da yara mata kike tsinewa na wasu? Daman kina tunanin zaki dauwama a duniyar ne?  zamu mutu, ta hanyar da Allah ya tsara mana a cikin littafinsa. Sultan yana dafe da Kuncinsa ya Karaso kusa da Abbansa ya ce, “Abba, Anti.�? Sunkuyawa ya yi ya rungume yaron, “Ka yi hakuri Sultan, zuwa gobe sai mu Je mu dauko ta. Ka ga yanzu Karfe goman dare.�?

Sultan ya girgiza kai, “A’a Abba idan ba mu je yau ba, za ta mutu ni kuma bana son ta mutu.�? Murmushi ya yi “Yadda kace haka za a yi Sultan. Amma ina son ka sa a ranka, kowani ,  rai sai ya dandani dacin mutuwar nan. Ba mu Zo domin mu zauna a duniyar ba. Ta so mu je.�?

Hajiya Salma, da taji gabanta ya fadi, ta fice daga dakin ranta a matuKar bace. Tun kafin ya fara tuki ya kira ‘yan sanda ya yi masu bayani tare da kwatanta masu wurin yana son su riga shi zuwa. Yana kashe wayar ya kira Asibiti, ya ce yana buKatar motarsu tare da kwatanta masu wurin. Sultan dai sai kallon fitilun gefen titunan yake yi ransa a jagule. ba kamar dazu ba, da yake jin nishadi. Gani yake kamar mahaifinsa baya sauri. Duban yaron ya yi bayan ya murza sitiyarin ya sha kwana, “Sultan, ka yi min murmushi mana. Ka ganka kuwa? Gabadaya fushi baya yi maka kyau, sai ka koma sak! Hajiya Gwaggo.�?

Kallon mahaifinsa ya yi idanunsa cike da hawaye, “Abba sai andauko anti.�? Lallai tunda yau ya kasa samun fara’ar yaronsa, ya san abin da gaske ne. Shi kansa yana jin kwatankwacin abinda yaronsa ke ji.

Tunda suka yi fakin Sultan ke bin motar ‘yan sandan zuwa motar asibitin da kallo. Gaba daya ya kasa sauka sai da mahaifinsa ya yi masa

magana. Shi kansa Alhajin yadda ya kula da kamar hankalin ‘yan sandan a tashe ya isa ya gamsar da shi akwai matsala. A tare suka iso suna mai sake kafe su da idanu. Daya daga cikin su ya Karaso hannunsa rike da wayar sadarwa, “Alhaji muna isowa muka hadu da tashin hankali. Baiwar Allahn da ka kwatanta mana ita ga ta can kwance cikin jini, wasu marasa imani sun sassare ta har Allah ya yi mata cikawa. Mun iso dai-dai sun gama ta’asar. Mun yi iya bakin Kokarinmu mu kama su, amma hakan ya gagara-. Tarasu.�?

Sultan da jikinsa yake kyarma, ya durKushe Kasa yana wani irin kuka, “Ant Saudat!! Me za ki gaya min?�? Iya abinda bakinsa da ke karkarwa ya iya furtawa kenan. Sauran maganar ta maKale a makoshinsa. Kuka ya tokare masa ya hana su fitowa, Alhaji Lukman ya lumshe idanunsa, “Ya Salam!�?

Hawaye suka cika masa idanu, yasa hannu ya sharce. Jikinsa ya yi matuKar sanyi, “Allah ya jikanki.�? .

Sultan ya mike cikin kuka ya isa kan gawar da ke shimfide da Katon cikinta a gaba.

Duban ‘yan sandan ya yi yana ganin su dishidishi. Har sun kammala daukar hotunanta da kuma rubuce-rubuce. Idanu ya zuba mata har zuwa yatsunta da ke ‘dauke da wani zobe mai kyau. Kurawa hannun ido ya yi. Ya sa nasa hannun ya rike ta, yana jin kamar numfashin zai dauke. A hankali ya :zare zoben da ke hannunta ya mayar cikin aljihunisa.

‘Yan sandan sun so su raba shi da gawar, Abban ya dakatar da su, “Ku bar shi ya rage radadin da ke damunsa, tun dazu yake mana magiyar mu je mu dauko ta ashe mutuwa za ta yi .�? Kwalla ta ziruro masa daga idanunsa, ya girgiza kai kawai. A dai-dai lokacin kiran Hajiya Salma ta shigo wayarsa. Ya ji duk ya tsaneta. Ya tabbata duk namijin da ya ce zai biye wa shawarar wata macen sai ta kaishi ta baro. Dauka ya yi ya sa a kunne yana magana cikin rawar murya, “Baiwar Allan da take miko hannu take bukatar taimako kika hana, saboda dalilin kin tsani zina, kin tsani mai dauke da cuta, kin tsani wacce ta tuba ta koma addininki. Wadanda suka fi ki tsanar wadannan abubuwan sun kashe ta sun kawar da ita daga duniyar gaba daya.�? Sauke

Shin me zai faru? Kudai kuci gaba da bibiyar mu

Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na  RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA da MISBAH kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427*idan baki shirya siye ba kada kiman mgn ki bari sai kin shirya

��RUBUTACCIYA BOOK 1

            CHAPTER 2

   *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*

JIYA MUN TSAYA

Yan sandan sun so su raba shi da gawar, Abban ya dakatar da su, “Ku bar shi ya rage radadin da ke damunsa, tun dazu yake mana magiyar mu je mu dauko ta ashe mutuwa za ta yi .�? Kwalla ta ziruro masa daga idanunsa, ya girgiza kai kawai. A dai-dai lokacin kiran Hajiya Salma ta shigo wayarsa. Ya ji duk ya tsaneta. Ya tabbata duk namijin da ya ce zai biye wa shawarar wata macen sai ta kaishi ta baro. Dauka ya yi ya sa a kunne yana magana cikin rawar murya, “Baiwar Allan da take miko hannu take bukatar taimako kika hana, saboda dalilin kin tsani zina, kin tsani mai dauke da cuta, kin tsani wacce ta tuba ta koma addininki. Wadanda suka fi ki tsanar wadannan abubuwan sun kashe ta sun kawar da ita daga duniyar gaba daya.�? Sauke

ZAMU TASHI

wayar ya yi, tare da kasha ta, yana jin danasanin biye wa matarsa.

Kallon likitan ya yi yana_ sauraren maganarsa. “Yallabai ina tunanin idan aka yi gaggawa zamu iya ceto abinda ke cikinta, ta hanyar yi mata aikin gaggawa.�? Gabadaya aka yi amanna da bayanan likitan. Sultan yana rike da ita yana sharar hawaye, rigarsa duk jini gani yake kamar za ta tashi. Abbansa ya zame hannayensa bisa gawar saudat. Yana kallo aka sata a mota. “Ruwa! Ruwa!!�? Sautin muryarta, ya dake shi.

Kufe idanunsa ya yi domin ya baiwa hawayensa daman sauka. “Ku taimakeni ku raba ni da nan, za a kashe ni. Ku taimake ni ina son abinda ke cikina.�? Kalamanta suna yi masa kuuwa da Karfi. Shiru ya yi yana duban su Abbansa. Ganin ba ya kallonsa ya shige Karkashin motar nan ya jawo buhun yana bincike a ciki, Ya ci karo da littafi Kato, dauke da hotuna wanda bai tsaya duba komai ba, ya mayar cikin nigarsa. Muryar Abba ya ji yana Kwala masa kira, ya yi sauri ya fito. Ya kama hanyar shiga motar hawaye suka sake tsinke masa. Yana goge wasu, wasu kuma suna sake kwaranya.

Sun kama hanya, muryar Saudat ta ci gaba da yi masa kuuwa, “Zan gaya maka wani abu.�? Sultan yasa hannu ya toshe kunnuwansa da Karfi. “Abba…�? Ya ja sunan mahaifinsa da Karfi tare da fashewa da kuka. Abba ya cika da al’ajabin irin kukan da Sultan yake yi, domin har kiransa ake yi mai taurin zuciya. An sha a yi mutuwa kowa na kuka, amma idanunsa ko gezau baya yi. Abba da ya gama karya hanya yasa hannunsa daya ya jawo shi jikinsa. “Abba tana ta kirana da hannu, amma kuka rabani da ita, tana son ta min maganar da kowa ya kasa sauraronta, amma baku ji tausayinta ba, kuka hanani sauraronta. Ban san me take son gaya min ba. Me yasa Abba?”Shi kansa hawayen danasanin ne kwance a idanunsa. Bai san me yasa mutuwar Saudat ya tsaya masa a rai ba. Bai taba kawowa zai taba shiga irin wannan damuwar ba. “Kayi hakuri Sultan, Allah ya riga ya aiko bamu isa mu kaucewa Kaddarar mutuwarta ba. Kayi shiru ka daina kukan haka. Kukanka yana karyar min da  zuciya. Ta fi buKatar addu’arka fiye da wannan kukan�? Shi dai Sultan saurarensa yake ba don yana fahimtarsa ba. Kwanciyarsa ya yi a jikin mahaifinsa yana faman sauke ajiyar zuciya. Wannan karon duk sonsa da kallon titi, bai kalla ba, domin zuciyarsa a Kuntace take, ta yadda komai ba ya yi masa dadi. Kai tsaye aka iso da gawar (GIWA HOSPITOL) Asibitin da ake matuKar ji da shi a garin na Kaduna. Cikin gaggawa aka karbe ta tare da shirye-shiryen shiga da ita aiki. Su Abba suna nan tsaye aka wuce da ita, don hakane suka yi ta kaiwa da komowa. Tun suna sa ran fitowarsu har suka gaji suka koma gefe guda. Hajiya Salma kuwa duk da jikinta ya yi dan sanyi da mutuwar Saudat sai da ta tsinci bakinta da cewa, “An rage mugun iri. Da haka ake bin mazinatan nan, ana kashewa da masifu sun yi mana sauki.�? Ita damuwarta danta da mijinta su dawo gida, Agogon yana buga sha biyu dai-dai na wannan dare, aka fito da yara biyu a nannade cikin zani. Daga ‘yan sandan har zuwa Sultan an rasa wanda ya riga wani isowa gun yaran..  Mikawa Abba yaran ta yi_, tana murmushi, “An ciro mace da namiji a cikin mahaifiyarsu. Sai dai yanzu za mu mayar da su, saboda yunwa ta fara lalata masu jiki. Ya yi wani irin yanayana alamun dai yunwa ce, don haka yanzu za a ci gaba da basu taimakon gaggawa. Sultan dai bai karbe su ba, amma kuma yana tsaye yana kallonsu daga hannun mahaifinsa. Doctor din ya Karaso ya ce yana son ganin Abba a office dinsa. Suna isowa ya dubi Abba ya ce, “Alhaji za a mayar da yaran domin kulawa da lafiyarsu , za kuma a bar mana ‘yan sanda a nan saboda kada mutanen da suka kasheta su sake dawowa kan yaran. Ita kuma idan Allah ya kaimu gobe sai mu bayar da gawarta. Allah ya jikanta ya raya marayun da ta bari.”Sultan da ke zaune ya hada kai da guiwa ya sharce hawayensa yana jin Kaunar da yake yi wa Saudat tana dawowa kan ‘ya’yanta, Yana ji a ransa Zai iya cikawa Saudat alKawarinta, ko da kuwa wannan shi ne aiki na Karshe da zai yi a duniya. Sai dai tarin damuwar rashin matar da a lokaci daya ta shiga ransa, ya kasa yunkurin barinsa ko taba yaran ya yi. “Me ya sa kuka yi  gaggawar kashe ta? Me ta yi maku? Anti Saudat! Me za ki gaya min? Me yasa Umma ta hana ni saurarenki? Wasu hawaye suka shiga kwararowa daga idanunsa. Sosai yake shessheKa. Mahaifinsa ya kamo shi suka nufi mota. Sai da ‘yan sandan nan suka raka Alhaji Lukman har gida kafin suka koma. A falo suka ci karo da Hajiya Salma. A cikin Kwayar idanunsu ta karanci saKonni kalakala da kai tsaye yake mata nuni da haushinta suke ji. Kawar da kanta ta yi kamar bata san suna yi ba. Sultan kuwa zama ya yi a Kasa idanunsa sun ki daina zubar da hawaye. Barci ke fizgarsa, dole ya wuce dakinsa ya yi wanka ya cire kayan da jini suka bata masa. Zoben nan da littafi da hotuna kuwa, ko kallonsu bai yi ba, ya cusa a cikin wani akwatinsa ya mayar ya rufe. Jallabryarsa ce a jikinsa har barci ya kwashe shi a nan, ba tare da ya tuna da addu’a ba. Alhaji Lukman ya mike da nufin duba dansa, cikin rashin sa’a idanunsa ya hadu da na �? Hajtya Salma. Dukkansu suka dauke kansu. Dakin Sultan ya shiga ya gyara masa kwanctyarsa tare da addu’a ya tofa masa. Ya  fito ya jawo masa Kofa. A falon ya sameta, zai wuce ta sha gabansa. “Me hakan ke nufi?�? Harara ya sakar mata, “Abinda zuciyarki ta gaya maki.�? Shiru ta danyi tana nazarin inda kalamansa suka nufa. “Kana nufin akan wata za ka juya min baya?�? “Eh idan har ta kasance abar halitta ce, kamarki zan yi abinda ya fi haka.�? Zamewa ya yi zai wuce sai kuma ya juyo, “Ki shirya zaman yaran da aka ciro daga cikin mazinaciya, ki shirya renon yaran da aka ciro daga jikin mai dauke da ciwon nan da ke karya garkuwar jiki. Haka ki shirya zama inuwa daya da yaran da uwarsu ta aro addininki kike yi mata gori.�? Kafin ta dawo daga doguwar sumar da ta yi, har ya shige dakinsa. Bata bishi ba, ta tsaya a falo tana faman kaiwa da komowa, “Wallahi! Babu wanda ya isa ya kawo min dan shege gida in rene shi. Ashe Alhaji ya dibo tashin hankalin da bana jin sauke shi zai yi masa sauki. Lallai a tsawon shekaru goma sha takwas da muka yi a tare, bai taba sanin wace ce, Salma ba, amma daga yau zan fito masa da asalin kalata.�? Dakin ta shiga. A kishingide ta same shi, yana karanta labarai a cikin wayarsa. “Ina son magana da kai.�? Hajiya Salma ta yi maganar cikin shan mur da nuna masa da gaske take, kuma tana nan akan bakanta. . “Kunne ke ji.�? Ya bata amsa ba tare da ya dago ya dubi inda take ba. Ta gyara tsayuwarta ta sake cika ta yi tam! Ta ce, “Kada ka dauko masifa da hannayenka ka kawo cikin gidanka, kayi tunanin zaman lafiya.�? Har yanzu bai dago ba kuma bashi da alamun dagowar. Ya ce, “Namiji ke da iko da gidansa, -shi ya sa aka halatta mana, mu je gidajenku neman aurenku, mu bada sadaki. Daga nan mu dauki nauyin ci da shan ku. Idan kuwa .har za ki iya shimfida doka a gidan mutumin da ke da ikon daga Kafafunsa ki shiga Aljannah, ina ganin da tuni an halatta maku ikon aurenmu, da kuma ikon mika sadaki.�? “Duk maganar da ka gadama ka gaya min a kan matar da baka sani ba. Amma sai ka fara gaya min wacce waina kake tunanin za a toya a  cikin gidan da ke dauke da shegu marasa addini?�? Sai yanzu ya dago kai yana dubanta fuskarsa dauke da murmushin da ke nuni da murmushin takaici yake yi. Ya ce “Wainar Kasa za a toya. Dagowa ta yi a fusace ta ce�? Sanin kanka ne wainar Kasa ba za ta taba ciwuwa ba.�? Tashi ya yi da wayarsa a hannu zai bar dakin, dai-dai saitinta ya tsaya yana yi mata duban kin bani mamaki, sannan ya _ ce, “Kin san ba zai ciwu ba kuma kike�? son ci? Kamar yadda kike tunanin wainar Kasa ba za ta ciwu ba, haka kema tsarin da kike son shimfidawa a gidan da ba mallakinki ba, ba abu bane mai yuwuwa ba. Don haka ki gyara wannan kuskuren da kike KoKarin tafkawa idan bahaka ba, zan auro wacce za ta iya tsayawa ta yi min rainon marayun nan, ta inganta min rayuwarsu, Kila a dalilin taimakon nan da zan yi inshiga Aljannah. Kada ki sake biyo ni idan ba haka ba, zanyi mummunar saba maki.�? Ya sa kai ya fice abinsa. Hajiya Salma da wani irin kishi ya cika mata zuciya, ta durkushe Kasa tana kuka. Haushin Sultan yafi yawa a zuciyarta, da bai kawo masu masifar nan ba, da babu abinda zai Sanyata sa’insa da mijin da take matuKar so kamar ta kashe kanta. Mutumin da ya ce baya sha’awar aure yau shi yake fadin zai Karo mata kishiya? Ita kuwa da ya Karo wata mace a gidan nan da sunan aure gara mala’ikan daukar rai yazo ya dauki ranta tun kafin zuwar ranar. Ta rasa menene mafita? Allah-Allah take yi gari ya waye, ta kira Yayanta Alhaji Mu’azu, domin shi kadai ya isa ya gayawa mijinta ya Ji. A wannan dare Alhaji Lukman ya kasa barci, sai juyi yake yana tunanin ta hanyar da ya kamata ya biyowa matarsa. Ya tsani abinda zai ° kawo masu rashin jituwa a_ tsakanin su. Washegari da sassafe ya wuce Asibitin, ya bada * kudi aka yi wa yaran siyayya, daga can yasa aka daukota akayi mata Sallah a Masallaci aka kaita gidanta na gaskiya. Alhaji Lukman ya kira Kanwarsa ya nemi taimakonta, Anti lyami, ita ta tsaya akan yaran har aka basu sallama suka kwaso zuwa gida. A lokacin Sultan ya dawo daga Makaranta dama kuma tun da ya tashi gaisuwa ce kawai ta hada shi da mahaifiyarsa,
haka yanzu din ma, gaishe ta ya yi ya nufi hanyar ficewa. Hannunsa ta jawo tana dubansa, “Yanzu Sultan akan bare kake fushi da ni? Insha wahala akanka amma yau da ni kake fushi? Kana son ka gama da duniyar nan lafiya kuwa? Abbanka ya yi min kaima kayi min?�? Jikin Sultan ya danyi sanyi, don haka ya bata hakuri kansa a Kasa, sannan ya wuce. Duk da haka dai yaki sakewa. Jin Sallamarsu yasa Sultan dawowa da baya ya kafe mahaifinsa da ~ idanu, haka ya kasa murnar ganin jariran kamar yadda kowa ya za ta. Anti Iyami ta zauna tana gaban mahaifinsa yana gaida shi. Abban ya mika masa da namijin ya ce, “Sultan ga amanar da ka dauka. Wadannan ‘ya’yan ka dauka cewa ‘ya’yanka ne. Namijin Nawfal, macen kuma Nasreen. Ina fatan ka san ma’anar Nasreen?�? Sultan ya daga masa kai ba tare da ya iya furta komai ba, haka kuma bai da alamun karbar yaron, kamar yadda mahaifinsa ya buKata. Anti Iyami ta mike tana murmushi, ta ajiye masa Nasreen a jikinsa, wacce take ta faman tsotson  hannu. Karbarta ya yi ya tsura mata idanunsa, yana son dole sai ya Kare mata kallo. Yarinyar bata da auki, amma kuma sambaleliyar mace ce. Yatsun Kafafunta ya kafe da ido gabansa yana fadi da Karfin gaske. Amma kuma ya rasa dalilin irin wannan faduwar gaban. A hankali ya yi magana wanda kaf falon babu wanda baiji ba, “Allah ya rayaku. Allah yasa ku yi wa addinin musulunci hidima.�? Sau tari Abba yana mamakin irin iya tsara magana da Sultan yake yi, wanda ko babba sai hakan. Hafsat da Haidar suka Karaso suna leKen yaran. Sai kuma suka dago suna duban Sultan, “Yaya Sultan Umma ce ta haife su?�? Hajiya Salma da dama jira take yi ta mike tsalam jikinta har kyarma yake yi. “In ji uban wa? Allah ka raba zuri’ata da haihuwar kwararo haihuwar titi, haihuwar KarKashin babbar mota! Wadannan yaran da kuke gani, shegune ake neman liKa mana tsiya.�? Abba ya mike jikinsa yana kyarma ya ajiye Nawfal ya daga hannu da nufin zabga mata mari, sai kuma ya dakata sakamakon muryar Sultan da ya ji ya ce, “A’a Abba!�? Hajiya Salma ta ware manyan idanunta tace, “What! Alhaji ni za ka mara a kan ‘ya’yan arna? Ni za ka mara akan ‘ya’yan ‘shegu?  TirKashi! Tun yanzu kenan suna cikin tsumma, ina kuma ga sun girma? Don Allah zo ka mare ni kada ka fasa. Kai kuma Sultan! Daga yau ka dauka cewa ni ba mahaifiyarka ba ce, ka je gun ubanka dake daure maka gindi ni na cire ka daga jerin ‘ya’yana.�? . Ta sa hannu ta finciko Haidar da Hafsat, ta ce, “Daga yau su Hafsa sune jinina ba kai ba Sultan. Na yafewa duniya kai. Yaran nan kuma sai sun koma inda suka fito indai ni ce Ummu Salma!�? Yaron ya zuba mata idanu kawai ba tare da ya iya furta komai ba. Haka bata ga ko alamun razana daga idanunsa ba. Abba ya dube ta jikinsa a sanyaye, domin baya son Salma tana yiwa ‘ya’yanta baki. “Salma�? Ki dauka cewa. Nasreen RUBUTACCIYA ce daga Allah. Haka Nawfal RUBUTACCE ne daga Allah. Tunda Allah ya rubuta za su fito daga cikin matacciya kuma a raye, bana jin ke Karamar alhaki zaki iya yi masu  abinda ba Allah ne ya rubuta ba. Sultan tashi mu je ciki.�? Iyami ta mike tana yiwa Salma kallon mamaki, amma ko a jikinta. Tare suka shige, Iyami ta yi masu wanka, ta sauya masu kaya, sannan ta dauko madarar su mai dauke da sinadare ta basu suka sha sosai. Sultan dai kafe yaran ya yi da ido, ya rasa mai ke masa dadi. Ji yake kamar bashi bane wani Sultan din aka aro. A zuciyarsa ya maimaita, RUBUTACCIYYA. Hakika mahaifinsa ya yi gaskiya. Anti Iyami ta koma gida ta bar Sultan da yaran. Dole ya naimi taimakon Mairo mai aikinsu, don haka ne take taya shi kula da yaran. Hajiya Salma ce da Alhaji Mu’azzam_ babban wansu. wanda shi yake matsayin kamar mahaifinta, tunda shi ya raineta tun suna Kanana. �? Malami ne sosai, haka bai taba sa doka ankarya masa dokarsa ba. Kusan halayyarsa guda da hajiya Salma, gashi dai yana da sani a addini sosail, amma kowa yasan mutum ne mai akida. Kowa tsoronsa yake ji. Alhaji Mu’azzam ya dubi Alhaji Lukman ya ce, “Wai da gaske ka kawo ‘ya’yan shegu cikin gidanka?�? Alhaji Lukman ya hada rai sosai, “Na kawo marayu gidana, ba ‘ya’yan shegu ba ne. Ina kuma roKonka da kayi amfani da sanin da Allah ya yi maka, kayi adalci. Ya zama dole ko kare na kawo gidana Hajiya ta girmama min. Bai kamata ina fada tana fada ba.�? Alhaji Mu’azzam ya mike yana dubansa, “Gaskiya na raina wayonka Alhaji Lukman, da girmanka da darajarka a idon duniya za ka je ka kawowa kanka masifa? Matarka tana KoKarin dawo da kai hanya, amma ka zama makaho? To ka sani, babu ruwana da mazinaci ma, ni idan na �? ganshi zann iya kashe shi, ba na yiwa mazinaci uzuri. Bare kuma a kai ga cikin shege. An ce fa tsintar uwar ka yi. Ka canza tunani zan sake dawowa.�? Ya mike ya fice abinsa. Alhaji Lukman ya bi shi da ido, yasan za a rina, Sai dai yana jin ko mahaifiyarsa ba za ta hana shi taimako ba, bare yayan matarsa. Karin Jin dadinsa ma, da Hajiyarsa ta nuna masa goyon bayanta akan renon yaran. Haka kowa ya bar   gidan zuciyoyi babu dadi. Shi kuwa Sultan Makaranta kadai ke raba shi da yaran. Kullum yakan tasa su a gaba ya yi ta kallonsu kamar mai son gano wani abu. Mahaifiyarsa bata shiga sabgarsa, haka ta hana Kannensa shiga huruminsa, idan ya gaishe ta bata amsawa, shi kuma bai fasa ba. Hajiya Salma ta sauke wayar da ta gama yi da Kawarta Hajiya Ladidi ta kuma yi na’am da shawarar da Kawarta ta bata. Don haka ne ta sami Alhaji da ke zaune yana duba Jarida fuskar nan babu fara’a ta nemi wuri ta zauna, “Alhaji ka ~ yi hakuri ka yafe min, na tuba. Fushinka yana daga min hankali. Na amince ‘yan biyu su zauna �? a gidana, amma da sharadi.�? Alhaji Lukman ya dube ta da fara’a sosai a fuskarsa domin shi kansa ya yi kewar matarsa. “Ina jinki fadi sharadin.�? Muskutawa ta yi tana murmushin mugunta, “Sharadina ba zan tsaya kulawa da yaran ba, ka ga kasuwancina ma ba zai barni ba, sai dai a Karo masu kula da yaran, ni zan dinga biyan ma’aikatan domin bada gudumawata. Shi kuma Sultan ina son in nuna masa kuskurensa na  gujewa maganar mahaifiyarsa. Don Allah ka bar ni a hakan mu shirya kanmu.�? Alhaji Lukman ya dubi matarsa, yana jinjina ita mace har tsufanta da yarinta a ciki. Don haka babu dogon tunani ya ce ya amince, ya kuma ji dadi da har Hajiya za ta iya bada gudumawarta wajen kawo masu aiki. Miji da mata sai Allah, a nan suka shirya kansu. Babban damuwar Sultan a yanzu bai wuce yadda mahaifiyarsa ta nunawa Kannensa Sultan a matsayin maKiyinta ba. Yanzu Kannansa bayan gaisuwa basa shiga huruminsa. Yau Asabar bayan ya tafi wurin motsa jika ya wuce Islamiyya daga nan, da _ yake Islamiyyarsu ba daya ba ne da Kannansa, don haka ya dawo gida ya zauna daga farfajiyar gidan ya kurawa Kasa idanu yana kallo. Ya rasa tunanin me yake yi, kunnuwansa suka jiyo masa kukan jariran. Tashi ya yi ya nufi dakin renonsu, a nan ya sami Haidar da Hafsat da bulalai suna tsulawa jariran nan. Babu kowa akansu, hakan ya tashi hankalin Sultan ya jawo su, ya yi masu  wani irin mugun duka, wanda ya dasa masu *

BOOK 1

            CHAPTER 3

      *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*

*Wannan littafin na kudine idan kina bukata kiyi magana ta wannan number 09068032427*

A JIYA MUN TSAYA

Yau Asabar bayan ya tafi wurin motsa jika ya wuce Islamiyya daga nan, da _ yake Islamiyyarsu ba daya ba ne da Kannansa, don haka ya dawo gida ya zauna daga farfajiyar gidan ya kurawa Kasa idanu yana kallo. Ya rasa tunanin me yake yi, kunnuwansa suka jiyo masa kukan jariran. Tashi ya yi ya nufi dakin renonsu, a nan ya sami Haidar da Hafsat da bulalai suna tsulawa jariran nan. Babu kowa akansu, hakan ya tashi hankalin Sultan ya jawo su, ya yi masu  wani irin mugun duka, wanda ya dasa masu

ZAMU TASHI

soron shi fiye da tunanin su, kasancewar bai taba kai hannu jikinsu ba. . Hajiya Salma ta fito a gujen gaske tana ganin abinda ya faru, ta sa Salati da Karfi tare da dafe Kirji. Tana Karasowa ta dauke shi da mari. Ya rike fuskarsa zuciya tana wani irin cinsa. Ji yake kamar dukan da ya yi masu bai gamsar da shi ba, yana jin zai iya aikata komai akan yaran da ya Kwallafa ransa a kansu. Sultan ya juya kawai zai tafi, Umma ta sake fizgo shi, “Zo nan shugaban marasa imani, ba ka isa ka tafi  ba, sai ka kashe su. Zo ka kashe su, ka fita duniya ka gaya masu ka nakasa Kannenka saboda ‘ya’yan shegu.�?

Sultan dai bai ce komai ba, har ta gama  masifarta ta fice da yaranta. Shi kuma ya fice yana Kwalawa masu kula da yaran kira. Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, sau tari suna mamakin yaro Karami ya tsaya yana basu manyan dokoki. Su dai sai hakuri suke bashi. Ya karisa ya dauki naufal yan girgizashi ya bashi madara Yasa bakinsa a kunnensa yana masa addu’a har barci ya kwashe shi. Nasreen dai ta ki __ yin shiru sai kuka take tsalawa. Ya karbeta yana

kallonta. Yadda ta bude idanunta tana kallon Sultan ya sa ya yi murmushi, “Ke sarkin kuka. Ke ragguwa ce ko? Oya yi min shiru ko in zane dan bakin nan.�? Cikin ikon Allah ta yi shirun, haka idanunta Kyar akansa. Hajiya Salma ce zaune da Hajiya Ladidi suna tattaunawa, “Wato ni abinda ke damuna, macen nan da aka Haifa. Tana iya girma ta zame mani matsala, Kila daga Karshe ta biyo halin uwarta na bin maza. Gara namijin bana jin akwai wata matsala da zai bani. Don haka ne nake neman shawararki yadda za a yi inbatar da Nasreen daga duniyar gaba daya.�? Hajiya Ladidi ta numfasa, “Maganarki gaskiya ce. Ai ina ganin ki ba su Rainbow aikin nan a kwana daya za su kashe kayan banza su watsar.�? Hajiya Salma ta yi na’am da wannan shawarar, don haka ta hadata da Rainbow ta gaya masu yadda take so. Cikin dare, Sultan ya idar da Sallar dare, haka kawai yake jin ba zai iya barci ba, idan har bai je yaga ‘yan biyu ba. A hankali ya fito yana takawa har ya iso dakinsu. A lokacin Rainbow ya shigo jin motsin Sultan yasa ya makale a gefe yana kallon ikon Allah.  Nasreen ce idonta biyu, shi kuwa Nawfal sai shaikan barcinsa yake yi. Sumbatar yaron ya yl ya sake tofe shi da addu’a. Nasreen kuma ya dauketa yana dubanta. “Abba ya ce ke RUBUTACCIYA ce, zai yi wahala mai nemanki da sharri ya same ki.�? . : Dauketa ya yi ya nufi dakinsa da ita yana jijjigata. Akan Kirjinsa ya kwantar da ita yana bubbuga bayanta har barci ‘ya sureta. A Kalla Rainbow ya kwatanta zuwa gidan yafi a Kirga, amma samun ko taba jikinta ya gagara, domin kullum yazo sai ya sami Sultan a tare da su. Wannan abu shi ya Karawa Umma jin tsanar Sultan a zuciyarta, kuma ta yi alKawarin indai ita ce sai taga bayan Nasreen. Shi kansa Abba yanzu hidimomin fice-ficensa sun sanya shi a gaba, don hakane baya samun wani cikakken zama Babu abinda zai baka mamaki sai yadda yaran suka yi bulbul suka yi wayo. Kullum kyawun yaran gai sake fitowa yake yi. Suna samun kulawa sosai daga Sultan, haka yaran sun yi wata shaKkuwa da Sultan har suna iya gane shi  da zarar yazo wurin su. Rashin jituwa tana sake kusanto shi da mahaifiyarsa. �? “Yau gaba daya suna zazzaune a falo suna cin abinci. Abba ya dubi Sultan ya ce, “Yanzu sai makarantar likitoci ko?�? Sultan ya girgiza kai, “A’a Abba na sauya ra’ayi Dan sanda nake son inzama.�? Umma ta dafe Kirji da Karfi, “Yau na shiga uku! Dan sanda a gidana? Wai me yake damun Kwakwalwarka ne? To ba ka isa ka zama dan sanda a wannan gidan ba. Yadda na tsani dan sanda Wallahi ba ka isa ba.�? Abba ya kurbi ruwan shayinsa yace, “Oh me kuma dan sanda ya yi maki? Ke kin huta komai baki so.�? Ya Karashe da yi mata gatse, Ta hada rai ta ce, “Ni dai na gama magana.�? Sultan da kansa ke Kasa ya dago ya ce, ““Abba dan sandan nake son inzama insha Allahu. Umma ki sa min albarka kawai.�? Umma ta sake zabura kamar za ta kai masa duka, “‘Albarkar wa? Ba zan sa ba shegen yaro kafaffe. Kaje indai dan sanda ne nawa ido.�? Abu kamar wasa har sai da maganar ta iso gun Hajiya Gwaggo, wanda ta yi mata fada sosai, ta kuma tursasata sai da tasa masa albarka  Mutane da yawa suna kallon Sultan a matsayin wani miskili wanda bai damu da magana ba, amma kuma idan ka same shi a cikin su Nasreen ya cika masu daki da kayan wasa, sai kayi ta mamaki kana cewa anya Sultan ne kuwa? A guje ta fito da ‘yar bebinta, kai tsaye jikin Sultan ta fada tana KyalKyaltan dariya. Sultan bai tabata ba, ya tsaya yana kallon wanda ya sa Nasreen irin wannan dariyar. Nawfal shima ya fito aguje yana bude haKoransa. Gaba daya gaban Sultan suka tsaya suna haki. Kamar ba zai yi masu magana ba, kasancewar bai jima da dawowa aiki ba, kuma ya gaji da yawa, amma dole ya amsa masu yana murmushi, “Me ya same ku kuke dariya haka?�? Nasreen ta dube shi da idanunta kamar madara, ta ce, “Dee ni zan fara gaya maka, Bros Nawfal ne ya biyo ni zai dakeni. Shi ne Anti Hafsa ta biyo mu da bulala za tayi mana dukan gaske.�? Fitowar hafsat a fusace yasa duk suka bita da kallo. Tana ganin Sultan jikinta ya yi sanyi ta koma da baya har tana tuntube. Nasreen ta shige jikin Sultan tana Boye kanta. Sultan ya dagota ya zuba mata ido  kanta ya sha gyara da Kananun ribom masu kyau. Kurawa Kafafunta idanu ya yi gabansa yana ci gaba da fadiwa da Karfi.

« BAYAN WASU SHEKARU

Doguwar yarinya ce, mai yalwataccen gashin kai wanda ya taho tun daga goshinta har zuwa bayanta. Tana da saje irin na mata wanda yake nuni da alamun yarinyar tana da gashi. Ba fara ba ce kai tsaye kana kallonta za ka kira ta mai kalar choculate. Duk da hasken ya rinjayi duhun. Ko alama ba ta da jiki, siririya ce wanda sirrancin ya yi matuKar yi mata kyau kasancewar ba ta da rama. Kugunta a dan bude suke, haka daga samanta Allah ya wadata dukiyar na Fulani. Har yanzu akwai yarinta a tare da_ ita, kasancewar shekarunta ba za su wuce sha shida ba a duniya. Tana da sassanyar kyau, haka da za a shiga gasar kyawawa da ita, babu abinda zai hana ta cinyewa, Muryarta ta cika sanyi da yawa, haka komai take yi a sanyaye take yinsa, kamar wacce ba ta dauke da kayan ciki. Fuskarta kullum dauke yake da murmushi ko da kuwa kuka take yi, sai ka hango murmushin nan. Sanye take da kayan Makaranta mai kalar blue hijabinta kuma fari tas! Shigowar Sultan yasa ta Karaso kusa da shi tana mika masa hannayenta, “Dee ka taimaka ka cire min abin hannun nan kada a Kwace min a Makaranta.�? Kafe ta ya yi da idanu yana tuna wasu abubuwa, sal kuma ya kama tsintsiyar hannun yana kokarin cire mata. Cikin sa’a ya dago kansa ita kanta shi ta kafe da idanu tana kallon sa. Manyan idanunta suka hade da nasa masu yawan lumshewa. Gaba daya suka sakarwa .. kansu murmushi, ‘sannan ya cire mata. “Lazy baby, ki yi sauri ni zan ajiye ku in wuce office.�? Marairaicewa ta yi , “Ayyah Dee, Kila ma kai kayi min baki shi ya sa har yanzu nake Lazy.�? Murmushi ya yi ya dauki jakar makarantarta suka fito. Umma ta dube shi ta riqe baki, “Oh wani sabon gulmar ce kuma yau Za ka rike mata jaka? Kullum da sabon salon iskancin da yarinyar nan take dauke da shi.�? Wucewa tayi . Sultan suka kalli juna da Nasreen sai duk suka basar.  Sultan zai tafi kwas wanda za a Kara masa girma, sai dai wannan ne karo na kusan hudu yana soke tafiya kwas dinsa sabod su Nasreen. Amma a yanzu tunda sun girma za su iya yin komai da kansu, yana da buKatar tafiya. Yafi tausayawa Nasreen da ta dora shaKuwar duniyar nan akan Sultan. Haka ya dinga shirye-shirye jikinsa babu Kwari. Nasreen ta shigo dakin ta dube shi ta ce, “Dee in kawo maka Assignment dina ka taya ni dubawa ko nayi dai-dai?�? = Dubanta yake yi kamar yau ya fara ganin ta, “Nasreen kin ga na gaji da yawa, ki bari sai ~ an jima ko?�? Gyada kanta ta yi tana duban yadda yake shirya kaya, “Dee ina za ka je da kayan nan? Na san ba za ka tafi ka bar ni da Umma ba ko? Umma ba ta sonmu ni da Nawfal, ban san me muka yi mata ba. Dee me muka yi mata?�? Shafar gefen sajenta ya yi yana KirKiro murmushi, “Babu abinda kuka yi mata, tana son baku tarbiyya mai kyau ne, Tana sonku kun ji? Ko kin taba ganin inda uwa ta tsani ‘ya�? yanta?�?  Nasreen ta yi narai-narai da idanun dake firgita “yan maza ta ce, “Ai ta ce ba ita ta haife mu ba, wai mu a Karkashin gada aka same Sultan da ya ji gabansa ya fadi, ya mike jikinsa har yana kyarma. Kai tsaye falon mahaifinsa ya nufa, wanda yake zaune da Umma. Ya dube su ransa a matuKar bace ya ce, “Umma don girman Allah ki daina cewa yaran nan bake kika haife su ba, har kina gaya masu daga inda suka fito. Yaran nan ba su san komai ba, bai kamata ana yi masu hakan ba.�? Abba ya dube shi cike da mamaki, haka ya dawo da kallonsa gun Hajiya Salma tare da ware ~ idanu, “Salma! Kina nufin duk irin gargadin da nayi maki baki ji ba kenan? Me ya sa za ki dubi yara Kanana kina gaya masu irin wannan maganar?�? Hajiya Salma ta dinga auna wa Sultan harara, ta kuma hada rai ta Ki yin magana. Haka Sultan yasa kai ya fice ransa a bace. Alhaji Lukman ya mike yana dubanta ya fice ya bi bayan Sultan. Sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba. Sultan dai ya bar garin zuwa Enugu, ba tare da wata matsala ba. Haka ya jaddada amanar Nasreen a gurin Mairo ya fi a Kirga. Da zai tafi yaran suka yi masa layi kowannensu ya yi tagumi. Gabadaya ji yake ya karaya. Ya sa hannu ya yafito su duk suka Karaso gabansa yana dubansu. “Nawfal, Nasreen ba za ku yi min dariya ba?�? « , Dukkansu suka fidda murmushi wanda kallo daya za ka yi masu ka fahimci iyakarsa fuska. Shafa kansu ya yi ba tare da ya iya furta komai ba, direba ya ja motar suka fice. Rintse idanunsa ya yi da Karfi yana jin gabansa yana tsananta fadiwa. Ji yake kamar ba zai dawo ya same su da rai ba. Hajiya Salma ta gama leka ko’ina ta tabbatar da babu Abba a gidan, hakan ya sa ta jawo Nasreen da Karfin tsiya ta fesa mata wani abu a cikin idanunta. Yarinyar ta sanya Kara mai Karfi, ta fadi tana shure-shure. Nawfal ya Karaso da gudu ya tallafo ta yana Kwala mata kira. Nasreen tana kuka Nawfal yana kuka, gaba daya an rasa wanda zai lallashi wani  Nawfal ya dago ya zuba wa Hajiya idanu, yana jin haushinta da tsanarta a cikin ransa. Ko da yake yaron yana da tabbacin Umma bata kaunarsu. Yana kallon yadda su Haidar suke kwasar dariya. Hafsa ta ce, “Shegiya ba kina taKama da idanunki ba ne? To an nakasa su sai mu ga wani abin yangar.�? Haka suka wuce suka barsu cikin kuka. Ita kuwa Nasreen saboda azaba a take ta suma. Umma ta sake dawowa, ta damki wuyar rigar Nawfal ta ce, “Wallahi kuka sake kuka fadawa waml Wai ni ce nay mata wani abun, sai na kashe ka Nawfal ya gyada kansa yana ci gaba da hayyacinsa saboda kuka. Cikin ikon Allah sai ga Abba ya dawo, kai tsaye ya nufi yaran don ya duba su. Haka yana son ya cika alKawarin da ya daukarwa Sultan zai hada shi da su. Ganinta a kwance bata motsi ya daga hankalinsa. Bai tsaya bin ba’asi ba, ya dauketa sai asibiti. Yana nan tsaye ya kasa zaune saboda tunanin mai ya sami Nasreen haka? Ya fi Karfafa zarginsa akan Hajiya Salma, idan kuwa ita ce,  babu shakka zai ya sakinta ta koma gidan su. Kiran wayar Sultan na biyar kenan, yana kasa dauka. Dole yasa wayar a kunne yana cewa, “Sultan ban iso gidan bane. Ka kwantar da hankalinka ina isowa zan hadaka da yaranka.�? Sultan ya cika da mamakin mutumin da ya ce masa yana kusa da gida, yanzu kuma zai ce bat iso ba. “Abba fa ka ce min kana kusa da gida, yanzu kuma ka ce baka iso ba. Abba ko dai da matsala ce?�? Jikin Abba ya yi sanyi, yau ya yi wa dansa karya har ya kama shi, “Ka yi haKuri Sultan babu matsalar komai, har na kusa gida aka sake ~kirana, wani abokin mu bai da lafiya shi ne yanzu na iso asibitin.�? Dole Sultan ya ajiye wayar yana ci gaba da saKe-sake. Lambar mahaifiyarsa ya kira, tana kallo ta Ki dauka gabanta yana fadi kada Nasreen ta farka ta ambaci sunanta. Da kiran Sultan ya yi yawa ta dauka cikin daga murya ta ce, “Wai menene haka kamar kana bi na bashi?””“Umma don Allah ki taimaka ki hada ni . da su Nasreen, Abba ya ce bai iso gida ba.�?  “Umma taja dogon tsaki, “To ba zan hada ka da su din ba. Ka ga Sultan? Ka kiyaye ni! Idan ba haka ba, ni na san yadda zan yi da kai. Kada ka sake kirana.�? Kawai sai ta kashe kiran. Wayarsa yabi da kallo yana jin kashe wayar har tsakiyar kansa. Ya kasa jure rashin jin muryar yaran, don haka ne ya ci gaba da jin damuwa da bacinrai. _  Likitocin suka fito suka bukaci Abba da ya biyo su Office. A nan suka yi masa bayanin wani Chemical aka zuba mata a idanun, a sakamakon hakan da wahala ta sake gani da idanunta, sai kuma-_wani ikon Allah. Abba ya yi suman zaune. A yanzu me zai iya gayawa dansa? Dakin da Nasreen take zaune ya shigo yana dubanta, “Nasreen.�? Lalube take yi tana fadin “Na’am Abba. Me ya sa bana ganinka? Abba ina Nawfal? Shi ma ba zan iya ganinsa ba? Abba ka bude min idanuna ina son inganka. Abba idanuna har yanzu Zafi suke yi min.�? Hawaye mai dumi ya biyo idanun Abba. Zuciyarsa ta karye, ba shi da wani Karfin guiwa. Zama ya yi kusa da ita ya kamo ta, ya mayar da  ita jikinsa, ‘“Nasreen dina. Wannan Kaddararkice, haka komai za a yi maki insha Allahu sai kin kai labari, domin ke RUBUTACCIYA ce, wanda Allah ya rubuta sai kin sha ruwa a duniyar nan. Ciwo kika ji za ki warke har ma ki fara gani da idanunki kin ji? Yanzu gaya min waye ya watsa maki abu a cikin idanu?�? Nasreen da ta gigice ta hau girgiza kai “Ni ma bansan waye ba Abba: Ka kai ni wajen Dee in nuna masa idanuna, bana ganin kowa sai duhu.�?  Wannan karon kalaman bakin Abba sun Kare, dole ya koma kamar kurma. Satinta guda a asibitin, kullum Abba ke kulawa da ita, haka ya Ki yin magana ne yana jiran a sallamota. Nawfal da Mairo mai aiki suke zaman kulawa da ita. Ranar da aka sallame su, suka tattaro suka dawo gida. A bakin Gate suka sami Nawfal kusa da mai gadi ya zauna ya yl shiru, kasancewar a ranar Abba ya hana shi zuwa ya ce ya bari kawai yau za su dawo da Nasreen din. Yana ganinsu ya taso ya Karaso da saurinsa kamar zai kifa. Ganin Nasreen tana lalube yasa Nawfal kafe ta da idanu. Abba ya jawo Nawfal yayi masa dabarar duniyar nan amma ya Ki fadin wanda ya yi wa Nasreen wannan aikin. A tunanin Nawfal da gaske Abba yake yl, yau Nasreen za ta fara gani da idanunta, kafe ta ya yi da idanu, zuciyarsa tana gaya masa Nasreen ta tabbata makauniya.Sai kawai ya hau kuka mai tsanani yana tausayawa ‘yar uwarsa. Abba ya dubi wayarsa yana kallon kiran Sultan, ya dubi yaran ya ce, “Ga Daddynku zai yi magana da ku, idan kun dauka ku tabbatar masa kuna lafiya kun ji? Idan ya san abinda ya faru zai fasa aikinsa ya dawo nan, ku bari har ya gama sai ya dawo sai ya gani. Nasreen ke kuma insha Allahu zamu nemo maki magani ‘har ki warke.”Dukka yaran suka amsa masa. Da kansa ya kira Sultan ya mika wa Nawfal. Muryar Nawfal da yaji yasa ya saki ajiyar zuciya, suka gaisa da yaron yana masa ‘yan tambayoyi. Daga bisani ya ce, a baiwa Nasreen. Cikin Shagwababbiyar muryarta ta ce, “Dee…�? Sai �? kuma_ tayi shiru. Siririyar muryarta ta ci nasarar tsinka masa zuciya, “Nasreen kin ‘yi kuka, Nawfal ma ya yi kuka, gaya min waye ya

*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA’ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427**

BOOK 1

            CHAPTER 5

         *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*

*Wannan littafin na kudine idan kina bukata kiyi magana ta wannan number 09068032427*

A JIYA MUN TSAYA

Ruwanku ne Hafsat da Haidar subi bayanta, sai dai ku sani irin naku rashin hankalin yafi kama da na uwar da ta haifeku, don haka binta zai fi burgeni fiye da zamanku a nan.�? Ya sa kai ya fice a fusace. Nasreen tasa kuka, wanda ya jawo hankalin Alhaji Mu’azzam kansu. Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da shi wanda bai taba jin irinsa ba. Bai taba ganin yaran ba, saboda irin tsanar da ya yi masu, sai yau da ya hada idanu da su. Bakinsa ya mutu murus, dole ya nemi wuri ya zauna, yana kallon yadda Hajiya Salma take kuka, Duk wanda ya san meke faruwa zai gane kukan korarta da Alhaji ya yi take yi. “Salma ki yi haKuri ki share hawayenki, ki zauna da ‘ya’yanki, Kada ki yarda akan ‘yar Karamar matsala ki baro dakin mijinki. Ni zan san matakin dauka haka zan lalubo inji wacce yarinya ce ya aura ma danki, Ki kwanter da hankalinki.�?

ZAMU TASHI

Daman ko bai ce ba, Hajiya Salma ba za ta iya tafiya ko nan da can ba. Don haka suka yi Sallama ya fice. Nasreen ta sa sandarta a Kasa tana KoKarin ficewa tun kafin fushinta ya sauka akansu. Nawfal ya rike mata sandar suka fice. Yau Sultan ya dawo garin, yana shaKar iskar garin Kaduna ya ji wata natsuwa tana shigarsa. Yana farin ciki yau zai ga twins dinsa. Mota tana yin parking a lokacin mahaifinsa ya fito zai fice. Farin ciki ya kama mahaifinsa, duk da sai da gabansa ya fadi. Rungume juna suka yi cike da farin ciki, haka yana nan a tsaye yana amsa gaisuwar ma’aikatan gidan. Daga nesa ya hangota fuskar nan dauke da farin ciki, tana rike da

sandarta tana laluben hanya. Nawfal ya Karaso wurinta ya rike mata sandar yana cewa, “Idan na gadama insakar maki sandar inrigaki zuwa inyi masa oyoyo. Nasreen ta yi dariya, ta ce, “Ai nasan ba za ka yi min haka ba.�? Sultan yana magana da mahaifinsa ya kasa Karasa abinda yake fada ya kafeta da ido babu ko kiftawa. Ya rasa wannan wani irin wasan kwaikwayo ne haka? Abbansa yabi inda yake kallo.da kallo, ba tare da ya furta komai ba.  Nasreen tana Karasowa ta saki sandar ta ce, “Didina ka kama hannuna intabbatar da kai ne.�? Sultan ya kasa yin motsi sai kallonta kawai yake yi. A zatonsa wasa take yi, amma yanzu ya tabbatar da babu wasa a lamarin nan. Nawfal ya kama hannun Sultan yana cewa, “Didi sannu da zuwa. Na riga wata yarinya rike hannun Didi.�? �? Nasreen ta saki dariya ta ce, “Babu damuwa zan rama watarana.�? A lokacin ta sami daman rike hannunsa kawai ta rungume shi. Hawaye suna sauka daga idanunta zuwa bayansa. Yana jin digar hawayen hakan yasa ya dan rintse idanu ya ware su da Karfin gaske. A lokacin ne Hafsat da Haidar suka fito. “Sannu da zuwa Yaya.�? Su kansu bai amsa masu “ba, hakan yasa suka tsaya suna duban yadda ya yi kamar wanda ya mutu a tsaye. Da gaske ya rasa me zai ce, wacce tambaya ya kamata ya fara yi, kuma idan zai yi din wa zai wa? “Abba Nasreen ta daina gani ne?�? Wannan ‘tambayar ce ta Kwace masa da karfin gaske ta : fizzo kanta ta samu ta fito. Abba ya girgiza kai, “Nasreen bata ganin komai. Kaddara ce ta Ssameta, muna fatan mu samu mu cinye. Ku zo   mu shiga ciki.�? Hannunsa daya yasa ya dan shafi bayanta kafin ya dagota daga kwancen da take, yasa hannu ya dauke mata hawayen idanunta, sannan ya riKe hannunta suka shiga ciki Har yanzu jikinsa a sanyaye yake haka ya kasa gazgata abinda ya gani. Dakinsa ya shiga ya kintsa sannan ya fito falon ya iso har gaban mahaifiyarsa ya duka ya gaidata. Ita kanta Hajiya Salma ta sani, kaf cikin ‘ya’yanta babu mai biyayyar Sultan, sai dai wani ra’ayi nata da yasa take jin haushin abinda yake aikatawa. A hargitse ya yi maganar da yasa kowa yake kallonsa, “Abba ashe ba zan iya barin amana a rike min ba? Waye zai aikatawa Nasreen irin wannan mugun abun? Nasreen ta makance amma ba a taba gaya min ba? Ko waye ya aikata mata wannan abun ba zan taba daga masa Kafafu ba.�? Ya ajiye maganar ba yadda ya kamata ba. Nasreen ta Karaso tana lalube har ta iso gabansa, “Dee, wanda ya aikata min hakan ya fi kowa sanin dalilin da yasa ya yi min. Kuma ni na yafe ma wanda ya yi hakan, Kada bakin ciki yasa ka furta wasu kalaman da suka cika yin nauyi. Kayi haKuri kamar yadda Abba ya ce min  inkarbi Kaddarata haka kaima ya kamata kayi. Ni bana jin damuwa, ina gode wa Allah a yadda ya �? bar ni. Idan kuma kace za ka dauki mataki bansan wurin wa za ka je daukar matakin ba, domin nima bansan wanda ya aikata min hakan ba.�? Sultan ya dubeta yana jin zuciyarsa tana yi masa wani zafi. Yana kallon manyan idanun nan masu tsari yau sunée a rufe bata gani da su. “Nasreen zan yi bincike zan kuma dauki mataki kamar yadda na fada. Bincike biyu ke gabana kuma Insha Allahu duk sai na aikata su. Duk wanda ya aikata maki hakan babu ko shakka zai iya yin kisan kai.�? Hajiya Salma ta yi maza ta tari numfashinta, domin Sultan gaf yake da zageta, “A’a ya isheni haka. Idan ka tashi yin binciken sai ka hado da ubanka domin shima a gidan ya kwana, ko kuma duk ka kama mu ka rufe har sai ka gama binciken. Idan za ka wuce kaje ka ci abincinka ka wuce, idan kuma tsayawa za ka yi ka samu a gaba kana yi mana tambayoyin rainin hankali Bismillah.�? Sultan ya duKar da kansa-ba tare da ya iya furta komai ba. Abbansa ya dafa shi, “Sultan, ka yi haKuri, kullum da Nasreen  nake kwana da ita nake tashi a zuciyata. Na rasa gano wanda ya yi wannan aikin. Ka je kayi bincikenka, nima idan na kama wanda ya aikata min wannan aikin insha Allahu zan tsaya sai naga anhukunta shi, ko wanene kuwa. Haka kaima ka dauki mataki, tunda a lokacin da za ka fara aiki, sai da kayi alkawarin tsayawa akan gaskiyarka, ko da kuwa ni mahaifinka ni ka kama da irin wannan laifin, don Allah ka dauki mataki kada ka ragawa mutum. Idan kayi hakan zan san dana ya tabbata a cikin dan sandan mai amana da gaskiya. Allah ya yi maka albarka. Zan �? bayyana maka matarka da zarar ta kammala Makarantarta, wanda bana jin za ta dauki lokaci, domin tana shekararta ta Karshe ne. Tashi kaje ka ci abincin.�? Sultan ya dan sami natsuwa da kalaman mahaifinsa, kafin ya tashi Nasreen ta fara tashi, tana lalube saura Kiris ta fadi ya Kwala mata kira, “Nasreen! Tsaya.”�? Babu musu ta tsaya ya Karaso ya kama mata sandar suka fice. Hankalin Hajiya Salma idan ya yi dubu to ya tashi, Sai taga kamar da Nasreen ta makancen sai abin yafi sake yin muni, Hankalinta ya Kara tashi ne da Hajiya Ladidi ta tabbatar mata, tunda  anyiwa danta aure, to Alhajin ne da kansa zai auri Nasreen din, domin kuwa shi namiji bashi da kunya. Zai reni abu ya kuma aureta. Hauka ne kawai Hajiya Salma ba ta yi ba, domin ita ta kasance mace mai zafin kishi, akan Alhaji Lukman za. ta iya kashe rai. Sultan ya tashi hankalinta Kwarai akan maganar binciken da ya ce, zai yi domin kuwa kallonsa take yi a matsayin mayen ‘yan sanda. A _ dalilin Kwarewarsa yasa ake ta Kara masa girma. Dole ta yi yunkurin daukar mataki akan abubuwan nan tun kafin tana ji tana gani danta ya garkameta a Police Station ‘yan jaridu su sami daman watsata a duniya. Haidar ta aika ya kirawo mata Sultan yana shigowa ta dube shi sosai. “Kana jina? Idan na sake jin ka sami ‘yan aiki kana yi masu bincike ko Kannanka ban yafe maka ba. Nasreen wani Kato ya shigo ya rufe mata baki ba mu ji ba, ya yi mata wannan abin. Kai baka yarda da Kaddara ne? Kai ka sani ko mugayen da suka kashe mahaifiyarta ne suka gane akwai yaran a gidan nan? Ni shi ya sa tun farko ban so rikon su ya zamana a nan ba. Bana  son kaje garin tone-tonenka ka jawo mana masifa har cikin gida.�? Sultan ya zubawa mahaifiyarsa idanu kamar mai son gano wani abu. Hankalinta ya Kara tashi ta ce, “Laaahh! Ni kake kallo haka kamar ka sami barauniya? To tashi ka wuce na gama magana. Bai ce komai ba, bai kuma tashin ba. Can ya nisa ya ce, “Umma wai har cikin dakinta aka shiga aka aikata hakan duk baku sani ba? A lokacin kina…�? A zafafe ta ce, “Ina dakin ubanka ne a lokacin. Ingama ce maka ka bar maganar nan amma kuma saboda tsaurin idanu za ka koma yi min tambayoyi? Sultan wai yaushe ka sauya ne? . Zuwan yaran nan rayuwarka sun sauya mun dana. Yauwa Sultan wai wacece matarka? Na yi bincike sosai antabbatar min ba ‘yar gidan Alhaji Mamman ba ce. Anya ya kamata ka amshi auren nan kuwa? Bana son yazo baka yi sa’ar mata ba, dan nuna min ita ko a hoto ne.�? A lokaci guda bayan ta gama masifar ta yi Kasa da muryarta kamar mai rada. Sultan da ya gaji da tsugunnon da yake, ya jawo wata ‘yar kujera ya zauna yana  fuskantar mahaifiyarsa, bayan ya dauki dabino | daya ya Sa a bakinsa. “Umma ban santa ba, ban taba ganinta ba, ban san sunanta ba, haka ban san ko ‘yar gidan waye ba. Kasan da ta tafi karatun ma ban san shi ba. Kawai abinda nake buKata addu’a Umma. Idan kika yi min hakan kin gama yi min komai. Kuma insha Ailehu zanyi maku biyayya wajen karbar zabinku.�? Umma ta Harare shi, “Wajen karbar zabin mahaifinka ko kuma zabina? Ni zabin da na ‘baka ka karba ne? Ina son ka bude kunnunwanka da kyau ka ji ni. Ka je ka sami mahaifinka kace sai ya hadaka da matarka ko gaisawa ce ku dinga _ yi. Ya zama dole musan wacece da me za ta shigo gidan. Idan ba ta yi ba, sai ka botsare masa ka saketa kawai ta kama gabanta.�? Muryar Abba suka ji yana magana, “Allah kadai zai iya shiryaki Salma. A duk ranar da shawararki ta yi tasiri a zuciyar danki ina tabbatar maki sai kin yi mugun danasani. Ba zan bayar da hoton ba, bazan kuma hada su ba, har sai lokacin da na gadamar yin hakan. Kai Sultan zo ka wuce.�? Babu musu ya mike ya fice abinsa yana al’ajabin mahaifiyarsa. Ita kuwa hajiya Salma dubansa ta yi ta ce, “Ka dai san babu kyau labe ko? Babu daman inzanta da dana sai ka hau masifa?�? Dubanta ya yi ya ce, “Labe? Waye dan naki? Yaron da kika ware shi a_cikin ‘yan’uwansa kika jawo masu rashin shaKuwa da juna? Ai da wannan kadai idan na bar ki Salma sai Allah ya hukuntaki.�? Bai tsaya saurarenta ba ya sa kai ya fice abinsa. Sultan yana nan ‘tsaye, bayan ya tabbatarwa mai tsaronsa ya wuce kawai ga shi nan zuwa. Yana nan a tsaye yana kallon tsakar gidan. Hafsat ta fito da wani dutse ta ajiye a hanya ta koma ciki. Ba ta kula da shi ba, haka shima bai kula da abinda hakan ke nufi ba, domin kuwa tunaninsa ya yi nisa. Nasreen ta fito tana lalube sai kawai ta ci tuntube da Katon dutsen nan ta fadi a wurin.Sultan ya zaro idanu a lokaci guda kuma Hafsat ta fito daga maboyarta tana kwasar dariya. Zata wuce kenan ta ji anfinciko ta. A razane ta dago tana hada idanu da yayanta ta tsure, “Yaya me nayi?�? Dau! Ya dauke ta da mari, daman kuma hannunsa babu kyau, a take fuskar ta kumbure ~ ta yi jazir, abinka da farar mace. Ya sake daga hannu ya yi ta kwada mata. Sannan ya watsar da ita. A gujen gaske ta yi cikin gida, domin wannan shi ne karo na biyu da ya taba dukanta a duniya, kuma duk akan mutum daya. Karasowa ya yi inda Nasreen din ke zaune ta yi shiru kawal. Yasa hannu ya kamota suka koma inuwa suka zauna. Yana jin dadin Kare mata kallo, baya gajiya da hakan. Ciwon da ta dan ji yake dubawa, bayan ya kama hannunta. A hankah yake shafar ciwon wanda yake sanya mata wata kasala, tana sake lullumshe idanunta, labbanta kamar za ta yi © magana, amman hakan ya gagara. Yanayin da ta shiga yasa mamaki ya kama shi, tambayar kansa yake ko dai ba Nasreen ba ce? Irin yanayin nan masoya kadai ke iya kasancewa a cikinta. Dayan hannunta tasa ta rike hannunsa tana girgiza kai, “Dee.. Na daina jin zafin yanzu.�? Murmushi kawai yaji, kafin kuma muryar Umma ta wargaza masu yanayin da suke ciki.  “Sultan! Yanzu akan yarinyar nan za ka yi wa Hafsat irin dukan nan? Ba ka da hankali ne ko mene ne haka?�? Sultan ya yi magana kamar baya son yl, “Umma idan kannena suka yi laifi babu daman in hukunta su kenan?. Haba Umma meyasa zaki wareni daban a cikin ‘yan uwana? Laifi ta yi na hukuntata. �?  Ta yi Kwafa kamar za ta kai masa duka, “Ita ta kusa da kai ba ta laifi ne ko me? Kada ka sake dukar min yara na gaya maka.�? Bai bata amsa ba haka bata daina masifar ba, har sai da ta gaji ta juya abinta. Shi kuma ya kamo hannun Nasreen suka shiga mota. Wani wuri ya kaita © mai dauke da sanyi irin na korama. Tana zama ta shaki irin Kamshin da wurin yake yi, ta ce, “Deedina ina jin wani irin yanayi mai dadi a jikina. Dee da ba ka nan na yi ta kewar ka, amma kuma ina yi maka addu’a.�? Sai da ya zauna bayan ya gama kallonta sannan ya ce, “Nima nayi kewarku ke da Nawfal kamar insa a kawo min ku, sai nayi tunanin karatun ku. Nasreen zaki iya tuna wanda ya watsa maki abu a idanu?�?  Hawaye suka gangaro fuskarta kamar daman tana jira ne, “Deena bansan waye ba. Ka bar maganar nan abinda Allah ya aiko kenan.�? Jawota ya yi ta kwantar luf a Kirjinsa tana sakin Wani irin ajiyar zuciya. Hakan ya haifar da abubuwa masu girma da wahalar fassarawa a tsakanin su. Sultan kenan! Kowa kallonsa yake miskili mara son hayaniya, haka alamu sun nuna idan ya kama mai laifi baya sarara masu. Idan ka ganshi tare da Nasreen za ka iya rantsuwa ba Sultan dan sanda bane. A kunnenta yayi magana, “Kada ki damu, akwai zaman da zamu yi da abokaina akan wata matsala, don haka zanyiwa Dr. Aslaf magana, akan idanunki zai bamu shawarar Kasar da ya kamata mu tafi da ke sai a duba idanunki. Idan ba haka ba, waye zai aurar min Nasreen dina a haka?�? Wani irin tafiya ta yi mai kama da tafiyar barci. Ga iska yana Kara kada su. Tana murmushi tana magana kamar wacce ta sha wani abin maye, “Deena, zan zauna tare da kai ba zan auri kowa ba.�? Dagata ya yi saboda da gaske ya gane tana cikin wani yanayi. “Tashi muje Office dina.�?  Girgiza kai ta yi, “Ina son indauwama a nan wurin. Kamshin filawowin suna sanya min nishadi da sanyi a zuciyata, wanda rabon da in ji �? hakan na jima. Dee wani abu ke tsaya min a Kirji yana min zafi sosai, ko nasha ruwa baya wuce wa.�? Wannan Karon tausayinta ya kama shi, Nasreen ta yi Karama da yawa da shiga irin wannan yanayin, “Ki dinga addu’a Nasreen kin ji? Mu je Office dina akwai abinda zan dauka.�? Da isar su Office din, “yan sanda suka taso ° suna sara masa, shi dai yana rike da hannun Nasreen. Gaba daya mutane idanunsu akan Nasreen yake, wani ma cewa ya yi koda take makauniya zai iya aurenta inhar Oga zai ba su ita. A kujera ya ajiyeta, a lokacin ne kuma aka gaya masa wani case ya ce, a shigo da matar a gurguje. . �? Tana shigowa tana bayani bai dago daga abinda yake yi ba bare ya dubeta, “Yallabai mijina ne ya zaneni,�? Yana rubutunsa ya ce, “Me kika yi masa har ya duke ki?�? Ta share hawayenta ta ci-gaba da magana, “Ya musuluntar da ni ne, ya raba ni da kowa, ya  ce min addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, nasha wahala da iyayena har na rabu da su, na zabe shi da addininsa. Amma tunda na aure shi kullum sai ya yi min gori akan addininsa, kullum idan na yi kuskure sai ya ce min matsalar tubabbe kenan. Yallabai ina son a raba aurena da shi, zan koma addinina, ko dan inhuta da gorinsa da na ‘yan uwansa.�? Tun bayan da ta ambaci ta koma addininta ya ajiye rubutun yana dubanta. Damuwa ce shimfide a fuskarsa. Har yaushe musulman mu za suyi hankali? A hakan wasu suke son jawo wadanda basa addininsu su dawo addinin su? Bai yi magana ba, har sai da ya gama nazari sannan ya ce ta fada inda za a ga miinta. Ta kwatanta ‘ya bada umamnin a je a kawo masa shi yanzu. Ya dubi matar ya ce, “Amma kafin in ce komai,  daina daukar musulunci haka yake. Musulunci abu ne mai sauki da kuma dadi. Idan kina cikin musulunci zaki sami hanyoyin warwarewar matsalarki, wanda ina ganin baki bi hanyar bane shi ya sa kike dan samun matsala. Haka kuma mu a cikin addininmu akwai jarabawa, da Allah yake yiwa bayinsa. A Karkashin jarabawar nan   zaki sami hanyar shiga Aljannah. Misali a cikin Alqur’ani akwai waraka a ciki. Ko malamin da ya musuluntar da ke bai gaya maki hakan ba?�? Sunkuyar da kanta Kasa ta yi ta ce, ‘“Malamin ya yi min bayani. Amma bai gaya min musulmi zai lya yiwa wanda ya aro addininsa gori ba, haka bai gaya min akwai duka a cikin sharuddan aurenku ba. Ina zuwa Islamiyya har yau ban ji inda malaman ta ce ana gorin addini ba.�? Sultan ya rintse ido yana kallon rubutun suna komawa kamar yashi. Saudat! Ita ta fado masa arai. Mahaifiyar Nasreen da Nawfal. Tasha gori akan addininmu amma kuma tana rike da mu. Hatta mahaifiyarsa har yau tana yi wa su Nasreen gori akan addinin da Saudat ta aro. Sultan ya girgiza kansa, “Hakane, haramun ne ma musulmi ya ci zarafin dan uwansa musulmi. A cikin addininku akwai na banza akwai na kirki, haka muma a cikin addinin mu, akwai irin hakan, Amma mu ba mu gorin addini, haka kuma ke kin fi shi rashin zunubi, saboda kin tuba kin musulunta. Addinin musulunci akwai dadi idan kika natsu a cikinsa. Dokokin mu basu da  tsauri. Haka a KarKashin wannan auren da kike son a raba zaki shiga Aljannah. Haka ina son ki zuba ido ki gani, tun aduniya Allah zai saka maki, akan mijinki idan har da gaske yana zaluntarki. Shi Allah baya barin azzalumi. Kada zuciyarki ta yi rauni kawai dan namiji yana cuzguna maki, ki dauka irin taki jarabawar kenan. Idan Allah ya dubi zuciyarki ya tabbatar a wadace take da imani, da son addininsa, sai shi kuma ya saka maki. Kada ki ce wai sai kin ji dadi sannan zaki yabawa addinin musulunci.�? A lokacin kuma aka shigo da Bala mijin Karima. A Kasa yasa ya zauna yana aika masa da mugun kallo mai cike da tsana. “Ka san wannan ko?�? Ya nuna masa Karima da hannu. “Yallabai na santa matata ce, shekarun mu uku da aure da ita.�? Sultan ya dinga jinjina yayi wuri ta fara fuskantar matsala, “Ta ce tana son a raba aurenku, saboda kana dukanta, don haka zan tura ku kotu, daga nan zaka amshi irin naka hukuncin.�?

*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA’ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number

🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*

            CHAPTER 4

        *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*

*Wannan littafin na kudine idan kina bukata kiyi magana ta wannan number 09068032427*

A JIYA MUN TSAYA

Abbansa. �? A falon ya tara kowa yana faman kaiwa da komowa ransa a matuKar bace.,“Ya zama dole ku gaya min wanda ya aikata wa Nasreen wannan abin,:ko kuma in hada ku dukka in kulle.�? Hajiya Salma da ba ta dauki lamarin zai yi irin wannan zafin ba, ta ware idanu, “Yanzu a kan wannan yarinyar za ka kulle su?�? Alhaji Lukman ya Karaso har gabanta kamar zai dake ta, “Me ya sa kike cire kanki a cikin mutanen da zan dauki mataki a kansu? Ke ce mace ta farko da zan fara kiran “yan sanda su tafi da ke, su tuhumeki. Domin na fi zarginki,

ZAMU TASHI

sannan abinda yasa na hada da ‘yan aikin nan, saboda ban san aikin me suke yi da har za a yi wannan rashin hankalin wai a ce dukkanku babu wanda ya ji. Don haka idan kuka tsince ku a Police Station duk za ku yi bayani.�? Yanzu Abban Sultan a kan yaran nan za ka zarge ni? Kana tunanin zan iya aikata wannan rashin mutuncin? Rashin imanina bai kai nan ba, duk abinda zan iya yi, ba zan iya kashe rayuwar idanun Nasrcen ba.�? Kawai tasa kuka mai tsuma zuciya. A take nadama ya shige shi, haka kuma ya gaskata ba ita ba ce, to amma idan ba ita ba ce wace ce? Ta ya ya duk suna cikin gidan a ce an rasa gane wanda zai yi wa Nasreen hakan? A fusace ya fice daga gidan gabadaya. Kai tsaye gidan mahaifityarsa ya nufa ya zayyane mata komai. Hajiya Gwaggo ta dinga Salati tana Karawa. Cikin kuka take ambaton bala’i ga duk wanda ya aikata mata wannan mummunar aiki, Alhaji Lukman ya yi shiru yana sauraren addu’ar mahaifiyarsa haka kuma yana amsawa da Ameen. Yana sane da yadda mahaifiyarsa take Kaunar ‘yan biyun

tamKar jininta. Karfe ukun dare agogon bangon ya buga, a wannan lokaci Alhaji Lukman ne tsaye cikin dogon nazari. An dade ba a yi abinda ya tashi hankalinsa ba, kamar mutuwar idanun Nasreen. Yana kallon yadda dan uwanta ke riKe mata sanda idan za su je Makaranta. Hankalinsa yana Kara tashi ne idan ya tuna duk ranar da Sultan ya dawo, me Zai gaya masa akan amanar Nasreen? Sultan ya dauki burin duniyar nan ya dora a kan yaran, yana hango masu tarin ilimi a nan gaba. Musamman Nasreen da take: gaf da sauke Alqur’ani. Yarinyar ta taso da wani irin ilimi na ban mamaki, wanda ya sake sanya Kyashi a zuciyar Hajiya Salma. Haka abinda ke damun ta, Hafsat ta zama cikakkiyar budurwa amma babu ko mutum daya da ya taba zuwa da sunan yana sonta. Amma Nasreen sai dai idan ba a ganta ba, sai an ce “Tubarkallah masha Allah.�? Wannan abu yana damun_ Hajiya Salma, shi ya sa ta yanke shawarar mayar da ita makauniya tun kafin wataran Haidar dinta ko Sultan din da kansa wani ya ce yana sonta. Idan  ta tuna hakan takan yi rantsuwa da sai ta batar da ita a duniyar gabadaya. Abba ya sami Kaninsa kasancewar shi ne babba a gidansu don haka suka zauna da Baba Sani ya yi masa bayanin tunaninsa da kuma hukuncin da ya yanke. Baba Sani, Anti Iyami, da kuma Hajiya Gwaggo duk suka yi na’am da wannan shawarar nasa. Suna zazzaune a falo, wayarsa ta yi Kara, ya daga yana murmushi. Haidar ya dubi Hafsat suka tabe baki, domin har sun gane idan har mahaifinsu yana fara’a to dan gaban goshinsa ne ya kira shi. Bayan sun gaisa ne, Sultan ya tambayi dukkan mutanen gida, daga bisani ya ce a baiwa Nasreen wayar. Abba ya Kwala mata kira, ta fito tana harba sanda, “Na’am Abbana gani nan zuwa.�? Za ta fadi Abba ya Kwala kira, ‘“Nasreen kada ki fadi. Tsaya kawai in Karaso.�? | Mamaki ya kama Sultan. Ya kasa gane me Abbansa yake nufi da kada ta fadi? Bai ce komai ba har lokacin da ya ji sassanyar muryarta tana kwarara masa Sallama. “Nasreen kina cikin “kuna cikin Koshin lafiya ko? Na ji Abba yana cewa kada ki fadi me ya sa za ki fadi?�? Shiru ta yi_ ta rasa me za ta ce masa, sai kawai ta gaida shi, ta fara ba shi labarin Islamiyyarsu. Ya ce, “Yi min karatunku na jiya in ji.�?  Nasreen ta gyara murya ta fara karatun da kaf dakin suka kafe ta da ido. Yadda take baiwa kowanne harafi hakkinsa ya isa ya sanya ka fi Kaunarta. Sultan da ke kwance ya sake mayar da kansa ya lumshe idanunsa, dama kansa wani irin ciwo yake yi masa ga gajiya ga shi yana son yin barci. Jin Kira’anta yasa ya sake samun natsuwa, yana lumshe idanunsa har barci ya yi awon gaba da shi. �? Nasreen tana saukewa ta shiga kiransa, “Dee.. Akwai gyara? Dee!�? Ta cire wayar daga kunnensa, “Abbana duba ka gani ko ya kashe © wayar ne?�? Abba ya karba yana sake duban Nasreen, ta burge shi Kwarai. Idan ya tuna rashin idanunta kuwa, sai ya ji kamar babu wanda ya kaishi zama cikin Kunci. Abba ya Kwalawa Nawfal �?  kira, ya shigo da Sallamarsa, ya dube shi, ‘“‘Nawfal kama hannun Nasreen ku koma ciki.�? Nasreen ta ta yi murmushi wanda gefen kumatunta suka lotsa ta ce, “A’a Abbana ni ma ina son in zauna a wurinku, ko ba zan iya kallo ba, zan ji sautin muryar talabijin din.�? Abba yana sake al’ajabin Karfin tawakkali irin na Nasreen, kwata-kwata bata da damuwa da irin wannan jarabawa da Allah ya yi mata. Nawfal ya riKe mata sanda suka Karaso falon ta zauna a Kasa tana aikin murmushi. Tana jin nishadi ne a duk lokacin da ta tsinci muryar Sultan yana mata magana. Hafsat tana son yin tsaki tana tsoron Abbanta, don haka ta yi shiru kawai tana kallon Nasreen cike da haushi da tsana. Abba ya sake kiran Sultan ya rarumi wayar ya manna a kunne yana sake lumshe idanu. Abba ya ce, “SP tashi mu yi magana.�? Babu musu Sultan ya tashi zaune tare da tattaro natsuwarsa ya zuba su a kan Abban. “Ina saurarenka Abba.�? Sai da Alhaji Lukman ya saci kallon Hajiya Salma sannan ya ce, “Jiya na je gidan Hajiya Gwaggo, ka san mitarta kullum ba za ka  yi aure ba? Sultan na zuba maka idanu inga iya gudun ruwanka sai dai baka da alamun raya sunnar manzon mu. Ga Kaninka nan shima har ya tasa. Hafsat kuwa ko yau miji ya fito za_ ta yi aurenta. Don haka kana babba kai ya kamata ka fara yin abu mai kyau wanda zai sa su yi koyi da kai. Na yi maka magana ko kana da yarinya amma sai kace min babu. Mahaifiyarka ta nuna min wata yarinyar Kawarta da suka so su hada aurenku, nayi irin nawa binciken ba za ku shirya da yarinyar ba. Na san abinda za ka iya zama da shi ka sami natsuwa, amma ba ‘yar Hajiya Ladidi ba. Don haka mun taru da ni da ‘yan’uwana mun yanke shawarar za ka auri yarinyar Alhaji Mamman da ke karatu a Rasha. Yarinyar tana da natsuwa da kamun kai. Na tabbata ba za ka yi da-na-sanin zabina ba. Za mu daura auren baka nan, amma kana dawowa za ka sami goron bikin zan adana maka koda kuwa ya bushe ne sai ka ci. Ina fatan amsar magana ta za ta kasance eh ne ba a’a ba?�? Sultan da gabansa yake tsananta faduwa ya rasa me zai cewa mahaifinsa? Kawai ya tsinci bakinsa da furta, “Duk abinda ka yanke a kaina  Abba dai-dai ne. Wannan ne amfanin haihuwar, idan har za ka iya sanya yaronka ya yi, za kuma ka iya hana shi ya hanu. Abba na kasa amincewa wata mace ne, a dalilin duk yawancin mata halayyarsu iri daya ce. Ka dubi duk irin zaman da kake da Umma, yau a kan taimako Umma ta watsar da lamarinmu, ta tsame ni daga cikin ‘yan’uwana, ta sa suna yi min kallon wani mugun mutum. Duk irin ilimin Umma da kuma girman tarbiyyar gidansu, amma Umma ta kasa karbar Kaddara. Abba abokin aikina Mahbub macen da take tsananin Kaunarsa taso ta kashe shi, abokina Ashrmnaaan matarsa ce take kawo masa maza a cikin gidansa, abokina Haisam, matarsa ce take aikata madigo a cikin dakin aurenta, dakin sunnah! Ba ta taba jin tsoron akwai ranar da Allah zai hukuntata ba. Abba ireiren wadannan matsalolin suna nan da yawan gaske, ta yadda idan ba rufe ido mutum zai yi ba, ba zai taba iya yin auren ba. Ina tsoron aure sosai Abba. Amma tunda ka amince nima na amince.�? , Abba da ke aikin murmushi ya ce “Kowacce da irin halayyarta, zai yiwu Fatima Dan borno ce ta sa. jarumanta a hakan, ba lallai a same su da irin halin ba, idan ma ansamu za ka gaa yanzu haka sun shiryu, tun daga lokacin da ta furta Alhamdulillahi ta kammala. Daman haushin abun daya ne, mutum yana aikata kuskure ya kasa tuba ya koma ga Allah, irin wadannan mutanen su ake gudu a rayuwa. Amma duk wanda zai tuba irin tuban da Allah ke so, ai abin a gode wa Allah ne. Sunan yarinyar Fa’iza bayan daura auren zan sa ta kiraka ku gaisa.�? Hajiya Salma ta mike a fusace ta tsaya masa a tsakiyar kai, “Wai Sultan dinne ka zauna da danginka suka bashi mata? In haifi yaro wasu su nuna min sun fi ni iko da shi? Me yasa a lokacin da zan haife shi baka kira danginka sun amshi nakudar da nayi ba? Ban yarda da wannan auren ba, dole zabina zai aura. Daman nasan kai kake sawa yaron nan yake raina ni.�? Sultan yana sauraren hayaniyar mahaifiyarsa hakan yasa ya yi saurin kashewa ya rike kansa, “Ya rasa asalin dalilin da yasa bai yi na’am da wannan auren ba. Zuciyarsa tana gaya masa akwai wani abu da yake so amma kuma ya rasa menene? Nasreen ta duKar da kanta tana jin damuwa sosai. Ta fi danganta damuwarta da irin tijarar Umma. Shi kuwa Abba har ta gama maganarta bai ce mata komai ba. Dukkansu suka mike fuuu suka fice. Falon ya rage daga Abba sai su Nasreen. Ya dubi Nasreen ya _ ce, ‘“‘Nasreen ke ma zan iya aurar da ke a kowani irin lokaci.�? Nasreen ta yi dariya har jerin haKoranta suka bayyana, “Abbana, duka-duka shekaruna sha shida a duniya. Ai ban isa aure ba, anti Hafsat ce ta isa aure da Yaya Haidar. Abbana na Kasa a yi auren Dee, sai mu koma gidansa da zama ko?�? Abba ya ce, “Kwarai kuwa.�? Nawfal ya ce, “Abba ni kuwa na isa aure ko?�? Gaba daya suka yi dariya. Haka Abba ya zauna a cikin su suna ta hirar su. Idan ya tuna Sultan zai dawo ya sami Nasreen babu idanu, sal yaji damuwarsa ta ninku. , Yau juma’a a yau ne Abba ya shigo hannunsa dauke da goro yana aikin murmushi. Hajiya Salma tana zaune idanunta sun yi jazir saboda kuka. Ajiye mata goron ya yi ya shige ciki wajen Nasreen. Goron ya dan gutsura ya ce,  Nasreen bude bakinki insa maki wani abu mai zaKin gaske a baki.�? Babu musu ta bude bakin tana fara’a “Abbana har na Kosa ka sanya min.�? Ta bude bakin ya sanya mata ballin goro. Ta rufe bakin tare da taunawa, “Abbana akwai zakin sosai. �? Ajiyar zuciya ya Kwace masa, �? “Wannan goron na daurin auren Daddynki ne. Kiyi masa addu’a.�? Murmushi ya _ wadaci zuciyarta zuwa fuskarta, “Allah ya basu zaman lafiya Abbana. Ka bani waya infara yi masa albishir.�? Babu musu ya zaro wayarsa ya mika mata, bayan ya danna kiran Sultan. Muryarta yaji cikin sanyi tana magana, “Ina tayaka mura Dee, Allah ya kade fitina. Yanzu na ci goron daurin aurenka.�? Sultan ya danyi jimm.. Alamun abin bai yi masa dadi ba, daga baya kuma ya ce, “Har andaura? Zan kawo maki tukuicin fara gaya min da kika yi. Allah ya yi maku albarka.�? Sama-sama suke magana, wanda ta fahimci yana cikin damuwa, dole ta hakura da hirar suka yi Sallama. “Abbana sai naji kamar Daddyna baiyi farin ciki da wannan auren ba. Abba me yasa baka barshi ya nemi matarsa ba? Ka bani matarsa a waya ingaya mata matsayina na “yarsa don ta fara gyara mana dakina da na Nawfal tunda can zamu koma da zama. Abba ya ce, “Idan bai yi farin ciki a yanzu © ba, na tabbata akwai ranar da dole zai yi farin cikin. Akwai ranar da zai gode min. Matarsa kuma ki bari ta kusa gama karatunta ta dawo, da zarar ta kammala sai ayi bikin tarewarta.�? Nasreen ta langwabar da kanta ta ce, “Haka Allah ke ikonsa. Na ci burin ganin irin matar da Dee zai aura. Ashe ba zan iya ganinta ba, sai dai in ji muryarta. Allah ya kawo mana ita lafiya.�? Abba ya rage murya ya ce, “Insha Allahu ba zaki dauwama a hakan ba. Ki kwantar da hankalinki kinji? Ina jiran dawowar Sultan ne a shirya a fita da ke Kasar”waje Bata ce komai ba, sai duKar da kai da ta yi, hakan yasa Abba saurin ficewa yana girgiza kansa. Yana ficewa Nasreen ta sunkuyar da kanta ta kama kuka sosai. Furucin da Umma da su Hafsat suke jifansu da shi yana sanya ta cikin damuwa da tashin hankali. Tasha kwatanta tambayar Abba sai kuma ta fasa. Nawfal ya shigo ya dafa guiwowinta, “Nasreen menene? Me ya saki kuka a ranar daurin auren Daddy?  mene ne ke damunki bai kamata kiyi kuka a irin wannan ranar ba.�? Nasreen ta lalubi hannun Nawfal ta rike tsam. “Nawfal! Umma ce take ce min mu ‘ya’yan shegu ne, haihuwar Karkashin gada. Me hakan ke nufi Nawfal? Ko dai ba mu da alaka da gidan Abba ne? Idan bamu da alaKa me yasa muke diban kama musamman da Umma? Abin yana damuna.�? Nawfal ya yi dariya, “Shi ne kike kuka? Mu ba shegu ba ne, Abba ya gaya min bata son mu ne kawai, ba wai don mun yi mata wani abu ba. Kuma mahaifinmu da mahaifiyarmu sun rasu ne a dalilin hatsari. Daddy shi ya yi ta kulawa da mu ya rene mu. Kuma ai ba mu kadai take yi wa hakan ba, hatta Daddy Sultan ba ta bar shi ba, kuma kin ga ita ta haife shi. Ki daina damuwa kin ji ‘yar uwata?”�? Ta gyada kanta kawai tana jin zuciyarta babu dadi. Karfe daya na dare, ya dawo gidan, a matuKar gajiye. Tsaye yake daga bakin tagar yana kallon yadda hadari ya hadu walKiya kawai ake yi. Idanunsa sun riga sun soye baya jin ko alamun barci. Yana tsintar kansa a cikin nishadi da kuma tunanin abubuwa masu mahimmanci a cikin rayuwarsa, sai dai yau akasin hakanne kwance a zuciyarsa. Yana son mahaifinsa fiye da kowa, bai taba yi masa musu ba, haka baya son yadda ya nuna masa Kauna a lokaci guda ya watsa masa Kasa a idanu, yasan yin hakan zai jawo mutanen cikin gidan su suyi masa dariya. Ya kasa amincewa kansa wai shi ango ne, akwai igiyoyin wata a kansa. Bai taba kawowa kansa yin aure yanzu haka ba. Akwai matsayin da yake kwadayin hawa wanda idan yana da aure a yanzu, zai dinga kaucewa zuwa kwasa-kwasan nan na Karin girma, Nasreen! Zuciyarsa ta ambata da Karfin gaske. Ya rasa dalilin da kwana biyu yake yawan ganin yarinyar a cikin farkinsa tana neman taimakonsa. Gaba daya ya ji garin ya fice masa a rai. Gida kawai yake hange. Sannu a hankali ya fice daga cikin dakin ya tsaya a bakin Kofa yana kallon yadda ruwan saman ke zuba a hankali, Nawfal da Nasreen kadai yake hange. A irin lokacin nan ne Nasreen da ke kwance a Katon gadonta ta lume cikin bargo sal juye-juye take yi tana jin ciwon kan, yana sake   ratsa kanta. Duhun da take gani kadai a idanunta yana damunta, bare kuma wani Katon abu da yake tokare a Kirjinta wanda yaki wuce wa haka ta rasa menene. Da gaske take kewar Dee dinta, ta Kosa ta ganshi ya dawo. Bata Kaunar ci gaba da zama a tare da Umma ta Kosa matarsa ta tare, su koma gidansa. Tashi ta yi ta yaye bargon da ta rufa, ta dinga lalube har ta isa ga bandaki. Alwala ta yi ta dawo ta fara gabatar da nafifili. Ta jima tana yiwa Sultan addu’a kafin ta bude Qur’ani tana karanta Suratul Maryam cikin natsuwa da zakin muryarta. Da safe ta gama shirin zuwa Makaranta jikinta yafi na kullum yin sanyi, ta jiyo hayantya, hakan yasa ta yafito Nawfal ta ce su je falon. Nawfal ya kafe Umma da idanu da ta rike Abba tana kuka tana fadin sai ya saketa ta bar masa gidansa, ba za ta iya ba. Ya sa danta ya rainata, yanzu kuma saboda a nuna mata iyakanta aka yi masa aure. Ta nemi a gaya mata wacece matar idan da hali a nuna mata hotonta amma yaki kallonta, don haka ita za ta bar masa gidansa. Haidar ne ya shigo yana duban mahaifiyarsu shi da Hafsat suka Banbare hannunta da Kyar Abba ya samu yana KoKarin ficewa daga gidan yana fadi a ransa zai yi maganinta. Kawai suka ci karo da Alhaji Mu’azzam! Kallon kallo suka aikawa juna sannan Abba ya dawo da baya suka gaisa babu yabo babu fallasa. Alhaji Mu’azzam. ya gyara zaman babbar rigarsa ya ce, “Anya Alhaji Lukman babu abinda ke damunka? Me yasa kake son mayar da kanka Karamin yaro ne? wanda bashi da ra’ayin kansa? Ta ya ya za ka yi wa Sultan aure wanda mu nan da muke dangin mahaifiyarsa bamu sani ba? Ko kana nufin bamu da hakki akansa ne? Akan ‘ya’yan zina kake son Sauya tsarin gidanka? To idan aure babu albarkar uwa auren nan bai dauru ba.�? Abba ya yi saurin bashi amsa, “A fatawarka ba! Amma ni ne uban yaro kuma na aurar da shi ga diyar da ta dace. Zina kuma babu mai tabbacin wane yana aikata zina, sai idan yana da shaidu, kawo shaidun kuma akwai wahala. Ina yiwa kowa kyakkyawan zato. Kowa a duniyar nan yana da tarin matsala akansa, idan baka zina, kana shan giya, idan baka shan giya kana caca, idan baka aikata dukkan laifukan nan kana aikata mummunar laifi wanda yafi muni, wato shirka, hada Allah da  wani. Ban ga dalilin da za ka dinga bin diddigin wani dole sai ka gano laifinsa ba. Kowa ya ji da tarin matsalarsa. Hajiya Salma kuma ta bi bayanka zan zo da abinda take buKkata, matar Sultan kuma bata isa ta santa ba, har sai ta tare, bare ta zagaya ta kashe masa auren. Ruwanku ne Hafsat da Haidar subi bayanta, sai dai ku sani irin naku rashin hankalin yafi kama da na uwar da ta haifeku, don haka binta zai fi burgeni fiye da zamanku a nan.�? Ya sa kai ya fice a fusace. Nasreen tasa kuka, wanda ya jawo hankalin Alhaji Mu’azzam kansu. Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da shi wanda bai taba jin irinsa ba. Bai taba ganin yaran ba, saboda irin tsanar da ya yi masu, sai yau da ya hada idanu da su. Bakinsa ya mutu murus, dole ya nemi wuri ya zauna, yana kallon yadda Hajiya Salma take kuka, Duk wanda ya san meke faruwa zai gane kukan korarta da Alhaji ya yi take yi. “Salma ki yi haKuri ki share hawayenki, ki zauna da ‘ya’yanki, Kada ki yarda akan ‘yar Karamar matsala ki baro dakin mijinki. Ni zan san matakin dauka haka zan lalubo inji wacce yarinya ce ya aura ma danki, Ki kwanter da hankalinki.�?

*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA’ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427*

🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*

             CHAPTER 6

     *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*

A JIYA MUN TSAYA

tsauri. Haka a KarKashin wannan auren da kike son a raba zaki shiga Aljannah. Haka ina son ki zuba ido ki gani, tun aduniya Allah zai saka maki, akan mijinki idan har da gaske yana zaluntarki. Shi Allah baya barin azzalumi. Kada zuciyarki ta yi rauni kawai dan namiji yana cuzguna maki, ki dauka irin taki jarabawar kenan. Idan Allah ya dubi zuciyarki ya tabbatar a wadace take da imani, da son addininsa, sai shi kuma ya saka maki. Kada ki ce wai sai kin ji dadi sannan zaki yabawa addinin musulunci.�? A lokacin kuma aka shigo da Bala mijin Karima. A Kasa yasa ya zauna yana aika masa da mugun kallo mai cike da tsana. “Ka san wannan ko?�? Ya nuna masa Karima da hannu. “Yallabai na santa matata ce, shekarun mu uku da aure da ita.�? Sultan ya dinga jinjina yayi wuri ta fara fuskantar matsala, “Ta ce tana son a raba aurenku, saboda kana dukanta, don haka zan tura ku kotu, daga nan zaka amshi irin naka hukuncin.�?

ZAMU TASHI

Bala ya shiga yayyanka idanu, “Yallabai a yi min afuwa, sharrin shaidan ne ba zan sake dukan ta ba.�? Sultan da zuciyarsa ke zafi, ya dubi Copral Ya ce, “Na tsani mutum ya aikata laifi da gangar yace sharrin shaidanne. Har yaushe musulmin Kwarai zai dinga barin shaidan yana shigowa cikin rayuwarsa, yana wanzar masa da sharri a cikin gidansa? Don Allah dauke min shi ka hukunta min shi har sai ya bani tabbacin shi ne shaidanin.�? Bala ya gigice yana bayar da hakuri hakan yasa Sultan sake watsa idanunsa akansa, “Gaya min sharrinka ne yasa kake dukan matarka, kake yi mata gori akan ta aro addininka ko kuwa har yanzu na shaidan ne?�? : Bala ya ce, “Yallabai sharrina ne kuma nayi kuskure.�? Sultan ya ajiye biro yana dubansu, “Malam Bala musulunci bai yarda miji ya dinga dukar matarsa ba, domin ba ankawo maka ita bane domin ka dinga dukanta ba. Musulunci bai yarda da gori akan komai ba, bare har akai ga gori akan babban abu, wato addini.

Musulunci bai yarda mumini ya dinga tauye hakkin iyalansa ba. Kai hakkin wani ma a waje haramun ne bare akai ga hakkin matarka. Yanzu kasa matarka ta hada mu gaba daya tana yi mana kudin goro, tana kallon malaminka da ya musuluntar da ita a matsayin mugu, tana kallon iyayenka da ‘yan uwanka a matsayin mugaye. Daga Karshe sai ta ji ta tsani musulunci tana neman ta koma wancan addinin da ka sameta a cikinsa. Bayan kai da kaje za ka aureta baka ji lokacin da malaminka ya ce hakkinka ne ka yi mata duka, da gori ba. Malam Bala ka ji tsoron Allah. Ka sani sai Allah ya saka mata, kamun Allah kuma ba.irin kamun mu bane mu hukuma. Kurkun Allah ba irin namu kurkun bane. Ka kiyaye abubuwan nan, za ka fi Karfin gidanka, cin matarka, shanta, rashin lafiyarta kaucewa gaya mata munanan kalamai. Domin kalamai wannan idan kana gaya mata su marasa dadi zaka wayi gari kalamanka su kasheta. Idan kuma kaima jahili ne ba ka san ilimin addinin musulunci ba, ka dauko ‘yar jama’a ka aurota kana yi mata koyarwa irin na jahilai don Allah kaje ka nemi ilimin addinin nan, kada kayi mana asarar mutum daya daga cikin musulunci. Ka �? ka kare hakkin matarka, da mutuncinta. Ina son Copral ka tafi da su, a kawo min malamin da ya daura aurecn da kuma wanda ya musuluntar da ita. “Ni Office dina idan anzo irin wannan case din sai na bi diddigi naji dalilin da yasa ake hakan. Idan mutum ya yi alKawarin gyarawa bai gyara ba, ina da hukunci kala-kala da zai sa mutum ya gyara ba don yana so ba. Bana daukar shirme. Haka bana barin a ci mutuncin mata! Domin ita mace ta wuce komai, sai da ita za ka sami natsuwa, ita ce ta dauki cikinka tana amai, tana kasa barci cikin dare saboda laulayi, a hakan za ta girka maka abinci, ta kai maka ruwan wanka. Tana renon cikinka tana renonka. Idan ta tashi haihuwa, ta kai sati tana naKuda. Wata ko nan take mutuwa, ko shekara ba za a yi ba, za ka Karo wata. Idan ta tsallake ta Haifa, ta shayar ta lura da lafiyarsa. Idan bai da lafiya ta zauna cikin dare tana nemo dabara, kai kuma kana can kana barci. Ta wanke masa kaya ta wanke naka. Mace dai ita ta kawoka duniya ita ta reneka. Shi ne don rashin hankali ka rasa abin wulakantawa sai ‘ya mace? Ka tambaya wane ne Abdullahi Lukman!  Bana daukar irin wannan shirman.�? Jikin Bala da Karima ya yi matuar sanyi, hakika D.P.O dinnan na daban ne, yasan hakkin dan adam. Ya dubi Nasreen yaga hawaye shimfide a fuskarta. Hankalinsa ya tashi don haka ya taso ya dawo kusa da ita, yasa yatsa yana dauke hawayen. “Nasreen menene? Waye ya bata maki?�? Fuskarta dauke da murmushi ta ce, “Babu wanda ya bata min. Ina godewa Allah ne da nayi sa’an dan uwan mahaifiya mai sanin ya kamata. Allah kadai yasan wahalar da mahaifiyata tasha kafin ta kawo ni gidan duniya. Allah ka sakawa mahaifiyata. Allah kasa mahaifina bai wulaKanta min ita ba. Daga Karshe Allah ya saka maka da renonmu da kayi tun muna cikin tsumma.�? Sultan ya mike ya dago ta, Zuciyarsa take gaya masa ya rungumeta, Don haka ya mayar da ita Kirjinsa ya rufe da hannayensa, Sannu a hankali natsuwa ta ratsa su, Nasreen ta sake lafewa a Kirjinsa tana sakin ajiyar zuciya. Da kansa ya ga dacewar ya janyeta, ya kamo hannunta suka fice. Mansur da ya gama kallon hotunan Nasreen ya zuKo tabarsa yana fesarwa a fuskar  su Hajiya Ladidi. Hajiya Salma ta Kufula don ta tsané rashin tarbiyya, za ta yi magana, Hajiya Ladidi ta matse mata hannu, dole tayi shiru suna ci gaba da kallonsa, “Hajiya wannan yarinyar ta hadu. Soyayyar Karya kuke son in nuna mata, amma a zahirin gaskiya ni sonta nake yi da yaske. Kuma Wallahi! Wallahi!! Sai na aure ta da Karfin tsiya. Wannan ai kalata ce. Hajitya ku bar kudinku wannan da kudina zan aureta.�? Hajiya Salma da Hajiya Ladidi suka yi ‘murmushin jin dadi. Abu kamar wasa soyayyar Nasreen ya mamaye ko ina na zuciyar Mansur, wanda har ya kasa hakuri ya shirya cikin shigar kamala ya je gidan da sunan hira. . A falo Hajiya Salma ta tare shi, ta kuma turo Naareen. Gaba daya ya shagala wajen kallonta, kwafsi daya ne, matsalar idanu, amma shi sannan babu shi a zuciyarsa, babban burinsa ya mallaketa ko ta halin KaKa.””Wanene kai? Me kake nema a wurina?�? Sai da ya shafi sajensa kafin ‘ya ce, “Sunana Mansur. Sonki nake yi, kuma Wallahi sai na aureki.�? “Ni kuma bana sonka, ka tafi tun kafin Abbana ya zo ya sameka anan.”Www.bankinhausanovels.com.ng Mansur ya mike yana tunkarota. A lokacin Abba da Sultan suka sawo kai. Da Karfi Abba ya ce, “Innalillahi wa inna ilaihirraji un.�? Wani irin jiri ya nemi ya kwashe shi ya riKe jikin bango, yana sake watsa idanunsa akan Mansur. Tuni Nasreen ta mike a gigice tana cewa, “Abba Wallahi ban san shi ba, ban taba jin ko muryarsa ba, Umma ce ta ce dole sai na zo, amma ban san shi ba. Ka yarda da ni Abba ba zan yi maka, Karya ba. Ta sake rushewa da kuka.�? _ Shi kuwa Sultan ya rasa dalilin da yake jin zai iya shake Mansur ya mutu har lahira. Don hakane ya wuce Abba ya shake shi, wanda duk Karfi irin na Mansur ya kasa Kwatar kansa daga irin rikon da Sultan ya yi masa. Idanunsa suka firfito waje. Umma da su Hafsat suka rugo a guje sakamakon jin Kakarin Mansur, Umma ce ta Kwace shi, sakamakon marin da ta dauke Sultan da shi, tana wani irin huci, “Sake shi mara mutunci kawai, Ina ruwanka idan saurayi ya zo wurinta? Ko za ka hanata aure ne? lyye Nace aure za ka hana tayi  Nine nan nayi masa izini tunda ya ce yana sonta da aure, ai ba jiKata zamu yi mu sha ba, dole za ta yi aure.�? Abba dai yana tsaye Kafafunsa duk sun yi sanyi. Sai yanzu ya sami ikon yin magana, “Kai zo ka fice min daga gida tun kafin ka yi nadamar haukan da kake shirin yi. Idan na sake ganinka a gidana zan yi maka mafi munin wulakanci. Nasreen share hawayenki baki da laifi. Laifin wancan ne, kuma zan dau mataki.�? Ya fada yana nuna Umma da yatsa. Mansur har ya kai bakin Kofa ya waiwayo ya kafe Nasreen da idanu, “Ina nan dawowa in aureki matata. Zan aureki ko da kuwa wannan ne abu na Karshe da zan yi in mutu.�? Sultan ya nufo shi, ya riKe wuyan rigarsa, “Za ka mutu kuwa! Idan wannan bai zama abu na Karshe da za ka yi ka mutu ba, zai zama ganganci na Karshe da za ka yi ka bakunci lahirar. Idan ka san da gaske kai mara kunya ne, anjima ba sai gobe ba, ka sake taka Kafafunka a Kofar gidan nan. Fice!�? Ya tunkuda Kyayarsa zuwa waje. Ya koma kawai ya zauna a kujera ya yi tagumi yana kallon mahaifiyarsa. Abba ya nuna ta da yatsa ya ce, “Ke ce ajalina Salma. Idan na fadi na mutu ke ce  sila.�? Hajiya Salma ta ce, “Oh ni kada ka sa min sharrin kisa. Yarinya dai dole za ta yi aure. Kai kuma lafiya kake kallona kamar tsohon maye? Ko dukana nima za ka yi ne?�? Mikewa ya yi kamar zai fita sai ya ji muryar Haidar yana cewa, “Gaskiya Abba ka tsani Umma da yawa, idan ba haka ba, menene a ciki don Nasreen ta yi soyayya? Duk kuka tashi hankalinku kamar kun kama ta da kwarto? Kuma…�? Sultan ya juyo ya watsa masa idanu tare da mika dan yatsansa alamun gargadi. Hakan yasa Haidar hadiye kalamansa, domin bai san cewa bai fita daga falon ba, da babu abinda zai sa shi tofawa. Sultan ya kama hannun Abbansa suka fice kawai. Shi dai Abba a ranar ko barcin kirki bai yi ba, wani tunani ne a cikin zuciyarsa da yake tunanin irin kuskuren da zai iya tafkawa, inhar ya zubawa Umma idanu ta Sauya masa tsarinsa a kan yaran. Haka acan dakin Sultan ya kasa barci, sai tunani fal cikinsa. Dole ya koma dakin Nasreen tana kwance cikin bargo, yasa hannu ya yaye bargon. Abinda ya ganine yasa shi saurin rufeta yana ambaton dukkan addu’ar kariya daga fadawa _ tarkon  shaidan. Motsinta ya ji ta tashi ashe ba tayi barci ba, tana KoKarin yaye bargon ta rungume shi, ya dakatar da ita ta ta hanyar rike bargon. Sai a lokacin ta tuna da irin kayan da ke jikinta, don haka ta shiga laluben hijabinta. Shi ya dauko ya taimaka mata tasa. “Nasreen! Me yasa kika fito wajen dan iskan nan? Don Allah Nasreen ki taimakeni inrike amanar da mahaifiyarki ta bani akanku. Na yi mata alKawarin zan iya, ki taimake ni in mutu ba tare da antambayeni yadda na rike amanarku ba. Na kasa barci Nasreen, ina da abubuwan ci gaba da nasa a gabana, amma saboda ku na kasa aikata komai, ina son in aurar da ke, Nawfal ya kama aikinsa, sai insamu nima inKarasa ayyukana. Za ki taimaka min nima burikan nan nawa su cika?�? A gigice take magana, “Wallahi Dee ban san shi ba, ka yarda da ni. Ina dakina Anti Hafsat tazo ta yi min jagora muka je falon. Ya ce yana sona, nace bana sonsa. Ajiyar zuciya ya Kwace masa, yaso a daren ya shiga dakin Hafsat, sai kuma ya canza tunani. “Allah ya yi maki albarka koma ki kwanta kiyi barci.�? Babu musu ta koma ta  kwanta, amma kuma bata sakar masa hannun ba, Zuba mata idanu ya yi yana jin wasu abubuwa suna sake canza mazauni a cikin jikinsa. Yana jin_kansa kamar ba shi ba, Dayan hannunsa yasa ya mayar da gashin kanta baya da suke Kokarin | rufe mata fuska. A hankali ya matso sosai ya bata fake a goshi. Wannan lamari yasa Nasreen nutsewa wata duniya. Wanda har bata san lokacin da ya zare hannunsa ya fice daga dakin ba. Dakin Nawfal ya leKa ya same shi zaune akan dadduma yana Sallah. Ibadan yaran yana burge shi, ya sake. gode. wa Allah da, dukkan abubuwan da ya dora su akai babu wanda suka kuskure masa; A hankali yayi maganar da ya ratsa kunnuwan Nawfal. Nawfal kada ka mance ni a cikin addu’arka. Haka, kada ka mance da mahaifiyarka.�? Ya sa kai ya wuce, Dakin Hafsat  haka yake yana da yawan leKa Kannansa domin tabbatar da lafiya lau suke kwance. Yana lekawa ya sameta zaune tana waya. Tana ganinsa ta katse wayar tana zare idanu, “Da wa kike waya? Ba zaki bani amsa ba!�? Jikinta na rawa tace “Abokin karatuna ne,�? Sultan ya zaro ido, “Abokin karatunki a wannan  daren? Haba Hafsat! A wannan lokacin da ya kamata ace kina ganawa da Mahaliccinki? Ance ki fito da miji ayi maki aure, kin ce baki‘da samari. Amma yanzu gashi kina waya da garjejen Kato ko? Ki kiyaye, ki kama mutuncin kanki, watarana ke uwa ce.�? Juyawa ya yi abinsa ya fice. so Sultan yana Office ya sami kira daga abokansa, sun hadu za su fara meeting. Da sauri ya Karasa dukkan abubuwan da ke gabansa sannan ya kama hanya. Gaba dayan su sun sami isowa shine na Karshe. Tajuddeen Abdulsalam jarumin littafin (Kowa ya kwana laftya), Haisam �? Hayat, Jarumin littafin (Zuciya), Aslaf Mai nasara Jarumin littafin (Sir) Mahbub Muhd Daura, Jarumin littafin (Mafarin lamarin), Ashmaan Ashraf Jarumin littafin (Akaran kaina) Sai kuma Soja, Khamis § Idris Jarumin littafin (Akaran kaina), ga kuma Al-ameen Rabi’u, jinin Sarauta jikan sarki, Jarumin (Akwai_ lokaci). Dukkansu suna zaune kowa da abinda yake yi. Sultan ya basu hannu yana murmushi, “Ga -ni kuma, jarumin Rubutacciyya! Na gaida Karfin Zumuci irin na ‘yar mutan Borno, hakika tayi namijin KoKari da bata barmu mun watse ba, da ba haka ba, Ashmaan shi ne mutum na farko da zai fara datse mana zumuncin nan.�? Dukkansu suka yi murmushi_ sannan Mahbub ya bashi amsa, “Idan Ashmaan bai kashe zumunci ba, ai kai sarkin watsar da zumunci, za ka watsar da komai. Kai dai kawai Allah ya sakawa ‘yar mutan Borno, ita ta riKe mu ta dage lya lyawarta da ba haka ba, da tuni kanmu ya rabu.�? Dukkansu suna ji da kansu, kowa ya ci ya ture. Haka ga -dukkan alamu suna_ cikin kwanctyar hankali suna samun kulawa daga matan su. “Tuzuru bude mana taro da addu’a Kila sanadiyyar hakan ka samu ka shiga daga ciki.�? Aslaf yake tsokanar Sultan. Murmushin ya _ yi sannan ya yi addu’a mai tsawo. Suka shafa. Wannan taron gaba dayansa akan Sultan akayi shi, saboda shi ya gayyato su. Don haka ya fara magana, “Da farko dai andaura min aure. Sai dai bana son doguwar magana, ko Korafi, Abba ne ya daura auren, ban santa ba, ban taba ganinta ba, yanzu haka wai yana jiran ne ta gama karatu ayi bikin tarewa. Ban wani damu ba, domin bani  da budurwa, hakan ke nuni da ina da bakin jini Irin na wannan yaran”�? Ya nuna Mahbub da hannu, duk suka yi murmushi. a hakan sai da suka yi korafin meyasa tun a lokacin bai gaya masu ba? Share su ya yi kawai ya ci gaba, “Ina da babban Case a hannuna na kisan kai, Case din akwai buKatar natsuwa da kuma sanya hankali a cikinsa: Mahaifiyar Nasrecn nake son sanin waye ya kasheta tsawon shekaru goma sha shida? Me yasa aka kasheta? Ta bani wani littafi da wasu hotuna, suna cikin wannan files din. Ban taba budewa ba, daman burina inkammala da kulawa da su, sannan insan,abin yi. Duk wanda ya kashe ta babu shakka ya yi kisan nan ne saboda gudun kada ta tona masa asiri, nayi alkawarin idan mahaifina ne mai kisan nan, saina daukar mata fansa, Sai kuma Nasreen da aka watsa wa guba aka makantar min da ita.�? Tajuddeen ya fara magana, ““Wannan case din case ne mai girma, musamman na kisan nan. Haka duk wanda ya yi kisan bai san Nasreen da Nawfal suna nan a raye ba, da sai sun nemi kashe su. Wadannan abubuwan da ke hannunka   za su tabbatar mana da komai. Don haka zamu yi lya yin mu muga abinda Allah zai yi. File din kuma za ka iya bani, ko kuma ka ba Mahbub, ko Ashmaan. Sai mu fara bincike. Abinda binciken mu ya bamu sai mu sake dawowa ayi meeting ko ya kuka gani? Dukkansu suka yi na’am da wannan shawarar. Al-ameen ya dube su, “Maganar idanun Nasreen, zan dauki nauyin fita da ita waje, ina da wani aboki da ya Kware da aiki akan irin wannan. Kafin nan zan fara bata kulawa a Asibitina. Dukkansu suka ce basu amince ba, sai kowa ya bada gudumawarsa a kan samun lafiyar Nasreen. Sultan ya rasa bakin magana sai duban su kawai yake yi. Da ace haka abokai suke da hadin kai tabbas da duniyar ma gaba daya ta zama abar sha’awa. Haka aka tashi taron Sultan kuma ya damka komai a hannun Barrister Tajuddeen, ba tare da ya bude ko shafi daya ba. Mahbub ‘yan sandansa suka bude masa mota, haka ma Sultan sauran kuma duk suka ja abinsu suka bace bat! Sultan yana isowa gida, ya watsa ruwa kafin ya iso falo inda mahaifinsa ke zaune. Bayan ya gaishe shi ne, yake gaya masa yadda suka yi da abokansa, daga Karshe ya rufe maganar da fadin za a yi wa Nasreen aiki a idanu, abokan suka dauki nauyi. Wannan magana da Hajiya Salma da ke shirin shigowa falon ta ji, shi ya tashi hankalinta taja da baya ta koma. Ko tambayar mijinta ba tayi_ ba ta dauki gyale. A gidan Hajiya Ladidi taja burki. Tana shiga ta sami Mansur a dakin, da alamu sun gama sheKe ayarsu da Hajiya Ladidi ne ya fito yana gyara .kwalar riga. Yana ganin . Hajiya Salma ya daure fuska, “Yauwa Hajiya ki gaya mata sai na dauki mataki akan dan nan nata sannan zan koma indauke Nasreen. Narantse da Allah sai na dauketa. Amma kafin nan sai na gama gyarawa danki zama.�? Hankalin Hajiya Salma ya tashi ta ce,  nan fa daya. Kada ka kuskura ka taba min lafiyar da. Za ka iya yin komai amma banda taba Sultan. Kuma Wallahi idan ka ce za ka taba shi sai kayi danasani, domin kana ganinsa nan ba Karamin tsayayye bane.�? Mansur ya yi Kwafa, “Na fi ki sanin hakan ni da ya shake ni na nemi sheKawa lahira. Amma  duk da hakan sai na koya masa hankali. Yanzu sauri nake yi zan sake dawowa.�? Ya sa kai ya fice. Gabadaya suka zauna Hajiya Salma tana yi mata kallo cike da Kyama, “Hajiya da ‘ya’yanki da_ girmanki kike irin wannan Kazantar? Gaskiya bana son zina ko alama, ina tsananin Kyamatarta.�? Hajiya Ladidi ta tabe baki ta ce, “Ba gara zinan ba, da irin ta’asar da kike yi a gidan mijinki? Malama ki fada abinda ya kawo ki kawai.�? . Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya ta natsu �? sosai, “Kin ga wannan shashashan yana son ya kawo mana matsala. Ina ganin abinda ya kamata kawai ki samo wasu daga cikin ‘yan iskanki su dauke yaran nan su kai su can wani gari mai nisa, su jefar da su. Wai Sultan ne yake son fita da Nasreen waje su gyara mata idanun da bana fatan ta sake kallon wasu zuri’ana da su. Don haka nake son ta bar cikin iyalina kowa ya huta. Na mayar da yarinya makauniya, sai take son ta mayar min da miji da da ‘yan jagoranta.�?

*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA’ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427*

🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*

             CHAPTER 7

       *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*

A JIYA MUN TSAYA

duk da hakan sai na koya masa hankali. Yanzu sauri nake yi zan sake dawowa.�? Ya sa kai ya fice. Gabadaya suka zauna Hajiya Salma tana yi mata kallo cike da Kyama, “Hajiya da ‘ya’yanki da_ girmanki kike irin wannan Kazantar? Gaskiya bana son zina ko alama, ina tsananin Kyamatarta.�? Hajiya Ladidi ta tabe baki ta ce, “Ba gara zinan ba, da irin ta’asar da kike yi a gidan mijinki? Malama ki fada abinda ya kawo ki kawai.�? . Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya ta natsu �? sosai, “Kin ga wannan shashashan yana son ya kawo mana matsala. Ina ganin abinda ya kamata kawai ki samo wasu daga cikin ‘yan iskanki su dauke yaran nan su kai su can wani gari mai nisa, su jefar da su. Wai Sultan ne yake son fita da Nasreen waje su gyara mata idanun da bana fatan ta sake kallon wasu zuri’ana da su. Don haka nake son ta bar cikin iyalina kowa ya huta. Na mayar da yarinya makauniya, sai take son ta mayar min da miji da da ‘yan jagoranta.�?

ZAMU TASHI

Hajiya Ladidi ta saki dariya sosai sannan ta ce, “Ashe ‘yan iskan nawa suna da rana? Shi yasa nace maki a hada aurensu da ‘yata amma wannan kafaffen mijin naki ya hana. Wannan aiki ne mai sauki, Rainbow dinnan dai shi za mu sake sawa ya yi aikin nan.�? A nan suka gama kintsawa akan idan Nasreen za ta je Makaranta a nan za a saceta ita da Nawfal. Tana isowa gida ta sami Sultan yana gyara mata gashinta, da take ta mitan yana damunta ya taimaketa ya aske mata. Bai ce mata komai ba, ya tattare mata gashin ya Kulle a cikin Katon ribom. Hajiya Salma kamar za ta yi magana, sai kuma ta hadiye da ta tuna da komai ya kusan zuwa Karshe. Mikewa ta yi tana fadin, “Dee kama ni ka kai ni daki ina son shirin zuwa Makaranta, bansan inda Nawfal ya tafi ba. Babu musu ya kamata ta shiga dakin, ya fitar mata da kayan Makarantarta kafin ya fice daga dakin ya tafi neman Nawfal. A tsakar gida ya same shi yana Kwallo, ya Karasa ya tallabi Keyarsa tare da riko

kunnensa daya. “Kai baka jin magana ko? Karfe nawa yanzu?�? Nawfal ya rike hannun Sultan yana rintse ido, “Wayyo Deedi ka yi hakuri don Allah na tuba ba zan sake ba.�? Hannunsa riKe da kunnan Nawfal ya tasa shi gaba har cikin daki. Da suka tashi tafiya Makarantar shi ya dauke su da kansa ya kai su har Makaranta. Daren ya tsala wuri ya yi shiru, baka jin motsin komai, sai na tsuntsaye. Nasreen ta fito tana lalube a yanzu ta haddace inda komai na gidan yake, don haka ta nufi dakin Sultan. Yau bai kwana a office ba, yana gida don haka ta iso har kan gadonsa. Yana kwance yana kallonta, haka ya zuba mata ido ne kawai ya ga iya gudun ruwanta. Lalubansa take yi har ta tabbatar ga inda yake, sannan ta kwanta shiru a Kirjinsa, “Deena me yasa bana iya barci sai da tunaninka? Me ke shirin faruwa da rayuwata ni Nasreen? Ina jin damuwa a kwana biyun nan, ina jin kamar zan rasa ka. Deee ka tashi ka gaya min mene ne ke shirin faruwa da ni? Dee.,.�? Ta ja sunansa tare da  dora hannayensa a bisa fuskarta da ke kwararar hawaye. Shi dai bai ce komai ba, sai kallonta da yake yi. Ya zama dole ya ajiye wasan kwaikwayon nan shi da Nasreen ya tabbatar mata da yana sonta. Irin abinda Nasreen take ji, shi ya fi ta jin fiye da hakan. Hawayenta ya kafe da ido yana dubanta. Da gaske tana bashi tausayi musamman rashin idanun da yafi so fiye da komai. Idan ta ware idanunta tana dubansa, sai ya ji kamar ta kwashe dukkan kuzarin jikinsa ne. Ta ya ya zai iya fitowa ya ce Nasreen yake so? Me yasa? Idan ya yi hakan zai sa rayuwar Nasreen a cikin matsala! Haka kuma ba zai taba samun natsuwar da yake nema ba, saboda mahaifiyarsa duk za ta hana hakan, Sannan ba Zai iya ce mata yana sonta ba, har sai ya gano su waye iyayenta? Me ya jefa mahaifiyarta a cikin irin wannan halin bakar rayuwar? Yatsunta ya kafe da ido gabansa yana tsananta fadiwa. Babu inda ya tsunta ya bambanta da na Haidar Kaninsa. Kafafunta kuwa iri daya da nasu. Wannan abu yana sake daure masa kai Sai yanzu yake takaicin Kin bude hotunan nan ya fi tunanin a nan ne zai gano komai. Sai dai yasan ko wasu irin hotuna ne ba zai wuce hotunan . mahaifiyarta ba, shi kuma idan har zai dubi hotunan nan sai mutuwar Saudat ta dawo mata sabuwa fil! ‘““Nasreen.. Ya kira sunanta, wanda yasa ta yi firgigit! Ba ta yi magana ba, don haka ya dora, “‘Nasreen kina jin son Deedinki a cikin zuciyarki? Nasreen babu aure a tsakanina da ke. Ki dauke ni a yadda kike daukana a da kin ji? Nasreen Abbana shi ne mahaifinki anboye ne saboda wasu dalilai idan lokaci ya yi zaki san komai kinji? Nima da farko da bansan hakan ba, irin abinda kike ji shi nake ji, daga baya na sawa raina hakuri. Sannan idan auren za a yi, ban yi maki girma ba Nasreen? Yaro Karami zan baiwa aurenki, wanda bai wuce sa’an Haidar ba. Kin ga ni na wuce talatin ko? Maza _ ki share hawayenki.�? Kukanta ya Karu da yawa, bata jin za ta iya cire abinda ke cikin zuciyarta, ba ta jin za ta iya rage son Sultan wanda bata ko tantama da soyayyarsa aka haifeta. Tana son tasan wacce irin alaKa ce ke tsakaninta da Deedinta. Duk da ta kadu da kalamansa, amma hakan baisa ko digo daya daga cikin soyayyarsa ta ragu ba.  Tana sonsa da gaske. Ta shirya wa tunkarar kowacce matsala a kansa. Sake damKe hannunsa�? ta yi tana jin duk wata kunya ta kau a idanunta, tana jin za ta iya gaya masa komai. “Dedena, ina son ka, zan iya mutuwa Ko babu aure a tsakaninmu zan zauna da kai. Ba zan taba iya yarda da wani namiji ba, yin hakan zai gurgunta rayuwata. Ka rike ni a gidanka zan zauna da matarka. Don Allah ka roKe ta kada ta raba ni da kai. Ban san kowa ba sai kai da Abba. Kai ka koya min wannan rayuwar, Sai dai na yi nisan da ba za ka iya cire min abinda ke cikin zuciyata ba.�? | Kalaman da Nasreen take ambatowa sun yi matuKar bashi mamaki, ta yaya Nasrecn ta iya irin wannan kalaman? Ya aka yi Nasreen tasan soyayya haka? Yaushe ta cire kawaicinta ta iya furta masa wadannan kalaman? Tausayinta ya kwaranyo masa, baya jin zai iya hada Nasreen da kishiya bare har ta cutar masa da ita, Yana yi mata irin son da duk wanda ya kama da cutar da ita zai dauki matakin da sai duniya ta girgiza da irin matakinsa. Ya danganta rashin kawaicinta a yau da rashin idanunta, ya tabbata da za ta hada  idanu da shi, ba za ta taba samun Karfin halin da za ta fada masa wadannan kalaman ba. Share mata hawayen ya yi ya rungumeta tsam a Kirjinsa. A lokaci guda yake jin kamar shaidan ke son cin galaba akansa, idan ya yi la’akari da yadda komai ya sauya daga cikinsa. Bisa labbansa yake magana, “Ina jin irin abinda kike ji Nasreen.�? Shiru ya biyo bayan hakan, sakamakon saKon da ya bata mai matuKar tasiri. A lokaci guda ya zame kansa, yana jin meyasa zai zama mutum na farko da zai gurbata amanar da Saudat ta bashi? Sai da ya natsu sannan ya ce, “Nasreen ki tashi ki koma dakinki.”Shiru ta yi sakamakon yadda Kafafunta suke rawa. Haka ta tsinci kanta cikin wani baKon al’amari. Yawun baki wani irin abu ne mai kama da guba, idan suka hadu wuri guda suna sanya zazzafar soyayya da kuma shaKuwar dake da wahalar rabuwa. Hakan ce ta kasance da Nasreen @ wannan daren. Hannunta ya kama suna mikewa tsaye ta yi baya za ta fadi, ya yi saurin dawo da ita ta fadi a jikinsa, “Nasreen! No kada ki yi min haka. Ki Karfafa jikinki don Allah. Ki tuba ga Allah wannan abun haramun ne kin ji? Kada ki sa shi a ranki kin ji?�? Ba tayi magana ba, amma ta dan Karfafa jikinta. Da kansa ya rakata dakinta ya kwantar da ita, tare da addu’a sannan ya jawo mata bargo ya rufeta. “Sleep!�? Ya furta tare da hure mata fuska. Luf idanun suka sake  rufewa. Ta shaki Kamshin bakinsa tana sake rurrufe idanun da daman a rufen suke. Ya tashi ya kashe mata wuta ya fice abinsa. Wannan lamari akan idon Umma ya faru, hankalinta idan. ya yi dubu to ya tashi. Abinda ya sake ba ta mamaki Abbansa ashe yana tsaye shi ma yana kallon su. Duban fuskar Abban ta yi da mamaki yadda yake ta murmushi. Ta sake leKa fuskar Abban ta tabbatar da murmushin yake yi. Kafin ta yi magana Sultan ya Karaso falon ya bude frij zai dauki ruawa. Domin ji yayi makoshinsa ya bushe saboda halin da ya tsinci kansa a ciki. Ji ya yi kawai an shaKo shi, kafin yayi wani abu, ya ji saukar mari ko ta ina @ fuskarsa, Sai huci take yi, “Kai kai! Baka isa ka kasheni ba, Zina kake aikatawa da Nasreen? ‘Ya’yan mazinatan ne suka shigo rayuwarka su Bata maka tarbiyya? Wallahi idan ka kasance  mazinaci ba zan taba yafe maka ba a cikin gidan nan, sai na tsine maka kabi duniya! Kaf zuri’ata babu mazinaci, kai kuwa baka isa ka jawo min wannan abin kunyar ba. Dama sonta kake yi dan ubanka! Za ka yi min magana ko sai na kasheka a gidan nan?�? Ta daga hannu da nufin sake marinsa, Ta ji anriKe hannunta. Abba ya tunkudeta gefe saura kadan ta kifa. Yana dubanta yana huci, “Insha Allahu ban haifi mazinaci ba, bana fata idan Allah ya jarabceni da da mazinaci ba zan tambaye shi dalili ba, haka ni nasan ban zagi ‘ya’yan wasu ba, sai dai idan alhakin zagin da kika yiwa ‘ya’yan wasu ne ya sauka akanki. Haka ba dai dana Sultan ba, sai dai idan ‘ya’yanki da kika lalata da irin halayyarki.  Wannan yaron da kike gani, shi ne dan da nake fatan ya gado ni kuma na gode Allah. Kada ki sake danganta min da da zina, yin hakan zai jawo maki mummunan bacin rai Wallahi!�? Umma ta dube shi da mamaki, “A gabanka fa ya fito manne da ‘yar iskar can!�? Abba ya yi saurin tare numfashinta, “Sai _me? Idan kin ganshi rungume da ita nace sai  mene? Kuma ina son ki gane, kin taba fuskar yaron nan na Karshe! Sultan ya wuce mari a yanzu sai dai nasiha. Kai Sultan zo ka wuce dakinka. Allah ya yi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya. Maza ka wuce.�? Sultan ya juya kawai yana jin dacin furucin mahaifiyarsa akansa. Ya maimaita Kalmar zina tafi a Kirga. Hakan yasa ya kasa barci. Tunanin ya yi nesa da Nasreen da iyayensa suka darsu a zuciyarsa. Ita kuwa Nasreen ta lashi labbanta da suka yi laushi ya fi a Kirga. Tunanin Sultan ya ci gaba da gallabanta. A haka har barci barawo ya sace ta Washegari suka shirya zuwa Makaranta, a lokacin Sultan ya jima da barin gida. Akan hanyarsu ta dawowa ne aka tare direban su aka cunkusa su a wata mota. Nasreen dai tana rungume da Nawfal bakinta bai fasa addu’a ba. Wani irin Kunci ya ziyarceta, Yanzu mutanan nan ina za su kaita? Ita dai damuwarta kada a rabata da dan uwanta. Da zarar ta tuna da Sultan Sai taji wasu hawaye suna kwaranya. Nawfal dai ko Kwakkwarar motsi ya kasa yi. Tafiya ake yi tun suna sa ran sauka har suka sadakar da kwanakin su a duniya ya Kare. Sai wajen  Magriba aka bude Kofar mota aka cillo su waje sannan suka Kara gaba. Nawfal ya dubi Nasreen cike da tausayawa ya ce, “Nasreen kin ga wata duniyar suka ajiye mu. Yanzu ina zamu dosa?�? Nasreen ta ce, “Duba ka gani akwai jama’a a garin?�? Ya dudduba ya ce, “Daji ne wurin babu wasu jama’a. Amma zo mu Kara gaba ko zamu sami abinda zamu ci.�? Haka suka yi gaba babu wanda suka samu sai wata mai siyar da abinci da take shirin rufe wurinta. Nawfal ya fara magana, “Sannu. Don Allah wani gari ne nan?�? Matar ta dube shi ta ce, “Ku kuma daga ina haka? Wannan garin Katsina ne Kankia. Me ya kawo ku nan?�? Nawfal ya dan yi shiru, “Wallahi wasu ne suka sato mu suka kawo nan. Don Allah ina Zamu sami makwanci? Sai ki daukeni aikin wanke-wanke kina ba mu abinci, ° Matar mai suna Amina ta nuna masu Kofar shagonta wanda akwai rumfa, “Sai dai ku dinga kwana a nan domin ba zan iya baku makwanci ba, kun san duniyar babu amana. Ita wannan makauniya ce?�? Ya dan durkusa, “Mun gode _ sosai. Makauniya ce�? Ta dan tausaya masu, sannan ta cire zanenta daya ta basu ta ce, su lulluba. Har ta tafi ba ta daina waiwayarsu ba. Ita kuwa Nasreen umartar Nawfal ta yi da ya samo masu ruwa suyi alwala. Bayan sun yi alwala ne suka raba dukkan sallolin da ke kansu sannan suka dan rabe. Nasreen tana jin yunwa, amma kuma ta kasa gayawa Nawfal yunwa take ji, saboda kada ya shiga damuwa. Shi kansa yunwar yake ji amma ya kasa furtawa. Can ya tuna da awaran da ya siyo daga Makaranta don haka ya ciro jakarsa ya fitar, a lokacin ne kuma Nasreen ta jiyo Kamshi da fara’arta ta ce, ““Nawfal menene wannan kuma?�? Sai da ya kai bakinta ta gutsura sannan ya bata amsa, ““Dazu ashe na siya wara na manta ne. Zai ishemu mu ci.�? A nan suka cinye warar, Nawfal ya dibo masu ruwa suka sha. Cikin dare dukkansu suka kasa barci saboda azaban cizon sauro. Shi dai Nawfal sai korarwa Nasreen Sauron yake yi. Ga kwanciyar Kasa, ga cinnaku, ga sanyi da ke ratsa su. Nasreen ta   dinga kuka ba tare da ta bari Nawfal ya sani ba. Can ta yi magana a hankali, “Nawfal waye zaiyi .mana haka? Me yasa za a raba mu da danginmu?�? Nawfal ya girgiza kai, ‘“‘Nasreen idan kina tunanin su Abba danginmu ne ki daina tunanin hakan. Da wahala idan ba tsinto mu aka yiba. Rannan naji Umma suna magana da wata Kawarta take cewa Deedi ne ya rakito mu, ya kawo masu masifa cikin gida. Amma tabbas! Mu ba “yan gidan bane. Ya zama dole mu mance duk wani jin dadi, mu fuskanci abinda ke gabanmu. Mu koyi zaman wahala mu koyi nema da kanmu, mu koyi maraici, tunda dama mu din marayu ne. Idan muka ce zamu yi ta zama a gidan nan watarana Umma za ta sa ashana ta Kona mu. Kin ga ta nakasa maki idanu, yanzu haka ita ta sa,a kawo mu nan, Don Allah Nasreen mu mance gidan nan mu jure dukkan gwagwarmayar nan watarana sai labari.�? Nasreen ta gigice da kalaman Nawfal, don haka ta bashi labarin yadda suka yi da Sultan a daren jiya, ta ci gaba da cewa, “Yanzu Nawfal mu dauka ba mu hada komai da su Abba ba, idan muka barsu munyi masu adalci? Wane hali yanzu su Deedi suke? Sun raine mu tsawon shekaru goma sha bakwai, yau don mun yi fushi sai mu guje su? Da wannan zamu saka masu kenan Nawfal? Ya kamata muyi tunani.�? Nawfal ya ce, “Nasreen bamu yi laifi ba idan muka yi hakan. Zamu bi su da addu’a wanda duk nisan inda muke zai je ya same su. Maganar kuma babu aure a tsakaninki da Deedi ya dai fada maki hakanne domin baya son ki damu da lamarinsa, yana hango tashin masifun da zaki iya shiga ne idan har Umma tasan akwai soyayya a tsakaninku. Don Allah mu mance baya mu fuskanci gaba.�? Nasreen ta fitar da kukanta fili, wanda har yasa zuciyar Nawfal ya karaya, “Nawfal ka yi min addu’a domin na fada cikin hatsarin son Deedi. Ba zan iya raba kaina da irin wannan soyayyar ba, domin bansan lokacin da ta shige ni ba.�? A lokacin wani Katon sauro ya cije ta ta kai wa kanta duka, Nawfal ya share hawayensa ya ce, “Zan taya ki da addu’a insha Allahu komai zai zama labari.”Www.bankinhausanovels.com.ng A can garin Kaduna kuwa, Sultan yana Office ‘ya ga kiran mahaifiyarsa, abin ya ba shi mamaki domin ba zai tuna ranar da ta kira shi ba. Ya dauka da Sallama tun kafin ya gaisheta ta fara magana, “Sultan su Nasreen ba su dawo daga Makaranta ba, ko kuna tare ne?�? Mikewa ya yi tsaye kafin ya ce, “Umma ban gane ba? Ina shi direban yake?�? Umma ta tabe baki, “Babu direba, babu su Nasreen. Allah ya sa ba wani gantalin aka wuce ba.�? Sultan ya katse wayar kawai ya hada ‘yan sanda suka fita a cikin motarsu. Kai tsaye hanyar Makarantar suka nufa, a nan suka sami direba a yashe, ga mota a gefe, haka mutane sun fara taruwa. Shi ya fara sakkowa daga motar ya tallabo Direban, Sumewa ya yi don haka yasa a kawo masa ruwa ya watsa masa, gabansa yana tsananta faduwa. Yana farfadowa ya ce, “Ina su Nasreen? Ina suke!�? Ya daka masa tsawa. A gigice yake magana, “Yau na shiga uku! Wasu suka zo a farar mota suka tafi da su.�? Sultan ya shake dircban nan jikinsa yana rawa, “Idan wani abu ya sami su Nasreen ina  tabbatar maka sai na kashe ka! Ka gaya min da su waye ka hada baki aka sace min su? Gaya min waye ya turo ku?�? Sultan fa ya haukace, ya fita hayyacinsa. Da Kyar ‘yan sandan nan suka Kwaci direba, sannan suka sa shi a baya tare da wani dan Sanda aka samu aka lallaba Sultan ya shiga motar gidansu dan sanda ya shiga ya wuce da shi gida. A lokacin Abba ya dawo, don haka ya Karaso gaban Abba jiki asanyaye. “Abba..�? Ya ja sunan mahaifinsa, ya kuma kasa furta komai. Sai dan sandan nan ne ya korawa Abba “bsyani Da Karfi Abba yake Salati. Sultan kuwa ya kasa magana, sai idanunsa da sukayi jazir kamar  gauta. Jikinsa har rawa yake yi. Ita kanta Umma yadda taga yaron nata ya sauya a lokaci guda yasa jikinta mugun sanyi.,,Gaba daya suka shiga falo, Abba ya baiwa dan sandan umarnin a bi ko ina a sanya cigiyarta. Kafin ka ce me? Gari ya dauka an sace “yan biyu mace da namiji, Sultan ya zauna a kujera jikinsa asanyaye babu Kwari, Haduwarsu kawai yake tunawa a jiya, ya kasa magana ya kasa duban Abbansa. Shi kuwa Abba tashin hankalinsa ya ninku da ya tuna bai sauke Katon nauyin da ke kansa ba. “Sultan nayi kuskure mai girma! Ban barka ka samu kyakkyawar zama da Nasreen ba.�? Dukkansu suka dube shi cikin rashin fahimta. “Sultan Nasreen matarka ce, matarka ce aka sace �? ta. Na hada aurenku domin ganin ka sami daman rike amanar Saudat da kyau! Yau sai gashi ka rasa matarka. Ban sani ba ko kasheta akayi, idan kuwa tana da rai za ta yi ta yawo da igiyar aurenka akanta.�? Ba Umma ba, hatta Sultan sai da maganar tayi masa girma. Damuwarsa ta sake ninkuwa. Daman Nasreen matarsa ce? Da , yasan matarsa ce me Zai sa jiya/ya gaya mata irin wannan kalaman? Rintse ido yayi yana jin | kamar mahaifinsa bai kyauta masa ba. Umma kuwa tunani take yi a zuciyarta me yasa batasa a kashe Nasreen ba kawai ta huta? A fusace ta mike, “Allah na gode maka da aka saceta. Ashe so ta yi ta kanainaiye min gida? Kana nufin Nasreen ita ce matar Sultan? Amma dai Alhaji ka gama cutata. Da inga wannan baKar ranar �? gara inga ranar mutuwata. Ita Iyamin da Sanin ai suna da ‘ya’ya maza, Me yasa basu aura masu

*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA’ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427*

*🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*

            CHAPTER 8

        *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*

A JIYA MUN TSAYA

Sultan nayi kuskure mai girma! Ban barka ka samu kyakkyawar zama da Nasreen ba.�? Dukkansu suka dube shi cikin rashin fahimta. “Sultan Nasreen matarka ce, matarka ce aka sace �? ta. Na hada aurenku domin ganin ka sami daman rike amanar Saudat da kyau! Yau sai gashi ka rasa matarka. Ban sani ba ko kasheta akayi, idan kuwa tana da rai za ta yi ta yawo da igiyar aurenka akanta.�? Ba Umma ba, hatta Sultan sai da maganar tayi masa girma. Damuwarsa ta sake ninkuwa. Daman Nasreen matarsa ce? Da , yasan matarsa ce me Zai sa jiya/ya gaya mata irin wannan kalaman? Rintse ido yayi yana jin | kamar mahaifinsa bai kyauta masa ba. Umma kuwa tunani take yi a zuciyarta me yasa batasa a kashe Nasreen ba kawai ta huta? A fusace ta mike, “Allah na gode maka da aka saceta. Ashe so ta yi ta kanainaiye min gida? Kana nufin Nasreen ita ce matar Sultan? Amma dai Alhaji ka gama cutata. Da inga wannan baKar ranar �? gara inga ranar mutuwata. Ita Iyamin da Sanin ai suna da ‘ya’ya maza, Me yasa basu aura masu

ZAMU TASHI

ba? Allah ya kara nesanta su da mu, yasa ko a lahira haduwar ta yi wuya.�? Hafsat ta mike ta ce, “Tabdijan! Nasreen matar Yaya Sultan? Allah ka tsaremu da hada zuri’a da shegu. Allah ya ga abinda ya gani.�? Haidar ya mike yana fadin, “Af yanzu sai a nemo wata matar amma dai ba Nasreen ba.�? Sultan bashi da Karfin furta komai, sai idanu da yake bin su da shi. Haka Abba ya kasa magana, ya tabbata yau zai yi barcin wahala na rashin ‘yan biyun da ya Kwallafa ransa akansu. Yaran suna da matuKar shiga rai. Sultan kuwa tunda ya duKar da kai bai sake motsawa ba. Shiru-shiru babu wanda ya sake yin magana hakan yasa mahaifinsa ya tsargu. Yana dago shi yaga baya motsi hakas yasa Abban sake gigicewa ya Kwala masa kirs yana girgiza shi. Umma da su Hafsat suka fito 8 guje. Ganin baya motsi yasa Umma ta dora hannu akai tana ihu. Haka ma Hafsat. Shi kanshi Haidar sai da ya yi Kwalla domin suna son? Yayansu fiye da komai, kawai hudubar uwarsu suke dauka. ) Cikin Kankanin lokaci aka isa da shi asibiti. Umma ta rike keken da ake gungura shi,

tana bin nursis din Abba ya fincikota daga jikin keken yana huci, “Ina ruwanki da shi? Dama kina sonsa kika ganshi a cikin wani hali kika sake tura shi ciki? Ashe kina sonsa kike watsa masa kalaman batanci? Idan Sultan ya mutu ke kika kashe min da kuma ba zan barki ba, dan sai nayi shari’a da ke. Salma ina matukar zarginki akan bacewar yaran nan. Yau da ina da hujja a hannuna da babu abinda zai hana ban kai ki Kara ba. Amma a juri zuwa rafi.. Abba ya koma gefe kawai yana sharar Kwalla. Ya sani, ya sani duk inda Nasreen suke suna cikin mawuyacin hali. Ya fi tausayawa rayuwarsu fiye da ta dansa. Umma kuka take yi sosai, ba don danasani ba, sai don halin da danta yake ciki, Sultan yana farfadowa ya zubawa mutanen cikin dakin idanu. Tabbas ya tabbata ba mafarki yake yi ba kamar yadda yake fata ba. “Abba angano inda su Nawfal suke? Abba a ina za su kwana? Wa zai dubi maraicin su ya basu abinci? Wa zai taimaka min ya yi aikin lada ya kula min da su? Abba a ina zan samo su? Shi kenan rayuwarsu Nasreen ya tafi kenan? Me ya sa ba ka gaya min Nasrecn matata ce ba? Da ka
gaya min da na gaya mata Kalmar da take ta dako ta ji daga bakina. Da ban yi mata Karyar babu aure a tsakanin mu ba. Da na bata kulawa a matsayinta na matata ko da sau daya ne tak! Abba ba zan taba sararawa wanda ya yi min wannan yankan Kaunar ba.�? Abba ya zura masa idanu yana kallon yadda Sultan ya fita hayyacinsa a wuni guda. Shi ya san Sultan zai shiga halin da ya fi wannan ma, akan su Nasrecn. Sunkuyawa ya yi yana shafa kansa, “Sultan kai ba yaro bane, bare in ce har yanzu baka gama tantance menene Kaddara ba. Kana da hankalin tantance baki da_fari. Rayuwarmu bata tafiya a dai-dai dole sai jarabawa ta dinga ratsa mu. ‘Insha Allahu Nasreeri za ta dawo ku ci gaba da rayuwa a matsayin miji da mata. Kada ka mance Nasreen RUBUTACCIYA ce, tun tana cikin mahaifiyarta take haduwa da Kaddara, har yanzu tana rayuwa. Dole duk inda Nasreen take ta dawo domin bata da wani wurin da ya wuce nan gidan. Ka kwantar da hankalinka mu dage da addu’a.�? Lumshe idanunsa ya yi yana tunanin a wani hali suke a yanzu? Wasa-wasa sai da Sultan ya yi  kwanaki biyar yana jinyar kansa. Ko da ya dawo gidan ma sai ya koma yi masu yajin magana. A take ya kira su Mahbub ya gaya masu komai, hakan yasa dukkansu suka baro aikin su suka iso wurinsa. Barr Tajuddcen ya fara magana kamar kullum, “Sultan akwai sarkakKiya a_ cikin wannan lamarin. Ta ya ya hakan zai faru? Ta ya ya za a sace Nasreen da dan uwanta? Dole mai wannan aikin yana kusa da kai ne. Nasreen -matarka ce? Daman da ita Abba ya daura maka aure? TirKashi! Abin akwai sarKaKiya.�? Haisam ya karBe da cewa, “Ko dai mahaifinsu ya gano akwai ‘ya’yansa a gidanku ne? Zai yuwu sai kawai ya aiko a sace su.�?
Aslaf ya girgiza kai, “Ni ma tunanin da nake yi kenan, idan ba haka ba waye zai sace su?”�? Mahbub ya girgiza kai, ““A’a mahaifinsu bai san da zaman su ba, bana jin shi ne zai yi wannan aikin. A dai sake bincike.”Ashmaaan ya dago yana duban kowa, har anfidda rai zai yi magana, sannan ya tanka, “Ku natsu sosai ku dubi maganar Mahbub, Idan har mahaifin nasreen yasan suna raye, ba zai bari su kawo wannan shekarun ba, zai aika a yi farautar ransu  kamar yadda ya yi na uwarsu. Amsar wanda ya aikata hakan yana wurin Sultan domin kuwa shi ne yasan mutanen da take takun saKa da su.�? Khamis ya dan murmusa ya ce, “Dadina da kai kaifin basira dan mutan Sudan. Maganar gaskiya ba mahaifinsu ba ne ya yi aikin nan, wanda ya aikata laifin nan makusancin Sultan ne, na kurkusa. Sultan kayi sakaci gaskiya. Yaran da suke dauke da abubuwa masu rikitarwa, za kabar su kara zube? Kana da irin matsayin nan a hukumance amma kake barin ~wani lagwanin direba ya jasu zuwa Makaranta? Ai yaran nan tsaro suke bukata. Ka mance na yi irin wannan sakacin aka tafin min da mata? Ka mance Ashmaan ya yi irin wannan gangancin aka kusa kashe masa mata? Daga Karshe me ya biyo baya? Dabararsa ta Kwace shi, da ya dauke matarsa ya turata London. Shi Mahbub da ya fimu dabara, ai hada matarsa ya yi da ‘yan sanda ya kuma sanya doka mai tsanani akanta. Yanzu dai menene abin yi?�? Al-ameen ya ce, “Aikin gama ai ya gama. If not da gidajen daya daga cikin mu ya kawota aka boyeta har a gama bincike, mu zaKulo masu laifukan. Yanzu maganar bincike a kan wadanda suka yi kisa dole a dakata tunda shaidun sun Bace. Kawai mu mayar da hankali wajen nemanta.�? Sultan ya girgiza kai, “Mahaifiyata ce kadai ta tsani Nasreen da dan uwanta tsana mai tsanani. To kaina ya kulle ko ita ce za ta sanya ayi hakan domin nisanta su da mu? Sai kuma wani dan iska da ya taba zuwa wai yana sonta Wai sai ya aure ta. A lokacin bansan andaura mana aure ba, zafin da mahaifina ya dauka ya bani mamaki. Su dai nake zargi.�? Barrister Tajuddeen ya danyi rubutu ya -. dago yana duban Sultan, “Sorry to say Sultan, Umma ita ce asalin suspect! Amma kuma tafi Karfin mu gaskiya. Sai dai mu bi komai a hankali har Allah ya warware mana ‘wannan tashin hankali. Sannan zamu sa malamai suyi ta sauka suna addu’a. Allah ya bayyana maka matarka da dan’uwanta,�?
Gabadaya aka amsa da Amin. Sultan ya dan shafi sajensa ya ce, “Zan bar garin nan. Ba zan iya zama a cikin gidanmu ba, sai in ga kamar zan ga Nasreen. Yarinyar da bata ganin gabanta ya za tayi rayuwa a wurin da babu tattali? Ba zan yi aure ba, zan tsaya in jirata har ta dawo gareni.ba�? Babu wanda ya nemi ya dakatar da shi, domin dukkansu sun dandani dacin soyayya. Haka suka tashi suka yi musabaha sannan duk suka rabu. Sultan yana isowa gida ya same su suna zaune ya gaida su, sannan ya dube su fuskar nan babu fara’a. “Abba nan da wasu lokuta insha Allahu zan koma Abuja da aiki. Sai a taya ni addu’a.”�? Abba ya dube shi da tausayawa ya ce, “Sultan ya zama dole kayi aure. Ba zan zuba ido ka kai wannan shekarun babu mata ba. Ka yi hakuri kada kayi fushi, ka raya sunnar manzo. Kullum matsayi sake zuwar maka yake yi, amma ka kasa haKuri da Kaddararka.�? Shiru ya yi yana sauraren Abbansa. “Abba zan jira ta har ta dawo.�? Shiru dakin ya yi har yaushe za a tsaya jiran dawowar Nasreen? Wa ya san rana? Kyale shi kawai ya yi domin ya samu natsuwa. Umma zata yi magana ya daga mata hannu. Sultan har ya fice zai shiga dakinsa ya dawo da baya yana kallon Kofar dakin Nasreen da babu kowa a ciki. Girgiza kansa kawai ya yi ya wuce., Duk wasu  kayayyakinsa da yasan zai iiya nema ya tattara su wuri daya. Hoton da suka dauka su uku ya kafe. da idanu. Shi Nasreen sai kuma Nawfal. Ya jima yana kallon hotunan kafin ya zuba su a cikin kayansa. Cikin gaggawa aka daga shi zuwa Abuja, a lokacin ne kuma ya sauya sabuwar rayuwa.

Da asubahi suka tashi suka gabatar da Sallah,
a lokacinne kuma mai abinci ta 1so tana Kokarin hada murhu. Nasreen da Nawfal suka gaishe ta, Ya jawo hannun Nasreen ya zaunar da ita a gefe guda, ya taya mai abincin hura wuta. Duk ruwan da ake dibo mata shi ya-diba mata, hakan yasa ta fahimci yaron yana da zafin nama, duk da jikinsa yana nuna hutu. Gari yana yin haske mutane suka shiga zuwa siyan abinci, a lokacinne kuma ta zuba masu nasu abincin ya {Karasa inda Nasreen take zaune ta yi tagumi ya janye tagumin yana dubanta, ‘‘Nasreen ki daina damuwa bana so. Ga abincin ki ci, ni zan je inwanke mata kayan miya.�? Tausayin Nawfal ya kama ta, yau kwatakwata bai huta ba. Tana cin abincin tana kuka. Ta rasa ta yadda za a yi ta taimakawa dan  uwanta yau yasha wahala sosal. Basu suka samu suka zauna a inuwa ba, har sai da aka kira Magrib. Haka idanuwan mazan nan ya koma kanta. Da zarar suka fahimci makaunlya ce sai su tausaya masu. Haka basu yarda angane a wurin �? suke kwana ba. Sai da dare ya yi sannan ya zagaya ta baya ya ajiye mata ruwan wanka, saboda Amina ta basu aron bokiti da soso. Ya ce, “Nasreen ta shi kije ki yi wanka.�?

Babu musu ta tashi ta zagaya. Yana nan tsaye yana gadinta har ta gama kintsawa, ta mayar da kayan makarantarta…RiKe hannun Nawfal ta yi, tana kuka, “Nawfal kana shan wahala da yawa. Nawfal ba zamu iya wannan rayuwar ba.�? Shima riketa. ya yi “Zamu_ iya Nasreen, ki Karfafa zuciyarki zamu _ iyaWatarana sai labari.�? Da haka ya samu yake Karfafa mata guiwa, Haka suka kwana cikin cizon sauro da cinnakai, gaba daya jikinta sun yi rudu-rudu saboda azabar cizo. Washegari ta ce, “Nawfal ba zamu nemi wani wurin kwanciyar ba? Na gaji da, nan.  Sai da ya yi murmushi sannan ya ce, “Allah ya bamu.sana’a mai dan Karfi ko Daki ne mu kama sai mu ga abinda Allah zai yi. Nasreen ta yi na’am da bayanan Dan uwan nata, wanda ya fita nisan tunanin, A kwanaki biyar kadai Nasreen ta fita hayyacinta, shi kuwa Nawfal har ya fara sabawa da wahala da kuma kwanar siminti, Sultan. kullum yana ¢ikin ransa, yasha komawa gefe ya yi kukansa yadda ransa ke so, ya dawo ya share hawayensa. Ana hakanne akayiwa Amina Sata a shago, aka likawa Nawfal wai shi ya saci kudin,: Wannan abu ya yi wa Nasreen ciwo. Amma sai Nawfal ya nuna mata babu kemai jarabawa ce, Haka ta kore su a ~ gaban jama’a ta kunyata su, ta dora masu laifin sata. Suka fice titi Nasreen tana bara ana ba su kudi a nan ne suke samun na cin abinci, Nawfal ya dube ta zaune a gefen titi ya ce, “Nasreen dole mu san abin yi, bara alamun mutuwar zuciya ce da ke addabanmu ‘ya’yan hausa, bana son mu kasance daga cikin su. Gara mu bemi na kanmu Zan dinga zuwa wajen mai garuwan nan yana bani ina siyar masa sai ya bani wani abu. Ni yanzu makwancin mu yafi damuna. . Na gaji da bin kangon nan da muke yi.�? Nasreen ta sharce hawayenta ta ce, “Nawfal ina son ganin Deedi, bansan halin da yake ciki ba, Nawfal mu koma gida don Allah.�? Girgiza kansa ya yi, “Gara mu mutu a nan da mu koma gida. Nasreen Umma tana neman rayuwarki ne, idan ta kashe min ke wa zan gani inji sanyi a raina? Wacce irin rayuwe zanyi ni kadai babu ‘yar uwar haihuwata? Nasreen har yanzu na kasa yafewa Umma da ta makantar min da idanunki. Na kasa ganin farinta. Don haka kiyi haKuri da talaucin mu, mu nemi-na kanmu. Zanje wani gida mai zaure mai kyau inroka mu dinga kwana a ciki kin ji?�? Kanta kawai ta daga ba tare da ta iya furta komai ba. Zazzabi ne mai zafi ya rufeta sai karkarwa take yi. Hankalin Nawfal ya kai matuKa a tashi dole ya fice ya nemo karare ya kunna mata, sannan ya nufi Chemist da ragowar �? kudin hannunsa ya siya mata magani. Wasawasa sai da Nasreen ta koma sai andagata ankwantar. Kullum magana daya take yi masa ya kaita wajen Deedinta kada ta mutu. Shi kuma ya yi alKawarin babu inda za su sake komawa a gidan nan.�? Kasancewarsa mutum mai zuciya. Haka kuma yana da lambar Sultan akansa da ta Abba, amma yaki barin ma tasan da hakan, domin yasan za ta matsa sai an je an kira su, shi kuwa roKon Allah yake yi Allah ya Kara nesanta
Su. Sultan cikin ikon Allah ya dinga samun daukaka da kuma Karin girma akai akai wanda hankalinsa yafi kwanciya da yake nesa da mahaifiyarsa, sai dai Nasreen da take nan daram kamar yau ya fara sonta. Ya Kara kyau da haske, sai “yar rama da ya yi: Baya son magana idan ba ta kama dole ba. Haka baya ziyartar gida aikin kawai yasa a gaba. Katon gidansa babu abinda babu na more rayuwa, haka gidansa cike yake da ‘yan sanda masu kare lafiyarsa. Ya zama aiki yake yi babu ji babu gani, wanda a yanzu ya hau kujerar G Wannan girma ba shi kadai ya shafa ba, hatta iyayensa da ke garin Kaduna sai da abin ya zame masu abin alfahari, a dan shekarunsa ya taka matsayin da ba kowa yake da wannan arzikin ba. Farin jininsa a jini yake, ya zama dan gaban goshi a cikin ‘yan sanda.  Ganinsa wahala yake yiwa jama’a haka bai cika zama a gida ba, saboda ayyuka. Da zuwansa ya kawo sauye-sauye na ban mamaki. Ya zuwa yanzu ya gama fahimtar ya rasa Nasreen har abada. Sai dai kuma ya fara samun surutai a gidajen jaridu akan rashin matarsa. Tun abin baya damunsa har ya koma yana daga masa hankali. Babban burinsa. Nasreen ta dawo ta shiga dakinta. Yau a wurin aiki ya kwana, saboda wasu mahimman tattaunawa da suke yi da IG. Yana dawowa gida daya daga cikin ‘yan sandansa ya sanar masa da zuwan iyayensa. Haka kawai ya ji baya farin ciki da zuwansu. Yana shigowa ya ga mahaifinsa yana zaune yana karanta Jarida. Farin cikin ganin mahaifinsa yasa shi murmushi. Frij ya nufa ya fincike hancin Coke ya dora a cikinsa, tare da _ furta, “Alhamdulillahi. Abbana na ji dadin zuwanka.�? A Kasa ya zauna sai ka ce ba shi ba ne idan zai fita yake shan, mur, ana biye da shi kamar wani sarki, Umma ta fito ita da wata yarinya, kallo daya ya yi mata yaji wani irin tsanarta a ransa. Kai da ganinta ka ga mara tarbiyya.
Sama-sama suka gaisa, kafin Abbansa ya dube shi ya ce, “Sultan baka da alamar aure. Baka san hakan tonon asirinka bane? Duniya tana kallon kowane shige da ficenka. Girma ne ya same ka tun kana da Kananun shekarunka. Don haka mahaifiyarka ta samo maka mata har andaura auren da kanmu muka kawo maka. Nasan kai mai biyayya ne, baka taba ce min a’a ba. Me kika ce Hajiya?�? . Sultan. ya .kafe mahaifinsa da idanu, sai yanzu ya kula da wata rama da ya yi abin akwai al’ajabi. Haka ya cika da mamakin yadda mahaifinsa zai amincewa mahaifiyarsa wajen nema masa mata. A sanin da ya yi wa mahaifinsa mutum ne mai Zafi, ba ya son wargi, haka ummansa tana shakkarsa duk kuwa_ irin masifarta. Yau ga shi Abba yana mata magana cike da ladabi. Yau ga Abba yana bin dukkan shawararta. Haka ya nuna alamun tsoronta da yake ji Karara. Sake zuba masu ido ya yi yana son ganin Karshen wasan, Umma ta dubi yarinyar da fuskar nan ta sha kwalliya ta ce, ‘“Kaima Alhaji sai ka bari ingabatar da ita. Wannan dai sunanta Zakiyya,  ita ce ‘yar Hajiya Ladidi da na taba yi maka maganarta. Ba ta da matsala za ka ji dadin zama da ita. Bana son Kananan maganganu don haka nake son ka riketa da amana, ka fito da ita duniya ta santa. Ko ya kace Alhaji?�? Abba yana magana kamar jikinsa har rawa yake yi, idan har ba idanunsa ne suke yi masa gizo ba. “Haka ne Hajiya. Ai shi Babana bai taba yi min musu ba. Allah ya yi maka albarka.�? Bai iya amsawa ba, sai idanu da yake bin kowannensu da shi. Suna nan zaune mai aikinsa ya kawo masu abinci, kowa ya zuba yana ci, amma Sultan ya kasa kai koda cokali daya bakinsa. Zama ya yi kawai yana zare safar Kafarsa, ya mike yana fadin zai dan watsa ruwa. Umma ta Kyafta mata idanu Abba sai faman yashe bakinsa yake yi. Sultan yana shiga yaga mutum ta biyo shi, bai ce mata komai ba, ya rage kayan jikinsa ya shige bandaki. Abin mamaki ita ma ta _ shigo tana dubansa, “Ko dai zan tayaka ne?�? Ya zaro idanunsa yana dubanta, “Za ki taya ni fa kika ce? Wai ke ba amarya ba ce? Don Allah malama fice min a daki ki bari sai na nemeki tukun.�? Haka ta fice jikinta babu Kwari. Tunda Zakiyya ta sake dora idanunta akan Sultan sai ta ji kamar duk duniya babu namiji mai kyansa da tsarinsa. Haka unifoam yana matuKar yi masa kyau. Ko a yanzu din ji take kamar ta rungume shi. Haka dai ta yi hakuri har su Abba suka shirya komawa. Abin mamaki Abba ke rikewa Umma Jakarta. Gabansa ya tsananta faduwa. Hakan ke nuna masa barinsa gidansu gidan ya sake lalacewa ne ya Kazance. Da Kyar ya samu ya jawo Abbansa gefe yana kallonsa da rinannun idanunsa, “Abba meke faruwa ne? Abba me ke damunka haka duk ka rame? Abba Allah ba zai Kyale ni ba idan har na bari wani abu ya same ka.�? Sultan ya Karashe maganarsa kamar zai sawa Abbansa kuka. Abba ya sude bakinsa da ya bushe ya ce, “Sultan ka kwantar da hankalinka babu abinda ke damuna. Sai dai bansan me yasa ba, nake tsoron mahaifiyarku. Yanzu ba na iya yi mata musu. Abubuwa kala-kala babu wanda ba ta yi. Kawai kaci gaba da taya nida addu’a Allah yasa ~ inciye jarabawata. Sai kuma maganar Nasreen,

*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA’ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427*

🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*

             CHAPTER 9

        *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*

A JIYA MUN TSAYA

Sultan yana shiga yaga mutum ta biyo shi, bai ce mata komai ba, ya rage kayan jikinsa ya shige bandaki. Abin mamaki ita ma ta _ shigo tana dubansa, “Ko dai zan tayaka ne?�? Ya zaro idanunsa yana dubanta, “Za ki taya ni fa kika ce? Wai ke ba amarya ba ce? Don  Allah malama fice min a daki ki bari sai na nemeki tukun.�? Haka ta fice jikinta babu Kwari. Tunda Zakiyya ta sake dora idanunta akan Sultan sai ta ji kamar duk duniya babu namiji mai kyansa da tsarinsa. Haka unifoam yana matuKar yi masa kyau. Ko a yanzu din ji take kamar ta rungume shi. Haka dai ta yi hakuri har su Abba suka shirya komawa. Abin mamaki Abba ke rikewa Umma Jakarta. Gabansa ya tsananta faduwa. Hakan ke nuna masa barinsa gidansu gidan ya sake lalacewa ne ya Kazance. Da Kyar ya samu ya jawo Abbansa gefe yana kallonsa da rinannun idanunsa, “Abba meke faruwa ne? Abba me ke damunka haka duk ka rame? Abba Allah ba zai Kyale ni ba idan har na bari wani abu ya same ka.�? Sultan ya Karashe maganarsa kamar zai sawa Abbansa kuka. Abba ya sude bakinsa da ya bushe ya ce, “Sultan ka kwantar da hankalinka babu abinda ke damuna. Sai dai bansan me yasa ba, nake tsoron mahaifiyarku. Yanzu ba na iya yi mata musu. Abubuwa kala-kala babu wanda ba ta yi. Kawai kaci gaba da taya nida addu’a Allah yasa ~ inciye jarabawata. Sai kuma maganar Nasreen,

ZAMU TASHI

Sultan har yanzu babu labarinsu. Wannan ciwon na tabbata da shi zan koma ga Mahaliccina.�?  Hawayen da Abba yake Kokarin dannewa sai da suka zubo, ya sa hannu da sauri ya goge kamar mai tsoron wani ya gani. Sultan ya kasa cewa uffan har Abban ya gaji ya juya wurin motarsu da ‘yan, sanda za su jagoranci tafiyar tasu, saboda yanayin hanyar. Hannu kawai ya iya daga masu har suka fice. Cikin sauri-sauri ya shirya cikin

kakinsa ya fito hannunsa dauke da wayoyl. �? Zakiyya ta yi narainarai da idanu tana dubansa, “Ka zauna a gida ma.. Hannu ya daga mata ya wuce abinsa. Abinda bai sani ba, yana fita Zakiyya ta gayyato ma’aikatan jaridu tasa aka dauke ta hotuna, tayi bayani dalla-dalla a matsayinta na matarsa. Ta kuma cewa a daina cewa mijinta bai da mata ita ge matarsa, Kwanan Sultan biyu bai leKa gidansa ba, ita kuwa ko a jikinta. Haka tana sane da ya sallami mai girkin gidansa kasancewarsa namijl, amma ko sau daya ba ta taba Sa tsintsiya ta share ko da falo ba. Haka ruwan fridge ya dinga zuba  yana shiga KarKashin kafet din, nan da nan dakin ya dauki wari. Kitchen kuwa wasu abubuwan da ba a sanya a fridge ba, har sun lalace suna wari. Ko a jikinta, ita dai idan ta samu ta ci abinda take son Ci, Za ta nemi wuri a falo ta sa film din batsa tana kallo. Gabadaya Sultan ya mance da Allah ya yi ruwan wata Zakiyya a cikin gidansa. Tunanin halin da mahaifinsa yake ciki ya fi komai daga masa hankali. Kai tsaye ya gane mahaifiyarsa ta yi amfani da bokayen tsubbu domin cimma burinta. Mahaifiyarsa ta yi nisan da ba ta jin kira, �? tayi nisan da take mance girman Aljannah, da kuma abubuwan da ya kamata ta bi domin shigarta Aljannah. Gabansa ne ya fadi da Karfi da ya tuna da Kannansa da ke cikin gidan, yana —tsoron lalacewar tasu tarbiyyar. Ya zama dole ya je idan har abin da matsala ya kwashe su daga gabanta. Yana tsoron bakin da Umma take yi wa ‘ya’yan wasu ya faru akan ‘ya’yanta. Duk yaron da ta gani dan iska ne, nata ne masu kirki. Kowa ta gani mazinaci ne, nata ne masu kare kansu daga sharrin zina, kowa ta gani aron addininta suka yi,
nata ne wadanda suke da asali a cikin addini. Ta ya ya Allah ba zai aiko da jarabawa cikin gidansu ba? Ta ya ya Zakiyya ba za ta zamo matarsa ba? A bayyane ya yi magana, “Ya Allah! Ban kasance mazinaci ba, kada ka jarabceni da rayuwa da mazinaciya. Allah ban taba jayayya da yinka ba, kada ka jarabceni da_laifin mahaifiyata. Allah mahaifina bai ° kasance azzalumi ba, kada ka jarabce shi da macen da za ta zalunce shi. Allah ka warware mana wannan matsalar da ke tunkaro mu, ka kare min Kannena a duk inda suke. Allah ka bayyana min Nasreen da dan uwanta cikin Koshin lafiya.�? Zare rigarsa ya yi ya kama hanyar gidansa jikinsa a sanyaye. Har a lokacin babu dan sandan da ya gaya masa cewa Zakiyya ta gayyato ‘yan jarida. Yana sa Kafafunsa a cikin gidansa hankalinsa ya ninku a tashi. Ransa ya yi mugun baci, ya dubeta rai a Bace ya ce, “Ke ba ki da hankali ne? So kike ki mayar min da gida dafidalin wari? Ko bola kika samu ne? Ki tashi ki gyara gidan nan tun kafin bacin raina ya sauka akanki.�? Jikinta yana rawa_ saboda_tsoron  yanayin da taga Sultan, ta wuce kitchen domin dauko tsintsiya. A lokacinne ya bayyana a kitchen din. Ya ma kasa magana saboda azabar warin da ya ziyarci hancinsa. Dole ya sa hannu ya toshe hancinsa. Haka ya koma hankalinsa a tashe. Sultan ya tsani Kazanta fiye da tunanin mutum, dakinsa ya koma ya kwanta yana kallon sama, cikin tunanin da shi kansa bai san ko na menene ba. Nazari yake yi ta yadda za a yi ya iya rayuwa da Zakiyya a matsayin mata. Yana nan kwance bai motsa ba, ta gyara dakunan sama-sama ta je ta sheKa wanka ta antaya maganin da uwarta ta ba ta, sannan ta Kara shiga ruwan zafi, kamar yadda Hajiya Ladidi ta karanta mata, domin aikin da aka yi mata don ta koma budurwa har yanzu tana dan jinsa. Ita kanta yadda aka dinke ta abin yana bata tsoro, haka tana shakkar zai iya ganewa cewar ita ba budurwa ba ce, idan hakan ya faru tana da tabbacin Sultan korar kare zai yi mata. Shi kuwa wanka ya shiga ya fito daure da tawul yana tsane ruwan jikinsa. Ta shigo dakin babu ko sallama, kallo daya ya yi mata ya dauke  kansa gabansa yana fadiwa. Babu laifi yarinyar tana da kalar tata kyan, sai rashin kamun kai da ke dawainiya da ita. Jikinsa ta Karaso tasa hannu ta rungume shi. Kamshin maganin da ta yi amfani da shi, ya yi ta dawainiya da shi, don haka ya fara mayar mata da martani, da taimakon tsaftace jikinta da ta yi. Ba shi ya farka ba, sai da asubahi. Ware idanunsa ya yi yana duba irin barnar da ya yi wa ‘yar mutane. Mamakin samunta a budurwa yafi komai tsaya masa a rai, domin yadda yaga bai taya taba, ita ta fara kawo kanta yasan da matsala. Haka wannan budurcin da ya samu ya sanya ya Kara ganinta da girma da mutunci a idanunsa. Gabadaya zanen gadonsu ya lalace da uban jini. Tana nan kwance kamar kayan wanki tana shakar barcinta. Mamaki ya sa ya kafe ta da ido, yaushe za a yi wa mace hakan ta kwantar da hankalinta? A hankali ya zame kansa ya shiga bandaki ya tsaftace jikinsa, kafin ya sa hannu ya tasheta, tana bude idanu ta fara magana cikin magagi, “Bilal ka rabu da ni barci nake ji.�? Sultan ya zaro idanu yana sake dubanta, “Bilal kuma? Waye Bilal?�?  Ware idanunta ta yi gabanta ya fadi da Karfi, sai yanzu ta tuna abinda ya faru, don haka ta fara raki, “Wash! Don Allah ka taimaka min ba zan itya tashi ba.�? Sultan dai kallon ta kawai yake yi, haka kuma zai iya makara yin Sallar asuba, don haka yace “Ki yi haKuri Zakiyya zan makara.�? Ya sa kai ya fice abinsa. Yana fita ta mike ta shige bandaki ta gasa jikinta, sannan ta cire zancn gadon ta shimfida masa wani ta sake hayewa gadon tana shaKar barcinta. Babu Sallah bare Salati. Yana dawowa ya dube ta yana tantaman anya ta yi Sallah? Sai kuma ya kau da wannan tunanin a cikin ransa, ya yi tagumi. Wannan ranar ya tanadarwa Nasrcen dinsa, sai ga shi a lokaci guda Allah ya yi ikonsa, wanda babu wanda ya isa ya yi jayayya da yinsa. Shirin zuwa office ya fara, yana tunanin dole sai an samo ma’aikata sun yi masa gyaran gidansa domin har yanzu wari yakeyi sosai. Tashinta ya yi yace ta koma dakinta zai rufe Kofarsa. Ba ta yi mamakin rashin mutuncinsa ba, domin tuni ta fara haddace su. Tana dingishi ta fice.
Faruwar wannan lamari tsakanin Zakiyya da Sultan ya sanya mata wani irin sonsa, a cikin zuciyarta kamar ta mutu. Tana jin bata taba  mu’amala da wani namijin da ya gigita tunaninta irin Sultan ba. Duk inda ake neman namiji mai mantar da mace damuwarta, Sultan ya hada abubuwan nan. Tana jin ko dukanta zai dinga yi kullum ba za ta rabu da shi ba. Haka ta raina iyawar Bilal duk yadda take yabonsa kuwa. Shi kuwa ya kasa farin ciki da irin sabon lamarin da ya shiga, abin ya kasa burge shi, haka shi bai san yadda budurwa take ba bare ya fahimci abinda Zakiyya ta yi. Yan sandan ya basu umarnin su samo masu aiki a tsaftace masa cikin gidansa, a fitar da dukkan abubuwan da suka lalace.. Jaridar da ya samu a cikin motar ya dauka yana dubawa. Gabansa ya fadi da ya ga hotonsa hade da na Zakiyya. Cikin sauri ya ware ya fara karantawa. Ya gigita iya gigita, don haka ya ce wa direba ya juya gidan. Yana fitowa daga mota ya dubi-~daya daga cikin ‘yan sandansa yana tambayarsa yaushe akayi wannan hirar? Cike da tsoron yadda ya ga yanayin Ubangidansa ya gaya masa komai. Sultan ya daga hannu ya wanke shi da mari, ya sake daga hagunsa ya dauke shi da mari yana huci. “Ashe baka san aikinka ba aka kawo min kai? Ashe idan kashe ni za a yi zaku iya ba barawon hanya? A cikin gidana zaku bar ‘yan jarida su shigo har falona? Wannan wani irin shirme ne�?  sandan ya ce, “Sorry sir! Mun so mu hana su, madam ta fito ta zage mu ta ce su shigo.�? Sultan ya daka masa tsawa, “Ka yi min shiru bana son bayanin nan. Ita kuke yiwa aiki a gidan nan ko kuwa ni? Daga yau babu wata mace da za ta sake sa doka wani a cikin ku ya bi, ba tare da ya tuntubeni ba. Saboda kune sakarkaru har ayi wannan abun tsawon kwanaki babu wanda ya taba gaya min? A kan me?�? Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, za su iya rantsewa tunda suka fara aiki da shi, ko tsawa babu wanda ya taba yiwa, amma yanzu harda mari, lallai ankai shi Karshe kenan. A fusace ya taka ya shige dakin Zakiyya. Tana zaune tana waya tana bada labarin yadda suka kasance da Sultan, wanda karaf a kunnensa. A duniya ya tsani mace mara sirri, ji yake kamar ya shaketa ya huta. Tana ganinsa ta cire wayar tana zare idanu. “Ke ashe baki da hankah? Da izinin uban wa kika je kika yi hira da ‘yan jarida? A ina kika sami lambarsu da har kika gayyato min su cikin gidana?�? Yadda ya harde hannayensa ya kafeta da idanu ta gane amsar kawai yake buKkata, ta ce, “Wata Kawata ce da ke aiki a gidan jarida, ta hada ni da su, shine suka zo. Kayi haKuri bansan zai bata maka rai ba.�? Sultan mutum ne mai son

*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA’ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427*

🦚RUBUTACCIYA BOOK 1 KARSHE🦚*

        CHAPTER 10

       *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*

A JIYA MUN TSAYA

sandan ya ce, “Sorry sir! Mun so mu hana su, madam ta fito ta zage mu ta ce su shigo.�? Sultan ya daka masa tsawa, “Ka yi min shiru bana son bayanin nan. Ita kuke yiwa aiki a gidan nan ko kuwa ni? Daga yau babu wata mace da za ta sake sa doka wani a cikin ku ya bi, ba tare da ya tuntubeni ba. Saboda kune sakarkaru har ayi wannan abun tsawon kwanaki babu wanda ya taba gaya min? A kan me?�? Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, za su iya rantsewa tunda suka fara aiki da shi, ko tsawa babu wanda ya taba yiwa, amma yanzu harda mari, lallai ankai shi Karshe kenan. A fusace ya taka ya shige dakin Zakiyya. Tana zaune tana waya tana bada labarin yadda suka kasance da Sultan, wanda karaf a kunnensa. A duniya ya tsani mace mara sirri, ji yake kamar ya shaketa ya huta. Tana ganinsa ta cire wayar tana zare idanu. “Ke ashe baki da hankah? Da izinin uban wa kika je kika yi hira da ‘yan jarida? A ina kika sami lambarsu da har kika gayyato min su cikin gidana?�? Yadda ya harde hannayensa ya kafeta da idanu ta gane amsar kawai yake buKkata, ta ce, “Wata Kawata ce da ke aiki a gidan jarida, ta hada ni da su, shine suka zo. Kayi haKuri bansan zai bata maka rai ba.�? Sultan mutum ne mai son mutumin da

ZAMU TASHI

zai aikata kuskure ya kuma amsa ya aikata har ya bada hakuri. Don haka ya sassauto, “Ki kiyaye kanki, ki kiyaye mutuncinki, matar aure ce ke, bai kamata ace kin fito a haka a gidan jarida ba, kamar ba matar aure ba. Idan kin siya min mutunci kanki kika siyawa. Daga Karshe kada wani ya sake shigo min gida ba tare da izinina ba, yin hakan zai jawo maki tarin matsalar da baki taba tunani ba.�? Ya juya abinsa cike da takaici. Ashmaan ya kira shi a waya, sun jima suna tattaunawa, sannan suka yi Sallama. Yana isa office yaga babu wani aikin kirki, ya shirya motar ‘yan sanda suka kama hanyar Kaduna. Nasreen tana zaune ta hada kai da wani abun, gaba daya ta yi baki, ta rame ta sauya daga Nasrcen din Sultan ta koma Nasrcen Kankia. Nawfal ya koma kamar mai sana’ar bola, haka duk inda ake meman dan uwa Nawfal ya wuce hakan. Hakika da babu Nawfal da rayuwar Nasrecn ya zama abar Kyama. A zaman su maza sun sha kawo mata farmaki, Nawfal ke tsayawa kai da fata wajen ganin ya kareta. A Kalla da zuwansu garin nan, sun yi sana’a yafi kala ashirin. Haka sun

kwana a wurare mabambanta, A yanzu haka ma Kosai ya siyo mata ya ajiye a gabanta tana ci, sai da ta gama sannan ta fara shan kokon, idanun Nawfal suka hasko masa hoton Sultan. Ya yi saurin dauka yana dubawa. Hotonsa ne tare da matarsa. Nawfal ya kafe su da idanu, ya gama karantawa yana al’ajabin irin wannan matsayin da Sultan ya samu, wanda a yanzu wane su su iya tunkarar gidansa? Bakinsa ya subuce ya ce, “Nasreen Deedinmu ya tare da matarsa yanzu ya zama A.I.G Kin ga yadda ya Kara kyau kuwa? Sai dai matar ko lullubi babu a jikinta.�? Nasreen ta gigice iya gigicewa ta hau lalube, “Nawfal a ina ka gani? Ya zan yi in gani ni ma?�? Bai dube ta ba ya ci gaba da duban jaridar Kosan, “A jarida na gani, wanda a ka Kunsa maki Kosai. Nasreen ke da ba idanu gareki ba ya za a yi ki iya gani?�? Nasreen ta goce da kuka. Hakan yasa Nawfal ajiye jaridar ya kafeta da idanu ya rasa me zai ce mata kawai sai ya zuba mata idanunsa wanda shima hawayen ke zuba daga kwarmin idanunsa. A hankali ya fara magana, “Kin gani ko? Deedi ya fi Karfinmu a yanzu. Dole zamu ci gaba da zama a nan, domin gujewa abinda zai sa hankalinsa tashi. Na san soyayyar da zamu nuna masa kenan mu yi nesa da su. Ki kwantar da hankalinki akwai ranar da wahalar nan za ta zama labari.’�? Muryar wani suka ji yana cewa, “Alhamdulillahi gasu can a lungun can.�?
Nawfal duba Nasreen yace, “Mun shiga uku, waka gani waye?�? , ne Mansur ya Karaso yana kwasar dariya, “Nasreen ni ne nan mijinki Mansur. Zuwa nayi insauya maku rayuwa inkuma ajiyeki ki zama matata.�? Nawfal zai yi magana, wasu suka kama shi suka tura cikin mota, haka ita ma Nasreen din aka dauketa sai mota. Lalube ta shiga yi tana neman Nawfal, hakan yasa ya kama hannayenta, ta shafa fuskarsa zuwa kansa ta tabbatar da shi ne, don haka ta saki ajiyar zuciya. Ta riga ta sadakar mutuwa za ta yi, ta fi son idan za a kasheta Nawfal ya kasance yana kusa da ita. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske, kafin suka sauka a wani Kauye. A kuma Kofar wani gidan Kasa. Haka suka sauka suka shiga ciki Mansur ya umarci mutanansa da a shigar da su. Nawfal ya ce, “Dakata! Za mu iya shigar da kanmu ba sai wasu sun sake taba mu ba. Ya kamo hannun Nasreen suka shige ciki. Mansur ya nuna masu daki ya ce su shiga zuwa anjima zai zo. Haka suka shiga suka dunKule wuri guda daki komai sai ledan Kasa. Aka kawo musu abinci maradadi, haka suka tuttura suka sha ruwa
Mansur bai bata lokaci ba ya dawo hannunsa dauke da kwanon sha cike da fura yana isowa gabansu ya dubesu duba a tsanake sannan ya fara magana, “Na sha matuKar wahala wajen nemanki Nasreen. Hajiya Salma ta bani aiki akanki, domin in aureki in wahalar da ke, a lokaci guda kuma sai na ji ina son ki da gaske. Da naje gidanku sai Sultan ya watsa min Kasa a idanu, ya wulaKanta ni, ya shake ni yana neman ya kai ni inda ban shirya zuwansa ba. Ina cikin shirya wa Sultan kawai naji labarin Hajiya Salma tasa a sace ku saboda wasu dalilanta marasa tushe. A ranar da na sami labarin nan na yiwa Hajiya Salma gargadi akan duk abinda ya sameki ita ta siya da kudinta dan sai na fanshe bacin raina akanta. Hakan yasa ta tsorata ta gaya min inda aka kaiku. Daga Karshe take sanar min ashe kece matar da aka daura maki aure da Sultan. Bacewarki ya sa mahaifinsu gaya masu gaskiya, Sultan mijinki ne.�? Nasreen da Nawfal suka ji dirar maganarsa kamar wani labari wanda ba zai taba faruwa ba. Ta gigice, ta shiga rudu, tana son ta Karyata shi domin Nawfal yaga jarida dauke da matarsa. Don haka ta girgiza kai tana kuka, “A’a ni ba matarsa ba ce, matarsa a yanzu haka tana gidansa.�? Mansur ya kafe ta da ido, duk da ta lalace, amma har yanzu yana sonta, kuma da gaske yake ya shirya fuskantar kowacce irin matsala akanta. Zai jure koma menene yaga ya mallake ta.  Girgiza kansa ya yi yana murmushi, “Ke ce matar Sultan ta farko, daga baya ne da aka yi ta jiran dawowarki aka ga shiru sai Hajiya Salma ta shiga ta fita ta mallake Abbanku, daga nan aka hada aurensa da Zakiyya ‘yar wajen Hajiya Ladidi, ba tare bada saninsa ba, sai ganin mata ya yi. Ya so ya ci musu ya Ki karbanta a matsayin mata, sai mahaifinsa ya yi masa nasiha, kasancewarsa mutum ne mai jin maganar mahaifinsa shi ne ya karbi Zakiyya a matsayin mata. Allah kadai ya sani ko suna zaman lafiya ko basa zaman lafiya. Amma tabbas ke matar aure ce, matar Sultan, Zakiyya ita ce matarsa ta biyu. Ni kuma ina son ki a yanzu haka, na shiryawa mutuwa akanki. Ki yi tunanin mafita, ina sonki babu idanun zan iya zama da ke. Zuwa anjima zan dawo in ji shawarar da kika yanke, ko aurena, ko kuma ki zama dadirona.�? Mansur ya miqe ya fice, ya barsu cikin tashin hankali mara yankewa. Nasreen ta labubo hannun Nawfal ta ce, “Nawafal saita ni gabas don Allah.�? Nawfal ya saita ta ta kai goshinta Kasa ta yi sujjada, “Allah na gode maka. Allah kai ne Allah, Allah ka bamu ikon bauta maka a bisa hanya madaidaiciya. Allah kai ka shirya wannna lamarin ka kawo min Karshensa. Allah na gode maka da ka  amsa addu’ata a lokacin da ban za ta ba. Allah ka nuna min ranar da mijina zai dawo gareni.�?
Farin ciki ya kama Nawfal ta yadda bakinsa ya kasa rufuwa. Haka ya shiryawa komawa ya damKawa Sultan matarsa. Ya kafe Nasreen da idanu yana kallon yadda take cikin farin ciki da annashuwa, wanda rabon da ya ga hakan tun suna gidan su Sultan. Daga baya kuma ya ga ta fara kuka tana magana cikin kuka, “Me muka yi wa Umma haka? Me yasa za ta sa rayuwar Abbanmu a cikin matsala? Duk Kokarin da Abba yake yi don yaga ya faranta mata sai da ta kai shi mahallaka? Me ya sa Deedi zai auri Zakiyya? Umma da kanta take siyo masifa tana kawowa cikin gidanta da sunan gyara? Rayuwar Abba a yanzu shi yafi bani tausayi. Yanzu tuntuni ni matar aure ce? Dama goron da Abba ya kawe min cikin farin ciki na daurin aurena ne? Me yasa Abba bai gaya min ba? Ina tafe da igiyar aure akaina ban sani ba? Allah ka sake hada idanuna da suke rufe da mijina ko da sau daya ne. Nawfal yanzu za ka daina nesanta ni da mijina? Yanzu ka amince son da nake yiwa Deedi a cikin jinina yake? Ka amince Allah ya riga ya hada jinin mu da su Umma? Abu daya ya rage mana shi ne mu gano su waye danginmu? A ina suke? Waye zai gano mana su? Deedi kadai yake da amsar wannan tambayar.�?
Nawfal yasa hannu ya goge mata hawayen fuskarta, “Nasreen ba wannan ne a gaban mu ba, abinda ke gabanmu yafi Karfin wannan. Ta ya ya zamu iya rabuwa da mutumin da ya kira kansa da Mansur? Yanzu yafi Umma zama matsala a cikin rayuwar mu.�?
Cak! Ta daina kukan, ta yi shiru kamar mai tunani, “Nawfal tunani ya Kare min, ban san ya zanyi ba. Mu ci gaba da addu’a kawai.�? Dakin ya yi shiru Kowa da irin tunaninsa. A haka Mansur ya dawo ya same su, ya yi maganar duniya babu wanda ya iya ce masa ko zo ka c1 kanka. Sultan ya iso Kaduna cikin awannin da basu gaza biyu ba, ya wanzu a Kofar gidansu. Kallo daya ya yi wa gidan Nasreen ta fado masa a rai. Har ya juya ya ji muryar mahaifinsa yana masa sannu da zuwa. Ya dubi mahaifinsa sosai, a irin wannan lokacin kamata ya yi ace yana Office.
Tare suka shiga ciki suna rike da hannun juna. “Abba barka da gida.�? Bai amsa ba, sai da ya dire shi a falon, sannan suka zauna. “Sultan idonka kenan?�? Kafe hoton Nasreen ya yi da idanunsa har yanzu ba a cire hoton ba. “Abba ka yi haKuri na kasa . mance Nasreen. Abba komai ya sauya a rayuwar gidanmu abin yana ba ni tsoro. Ina Umma?�?  Abban ya dan yi shiru kafin ya ce, “Bana dan jin dadi ne shi ne na turata Office din taje ta sallami mutanen da suka yi Order tasa hannu.�? Sultan ya girgiza kai yana al’ajabin yadda Umma za ta shiga harkar da ba nata ba. Haka kuma duk tsauri irin na Abba yau shi ne yake ba Umma izinin tafiya Office dinsa? Hafsat ta shigo ya kafeta da idanu, ta yi wani irin haske ta rame. “Barka da zuwa Yaya.�? Murmushi ya yi ya mika mata hannu ta Karaso kusa da shi tana sunkuyar da kal, “Hafsat babu abinda ke damunki ko?�? Girgiza kai ta yi tana sake duKar da kai. Sallamar Umma da Hajiya Ladidi yasa duk suka bi su da kallo. Hajiya Ladidi tana shigowa ta kwaye lullubnta tana satar kallon Abba. Ta jima tana kwadayin Alhaji Lukman a matsayin miji, amma bai taba kallonta ba. Sultan ya dan rankwafa ya gaida su, suka amsa cike da farin cikin ganinsa. Hajiya Ladidi ta ce, “Oh ashe kai ne a tafe? Shi ya sa muka ga garin hadari ya hadu. Ya su Zakiyyan? Ai mun ga �? hira a jarida hira ta yi kyau sosai.�? Sultan ya kauda kai kamar bai ji ba, ya dubi mahaifiyarsa ya ce, “Umma daga ina haka?�? Tana shirin yin magana Haidar ya shigo yana sunkuyar da kai. Mamakinsa ya karu. Me yasa yaran basa son hada idanu da shi ne? Bayan sun �? gaida shi  ya dubi Haidar ya ce, “Haidar ka kammala karatunka me kuma kake jira?�?
Ya dan sosa kai, “Har yanzu aikin bai fito bane.
Jinjina kansa ya yi, “Ka ba ni takardunka soja zan turaka. Zan ba Khamis shi zai yi maka komai.�? Haidar baya son aikin soja, hankalinsa ya fi kwanciya a irin aikin Yayansa, amma kuma ba shi da yadda zai yi dole ya yi shiru kuwai. “Umma ki ba ni Hafsat intafi da ita Abuja.�? Hafsat ta zaro idanu, yadda ta tsani takura idan ta koma gidansa ai ta shiga uku. “Ni dai Yaya nafi son nan.�? Bai ce komai ba ya mayar da hankalinsa kan mahaifiyarsa da gaba daya ta sauya kamar ba ita ba. Umman ta daure fuska sosai, “Lafiya kake kallo na haka? Ni ka sanni Sarai na tsani irin kallon nan mai kama da na raini.�? Murmushi yayi sannan ya dubi agogo, “Ya kamata in zo inkoma kada inyi yamma.�? Abba ya girgiza kansa, “Babu inda za ka je, muna da bukatarka yau a gidan nan. Ka bari sai gobe sai ka koma.�? Sultan bai zo da niyyar kwana ba, don haka ya fara zare agogonsa zuwa cire takalminsa. “Abinda  kace ayi shi za a yi Abba. Idan ma kace in ajiye masu kakinsu indawo gida hakan zan aikata.�? Abba ya ji dadin kalaman Sultan ba kamar su Haidar ba, da kullum suke yi masa rashin kunya. Zuwan Sultan ne yasa suke yi masa komai cikin girmamawa. Ya Kosa Hajiya Ladidi ta tafi, amma sai ta zauna a tsakiyarsu ta hana su motsawa. Hakan yasa ya dubi Abban ya ce, “‘Abbana zan je gidan Hajiya Gwaggo.�? Abban ya mike yana satar kallon Hajiya Salma, “Muje nima na rabu da zuwa wurinta.�? Sultan ya dan dakata yana kallon Abbansa. Bai iya yin magana ba, suka fito aka bude masu mota suka shiga. Sun fara tafiya ya dan waiwayo ya dubi Abba, “Yanzu Abba kana nufin Hajiya Gwaggon baka zuwa duba ta?�? Abba ya hadiye yawu da Kyar ya ce, “Wato Sultan Hajiya Salma ta wuce duk yadda kake tunani. Ta kama komai ta yi kane-kane a kai. Yaran nan kada ka so kaga rashin kunyar da suke yi min. Ni na gaji watarana zaku iya nemana ku rasa.�? Sultan ya yi shiru bai yi magana ba, gudun kada ‘yan sandansa su ji sirrin cikin gidan su. Hajiya Gwaggo tana jin murya ta tsaya kawai tana kallon su, kafin tai wuf ta shige cikin daki tana share
hawayenta. Abba ya durKusa a gabanta yana roKo.  amma ko kallon sa ba ta yi_ ba. Sultan ya harde yana dubansu, har sai da ya tabbatar da ba za ta yi maganar da gaske ba, sannan ya shigo ya zauna kusa da ita. “Hajiya fushi kike da Abbana? Hajiya kin taba zama kinyi tunanin dalilin da zai sa danki ya gujeki bayan yafi kowa zumunci duk_ cikin ‘ya’yanki? Ashe danki ba zai iya shiga hatsari ki jawo shi jiki ki ji matsalarsa ba? Hajiya kin taba zama da danki kin ji matsalarsa? Mahaifina yana cikin wani halin da yake da buKatar addu’arki.�? Sultan ya Karashe maganar idanunsa jazir, yana jin da zai iya zubar da hawaye babu shakka mahaifinsa zai fara yiwa kuka.�? Hajiya ta dan sassauto ta dubi Sultan ta ce, “Sultan har gidansu naje a gabansa Hafsat da Haidar da uwarsu suka wulaKanta ni, amma ya kasa magana. Ban yi fushi ba, na sake dawowa haka suka sake cin mutuncina. Kai ba zan. taba mance wannan abun ba.�? Sultan ya dan yi shiru kafin ya girgiza kansa, “Hajiya ki yi hakuri. Abba ya sauya daga Abban da muka sani shekaru talatin baya. Umma tana neman tasa Abba a wani hali. Hajiya kiyi wa Abba addu’a ta haka ne zai sami sassaucin abinda ke damunsa. Abinda yasa na tsani zuwa gida Hajiya kin sani, saboda su Nasreen. Da zarar na shigo sai zuciyata ta dinga gaya min zan gansu a kwance a daki. Hafsat  kuma da Haidar ki zuba ido ki ga irin matakin da zan dauka akansu. Kin wuce mu tsaya muna kallon wasu su wulakanta mana ke, bare kuma mu da kanmu.�? Haka ya yi ta ba ta baki har ta sauko ta kuma sawa Abba albarka, wanda yake jin kamar ansauke masa wani tarin kaya ne a kansa. Hajiya Gwaggo ta kawo masu_ tuwon shinkafa, suka ci kwano daya da mahaifinsa, sannan ‘suka bar gidan. A hanya suka wuce gidan Alhaji Mu’azzam, wanda ya fada harkar siyasa babu ji babu gani, kullum yana gidajen radio yana kumfar baki. Shi kansa ya ji dadin ganin Sultan har ya nemi taimakonsa akan abubuwan da yasa a yaba, Sultan ya nuna masa babu damuwa. Abin mamaki har suka dawo Hayjiya Ladidi tana nan a gidan, hakan yasa ya wuce dakinsa yana kallon yadda aka tsaftace dakin.
Shiru ya yi yana tuna ranar da ya kasance tare da Nasreen, wannan daren ya kasa Bace masa, haka sai da aka gaya masa matarsa ce ya tuna da irin murmushin da Abban ke jifarsu da shi a ranar da ya kamata ya yi masu fada. Rintse idanunsa ya yi, Ashmaan yana can yana bincike a kan mutuwar mahaifiyar su Nasrcen, ya Ki bari wai sai sun bayyana tukunna, kamar yadda suke tunani. Yana nan kwance ba barci yake yi ba, jira yake Hajiya Ladidi ta bar gidan ya ci mutuncin° Kannansa, domin abinda suka yi wa Hajiya Gwaggo ya tsaya masa a rai. Daga dakin yake jiyo surutai hakan yasa ya fito yana duban yadda Hafsat da Haidar suka hayayyakowa mahaifinsu, suna cewa yaje ya kwashe komai ya gayawa Sultan. Sultan ya kirawo ‘yan sandansa ya ce yana son su sauyawa Haidar kamanninsa. Ita kuma Hafsat ya zare belt ya dinga auna mata. Umma fa ta gigice, sai ta yi wurin da ake dukan Haidar da gudun gaske tana kuka, sai kuma ta koma tana zagin Sultan tana cewa idan bai daina dukan Hafsat ba za ta tsine masa. Ko kallon ta bai yi ba, hukunci kawai yake yi. Sai da Abbansa ya yi magana sannan ya dakata da dukan Hafsat ya kuma dakatar da dukan Haidar, wanda tuni ya zube a nan yana numfarfashi. Sultan ya dinga masifar da ya basu tsoro, ya botsare masu ya sauya kamar ba Sultan din da suka sani ba. Yana ji a ransa ba zai iya barin mahaifinsa a cikin gidan nan ba, kada watarana su kashe masa mahaifi su barshi da maraici. A take ya kira Khamis ya zayyane masa komai, Khamis ya ce, kawai ya turo shi Abujan shi zai yi maganinsa, kuma dole ya tafi aikin sojan nan. Don haka Hafsat kadai zai barwa Umma a gidan. Umma ta Karaso tana masifa ya dube ta duba sosai ya ce, “Umma zan dauke mahaifina daga gidan na rasa me ke masa dadi? Tunani ne fal a cikinsa. Ji ya yi ankwanta a bayansa, bai hanata ba, haka bai hantareta ba, kamar yadda zuciyarsa ke gaya masa, Haka ta shammace shi suka sake komawa wata duniyar. Shi dai ko dan bai saba bane? Idan ba haka ba, ya kasa jin wani abu mai kama da dadin kasancewarsa da ita. Amma kuma tana da Kima a idanunsa musamman da ta kama kanta. Barci take shaKa harda minshari, wannan abu ya sake daure
“masa kai. Minsharinta ya dame shi Kwarai domin ya tsani namiji ma mai minshari bare kuma mace,
Bubbuga ta yayi ta farka tana sake luma idanunta a
cikin nasa; Zakiyya wata irin jarababbiyar yarinya ce, wanda a farko ta yi masa kawaici amma a yanzu ba za ta iya ba, ya zama dole su sake komawa duniyar da suka fito. A idanunta ya fahimci abinda take nufi, ya ce, “TirKashi! Ni mace ma ba ta gabana bare har in iya yin abinda kike nufi.�? �? Mikewa ya yi ya shige bandaki ya sa key Zakiyya ta mike ta shige dakinta tana cizon yatsa Ya riga ya dandana mata zuma mai wahala mancewa. Shigewa dakinta ta yi ta kira mahaifiyarta, “Momi mutumin nan fa ya iya komai Naji dadi da kika hada ni da shi. Wallahi yanda nake jin sa babu abinda zai raba ni da shi, gashi baya ~ son hayaniya.�? A nan ta yi ta ba mahaifiyarta labarin yanayin Sultan, wanda karaf sai a kunnensa.

MU HADU A LITTAFI NA BIYU

*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA BOOK 2&3&4 da UMM ADIYYA by aziza Idris gombe  kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427*Idan baki shirya siye ba kada kiyiman magana ki bari saikin shirya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button