Sponsored Links
Captain Sadiq Hausa NovelHausa Novels and Love Stories

Captain Sadiq Hausa Novel

Sponsored Links

[3/8, 5:34 PM] Salma😝: CAPTAIN SADIQ
👮🏼‍

written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Blood sister deejah

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM 🐄

follow me on wattpad username:  salmamasudnadabo
1_2

    Yarinya ce yar shekara 10 na hango, tana tafe tana rusa kuka kamar anmata mutuwa, fara ce sosai ita ba siriri ya ba, ita ba lukuta ba, d’ankwallinta ne a hannu hakan ya sa na kalli gashin kanta, bak’i ne sosai amma saboda tsabar datti yayi jawur, kallo d’aya na mai na gane mai laushi ne, rashin kullawa ne yasa yayi haka, Hancin ta yayi jaga-jaga da majina, gata da manyan ido,tana tafe tana kukan, dan ba dainawa tayi ba, dai-dai wani madaidaicin gida ta tsaya chak, gidan kasane natallakawa sosai, dan ko k’ofar gidan bata samu ishashiyar kofa ba, Ihu ta Kara saki kamar an watsa mata ruwan zafi, inna da ke kurya d’aki ta fito tana gyara zani, inda sabo to ya kamata ta saba da halin fatuha, amma ba yadda ta iya dole ta fito inba fitowa tayi ba to wallahi sai  dai maqota su fito, ganin inna ta leko yasa fatuha tuma a k’asa tana ihu.
inna ta gyara tsayuwa. ta ce,  “ohni fatuha nabani yau kuma wakika tsokana kika ci duku, fatuha ciki murya tsiwa irin na yara masu wayau masu rashin ji ta ce “inna wallahi tallahi kwarankwatsi dubu bani na tsokane shi ba inna” ta k’ara rushewa ta saban kuka inna  ta san halin ta sarai shiyasa ta ja bakin  ta tayi shuru can  kuma  ta ce, “to fatuha waya bige ki?
“wallahi inna Rabi’u ne  ya bigeni har da taka min ruwan ciki” ta k’ara rushewa da saban kuka  kuma inna billahilazi ba zan yarda ba”  ta inda zancan tana katse majina hancin ta  saboda inna ta san karya irin  ta fatuha tasan ba yarda za’ayi rabi’u ya bige ta har ya taka mata ruwan ciki, sai dai in laifi ta masa kuma ko bugun ta yayi bai taka mata ruwan ciki, qila ma satan mangwaro taje  ya kamata Inna  ta  ce, “yi hakuri fatuha ki kyale shi kin ji kuma kiga Rabi’u ba sa’an ki bane kin ji diyar baffan ta”
“kambuuuu..! ta zaro manya idanuwan ta “qur’an inna ban hakura..!
“haba fatuha yi hakuri Zan baki biyar kin ji”  washe baki tayi kamar ba ita ke ihu da koke-koke ba ta  ce, to inna na hakura kwarankwatsi” Inna ta washe baki fatuha ko ba wai har cikin zuciyar ta ta hakura ba,  dan ta dau alwashi sai ta rama dukan da Rabi’u ya Mata haka ta bi inna cikin uwar d’aka tana matse kwalla da katse majina .

        Misalin karfe hudu na yamma fatuha ce zaune tsakar gida wadda take share kwal, ba dati ko d’aya da yake inna akwai san tsafta duk yadda ta so ta gyara fatuha da ta fita zata dawo kamar almajira ko sabuwar mahaukaciya saboda tsaban rashin ji ko wanka sai anyi da gaske, inna ke samu ta dirje ta  fura take sha hankali kwance daga gani fura na kai mata karo dan sai rausaya kai take kamar kadangaruwa, inna ce ta lek’o daga uwar d’aka ta  ce, “fatuha yi sauri ki shirya ki tai makaranta allo.! baki ta turo gaba kamar zata tunkud’i birji ta  ce, “gaskeya yau inna ban zuwa, na gaji qur’an kullun Malam d’alha sai ya bigeni” ta inda zancan tana matsar kwalla”
“to fatuha in baki je  makarantar ba inaa zaki sauke? baki so na siya maki shanun a yanka ranar sauka? washe baki tayi ta ce,  “to inna zani wallahi ko dan ki yanka min shanuwa babba tafi tasu fatsima kwarankwatsi”
“yawa yar albarka  maza ki shirya” hijabin ta dake saman igiya ta janyo ta zura ta fita da gudu inna ta girgiza kai ta dau kwanan fura ta Kai madafi ta aje.

    Fatuha da ke tafe tana yan surutai wanda ko ni (salma) bajin ta nake ba chan ta tsinkayo muryar malam dalha taja birki ta tsaya tana raba ido dan tasan kashin ta ya bushe, dan ba k’aramar makara tayi ba, Malam d’alha ne ya juyo sukayi ido 4 da fatuha ya kwallo ido waje  ya  ce, keeeeeeeee!! fatuha dan uban ki yanzu ne lokacin zuwa makaranta shegiya mai Kama da mayu, duk kauyan nan kin raina uban kowa” yana huci ya cigaba  da  cewa, “yau zaki ci gwafar ubanki wallahi” fatuha dake ta raba ido ta duqa da niyar rarumo takalmin ta ta ruga muryar Malam d’alha ce ta tsinke mata tunani  “wallahi kika ruga sai na sa basiru ya dauko min ke akai” kasancewa tasan basiru Ba k’aramin kato bane yasa taja ta tsaya chafka d’aya Malam d’alha ya mata yana muzurai kuka ta farayi tana yarfe hannu tana bashi hakuri Allah annabi amma yayi biris ya fisgota ya fara kila kamar an aiko shi, ihu take jera mai da Allah ya isa bugun ta yake amma bakin yaki mutuwa dan kan shi ya gaji da dukan ta ya hakura, fatsima da ke gefe sai matsar kwalla take tana yimai daquwa  ta hijabi ta, lalla6owa gefan fatuha tayi  Malam D’alha be ganta ba ta  ce, “yi hakuri fatuha kin ji Allah sai ya saka maki” fatuha dake matsar kwalla ta turo baki gaba ta  ce, “billahilazi sai na rama fatsima, ba yana zuwa gidan qilu zance ba da yamma ba, kwarankwatsin dubu sai nayi maganin shi fatsima”
“Kai fatuha ki kyale shi dan wallahi ki kai mai iskanci har gida zai biki dan Malam D’alha ba wayau garashi ba, ya hadaki da baffa”
“yo nima wayau ya isheni? ta karashe zancan tana washe baki fatsima taja bakin ta tayi shuru haka suka cigaba da karatun su dai-dai gwargwado fatuha na da k’okari sai dai bata jin magana ko  kad’an, ba wanda bai san ta akauyan su ba.

      Mayan motoci ne kira bentley guda 5 suka nufi wani katafarin gate kallo d’aya nayi ma motocin na hadiye miyau dai-dai katafarin gida motocin suka kunna Kai wurin parking suka nufa suna gama parking da sauri wasu sojoji guda 4 suka foot daga ciki motar gaba at the same time sojojin 4 na cikin motor baya suka nufi  motar tsakiya  ahankali d’aya daga cikin  sojojin ya bud’e mai murfin motar tsakiya wani  had’addd’en  kafa nagani mai sanye da booth yana cikin kakin shi na sojoji karfafen namijine kyauwan sa  ya  isa wow fari ne Sol idanu sa manne da glass fari wadda ya fido da zala kyan shi da qwarjinin shi dogo ne sosai jikin shi  murd’e yana da fad’and’an kirji gashin kanshi mai laushi ne duk da  gashi na cikin hula shi na uniform hakan be hana gashinshi bayyana ba, ga sajan shi kwance  hanci shi kamar pencil dan tsini briefcase din shi ya amsa hannu daya daga cikin yaran sa, fuskarsa murtuke Ba alamar dariya kamar an aiko mai da wahayin mutuwa, (na ce ohni Salma da guy dinan zeyi dariya da ba k’aramin kyau zaiyi ba) haka yaran suka bashi guri ya wuce Kai tsaya main palour ya nufa wow fad’i tsaruwar palour bata lokaci ne saboda ba karamin haduwa yayi ba  baba jummai da ke gafe cikin washe baki ta tsugunna tana kwasar gaisuwa cikin isa kamar mai koyan magana ya amsa tare  da  cewa, “mom fa?
“ah mai gida tana sama” K’ara d’aurewa yayi dan wannan suna k’ona mai rai yake a hankali yake taka matatakala cikin isa.

    Kai tsaye d’akin mom  ya shiga had’add’an d’aki ne  mai kyau sanyin AC sai ratsa d’akin yake hajiya da ke zaune saman kujera dressing mirror tana shafa turare tasha had’add’en leshin ta mai kyau, fara ce bafulata na kallo d’aya zaka mata kasan hutu ya zauna mata, ahankalin ya k’araso yayi huging nata cikin fara’a ta juyo dan tasan ba mai mata haka se son, kiss ya sakar mata a kumatu ya  ce,  “Mom I miss you..!
“miss u more son welcome back dear, baby ka k’ara girma kamar ba Kai ba” turo baki yayi ya langwabe Kai alamar shagwaba ya  ce, “Kai Mom ni dai  gaskiya ban girma ba”
“AI ka ji da shi, yanzu dai kaje kayi wanka ka dawo your food is ready a dinning area”
“ok Mom..! ya fice yana murmushi kamar bashine Wanda ke d’aurewa d’azu ba…!

VOTE
COMMENT
[3/8, 10:06 PM] Salma😝: CAPTAIN SADIQ
👮🏼‍♂
written
by
Salma mas’ud nadabo

    Edit by
blood sister deejah

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
Follow me on wattpad: salmamasudnadabo

3_4

Kaitsaye bedroom nashi ya wuce komai na bedroom d’in golden colour ne wani makekyen gado ne atsakiyar d’aki wanda ke kama da ba a kwanciya a saman shi, dan komai na d’aki very neat ne dressing mirron din shima abin kallo ne kayan shafa ne kamar suyi magana dan yawa,  perfume kam ba’a magana da man gyara gashi tsayawa lusafa maku haduwar d’akin 6ata lokaci ne, kayan shi ya fara cirewa
ya shige toilet, wow toilet d’in ma abin kallo ne dan ya had’u iya had’uwa baifi  30 minutes ba ya fito d’aure da towel a qugun shi d’aya kuma yana goge gashin kanshi da shi dressing mirror ya nufa ya shafe jikinsa da mayuka masu kamshi tare da gyara sumar sa da sajan shi wardrobe nashi ya bud’e, wow wardrobe din ma abin kallo ne saboda kaya ne a ciki kamar gurin saida kaya suit kala2 da uniforms d’in shi na sojoji kamar suyi magana da yake shi mutun ne ba mai yawan sa manyan kaya ba, dan haka k’ananan kaya sunfi yawa hannu yasa ya ciro T-shirt din shi white mai gajeran hannu da 3quarter black,  ba k’aramin kyau yayi ba haka yasa kyan shi ya bayana sosai agogo ya mak’ala ma hannu shi mai tsada silver na azurfa har ya kai bakin kofa phone nashi ya fara ringing wayarsa kira iPhone 7 white chak ya jaa ya tsaya hannu ya kai saman dressing mirror nashi sweet Mom ne rubuce a screem d’in phone din ahankali yasa hannu ya  d’auka ya  ce,  “hello Mom..!
“son na d’auka bacci ya d’auke ka?
“no mom yanzu zan fito”
“ok..  datse kiran tayi daga dayan bangaran  cikin isa yake saukowa daga steps  hannu sa d’aya cikin aljihu Jidda dake dining ce ta rugo da gudu ta rungume shi ta ce, “daddy welcome back..!  d’aga ta sama yayi yana mata wasa tana dariya har suka qaraso dining tana rik’e a hannu shi Mom sai murmushi take ita tayi serving d’in su  shinkafa ce da miya wadda taji kaji da namomi  da ganyaye  cikin kwanciyar hankali suke cin abincin, wadda sadiq da kanshi yake feeding Jidda itama tana feeding nashi yarinya ce wadda baza ta wuce 4 years ba chocolate Colour ce mai kyau da ita gashin kanta yasha gyara sanye take da gwon pink mai dan siririn hannu, yadda sadiq ke bata kulluwa hakan zai gwada ma ba k’aramin ji yake da ita ba, Mom dake zaune tana Kallan su sai taji tausayin Jidda ya kamata, da shi kanshi d’an nata Jidda ce  ta  katse shuru da cewa, cikin muryar ta mai tsamin, “daddy Ina tsaraba na? kallan ta yayi yana murmushi ya lakace mata hanci ya  ce, “sweetheart ki bari daddy ya gama lunch mana” baki ta turo gaba ta  ce, “Uhm daddy na k’osa naga tsaraba ne”
“Uhm na sani swetheat bari mu gama tukun” Mom ce ta washe baki ta  ce, “ke dai baki gajiya duk san da yayi tafiya fa sai ya maki tsara”
“to ai  grandma  Ina so ne” ta ida zan can tana turo baki
“ke ko Allah ya shirye ki” cewar  Mom duk hiran da suke idan sadiq nakan little daughter d’in shi wadda ya ke jin ta har cikin ranshi sadiq  ya  ce, “oya cigaba da cin abinci sweetheart mu gama na baki tsaraba ki, sannan muje shan ice cream ko dear”
“yes dadd.! haka cikin wayau ya samu yayi feeding nata.

                       *******
Fatsima da fatuha ne tafe antaso daga makarantar allo suna tafe suna tsoka dan wannan ya zamar masu jazaman, in antashi daga makaranta sai sunyi tsokana san ransu suke komawa gida, wata Rana da kuka wata rana da gudu suke komawa gida yau kam a guje suka koma gida, fatsima ta shige gida fatuha ta shige gidan su baffa ne zaune bisa tabarma Inna na gefe tana zuba mai ruwa abuta saboda magrib ya kusa, fatuha ta kunno kai tare da sallama ta yarda hijabin ta k’asa baffa ya bita da kallo, washe baki tayi ta ce, “baffa sannu da gida”
“yauwa yar albarka, an dawo daga makaranta kenan?
“eh baffa”
“yauwa ya karatun”
“lahiya lau baffa”  taje ta amshi buta da ke hannu inna ta kawo ma baffa yayi alwala ya wuce masallaci bashi ya dawo ba sai bayan isha’i, inna da fatuha na zaune suna cin tuwan dawa ta miyar kubewa wadda tasha man shanu baffa ya shigo da sallama, fatuha ta ruga da guda ta rungume shi “ah’ah zaki karya ni fatuha wai ke baki san kin girma ba” baki ta turo ta  ce, “gaskiya baffa ban girma ba”
“to naji” ya ja hannu ta suka zauna bisa tabarmar da Inna ke zaune murmushi inna tayi ta tashi ta shige madafi ta d’auko kwana abinci Malam ta aje mai yana samata albarka bayan sun kamala cin abinci fatuha ta kwashe kwanikan ta dawo ta zauna kusa baffa ta  ce, “baffa..!
“na’am fatuha”
“Baffa Ina so gobe na bika gona dan Allah”
“makaranta fa fatuha” baki ta turo  gaba ta  ce, “ai gobe litinin baffa ba ta sahe” inna da ke gefe ta ce, “toh fatuha kin san sai 5:00 Malam ke dawowa ki bari sai ranar alhamis ki bishi kin ji” kwalla ta Fara matsewa baffa ya ce, “yi hakuri ki shirya goban sai muje ko” washe baki tayi dan ita akwai abinda take san daukowa a gona shiyasa zata bishi inna ce ta katse mata tunanin da cewa, “haba Malam wai me yasa kake biyewa fatuha dan Allah, taita sangarcewa”
“kinga ladingo bana san haka haba dan Allah, Allah ya bamu yarinya sai baza mu faranta mata ba, mun dad’e muna san yara Allah bai bamu ba sai yanzu, yanzu kuma ya bamu sai muki faranta mata, gaskiya bazaiyu  ba ladingo, ke ma kin fara d’aukar maganar mutanan waje Kenan, toh yayi ni dai ba maimatsa ma d’iyata akauyan nan” kyale shi ladingo tayi ya ida zan can tare da d’aukar fatuha wadda tuni bacci ya kwashe ta inna ta bishi da ido tare da kwashe tabarmar tsakar gida.

                         ****
After dinner mom da sadiq ne zaune a palour suna kallan news Jidda na kwance  jikin shi, da alama tana wasa bacci ya d’auke ta Teddy’s d’in ta a baje cikin palour baba jummai ce ta leko daga d’akin ta ta zo ta fara kwashe kayan wasan tana kaiwa d’akin jidda dakine mai kyau fadi tsaruwa dakin 6ata lokaci ne sai da ta gama kwashewa ta zo d’aukar jidda dake mak’ale da baban ta sadiq  ya ce, “ah baba barta yau tare zamu kwana”
“to shikenan maigida bari na mata wanka nasamata kayan bacci”
“to shikenan” ya miqa Jidda  Mom ta juyo ta kalle shi tana sanyin magana amma ba tasan 6acin ran son shiyasa taja bakin ta tayi shuru, can ta ce, “ni ko baby aikin da baba jummai take bai mata yawa ba, gashi ba yarinya ba ce”
“haka ne Mom tunda Mary ta tafi ba a kawo wata ba, ni wallahi Mom tsoran d’aukowa sweetheart wata yar aikin nake duk  basu  iya  komai  back wallahi” ya ida zancan yana 6ata fuska  Mom  ta  ce, “ya zamuyi dole a samo wata  saboda aikin ya mata yawa”
“to shikenan duk yadda kukayi ki fad’a min”
“to.. kun koyi waya da abban ka”
“yes munyi jiya lokacin yana airport yace sai yayi 2weeks zai dawo”
“eh haka kasan har yanzu suna magana kan kwangillannan ne”
“eyya to Allah ya taimaka”
Mom ta ce, “amin gobe kai da Jidda in ka dawo daga wajan aiki ka kaita gidan sister ka ya kamata ka leka, ka bama su hanan tsaraba su ko”
“tam bari mu gani idan na dawo da wuri  sai muje” sai ga baba jummai dauke da Jidda ya amshe  ta yayiwa  Mom sai da safe..
CAPTAIN SADIQ
👮
written
by
Salma mas’ud nadabo

    Edit by
blood sister deeja

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄

                           5_6

ASUBA TAGARI

      fatuha ce ta tashi tunda safe ta fito daga d’an akurkin d’akin ta wanda ko lafiyaya katifa bai samu ba, inna dake gefe ta na hura wuta Fatuha  ta gaishe ta tare da d’aukar tulun da ke kusa ta inna, ta fice zuwa d’iban ruwa rafi gidan su fatsima ta wuce kai tsaye dai-dai bakin kofa suka ci karo da Fatsima ta washe baki ta  ce, “kai fatsima qur’an na d’auka baki tashi ba da billahilazi na higo ruwa zan heqamaki”
“aiko da anyi heqa-heqa”  suna tafe suna tsokana magidanta da suka fita siyaya safe har su qarasa rafi, yan’mata ne da sa’anin su birjik suna d’iban ruwa haka suma suka qarasa, duk yarinya data gansu indai sa’ar su ce sai ta matsa saboda tasan hali in bata matsa ba ta ci na jaki, fatsima ce ta hango Rabi’u shi da larai suna tad’i fatsima ta zuguro  fatuha ta nuna mata da baki ta  ce,  “kin tuna abin da ya mana jiya?
“qur’an ina sane wallahi ai ban yafe mai ba, kawo kunnan ki kiji abinda zan mai” magana su kayi a kunne (wadda ko ni salma banji ba) sannan suka kwashe da dariya fatsima  ta  ce,  “kai fatuha billahilazi hiyasa nake sonki wallahi kin san maganin d’an iska” ta ida zancan tana daukar tulun ta fatuha tayi gaba haka suka jero suna tsokana sannan kowa ce tayi gidan su.

      Tana  shiga gida inna har ta sheka koko, nata na cikin kwannan samira ta Kafa kai ta shanye baffa ya fito daga uwar d’aka washe da baki ya  ce, “yauwa yar albarka har kin gama d’ibar ruwan”
“eh baffa na gama kai nake jira mu tafi”
“to bari na d’ako fatanya na a buka sai mu wuce” to ta  ce, ta ruga da gudu ta d’ako hijabin ta suka ma inna sallama suka fita.

                          *****
Sadiq ne  ya fito daga toilet sanye da bathrobe a  jikin shi ahankali ya leka fuskar Jidda da ke bacci yana shafa kanta, ahankali ya kai mata kiss a goshi, bud’e ido tayi ta sakar mai murmushi  ta  ce,  “daddy good morning”
“morning  sweetheart oya tashi muje ayi wanka”
“tam papa.! d’aukar ta yayi suka shiga toilet ya wanke ta tas suka fito yana mata cakulkuli tana gantsarewa tana dariya ta  ce, “daddy please stop”
“naqi dear ba daddy zaki ma wayau ba”
“no daddy ba wayau zan ma ba fa”
“to menene to.!
” uhm wani abu” ta ida tana hada hancin ta dana sadiq, kamar an mintsile sa ya ce, “oya tashi na shirya ki”
“tam papa” mai ya shafa mata ya sa mata jeans blue and pink t-shirt mai kyau da manyan flowers ya raba mata gashin ta gida biyu ba k’aramin kyau tayi ba Masha Allah peck ya mata a kumatu  ya  ce, “oya wuce wajan grandma, gani nan zuwa dana gama shiryawa”
“to daddy” ta fita da gudu ya bita da kallo shiryawa yayi cikin kakinsa na sojoji tare da gyara sumar sa ba K’aramin kyau yayi ba wow duk inda namiji ya ke to sadiq ya kai, briefcase nashi ya d’auko wanda ke gefen gado tare da ficewa dinning area ya nufa.
“Mom good morning ”
“morning son how was your night?
“cool Mom and your’s? ya ce tare da kai mata peck kumatu ta  ce, “the same”
“good” atsaitsaye yayi break saboda ya kusa makara ya fita yaran shi suka fara qamewa tare da  miqa gaisuwa motar shi wadda tasha wanki benz fara mai daukar ido ya shige yaron sa ya rufe suka fice daga gidan.

                           *****
Baffa da fatuha ne a gona sai aiki suke cikin jin dadi fatuha na ma baffa hira, sosai ya ke jin fatuha a ranshi fatuha ce ta katse shurun da cewa, “baffa zanyi fitsari”
“to fatuha ki qarasa can gefe kiyi kin ji, ki kulla da kafar ki”
“to baffa” ta kutsa kai cikin gona sai da ta tabatar baffa baya hangen ta sannan ta lalla6a ta qara shigewa jejin  wani sasak’e  icce ta d’iba ta kule a leda, tana dariya ta matse azanin ta baffa da yaji shure ne ya fara kwala mata kira da gudu ta qaraso tana cewa, “baffa gani” tana hakki
“yauwa yar albarka yo Ina kika shige yin fitsarin” baki ta washe ta qara gyara zanin ta hannuta ya ja suka zauna suna cin dumaman tuwon da inna ta aiko masu da shi suna gama ci bacci ya kwashe fatuha baffa ya ce “ikon Allah har kinyi bacci kenan.. ya tashi ya cigaba da aikin shi.

*****
Cikin natsuwa yake aikin shi a office, office d’in Masha Allah sanyi AC sai ratsawa yake sosai, abokin shi majid ne ya shigo dauke  da  sallama ya ce, “ah big man ashe ka shigo”
“yap tun 8:00am.. hannu ya mika masa suka gaisa ya samu guri ya zauna ya  ce, “big man ya Mom and sweetheart?
“lafiya lau yauma rigima tamin zata biyo ni taga uncle majid”
“Allah sarki me yasa baka zo min da  ita ba”
“haba wallahi tana zuwa nan zata cikani da to much of surutu”
“uhm kai dai ka sani mutun sai muskilanci”
“naji d’in idan wannan surutun ya kawo ka to ka fita”
“to ban fita tunda ba kaika kawo ni ba”  shuru sadiq yayi ya cigaba da aikin shi kiran sallah la’asar ne yasa suka fito su kayi sallah  suka koma.
bashi ya dawo gida ba sai 5:30pm part nashi ya shige ya yayi wanka ya wuce bedroom din Mom  zaune take sama sofa tana karanta azkar yayi sallama ya mata peck Jidda ce ta rugo ta bashi hug ta  ce, “dady I miss u”
“miss u more dear..!

      After ya gama lunch ya shirya Jidda da kanshi ya ja hannu ta suka je parking space, yaran shi har sun taso ya d’aga masu hannu alama su kad’ai zasu  kaitsaye gidan Anuty bilki ya nufa.

       Dai-dai wani madaidaicin gida su kayi parking mai gadi ya wangale masu gate, Masha Allah gidan ya had’u sosai plat ne mai kyau su hannan na filin gida suna wasa ganin uncle sadiq ya sasu rugawa aguje suna mai oyoyo, ya chabe su yana masu wasa tare suka karasa palour Maman hannan na ganin shi ta washe baki ta qwalawa talatu kira ta kawo mai abin motsa baki, dangin su fruit da sauran su har k’asa talatu ta duk’a ta gaishe shi Aunty ta  ce, “ah baby yau kai ne a gidan nawa hala Mom ce tace ka zo to yayi” smile  yayi  ya  ce, “oh kina nufi ban zuminci ko?
“kamar hakan dai”
“a’a aunty ke ma kin san bana zaman a naija sosai, but now na dawo Nigeria zanrinqa zuwa har saiki gaji dani”
“toh shikenan Allah yasa da gaske kake”
“haba anuty billy” ya ida zancan yana shagwabe fuska “ohni baby wai yaushe zaka daina shagwaba, duba fa har da d’iyar ka budurwa” dariya ya fashe da  ita, “ni dai sister kin samin ido wallahi” sannan ya kora lemo “toh naji na daina”
“uhm wai ina mai gidan”
“bayanan yana dubai”
“ok..
“sai end of this week zai dawo”
“Allah ya maido shi lafiya”
“ameen” hira sukai sosai da yar ‘uwarsa Kiraye-kirayan sallah magrib ne yasa suka tashi sadiq ya wuce masallaci.

                         ********
Misali karfe 5:30pm har baffa ya gama komai a gona fatuha na kwance kamar maiyin bacci dare, saboda yasan halin ta in ta kwanta bacci bata san a tashe ta, yasa hannu  ya d’auke ta har suka iso gida inna na ganin su ta washe baki, tare dayi ma malam sannu da zuwa tare da kar6ar fatuha da ke sharar bacci d’aura alwala baffa yayi ya tafi masallaci bashi ya dawo ba sai bayan isha’i, lokacin fatuha ta tashi tana cin abinci hira suka d’an ta6a sama-sama sannan suka wuce ma kwantan su Inda fatuha ta matsu gobe tayi dan ta aikata abinda ke ran ta.

*****
Bayan isha’i sadiq ya dawo yayi sallama da sister nashi sannan ya raba ma su hannan tsarabar su, karku  so kuga murna wajan su bayan sun fito haka ya biya da Jidda wajan shan ice cream ya mata siyaya sosai sannan suka dawo, tun akan hanya ma bacci ya d’auke jidda dan haka tana kwance a kafad’ar shi cikin sallama ya shigo Mom na palour tana kallo ita da baba jummai, baba jummai ce ta tashi washe da baki tare da amsar jidda shi kuma ya wuce dakin shi yasa ice creams din a fridge.

        Baba jummai tana zuwa d’aki tayi ma jidda wanka ta samata night dress nata blue riga dai-dai gwiwa, shima yana zuwa d’aki wanka yayi saboda ya gaji sosai ko da ya fito Mom har ta shinfid’e jidda saman bed kayan bacci shi yasa tare da jawo laptop din shi yana shan coffee ya dad’e yana aiki sannan bacci ya dauke shi.

****
Kiraye-kirayan sallah asuba ne ya tada fatuha bakin ta washe ta  ce, “kai narantse da Allah jiya da kyar bacci ya suran yadda na matsu yau tayi, wallahitalahi yau Rabi’u sai ya gane kuran shi qur’an ciki sauri tatashi  tayi sallah.

   Yau dai ba laifi fatuha ta taya inna aiki sosai ba dan komai ba sai dan tabarta ta fita, saida suka gama komai ta gyara zaman zanin ta wadda kullun jiya na leda na habar zanin ta sannan ta ce, “inna zani gidan su fatsima”
“to fatuha karki dade”
“to inna.. ta fita da gudu gidan su fatsima ta shige inna fatsima na tsakar gida tana wanke-wanke gaisheta tayi ta amsa da  cewa, “fatuha ya inna”
“inna lahiya lau”
“ki ce ina gaishe ta inkin koma gida”
“to za ta ji inna, ina fatsima?
“tana uwar d’aka”  fatsima da ke shara bacci saman tabarma fatuha ta d’aka mata bugu ta  ce,  “ke tashi..! firgigit ta tashi “kai fatuha..”
“ke banza tashi muje”
“oh na tuna fa Qur’an ban san sanda bacci ya sure ni ba” dankwalinta ta daura suka fita suna tafe suna tsokana dai-dai wata gona suka ci birki Rabi’u ne gindin bishiyar mangwaro da alamar rake ya gama sha bacci ya dauke  sa  saboda duk ga abin rake zube, lafewa fatuha  tayi  jikin bishiyar bedin ita da fatsima suna lekyan shi fatuha ta ce, “fatsima bilahillazi yayi bacci” ta kwashe da dariya “ai sai ya ci uba sa” qulin leda ta ciro daga habar zanin ta  ta nufi Rabi’u cikin sand’a ta bud’e ledar ta zuba masa tana k’ok’arin rugawa da guda bayan bedi Rabi’u da ke bacci cikin bacci ya fara jin rad’ad’i na susa ba arziki ya tashi yana soshe-soshe, yayi zuru-zuru su fatuha da ke bayan bishiya sai dariya suke sannan suka fito daga nesa dashi  ta  tsaya ta kwalamasa Kira ya waigo ta  ce, “ai dama na fad’a ma kwarankwatsi ba’a buguna na hakura” fatsima ta bushe da dariya ta ce,  “ka je gida mai tafasa tama magani kaji rabe’ dagowa yayi idanun shi sunyi jaaa saboda  azaba ya  ce, “bala’iiiii zan ci uban Ku dama  kune kuka fesa min asosa? narantse na sha magani sai na zo har gida na ci uban ku”
“yo zancan banza, ka zo muk’arama wani” injin fatuha taja hannu fatsima suka bargun suna dariya shikuma Rabi’u na soshe-soshe
CAPTAIN SADIQ
👮
Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
blood sister deejah
Follow me on wattpad: salmamasudnadabo

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄

                      7_8

Rabi’u yasha wahala sosai idanun sa sunyi jawur sai ihu yake, ado ne zai wuce ya hango shi yana birgima ya qaraso da  sauri  garesa  yana  Cesar,  “subhanilillah lahiya Rabi’u me ya faru?
“fatuha ce..? yana ihu haka malam ado ya taimaka mai ya kai shi gida jikin nan nashi yayi jawur abunka da bafulatanin mutun, inna maitafasa tana gyaran tafasa taji sallamar Malam ado ta tsame hannu ta dake cikin tafasa ta yafa mayafi ta leka  waje ganin  malam ado  rik’e  da  Rabi’u ta  ce, “lahiya Malam ado me ya sami Rabi’u ni?
“nima dai  ban sani ba  amma da alama sosa ce”
“toh fa kai ko Rabi’u mai ya had’a ka da sosa garin ya haka ta faru? ta ida zancan tare da riqe haba zani tana matse kwalla cikin murya wanda yasha wahala ya ce, “inna wallahi fatu ce da wannan iskancin”
“bala’i kambuuu alqawalin Allah ban yarda yau sai naga uban ta jauro billahilazi” ta ida zancan tana yarfa hannu sama Malam ado ya ce, “a daiyi hakuri yarinya ce”
“yarinya uban wa? Mai  tafasa  ta k’arasa  maganar da dafe qirji ta  ce, “yarinyar da aure yau haihuwa bad’i shegiyar yarinya mai kama da mayu duk  ta  adabi  mutanan  kauyan nan  da  bakin  halinta, wallahi Malam ado ban hakura shigo da shi namasa magani na je na samu uban nata, haka aka, shigowa yayi da Rabi’u yayi zuru-zuru aka shinfide shi bisa tabarma.

“Qur’an fatuha baki da mutunci”
“yo ni ta wasa ce ai dama na fad’a maki saura malam D’alha ai qule nake da shi kwarankwatsi”
“hehe kai qawata ina san ki qur’an”  fatuha ta washe hak’ora”
Ta  ce, “nima haka billahilazi” haka suka dawo gida ko da suka dawo gida fatsima gida ta wuce gidan su fatuha ta shigo da sallama yau zuciyar ta fes take da farin ciki inna da ke shara ta amsa sallamar, ta kauda kai ta  ce, “yanzu dan Allah fatuha kin kyauta kenan tunda safe da kika fita sai yanzu zaki dawo? bata idaa  rufe bakin ta ba mai tafasa tayi sallama cikin tsiwa inna ta amsa fad’owa  tayi  cikin gidan da  masifa  ta  ce,  “keeeee!! ta cakumo wuyan fatuha inna ta ce, “lahiya mai tafasa?
“lahiya  kenan bari uban ta jauro ya zo billahilazi yau ban yarda, kuma duk abinda ya samu d’ana  ke ce ni zaki kashe ma d’a har kin isa to  baki  isa  ba” inna sai bata hakuri take amma taqi sakin fatuha wanda tayi wiki-wiki da ido dan tasan tayi, baki ta turo gaba take ce,  “ke ki cika ni..! tare  da finci ke kanta daga ruqwan da mai tafasa ta mata cike  da  rashin  kunya  da  tsiwa ta  ce, “yo ba d’an naki bane jiya ya bige ni ba, kuma na rama yau” ta ida zancan ta murguda baki “dan uban ki idan zaki rama saiki sa mass asosa?  inna ta ce, “fatuha ince jiya ban maki magana ba?
” yo inna jinayi ban iya hakura” ta fada cikin tsiwa haka maitafasa ta gama zage-zagen ta da kumfar baki ta fice acewarta in Malam jauro ya dawo zata zo ta same sa.

                         *****
“Daddy please muje shan ice cream”
“sweetheart akwai a fridge muje na baki”
“ok papa thank you” ya lakace mata hanci ya ce,  “that is my angel” ta washe hakora part nashi ya kaita ya bata ice cream shi kuma ya shige gym room nashi ya dad’e yana gym sannan ya fito riqe da towel a hannu shi yana goge zufar fuskarsa, gefen da Jidda take ya kalla har tayi bacci ahankali ya karasa saitin fuskarta yayi kala tausayi a hankali  cikin  murya  mai  sanyi  ya  ce,  “my angel I now you miss your Mom sam  baki  samu  d’umin uwa ba, why KAUSAR me yasa kika tafi kika barni ni da Jidda why kausar..! yana maganar kamar zautace yana share hawayan fuskarsa y’all ce,  “I miss you more my wife naso ace yanzu  kina ganin angel my wife, dake take Kama sosai naso ace tare zamu bata good caring ya kai lips din shi dai2 goshin Jidda ya mata peck

           *Asalin labari*

Malam idi zaunan d’an kauyan Kano ne wato rano su fulanine sosai Allah yayi ma malam idi rufin asiri, dai2 gwargwado yana kiwon shanu sosai, har ma da kaji gashi mutumin kirki shiyasa kowa ya sanshi a kauyan rano, yana da mata tani sosai yake san tani Allah ya basu ya’ya 3 maza 2 mace 1 kabiru shine babba mai bimai Ibrahim sai rukayya.

Zaune suke zaman lafiya cikin kauyan inda lokacin kabiru ke aji shida na secondary, shi kuma Ibrahim aji 5 rukayya na aji 3, sosai suke karatun su saboda Malam idi mai san karatune.
Akwana atashi ba wuya wajan Allah yau garin rano zaman lafiya yayi qaranci, saboda 6arayi na zuwa su kwashe ma mutun dabobi sannan su kashe ka  da iyalan ka, Malam idi ne ya shigo gida cikin sallamar shi tani da ke wanke-wanke ta amsa ta  ce,  “ince dai malam lafiya”
“wallahi tani kauyan nan ba lafiya” kabiru da ke uwar daka ya leko sukayi tsaitsaye can idi ya yanke shawarar saida dabobin shi su koma birni cikin garin Kano, ba yarda idi ya iya haka ya saida shanun shi cikin ikon Allah ya samu kudi mai yawa ya sama masu madaidaicin gida a rijiyar zaki, sannan yaba abokin shi Malam tanko kudi wanda ke birni ya siya  masa shago a kasuwa kwari a zuba komai a ciki.
ya tataro iyalan shi suka dawo cikin garin kano, lokacin Ibrahim ya gama secondary da yake Ibrahim yaro ne mai san karatu result nasu na fitowa ya samu admission  a biyuke, idan yake karanta business admin shikuma kabiru ya cigaba da kasuwancin sa tare da mahaifin su sosai suke samun rufin asirin su.

     Kwanci tashi asarar mai rai yau Ibrahim ya gama karatun shi inda ya samu aikin kwangila sosai yake  samun cigaba, inda ya had’u da Hauwa’u  sukayi auran soyayya  ankai amarya rijiya zaki kusa da gidan kabiru inda yake zaune da matarsa Aisha  tsakanin amarya da Ango soyayya sosai suke zubawa, bayan   wata biyu hauwa’u ta fara laulayi sosai take samun kullawa wajan mijin ta da surukar ta, har ma da Aisha matar kabiru lokacin rukayya na FCE cikinta ya shiga watan haihuwa bata wani sha wahala ba sosai ta haihu d’an ta mai kyau sosai ibrahim yayi murna sosai.

       Kwana bakwai da haihuwa akayi suna inda yaro yaci suna idiris wato suna Malam idi, Ana mai lak’abi da jawad sosai rana suna akayi shagali bayan shekara biyu ta k’ara samun wani cikin, lokaci Ibrahim yayi kudi sosai ya qara murjewa shi da Hauwa’u daka gansu kaga Hutu inda yake ba Hauwa’u kulawa sosai har ta haifi d’iyar ta lafiyaya rana suna taci Bilkisu, sosai suke samun kulawa wajan iyayan na su.
CAPTAIN SADIQ
👮

CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*written by*
*Salma mas’ud nadabo*

    *Edit by*
*Blood sister deeja*
Follow me on wattpad: salmamasudnadabo

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM 🐄*

                  9_10

Yau kusan shekara 2 da haihuwar bilkisu inda Alhaji ke sa ran Hauwa’u zata samu wani cikin amma shuru hakan yasa hankalin shi ya tashi, musanma shi alhaji Ibrahim mutun ne mai son haihuwa ne haka suka cigaba da rayuwa cikin so da kauna inda alhaji Ibrahim yake faranta ran Hauwa’u amma cikin zuciyar shi nan maqale da san yaga ta qara haihuwa.
gidan su ko na rijiyar zaki sun rushe shi sun ginawa iyayan nasu katafarin gida mai kyau family house.

     Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi da san juna yau shekarar Hauwa’u 3 ba ciki kuma yau ne tatashi da wani irin zazzabi da ciwo kai sosai hankalin alhaji ya tashi haka ya kai ta asibiti akai mata yangwaje-gwaje inda aka shedawa alhaji Hauwa’u na dauke da juna biyu, zo kuga murna wajan alhaji baki har kunne ya daurawa cikin san duniya haka suma ya’ya nashi saboda basu da burin da ya wuce Momin su ta haihu su sha suna, locakin itama Aunty aisha nada ciki matar kabiru zo kuga yadda surukar su ke basu kulawa da nuna masu soyayya duniya ta zamar masu sabuwa yayin da mazan nasu ke rawar kafa kan cikin .
Cikin su na da wata 7 akayi bikin rukayya da mijin ta aliyu ansha shagali anyi bidiri sosai ankai amarya kaduna GRA.

     Akwana atashi ba wuya wajan Allah yau safiyar lahadi Hauwa’u tatashi da naquda kaitsaye asibiti suka wuce tahaifi kyakyanwa dan ta namiji, murna wajan alhaji Ibrahim ba’a magana da Aisha ta zo barka da tsohon cikinta ita da kabiru sun dade sosai a asibtin ita ma Aisha tunda safe take jin naquda tana daurewa, kasancewa ita haihuwar farko ne saboda sun dade basu haihu ba, basu suka fara shirin barin asibitin ba sai dare a dai-dai bakin kofa ta fara naquda nurses suka bata taimakon gagawa Alhamdullilah itama ta haifi dan ta namiji zo kuga murna wajan su ba’a magana, ba a salame su ba sai washe gari da safe murna wajan family ba’a magana kamar ranar aka fara haihuwa.
Kwana 7 da haihuwa akayi gaggarimin suna a family house nasu inda dan Ibrahim yaci sunan kakan shi na wajan mahaifiyarsa wato *Abubakar sadiq* ana mai lakabi da baby shi kuma dan kabiru *Abdulmajid* sosai akayi bidiri anzubar da kudi yadda ya kamata bayan suna da kwana daya alhaji Ibrahim ya koma katafarin gidansa daya tsara a sultan road, sosai gida ya hadu inda duk wani abin morewa na rayuwa akwai agidan sosai kowa ya tayasu murna.

****
_Bayan shekara biyu_

    sadiq yayi wayau sosai bashi da aboki sama da majid inda aka dau son duniya aka daura masa, yaro kullun kara kyau yake kamar dan larabawa kowa bama sha’awa yake amma sai Allah ya daura masa qiwuya kamar me gashi abu kadan bai isa yasasa dariya ba idan kaga yana dariya to yana hannu Mom ko Abba to wannan dariya har qyaqyatawa

        20YEARS LETTER
******
wani kyakyanwan saurayi ne shida wani shima ba laifi ya hadu ba kowa bane sai sadiq da majid awajan shakatawa sosai suke hira cikin jin dadi lokacin sun gama karatunsu har sun fara aiki su na sojoji, sosai suke jin dadi wasu yan mata ne nesa dasu sai kallon su suke ba kowa ba ce sai kausar da kawayan ta suma sun zo shan iska Nana ce ta zuguro Kausar  ta  ce, “wow kawata kalli wayan can guys din sun hadu sosai” kamar bazata juyo ba sai  kuma  ta  juyo tana juyowa sukayi ido hudu da sadiq takenan zuciyarta ta fara harbawa wani irin sonsa da kaunar sane suka kama zuciyarta lokaci daya haka suka bar gun tana cike da kaunarsa da begen sa shiku bai ma san tanayi ba gida suka koma suma tun daga ranar kausar ta rasa nutsawarta, duk wata hanya da tasan zata ga sadiq ita take bi ta sha wahala sosai kamin ta samo number shi tun tana kira bai dauka har ya fara dauka suna dan taba hira.

        Haka rayuwa ta cigaba ta tafiya soyayya mai karfi ta shiga tsakanin kausar da sadiq har ta kai ga iyayan su sun  sani, sosai iyayan sun ji dadin haka murna wajan kausar da sadiq ba’a magana musanma kausar da ita ta cusa kanta ga sadiq din.
shirye-shiryan biki ake sosai inda kowa ni gida ka leka abubuwa ake gudanarwa sosai ranar asabar aka daura auran *kausar Umar and sadiq Ibrahim* sosai kowa yayi murna ankai amarya gidan mijin ta dake sultan road gida mai kyau sosai wanda daga gidan su ba nisa zuwa gidan su sadiq.

      sun raya wannan dare nasu da sunna manzon Allah (S A W) bayan komai ya wakana tayi kuka ranar har ta gaji saboda sadiq ba qaramin namiji bane, dan ya dirje ta yadda ya kamata shida kanshi ya taimaka mata tayi wanka sannan ya barta tayi na tsarki ranar ko yasha shagwaba har ya gaji sosai yake samata albarka kasancewa ta zo masa da budurcin ta har gidansa, sosai yake jin kaunarta wani irin so suke ma juna su kamar su cinye juna.

         *****
_2years letter_
kausar ce asibiti ita da doctor kuka take masa sosai tana cewa, “wallahi doctor bazan iya jurewa rashin haihuwa ba saboda ko ban haihufa ba, wannan ciwon zai iya kashe ni kowani lokaci, ina son na haihu doctor bana so sadiq yasan cewa Ina da wannan ciwo”
“why kausar ya kamata ki sanar da mijin ki ko shine yaji haka zai tausaya maki, bai taba yadda ki zauna da wannan cikin saboda wannan cikin ajalin ki ne..! bawai nasan gaibu bane amma duk wani mai cutar ANEMIA bai iya daukar ciki ki duba ki gani ke kanki duk month sai an maki karin jini bale kuma yanzu har da baby a jikin ki” wani irin kuka mai ban tausayi ta saki ta  ce, “gaskiya doctor bana iya zubar da cikina doctor, bana iya zubar da jinin sadiq no I cant doctor..! turo kofar da akayi ne yasa doctor saurin miqewa kausar kuma tayi sauri fara goge hawayanta da bayan hannuta tana girgizawa doctor kai alamar karya tona mata asiri washe bakin karfin hali yayi ya  furta, “congratulation captain sadiq matar ka na da juna biyu ”
“what..! ya zaro ido yana washe baki ya  ce, “thank god finally  am  gonna  be  a  farther” ya kai ma kausar hot kiss a lips dinta yana shafa cikinta murna yake sosai inda doctor ke ta binsu da kallon tausayi sosai sadiq yayima doctor tukwici saboda  kyankyawan albirin  daya  masa.
kaitsaye gidan Mom suka wuce suna shiga da sallamar su kausar sai sunne kai take kafadar Mom sadiq ya daura kansa ya  lunshe ido jawad da ke zaune da yake ya zo da iyalan shi Nigeria kasancewar shi ba kasa yake zaune ba yana zaune a London da matarsa da d’ansa jawahir wanda ke da shekara3 yana zaune saman three sitar ya  ce, “wai yaushe zaka girma ne baby? Yar dariya  sadiq  yayi  ya  ce, “sai ranar da my wife ta haihu ka fara qirga month daga yau am going to be a father” wani irin dadi ne ya lullu6e Mom ita ko kausar sai sunne kai take da jin kunyar abinda sadiq keyi da tausayin kanta kuma, Bilkisu ce ta dungure masa kai ita ma lokacin Hanan na da 6years ta ce, “kai dai baka da kunya wallahi”
Mom  ta  ce, “ku kyale min yaro to me? dan ya fada mani?
“yauwa Mom that  is why I  love you” ya kaimata peck a cheeks Mom ko ta zage sai nan take da kausar ita da Bilkisu da matar jawad sosai suke gwada mata soyayya.
hakan yasa kausar ta shige toilet tayi kuka ta gaji tabbas tasan tayi dace da  dangin miji burinta bai wuce ta haihu ba, tasan zasu riqe mata amanar babyta ko  bayan  ranta, shafa cikinta tayi tana share hawayanta da bayan hannu ta.

Sosai kausar ke samun kulawa da so da kauna wajan sadiq, inda yake gwada mata tsantsar soyayya har take jin dama karta mutu ta danwama dashi a gidan duniya, a  duk  lokacin  data  tuna  ciwonta, kuka take sha sosai sannan ta share hawayan ta cikin ta har ya kai wata 5 bata samun wata matsala ga kuma sadiq da ke tatalin ta kamar akwai.

      Sadiq ne tsaye gaban dressing mirror yana shiryawa cikin uniform nasa ba karamin kyau yayi ba kausar ta qaraso wajan shi tana sanye cikin night dress nata fara riga dai-dai gwiwa tana  bin  sadiq  da  kallo  mai  cike  da  tsantsar  so  ta  ce, “habibina..!
“Na’am honey”
“uhm.! tana maganar tana gyara masa ma6alin rigarsa ta ce, “gaskiya kayi kyau sosai”
“ko.?
” eh mana” ta shagwabe fuska ta  furta, “har  na  ji  kishi Allah yasa kar yan’mata su kalle min kai” hancin ta ya ja ya  ce, “honey bame kalle miki miji kinji”
“tam.! Sadiq ya kai hannu ya shafa cikin ta ya  ce, “ya lafiyar baby na?
“lafiya shi lau habibi” smile ya saki mai sanyi yayi kissing goshin ta da cikin ta mika masa briefcase nashi tayi yana fita da gudu ta shige toilet ta fara aman jini-jini ta hanci ta baki, jiri take gani sosai har bata iya ganin gaban ta a dadafe ta rarafa ta hau gado tana numfashi sama-sama.

        Har yayi nisa da gida ya tuna yayi mantuwa ribas ya ci ya dawo ko da yayi sallama bai ji motsin kausar ba, daki ya nufa a tunanin shi bacci ya dauke ta musanman yadda ya lura cikin mai sata bacci ne lullu6e take cikin blanket sai kyarma take ya shigo dakin har zai fita ya dawo yaye blanket din mai zai gani kausar ce a sume sai hancin ta da jini ke biyowa.
sosai hankalin sadiq ya tashi daukarta yayi kamar baby duk ya rode ya sakata cikin mota kai tsaye asibitin wajan aikin shi suka wuce wato na sojoji, yana isa nurses suka fito suka basu taimakon gaggawa.
Idan  hankalin  sadiq  yayi  dubu  ya  tashi  ya  kasa  zaune  ya  kasa  tsaye  sai zarya yake.
Bangaran  kausar  kuwa doctors sun dukufa akanta domin ceto ranta, Mom sadiq ya kira yana kuka kamar qaramin yaro yana fada mata yadda akayi, Mom na  jin  haka ita da baba jummai suka taho asibitin sosai Mom ke kwantar masa da hankali da  created, insha Allah kausar zata  samu  lafiya”
wajan laida biyar kausar tasha na jini biyu na sadiq biyu na jawad daya na majid sosai hankalin su ya tashi doctor ne ya fito daga dakin yana goge zufar fuskar shi da sauri suka karasa wajan doctor suka  hada  baki  wajan  furta, “ya  jikin  kausar?
“Alhamdulillah munshawo kanta dakyar yanzu tana samun hutu ne” sadiq ya kira da yayi zuru-zuru harda yar rama yini daya yayi ya ce, “ka same ni a office”
“to Dr yakub” cikin sauri ya bishi suna shiga yakub ya cire glass din dake  manne idanusa yana  kallon sadiq  ya ce, “A gaskiya sadiq ka bani mamaki ya za’ayi ka yadda matar ka ta samu ciki bayan kasan tana da AMENIA why sadiq?
“what..! ya  furta zunbur sadiq ya mike ya ce, “yakub bangane mai kake fadi ba Ina tunanin kunnena bai ji dai-dai ba ko?
“oh karka raina min hankali mana kana nufin baka san tana da shi ba ko me? ras  qirjin  sadiq  ya  bada wasu hawaye ne masu zafi zuka zubo masa ya ce, “why kausar me yasa zakin min haka” kuka yake sosai har saida Dr yakub ya tausaya mashi ya rugumesa yana shafa masa baya alamar lallashi a hankali yake magana cikin sarkewa harshe ya ce, “yakub I don’t no kausar na da ANEMIA ban sani ba me yasa zata 6oye min why yakub she no I love her Allah nafi son ta akan baby serious yakub, please ka cire mata cikin please bana iya rayuwa bada kausar ba..! ya kara rushewa da wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro sosai yakub ke lallashin sa har ya samu ya samu nutsuwa ya bashi fresh milk mai sanyi yasha ya rage kuna da zuciyarsa ke masa a hankali ya fita daga office din ya shige dakin da a kwantar da kausar tana kwance fuskar nan tata tayi fayau alamar ciwo ya cita sosai, kallo daya ya mata idanusa suka ciciko da kwalla jikin Mom ya fada cikin dashashiyar murya ya fara ba Mom labarin abin da ya faru, sosai Mom ta girgisa da batun sadiq har da yar kwalata  sadiq ya cigaba da cewa, “me yasa kausar zata min haka mom? ya kara rushewa da wani saban kuka kamar karamin yaro..

Writing by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Blood sister jeedah

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄

11_12

Turo kofar da akayi ne yasa Sadiq  tsagaita kukan da yake, Abba ne tsaye bakin kofa cikin sasarfa sadiq ya qarasa wajan Abba,  ya qara sakin wani sabon kukan Abbane ya rugume shi alamar lallashi ya  ce,  “shhh!! Sorry son be are strong man sai ka ce ba soja ba, insha Allah she will be fine” Abba ya  juyo kan  jawad  ya ce,  “Jawad ka kaishi gida ya samu hutu kaji”
“Daddy..!
“Shhhh..! ya isa kaji jawad  ka kai shi gida kawai” Haka ko akayi.
jawad ne ke driving nasu cikin mota ba wanda yayi ma wani magana, sadiq idanun shi a lumshe har suka iso gida bala mai gadi ne ya bud’e masu  gate tare da  jajanta masu, parking space yayi parking suka fito a tare.
bedroom d’in sadiq suka shiga ya kwanta saman bed tare da lumshe idanun sa, zuciyarsa na wani irin suya musanman idan ya tuna da halin da abin kaunarsa ke ciki, Jawad ne ya katse masa tunani ta hanyar shafa sumar kansa, ahankali ya ware sexy eye’s ball’s d’insa ya  d’aura su  kan jawad riqe yake da glass cup da fresh milk a ciki ya ce,  “Sadiq please ka daure ka ci wani abu nasan tun breakfast d’in safe baka qara sa komai a cikin ka ba, please ka gama ka sha magani headachen nasan yana damun ka” numfashi ya ja ya cigaba  da cewa, “insha Allah wife naka zata samu sauki kaji baby” kamar ba zai sha fresh milk d’in ba, amma saboda bai ga wasa a idanu yayan nashi ba ya amsa, Sha biyu zuwa uku yayi ya aje saman stool ya qara lumshe ido maganin headache jawad ya 6alo tare da ruwa ya bashi ya sha, sannan ya lullu6esa da blanket ya fita.

      Bacci ne mai nauyi ya d’aukesa bashi ya tashi ba sai yamma liqis wanka yayi yasa Jean’s n shirt bleu mai dogan hannu sannan yayi sallah la’asar, ba qaramin kyau yayi ba sai dai fuskan nan fayau saboda kukan da yaci sannan cike take da alamar damuwa, car key nashi da ke saman stool ya d’auka ya fita.
kaitsaye asibiti ya wuce yana parking motarsa a harabar asibitin aka fara kiraye-kirayan sallah magrib Masallaci ya shiga yayi sallah zai futo kenan suka had’u da Abban kausar, hakuri yake ta bashi ankan cewa bai san kausar bafa fad’a masa larurata ba sadiq  ya  ce, “ba komai Abba”
“Toh shikenan Allah ya bata lafiya”
“Ameen.!!
d’akin da a kwantar da kausar ya shiga Mom na saman daduma tana lazumi, gaisheta yayi ta amsa a takaice sosai taji dad’in ganin sauyawar sadiq  ba kamar d’azu ba, Kausar ya kalla wanda ke kwance saman gado kamar gawa oxygen ne manne a hancin ta sai jini da ake qara mata, idanuwansa ne suka ciciko da kwalla tabbas yasan ya rasa kausar ya rasa mata tagari,  cikin  zuciyarsa  yake  sanbatu  da  cewa,  why mai yasa zaki mana haka kausar..! hawayan da ke neman zubo masa ya had’iye Mom ce ta katse masa tunani da cewa, “Baby ni zan wuce ka kulla da ita anjima matar jawad shukura zata kawo maku dinner, Son please ka rage damuwa wannan” Mom  ta  fad’a tare da shafa gefen fuskansa kamar jira ya ke hawaye suka fara mai zarya “shhh..! ya isa mana idan kana kuka ita kuma mai zatayi sokake ka tada ma kausar hankaline baby? Girgiza kai yayi tare da d’aura hannusa kan na Mom ya ce, “toh na daina”
“ko Kai fa idan kasan kuka zaka cigaba dayi to sai mu koma gida Bilkisu ta kwana da ita”
“Uhm Mom bazan sake kuka ba” wasu sabin hawaye ne suka zuba masa ya  ce, “Mom na rasa yarda zanyi control kai nane Mom nasan sarai na rasa my wife saboda wannan cikin” ya ja numfashi ya  cigaba da  cewa, “Mom kausar bata iya rainun cikin nan, Mom ki duba ki gani ita kanta duk month tana buqatar jini bale kuma yanzu data ke tare da ciki” ya ida zancen hawaye na zubu masa Mom ce ta share kwallan idanu ta ta  ce, “son ya isa haka kayi mata addu’a insha Allah lafiya lau zata raini cikin ta har ta haihu kaji” kai ya gyad’a mata tayi  peck nasa agoshi sannan ta masa sai da safe.

     Gashin kanta ya shafa  ahankali tare da kai mata peck a goshi ya  ce, “Allah ya baki lafiya my wife” sannan ya d’aura kansa saman gadon, a hankali take bud’e eye’s balls din ta tasauke su kan sadiq da idanun sa ke lumshe kamar maiyin bacci,  a hankali ta miqa hannu ta saman sumar sa tanajin wani son mijin na ta na qara narke mata a zuciya, a hankali ya dago sexy eye’s  ball’s din sa ya sauke a kan wife din sa da  suka  canza  launi  saboda  kuka,  murmushi ta saki tana qoqarin tashi zaune ya  dakatar  da  ita  da  cewa, “no ki koma ki kwanta kiji my wife” ya ida zancen yana shafa cheeks nata ya  ce,  “My wife mai yasa kika 6oye min sick naki why? Idanun tane suka ciko da kwalla ta bud’e baki zatayi magana, sadiq  ya  ce, “Shhhh.. ya had’a bakin su waje d’aya yana mata salon sa mai kashe mata jiki..

                            **
Rayuwa haka ta cigaba da tafiya sosai kausar ke samun kulawa wajan sadiq, inda suka bud’e babina soyayya, soyayya suke sosai kamar su cinye juna su inda duk month sadiq sai ya kaita asibiti an qara mata jini.

   Misalin qarfe 3:00am na dare sadiq kwance kausar na manne aqirjinsa ahankali yasa hannu yana cire mata hula da ke kanta, wadda bata bari ya cire mata, wasu siraran hawaye ne suka zubo masa saboda kusan rabin gashin ta ya zube saboda wannan ciwon, kuka ya sha sosai cikin daran sannan ya tashi yayi sallah ya nemamata samun sauqi wajan Allah, tabbas yasan ya rasa kausar ya rasa wani 6ari na rayuwarsa da irin wannan tunanin bacci ya d’auke shi.

   Akwana atashi ba wuya wajan Allah yau kausar cikin ta ya kai 9month, sadiq ne akwance yana bacci ya fara jin,  wash.! sadiq.! zunbur ya tashi hankali tashe kai tsaye asibiti suka wuce nurses suka kawo masu taimakon gagawa, gabaki d’aya sadiq ya rud’e har da yar kwallan sa, waya ya curo ya kira Mom ya fad’a mata cikin muryar kuka.
Zirga2 sadiq ke yi ya kasa zaune ya kasa tsaye, Majid ne ya dafa shi  ya  ce, “cool down sadiq” tare da rugume sa alamar lallashi,  Doctor’s ne ke kan kausar sosai suke aikin su dan suga ta haihu da kanta amma abin ya gagara.!!

          Doctor yakub ne ya fitu yana goge zufar face nashi, da sauri sadiq ya k’arasa wajan su da Mom da majid a  tare suka jefama doctor yakub tanbaya  “Ya kausar.?
“da sauki muna kan bakin qoqarin mu, ga wannan paper captain sadiq kasa hannu kausar ta kasa haihuwa da kanta” jikin shi narawa ya amshi paper yasa hannu aka shiga tiyata tun dare ake abu daya sai da safe suka fito.
daga Mom har sadiq ba wanda ya rintsa addu’a kawai suke, bayan ta haihu doctor ya sheda masu ta haifi baby girl murna wajan su Mom ba’a magana da sadiq.

      Kwance take a d’aki ita kad’ai tasan rad’ad’in da take ji wasu hawaye ne masu zafi  suka zubu mata tasa bayan hannu ta ta goge, gefen da baby take ta kalla jin an bud’e kofar ya sata d’ago eye’s ball d’in ta, wani lallausan murmushi ta saki tana qoqarin tashi,  Sadiq ya qaraso ya  ce, “my wife” tare da kai mata peck a goshi yana qoqarin maida hawayansa kausar  ta ce, “Habibina.! cikin sanyin murya  Baby  sadiq ya d’auka yana  murmushi  ya  ce, “Masha Allah baby mai kyau da ita kamar  ke”
“habibina..!
“Na’am”
“ga amanar baby mun na baka please ka kula da ita”
“shhh insha Allah tare zamu raini baby mu” yana qoqari boye hawayan da ke maqale a idanusa,  hannu ta kai  ta  shafa sajan fuskarsa mai laushi ta ce, “Wani suna zamu sama baby mu? Lallausan murmushi yayi ya ce, “Hauwa’u suna Mom, za’a mata laqabin ta Jidda” Fad’ad’a murmushinta tayi ta ce, “Jidda..! ta shafa cheeks d’in baby hannu ta ya riqe ya sunbata, tarine ya subuce mata jinine ya fara bi mata ta hanci da baki.
Da sauri sadiq ya mik’e zai kira doctor, hannu sa ta riqe tana girgiza masa  kai  tana motsa baki can yaji jikinta yayi sanyi cikin  wata  irin  murya  rikice  ya  ce,  “Noooo..! Sulalewa k’asa yayi sumame.

Writing by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Blood sister deeja

📘 REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM

13_14

Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un duk wani mai rai mamacine yau dai kausar ta rigamu zuwa gidan gaskiya, shi kuma sadiq aka wuce da shi emergency dan bai san inda kansa ya ke ba, dangi sunyi kuka sosai na rashin kausar saboda kausar mutuniyar kirkice.

Yau kusan sati daya kenan da rasuwar kausar sadiq na asibiti sosai yake samun kulawa wajan su jawad da majid, wanda bai ma san suna yi ba, Jawad ne zaune a d’akin asibiti saman three star yana shan coffee yana d’an kallon sadiq dake kwance har yau tamkar gawa, sosai yake damuwa da halin da d’an uwan nasa ke ciki.
A hankali yake bud’e sexy eye’s balls d’in sa, abubuwan da suka faru na dawo masa tamkar yanzu akayi su, wani irin kuka ya fashe da shi maitsuma zuciya yana qoqarin tashi ya cire drip din da ke maqale a hannusa, Jawad ne ya taso ya rungumesa alamar lallashi kuka ya qara fashewa da shi yana fisfisgewa kamar zarare yana cewa, “Bros I cant live with out my wife please bros ka barni na bita” ya qara fashewa da wani sabon kukan, ganin abin nashi kamar ba kai d’aya ba ya sa jawad yayi ma d’aya daga cikin yaran sadiq masu tsaron lafiyarsa magana dake tsaye bakin kofa ya ce, “Kiran Dr yakub.
Jum kad’an Dr yakub ya shigo shi da nurse tana d’auke da trayn alururi, dakyar Dr da jawad suka samu suka danne sadiq aka masa alura bacci, sai da yayi kusan 30 minutes yana sanbatu sannan bacci ya d’auke sa Jawad ne ya ce, “Dr Ina fatan dai sadiq ba brain nashi bane ya sami problem ba? ya ida zancan yana matsar kwalla “karka damu kawai mutuwar ta firgi tashi ne amma, insha Allah zai samu sauki daya tashi komai zaiyi normal, Allah bashi lafiya”
“Ameen Dr.

2weeks letter

Sosai Jidda ke samun kulawa wajan Mom da baba jummai da mai aikin ta Mary, sadiq ko duk wata walwala ya daina idan kaga yana smile to Jidda na hannusa, inda ya d’aura mata son duniya nan wani bangare na zuciyarsa kuwa ji yake Nigeria ma ta isheshi saboda ya rasa abar kaunar sa, daga karshe ya yanke shawawar barin kasar bai samu wata matsala ba wajan aikinsa ya d’au hutu sheraka d’aya, Mom ce zaune a parlour sadiq na riqe da jidda wanda bacci ya d’auke ta acinyar sa cikin sanyi murya kamar mai koyan magana da yanzu magana ma wuya take masa ya ce, “Mom Ina san nabi jawad londan idan zai koma”
“toh ai shikenan son”
“Amma Ina san idan zan koma na koma da Jidda, saboda sai hankali na yafi kwanciya” Mom ce ta daka tsale ta dire ta ce bata san zancan ba, ba inda zai tafi da ita duka yarinyar nawa take zai tafi da ita, ba yarda ya iya ya hakura wannan kenan.

CIGABAN LABARI

A hankali ya d’au jidda wanda ke bacci ya kaita bedroom ya kwantar da ita ya shiga wanka, inda yake jin mutuwar kausar ta dawo masa sabuwa sai da ya zubar da kwalla sosai, 30 minutes yayi yana wanka ya fito sanye da bathrobe, A hankali ya kai lips d’in sa goshin Jidda ya mata peck, ware manyan eye’s ball din tayi ta ce, “Daddy.!
“oya tashi ayi wanka muje yawo wajan hajiya da Umma” baki ta washe ta ce, “ok daddy.! d’aukarta yayi ya kaita bathroom ya wanke ta tas suna wanka suna wasan ruwa.

****
Yanzu saboda Allah fatuha kin kyauta kenan? ince bana ce ki kyale Rabi’u ba eh?
“yo inna ji nayi kwarankwatsi bana iya hakura”
“Aikin kyauta tunda kin sa maitafasa tamin tanadi kinji d’ad’i saiki zubar da ruwa a qasa kisha” baki ta turo gaba ta ce, “Gaskiya inna baki so na kwarankwatsi Baffa yafi sona” ta ida zancan tana matsar kwalla inna ta ce, “Fatu kenan kin ta6a ganin inda uwa ta haifi d’a tace bata so, Kawai dai halin kine ban so fatuha, ki daina tsokana” baki ta washe ta ce, “yo ahe kina so na kwarankwatsi na daina tsokana amma bilahilazi duk wanda ya shiga gona ta sai ya ci wuya Qur’an” Sannan ta zuri takalmanta ta ce, “Inna na tafi makarantar allo”
“Toh Allah ya shirye ki”
“ameen inna..!

*****
Bayan sun fito daga bathroom ya shirya ta cikin gown maroon mai d’an siririn hannu sai mai dogwan hannu a ciki ya gyara mata gashin ta, masha Allah sosai Jidda tayi kyau kamar d’iyar larabawa, peck ya mata a cheeks ita ma ta masa ya ce, ” good girl tayi kyau” baki ta washe ya ce, “oya je ki wajan grandma gani nan zuwa”
“OK daddy” ta ruga da gudu ta fita ya bita da kallo yana smile, shima shiryawa yayi cikin jeans black and red t-shirt mai ratsin black sannan ya maqala ma hannu sa agogo black na zalla fata sai sheki yake, ya zura takalman sa black ba qaramin kyau yayi ba abin ka da farar fata d’an hutu sajan nan nasa ya kwanta luf-luf, a hankali yake sakowa downstair, a parlour zaune ya samu Mom Jidda na zuba mata surutu, cikin natsuwa ya gaishe ta ta amsa sannan yaja hannu Jidda suka fita Mom ta masu a dawo lafiya.

****
Zauna suke suna karatu fatuha tace, “kwarankwatsi na gaji, yo hi haka akeyi ya tasamu gaba ana abu daya”
“Rabu da shi Qur’an nan kadai ya iya a karatun” cewar Fatsima dariya suka kwashe da ita, ashe Malam D’alha ya ji dariyar ya fido so waje yana zare masu idanu ya ce, “Dan buhun uban ku kun raina mutane ko? yau zaku ci uban kune” sai da ya zane masu jikin rad’au sannan ya kyale sun inda suka rinqa jeramasa Allah ya isa.

*****
Dai-dai parking space yayi parking ya fito riqe da hannu Jidda part d’in hajiya suka fara shiga, d’auke da sallama suka shiga hajiya da ke zaune saman two star ta washe hakora tana cewa, “Ah’ah wana ke gani yau, kaine a gidan namu amma yau 6atan kai kayi maigida” Smile sadiq yayi ya langwabe kai ya ce, “Kai hajiya sokike ki ce bana zuminci ko? sannan ya samu waje ya zauna hajiya ta ce, “Dama yi kake? ta ida zancan tare da qwalawa Asiya mai aikin ta ta kawo masu kayan motsa baki “oh ashe da wannan yan neman ka zo” hajiya ta fad’a tare da jan Jidda ta d’aura saman cinyarta sadiq ya ce, “Kawo maki ita nayi ta maki 6ana”
“lallai kam aiko da taci na jaki” su duka suka kwashe da dariya sun dad’e sosai suna hira sannan suka wuce part d’in Umma.
Da sallama suka shiga Umma dake kitchen ta leko ganin sadiq ta washe baki ta ce, “ah’ah yau za’ayi ruwa da qanqara” da gudu Jidda ta ruga ta rungume Umma, Shagwabe fuska sadiq yayi tare da zama yana cewa, “Umma har da ke cikin masu ce min bana zuminci” kamar daga sama ya ji saukar magana “Toh dama yin zuminci kakeyi” cewar majeed juyowa yayi ya dallama majid harara, sanye ya ke da kayan ball green da alama daga ball yake sadiq ya bud’e baki ya ce, “Toh d’an hana ruwa gudu” yar shewa majeed ya saki ya hau upstairs.
Basma ce ta fito qanwar majeed baza ta wuce 15years ba ta gaishe da sadiq ya amsa ta ja hannu Jidda suka je dakin ta, sun dad’e sosai suna hira da Umman sannan ya bi bayan majid.
D’akin majid ya shiga ya zauna saman sofa lokacin majid na wanka, sanye da bathrobe ya fito yana murmushi ya ce, “Ashe ka biyo ni? harara sadiq ya balla masa majeed ya ce, “bani na kar zoman ba rataya aka bani, ka zo sai yi ma mutane borin kunya kake” ya ida zancan yana dariyar shaqiyanci, basu suka bar gidan Umma ba sai isha’i lokacin su Alhaji sun dawo daga kauya.

****
Fatuha da fatsima ne bakin rafi suna shan mangwaro “bilahillazi mangwaron ga zaqi garai” cewar Fatu
“sosai ma Qur’an” inji fatsima fatuha ta ce, “kin san wani Abu na matsu baba jummai ta zo mu ci d’ad’i nifa tsarabar nake mawa”
“ke dai bari fatuha”
“nima wallahi duk cikin tsarabar wannan bak’in abun yafin dad’i” ta washe baki ta ce, chakule ko (chocolate) lol….

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Blood sister deejah

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄

                                15_16

                   Shirye-shiryan ake sosai kasancewar yau ALHAJI Ibrahim zai dawo daga UK, sosai Mom ke gyara kanta kasancewar Mom irin matan nan ne wanda girman bai hana su gyara kansu wajan miji, abinci ne kala-kala anyi domin abirge Alhaji yau kusan 2week baya nageria.

“Daddy..! daddy..! please wake up daddy” saman ruwan cikin sadiq jidda ke tsale tana kiran suna sa  sadiq  daya  bud’e  idanusa  dake  d’auke da  bacci ya  ce, “oh no angel so kike daddy yayi ciwon ciki, ash bakya ji ko? Cakulkuli ya shaga  yi mata tana dariya tana  cewa, “daddy stop please” ta ida zancan tana mai da numfashi tsakaitawa yayi da yimata cakulkuli ya  ce, “Uhm my angel mai ya tashe ki haka da wuri har kina so ki hana daddy bacci? bayan kin san today is weekend” ya ida zancan yana langwabe kai ala dole yima jidda shagwaba yake, (ohni salma shi dai shagwababe ne ko da yake d’an auta ne… Lol”)  jidda  ta  ce, “uhm’uhm daddy grandpa ne fa zai dawo yau” tana maganar tana wasa da ma6alin rigar sadiq na bacci ya  ce, “Inyee little princess of grandpa” ya lakace mata hanci wangale  baki  tayi  ta  ce, “daddy I miss grandpa”
“I now angel yau zakiga grandpa har ki gaji ko angel?
“yes daddy”
“oya tashi muje na maki wanka na maki make up kifi su Hanan kyau ko? washe baki tayi sadiq  ya  ce, “good girl..! ya d’auke ta suka wuce bathroom.

                           *****
“Inna.! inna..!
“Na’am ohni fatuha wai yaushe zaki girma ne Dan Allah? mutun shekara goma shad’aya amma mutun kullun girma yake yana cin qasa”
“yi hakuri inna wallahi zanina nake nema inna, wanda baba jummai ta siyo min abirni”
“ah yau antuno da baba jummai kenan to zanin yana uwar d’aka na”  Washe baki tayi ta  ce, “eh inna Qur’an na matsu ta zo kwarankwatsi inna”
“ai zata zo insha Allah aikin san duk qarshan shekara ta ke zuwa, amshi kwanan ki kaima Baffan ki kinji”
“to inna.! Baffa na zaune saman tabarma ta aje masa kwanan tare da gaishe shi washe da baki ya amsa da  cewa,  “Fatuha yan’mata.! rufe fuskarta tayi ita ala dole kunyar Baffa take ji  tana  wani  sunne  kai  ta  ce, “Qur’an Baffa ni ba yan’mata ba ce su Tanine yan’mata” yar  dariya  Baffa yayi  ya  ce, “alalai d’iyar Baffan ta ke ma ai yan’mata ce, matso mu ci abincin tare nasan baki ci ba saboda baki iya cin abinci ke kad’ai, kuma inna nasan batayi kalaci ba.
“toh Baffa matsowa tayi tana cin abincin inna ta shigo washe da baki  tana  cewa,  “Kai dai Malam baka gajiya da shagwa6a fatuha da girman ta amma har yanzu tare kuke kalaci baka bari muci tare”
“ah ke ma in zaki ci ki zo muci nasan kishi kike mun ware ki ke kad’ai” murmushi inna tayi ta zauna suka cigaba da kalacin..

                            ****
Misalin karfe 1:00pm flight d’in su Alhaji ya sauka Kano,  a hankali yake takowa ta matatakal jirgin da ka gansa kaga babba mutun sanye yake da shada blue babba riga anmata aiki da dark blue zare sosai d’inkin ya haushi yayi  kyau.
sadiq na jingi ne jikin motarsa black Benz kasancewar shi  ya  zo  d’aukar Abba, qad’an-qad’an ya duba agogo d’ago kai yayi yana kale-kale can ya hango Abba washe baki yayi ya qarasa da sauri ya rugume Abba ya  ce, “I miss you.!
“Miss you more Son” tare da shafa masa gefan fuskarsa bud’e masa murfin moto yayi ya shige shima ya zagaya ya shige driver ya jasu.

Mom ce zaune a bedroom  saman sofa tasha danqareran leshin ta green mai ratsin white flowers, anmata bubu da leshin mai kyau tasha d’auri ture kaga tsiya gashin ta ya leqo sai kamshi ke tashi ba qaramin kyau tayi ba.
dai-dai parking space driver yayi parking Alhaji ya fito shida sadiq yaran sadiq sai qamewa suke tare da kwasar gaisuwa wajan Alhaji, Washe da baki suka shigo gidan cikin sallamar su,  Jidda da ke zaune a palour suna wasa da Jamal qanin Hanan d’an Bilkisu, da gudu Jidda ta rugo wajan grandpa ta rungum sa ita da jamal d’aukar su yayi yana cewa “Ah’ah my little grandchildren kun girma musanman angel, Angel me daddy ke baki? kin qara girma” Dariya tayi ta ce,  “grandpa kullun daddy sai ya bani fresh milk da safe”
“good girl yanzu kin fara cin abinci kenan? washe baki tayi.
Mom ce ke takowa downstairs a hankali d’auke  da  murmushi a fuskarta, A hankali alhaji ya daga kai ya hadiya wani miyau mukut yana binta da mayen kallo (ohni salma tsohuwar zuma tatashi lol) Katse masa tunani tayi ta hanyar cewa,  “Abban sadiq sannu da zuwa”
“Yauwa”
ya hanya?
“Alhamdulillah”
kun zo kun fara cika grandpa da surutu ko? Cewa  aunty  bilki  da  fitowar  kenan  daga  bedroom washe baki su kayi su duka Anuty bilki ta ce, “oya ku wuce kuyi wasa”
Hanan ce ta zunboro baki ta  ce, “Momi nafa girme su ni ai bana wasa”
“Toh yayi uwar mata”
Mom ta bushe da dariya tare da jan hannu alhaji suka wuce bedroom.
Ita da kanta ta taimaka masa ya cire kayansa ya shige wanka inda yake ta zuba mata soyayyya.

             After 1hour Alhaji ne ke sakowa daga stairs shi da Mom sanye yake da jalabiya milk ya fito sak bafulatani glass na manne a fuskarsa dining area suka wuce lokacin kowa ya halara.
Mom ta jaa ma Abba kujera ya zauna itama ta zauna, Mom ta fara serving nasu lunch cuscus ne da miyar dankali taji kaji sosai aciki sai lafiyayan so6o mai sanyi ta zuba ma Abba cikin  nutsuwa suke lunch inda sadiq ke feeding Jidda da Jamal.

                               ****
Bayan sun gama  kalaci fatuha ta kwashe kwani kan ta wanke, ta wuce gidan su fatsima suka wuce rafi, tafe suke suna tsokana dan har yanzu da suka fara irgandangi ba dai  tsokanar su kayi ba, fatsima  ce  ta ce,  “Fatuha kalli wancan ba d’an maigari  bane da kandala”
“Qur’an shine ta6 aiko ya ja ma kanshi tona asiri taho mu qarasa”
Dan mai garine da kantala mai tallah  suke  aikata masha’a bayan bishiya da  sauri  su  fatu  suka  qarasa cikin  d’aga  murya  fatu  ta ce, “asirrin ku ya toni bilahilazi kamar a gaban mai gari” cewar fatuha bala cikin sauri ya fara maida zariyar wandon shi yana zare ido kandala ta fara gyara riga zata d’au tulun ta  .. Fatuha  ta  kada  baki  ta  ce,  “Qur’an ba inda zaku mun kama kwartaye ehe”
“keeee!! Ni sa’an kine zanci uban ku fa yana magana cikin borin kunya
Yar  shewa  fatu  tayi  ta  ce, “bilahillazi Bala ka raina mana wayau mun Kama ku kuna iskanci shine dan baka da kunya zaka zagemu, toh Qur’an sai mun tona, dama rana nan na  d’auki gyadar kandala  tamin raini wayau  to zan je na fad’a ma  malam abinda kike in kin fito tallah..! Kwala kandala ta fara matsewa tana ba ma fatuha hakuri shima bala haka har  ya masu Alqawarin zai basu murtala sannan suka hakura, suka tafi suna dariya.

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Blood sister deeja

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄

                               17_18

                       After lunch sadiq ya kwashi su jidda da Hanan da Jamal zuwa shan ice cream sosai sunje yawo daga nan ya wuce dasu munjibir park, cikin jin dadi suke wasan su duk inda ka kalla a wajan yara ne da manya ke hutawa har ma turawa, resting chair ya samu ya zauna yana Kallan su Jidda yadda suke wasannin su cikin nishad’i daga nesa kuwa yan’mata sai yaba kyansa suke da tsarin shi wasu mamaki su kar dai ace duk yaranan nashi ne, dan iya kar haduwa sadiq ya hadu wasu ma sai jan su Hanan suke a jiki dan su samu damar yi ma sadiq magana ganin ba wasa a fuskarsa ya suka hakura basu suka bar munjibir park ba sai gab da magrib.

               Dai-dai parking space yayi parking ya fito riqe da hannu jidda, Jamal kuma na kafadar sa yaran shi yayi ma alamar su kwaso kayan dake cikin motar su biyo shi da su, haka ko akayi suka kwaso kayan ba komai bane sai kayan zaqi kala-Kala da teddys da kayan wasa da ya saima su.
Anuty bilki na zaune a parlour saman three star Hanan ta rugo take fada  jikinta  ta  ce, “Momi.!
“yeee yan’matan Momi sun dawo” bata ida rufe bakin ta ba sadiq ya shigo yana  Cesar,  “Ah sister ke kadai ce a parlour Mom fa?
“tana part din Abba”
“ok.!  ina baba jummai?
“Tana kitchen”
“ok Hanan kira min rabi’a ta amshi kayanan ta kai maku su d’akin angel”
“OK uncle” rugawa tayi kitchen ta Kira rabi’a.. sanye take da farar riga mai dogwan hannu sai mini skirt da alama wannan kayan unform ne na yan’aiki.

              Har qasa ta duqa ta gaishe shi tare da amsar kayan ta wuce da su bedroom d’in Jidda sadiq  ya  ce,  “sister ni zan wuce masallaci may be sanda zan dawo kin tafi”
“Ai kwana zanyi a gida” waro ido yayi ya ce, “Gidan naki fa” yar  shewa aunty bilki  tayi  ta  ce, “ka manta mai gidan baya nan sai gobe zan koma”
“oh haka har yanzu bai dawo ba?
“eh.!
sannan  sadiq  ya sa kai ya fi ce zuwa masallaci.

                             *****
Duk wata gona dake da bishiyar mangwaro sai da suka leqa suka tsunko nunanu, daga nan suka biya wajan shafi’u mai rake suka amso bashi, acewar duk sanda bala dan mai gari ya basu murtala zasu biyasa bayan  sunyi  tafiya  mai  nisa  fatsima  ta ce, “Kai wallahi na gaji”
Fatu  ta  ce, “ai sai  da nace maki mu zubar da ruwan tulun mu zuba mangwarayan mu cikin tulun, idan mun koma gida sai muce biyo mu akayi muka fasa dibar ruwan”
“kwarankwatsi ke dai fatuha wayau gare ki amma kinsan wani Abu”
“a’a saikin fada.!
“qara muje da ruwan Qur’an saboda mun dad’e”
“Haka kuma fa ga wancan Malam D’alha d’in sai sauri ya ke yaje ya fara zalinci”
“ke dai bari” ta qara gyara tsayuwar tulun ta
“kinko iya qarin jiya fatuha?
“hehe yo tun yaushe na iya shi, Ke nifa Malam D’alha ne baimun ba shiyasa bana bashi hada amma Qur’an na iya”
“toh bilahillazi yau sai kin bashi saboda yau ban shirya ma bugu ba, Ko bishiyar nan da muka hau na maqale duwawuna sai zinga yake” Fatuha ta kwashe da dariya ta  ce, “Sai ki je gida kiyi gashi da ruwan d’umi Inmaki na maitafasa”

       Cikin sallama ta shigo gida inna ta amsa, Inda Sabo ya kamata ta saba da wannan baqin halin na fatuha in ta je d’iban ruwa sai ta shekara bata dawo Ba.
“Inna Ina abinci na?
“yana madafi” kwanan samira ta jawo tuwo ne miya kuka yasha manshanu sai kamshi yake loma daya zuwa biyu tayi, fatsima tayi sallama cikin shirin ta na zuwa makarantar allo, tare suka zauna suka ida cin tuwo zata d’au  hijabin ta kenan inna ta leko daga uwar d’aka ta ce, “yanzu saboda Allah fatuha sai na ce kiyi wanka zakiyi kome? raban ki da wanka tun shekaran jiya wuce kiyi wanka nan ku tai makarantar” baki ta turo gaba tana dire-dire “gaskiya inna ki bari sai na dawo nayi”
“Aifa baki fita sai kinyi wanka”
Da kuka da komai fatuha tayi wanka sannan ta fito suka wuce makaranatar allo.

       Zaune suke a parlou suna hira cikin ni shadi su Jidda sai wasa suke aunty bilki  ta  ce, “Ku dai baku gajiya da wasa ko, Ince dazu ba manjibir park kuka je da uncle ba duk wasan da kukayi a can bai ishe Ku ba ko? Oya ku wuce ku shige bedroom kuyi bacci” su duka suka hada baki wajan  cewa, “sorry Momi..! tare da lagwa6e kai duka parlou aka fashe da dariya.
Abba  ya  katse  dariyar da  cewa,  “Yauwa gobe Ina so ku shirya da wuri  zamu  je family house meeting”
“Toh Allah ya kai mu Alhaji” inji mom sun dad’e sosai suna hira a parlour sannan kowa ya tafi part nashi, Inda su Jidda suka maqale ba su kwana ko Ina sai part din sadiq haka ko akayi da yake shi mutun ne mai son yara.

        Bangaran su alhaji ko sosai suke zuba soyayya tare da gwada wa juna su yarda sukayi kewar junasu, sosai alhaji ke gwada ma Momi salan sa daga nan suka lula duniyar ma aurata.

                         *****
Zaune suke Malam Dalha sai amsar hada yake da zabgegiyar bulala shi a hannu, burin shi bai wuce ya ga su fatuha sun kasa ba ya wanke su da bulalar.
“Ke tashi ki bani taki hada” cikin tsiwa fatuha ta tashi ta fara karanta wa Masha Allah cikin murya mai sanyi da dad’i (ni kaina sai danayi mamaki wai dama  fatuha ta iya karatu haka) Malam Dalha ko sakin baki yayi har ta gama sannan ya koma ya zauna gwiwa sage. lol

                               ***
Tsale-tsale suke kamar ba dare ba cikin bedroom d’in sadiq wasan pillow suke haka shima ya shiga cikin su, wasan su ke cikin nishad’i haka shima sadiq ya biye masu shima kamar qaramin yaro suna haka har bacci ya kwashe su.
Ahankali yasa hannu ya bud’e wardrobe ya ciro picture d’in shi da kausar na maqale a qirjin shi a hankali wasu hawaye masu zafi suka zubo masa, yasa bayan hannu shi ya goge, bazai ta6a  mance wannan ranar ba bayan sun gama wasan pillow shi da kausar suka je waje suna wasan ruwa, anan su kayi picture d’in da  camera cikin  sanyin  murya  ya  ce,  “I miss you my wife..! yana  rungume da pic d’in har bacci ya dauke shi…

Written
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Blood sister deejah

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄

             19_20

Duk yadda Malam D’alha yaso ya daki su fatuha yau dai bai samu hanya ba har aka tashi.
Cikin sallama ta shigo gida, Baffa na tsugunne yana shanya zogala Washe da baki ta gaishe sa Baffa ya ce, “yar Albarka har kin dawo kenan?
“Eh Baffa na dawo”
“Masha Allah ana dai karatu dai ko?
“Eh Baffa”
“Ai haka ake so.! qoqarin cire hijabinta take ta ce, “Baffa ina inna?
“ayo ai yanzu inna ki ta leqa gida su fatsima baki had’u da ita ba?
“Eh..! bata ida rufe bakin ta ba sai ga inna ta shigo, sun dad’e suna hira sama-sama daga nan Inna ta shige madafi..

                    ***
Bathrobes ne sanye a jikin su jidda suna ta tsale-tsale a cikin d’akin sadiq, a hankali shima ya fito daga toilet kamar wanda ke jin tausayin k’asa babu alamar walwala a tatare da shi kasancewar yau ji yake mutuwar kausar ta dawo masa sabuwa yaran ne suka had’a baki wajan cewa, “daddy morning.!
“morning too my little children” Fridge ya bud’e ya ciro fresh milk ya zuba masu a cup’s kowa ya sha.
Anuty bilkisu ce ta shigo part d’in cikin sallamarta ita da rabi’a, sadiq na qoqarin ya shirya su Anuty Bilkisu ta shigo ta ce, “ah bros yaran nan sun hana ka hutawa ko?
“No.!
“oya ku wuce muje baba jummai na bedroom dina tana jiran ko”
“ok Momi..! suka fita a guje ….

Gyaran murya Anuty bilkisu tayi a hankali ta shafa gefen fuskar sadiq wanda ya lula cikin duniyar tunani, A hankali ya dago sexy eye’s ball’s din shi ya ja numfashi ya ce, “Sister..! tare da d’aura hannun shi saman nata, “baby wai meke damun ka ne uhm? gaba d’aya ka chanza yau a ganka da walwala gobe a ganka ba walwala” hawayan da ke maqale a idanun sa yayi qoqarin mai dawa ya qaqaro murmushi wanda iya karshi lips din sa ya ce, “sister ni fa ba abinda ke damuna”
“Toh shikenan naji mai yasa kake kora masu kula da jidda why? Kafi so ka cigaba da kula da ita da kanka ne? bayan kasan hakan ba zai yuyu ba saboda kana zuwa aiki, ka gani baba jummai ba yarinya ba ce bata iya dawainiyar ku kai da Jidda sai dai na Mom, haka gyaran bedroom naka ka hana kowa yama sai ita mai yasa baby ka chanza? ta ida maganar cikin rawar murya langwabe kai yayi kamar qaramin yaro ya ce, “sis ni fa ban chanza ba kawai dai yan’ aikin ne basu ji sis shiyasa, dana aje kudi sai su d’auka baba jummai ce kad’ai bata d’aukar abinda ba’a bata ba, kuma ko aikin basu wani iya ba sai shirme”
“Toh naji yanzu dai ga rabi’a tana parlour ka zata fara gyara ma d’aki daga yau kafin baba jummai ta je kauye ta samoma good girl wadda batada d’an hali” 6ata fuska yayi ya ce, “sis kin…..!
“Shhhh please kayi hakauri for some days baby”
“toh sis” peck ya mata a hannu ta, ta masa a goshi.
Sannan aunty bilki ta cigaba da cewa, “Uhm kayi sauri ka shirya kasan yau akwai family meeting”
“I now gani nan fitowa”
“OK.!

Rabi’a na takure saman one star cikin uniform din ta na yan aiki wanda bata tunanin sadiq ko giya wake yasha bai yarda ta masa aiki saboda so biyu yana kamata zata masa sata, Anuty bilki ta qaraso washe da baki ta ce, “Rabi’a daga yau zaki Fara aiki anan part din na wani d’an lokaci please ki kula saboda na lura ba son aikin naki ya ke ba”
“to.! ta ce tana maida numfashi tare da washe baki, Anuty bilki tasa kai ta fice.

*****
“Fatuha..! Fatuha.!
“Na’am inna”
“zo nan wad’an nan kayan wakika barmawa su raban ki da wanki har kin manta wai yaushe zaki fara tsaf ta ne fatuha eeeeh,? kin fara girma amma kullun rashin jin ki dad’uwa yake, yi maza ki wanke su tas ki shanya” Kuka tasa har da birgima kasa tana cewa, “Qur’an inna ban iya wankin ba alqawalin Allah”
bakin ta inna ta bige ta ce, “wallahi in bakiyi wankin nan ba baki zuwa gad’ar tunda baki san kin girma ba, kuma indai baba jummai ta zo kina ji kina gani zan bayar da tsarabar data yi maki” matse kwalla tayi ta ce, “Toh inna zanyi Qur’an”
“Ah karma kiyi ai ba dole” Inna ta fara tatara kayan zata shige da su daki, jiki a sa6ule fatuha ta amshi kayan ta fara wankin.

*****
Tsaye yake gaban dressing mirror yana feshe jikinsa da turaran intense mai sanyayan kamshi, sanye yake da shirt blue mai dogwan hannu sai jeans dark blue hannu shi maqale da agogo silver na zalla azurfa, farin glass din shi yasa ya fito kamar balarabe ba qaramin kyau yayi ba amma fuskar nan d’aure, qwanqwasa kofar d’akin sa akayi ya juyo tare da furta “yes come in.! rabi’a ce jiki ba kwari kallo d’aya ya mata ya watsar cikin kakausar murya ya ce, “what.?
“Uhm dama kai nake jira ka fita na gyara bedroom d’in” wani irin kallo ya qara wurga mata ya matso gab da ita yana jifanta da kallon tsana ya ce, “Kinsan Allah zan fita ne na dawo wallahi na shigo d’aki na naga banga tsinke ba, huh you will see” fuuu ya ja ya fita ya barta sai 6ari take.

Ahankali ya ke sakowa downstairs fuskarnan tamau dinning area ya wuce, lokacin kowa ya halara za’a fara breakfast gaishe da iyayan nasa yayi tare da yi masu peck a goshi sannan ya samu waje ya zauna.
Anuty bilki ce tayi serving d’in kowa suka fara cin abincin, Mom na lura da sadiq dan ba wani cin abincin yake ba ga fuskar shi d’aure haka shima Abban nashi yake lura, Inda sabo ya kamata su saba da irin wannan halin nashi yau da fara’a gobe babu, a hankali ya ke cin abinci loma uku zuwa hudu ya miqe Mom ta ce, “Son..!
“yes Mom”
“Har ka qoshi?
“Eh na qoshi”
“Amma kasan ba zamu shirya ba ko wannan ai ba abinci ka cin ba” Abba ya amshe zancan da cewa, “shiyasa Jidda bata san cin abinci shiya ke koya mata hakan” Shagwabe fuska yayi ya ce, “Abba na sha fresh milk a d’aki da yawa shiya bana jin yunwa”
“uhm lallai dama fresh milk abinci ne? inji Anuty bilki 6ata fuska ya kuma yi ya ce, “to ni ina sha na ko shi” Langwabe kai yayi ya ce, “Angel wai daddy ne ya koya maki rashin cin abinci?
“no daddy kai da kake cin plate biyu” kowa na dining sai da yayi dariya har da sadiq din wanda tun tashin shi baiyi dariya ba Mom ta ce, “Ohni Jidda wato kare daddy ki zakiyi ko? Mom ta ida zancan tana lakace mata hanci.

******
Ba ita ta gama wankin ba sai yamma likis ta wanke su tas suka fita, inna washe da baki ta ce, “ko ke fa d’iyar Baffan ta” turo baki tayi gaba tare da zubar da ruwan d’aurayar a maguji Inna ta ce, “Oh fushi ake dani dan nace ayi tsaf ta? sallamar Baffa ce ta katse mata zancan washe da baki ya shigo had’e da sallama.
Ledar dake hannu Baffa fatuha ta amsa ya ce, “yar albarka yau wanki akayi kenan? inna ta amshe zancan da cewa, “kasan ko faman dana sha da ita sannan tayi wanki?
“ki ce min dai matsa mata kikayi”
“ai dama kai baka ganin laifin ta”
“hmm fatuha dama Ledan nan tsarabar yallo ce na makin” washe hakora tayi ta ce, “Toh Baffa na gode.!
“Yauwa yar albarka” inna ta shige qurya ta kwaso ma Baffa abincin sa.

Cikin jin dadi ta gama wanke yallon da zubo masu inna na su, sannan ta d’au nata dana fatsima ta fice.

               *****
After sun gama breakfast kaitsaye family house suka wuce.
karku so kuga soyayya dangi ba tsangwama ba tsana sai tsantsar soyayya, wadda uwar mazajan na su ke gwada masu ba tare data banbanta wani ba.
Wani katafarin parlou ne wanda ya amsa suna shi yasha red carpet mai laushi sai manyan kujeru red n black, sosai tsarin parlou ya had’u Alhaji kabiru ne ya fara magana cikin muryar shi ta manya da natsuwa yana fadin irin kadarurin da suka samu a kasuwancin su, inda Baban nasu ya yanke hukunci za’a raba kudin kashi biyar, kashi 5 nasu kashi biyar na taimakon Al’umma, Kashi 2 za’a kai gidan marayu kashi 1 asibiti kashi 2 taimakawa marasa karfi, sosai sunji dad’in yarda Baban nasu ya tsara abin bayan sun gama tattaunawa akayi addu’a aka tashi kowa ya koma harkar gaban sa.

“Big man wai lafiya yau sai wani cin magani kake? inji majid sadiq ya ce, “to wazan ci ma magani kai wallahi ka bani sai shegyan surutu” ya ida zancan ya furzar da iskar bakin shi, “Naje nayi surutun in fitsari arhane wani yayi mu gani, wani saboda tsabar rashin yin maganarsa bakinsa wari ya ke” ya ida maganar yana dariya “oh dani kake ko? da gudu majid ya ruga part d’in Ammi sadiq ya bisa Ammi da ke hira da surukanta.
majid ya zo ya boye bayan ta Ammi ta ce, ” Lafiya kai kuma?
“wallahi Hajiya.! bai ida zancan ba sadiq ya shigo fuska d’aure Ammi ta ce, “Ayo ai sai ka ce min wannan mai bakin ran ka tsokano” kowa na d’akin sai da ya murmusa, langwabe kai sadiq yayi ya ce, “Ammi yanzu nine mai bakin rai, kin san mai yamin kuwa?
Alhaji ya ce, “rabu da su aikai d’an wuri nane kaji” Majid ko gwalo ya masa bai san Ammi ta gansa ba ta ce, “to ja’iri Ashe kai ka tsokane sa tashi ka ban guri” dariya kowa na parlou yayi.
Sosai jin dadi suke family inda suke hira cikin ni shadi..

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Blood sister deejah

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄

21_22

Basu suka dawo daga family house ba sai 9:00pm, Anuty bilki ta wuce gidan ta.
A gajiye likis ya dawo dan haka direct toilet ya shiga yayi wanka yana fitowa ya d’au jidda ya mata wanka sai rigima take masa, sai daya gama shirya ta tsaf ya samata night dress pink wando da riga ya raba mata gashin ta gida biyu sannan ya kwatar da ita ya ce, “Oya yanzu ayi bacci”
“Bana jin bacci daddy please ka bani story”
“Ok angel bari daddy ya shirya”
“Toh daddy am waiting” Sai daya shirya sannan ya qarewa d’akin kallo ba laifi ta gyara d’akin amma dai shi gyaran bai masa ba, riqe da story book din jidda ya dawo saman bed lokacin har tayi bacci smile yayi tare da yi mata peck ya jawo laptop d’in sa ya cigaba da aiki, bashi ya gama aikin ba sai 12:00am sannan ya kwata tare da jawo Jidda jikinsa kamar za’a kwace masa ita.

****
Sosai suke kallan gad’a washe da baki kasancewar yau suka fara zuwa Fatuha ta ce, “ta6 Alqawalin Allah kallo na wuce mu”
“Sosai ma” inji fatsima
“ke ni daga yau ban qara fashi wallahi kullun sai na zo”
“nima haka Qur’an” haka suka sha kallan gad’a daga nan kuma suka fara tsokana dan wannan ya zamar masu jiki sannan suka dawo gida.

****
Tunda safe ya tashi kasancewar yau Monday cikin shirin shi na uniform ya ke shiryawa ba qaramin kyau yayi ba, gafen da Jidda ke kwance ya kalla da alama baccin ya mata dad’i dan haka sai bai tashe ta ba hakan yasa baiyi mata wanka ba, briefcase nashi ya d’auka tare da yi mata peck ya fita.
A parlou shi ya ci karo da rabi’a na shara, kallan tsana ya bita da shi har yayi gaba ya dawo ya ce, “Keeee..! cikin tsoro ta d’ago qara murtike fuska yayi ya ce, “Angel na bedroom tana bacci so kibi hankali karki tashe ta, kuma idan tatashi ki mata wanka kina jina..!
“Eh..! ya watsa mata harara ya ce,
“saura na dawo naga kin min sata” ya ja tsoki ya fice.

A main parlou ya samu Mom zaune tana karanta azkar, har qasa ya duk’a ya gaishe ta tare da yimata peck Mom ta ce, “baby..!
“na’am..!
“Ina Jidda sarkin kiriniya?
“Jidda na bacci.”
“Ok shiyasa ban ji motsinta ba kenan”
“eh Mom so nake ma na samama Jidda school da malamin islamiyya ya rinqa mata a gida”
“Ai hakan na dakyau kamar kasan maganar dana ke san yimaka kenan ka rigani” smile yayi tare da wucewa dining area a tsaitsaye yayi break ya fita.

*******
Tana tashi tayi wanke-wanke sannan ta share gidan su qwal ba laifi yanzu fatuha anfara yin aiki shima din sai tasa kanta, inna ce ta fito washe da baki ganin abin arzikin da fatu tayi ta ce, “Ah’ah fatuha an fara zama yan’mata, dubi yarda gidan yayi fes gwanin birgewa” rufe fuskarta tayi ala dole kunyar inna take ji inna ta ce, “ohni fatuha kunya na ake ji to madalla Allah ya shirye ki?
“Ameen inna” tare suka shiga madafi yau dai ba laifi fatuha tayi aiki sosai dan yau ko damar zuwa gantali bata samu ba.

****
Baba jummai ce cikin d’aki sai harhad’a kayan ta take cikin ganamasgo cike da tsantsar farin ciki Mom ce ta lek’o dak’in tana cewa, “Baba sai sauri kike ki tafi harkin had’a kaya” Washe baki tayi ta ce, “wallahi na matsu na ganni a wudil d’in nan na dad’e banga d’an uwana ba jauro”
“gaskiya kam, yauwa maganar samomin yar aiki fa? dan Allah baba jummai ki samomin natsatsa wadda zata iya aikin nan kisan halin baby da shegiyar tsurfa”
“Insha Allah zan duba maki” Sannan Mom ta ciro maqudan kudi tabawa baba jummai tayi tsaraba tare da had’ata da driver ya kaita tasha, murna wajan baba jummai ba’a magana,
Ana kaita ko tasha ta samu motar zuwa wudil dama mutun d’aya ake jira tana shiga mota tatashi.

***
Baffa ne tsaye bakin kofar d’aki yana cewa, “ladingo ni zan wuce yau da wuri zan dawo karki aiko min da abinci”
“toh malam” fatuha da ke zaune bisa tabarma ta ce, “Baffa zanbi ka”
“kinga zafi ake ga rana idan muka je tare wuya zaki sha fatuha” baki ta turo gaba ta fara matsar kwalla Baffa ya ce, “toh shikenan d’ako hijabin ki muje” washe baki tayi tare da shigewa akurkin d’akin ta ta d’auko hijabinta suka fice.

Misalin karfe 2:00pm motar su baba jummai ta tsaya a tasha wani irin dad’i ne ya lullu6e ta yau ta zo mahaifarta zata ga d’an uwanta da iyalan sa mashin tatara kasancewa mota bata shiga cikin garin sai dai mashin ko amalanke.

Direct gidan Baffa aka sauke ta tare da biyan maimashin sannan ta sauke yan kayan ta da tsaraba, washe da baki ta shiga gidan tare da sallama, inna dake qoqarin fitowa daga madafi chak ta tsaya, saboda tsabar murna ta rasa ina zata tsoma kanta ta ce, “Ah’ah muta nan birni sannu da zuwa” ta qarasa zancan tare da shinfid’a mata tabarma ta d’ebo mata ruwa a kwanon sha na randa mai sanyi Baba jummai ta ce, “ah ladingo sai hidama kike kya bari mu gaisako” Washe baki tayi ta ce, “mutun ya sha tafiya ruwan sha ya gagaresa, toh ya hanya?
“Hanya lafiya lau, ina fatuha yan’mata nasan yanzu dai samari sun fara yi mata layi masha Allah, indai kyau ne fatuha akwai shi”
“Hmm..! inna ta ce ta marairaice ta ce, “sun fita da Malam zuwa gona, maganar samari kuwa fatuha babu su, fatuhar da bata ganin kowa da gashi a kauyan nan wani uba ne zai yarda d’an sa ya auri fatuha bayan ta masu rashin kunya, malam baya ganin laifinta ko kad’a ko nayi mata magana zai fara sababi”
“alallai jauro haka ya bar fatuha ta zama abinda ta zama ohni jummai.! bari shi jauron ya dawo ya same ni” Haka inna ta rinqa lalla6a ta dan bata so tayi ma Baffa magana saboda kan fatuha bai jin kunyar maida magana haka baba jummai ta gama kunfan baki.

****
koda jidda tatashi bata ga daddy din ta ba, dakyar ta yarda rabi’a ta mata wanka shima sai da Mom tasa baki, ana gama mata wanka ta sako downstair wajan Mom tana mata surutu can ta ce, “grandma Ina baba jummai yau bata min wanka ba ita da daddy” ta Ida zancan tana matsar kwalla Mom ta ce, “sorry angel” tare da goge mata kwalla sannan ta jata jikinta ta ce, “baba jummai ta je kauye lokacin da zata tafi kina bacci shiyasa angel”
“Grandma shi kuma daddy fa ya tafi ya bar little princess d’in sa at home”
“sorry angel ai zai dawo kin ji.!
“grandma please call him”
“Ok angel amma sai kinyi breakfast sannan”
“ok..!
“oya muje nayi feeding naki.
Alhaji ne yayi gyaran murya ya ce, “uhm kina shan fama babanta ya maki rigima ita ma ta maki” murmushi tayi tare da shafa sumar Jidda wadda tasha gyara, tana feeding Jidda sai da suka gama tsaf sannan shima Alhaji ya wuce office.

After sun gama cin abincin Mom ta kira sadiq, yana zaune saman kujerar sa ta office idanun sa a lumshe kamar maiyin bacci wayar sa ta fara ruri a hankali ya bude sexy eye’s ball d’insa ya sauke su kan screem d’in wayar, sweet Mom ne rubuce hannu ya kai ya d’auka.
daga d’ayan bangaran Mom ta ce, “hello baby ya kake ya aiki?
“lafiya lau Mom”
“Dama wannan ja’irace ta matsamin ka tafi aiki baka tashe ta ba, sai rigima take mani” murmushi yayi daga dayan bangaran hakan sai ya qara fitowa da zallan kyan sa numfasawa yayi ya ce, “Mom bata wayar”
“ok..!
Jidda dake zaune saman cinyar Mom ta washe baki tare da amsar wayar ta ce, “daddy..!
“yes angel” 6ata fuska tayi kamar yana ganin ta ta ce “shine daddy ka tafi work baka tada little princess d’in kaba”
“sorry angel lokacin kina bacci bana so na tada little princess na bacci that is why my angel”
“ok daddy inka dawo zamuyi wasa ko?
“yes mana” washe hakora tayi sannan ta ce, “uhm daddy.! ta qara bata fuska ta ce, “daddy baba jummai tatafi kauye ban dani bayan tamin promise tare zamu tafi”
“sorry angel next time tare zamu tafi kinji”
“Yeeee love u daddy.!
“Love u more angel bye” sannan ya katse wayar tare da binta da kallo.
“Yanzu tunda kinyi wayar da daddy naki sai ki huce ko” cewar Mom dariya tayi ta cigaba da zuba ma Mom surutu..

****
Aiki Baffa yake sosai fatuha na gefe tana taya shi, tare da bashi labari tana fadin abin dariya ya dara haka har suka gama.

d’auke da sallama suka shigo inna na zaune saman kujerar tayani gulma tana dama hura saboda Baba jummai nasan hura musanman damun inna, washe da baki suka qaraso fatuha ko jikin Baba jummai ta fada tana mata oyoyo Baffa ya ce, “Ah’Ah wanake gani kamar mutanan birni sannu da zuwa” sannan Baffa ya samu guri ya zauna inna ce ta ce, “ohni fatuha yaushe zaki girma kin fada mata jiki salan ki karya ta.! baki ta turo gaba ta ce, “Kai inna har wani nauyi ke gareni tare da matse yar kwalla, baba jummai ko dariya abin ya bata…

Writte by
Salma mas’ud nadabo

Editing Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄

                          23-24

        Tashi tayi daga jikin inna tana zun6uro baki gaba,  Inna ta ce “Yar nema ba’a isa ayi maki magana bane ko me?
“Haba ladingo  wai me yasa kike so ki rinka takura wa yarin yan nan ne? cewar Baffa Baba jummai ce tasa baki ta ce, “Ah kuyi hakuri dai, Indai jiki nane ai ta sauka ko? Inna ta murmusa batace komai ba.

           Duk wata tsaraba data kawo haka ta bajewa fatuha kayan zaqi  fatuha ko baki har kunne dan dadi saboda har da bakar alawa, wato (chocolate) haka shima d’an uwan nata da matar sa ta basu nasu tsarabar, sosai sunji dad’i musanman ladingo wanda take ganin baba jummai ta d’auke ta tamkar ciki d’aya suka fito, so da yawa tana fifitata kan jauro d’in ma saboda karamci irin na baba jummai da sani darajar d’an adam, sosai suka ji dadin wannan tsarabar.
A guje fatuha ta qaraso gidan su fatsima kawo mata nata tsarabar, saboda dama ta mata alqawari duk sanda baba jummai ta zo, to zata kawo mata bakar alawa”(chocolate) .
Washe da baki ta qarasa cikin  gidan  nasu  tana  cewa, “Fatsima! Fatsima!
“ohni fatuha lafiya nagan ki haka? ko yauma tsokana kukayi? inji gwaggon fatsima washe baki tayi ta ce, “Wallahi gwoggo baba jummai ce ta zo yau shine na kawo wa fatsima tsarabar ta”
“Ayya ki ce min mutan birni sun zo, aiko fatsima na kewaye ki jira ta tafito” bata ida rufe bakin ta ba fatsima ta fito washe da baki Ta ce “Fatuha”
“na’am..! tare da qarasawa wajan fatu  ta  ce, “ke baba jummai fa ta zo Qur’an”
“Dan girman Allah? washe baki ta kuma yi ta ce .”Tayi tsarabar baka alawa?
“Eh Qur’an gama taki nan na kawo maki,”
“kai amma naji dadi” haka suka shige akurkin dakin fatsima suna ta hira tare da sherance muta ne inna da ke tsakar gida sai cewa ta ke Allah ya shirye su.

                         ****
A gajiye ya dawo gida  briefcase din shi da ke hannu yaronsa OLA ya amsa cikin sallama ya shigo falon, Mom na zaune a parlou tana kallo angel na kusa da ita tana bacci, A hankali ya qaraso yayi hug din Mom ta baya ya ce  “Wash Mom am tied” juyowa tayi suna facing d’in juna ta amsa masa da cewa “Sorry son ka je part d’inka kayi taking  shower lunch inka  na jiran ka”
“Ok, face din Jidda ya dan shafa.. sannan ya haura  upstairs.

Yana shiga part na shi bathroom ya wuce yayi wanka ya fito sanye da bathrobe white, A hankali ya  nufi dress mirror ya fara shafa lotion mai kamshi yabi ko ina na jikinsa da shi, kai tsaye Wardrobe d’insa ya nufa ya curo three quarte black sai armless t-shirt ya sa , ba qaramin kyau yayi ba masha Allah.

         Cikin natsuwa ya ke sakowa daga downstairs  ya qaraso  parlour inda ya bar Mom har yanzu nan take, Dining area ya nufa, ya ja kujera ya zauna rabi’a na gefe a hankali ta fara saving na shi tuwan shinkafa miyar egushi wanda taji kaji da yan ciki kamshi sai tayi yake, sai data gama serving nashi  sannan ta mike, harara ya dala mata  dan shi kwata-kwata yan’ aikin kona masa rai suke musanman yan’mata wayanda ba abinda suka sa gaba sai halin bera, wani wawan tsoki ya kuma ja wanda yasa rabi’a kyarma, dagowa yayi da sexy eye’s ball’s din shi ya ce… “Keeee!Tunda kin gama zubamin abincin ai sai ki tafi ko? ko sai kin gama qaremin kallo eeye.”

Mom dake parlour sai data ji tsawar da Sadiq ya daka ma rabi’a juyowa tayi ta ce, “Why son? Wai me yasa kai kullun sai an jika da masu aiki ne  baby? gashi nan yanzu garin fad’an ka ka tada angel daga bacci” Bata fuska yayi kamar qaramin yaro ya ce, “Mom ni wallahi bana san yan’aikin nan yawancin su duk barayi ne Mom kuma  qazamai” ya ida zancan yana tsame hannu sa daga cikin plate d’in abincin  tare da dalla wa rabi’a harara y’all ce, “ai saiki zo ki kwashe ragowar abinci ki cinye mara mutunci kawai..! ya qara jan tsoki mtssss..! ya dawo  parlour ya zauna tare da d’aura Jidda a cinyar sa ta  ce, “Daddy please muje shan ice cream”
“Ok angel bari na d’ako car key sai mu fita” aje Jidda yayi saman three star sannan ya haura sama.

                            *****
Sai da suka kusan cinye rabi alawar, sannan suka saurara mata sai dai muce Allah ya  tsare kar ayi zawo.
Sai yamma likis fatuha  ta waiwayi gida shima d’in ma dan zata canza kaya dan ta je gad’a Washe da baki fatuha ta qaraso gida, Inna da baba jummai sai labari suke saman tabarma ta zo ta wuce su, baba jummai washe da baki ta ce, “Fatuha yan’mata” murmushi tayi tare da shigewa uwar d’aka, baba jummai ce ta qare mata kallo tsab ta ce “Masha Allah fatuha kyakyawa ce sai dai  rashin jita baya bari a gani” tana da d’an tsawo dai-dai gwargwado ita ba gajera ba kuma baza’a kirata doguwa ba, tana da karan hanci kamar biro, bakin ta d’an qararami ne pink, ba laifi tana da hips sai dai yanzu ne ta fara kirgan dangi , wannan kenan, baba jummai ce ta numfasa ta ce…”Ni ko ladingo ina so inzan koma zan tafi da fatuha, dama  hajiya tace na nema mata wanda zata dinga taimakama yar jikarta saboda yarinya ce, shine da na yanke shawara idan jauro ya dawo daga gona sai mu tattauna kan zancan”
” Ta6 baba jummai bana jin malam zai yarda da batun ki, saboda  baya bari taje ko ina iyakar ta cikin kauyan nan, baba jummai da malam zai yarda da haka nima da zan so hakan, ko dan fatuha ta gyaru tunda nasan birni da kauye ba d’aya bane dole inta je can ta nutsu suma  yan  kauyan  su  huta” nisawa baba jummai tayi ta ce, “Bari jauron ya dawo ni na masa magana”
“toh Allah yasa ya amince..

  Fatuha ce ta fito washe da baki daga uwar d’aka, tasha jan baki a dole yau itama gad’a zata ta ce “Inna nayi kyau? murmushi inna tayi ita da baba jummai suka hada baki suka ce, “Kinyi kyau fatuha” qara washe baki tayi sannan ta sa kai ta fice.

                         *****
Riqe da car key ya dawo main parlour tare da d’aukar Jidda ya ce, “Mom zamu fita shan ice cream may be mu biya gidan Anuty bilkisu”
“OK a dawo lafiya, angel amin tsaraba fa”
“toh grandma” sannan suka fita.

    Ko da suka fita anwanke masa motarsa CRB black, Kaitsaye wanja motar suka wuce  ola ya bud’e masa murfin motar dana Jidda tare dayi ma Jidda wasa sannan suka sa kai suka fita, sosai yayi yawo da Jidda, daga nan suka wuce gidan Anuty bilki.
Cikin jin dadi ta tarbe su inda ta cika Sadiq da kayan fruit Jidda ko sai wasan su suke ita da jamal, da murmushi Aunty bilki ta ce…”Ohni baby yanzu an fara zuminci” tana fadin hakan ne cikin zollaya, harara ya wurga mata ya  ce,  “oh you mean da bana zuminci ko tunda haka kika ce bari na tashi na tafi” hararar wasa ita ma ta masa ta  ce, “tab naga yarda zaka fita daga gidan kuwa” hira suka sha sosai daga nan suka wuce family house.

     Part din ammi ya fara zuwa  tana zaune saman one star tana kallon film din India wanda ko za’a kashe ta bata san me suke cewa ba, washe da baki ta juyo tana cewa “Ah’ah yau mai gidana da kansa? ya  Hauwa’u ita da  Ibrahim d’in?”
“lafiya lau” ya ce tare da zama
“Ka ce min da sarkin surutu ka zomin yanzu ta fara min wannan yaran nasu na yahudawa” Murmushi Sadiq yayi ya ce, “Kisha kurimin ki Ammi ai koya maki take”
“Ah ni ina zan iya wannan gwalangwatsin wannan sai ku” Asiya ta kwallawa kira, cikin sauri ta qaraso  tare da gaishe da sadiq Ciki-ciki ya amsa kamar mai koyan magana Ammi ta  ce, “Yauwa yan’nan kawo ma mai gida furar dana dama d’azu tana cikin fridge”
“toh Ammi” ta mike ta wuce kicin.
Haka akayi ta kawo masa fura ya sha sosai, saboda shi Sadiq mutun ne mai son fura sai da ya sha ya koshi sannan suka wuce part d’in Umma,

  Suna shiga part d’in da Basma suka ci karo, sanye take da riga da wando riga mai dan gajeran hannu pink mai manya flowers tayi kyau sosai duk da yarinya ce hakan yasa shape din ta fitowa, Kallo d’aya Sadiq ya mata ya watsar Gaishe sa tayi tare da jan hannun Jidda tana mata wasa  sadiq ya ce “Basma ina umma?
“Umma na bedroom”
“OK ki  ce  mata  na  zo” Sannan ya samu  guri ya zauna.
Umma  da murmushi ta fito sun dad’e suna hira, Inda tasa talatu ta cika masa tray da kayan motsa baki ,suna cikin hira majid ya dawo suka dasa sabuwar hira.

                        *******
Sosai suke jin dad’i gadar inda yau sai da su fatuha suka taka, duk da ba wani abu suka iya ba, Sosai sun burge mutane ita da fatsima saboda cikin tsari suke rawar su kamar manyan yan’mata….!
Writing by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘 REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★ we are the best★

https://mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&_tn_=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

                    25_26

         Basu suka dawo gida ba sai bayan isha lokacin har jidda tayi bacci,  d’auke yake da ita har suka qaraso  parlour, lokacin rabi’a tana qoqari fitowa daga kitchen, wani irin kallo ya wurga mata jiki ba qwari  ta gaishe shi har tayi gaba ya ce, “Keeee.! Tsayawa tayi cikin tsoro da fargaba, Harara ya qara wurga mata cikin tsawa ya ce mata “Sai ki zo ki amshe ta ko?” Jiki a sa6ule ta amshi jidda, ya  ce,  “Kiyi mata wanka sannan ki samata night dress ki kawo min ita d’aki na dan ban yarda ta rinqa kwana da ke ba ki koya mata halin bera” tsaki yaja  Mtsss, sannan ya wuce part din Abba.

            Abba na  zaune  saman two star fuskar shi manne da glass, sanye yake da fara jalabiya blue remote ne a hannusa yana kallon news, Mom na gefen sa tana yanka fruit.
D’au da  sallama ya shigo tare da gaishe da Abba,  cikin fara’a Abba ya amsa ya ce “Ah har kun dawo daga zuminci?
“Eh Abba”
“toh masha Allah ina jidda?
“jidda tayi bacci”
“madallah” sun dad’e suna hira sama-sama daga nan Sadiq ya wuce part nashi, ko da ya shiga d’akinsa ya iske ankwantar da jidda shima bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito sai da ya gama shirin shi na bacci sannan ya had’a coffee yana sha yana dana laptop din shi ,ya dad’e a haka sannan ya ture laptop d’in tare da janyo jidda jikin shi bacci ya d’aukesa.

*****
Bayan an gama gad’a kowace ta wuce gidan su, da sallama fatuha ta shigo gida lokaci Baffa ya dawo gida yana zaune bisa tabarma inna na kusa da shi baba jummai na gefe su, gefan baba jummai ta je ta zauna washe da baki itama baba jummai murmusawa tayi sun danyi hira sama-sama da fatuha daga nan bacci ya sureta.

      Baba jummai ce tayi gyaran murya ta ce “Dama jauro ina so muyi wata magana da kai” inna da ke kusa da Baffa tayi qoqari tashi baba jummai ta ce “Kema  zauna” haka ko akayi inna ta samu guri ta zauna.
Gwoggo  ta  cigaba  da  cewa, “Dama so nake nama ka magana kan fatuha ina so idan zan koma birni sai mu koma tare,” Zaro ido Baffa yayi waje yana kallon yar uwar tasa a zuciyarsa ya ce “Anya ko baba jummai tasan me take fada kuwa?”qara murmusawa tayi ta ce, “jauro ina fatan ba za ka watsamin qasa ido ba, a ganina fatuha nima d’iya tace  jauro,” Baffa ne  yayi tsale  ya dare ya ce bai san zancan ba babu inda fatuha zata tanan kauyen nan tare da shi baze lamunci hakan ba, baba jummai ce ta fara matsar kwalla tana cewa “Ba komai jauro dan ka ga Allah bai bani haihuwa ba shine zaka wulaqanta ni kan diyar ka, jauro da Allah ya bani haihuwa da yau ba zanji zafin abinda kayi min ba,” tana maganar tana kuka inna sai lallashinta take, ganin kukan da take yasa jikin Baffa yayi sanyi dan shi a ganinsa babu abinda baba jummai zata nema a rayuwar shi ya hana ta, sai  gashi  kan  fatuha suna  neman  samun  Matsala da  yar  uwarsa.
Bayan da ya iya haka ya hakura ya amince  tatafi da fatuha, aiko washe da baki ta masa godiya tare da yi masa alqawarin zata riqe amanar fatuha sosai daga nan kowa ya wuce dakinsa.

******
Ko da ya tashi ya gama shirin sa ciki uniform masha Allah yayi kyau sosai,  zai d’au briefcase d’in sa kenan jidda ta tashi washe da baki ta ce, “Daddy morning”
“morning too angel”
“uhm yau ma daddy guduwa zakayi ka bar little princess din ka a gida? langwabe kai yayi ya ce “Sorry angel daddy work zai tafi kinji kuma yara basa zuwa, kema very soon zaki fara zuwa school ai kinaso ko angel? washe baki tayi ta ce “Yes daddy zan fara zuwa school kamar yarda su yaya Hanan ke zuwa da Anuty Basma ko?
“Eh mana angel” tsale tayi ta kai masa hug “thanks my daddy” smile yayi tare da yimata peck ya  ce,  “please angel ki tsaya rabi’a ta maki wanka kin ji, naji grandma na cewa kullun sai kin yi rigima” 6ata fuska tayi ta ce, “Daddy…!
“shhhh.! tare da yi mata peck a kumatu ya fice.

      A dining area ya had’u da Abba shima yana breakfast, Mom na  gefen shi a hankali ya qarasa yayi masu peck sannan ya samu waje ya zauna ya fara breakfast, lafiyayan chips ne da plantain and egg sai tea mai kauri wanda ya sha ovaltine, cikin natsuwa suka gama break d’in su, Abba da Sadiq tare suka fito inda yaran Sadiq ke ta kwasar gaisuwa wajan Abba   tare da qamema Sadiq d’in cikin natsuwa motocinsu suka fita daga harabar gidan.

                         ****
Ko da fatuha ta tashi wanke-wanke tayi, sannan ta d’au tulun ta gidan su fatsima ta biya tare suka fito suna tafe suna hirar su, kandala suka hango d’auke da farantin gyadarta qarasowa su kayi wajan ta, Kallon su take jiki ba kwari  harara suka wurga mata tare da cewa “Bamu gyad’a ta murtala” jikinta baqwari ta fara zuba masu gyad’ar tasan ko zata mutu baza su bata kudin gyad’ar ba, kuma ta matsa masu  su tona mata asiri sai da ta gama zuba masu sannan fatuha ta amsa ta ce  “Cikin Murtala da d’an mai gari ya mana alqawari ne muka amshi gyadar, sannan kice masa ko ya bamu murtalar mu ko kuma murtala ta rinqa haihuwa” sannan suka wuce suka barta tsaye tana matsar kwalla.

            Suna isa rafi suka aje tulu nan su gefen rafi suka wuce gonar mai gari suka fara tsinkar mangwaro da gwaba, sai da suka d’iba son ransu sannan suka zo zasu fita mai gadi ya kama su.
“kai-kai uban wa ya baku ikon shigowa gonar mai gari? har ku tsinke  masa mangwaro.! Fatuha ce ta turo baki gaba ta ce, “bala ne ya bani izinin shigowa”
“shegiya mai kama da mayu, shi balan sa’an kine? Koko  sabo  da  raini  irin  naki  dama  kin  rai  uban  kowa, inama kika san balan? harara fatsima ta wurga masa ta  ce, “idan baka yarda ba sai ka kai mu wajan shi ka ji da kunnan ka” ta ida zancan tana gyara d’aurin zaninta.
“Ai  dama  ba  kunya  ta  ishe  ki ba mindin   naji  akasin  haka  na  lahira  sai  ya  fiki  jin  dad’i ”
Aiko haka akayi mai gadi jan su fatuha yayi har gaban bala, sai yan harare-harare suke koda ya  suma bala ya  masa  bayani sai ya ce, “shi ya ce su d’inba dan yasan in bai ce ba tuna masa asari zasuyi, na  sun  ta6a kamasa  da  kandala gari  kowa  ya  sani  ana  ganin sa  da  mutunci sannan yasa mai gadi ya sake su wani irin dad’i suka ji suna ta shewa suka isa rafi suka debo ruwa.

*****
Bai zame ko ina ba sai Yandutse college dan samoma jidda admission, bai sha wani wahalla ba ya samama ta inda duk angama abinda za’ayi, ranar Monday sai ta fara zuwa school sannan ya wuce office, a cewar shi inya dawo gida da yamma zai samamata malamin adini.

****
Kwanci tashi asarar mai rai yau satin baba jummai d’aya a wudil inda take ta had’a kayanta dana fatuha, Fatuha sai kuka take har da  majina dan ita a ganinta baba jummai bata mata adalci ba ita tace mata tana son birni da zata kwashe ta su tafi, toh Wallahi sai nayi rashin mutunci idan sunje  kenan, cewar  fatu  a zuciyarta baba jummai ce ta juyo ta  ce, “haba fatuha sai ka ce za’a cinye ki sai kuka kike haba fatuha kinsan muna tare kuma zan kula da ke kamar yarda inna zata kula da ke, dan Allah kiyi hakuri kiyi shuru kinji” Inna da ke gefe duk da tana jin wani irin amma tasan baba jummai ba zata tayi abinda zai cutar da fatuha ba amma ko yaya tana jin zafin rabuwa da fatuha saboda fatuha yarinya ce mai shiga rai, ta  wani  fanni  kuma  gara  fatun  ta  tafi  ko  muta  nan  kauyan  sun  huta  da  jarabar  fatuha, a hankali inna ke lallashin fatuha har tayi shuru haka shima Baffa da ke gefe haka baba jummai ta gama had’a kayan fatuha cikin yar leda gari yayi zafi ta miqa mata ta rungume.
Baffa kuma yaje taro masu mashin,  Sallama fatsima tayi ta shigo falon kallo d’aya zaka mata kasan itama ta ci kuka har ta gaji, wani saban kuka suka dasa ita da fatsima dakyar aka lallashe su sannan baffa ya shigo ya sheda masu gamai mashi din.
Suna kallon su har suka 6ace maganin su Baffa ya goge yar kwallar shi, dan shi kad’ai yasan yarda yake ji, suna isa tasha suka samu motar Kano basu wani dad’e ba motar ta tashi.

*******
Idanuwansa lumshe kamar wanda ke bacci,  zaune yake saman resting chair yayi crossing leg’s nashi ta6a shin da akayi ne ya sasa ware sexy eye’s ball’s d’in sa ba kowa bane sai majid murmushi yayi ya ce “Yaushe ka zo ban sani ba?
“yanzu na shigo Mom ta ce min kana nan” sannan ya zauna daya daga cikin chairs din sadiq  ya  ce, “OK ya aiki?
“Alhamdulillah soma nake na dawo nan da aiki, kai Allah ya taimake ka har yau basu ma transfer ba”
“Aiko dai ai bana fatan hakan wallahi” murmushi sukayi su duka suka cigaba da magana a matsayin su na abokai kuma yan’uwa…

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

     https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

27_28

         Misalin karfe 5:00pm motar su fatuha ta tsaya a tasha lokacin har bacci ya d’auke ta tana kafadar baba jummai rungume da jakarta gari yayi zafi, ahankali baba jummai ta shiga tashin ta, aiko nan tatashi tana wani wiqi-wiqi da idanu da qarewa tashar kallo, mutanene birjik haka suka zuro kafafun su suka fito daga motar, Baba jummai ce ta zaro wayar ta cikin zani y’ar baby nokia ce ta  fara  kiran  Mom  ta  sheda  mata  isowarsu bugu d’aya zuwa biyu Mom ta d’auka washe da baki baba jummai ta  ce, “hello hajiya gani na iso ina tasha.! daga d’ayan bangaran Mom ta  murmusa  ta ce.. “masha Allah yanzu zan aiko driver ya d’auke ku”
“Toh hajiya” sannan ta datse kiran tana Murmushi ta kalli fatuha ta  ce, “Yanzu za’a zo d’aukar mu kin ji yan’nan” kad’a kai fatuha tayi dan ita a wannan lokacin haushin kowa take ji.
Ba’a fi  30 minutes ba driver ya qaraso tare da kwashe kayan su ya zuba cikin mota, inda yayi-yayi da fatuha ta bashi Jakarta ta qi ba yanda ya iya haka ko suka tafi.

          Kai tsaye sultan road suka wuce nan fa fatuha ta fara zare ido tana qarewa unguwar kallo kamar wadda ta zo aljana haka take gani, Washe baki tayi ta juyo tana  kallon  baba  jummai ta ce… “Baba jummai dama ashe aljanna kike zuwa? Baba jummai dariya tayi ita da driven ta ce.. “a’a fatuha nan ba aljanna bane birni kenan”
“kai amma kwarankwatsi  kinyi da kika zo dani dafa tare da fatsima kikaso zuwa ko?
“ke da kikaita kuka baki san zuwa”
“Qur’an yanzu ina san birnin 😃.! ta ida zancan lokacin yayi dai-dai da isowarsu katafarin gate din gidan Alhaji Ibrahim, zanso kuga yanda fatuha ke zarar ido.😂
Dai-dai parking space drive yayi parking baba jummai ta kwaso masu kayan su fatuha dai na maqale da ledar ta, ta gari yayi zafi.

       Katafarin parlourn gidan suka shiga, qauyanci wajan fatuha ba’a magana dan ko zama taqiyi saboda tayals sai da baba jummai tayi da gaske sannan ta zauna saman carpet  tana ta zara ido.
Mom ce ke saukowa daga upstairs cikin murmushi ta ce, “ah sannu da zuwa baba jummai” tare da qarasowa parlour da zama saman  two star tana facing d’in su baba jummai d’in ta  ce, “ya hanya? tana murmushi.
“Alhamdulillah,” baba jummai ta ce, “oh tare da yarinyar kuka zo kenan gaskiya naji dadi” fatuha dake ra6e jikin baba jummai ta gaida Mom cikin girmamawa, baba jummai ce ta washe baki ta ce, “Ai diyar qanina ce jauro”
“a’a ki ce min yar tashi ta yi girman haka”
“aiko dai hajiya” Sunyi hira sama-sama inda fatuha ke ra6e jikin baba junmai tana qarewa gidan kallo tare da santinsa.

      Lafiyayan abinci Mom ta basu shinkafa da miyar kaji wadda taji coslow kauyanci ko wajan fatuha ba’a cewa komai, saboda bata ta6a cin irin abinci ba dan haka ta saki tinbi ta ci har da sid’e kwano da qari, Baba jummai dadi taji dan taga fatuha ta saki jikinta.

        Bayan sun gama cin abinci Mom ta kai fatuha d’akin jidda ta gwada mata toilet da duk yadda zatayi anfani da komai na toilet d’in tare da ciro mata uniform din yan’aiki farar Riga da skirt dai-dai gwiwa.
ba laifi fatuha duk abinda Mom ta gwada mata haka tayi..
wanka sosai tayi ta dirje jikinta tare da wanke kanta da shafo, masha Allah gashin fatuha har gadan baya sai dai rashin kulla da shine yasa duk ya cure gu d’aya amma hakan bazai hanaka ganin kyan gashin ba,d’aure da towel ta fito, Mom na zaune saman sofa tana jiran fitowar ta, koda ta d’ago kanta Mom d’in, tayaba da kyau irin na fatuha, Hakan yasata yin murmushi ita ko saitahau sunne kai  Mom  ta  katse  ta  da  cewa,  “Ah har kin fito? D’aga mata kai tayi alamar Eh , uniform din Mom ta d’auka ta bata ta  ce, “ga wannan kayan kullun su zaki rinqa sawa akwai su da yawa cikin wardrobe ranar Friday ne kadai zaki sa kayan gida suma akwai su cikin wardrobe, na ki kuma anfidda su waje sannan in kayan sunyi dati ki aje su akwai mai wanki zai wanke maki su ya goge” Washe da baki fatuha ta ce, “toh.!

   Mom har takai bakin kofa ta dawo tare da cewa, “gobe ki shirya za’a kaiki wankin kai” to tace tare da yima mata godiya Mom na fita ta shafe jikin ta da mai tare janyo kayan da Mom d’in  ta aje mata a saman gado farar rigar ta fara janyowa ta saka amma sai da tasha wuya sannan ta iya balle ma6allin rigar, dai-dai gwiwa rigar ta tsaya mata kallon rigar  fatu  tayi  ta  furta  a fili “Kwarankwatsi gidan ga gidan yan’iska ne yo jifa yadda rigar ta min” skirt din ta janyo ta sa tana sawa taga ya tsaya a gwiwa shima ta  ce, “kut amma Qur’an mutanan sun rainani yo in ban da iskanci haka zanbi gari qafafu bude ta6 bilahilazi ban fita haka” guri ta samu tayi zamanta tana ta kunfar baki tare da jero Allah ya isa.

    Mom dake zaune parlour jin fatuha shuru bata fito ba yasa ta leqo dakin zaune ta same ta har bacci ya fara neman d’auketa saboda  gajiyar tafiya,  ta6ata tayi tare da cewa “Fatuha.! Nanta ware manyan idanunta  Mom tasakar mata murmushi take ce, “hala kin kasa sa kayan tashi kiga yadda ake sawa” nan Mom ta shiga gwada mata masha Allah kayan sun mata kyau duk da fatuha tsine wa kayan take a zuciyar tare da jin haushi kayan.
Bayan Mom ta gama gwada mata ta bata d’ankwali ta rufe  kanta ruf kamar wadda tayi acuci yadda kan ya gwada, sannan ta ja ta suka je parlour suka zaune saboda Sadiq sun fita da jidda shan ice cream.

        Bayan sun gama shan ice cream suka biya shoprite ya siya wa jidda new Teddy’s masu kyau da kayan wasa jidda ko sai murna take a gajiye suka dawo gida, Sadiq na d’auke da jidda a hannusa yana  mata cakulkuli tana dariya *ola* na bayan su riqe da kaya cikin sallama suka shigo, Mom na zaune tana kallo fatuha na gefan ta a takure, a ahankali Sadiq ya qaraso jidda na maqale a jikin sa ya kai ma Mom peck a kumatu, Mom ce ta murmusa ta ce, “baby har kun dawo?
“yes Mom” sweet voice din Sadiq ne ya doki dodan kunnan fatuha ta waigo baki bud’e tana qare masa kallo shi da jidda sakin baki tayi a zuciyarta ta ce, “dama ashe ina da raban ganin yan makka kai baba jummai kwarankwatsi kin dubamin, duk wannan zancan da take idanun ta na kan su jidda, dagowar da Sadiq zaiyi su kayi 4 eye’s da  Fatu harara ya wurga mata saboda yarda  ta  tsare sa  da  idanu ya kauda kansa ya  ce, “wannan wacece bata  iya  gaisuwa  ba  sai  kallon” murmushi Mom tayi ta ce “wadda zata dinga kulla da jidda ce diyar qanin baba jummai ce” kallon fatuhan yayi wadda ke kallon su bata dauke ido ba baki  sake harara ya qara banka mata sannan fatuha ta ankara ashe harara yake aika mata aiko itama ta fakaici idon Mom ta banka masa harara har da murgud’a masa baki,  sakin  baki  baki  captain  sadiq yayi yana mamakin wannan wacce mara kunyar mai aiki ce Mom ta samu wadda bata da kunya haka  har  lokacin  tana  banka  masa  harara a fusace ya tashi ya ce, “keeeee!! Ni sa’an kine..! Kike  kallo  na  haka? Mom da ke zaune ta ce “Sadiq lafiya yarinya na zaman zamanta ka fara yi mata bala’i ka bari mana ta kwana biyu sannan ka nuna mata bakin halin naka, wai me yasa kake haka ne baby? fad’a Mom  ta masa sosai cikin zafi rai ya bar parlour sannan ta shiga ba fatuha hakuri  washe da baki ta ce “ba komai” Mom ta gwada mata jidda ba qaramin dad’i fatuha taji ba zata kulla da balarabiya bayan Mom ta gama yi mata bayani sannan taqara mata da batun zata riqa gyara part din baban jidda sosai fatuha taji dadin hakan.
a cikin zuciyar ta kuwa cewa ta ke Qur’an daba balarabiya ba ce da wallahi bani kula da Ita, shi kuma wancan balaraban ni zaiwa iskaci  wai dan yana da kyau. Qur’an gyara mai zama zanyi bilahilazi duk wannan maganar tana yin tane a cikin  zuciyar ta.

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

    📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★

https//,mobile.facebook. com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&_yn_=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

                      29_30

Mom ce ta haura upstairs ta bar jidda da fatuha zaune a parlour ,a hankali fatuha ta matso kusa da jidda washe da baki tace “Ya sunan ki?” smile jidda tayi tare da fad’a mata sunan ta, sun dad’e a parlour zaune sannan jidda ta ja fatuha suka koma bedroom d’in jidda, jidda ta fara kwaso wa fatuha kayan wasa, washe da baki fatuha ta amshi teddy tana  cewa, “kai Al Qur’an birni dad’i garai yanzu saboda Allah ji wanga halita duk wasa ake da ita kai jama’a” jidda ce ta katse mata zance da cewa, “Anuty garin ku ba wannan teddy ne? nima daddy ke siyo min” dariya fatuha ta fashe da ita ke kekika san wani Daddy mtsss, kuma me Anuty da tedil (teddy)? jidda dariya tayi ta ce, “Aunty  ba sunan shi tedil ba sunan shi teddy, Anuty kuma idan mutun ya girme kane sai ka dinga ce masa Anuty”
“aiyo ai mu a kauyen mu yaya ake cewa ko gwaggo, Ah wanga suna Qur’an dad’i garai haka birni ya ke” jidda dai washe baki take tayi ta samu yar’uwa kamar ta me shegen surutu.
Haka suka rinqa zuba hira tare da wasa ita dai fatuha, zuciyar ta fes dan a ganin ta ta samu gurin zama kiran sallah magrib ne yasa suka tashi, fatuha tayi alwala tare da jidda sannan suka fito dan gabatar da  sallah.

            Bayan sun gama sallah suka dawo parlour, parlour ba kowa sai baba jummai da ke ta jera abinci ita da rabi’a washe da baki fatuha ta gaida baba jummai da rabi’a, baba jummai ce tac e, “Ah fatuha anware kenan?” dariya kawai tayi “toh ga abinci nan idan kuna jin yunwa ku zo ku ci ki tabatar kin ba jidda ta ci ta koshi” inji baba jummai, “toh.! kawai fatuha ta ce mata sannan baba jummai da rabi’a suka shiga  kitchen.
Kamar jira take su shige tayi tsale ta haye kujera dining area dakyar ta iya bud’e kulolin farfesun yan’ciki ne sai dafafan doya da miyar kifi, tunkan ta fara ci miyan bakinta ya tsinkewa, zubawa ta fara yi sai da kwanan ya kai har baki sannan ta tsayar da zubawa, jidda ko sai zaro ido take tana mamaki irin ci na sabuwar Aunty ta,
lol.

   Washe baki tayi ta ce, “Yauwa jidda sauko muci dan Qur’an ban iya ci a saman wannan abin,” haka ko akayi suka sauko qasa suka fara ci, fatuha na ci tana zaro ido saboda dadi kuma ba wai qaramar loma take ba haka zata dauko doya biyo ta turawa kanta ta kuma turawa jidda.

        Zaune yake saman sofa da alama daga wanka ya fito, shafe jikinsa yayi da lotion  mai kamshi, yana gamawa ya feshe jikinsa da turare mai sanyi dad’i, wardrobe ya bud’e ya ciru 3quarte black sai fara t-shirt hannu rigar  dai-dai tamatsa ba qaramin kyau yayi ba bodybuilding  nasa  yafi  gwanin ban  sha’awa da  birgewa gashin nan nashi ya kwanta abin sha’awa luf-luf, ahankali ya kama handle d’in kofar part nashi ya fito.
Cikin natsuwa yake  sakowa daga upstairs, sanye yake da bakin Sweet yayi masifar yi masa kyau, fatuha da jidda na  zaune a k’asa ga plate a gabansu sai loma fatuha ke tura wa jidda, dan ita har ta koshi kuma da hannu take bata abincin, a fusace sadiq ya qaraso tare da dakawa fatuha tsawa “Keeee.! Are you mad? you are very stupid” futaha ko ware ido tayi washe da baki ta kalle shi tace, “Ta6 kai ka san wannan gwalangwatsin Qur’an” sannan ta cigaba ta d’irkawa jidda doya jidda ko sai amsa take hankali kwance, lumshe ido sadiq yayi ji yake kamar ya shaqe fatuha dan haushi daka mata wata tsawar yayi ya ce, “Dan ubanki baki jin nane? uban waye yace kiyi feeding  angel da  hannu ba  spoon ne eeeh?” Turo baki gaba fatuha tayi ta ce, “yo ni ban san inda fida (feeding) take ba ashe ba’a yaye taba Qur’an ban sani ba” sannan fatuha ta ce da jidda “shine kika saki tinbi ina ta dirka maki abinci,to ta yaye kanta sai ka zubar da fida(feeding)lol.
Wani irin baqin cikine ya turniqe sadiq  ya qara wurga mata harara , aiko itama ta rama tana  cewa, “yo a kan me mutun tunda na zo gidan su sai aika min harara yake, ba dan nayima Hajiya Alkawari zan zauna da ita iya wuya ba, da  sai nace banyin aikin ko ana dole ne, kama gode wa Allah saboda Kuna kama da larabawane shiyasa na tsaya da bilahilazi da tuni nayi tafiya ta aha” tare da gyara tsayuwar ta, sadiq ko baki ya saki yana mamaki irin wannan iskancin da  kauyanci tare da  tsantsar  rashin  kunya da  rashin  tarbiya irin  na  fatu  wanda  ko  girman  sa  bata  gani, tsawa ya kuma daka ma fatuha wadda tasa yan’hancita katsawa “dan ubanki ni sa’an kine ni eeeeeh? ido fatuha ta qara zarowa, sannan ya nuna ta da yatsa ya ce “Wallahi duk sanda na qara magana wannan dan banzan bakin naki ya maida min sai na fasa shi” ya qara wurga mata harara sannan ya sa hannu zai d’auki jidda, ihu fatuha ta saka hakan yasa sadiq  juyowa yana mata kallon  wulaqanci, “Qur’an ba inda zaka da balarabiyan nan kwarankwatsi, ko na fada ma hajiya tunda ita ta bani ita” dariya abin ya kusa ba ma sadiq amma sai ya d’aure ya wurga mata harara, a rayuwarsa  bai  ta6a ganin mara  kunya  irinta  ba  yar  kauye wadda  bata  jin  ko  tsoron sa.

    Mom dake bedroom taji ihu fatuha hakan yasa ta fito da sauri, ganin sadiq d’auke da jidda fatu  na gefe tana ihu yasa mom qarasowa, harara ta aikawa  sadiq tare da cewa, “Lafiya fatuha? me kuma ya miki?” turo baki tayi ta ce, “Yanzu saboda Allah hajiya ba ke kika bani wannan balarabiyar ba, na kulla da ita, to shine wai daga yaga ina bata abinci ya hau zagina har da ce min wai fida take sha” hajiya ko dariya abin  ya bata saboda ta gano abinda fatuha take nufi, sannan fatuha ta ce, “To shine hajiya yasa hannu zai d’auke min ita Qur’an ban yadda ya maido min abuta” murmusawa hajiya tayi  tana  konshe dariyarta ta ce “Yi hakuri fatuha ai baban ta ne shiyasa”
“aiyo toh shine hajiya bai iya fada min dan girman Allah, ki ce ya ban  yarinyar dan Qur’an sonta nake” tare da matse kwalla, Mom ko dariya abin ke bata sadiq ko mamaki abin ke ba shi yau shida d’iyar sa za’a masa qarfin hali, Mom  ta  ce, “Toh shikenan sadiq bani jidda idan ta mata wanka sai ta kawo ma ita, ai shikenan anraba rigama ko fatuha? sadiq 6ata fuska yayi ji yake kamar ya shaqe fatuha dan haushi.
Haka sadiq ya miqa wa Mom jidda tare da haurawa sama, sannan ya d’au alwashin sai ya gyarawa wannan yarinyar zama dan yaga alamar da rashin kunya tazo.

       Fatuha ko washe da baki ta amshi jidda, jidda ko sai raba ido take gashi cikin ta ya cika dam kamar yayi magana……

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★

https//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial&_yn_=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook. com/REAL HAUSAFULANIWRITRESFORUM.com

*rip rip this page is for you my lovely one so enjoy the page this na for u no be so*😉

                        31_32

Washe da baki fatuha ta amshi jidda ta wuce da ita bedroom ta cire mata kaya, direct toilet ta shige da ita sai da ta wanke jidda tas sannan suka fito.
Wash Fatu ta  ce,  tare  da  cewa, “Ah bilahilazi birni tayi yanzu dubi sau biyu ina sab’e ki, ko  gajiya  bakiyi  da  wanka  kamar  kwad’o” jidda ce ta washe baki ta ce “Anuty daddy baya son dati shiyasa, always yake min wanka yayi ma kansa”
“uhm..! ta6e baki fatu tayi ta ce, “yo ke ki kasan wannan,” washe baki jidda ta kuma yi ta ce, “baba na fa nake nufi Anuty”
“aiyo wai wannan baban naki ai dole yake wanka daga ganin shi ya cika tsirfa”
“daddy nawa”
“uhm shi  fa, ke ni wani mai ake shafa maki idan anmaki wanka” smile jidda tayi ta d’auko mata lotion d’in ta mai kamshi fatuha ta amsa tana  jujuyawa ta  ce, “ah’ah wanga farin mai haka fa? yo ai wannan kamar turare ne” jidda ce ta fashe da dariya ta ce, “Anuty ba turare bane maine ga turare na chan saman dirss mirror wanda daddy ya siyo min a uk,”
“tir qashi me kuma uk? washe da baki jidda ta ce, “wata qasa ce haka”
“a’a ha shi baban naki har shawagi yake qasa-qasa ta6 kinga matso  na shafe ki da mannan kar yaji shiru ya zo ya min tijara dan na lura dan ta kife ne baban naki” haka ko ta shafe jikin jidda da lotion tare da anyana man a ranta ita ma ta gama shafa basilin dan ita yanzu ta zama yar birni.

        Sai da ta gama shafe jidda da mai tsaf sannan jidda ta gwada mata inda night dress din ta suke kar ku ga abu komai fatuha ta gani sai ta mai sharhi, bayan ta gama shirya ta tsaf, sannan  ta d’auke ta dan kai ta d’akin baban nata wanda tayi ma laqabi da sangami.

     Direct part din Sadiq suka wuce a hankali ta murd’a handle d’in kofar  ta shiga, jidda  tana ta  zuba mata surutu, tana shiga parlour ta saki baki da hanci bata san sanda ta dire jidda ba a qasa wani irin sanyi dad’i ne da kamshi ya doki hanci ta kasancewa sadiq mutun ne mai san sanyi da kamshi, shiyasa part d’in shi yafi na kowa sanyi a gidan, washe baki tayi tana qarewa parlour kallo saboda iya kar had’uwa parlour ya hadu.

    Jidda ko bedroom ta shige da gudu lokaci sadiq ya fito daga wanka, sanye yake da bathrobe hannu shi riqe da towel, yana goge gashin kan shi jidda ta ruga ta rungume sa  ciki  da  farin  ciki  ta  ce, “daddy..! wani irin murmushi ya saki tare da shagwabe fuska ya ce, “uhm ni fushi nake da angel” tare da d’aukar ta ya zaunar da ita saman bed ya cigaba  da  cewa, “shine saboda kinyi new Anuty kika manta daddy ko angel? shagwabe fuska ita ma tayi tare da d’aura hannu ta saman cheeks d’in sadiq ta ce, “sorry daddy” ta marairaice kamar za tayi kuka, dariya yayi tare da fara yi mata cakulkuli, dariyar su  jidda  ta ankarar da fatuha washe da baki ta nufi kofar bedroom ta bud’e a hankali ta shige, zaro ido tayi  waje tana kallan d’akin baki bud’e tana  cewa, “kai Amma wanga gida ya had’u kwarankwatsi yanzu gobe ni zan gyara wanga gurin,” baki ta qara washe wa duk wannan maganar tana yin tane cikin zuciyarta, sadiq dake ma jidda cakulkuli tana dariya jin kamar an bud’e daki  an shigo yasasa da gowa a hankali,   ya sauke sexy eye’s ball’s din shi kan fatuha wani irin kallo ya wurga mata ita dinma shi take kallo tana aiyana irin kyau na sadiq a zuciyarta “ta6 amma dai sangami ba qaramin kyakyawa bane Qur’an” washe baki ta kuma yi  ta ce “Amma fa sai bakin rai kamar fir’auna tir da wannan hali wallahi ga kyau ga bakar zuciya, ko da yake na kusa maganin shi ai,” daka mata tsawar da sadiq yayi ne yasa ta dawowa daga dogon tunanin da take tayi wiqi-wiqi da ido, “you are very stupid ina maki magana kin yi shiru ehhh ? are u deaf or what” tsawar da sadiq ya daka wa fatuha har wani fitsari taji ya taho mata gadan-gadan ganin yana nufo ta yasa ta bud’e kofar tafita daga d’akin da gudu sai da taje dai-dai kofar parlour ta bud’e baki yadda zai jita ta ce, “Allah ya isa mugu kawai” sannan ta bud’e kofar ta ida fita a guje sadiq dake bakin kofar bedroom yana jin ta lumshe ido yayi yana jin wani irin tsanar fatuha na ratsashi da mamakin rashin kunyar ta ,a hankali ya ja jikinsa ya koma saman bed lokacin jidda har tayi bacci shima kwantawa yayi tare da kara masu gudun AC  ya ja masu blanket.

        Tana isa d’aki ta kulle da makuli gudun kar sangami ya shigo wato sadiq, toilet ta shige da gudu tayi fitsarin data matse saboda tsabar tsawar da sadiq ya daka mata shi ya haifar mata da fitsarin dole, tsoki ta ja tare da cire kayan jikin ta tayi wanka sai da ta wanke jikin ta tas sannan ta  d’auki k’aramin  towel ta daura ta fito, rigar baccin da Mom ta gwada mata ta ciro ta sa duguwar riga ce pink mai manyan follows milk rigar ta wuce gwiwa ba qaramin kyau tayi ma fatuha ba, ita kanta sai da ta yaba kyan rigar sannan ta kwanta saman bed tare da janyo blanket ta lullu6e ko 2 minutes ba tayi ba bacci ya sureta.

           ASUBA TA GARI

tsaye yake gaban dress mirror yana shiri cikin uniform nashi kasancewa yau Monday ba qaramin kyau yayi ba, kofar bedroom ya kalla tare da jan tsaki sannan ya kalli bed jidda na bacci.

      Bangaran  Fatuha ko yau bacci har da munshari ba ita ta tashi ba sai 6:00am, cikin sauri ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan tayi wanka ko mai bata tsaya shafawa ba  tayi sauri ta zura uniform din ta, kasancewa Mom ta fada mata jidda na zuwa school shiyasa take shirin cikin sauri cikin sauri ta nufi part d’in sadiq dai-dai bakin kofa tayi tsaye gaban ta na dukan uku-uku saboda ta tuna artabun da suka sha da sangami jiya kawai shahada tayi tare da qundun bala ta bud’e kofar ta shiga tare da yin sallama,  ba kowa parlour hakan yasa ta murd’a handle d’in kofar bedroom sadiq ta hango tsaye gaban dress mirror a hankali  ya dago sexy eye’s ball’s din shi wani irin kallo ya wurga mata tare da jan tsoki, cikin  tsawa ya ce “Yanzu ne time din da ya kamata ki shigo eeh?  baki san tana zuwa school bane, koko rashin sanin muhinmanci ilimi yasa kika zauna baki zo ba eeh? nuna ta yayi da yatsa  ya ce, “as from to day karki qara kai wannan time din baki zo ba stupid girl kawai” duk da bata san Kalmar da ya fadi aqarshe ba amma jikin ta ya bata zagin ta yayi sai da ta fakaici idon sa sannan ta bala masa harara tare da d’aukar jidda daga saman bed zata fita da ita har ta kai bakin qofa, ya kara daka mata tsawa ya ce “Kin makarar da ita yanzu Kuma ina zaki kaita? oya wuce ki mata wanka a bathroom d’ina” wiqi-wiqi da ido fatuha tayi dan ita bata san me ye bathroom ba, wata uwar tsawa ya kuma daka mata y’all ce, “oh waike wace irin yarinya ce ehh ki kai ta ban d’aki na kiyi mata wankan yar qauye kawai mtss, saura kuma inkin je kinmin kauyan ci” jiki ba kwari fatuha ta shiga toilet din ba laifi dan kauyanci da tayi kadan ne sannan tayi ma jidda wankan, tana mata tana zuba mata surutu d’auke da ita ta fito sannan ta zauna da ita saman bed sadiq na zaune saman sofa yana kallonsu  shafe jikin jidda tayi da mai sannan ta dau uniform din jidda zata sa mata nan fa kar ku ga zare ido dan ta rasa ta inda zata samata rigar saboda gown ce irin mai kamar biri da wando d’inan tayi tsuru-tsuru, sadiq jan tsaki yayi tare da fisge rigar ya shiga sama jidda fatuha duk tana kallon yadda ya ke samata sai da ya gama shirya jidda sannan ya mata peck ta  ce, “daddy good morning”
“morning too angel how was ur night,?
“cool daddy”
“good” fatuha ko sakin baki  tayi tana kallon su.

    Sai da suka gama shiryawa tsaf sannan sadiq ya d’au briefcase din sa, fatuha kuma ta d’auki jidda suka sauko downstairs Mom da Abba na zaune a dining area har sun fara breakfast cikin ladabi sadiq ya gaishe su haka ma fatuha da jidda Mom ce ta kalli fatuha washe da baki ta ce “Ya kwanan baqunta?” murmushi fatuha tayi tare da jama jidda kujera ta zauna cikin natsuwa ta shiga saving din jidda abinci,  da ta gama sai ta zauna shima cikin dari-dari  sannan ta sa hannu cikin plate d’in wata irin tsawa sadiq ya daka mata wadda tasa fatuha fara matsar kwalla, cikin kakausar murya yafara cewa “Wai bana ce maki ki daina feeding din angel da hannu ki bane eeh” Mom ce ta kalle shi tare da wurgamasa harara take ce, “baby wai me yasa ka ke haka ne eeh” fada ta masa sosai sannan shima Abba ya dasa da cewa,  “Kai haka ake a rayuwa? kai kullun cikin zafin rai sadiq wai me yasa baza gyara halin ka bane eh baby? kullun ciki  rigima  da  masu  aiki” shiru sadiq yayi tare da aikawa fatuha harara ita ko tayi kamar bata gani ba sai ma gwalo da ta aika masa cikin nutsuwa suka gama breakfast.

     Briefcase din sa sadiq ya d’auka fatuha na d’auke da jidda suka fito harabar gidan, haka fatuha ta rinqa zare ido tana qarewa yaran sadiq kallo *ola* ne ya qaraso cikin sauri tare da amsar briefcase din sadiq ya kai masa mota fatuha na biye ta shi suna zuwa gaban mota fatuha ta aje jidda cikin mota , zata juya sadiq ya fisgota ta fado jikinsa, da sauri ya ture ta tare da taka mata qafa da booth din kafar shi ya murzashi sosai, jin za tayi ihu yasa ya matse mata baki da hannun shi da karfi yana kallon ta ido cikin ido ,idanun fatuha sun cika da kwalla taf saboda ita kad’ai tasan azabar da take ji, ture ta yayi tare da nunata da yatsa ya shige motarsa har zai tada yajiyo muryarta tana magana da yake ahankali take magana shiyasa baiji abinda take fadi ba, kwafa yayi ya tada motar suka bar harabar gidan, fatuha ko Allah ya isa ta shiga jeramasa tana  kuka tare da shigewa  gida a guje.
Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★

http//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_yn_=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook. com/REAL HAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

      *👏🏼Godiya ta musanman ga masoya na ❤ina jin dadi addu’ar ku ta fatan alheri😍 nima ina son ku ana mugun tare*🤝🏽

*Wannan shafin nakune masoya na asha karatu lafiya*❤

                        33_34

       Parlour ta qaraso tare da share yar qwallar da ya taru a idonta, Mom na zaune saman three star tana kallo juyowa tayi cikin murmushi tare da kallan fatuha, ita ma fatuha murmushi tayi tare da fara kwashe kayan abinci da ke dining area Mom  ta  ce, “ah fatuha da kin bari rabi’a ta zo ta kwashe” washe baki tayi tare da cewa, “barshi kawai hajiya” Mom murmusawa tayi tare da cewa “Ni ko fatuha da kin daina ce min hajiya nan da yafi! Ki rinqa kira na da sunan da sadiq ke kira na” murmushi fatuha tayi tare da cewa, “toh.! sannan ta kwashe kayan ta kai kitchen Mom kuma ta cigaba da kallon ta tana ayana wasu abubuwa a ranta, tana fituwa direct part d’in sadiq ta wuce ta gyara part d’in sosai,  tana gamawa ta shiga toilet shima toilet d’in sai daya sha wanki dan fatuha gyara tayi bana wasa ba, tana gamawa ta washe baki tare da zama saman sofa tana qarewa d’akin kallo hotan sadiq ta hango manne jikin bango tangameme shi da kausar sunyi murmushi.

     A hankali ta qaraso wajan hotan tare da washe baki tana kallon hotan ta  ce, “ohni ashe sangami na murmushi, ah ji yadda ya washe hakora dan Allah ai da haka yake kullun daya fi kyan gani” murmushi tayi tare da d’aura hannuta saman pic din ta ce, “uhm gaskaya kana da kyau Qur’an” chan kuma sai ta bata fuska tare da cije lips dinta dariya tayi sannan ta ce, “Kwarankwatsi zaka zo ka same ni wallahi ba kasan *wacece fatuha ba yar gidan Baffa jauro*” sannan ta bala wa pic din harara  ta fita daga part din.

   Tana sakowa downstairs ta shige bedroom dita wanka ta kumayi, tana fitowa ta shafe jikin ta da lotion tana shafa lotion din tana washe baki tana  surutu da  cewa, “Qur’an wanga mai sanyi garai ga kamshi, wallahi birni tayi” sai da ta gama shafe jikin da mai tas  sannan ta sa wasu uniform din.

**
Cikin school yayi parking tare da fituwa ya budewa jidda murfin mota smile ya mata me sanyi, sannan ya ciro mata lunch box  dita ya miqa mata, 6ata fuska jidda tayi tare da cewa “Daddy am going to miss u daddy” saman kanta ya  shafa  tare da cewa “Sorry angel soon za’a tashi aiko? sai inna dawo gida sai muje shan ice cream ko my angel” washe baki tayi tare da yi mashi peck sannan ta shige class yana kallonta har ta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya ya shige mota yatafi.

       Bayan ta gama shirin ta tafito parlour ba kowa sai kamshi da ke tashi na girki, kitchen din ta nufa tare da sallama baba junmai ke girki sai rabi’a na gyara salat murmushi tayi tare da gaishe su washe da baki baba jummai ta amsa tare da cewa “Yar albarka kin zo taya ni aiki ne?” daga kai tayi alamar  Eh, can kuma fatuha ta bata fuska tare da cewa, “baba wai ina kike kwana jiya kika barni ni kad’ai,” washe baki baba jummai tayi tare da cewa, “aini fatuha banan nake kwana ba a gida na nake kwana sai da safe na zo” turo baki fatuha tayi ta ce, “gaskiya baba yau binki zanyi,”
“ah ba za’ayi haka ba ki zauna nan nima ai gidan bacci ke kai ni” baba jummai ta shiga lalla6a fatuha.

    Taya su aiki tashiga yi sosai can baba jummai  ta miqawa fatuha kwano ta d’ebo  man da za’a soya kaji a store, wani irin murmushi tayi tare da shiga store d’in nan ta zuba a kwano tare da qule wani a leda tasa a aljihun skrit d’in ta ta fito, sannan tayi ma baba jummai sallama ta koma parlour  ta cigaba da kallo tanayi tana washe  baki, Mom ce  ke saukowa daga stairs sanye da mayafi da car key a hannu ta kallon gefan da fatuha take tayi tare da cewa “Oh na manta, nayi da ke jiya zan kai ki gyaran kai wallahi na manta gashi yanzu fita zanyi” murmushi fatuha tayi ta ce, “ba komai gobe maje,”
“toh shikenan idan na  manta ki tuna min please” toh ta ce mata tare da rakota har bakin kofa sannan ta koma parlour ta cigaba da kallo.

Tana kallo har bacci ya kwashe ta a parlour, cikin bacci taji ana sallama tashi tayi tare da ware  idanuwan ta ta sauke su kan  Anuty bilki, ware ido ta kuma yi tana qarewa Anuty bilki kallo dan tabbas tayi mata kama da sadiq sai dai sadiq ya fita kyau sosai qaqaro murmushi tayi bakin ta na rawa ta gaida Anuty bilki, zama tayi tare da amsawa tayi ma fatuha murmushi fatuha  ta  ce, “uhm hajiyar ba ta nan ta fita? murmushi Anuty bilki tayi ta ce, “ai na sani munyi waya yanzu zata dawo ba dad’ewa zatayi ba” fatuha kitchen ta shige ta fada ma baba jummai anyi baquwa lemo ta zuba mata a tray da kayan motsa baki tare da ce mata gata nan zuwa taga baquwar, Anuty bilki ko kayan jikin ta ta rage tare da haurawa upstairs dan ta watsa ruwan , fatuha na zuwa parlour taga ba baquwa sai Afra da ke bacci saman kujera baba jummai ta qwalawa kira ta fitu a rud’e ita ma Anuty bilki da shigar ta bedroom kenan ta sauko, turus baba jummai tayi a parlour tana  cewa, “lafiya fatuha me ya faru” bakin  fatu  na  rawa  ta  ce, “baba wallahi baquwar ce ban gani ba gashi ta bar yar ta a nan” Anuty bilki ce ta qaraso, da  murmushi  a fuskarta baba  jummai ta  ce,  “ah wai Bilkisu ki  ka  gani kike  nufin baquwa ai yar gidan ce amma tayi aure ganin gida tazo yi” murmushi fatuha tayi ta ce, “Aiyo aini ban sani ba shiyasa” itama Anuty bilki dariya tayi sannan ta haura sama tare da ba  fatuha afra ta kula da ita kafin ta fito.

        Misalin karfe 12:00pm jidda ta dawo school ita da Jamal, kasancewar school d’aya suke da yan’yan Anuty bilki cikin murna fatuha ta tare su , kasancewar fatuha me son yara ce, ta ja jidda da Jamal bathroom ta masu wanka suka fita tas, sannan ta sa masu kaya ta zo da su dining area suka ci abinci sannan ta dawo parlour da su suna dan ta6a hira sama-sama duk  cewa  kusan  rabin  hira  duk  shirme  yafi  yawa, can sai ga Hanan ita ma ta dawo daga school washe da baki ta qaraso ta fad’a jikin Anuty bilki take ce, “wash Mom am tied”
“sorry sweet je kiyi wanka ki canza kaya” fatuha ko washe baki tayi tana qarewa su Hanan kallo, tsakanin Hanan da fatuha kunsan sa’anin ne shiyasa tunda ta shigo fatuha ke kallon ta hakan sai yasa ta tuna da fatsima kwalla taji ta zo mata gaskiya ta san tayi kewar su inna da fatsima d’aki  ta shige tayi kwanciyarta Hanan ce ta shigo ta shige toilet tayi wanka sannan ta fito d’aure da towel suna hada ido da fatuha tayi murmushi take ce, “sannu ki”
“yauwa” fatuha tace mata, nan Hanan ta fara janta da hira sama-sama, Hanan dama kawa take  so  gashi ta samu aiko nan hira ta barke tsakanin su idan fatuha ta fadi wani abu Hanan tayi dariya sosai har cikin ta ya kule.

    Sai yamma likis su Hanan suka tafi, har bakin mota fatuha ta rako su ita da jidda, kamar kar su tafi saboda fatuha taji dadi hirarsu da Hanan.

     Bayan sun tafi suka koma bedroom din  jidda, taci gaba da zubama fatuha surutu can kamar  an mintsili fatu ta tashi ta koma parlour kad’an-kad’an  ta leqa waje.

     Motar sadiq ce ta kunno kai cikin gidan, wani irin murmushi fatuha tayi tare da yin sauri da haurawa, upstairs part d’in sadiq ta shige direct toilet din shi ta shiga ta fido da man da ta kule a leda ta juye shi qasan toilet d’in sannan ta fito tana dariya tana waigen part din ji tayi ta fada jikin mutun, idanunta ta zaro cikin tsoro da fargaba, tayi  lamo tana jiran aradu, wata irin tsawa sadiq ya daka mata tare da ture ta, ta tafi tagalgal zata fadi ya fisgota tare da qanqance idanu yana kallonta, fatuha kuwa har ta fara matsar kwalla, cikin kakausar murya ya ce “Ke wace irin mahaukaciya ce? ya karasa zancan da murya mai sauti wanda yasa fatuha sakin kuka saboda a iya rayuwar ta ba wanda ya ta6a mata irin wannan ihu haka  ko  tsawa, kuka take sosai tana girgiza mai kai janta ya cigaba dayi har sai da ya kai ta last stairs sannan ya ban kada ta ta fadi qasa tayi zaman yan bori nunata yayi da yatsa tare da cije lips din shi ya d’au briefcase din shi ya shige part nashi fatuha ko kuka tayi san ranta dakyar ta tashi saboda qugun ta ya riqe bedroom ta shiga tare  da shiga toilet dan watsa ruwa ta  gasa  jikin  ta  dan  ba  karamar  buguwa  tayi  ba, bata jima ba sosai ta fito d’aure da towel ta shirya cikin riga da skt  na  uniform nata sosai tayi kyau masha Allah ta fito parlour can kuma sai tayi murmushi ta haura sama cikin  sand’an.

     Sadiq na Shiga daki saman bed ya fada tare da lumshe ido, yana maida numfashi a hankali wata irin tsanar fatuha na ratsashi ware sexy eye’s dinshi yayi tare da tashi tsaye, ya je gaban fridge ya bude ya curo fresh  milk ya sha sannan ya fara jin zuciyar shi ta daina kuna, ya tashi ya cire uniform dinshi yashiga toilet….

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★

http//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red opare-speed_dial_yn_=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com

                           35_36

    A hankali ya murda handle d’in kofar toilet ya zura kafar shi ji kake suuuu gwajaf yayi fad’uwar yan bori, fatuha da ke maqale bakin kofa ta kasa kunne jin fad’uwar sadiq ya sata bushewa da dariya har da rawar tanbola dan shauqi, bud’e kofar tayi ta shigo bedroom tana shigowa ta qara fashewa da dariya, saboda zaman da sadiq yayi a qasan toilet qarasowa tayi bakin kofar toilet din, a hankali sadiq ya dago sexy eye’s ball’s din shi ya sauke su kan fatuha wani irin kallo ya wurga mata dariya ta kuma saki tare da bala masa harara ta  ce, “ah mai kyau ansha qasa..! dariya ta kumayi tare da gyara tsayuwa ta  ce, “toh mai kyau bari na kirama hajiya ta kirama mai d’auri saboda nasan ka goce koka kare  dan  ba  karamar  faduwa  nasan  kayi  ba” ta qara bushewa da dariya, sadiq ko cije lips yayi yana jin wani irin rad’ad’i da tsanar fatuha na ratsa sa, kenan  ita  tasaka  masa  mai  a  toilet  dan  ya  fad’i kallon banza ya wurga mata yana qoqarin tashi amma ya kasa wani irin rad’ad’i qugunsa ke masa dan  ba  karamar  fad’uwa  yayi  ba  sosai  yake  jin  rad’ad’i a kugunsa, cije lips yayi ya zauna dan baya iya tashi dariya fatu take saki  ganin  yarda  yake  cije  le66e yana  rinrintse ido ta ce, “Kwarankwatsi baka iya tashi Qur’an ka bugu ba kad’an ba qila ma ka kare ko ka goce”, dariya ta kumayi ta nuna idanuwan ta da yatsu biyu sannan ta nuna idon sadiq wanda ke binta da kallon tsana sa’a  kawai  yake  nema  ya  wawuro  ta  ya  cigaba  da  duka saboda  ya  kai  maqura iya  maqura, daure fuska tayi ta ce, “ka tuna turani da kayi d’azu a matatakala na fadi? toh Allah ya isa  ba kasan wacece fatuha ba ko? kaje kauyan wudil ka tanbayi *wacece fatuha diyar Baffa jauro qawar fatsima*, sannan ta qara fashewa da dariya ta ce “Kuma daga yau zan fara nuna ma irin kala haukar fatuha, kuma wallahi kasani fatuha ba’a mata abu ta hakura ko ta dangana, d’azuma a lokaci ba hakuri nayi ba shi yasa na rama,” ta bala masa harara tana qoqarin fita, sadiq ko wani miyan bakin ciki ya hadiye yana jin wani irin bakin ciki ,ji yake kamar ya tashi ya shaqe fatuha har sai numfashin ta ya kusa daukewa ya sake ta lumshe idanuwansa yayi zuciyarsa  na  masa suya  da  tafarfasa  tamkar  garwashi, yana  matukar  mamakin  yarda bagidajiyar yarinyar bata  shakar sa tunda Mom  ke  kawo  masu  aiki  bai  ta6a cin  karo  da  mai  aiki  irinta ba, alwashi ya  d’aukarwa kansa  sai  ya  gyarawa yarinyar  zama  ko  yana korata.

         Washe da baki fatuha ta fito daga part d’in sadiq  jin  zuciyarta  take  fes  tamkar  an  zuba  k’ank’ara sai da ta daidaita kanta sannan ta fara matsar kwallar gulma, bedroom d’in Mom ta nufa tana yarfe hannu  a hankali ta bud’e k’ofar d’akin Mom ta hango kwance saman bed tana karanta azkar, cikin nutsuwa ta shigo tana matsar kwalla Mom ce ta d’ago su kayi 4eye’s da fatuha murmushi ta saki tana qoqarin tashi  zaune ta ce, “fatuha qaraso mana” jikin kofa ta qara maqalewa tana matsar kwallar gulma dakyar ta iya furta, “Mom dama baban jidda ne ya ce na kawo masa ruwa ina shiga dakin na ganshi ya fadi a kewaye kuma ya kasa tashi” tana ida zancan ta fashe da kukan munafurci Mom tashi tsaye tayi cikin tashin  hankali a rud’a ta  ce, “muje bedroom d’in nashi naga ko lafiyar baby” Mom na gaba fatuha na baya tana aika gwalo suka shige part din direct bedroom d’in sadiq ta shige yanan zaune inda fatuha ta barshi yayi-yayi ya tashi amma ya kasa Mom ce ta qaraso tare da kiran sunan shi cikin damuwa ya juyo yana kallonta fatuha na bayan Mom tana matsar kwalla da sun hada ido da sadiq ta aika masa gwallo shikuma ya aika mata harara Mom  ta  ce,  “sannu baby kaji bari mu taimaka ma ka tashi,”
“no Mom ba ku iyawa a miqomin phone d’ina tana saman stool na kira *ola* da *Sunday*” cikin sauri Mom ta miqa masa wayar fatuha na gefe ra6e zuciyar ta fes.

    Bugu daya biyu *ola* ya daga kiran sadiq, sadiq ya sheda mashi yana neman su, shi da *Sunday* cikin sauri suka qaraso  bedroom din, ganin su Mom tsaitsaye yasa jikin su *ola* yin sanyi hango sadiq su kayi zaune a toilet yayi zaman yan’bori a hankali *ola* ya qaraso tare da gaida Mom cikin hausar su wadda bata fita amsa masu tayi sadiq a hankali ya ce, “*ola* taimaka min na tashi kai da *sunday*”
“OK boss” Sunday da ola suka taimaka ma sadiq ya miqe suka d’aurashi saman bed  Mom sai sannu take masa itama fatuha sannu ta masa wani irin mugun kallo ya mata, ya kauda kai Mom ce ta ce, “baka ji fatuha na ma sannu bane” lumshe ido yayi tare da ware su ya ce, “ban ji ba.! ya qara maida idanuwan shi ya rufe, wayar shi Mom ta curo ta kira doctor yakub ba ayi  minti 39ba sai ga doctor yakub riqe da briefcase din shi ya shigo, fatuha ta masa isowa har bedroom din sadiq gaida Mom yayi sannan ya shiga duba sadiq tare da tataba inda ya bige sannan yayi yan rubuce-rubuce, gyaran murya yayi ya ce, “Alhamdulillah  buguwa ce amma bai goce ba kuma bai kare ba, abin ya zo da sauki”  murmushi Mom tayi tare da hamdala, sannan doctor ya bashi magani da ze shafa da kuma na ciwon jiki  sannan yayi ma su mom sallama ya tafi, Mom da fatuha kuma suka fita.
cikin cool voice nashi sadiq yace da ola ya taimaka ya kai shi bathroom ya watsa ruwa amma ya fara goge man da ke zube a toilet sai da ola ya wanke toilet din tas sannan ya taimakawa sadiq ya shiga toilet,  ola na bakin kofa yana jiran sadiq yana gama wanka ya kira ola ya taimakamasa ya fito ko da ya fito ola ya fito masa da jalabiya milk bayan ya gama shafe jikin shi da mai sannan ola ya taimakamasa ya shafa masa magani sannan yasa jalabiya ya koma saman bed ya lumshe ido ,ola ne ya 6alo magani da ruwa ya bashi ya sha yana gama sha ya lumshe ido bacci mai nauyi ya d’auke sa, ola ya koma saman sofa ya zauna Sunday kuma ya kwashe kayan da suka baci da mai  ya fita.

  Fadawa  gado  fatu  tayi  ta  ce, “Wash Qur’an yau nayi aiki inama a ce fatsima na kusa” ta qara bushewa da dariya, ta kalli bed jidda na kwance tana sharar bacci dariya tayi ta ce “Allah sarki angal wato(angel) yau na naqasa baban ki sai hakuri angal na san in zafi yayi zafi har sunnan ki sai ya fada” ta kara fashewa da dariya tare da rausayar da kai to ce, “Amma fa gaskiya ban duba masa ba” ta ida zancan tana cire kayanta ta shige toilet tayi wanka d’aure da towel ta fito lokacin jidda tatashi, murmushi tayi ma jidda tare da d’aukarta dan lokaci 4:00pm saura malamin jidda ya kusa zuwa wanka ta mata a tare suka fito suka shirya sallah su kayi saboda anata kiraye-kirayan sallah bayan sun gama sallah fatuha ta rako jidda har waje lokaci har malam ya zo ji tayi itama tana sha’awar karatun, cikin gida ta juya tare da shiga bedroom din Mom, Mom na zaune saman daduma karasowa tayi tare da murmushi ta tanbayi Mom itama tana so  ta fara zuwa malam na qara mata karatu Mom ta ce, babu komai ita  ma  ta  je washe da baki ta fita, taje wajan malam itama ba laifi fatuha ta d’an san sururi da yawa sai dai karatun nata ba tajweed shine kad’ai ya d’an bata karatun ba laifi sunyi karatu sosai inda fatuha ta nutsu tana ta karatu, dan wannan malamin ba karamin malami  bane.

     Bayan sun gama karatu misalin karfe 6:00pm suka shigo gida cikin farinciki, Mom na zaune saman three star tana kallo abba na gafenta gaishe su tayi cikin nutsuwa sannan ta shige daki jidda kuma ta fada jikin Abba tana zuba masa surutu kiran sallar magrib ne ya sa Abba tashi ya wuce masallaci, jidda kuma ta shige bedroom lokacin fatuha ta fito daga toilet daure da alwala, murmushi fatuha tayi ta ce, “Jidda yi maza kiyi alwala kiyi sallah kiyi ma baban ki addu’a, bai da lafiya kinji”  waro ido  jidda  tayi ta ce, “Anuty me ya samu daddy” take Ida  zancan tare da rugawa wajan kofa zata fita, jawo ta fatuha tayi ta ce, “yi hakuri mu fara yin sallah sai na kai ki kinji jidda” toh tace mata tana matsar kwalla fatuha kuma na lallashin ta.

    Bayan sun gama sallah fatuha ta shirya jidda cikin night dress din ta blue n white wando da riga ba qaramin kyau su kayi mata ba, ta ja hannu ta suka wuce part din sadiq.

       Suna Shiga suka samu ola zaune saman sofa, sadiq ma zaune saman bed, yana shan coffee da gudu jidda ta fada jikinsa tana kuka ta  ce, “daddy..! lallashin ta ya shigayi yana  cewa, “angel menene yake damun ki? bata fuska tayi ta ce “Daddy ashe baka da lafiya shine baka fada min ba? ta ida zancan tana matsar kwalla sadiq y’all ce, “sorry angel lafiyar daddy qalau, waya fada maki daddy bai da lafiya? fatuha ta nuna da ke manne jiki kofa kamar ka ce tak ta arce wani irin kallon tsana ya gefa mata tare da qaqaro murmushi yayi wa jidda yana kallonn fatuha ya  had’e  rai  tamkar yayi  bindiga ya  ce, “angel na rasa yadda akayi grandma ta samomaki new Anuty mahaukaciya” ya ida zancan yana kallon fatuha ido cikin ido, kauda kai tayi tare da turo baki gaba angel tattoo ce, “daddy new Anuty ba mahaukaciya bace ba”
“injiwa ya ce maki ba mahaukaciya ba ce” fatuha ko wani irin tsoki ta ja tare da jan kofar bedroom da karfi ta fita lumshe ido sadiq yayi yana tunanin irin hukuncin da zaiyi ma fatuha in ya tashi…

written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★

http//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167refid-52&red opare-speed_dial_yn_=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail. com

*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com

                37_38

Fatuha bedroom ta shigo tare da yin sallah isha’i saboda tana da alwalata, bayan ta gama sallah ta rage kayan jikin ta yar rigar bacci tasa wadda yanzu ta zamar mata jiki, idan batasa ba ko bacci bata iyawa kanta ta qarewa kallo ta cikin mirror ita kanta mamaki kanta take saboda ta wani qara haske, da kyau sannan komai na jikin ta ya ciciko rufe idanuwanta tayi tare da ware su, ta sauke su kan qirjinta wanda yanzu ya fara cikowa sosai, murmushi tayi tare da jin kunya ta bar gaban dress mirror din ta fada gado tare da yin addu’a lumshe idanuwanta tayi sadiq ne ya fadu mata a rai tayi sauri ware idanuwan ta tare da sakin dariya, saboda duk lokacin da ta tuna da zaman yan borin da sadiq yayi sai ta dara a haka har bacci ya kwashe ta.

         Duk juyi dayayi sai ya zabga tsaki saboda bacin rai ola ne ya juyo ya ce, “boss are u ok? lumshe ido yayi ya ce, “Yes.!
“ok good night boss if u need something talk to me please,” ok  tare da juyawa ya gyara kwanciyar  shi a hankali ya shafa gashin jidda sannan ya lumshe ido, daya lumshe ido fatuha yake gani tana masa dariyar qeta wata irin iska ya furzar mai zafi daga bakin shi ba abinda zai hana shi yima fatuha horo mai tsanani, wanda ko wani aka ce tayima irin cin kashin da ta masa ba zatayi marmarin maimaitawa ba, tsaki ya kuma ja saboda takaici a haka har baccin barawo ya d’auke shi.

*Asuba ta gari..*

    Tunda asuba fatuha ta tashi saboda tasan in yau bata tashi da wuri ba Allah kad’ai ya san jarabar da sadiq zai mata, d’an tsaki ta ja can kuma tayi murmushi ta ce, “ko ba komai  ina ganin mai kyau Qur’an naji dadi..! sannan ta shige toilet tayi wanka tare da yin brush da dauro alwala tayi sallah sannan tasa uniform komawa tayi ta zauna saman bed tana kallon agogo karfe shida take so ta shiga part din sadiq.

         Ba laifi daya tashi sallah asuba kafar ta saki tunda har ya taka bada taimakon ola ba, toilet ya shiga yana shiga abinda ya faru jiya ya fara dawo masa kamar yanzu, murmushi yayi ya ce, “fatuha baki ji” sannan ya qara jan tsoki yana  mamaki  yarda  ya  rike  sunan  ta ya dauro alwala  tare da yin wanka ya fito ko da ya fito jalabiya white yasa ya tada sallah yana gamawa ya koma ya kwanta saboda har yanzu jikin nashi yana jin shi wani irin.

    Bud’e handle din kofa tayi ta fito direct part d’in sadiq ta wuce kai tsaye, bedroom ta shige kallo daya tayi ma d’aki ta  hango ola  kwance yana ta share bacci har da munshari saboda dad’i,  dariya  ta so ta kubuce mata ta guntse dariyar kallon bed tayi sadiq na kwance rungume da jidda murmushi tayi a hankali ta qarasa tare da leka fuskar sadiq ta ga dai bacci yake cikin dubara ta shiga janye jidda daga jikin sa, hannu ta ya kama a tunanin shi jidda ce zaro ido waje fatuha tayi tare da fara matsar kwalla a tunanin ta tashi yayi jin baiyi magana bane ya sata lumshe ido a hankali  ta zare hannu ta ta d’au jidda suka fita, direct bathroom ta dire jidda ta fara yi mata wanka , washe da baki jidda ta ce, “Anuty good morning”
“ta6 ke kika san wannan” dariya jidda tayi ta ce, “ina kwana fa nake nufi Anuty”
“aiyo aini ban sani ba, a ina ake koya maki wannan abun wai? washe baki jidda tayi ta ce “A school ”
“aiyo wai makarantar da zaki yanzu? daga mata kai jidda tayi Alamar eh, murmushi fatuha tayi tare da daukar jidda suka fito bedroom ta dire ta saman bed  tare da janyo lotion tana shafa mata tana cewa, “kai Amma gaskiya yarannan nada dadi jidda zaki rinqa koya min ko? murmushi Jidda tayi ta ce, “Anuty kije daddy ya fara koya maki nima ai shi ya fara koya min” ta ida zancan tana washe hakura, fatuha zaro ido tayi ta ce, “ta6 lallai yarinya har yanzu baki san bak’in halin ubanki ba Qur’an..! wannan zancan tana yin shine a zuciyar ta, washe baki fatuha tayi ta ce, “ah ni nafi son ki koyamin kinji kinga daddy aiki yake zuwa ko” daga kai jidda tayi tare da cewa, “toh Anuty zan koya maki” murmushi fatuha tayi  tare da zurawa jidda uniform suka fito dining area lokacin su baba jummai sun gama jera komai bud’e kololin ta fara marfesun kaji ne da soyanyan chips da egg da tea, murmushi fatuha tayi dan tunda ta zo birni ba abinda keyi mata dadi kamar chips shiyasa duk sanda akayi sakin tunbi take  taci sosai  zuba ma jidda tayi a plate tare da jamata kujera ta zauna, zata fara feeding nata kenan sai ga su Mom sun iso, gaishe su tayi cikin ladabi suka amsa plate ta jawo ta fara saving nasu Mom sai murmushi take ita dai fatuha ta mata ko dan abin dariyar ta, tana cikin saving nasu sai ga sadiq ya qaraso dining yana tafiya a hankali yana dingishi, a hankali fatuha ta kalli qafar wata irin dariya ce ta zo mata saboda yadda yake harba kafar kamar tsangal gumtse dariyar tayi ta cigaba da abinda take shiko sai aika mata mugun kallo yake, cikin nutsuwa ya qaraso wajan Mom tare da yi mata peck a goshi ita da Abba, abba murmushi yayi tare da shafa sumar shi ya  ce, “baby ya jiki? shagwabe fuska yayi ya ce, “Abba da sauki”
“good amma dai gaskiya yau baza kaje aiki ba ko? d’an 6ata fuska yayi ya ce, “zani Abba”
“gaskiya baby bazaka office yau ba ka bari zuwa gobe ka warware sosai”
“Abba..!
“shhh..! kawai ka hakura kaji” ya ida zancan yana shafa gefan fuskar sadiq fatuha ko Sakin baki tayi da hanci, ta ce “Ohni sangami duk wani shaqiyanci ya iya, yo in banda iskanci qatoto da shi sai zuba shagwaba yake sai ka ce Jidda, kai kwarankwatsi mai kyau dan bariki ne” duk wannan maganar tana yinta ne a zuciyarta kallon da sadiq ya wurga mata ne yasa ta dawowa hankalin ta ba  shiri Jidda ya jawo jikinsa ya  ce, “yau daddy ne zaiyi feeding angel so bana buqatar ganin ki a nan” tare da warce spoon din hannu fatuha, Mom ce ta bala masa harara 6ata fuska yayi kamar qaramin yaro ya cigaba da feeding din jidda tana masa surutu, fatuha ko qoqari tashi tayi Mom ta ce,”fatuha aike sauki kika samu zauna ki ci abincin ki kan lokaci” murmushi tayi tare da kad’a kai ta zauna ta zuba dai-dai cin ta tasa hannu ta fara ci hankalin ta kwance tana ci tana lumshe ido saboda tana son chips sadiq bala mata harara ya ke tayi wata loma da tayi sai da abin ya kusa bashi dariya da haushi duk suka had’e masa ita ko ko a jikin ta su Mom ma harkarsu suke.

        Bayan angama breakfast har bakin mota sadiq ya raka jidda, fatuha na riqe da lunch box din jidda sai da ta tafi sannan suka juyo zasu koma gida, da gudu fatuha ta wuce sadiq sai da taje bakin kofa sannan ta juyo ta masa gwalo tare da kwaikwayar yarda yake tafiya ta fashe da dariya ta shige da gudu, cije lips din shi yayi tare da tura hannu shi cikin sumar sa ya  ce, “oh Allah ka bani ikon cima yarinyar nan sannan shima ya qarasa parlour ko da ya shigo ba kowa sai baba jummai da ke kwashe kayan breakfast, gaishe ta yayi ta amsa washe da baki, part din shi ya wuce ya murda handle din kofar ya ji rufe mamaki ne ya rufe shi fatuha da ke jingine jikin kofar ta ce, “mai kyau kwarankwatsi ban bud’e ma kofar nan sai na gama aiki na dan nasan halin ka kai mugune wallahi, ka na shigowa zaka bigeni” sadiq da ke wajan kofa yayi sororo yana mamakin raini da fatuha ta masa cige  lips yayi tare da barin gurin saboda ya san idan ya cigaba da tsayawa har kashe ta sai yayi dan bacin rai, fatuha jin ya tafi yasa ta cigaba da aikin ta tanayi tana yan’wake-wakyan ta har ta gama tuni daki yayi kyau sosai sannan tabi part din da turaran wuta tuni part din ya dau kamshi da kyau sannan ta qara gudun AC dakin ita kanta sai da taji kamar tayi bacci dan Kyan da part din ya mata.

     A hankali taje bakin kofa ta murda handle ta leqa taga ba kowa, sannan ta fito da sauri ta wuce sadiq da ke kwance  saman three star idanuwan shi lumshe kamar me bacci yana kallon fatuha ta ruga daki da gudu ta kule, tsoki ya ja tare da tashi duk kiyi ki gaba zan kamaki ne tare da wucewa part nashi dan bacci yake ji ko da ya shiga part din shi da kanshi sai da yayaba kyan da part din yayi, ga kamshi sai tashi yake da sanyi irin yadda yake so lumshe ido yayi ya ja jiki ya hau bed ya kwanta.

       Tana shiga bedroom kayan jikin ta ta rage ta shiga toilet,  tayi wanka sosai dan yanzu ba qaramin jin dadi take ba idan tana wanka  amma da a kauye sai anyi da gaske, yanzu ko fatuha ansan muhinmancin wanka, daure da towel ta fito ta goge jikin ta tare da shafe jikinta da lotion mai kamshi ta feshe jikin ta da turare yar hoda da murza duk ba wata kwalliya tayi ba masha Allah fatuha tayi kyau, uniform din ta ta zura sannan tataro gashin ta wanda ya cure gudaya tana qoqari kamashi amma ta kasa saboda yawan shi da tsaho 6ata fuska tayi tace, “Allah sarki inna da kina kusa da kin gyara min” magana da su kayi da Mom ce ta fado mata daure kan tayi da sauri ta haura upstairs dakin Mom ta shiga ba ta nan neman ta ta shiga yi,  kitchen ta shiga tare da tanbayar su rabi’a ina Mom, ta ce mata tana part din Abba ,toh tace tare da komawa parlour ta samu wuri ta zauna tana kallkn film din India tana washe hakora.

Mom ce zaune da Abba a bedroom din shi tana zaune saman kujera a hankali ya qaraso ya rungume ta ta baya, murmushi tayi ya  ce, “madam kullun qara kyau kike baki tsufa gashi har da jikoki,” dariya tayi ta ce “Ya za’ayi na tsufa bayan mijin nawa kullun yaro yake komawa”  hancinta ya ja cikin tsokana ya ce, “uhm next week zan koma uk kan magana nan gaskiya this time around ban tafiya ni kad’ai, tare nake so mu tafi” murmushi Mom tayi ta ce “Kamar kasan abinda ke raina kenan” smile yayi  ya  ce, “uhm kuma sai gashi na rigaki fada ba,” ya ida zancan tare da yi mata kiss a kumatu ta  ce, “ni ko Abban sadiq kunyi waya da jawad kuwa?  dan murmusawa yayi ya ce, “Eh jiya munyi waya ya ce min yanzu shukura tsohhon ciki gare ta, so yake in ta haihu sai su zo ganin gida” murmushi Mom tayi ta  ce, “Allah ya sauke ta lafiya kamar  kasan nayi missing nashi wallahi ya kamata jawad ya dawo Nigeria da aiki, amma nasan ba lallai bane ya so ba saboda na lura yafi sin London sosai,”
“uhm ke dai ki ce d’anki kike san gani, yauwa gobe ki shirya ina so muje wajan Ammi muyi masu sallama kafun mu tafi” to tace masa tare da tashi zata fita jawo ta yayi jikinsa ya  ce, “please idan kinje karfa ki dad’e ki bar tsohon mijin ki da jira kinji” murmushi tayi tare  da kashe masa ido.. lol ah tsofafi na konewa hehe.

  ( shawara ga mata please mata ya kamata musani tsufa baya hana soyayya karki ce dan kina da manyan ya’ya ki ce ke kin girma ita soyayya bata girma, kuma gyara da tatalin miji shi ke qara dankwan soyayya, so da yawa wasu matan suke jawa maza jansu bin mata saboda kina ganin kin girma komai sai ki daina, idan mijin ki mai so ne daga nan zai fara bin ya’ya cikinsa a waje suna masa yana jin dadi please mata mu kiyaye) .

      Fatuha da ke zaune saman kujera tana kallo, Mom ce ta sauko daga upstairs, cikin ladabi fatuha ta gaishe ta tare da tuna mata maganar gyaran kan, toh shikenan Mom  ta  ce, “je ki shirya mu tafi,”
“Mom bada wannan kayan zani ba?
“eh kisa kayan gida” toh tace mata ta shige bedroom, Mom ko part din Abba ta koma ta tanbaye shi zata fita ya bata izini, sannan ta dawo dakin ta ta shirya cikin atamfa  black mai ratsin red n yellow bubuce mai  kyau tuni Mom ta fito sosai bedroom d’in fatuha ta wuce tsaye, ta same ta ta rasa kayan da zata sa washe da baki momt ta qaraso ta  ce, “fatuha har yanzu baki shirya ba? shagwabe fuska tayi ta ce, “Wallahi Mom na rasa kayan da zansa ne, zabamin dan Allah” to tace mata wata hadadiyar gown Mom ta janyo brown colour mai ratsin milk da Stone’s a jikin rigar mai dogwan hannu ce  sai veil milk, masha Allah fatuha ba qaramin kyau kayan suka mata ba cib suka mata qirjin ko kamar tasa bara saboda yadda kayan suka mata rolling veil din tayi da gashin ta data daure sai abin ya bada kala ta fito fes, takalmi tasa black mai kyau  suka fito,  direct parking space suka wuce Mom ta jasu suka fita sai fatima salon da ke gandu.

   Basu wani dad’e ba a Solon din ba sosai aka gyara gashin fatuha dan ko  mai ba’a sa  mata  ba saboda laushin gashin ta dan idan aka sa masa mai, zai iya konewa gyara shi kawai akayi masha Allah ita kanta fatuha sai da ta tsorata da gashin ta saboda har qugunta ya kai, da yaji gyara amma sai ya rage yawa su kansu yan wajan yaba gashin su kayi  ana gamawa suka dawo gida, a parking space moym tayi parking suka fito har zasu shiga gida sai ga driven jidda ya kunno kai yayi parking da gudu jidda ta qaraso tare da rungume fatuha ta ce “Anuty kinyi kyau,waya maki kwalliya?” dariya fatuha tayi dan ita ba wanda ya mata kwalliya d’aukar jidda tayi suka qaraso parlour sadiq na zaune saman two star yana shan coffee gefensa kuma baba jummai ce suna d’an taba hira da shi da alama tafiya zatayi.

      Cikin sallama suka qaraso, sadiq ya amsa sallamar, fatuha  ke dauke da jidda, jidda ta zame daga jikin ta ta ruga wajan sadiq ta rungume sa wasa ya shiga yi mata tana dariya  qarasowa Mom tayi ta zauna saman three star ta ce “Oya a wuce aje a cire uniform, kin bar Anuty na jiran ki ” sadiq ne ya dago ya kalli fatuha ya wani tabe baki tare wurga mata harara ya miqa mata jidda, baba jummai ko sai yaba kyan da fatuha tayi take tare da yima su Mom sai da safe fatuha kuma ta ja jidda zuwa bedroom.

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail. com

*fan’s ana mugun tare dinnan sosai*🤝🏽

                      39_40

Bayan ta gama ma jidda wanka ta shafe ta da mai tare da saka mata kaya jeans n t-shirt riga pink wando bleu sannan ta gyara mata gashin ta, tuni jidda ta fito tayi kyau masha Allah, toilet ta koma ta d’auro alwala kasancewa 4:00pm tayi ita da jidda suka gabatar da sallah suna idarwa fatuha ta cire veil din kanta tana kallon gashin ta a mirror tana washe baki, jidda ce ta ce,  “Anuty gashin kine haka? jiyowa fatuha tayi washe da baki ta ce,  “kema kin gani ko? Ai Allah daga yau na gama yawo da d’ankwalli wallahi wannan gashi kamar ba nawa ba”
“gaskiya Anuty kina da gashi dama ki qaramin.! Jidda ta ida zancan tare da washe hakora murmushi Fatuha tayi tare da maida dankwallin ta jawo hijabinta dana jidda suka  wuce wajan malam.

           Sosai suke karatun, damma karutun ya zo ma fatuha da sauki dan duk wani qari da malam ya mata jiya ta juye masa shi, shi kansa yana yabawa da qoqarinta,  qara musu yayi, dan haka basu suka shiga gida ba sai 6:00pm

    Sadiq dake tsaye gaban dress mirror yana gyara sumar shi a hankali ya ji an bud’e kofar dakinsa, cikin zafi rai ya juyo a tunaninsa fatuha ce ta zo masa da wani sabon rainin sai kuma idanuwansa ya gane masa majid.😀
6ata fuska yayi tare da juya masa baya yana  mai  cigaba  da  shirinsa  cikin  nutsuwa, smile majid yayi ya qaraso with full confidence nasa ya  ce, “big man fushi kake dani ko?
kauda kai sadiq yayi ya nufi wajan drawer yana ciro kayansa murmushi majid yayi tare da zama saman sofa, tsaf sadiq ya gama shiryawa fuskarsa daure ya dau phone nashi da ke bedside drawer, zai fita majid ya riqe masa hannu tare da shagwabe fuska ya  ce, “sorry bros.! juyowa sadiq yayi ya wurga masa harara ya  ce, “leave me alone..! tare da fisge hannusa zai murda handle na kofa kenan majid ya ce, “haba  sadiq am sorry nine fa majid” juyowa sadiq yayi yana kallonsa ya qara bala masa harara ya  ce, “kasan da haka shine ka manta dani ko?
“sorry kasan bana zama sosai shiyasa amma ai na kusa dawowa nan da aiki, ka ga dawo ka zauna muyi magana”  Jin hakan yasa sadeeq sakin handle d’in kofa ya dawo ya zauna majid ya  ce, “baby me ya samu qafar ka naga kamar kana d’ingishi?
jan tsaki sadiq yayi ya ce “tsautsayi ne kawai”
“eyya sorry ” sadiq ya  ce, “Tashi muje parlour na gaji da zama a bedroom”
“OK.. Majid yace
parlour suka koma suka dasa sabuwar hira basu suka daina hira ba sai magrib, dauro alwala sukayi tare da wuce wa masallaci

“Aunty..!
“na’am.!
“dan Allah ki koyamin qarin d’azu ban iya ba sosai,”
“to shikenan nima zaki koya min na boko ko?
“eh zan koya maki mana Aunty”
“To bari mu fara yin sallah”  Tashi sukayi tare da dauro alwala suka gabatar da sallah  bayan sun idar fatuha ta qara biyawa jidda karatun sannan jidda ta fara koyawa fatuha ABCD karku so ku ga kwamacala dakyar-dakyar ta dan iya shima ba sosai ba amma tasa ma ranta sai ta iya ko dan ta dinga jin abinda sangami ke cewa wani lokacin.

Bayan sun dawo masallaci majid ya fad’a two sitar ya  ce, “wash am tied..!
Guntun tsaki sadiq ya  ja  ya ce “kai dai kam ka bani daga zuwa masallaci har ka gaji sai ka ce ba namiji ba mtss..!  fruit ya curo a fridge ya fara ci majid ya zuro hannu suna ci suna hira majid  ya  ce, “ni fa na fara gajiya da wannan gwarancin aura zan zo nayi wallahi.! smile sadiq yayi ya ce, “aiya kamata kam dan  gaskiya  ka  dade  ba  aure”
“aikai ma ya kamata kayi wani auran sadiq, duba da yau kusan shekara kausar 5 da rasuwa sadiq, ya kamata kayi aure haka ko saboda angel..! 6ata fuska sadiq yayi ya ce,  “majid bana tunanin zanyi wani abu wai shi aure yanxu, tunda na rasa kausar na rasa wani 6ari na rayuwata, majid kafin a samu mata kamar kausar sai antona, kausar tatara komai dana ke so agun mace, bana tunanin akwai wata ya’mace da zata iya maida gurbinta” ya ida zancan cikin  sanyin  murya hawaye masu zafi na zubomasa kallon tausayi majid ya masa cike  da  lallashi  ya  ce, “sorry baby na famama inda kema ciwo ko? girgiza kai yayi tare da goge hawayan idanusa da bayan hannu  yayi smile ya ce, “majid baka famamin komai ba, indai tunanin kausar ne ba yau na fara ba, yau kusan 5 year da ita nake kwana da ita nake tashi majid.! murmusawa majid yayi tare da qoqarin canza topic dan a duniya ba abinda ya tsana irin damuwar sadiq haka shima sadiq ba abinda ya tsana irin damuwar majid, kallon ball suka shiga yi tare da yin musu dama sun saba ba yau suka fara ba danma yanzu sun girma ne, da da ne har kuka sai Sadiq ya sa majid cikin nishad’i suke kallon.

      “Kinga zo muje mu ci abinci muyi sallah na maki wanka kafin  baban ki ya biyo mu”  washe baki jidda tayi fatu  na  rike  da  ita suka koma parlour dining area suka wuce fatuha ta fara saving nasu tuwon shinkafa miyar taushe taji Alayahu da kaji  cikin nutsuwa suke ci a plate daya.

         bayan sun kamala fatuha ta kwashe kwanikan ta kai kitchen jidda kuma ta haura upstairs, dan tayi missing daddy tun da ta dawo daga school bata qara ganin sa ba, bata iya jira har sai an mata wani wanka, a hankali ta murda handle din kofa a zaune ta gansu a parlour rugawa tayi jikin majid tana cewa, “small daddy I miss you.! smile majid yayi, “miss you my angel how are you?
“fine uncle”  sadiq ne ya murmusa ya ce “ni fa yanzu fushi nake da angel tunda tayi new Anuty take mantawa da daddy” 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka take ce,  “uncle ba haka bane new Anuty na da kirki kuma tana min wasa kuma kasan wani abu daddy” sai ta zamo daga jikin majid taje ga Sadeeq tahau yimasa rad’a akunne, jin abinda take gayamasa yasashi yin wani killing smile… {Wanda koni Salma ban san me jidda take cemasa ba,} majid ya  ce,  “Na zo maki da ice cream amma tunda dadynki kawai kika fad’amawa bana baki ice cream dina” Jin abinda majid yace shiyasata jidda  tsalle tana kuka sai ya bata ganin da gaske kukan ta ke sanyi na gaske sai  ya ce, mata ta bari sai zai tafi ya dauko mata.. washe hakori tayi ta ce “thank u small daddy” tare da yi masa peck tanamaici gaba da cewa,  “Aunty bata san na gudoba dan  wanka zata min fa😀” murmushi majid yayi ya ce “to d’iyar Anuty kice ina gaida Anuty.!
Kallon sa sadiq yayi a zuciyarsa yace da kasan wacece fatuha da ko hanya daya baza ka so ta hada ku ba balle kuma wata gaisuwa ta6e baki yayi tare da jan tsaki ciki-ciki

         Tana fitowa daga kitchen ta fara neman jidda ba ita ba alamar ta upstairs ta haura saboda tasan bata wuce part din sadiq, tana last stairs kenan sai ga jidda ta fito daga part din washe da baki murmushi fatuha tayi ta ce.. “shine baki jira na maki wanka ba sokike daddy yamin fada ne?girgiza kai jidda tayi fatuha ta dauke ta direct bathroom ta dire ta ta fara yi mata wanka sai da ta wanke ta tas sannan suka fito ta aje ta saman bed ta janyo lotion da night dress din jidda sai da ta shafe  ta dashi, sannan ta zura mata kaya.

    “Big man bari na zo na wuce dare nayi”
“tun yanzu dare bai wani yi ba na d’auka fa kwana ka zo min wallahi kaga mun dade bamu hadu ba” murmushi majid yayi ya ce, “next time zankwana”
“To shikenan.
har bakin mota ya raka sa ya ciro ice cream din jidda ya bashi ya  ce, “gashi aba angel nasan Anuty ta maqale ta shiyasa bata fito ba ka shafa min kanta”
“ok ka gaishe min da Umma da Ammi”
“to zasu ji Alhaji da baba fa me suka tsarema da baza ka ce a gaishe su ba? dariya sadiq yayi tare da kai masa duka “wallahi majid ka rainani tunda na ce a gaida mutan gida ai suma sun shiga” harara majid ya bala masa ba “wani nan Ammi da Umma kawai ka ce kuma da yaushe ma ka girmeni har kake fadi na raina ka” harara sadiq ya qara wurga masa ya  ce, “ai dai na baka 4 hours ko qarya nayi” ya qarashe tare da hade ran wasa, dariya majid ya fashe da ita tare da ba mota wuta ya ce, “sai da safe ace ma Mom na zo tana part din Abba” Toh sadiq yace masa da daga masa hannu har sai da motar shi ta fita sannan sadiq ya koma cikin gidan.

      dauke da jidda fatuha ta fito, lokacin  yayi  dai-dai  da shigowar  sadiq  parlour ballama fatuha harara tare da kauda kai, itako tayi kamar bata gani ba, yana gaba suna bayan shi jidda na zuba surutu suna shiga part din a parlour fatuha ta aje jidda tana qoqari fita, kamar  daga  sama  ta ji  zazakar  muryarsa ta doki dodan kunna  ta “keee.. Yace da ita birki ta ja ta tsaya zuciyar ta na dukan uku-uku dan bata manta rashin kunyar da ta masa ba da safe  maganar sa  ce ta  kara  dawowa  da  ita  daga  duniyar  tunani “ba dake nake magana? ya fada cikin daka tsawa, juyowa tayi tana zare ido  ya ce, “kije kitchen ki hada min coffee ki kawo min” zaro ido fatuha tayi waje take ce, “uhm kwarankwatsi ban san me hakan ba” tsoki yaja mtss “yar kauyan banza toh  bunu nake nufi tea mara madara zaki had’a ki kawo min  karki sa sugar a ciki” ya ida zancan tare da balla mata harara abin ma dariya ya so ya ba fatuha wani lokacin sadiq idan yana harara kamar qaramin yaro a zuciyar ta ta ce, “bai ma san idan yana fada wani qara kyau yake ba..! ta dan ja tsaki ta fita, saida ta gama hada masa ta kai masa yana zaune parlour yadda ta barshi jidda na saman cinyar shi da alama bacci ya dauke ta hannu ya miqa zai amshi coffee tana bashi ya saki cup din ya fadi gaba daya ruwan tea din ya zube mata a kafa wani irin ihu fatuha ta bude baki zatayi wata  irin  fisgowa  sadiq  yama  fatu  ta  fado jikinsa tare da toshe mata baki yana kallon ta damn sanyayin  idanusa ido cikin ido, idanuwan fatu t cicikowa sukayi da kwalla hawaye daya nabin daya saboda  azabar  ruwan  tea  din  daya  konata.
murmushi mugunta  yayi na  gefan baki komin banza ya sata kuka, gashi matsar da yayi ma bakin bana wasa bane dan bakin sai radadi yake mata, sai da tayi kuka san ranta sannan ya sake ta tare da hankada ta ta fadi kasa sannan ya tashi ya kashe kayan kallo ya matso gaf da ita har tana jin saukar numfashinsa tana  sauke  ajiyar  zuciya  sama-sama tuni  idanu  ta  sun  rine  zuwa  ja  sadiq ya ce cikin cool voice nasa “wannan kad’an na maki akwai saura nan tafe..! ya ja saki tare da daukar jidda sai da ya kai bakin kofar bedroom ya juyo tare da yin killing smile din shi ya cigaba da cewa, “kuma ki tabata kin gyara gurin kafin ki bar wajan? Yana fad’in hakan ya shige bedroom ya barta tana matsar kwalla tare da jera masa Allah ya isa ta  ce, kuma indai gyara gurine wallahi banyi mugu kawai sannan taja kafar ta wadda ta kone wajan har yayi ja bakin tama haka saboda ya ji matsar manya.

      Direct bedroom dinta ta wuce  tare da rage kayan jikinta, bathroom ta shige tayi wanka ta fito daure da towel tana shafa mai tana mai cigaba da jera masa Allah ya isan, a haka har ta gama shirin tafada saman bed se bacci…

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★

http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&_yn_=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANI WRITERSFORUM.com

                         41_42

Kiran sallah asuba ne ya tada fatuha, alwala ta d’auro tare da yin wanka bayan ta idar da sallah ta shafe jikin ta da mai kamar kullun tare da fesa turare  uniform ta zure sannan ta d’aure gashin kanta wanda dakyar ta kama sa, ganin bai kamuwa yasa ta sake shi haka kawai ta fita direct part din sadiq ta shiga tana karema parlour  kallo, har yanzu glass din jiya nan zube a parlour baki ta ta6e ta shige bedroom sadiq na kwance jidda na maqale a jkinsa da alama daga masallaci ya dawo bacci ya kwashe shi dan jalabiya ce a jikin sa ba night dress ba sajan nan nashi yayi luf-luf kwance, qare masa kallo fatuha tayi sannan ta bala masa harara  ta  ce, “kamar idanuwan shi biyu..!  a hankali ta sa hannu ta fara janye jidda daga jikinsa jawo jidda ya qara yi ya maqale ta, abin ma dariya ya ba fatuha qara jan jidda tayi shima ya qara jan jidda haka suka riqa ja inja  qara leqa fuskar sa tayi taga dai bacci yake a hankali ta qara miqa hannu zata janye jidda cikin dubara  ta janye jidda direct bathroom ta dire ta, kamar kullun ta shirya jidda murmushi tayi  washe da baki  ta ce, “Anuty I like you” murmushi fatuha tayi tare da langwabe kai ta shafa kan jidda tare da cewa, “jidda kisan ban iya wannan yaran ba” murmushi jidda tayi take ce, “ina nufi kina birge ni Anuty” murmushi fatuha tayi wadda ya baya kyawawan hakoran ta ta ce, “nima haka Jidda” peck jidda tayi mata itama fatuha peck tama jidda.

     Jawo hannun jidda  tayi cikin nishadi suka qaraso dining area tea ta shiga hada ma jidda mai kauri, wanda yaji ovaltine da madara  tare da bread n egg a hankali ta shiga feeding din jidda tana amsa itama idan taji dadi sai ta gutsuro bread din taba fatuha, Mom da Abba ne suka qaraso cikin fara’a dining area cikin ladabi fatuha ta gaishe su, cikin  fara’a suka  amsa hada masu breakfast fatu ta shigayi, jidda ce ta washe baki tare da cewa, “morning grandma n grandpa”
“morning too angel” suka amsa a tare  bayan fatu  ta gama hada masu ta aje masu cikin nishadi suke breakfast.

    Tsaye yake gaban dress mirror sanye da bathrobe hannu shi riqe da qaramin towel yana goge sumar kanshi da alama daga wanka ya fito, cikin nutsuwa yake shirinsa lotion ya shafa tare da saka uniform din sa sannan ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi, booth din shi ya curo ya saka black sai sheqi yake tsaf ya fito sojan shi hula shi ya dauko ya sa sai agogo silver na azurfa wanda  ya  dace  da  tsintsiyar  hannusa wani irin kyau yayi ba d’an kad’an ba  sai dai fuskar nan d’aure ba  wani  walwala  kamar  kullun briefcase nasa ya dauko tare da d’aukar wayarsa da ke bedside drawer a hankali ya bud’e kofar bedroom kallo daya yayi ma parlour tare da jan dogwan tsaki ya  furta, “fatuha kin rainani wallahi..! sannan yasa qafa ya fito daga part din a hankali yake saukowa daga upstairs tuni kamshi turaran shi ya mamaye parlour fatuha da ke feeding din jidda ta dago idanuwa tana qaremasa kallo sosai  take  ganin  kyan  sadiq har ta  manta  kanta  wajan  kallonsa, cikin isa ya qaraso wayar shi ya cure ya kara a kunne cikin nutsuwa yake wayar.
“holle ole.! daga daya bangaran ola ya ce, “hello boss”
“ka zo ka amshi briefcase dina” to ya ce masa tare da kashe wayar ya qaraso dinning area smile yayi wanda  iyakar  le66ansa tare da gaishe da su Mom jidda washe da baki ta gaishesa haka fatuha banza yayi da ita kamar bai ji ba tare da qare mata kallo  ganin  yarda  gashin  ta  ya  kwata  har  gadon  baya,  tsintar  kansa  yayi da  maganar zuci, “yau kuma wani sabon iskancin yima mutane yawo a gida ba dankwali  ya  kamata yana yin maganar ne  duk cikin zuciyarsa.
a hankali ta jawo cup da niyar hada masa breakfast hannu ta ya rike ya wurga mata wani irin kallo ya aje hannu tare janye cup din Mom ce ta aika masa harara sai yayi kamar bai gani ba ya cigaba da aikin da ya ke ole ne ya shigo cikin sallama suka amsa sannan ya amshe briefcase din sadiq ya fice da ita Abba ne ya katse shurun da cewa,  “Alhamdulillah ka ce min qafa ta warke? murmushi sadiq yayi tare da cewa, “eh Abba.!
“toh masha Allah”
“Abba ya maganar kwangilar ku kunko samu?
“a’a munan dai muna fama amma insha Allah this time around zamu samu abinda muke so insha Allah” murmushi sadiq yayi tare da cewa, “Allah yasa” Mom ta amsa da ameen tashi yayi tsaye tare da cewa, “oya angel mu tafi” Mom  ta  katse  sadiq  da  cewa “baby karka ce min ruwan tea din har ya isheka ba bread ba komai”
“eh Mom na koshi”
“toh shikenan, ka  dai  kula  da  kanka” hannu jidda ya kama har sun kai baki ko Abba ya ce, “yauwa baby ina san fadama ranar Sunday tare da Mom din ku zamu tafi uk”
OK sadiq ya ce tare da sa kai ya fita fatuha na biye da su da lunch box din jidda har gaban mota sannan ta miqa wa jidda lunch box din tare yi mata peck sadiq kallon su yayi tare da ta6e baki har  mamakin  shakuwar  jidda  da  fatu  yake  bai  ta6a ganin  mai  aikin  da  angel ta  shaku  da  ita  ba  kamar  fatu  ba  kawar da  tunanin  yayi sannan ya shige mota.

     A hankali ta juyo ta shige gida, kwashe kayan breakfast din tayi Mom na zaune a parlour tana kallo fatuha ta zo ta wuce kitchen, washe da baki ta gaida baba jummai itama baba jummai washe da baki ta amsa, rabi’a na gefe tana gyara kayan miya tayata fatuha ta shiga yi suka gyara tare sosai ta taya su  baba jummai, saboda aikin kitchen na burge ta kusan tare da ita aka dafa lunch baba jummai ko dadi take ji har qosawa take suje kauye jauro yaga yadda fatuha ta koma kamar balarabiya, ta  wani  siko  ta  zama  yan  mata bayan sun gama aikin fatuha ta wanke duk wani kwano da akayi anfani da shi rabi’a ko sai hanata take amma taqi bari sai da suka gama komai sannan fatuha ta dawo parlour, ko da ta dawo Mom ta bar parlour  bedroom ta shige tare da rage kayan jikinta bathroom ta shige ta watsa ruwa d’aure da towel tafito bayan ta gama komai sannan ta tuna ashe bata gyara part din sangamin ba,  ko mai bata shafa ba ta zura kayan ta direct part din sadiq taje ta fara gyara sai da ta gyara shi tas, sannan ta zauna a parlour saman three sitar tana maida numfashi  lumshe idanunta tayi tare da ware su, fita tayi daga part din ta koma bedroom ta kuma watsa ruwa sannan ta shefe jikita da mai tare da fesa turare da maida uniform din ta.

   Misalin karfe 2:00pm su jidda suka dawo, kasancewar yau sadiq bai da wani aiki tare suka dawo, part dinsa ya nufa masha Allah gyaran part din ya masa yana jin dad’in ganin part din shi a gyare, duk rashin jin fatuha tasan aikin ta shiyasa wata rana yake d’aga mata kafa, bathroom ya shige ya watsa ruwa ya fito cikin wando da riga ya shirya, kayan sun masa kyau sosai, bangaran su fatuha kuwa jidda na dawowa yadda ta saba yi mata haka ta mata sannan tace taje parlour ko da ta fito parlour  daddyn ta gani jikinsa ta fad’a tana zuba masa surutu shikuma yana sauraranta yana jin dad’i, Mom da Abba ne ke saukowa daga upstairs Abba sanye da shada malin-malin  brown Mom na sanye da atamfa pink mai ratsin green n bleu sanye da mayafinta ba qaramin kyau sukayi ba, parlour suka qaraso washe da baki jidda ta sauka daga jikin sadiq ta riqe hannun grandpa murmushi Abba yayi ya ce “Sadiq yau da wuri ka dawo daga wajen aiki  kenan?” smile yayi tare da cewa, “eh..!
“to mu zamu wuce gidan Ammi mu masu sallama”
“to Allah ya tsare”
“ameen.! jidda ce ta ce, “grandpa zan biku”
“toh shikenan yima fatuha magana” cewar Mom, “sai muje tare ko” rugawa tayi bedroom fatuha kuwa tunda jidda ta fita wani irin bacci ne ya sure ta ko da jidda ta shigo ta samu fatuha na bacci veil din ta ta d’auka tare da fita tana  cewa, “grandma Anuty na bacci”
“toh shikenan tunda bacci take mu tafi kawai ta samu hutu ne” washe da baki jidda ta bi su Abba, sadiq ya rako su har parking space sannan ya koma gida ko da ya koma wani irin killing smile yayi upstairs ya haura sannan ya fito kitchen ya shiga ya dako ruwa a fridge mai sanyi wanda har qanqara ya fara saboda tsabar sanyi a hankali ya murda handle din kofar dak’in fatuha ya shiga.
hangota yayi saman bed kwance tana sharar bacci gashin ta ya baje saman gadon,  da  alama  tana  jin  dadin  baccin cije lips yayi sannan ya qaraso sai da yazo dai-dai face nata ya bud’e murfin rubar ruwan ya juye mata shi, fatuha da ke bacci wani irin razana tayi ta tashi cikin  gigicewa ta yunkura zata fita saboda tsoro, sadiq ya jawo gashin kanta tare da dauke ta da lafiyayan mari,wani irin kuka fatuha ta saki tare da zama saman bed jajayan eye’s din ta ta dago tana kallon sadiq wani irin murmushi yayi ya ce “Fatuha yau zan koya maki hankali, bani kika so ki nakasa ba? toni yau kona maki gashi zanyi” ya ida zancan tare ya matse mata fuskarta, idanuwan fatuha sunyi jawur sai kuka take tana bama sadiq hakuri ganin  ya  koma  mata  bakin  kumurci  dama  ya  lafiyar  giwa  bare  tayi  hauka sosai  tsoron  sadiq  ya  d’arsu a zuciyarta  ganin  abinda  yake  kokarin  yi  ta  zaro  manya-manya  idanuta  waje, ashana ya ciro a aljihun shi ya kunna tare da fusgo gashin ta wani irin kuka fatuha tasa tana  cewa, “dan Allah mai kyau kayi hakuri wallahi bazan sake ba” ta ida zancan tana qara rushewa da sabon kuka “shhhh.! yimin shiru fitsarariyar banza..! nufo gashin ta yayi da wutar dake  hannusa take fatuha ta fashe da wani sabon kukan tare da tafiya luuuu ta sume, murmushi sadiq yayi ganin suma tayi ya ce, “marar kunyar qarya” kitchen ya koma ya d’ako wani sabon ruwan sanyi ya dawo bedroom ya qara juye mata shi wata irin ajiyar zuciya ta saki tare da fashewa da kuka tana bama sadiq hakuri sam  ta  kasa  kwatar  kanta  saboda  yarda  sadiq  ya  matse  ta  can  karshan  bed  har  suna  jin  saukar  numfashin  juna  su, da  sauri-sauri  numfashin su  ke  harbawa  harda  sadiq  din  daya  matse  ta, cije lips yayi yana qare mata kallo yarinya ce sosai amma sai rashin kunya duk a zuci yake wannan zancan, bindiga ya ciro ya daura mata akai tuni fatuha ta saki fitsari ta sauke numfashi agwagwame cikin sarkewar murya ta ce, “dan Allah mai kyau kayi hakuri bazan sake ba” tsaki yaja tare da cewa, “fitsari ma kikayi ko? ya  fada  cikin  daka  tsawa  bakin  fatu  na  rawa  ta  ce, “a’a wallahi ruwa ne haka wallahi” murmushi gefan  baki  yayi ya  kara  hada  rai dan yasan qarya take yana  kallon  gashin  kanta  daya  hargitse sannan ya ce, “daga yau sai yau kika qara min rashin kunya sai na 6ula maki kai da wannan abar kina  jina ? girgiza kai tayi alamar baza ta sake ba, sannan ya  hankada ta kanta ya bigi gado ta qara sakin wani sabon kukan sannan sadiq ya sa kai ya fita.

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★

http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_dial_&_yn=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

                       43_44

Sai da fatuha ta ci kuka sosai tare da jerawa sadiq Allah ya isa, sannan ta tashi jiki ba qwari ta nad’e zanin bed din  Allah ya taimake ta katifar akwai leda dan haka ruwan da fitsarin bai shige cikin katifar ba, iya karshi saman bedsheet tatare shi tayi ta aje ta shiga toilet ta watsa ruwa, tana gamawa ta fito ta d’auki bedsheet din ta wanke shi tas sannan ta fito da bokitin ta aje agefe sai da ta shirya tsaf sannan ta dau bokitin ta fita ko da tafi dasu ola taci karo da Sunday yaran sadiq suna ta shawagi a tsakar farfajiyar gidan, kai tsaye wajan shanya ta nufa ta shanya bedsheet din sannan ta dawo ta zauna saman wata resting chair da ke a farfajiyar gidan, lumshe ido tayi tana jin wani tsoro sadiq na ratsa ta, wasu hawaye masu zafi na zubo mata, dan yau ba qaramar wahala tasha a hannun shi ba take nan wani zazza6i mai zafi ya lullu6e ta sakamakon ruwan sanyin da sadiq ya sheqa mata, ganin masasarar taci qarfin ta yasa ta ja jiki ta koma parlour saman three sitar ta zauna ta qudindine waje daya  tana kyarma abin gwanin ban tausayi😰.

    Bangaran sadiq ko zuciyar shi fes bathroom ma ya shige ya sheqa wanka bai jima sosai ba ya fito daure da towel da dan karami yana tsane gashin kansa,  gaban dress mirror ya tsaya yana gyara kanshi da ya tuno da yanda fatuha tayi sai ya saki murmushi jin dadi bayan ya gama shiryawa cikin 3quarte  da armless t-shirt din shi cikin shirin shi na zuwa gym, sannan ya feshe jikinsa da turare masu sanyi kamshi a hankali ya bude handle din kofar tare da barin part din cikin isa yake sakowa daga upstairs, fatuha ya hango saman three sitar qudindine kauda kansa yayi yana qoqarin fita har yayi gaba sai kuma ya dawo saboda rawar  sanyi  da yaga jikinta nayi har ana  jiyo  had’ewar  hakoranta yasa yaji tausayinta kadan azuciyarsa, a hankali ya qaraso gaban three sitar  ya leqa fuskar ta wadda tayi jawur ga shatin hannu shi kwace a fuskar ta lumshe ido yayi tare da waresu a kanta, a hankali ya kai hannu ya ta6a goshin ta ji yayi goshi da zafi rau  kamar wuta, a hankali fatuha ta ware idanuwan ta ta fara rera masa kuka a tunanin ta wani muguntar ya zo ya mata, daurewa yayi tare da cewa, “yima muta ne shuru kafi na kife ki da wani sabon marin..! tsuru-tsuru tayi tana kallonsa cike  da  tsoro  da  fargaba ga wani irin zazza6i da take ji, lumshe ido tayi ta juya masa baya wayar shi ya ciro dake aljihunshi ya  kira  doctor bugu daya biyu Dr yakub ya dauka sannan ya sheda masa yana buqatar ganin shi, OK ya ce masa tare katse wayar sannan ya kalli inda fatuha take kwance hata gashin kanta jiqe yake, haka  nan  ya  tsinci  kansa  da  tausayinta miqewa  yayi  tsaye  hannuwansa na  zube  cikin  aljihu  yana  karewa  fatu  kallo a hankali ya kai hannu ya d’auki fatuha ita ko sai matsar kwalla take tana  mutsu-mutsu  a jikinsa  cike  da  tsoro tana bashi hakuri banza yayi da ita bai dire ta ko ina ba sai bedroom dinta, saman bed ya direta sannan ya dau ko hand dryer daya ke anfani da ita  fatu  nata  binsa  da  idanuta har  ya jona  hand dryer  jikin soket ya  tako  gabanta gashin  kanta  ya  kama ya busar mata da kanta fatuha ko sai bin shi take da ido AC dakin ya rage ma gudu tare da rufe ta da blanket har  lokacin  fatu  da  ido  take  binsa  tamkar  mutum-mutumi ya koma gefe ya zauna fatuha ko lumshe ido tayi kamar mai bacci.

   Ba’a fi 50 minutes ba sai ga Dr yakub sadiq ne ya masa iso har bedroom dinta, dudubata yayi sannan ya fito da alura da magunguna ya aje a gefe sai da ya gama zuko alura sannan yayi ma fatuha magana, “hajiya ki juya zan maki alura ko dan fever ta sauka” waro ido fatuha tayi ta fara kuka tana  cewa, “dan Allah kayi hakuri wallahi bana san alura” kuka take sosai sadiq ta shiga ba hakuri, banza yayi da ita kamar bai jinta, ohni fatuha yau na shiga 3 ban ta6a tunanin muguntar mai kyau ta kai haka ba duk wannan zancan tana yin shine a zuciyar ta ,Dr ne ya katse shurun da cewa, “please ki tsaya na maki alura kin ji ba zafi fa kuma ko dan ki samu  sauki masasarar da kike yi kinji” Dr ya ida zancan yana smile fatu  ta  ce, “wallahi bana san alura dan Allah kayi hakuri ka kyale ni” Dr yakub ne ya juyo ya kalli sadiq dake ta latsa wayar shi kamar ba mutun a wajan ya ce, “ka ji mara lafiyar ka bata san alura kuma irin wannan fever sai da alura yake sauka” dago sexy eye’s ball’s din shi yayi yana qarewa bed din kallo da fatuha take kwance saman bed din cikin isa ya qaraso  ya ce, “fatuha..! shuri tayi kamar bata ji shi  ba sarai yasan tana jinshi, wani sabon rainin ne haka ji yayi dama bai kira Dr din ba ya barta ciwo ya kashe ta inya tashi mamakin  kansa  ma  yake  yarda  ta  isheshi  kallo  yake  koda  yake  yana  yin  komai  ne  saboda  farin  cikin  angel daf da ita ya zo ya zauna tare jawo ta Jikinsa sosai  suke  jin  saukar  numfashin juna  su  da  yarda  zuciyoyin  su  ke bugawa kuka fatu tasa tana cewa, “ni ka kyale ni bana so” banza yayi da ita ya riqe ta gam Dr ya zunkud’a mata alura wani irin kuka ta saki tare da rungume sadiq gam tana kuka  sai da tayi kuka san ran ta sannan ta fara sauke a jiyar zuciya, dan guntun tsaki sadiq ya ja tare da zame ta daga jikinsa fatuha ko yana zame ta ta koma ta kwanta saman bed tana sauke ajiyar zuciya, sannu Dr yakub ya mata sannan ya dau briefcase din shi tare da yima sadiq bayanin yadda zata sha magani godiya ya mashi sannan ya rako shi har bakin kofa yashiga motarsa ya tafi, shi kuma ya koma bedroom din fatuha  ja mata blanket ganin  tayi  baccin  wahala sannan ya fita ita kuma bacci ya sure ta.

   Bangaran su Mom ko sun isa family house lafiya, direct part din Ammi suka fara shiga cikin fara’a ta tarbe su da jin dadi asiya mai aiki ta kira ta kawo masu fura mai sanyi da kayan motsa baki, aiko sakin jiki sukayi suka sha dan Ammi ba irin iyayan mijin nan ba ce mai takurawa surukanta ba  daukar su take kamar ya’ya ta Jidda ta janyo tana mata wasa ta  ce, “yan’mata baba ina baban naki kwana biyu shuru? murmushi jidda tayi ta ce, “Daddy na nan lafiya lau”
“to madallah kwana ki nake ji majid na cewa sadiq bai ji dadi ba” Mom ce ta ce, “wallahi ko faduwa yayi a toilet”
“Allah sarki ai abun ya zo da sauki”
“masha Allah”
“ai yanzu ya warware sosai da tare zamu zo ma”
“Ayya..! sun sha hira sosai da Ammi daga nan suka wuce part din Umma lokacin baba bai dade da dawowa daga kasuwa ba, baba jan Abba yayi suka shige part nashi suka dasa sabuwar hira abin ka da yan’uwa haka Umma da Mom suka bude sabon shafi na hira Basma ce ta fito sanye da gown ta zo har parlour ta gaida Mom, tare da kawo masu kayan motsa baki sannan ta ja jidda bedroom nata tana mata wasa tare da tanbayarta ina daddy washe da baki jidda ta ce, “yana lafiya lau”
“ok good idan kun koma gida ki ce masa anuty Basma na gaisheshi” to jidda tace mata, chocolate ta dauko a bedside drawer taba jidda sannan ta cigaba da assignment din ta da datake yi sun dade sosai dan kusan a can su kayi dinner sai kusan 9:00pm sannan suka fito, sai da Abba ya qara leqawa part din Ammi ya gaishe da alhaji sannan suka fito har bakin mota Umma da Baba da Basma suka rako su sannan suka juya cikin gida.

    Fatuha kuwa sadiq na lullube ta bacci ya kwashe ta, ba ita ta tashi ba sai da ake kiran sallar isha’i ko da ta tashi zazza6in ya sauka sai dai jikin ta ba qwari, a hankali ta yaye blanket din jikinta ta shige toilet alwala ta dauro bayan ta gabatar da sallah ta koma saman bed ta kwanta.
sadiq kuwa bashi ya fito daga gym ba sai  gab da magrib wanka yayi ya tafi masallaci bashi ya dawo ba sai bayan sallah isha’i ko da ya shigo gida yaji ba motsin kowa hakan tabatar masa da su Mom basu dawo ba, bedroom din fatuha ya leqa kwance ya hango ta,  jin shigowar shi yasa fatuha qara yin lamo haskyan dakin ya kunna tuni dakin ya gwaraye da haske, a hankali ya qaraso ya leqa fuskar ta tare da cewa, “fatuha..! banza tayi kamar mai bacci tsaki ya ja ya ce “Nasan kina jina ko? ki tashi ki sha magani kona qarasa ki da bindiga.! tunda dai mutuwar kike so” tuni fatuha ta tashi zaune tana zarar ido maganin ya shiga bale mata ya bata sai da ta sha sannan ya miqa mata fresh milk tace ta koshi wani irin kallo ya wurga mata ba arziqi ta kafa kai ta sanye, sannan ya fita daga d’akin yana fita ta ce ah ashe su sangami ana da kirki har da hada ni da madara mai dadi sannan ta ja dan guntun tsaki ta koma ta kwanta.

   Bayan ya fito daga d’akin fatuha  parlour ya dawo ya zauna tare da lumshe idanuwan shi kamar mai bacci cikin sallama su Mom suka shigo wani irin smile yayi tare da tashi zaune, ya qaraso wajan su jidda ce ta rungume shi tana cewa, “daddy I miss you”
“miss u more angel kin tafi kin bar daddy shi kad’ai a gida” turo baki tayi ta ce “Daddy Anuty nan bata taya ka hira ba ne ba  ko? ta ida zancan tana 6ata fuska
“eyya my angel Anuty ba lafiya fever take.! moym da zaman ta kenan saman three sitar ta ce, “me ya sameta sadiq ya ce, “Mom fever take dazu na ganta a parlour zaune tana rawar sanyi shine na kira mata Dr yakub”
“good baby ka kyauta bari na dubata” Abba da ke haurawa upstairs ya ce, “kice  ina mata sannu” to Mom ta ce tare da shiga ita da jidda, ko da suka shiga a lokacin fatuha tayi bacci cikin tausayawa Mom take kallonta domin sakanita da Allah take son yarinyar daga karshe tayi mata Addu’a suka bar dakin.

   yau ko sadiq shi da kanshi ya shirya jidda, sannan su kayi bacci jidda ko sai missing din Anuty fatuha take sadiq ko dadi ya ji komin banza ta saitu.
Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★

http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&_yn=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REAlHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

45_46

Misalin karfe 6:00am na safe fatuha ta tashi Alhamdulillah jikin nata da sauki, a hankali ta sauko d’aga gadonta ta shiga toilet wanka tayi tare da yin alwala, tana fitowa tasa doguwar riga ta shimfid’a daduma domin gabatar da sallah, kasancewar yau juma’a tana gamawa ta cire rigar ta saka wasu riga da wando mai ruwan zumuwa rigar ya tsaya mata har gwiwa, ba qaramin kyau kayan suka mata ba sai suka fito da shape din ta sosai veil din kayan ta dako sai yar hoda data murza sai lipstick ta sama lips din ta, tayi kyau masha Allah direct part din sadiq ta wuce.
a dai-dai bakin kofa ci birki tana zazare idanuwanta har ga Allah yanzu Sadiq ya fara bata tsoro daurewa tayi a hankali ta murda handle din kofar, parlour ba kowa sai sanyi AC da ke tashi da kamshi a hankali ta qarasa kofar bedroom ta murda a hankali ta tura kanta cike da fargaba sadiq ta hango gaban dress mirror, sanye da bathrobe yana goge gashin kansa da sallama ta qaraso bedroom din, ciki-ciki ya amsa kamar mai koyan magana jidda dake zaune saman bed itama sanye da bathrobe da alama da ya gama gyara kanshi zai gyarata washe da baki jidda ta ce, “Anuty..! tare da rugawa a guje ta rungume fatu 6ata fuska tayi ta ce “Anuty ashe baki lafiya shine baki fada min ba? ta ida zancan tana 6ata fuska murmushi fatuha tayi ta ce, “Ai yanzu na warke sauke ranki Jidda ta”
“toh shikenan Anuty” sadiq ko harkar gaban shi yake fatuha kuwa sai binshi take da ido a sace tana mamaki hali irin nasa har ta tsinci kanta da zancan zuci, ohni mutun sai shegen kinibibi kamar mace..! dan gutun tsaki fatuha ta ja tare da daukar jidda suka fita.

Bedroom ta dire jidda ta shirya ta cikin uniform din ta, sannan ta raba mata gashin kanta gida biyu taja hannun ta suka wuce dining area, Mom da Abba na zaune a dining area cikin nutsuwa ta qaraso ita da jidda ta gaishe su cikin ladabi a tare suka amsa tare da yimata ya jikin, washe da baki tace da sauki jidda ta jama kujera ta zauna sannan ta fara saving nata tana cikin saving nata sadiq ya qaraso dining area gaishe da su mom yayi tare da yi masu peck, sannan ya samu kujera ya zauna masha Allah ya sha kyau har ya gaji, kallo daya fatuha ta masa ta kauda kai cikin tsanarsa amma duk da haka sai da ta yaba kyau irin na sadiq har mamaki kyan sadiq ke bata, anya akwai wanda ya fishi kyau kuwa ta jefawa kanta tanbayar, musanman yau da yake sanye da manyan kaya yayi matukar kyau da kwarjini, tunda ta zo gidan yau ce rana ta farko data fara ganin mai kyau da manyan kaya shada ce sky blue yasa tasha dinki da dark blue zare anmasa irin dinkinnan na sarauta sai hula blue mai ratsin dark blue da kafa ma kansa ta zauna d’ansa, hannu ya kai ya d’au cup ya fara hada tea dan shi mutun ne ba mai san yawan cin abinci ba, bayan ya gama hada tea ya fara sha a hankali Mom ce ta kalle sa tare da cewa, “baby karka ce min yau ma tea kadai zaka sha? lagwabe kai yayi ya ce, “eh..!
“haba baby wai me yasa baka san cin abinci ne uhm” Abba da ke gefe ya ce “Sai kace ba soja ba sojoji da aka sani da cin abinci” shagwabe fuska yayi ya cigaba da shan tea din ganin Mom nata magana yasa shi cin chips din kadan fatuha sai da tabatar jidda taci ta koshi sannan ta kyale ta bayan sun kamala cin abincin sadiq ya dau jidda fatuha na biye da su da lunch box har bakin mota, sannan jidda ta mata peck ta shige mota juyowa tayi ta shigo gida da su Abba ta ci karo Mom ta rako shi riqe da briefcase din shi wuce su tayi ta koma dining area chips ta zuba ma kanta a plate da farfesun kifi bata wani ci da yawa ba saboda har yau bakin ta ba dad’i bayan ta kamala ta fara kokarin kwashe kwanikan, Mom ce ta shigo dauke da fara’a a fuskarta ta ce “Haba fatuha ke da baki da lafiya ina ke ina aiki ki? zauna ki hutu” washe baki fatuha tayi tana qoqarin yin magana Mom ta hanata kwalawa rabi’a kira tayi cikin ladabi rabi’a ta qaraso ta d’urkusa har kasa ta gaishe da Mom Mom ta ce, “yawa rabi’a kwanikan nan zaki kwashe sannan yau ki je ki gyara part din sadiq, saboda fatuha bata jin dadi har” cikin zuciyarta rabi’a bata so Mom ta ce ta gyara part din sadiq ba saboda basa wani shan inuwa daya jiki ba qwari ta kwashe kayan dining area din fatuha kuwa daki ta koma tasha magani bata wani dadi ba bacci ya kwasheta.

A cikin school yayi parking din motar shi tare da zagayowa ya budewa jidda murfin mota, ta fito lunch box din ya miqa mata tare da yi mata peck a kumatu ta ce, “daddy am going to miss you”
“I now angel karki damu anjima idan an tashi ni zanzo daukar ki kin ji angel” murmushi tayi tare da yi masa peck ta shige class yana kallon ta har ta shige, shi kuma ya wuce wajan aiki cike da kaunar diyar tashi.

Ba ita ta tashi daga bacci ba sai karfe 11:30pm ita kanta tayi mamakin baccin da tasha, toilet ta shiga tayi wanka ta fito tare da shafe jikin ta da lotion wardrobe ta bude ta ciro atamfa brown mai ratsin black n white atamfar ta hadu riga da skirt dinkin ya mata kyau sosai y’all zauna a jikinta tamkar an aunata qarewa kanta kallo tayi ta cikin dressing mirror, murmushi ta saki tare da cewa, “gaskiya birni tayi dubin yanda na koma kamar ba fatuha inna ba.! duk wannan zancan tana yinshi ne a zuciyarta, murmushi takara yi tana qoqarin kama gashin kanta bud’e kofar da akayi ne yasa ta saurin waigowa a tunanin ta Jidda ce sai taga Hanan washe baki tayi tare da cewa, “Hanan..! cikin fara’a Hanan ta qaraso dakin sanye take da lace sky green mai ratsin black sai veil dinta white ba qaramin kyau tayi ba ta fito yan’matan sak, zama tayi saman bed tare da cire veil din ta ce, “wash na gaji wallahi” dariya fatuha tayi take ce, “wai kin gaji, aiki me kikayi da kika gaji? murmushi Hanan tayi tare da cewa “Kai fatuha karki ce min wannan uban gashin naki ne?” fari da ido fatuha tayi ta ce, “na Hanan ne.! bugu Hanan ta kai mata cikin wasa ta ce, “kai amma fa kin ji dadi” murmushi fatuha tayi ta ce “Ina Jamal da afra?”
“suna parlour tare da grandma nima tanbayar ki nayi sai grandma ke ce min baki ji dadi ba, shine fa na shigo na maki sannu toh ashe har kin warke kin fara make up” ta ida zancan cikin tsokana, dariya fatuha tayi ta ce “Wallahi naji sauki danma Mom bata barni nayi aiki ba”
“ai ta kyauta wallahi”
“amma yau baki je school ba?
“eh exam muke na JSCE shiyasa ban je ba yau bani da paper Jamal kuma fever yake shiyasa,” murmushi fatuha tayi take ce, “ni wallahi ina san makarantar nan sai ma na shirya jidda zata tafi sai naji kamar na bita”
“ai karutu akwai dadi akwai wahala kiyi ma Mom magana mana” smile fatuha tayi tare da cewa toh jidda ce ta shigo bedroom din ta fada jikin fatuha murmushi tayi ta ce “Yan makaranta har andawo kenan?” daga mata kai jidda tayi ta “eh Anuty kin ga daddy ya siyo min ice cream da zamu dawo har da chocolate da yawa kuma fa naba daddy naki ya aje mana” murmushi fatuha tayi ta ce toh a zuciyarta kuwa cewa tayi ta6 wannan daddy naki ai sai ke Hanan ce ta katse mata tunani da cewa bari naje wajan uncle nima na amshi nawa tana fadin tana qoqarin daukar veil din ta zata fita ta ce, “fatuha idan kin gama shirya jidda ki same ni a parlour muyi lunch” toh tace mata bawai dan tasan me Hanan ke nufi da kalmarta na qarshe ba daukar jidda tayi ta shige da ita bathroom ta wanke ta tas sannan suka fito ta shafeta da mai tare da samata gwon pink mai qaramin hannu sai gashinta da ta gyara mata tayi kyau sosai masha Allah.

Direct parlour suka fito Anuty bilki na saman two sitar zaune, Mom na zaune saman three sitar suna kallo gaishe su tayi Mom tayi mata ya jiki ita da Anuty bilki da gudu jidda ta koma wajan Jamal da ke zaune saman daya daga cikin kujerin dining area itama ta zauna cikin fara’a fatuha ta qaraso ta fara saving din su, Hanan dake saukowa daga upstairs tana zunburo baki gaba cikin bacin rai ta qaraso dining area din fatuha ta kalle ta ta ce, “Lafiya naga kamar an bata maki rai ? dan guntun tsaki taja ta ce, “wallahi uncle ne ya bata min rai shi kullun cikin bakin rai maganar arziqi ba taba hada ku dashi” murmushi fatuha tayi ta ce “Yi hakuri kinji zauna mu ci abincin mu idan mungama mu fita farfajiya shan iska”
“yauwa tawa..! abinci suka ci cikin nishadi bayan sun gama fatuha da Hanan suka kwashe kwanikan sunka kai kitchen sannan suka fita farfajiyar gidan domin shan iska.

Saman resting chair suka zauna, suna dan taba hira fatuha ba qaramin jin dadi gurin take ba saboda har da yan shuke-shuke lumshe ido tayi ta ware su Hanan ta ce, “kai fatuha karki ce min wai bacci kike ji”
“ah ba bacci nake jiba kawai wajan yamin ne ina san guri kamar haka, shiyasa sanda nake akauye kullun muna bakin rafi ni da fatsima” murmushi Hanan tayi sun dade sosai a filin gida suna hira kiran sallah magrib ne ya tashe su a wajan suna tafe suna hira, sadiq da ke qaqorin fitowa zai je masallaci sanye da jalabiya milk fatuha bata lura da mutum ba tayi kansa ba tayi masauki ko ina ba sai saman fafad’an kirjinsa rintse ido fatu tayi tana zare ido tayi lamo a kirjinsa tana jira taji saukar aradu saboda tuni hancinta ya mamaye da kamshinsa, wata iri tsawa sadiq ya daka mata wadda yasa yan hanjin ta katsawa tayi baya zata fadi ya tarota cikin zafin nama idanusa waje kamar yarda fatu ta zaro nata duka waje kirjinta na bugawa da sauri da sauri, sakinta sadiq yayi da sauri Hanan ko take ta kama gefe jikin fatuha ta rabe, harara ya aika masu su duka cikin 6acin rai ya ce, “stupid girl’s kuna tafiya kuna kalle-kalle baku kallon gaban ku mtss..! sannan ya sa kai ya fita, sauke ajiyar zuciya Hanan tayi ta ce, “ba dai jaraba ba mtss, sannu fatu indai uncle ne haka yake kullun cikin bakin rai da hargowa” fatu data dauke wuta na wucin gani murmushi tayi ta ce, “ni zan fada maki haka..! sannan suka shige cikin gida.

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

                        47_48

      Bayan su idar da sallah parlour suka dawo suna kallo, kitchen fatuha ta shiga anan ta iske baba jummai tana farfesun yan’ciki gaishe ta tayi cikin sakin fuska ta amsa mata  tare da yimata ya jiki, da sauki ta bata amsa tana qoqarin bude fridge fruits ta debo ta zuba a boll na glass tare da wankewa sanna ta dauko wuka parlour ta koma Hanan da ke zaune saman one sitar ta duro qasan carpet tare amshe wuqar hannu  fatu ta ce, “Bari ni na yanka fruit din, kinga ke bakida lafiya” harara fatuha ta aika mata ta  ce, “waya ce maki bani lafiya? lafiya ta lau inda za’a auna mu qilama na fiki lafiya” dariya Hanan tayi ta ce “Wasa kenan” tare da cigaba da yanka fruit din sai da ta gama yanka fruits din sannan ta maida wuqar ta dawo parlour suka fara cikin fruit din cikin jin dadi  suna kallo suna taba hira.

         Anuty bilki ce zaune saman sofa Mom na saman bed zaune aunty  bilki  ta ce, “Mom yanzu sai yaushe zaku dawo?
“wallahi ban sani ba amma nasan sai mun kai 2weeks tunda shi wancan zuwan da yayi sai da yayi kusan 3weeks” shagwabe fuska Anuty bilki tayi ta ce, “amma fa gaskiya Mom zamuyi missing naki wallahi” murmushi Mom tayi tare da cewa, “kanku bazan zauna ba naqi bin tsohon mijina ba, akan wani dalili  zan barshi kullun yana zuwa uk ni ina Nigeria ni mai ya’ya, ya’yan da suna gidan miji,” dariya Anuty bilki tayi ta ce, “kai Mom..! harara ta wurga mata ta  ce, “kinga idan takuramin zakiya tashi ki ban gu kona samu na cigaba da hada shirgi na,”
“Mom wato kaya zaki kwasa da yawa kenan?
“laaaa yau Allah ya kawo mu ‘ya na tirtse uwar ta dan zatayi tafiya da uban ta, toh kaya zan d’iba da yawa kika bata min rai wallahi har wata sai muyi” ta ida zancan tana bude bedside drawer baqar leda ta curo ta ce, “yauwa ga wannan tun wancan satin na so na aiko baby ya kawo maki, to ban samu dama ba” washe baki Anuty bilki tayi  ta  ce, “kai Amma fa Mom naji dadi  Allah yasa wannan maganin irin wancan ne gaskiya wancan naji dadin shi” murmushi Mom tayi ta ce “Ai ina tunanin wannan yafi wancan, dan wannan dan sudan ne”
“amma fa na gode Mom kamar kinsan gobe zai dawo”
“toh ai shikenan daya garin da madara ake sha duk dare  shi kuma dayan da zuma ga turaruka nan masu kamshi idan kina anfani da su ko cup kika riqe sai yayi kamshi,” washe baki Anuty bilki tayi ta  ce, “thank you  Mom kamar kin san Abban Hanan nasan kamshi sosai wallahi”
“ah daughter waye baya san kamshi? sai dai idan mutum bai samu ba kamshi na da muhinmanci sosai daughter, ko kamshi kika riqe to wallahi kin riqe mijinki a hannun ki,” haka Anuty bilki ta dinga jerawa Mom godiya agogo ta kalla kusan 8:30pm ta  ce, “Mom bari muzo mu lalla6a mu tafi gida dare ya fara yi, ba dan gobe Abban Hanan zai dawo ba da mun kwana wallahi,”
“ai ko ba bazai dawo gobe  ba ban zan bari ki kwanar min gida ba, ke kullun kika zo yini sai ki bige da kwana, ai hakuri ake a zauna har miji ya dawo ya same ka ba wai  ka kwaso kafa kazo  gida ba” mayafinta ta janyo da  handbag dinta ta tura bakar ledar ciki  fitowa sukayi daga bedroom din Anuty bilki na gaba Mom na bayan ta suka sauko daga upstairs sai da ta iso parlour ta yafa mayafin ta, su Hanan da ke zaune parlour suna shan fruit Anuty bilki ta qaraso ta  ce, “Hanan ku tashi mu tafi dare nayi” bata fuska Hanan tayi ta ce “Momi na fa dauka sai 9:00pm zamu tafi ”
“ai kin san bana san driven din dare ko? kuma ba da driver nazo ba” Hanan bata so su tafi yanzu ba da ba exam suke ba da nan zata kwana fatuha ma haka bata ji dadi ba saboda idan Hanan ta zo tana de6e mata kewa Anuty bilki ce ta katse masu tunani da cewa “Hanan yima baba jummai magana  zamu tafi ta baki afra” bata ida rufe bakin ta ba sai ga baba junmai riqe da hijabin ta a Hannu afra na goye a bayan ta washe da baki ta ce, “ah kuma har kun fito yanzu na ke cewa bari na kawo maki Afra, yau nama yi daran tafiya da yake na tsaya yima mai gida farfesu,” Mom ce ta ce, “ku dai baku ji baby ya sata farfesu ke kuma kin miqa mata diya tana ta fama ga afra da shegen kuka”
“ba komai ai kuma ko kukan ba tayi ba”
“Allah ya taimake ki shi kuma baby bayan yasan baki wuce magrib shine zai daura maki wahala” murmushi baba jummai tayi tana qoqarin miqawa Hanan afra, dariya Anuty bilki tayi ta ce, “Mom da kin bar shiga tsakanin baba jummai da baby ko ka shiga kai zaka sha kunya” murmushi Mom tayi  aunty  bilki ta ce, “to ai sai mu wuce tare sai na sauke ki gida baba”
“toh shikenan” tare suka fito fatuha na kusa da Hanan sunata zuba surutu jidda na riqe da hannu Jamal duk suka rako su filin gida, Anuty bilki na qoqarin bude murfin mota sadiq ya shigo tsayawa tayi tana sakin Murmushi qarasowa yayi ya ce “Sister har zaki tafi? na dauka kwana zakiyi ai” ya fadi cikin zolaya, harara ta maka masa ta  ce, “baby ka rainani wallahi” dariya yayi ya  ce, “baba har dake zasu tafi da niyata na kai ki,”
“ah ba komai” Hanan dake kusa da fatuha sai turo baki take sadiq ne ya kalle ta tare da aika mata harara ya ce, “sister na kusa fara cima Hanan naga kwanan wani rashin ji ke damun ta,”
“ni ba ruwana wannan tsakanin ku ne,”
“toh shikenan” raurau da ido Hanan tayi tare da cewa, “uncle sorry.! harara ya kuma aika mata ganin bai da niyar hakura yasa ta ta6e baki ta shige mota tana yima fatuha bye bye su duka suka shige motar Aunty bilki ta ce “Idan anyi hutu this time around jidda gida na zatazo” toh ya ce mata ai sun kusa fara exam “I think this Monday zasu fara” eh Anuty bilki tace masa tare da jan motarta  suka bar harabar gidan sannan su fatuha suka jiyo riqe take da hannu jidda.

               Direct bedroom suka wuce sadiq kuma ya wuce dining area, ko da suka shiga bedroom  fatuha ta dire jidda tayi mata wanka sannan itama tayi  kusan tare suka shirya saboda itama yau ta gaji tasha surutu har da godema Allah, night dress suka sa  sannan ta dau jidda tana mata surutu suna haurawa upstairs a hankali ta murda handle din kofar part din sadiq, a parlour suka iske shi zaune yana kallon news da gudu jidda ta fada jikinsa ta  ce, “daddy…!
“yes my angel”
“uhm daddy ina ice cream din Anuty da chocolate din ta? laqace mata hanci yayi ya ce “yana bedroom” da gudu jidda ta shige bedroom fatuha kuma na qoqarin fita har ta bude kofar, jidda ta qaraso riqe da ledar shopping ta  ce, “Anuty ga naki”
“angel har dani a tsarabar” washe baki jidda tayi ta ce, “eh.!
“toh na gode” ta amsa ta fita.

        Direct bedroom din ta ta shige tare da kunna haske,  saman bed ta zauna tare da bude ledar shopping din tun kan ta fara shan ice cream din miyan ta ya tsinke, tana sha tana kada kai tana  cewa, “Amma fa wannan abu akwai dadi sosai gaskiya mai kyau yasan kan kwad’ai.! sai da ta cika cikin ta da ice cream sannan ta kwanta bacci yayi awan gaba da ita.

****
Akwana a tashi ba wuya wajan Allah sadiq ne janye da trolley din Mom dana Abba sai da ya zo bakin kofa ya ba ola da Sunday yayi musu umarnin da su sa kayan boot, ok boss ola  ya  ce fatuha ko na parlour zaune sai tsoro take yanzu idan su Mom suka tafi Allah kad’ai yasan muguntar da sadiq zai mata ranan unguwa ka dai suka je amma sai da ta d’and’ana kud’ar ta, bale kuma kwanaki duka wannan zancan a zuci take tare da kukan zuci dan tasan watan cin uban tane ya tsaya, su Mom ne suka qaraso parlour tana riqe da hannu jidda sai lisafa mata tsaraba da zata mata take washe da baki fatuha ta tashi tana yi masu Allah ya kiyaye hanya, Mom har ta kai bakin kofa ta juyo da kalli sadiq ta ce, “toh ga amanar fatuha sauran kuma idan na dawo naji ka  mata wani abu dan nasan hali” 6ata fuska yayi kamar qaramin yaro yana bin fatuha da harara tuni yan hanjin ta suka fara kadawa dan tasan kashin ta ya bushe, daurewa kawai take amma ji take kamar ta daura hannu aka ta sa ihu gashi baba jummai taje biki kauye daga ita sai rabi’a kuma rabi’a data gama aikin ta take tafiya, jidda ce ta katse mata tunanin datake tare da  janta har suka qarasa farfajiyar gidan, sadiq ne ya shiga wajan zaman driver da alama shi zai kaisu airport tuni jidda itama ta shige motar mom ce ta juyo ta ce, “fatuha duk abinda kike buqata kiyiwa baby magana kinji” toh tace mata tana raraba ido tana daga masu hannu har motar su ta fita daga harabar gidan.

*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas’ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM*🐄
★we are the best★

http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com

          49_50

   Su sadiq na fita harabar gidan, fatuha ta juyo gida cike da tsoro raurau tayi da ido kamar tayi kuka saboda tuntuni rabi’a ta tafi sai ita kadai kwal a gidan sai su ola, parlour ta zauna tayi tagumi kamar munafuka tana ta raraba ido kamar wadda tayima sarki qarya, ganin tsoran ba zai fishe ta da  komai ba yasa ta kuna kallo washe da baki ta dau remote control tana canza tashoshi Bollywood ta kai tayi shiru tana kallan film gaba ki daya imanin ta naga TV jin cikin ta ya fara kukan yunwa yasa ta tashi, dining area taje ta zubo macaroni da miya yaji kifi sosai kasancewa fatuha ba mai san macaroni ba ce yasa ta zuba kadan, ta dawo parlour saman three sitar ta zauna ta fara ci bayan ta kamala ta kai plate din kitchen tare da wanke wa bedroom ta koma tare da rage kayan jikin ta ta shiga wanka bata wani dad’e ba ta fito  ko da ta fito lotion ta shafa tare da feshe jikin ta da turare white t-shirt din ta na aiki tasa kasancewa rigar ta kawo mata gwiwa sai taji bata sha’awar sa skirt din gashin ta ta baza  ta sharce, masha Allah fatuha ba qaramin kyau tayi ba qarewa kanta kallo tayi a dressing mirror dariya tayi ta ce “Kai dan Allah dubi yadda nayi kamar ta cikin film din dana gama kalla hhhh lol”  ta kumayin dariya tana godema Allah da yawadata ta da gashi a haka tasa kafa tafita daga bedroom din.

Bangaran su sadiq yana kai su mom airport , ya wuce da jidda family house dan shi yama manta da wata fatuha part din ammi ya shiga riqe da hannu jidda, Ammi dake zaune ta ce, “a’a wana ke gani,” murmushi sadiq yayi tare da zama saman kujera yana gaisheta sannan ya ce, “Matar yanaga kin qara kyau?” washe baki Ammi tayi tana gyara daurin dankwalin ta tare da amsa masa ta qaraso parlour itama ta zauna, “ohni mai gida ace min jiki yayi sauki da har na fara dakan gunba ance min kana can rai hannu Allah ka zama dan gurgu” ta ida zancan tana dariya ,turo baki sadiq yayi ya ce “Haba ammi har so kike na bingire kenan? dariya ammi tayi tare da jawo jidda jikinta ta ce, “yar nema yau ba’a amin gwalangwatsin ba” smile jidda tayi kawai tare da cewa “Ammi ina gorubar da kika ce zaki siyo min ni da jamal?
“yar nema ashe baki manta ba ai tuntuni na siya tana daki na cikin drawer” da gudu jidda ta shige dakin ammi ta dan juyowa Ammi tayi tana facing din sadiq gyara murya ammi tayi ta ce “Ni ko Sadiq ya kamata kayi aure yanzu fisabilillahi dubi yadda jidda tayi wayau sosai yarinya na shirin zaman yan’mata, amma kai baka ko maganar aure bale nuna sha’awar ka ko dai baka lafiya ne Abubakar sadiq?” sadiq dake zaune saman three sitar ya hada gira sama data qasa kamar bai taba dariya ba, Ammi ta cigaba da cewa, “kai kullun baka so a fada ma gaskiya sai ka hau gunguni shi kuma Ibrahim ya zuba ma ido ko maganar aure bai ma,” sadiq ko  tunda ammi ta fara magana ya kai wuya dan shi bai da sharin yin wani aure yanzu, Alhaji ne ya qaraso parlour da alama yanzu ya dawo daga kasuwa ganin Ammi nata fada yasa Alhaji qaraso dan yaji ba’a sin zancan, ganin sadiq tasa gaba ya san maganar gizo bata wuce qoqi ya ce, “haba ladingo ya za ai ki tasa yaro gaba kina masa maganar aure? koma me ake samu a auran nan ai ya taba yi inya gaji da zama haka ai dole yayi aure tunda shi ba qarfe bane”, ammi tabe baki tayi ta ce “Malam kenan da yaranan na da wannan tunanin ta tuni yayi amma kwata-kwata banga alamar yin hakan ba,
“koma dai menene bakin  sasa gaba ba kina masa fada ba, ko abin motsa baki ba ki basa ba amma sai fada kike masa,” shiko sadiq dadine ya mamaye masa zuciya sai  murmushi yake Ammi tayi yake ta ce “Wallahi malam abin ya tsayamin araine?” Alhaji zama yayi kusa da sadiq tare da shafa gashin kansa ya ce,”yi hakuri kaji Abubakar sadiq,” qaqaro murmushi sadiq yayi wanda iya qarshi lips din shi alhaji ya ce, “yauwa ko kai fa,” ammi asiya ta kwalawa kira ta kawowa Alhaji abinci da sadiq, sadiq sai fama daurewa ammi yake bayan asiya ta kawo komai ammi tace ya sauko ya ci, “na koshi ya fadi a taqaice,” bude baki ammi tayi ta fara fada “yanzu ni sadiq ban isa nama magana ba ko na baka shawara sai ka nunamin ban isa ba, ko Ibrahim ai bai isa yamin haka ba” matsar kwalla ta fara Alhaji da ke gefe takaici ma ya hana shi magana sadiq ganin abun ammi da gaske ne ya sashi cin abincin tare da sakin rai sannan ammi ta ji dadi ba laifi ya dan saki jiki amma sai wani bangare na zuciyar shi ya ke ji kamar ta fama masa inda ke masa qaiqayi tabbas yasan yayi rashin kausar har abada bazai kuma samun wada zata maye gurbinta ba, amma wani bari na zuciyar shi yaqi yadda ya cusa son wata diya mace har ta samu gurbi a zuciyar shi numfashi ya sauke tare da miqewa tsaye yana kiran angel Ammi ta ce, “mai gida kardai ka ce min tafiya za kayi? ko har yanzu baka huce ba? murmushi sadiq yayi ya ce, “haba matar ni na isa nayi fushi dake nayi fushi dake gobe ina zan fake” washe baki ammi tayi ta ce, “yauwa dan albarka, Allah yasa ma Albarka”
“ameen ammi”
” bari na kirama yar neman nan nasan yanzu haka ta wargaza min daki” dariya Alhaji yayi ya ce, “aiko data kyauta,”
“malam har da kai cikin masu biye ma ifiritan nan? da yanzu Jamal zai zo su hade biyar baka siyan part din nan” dariya Alhaji yayi tare da shigewa bedroom din shi, ammi kuma ta shige nata tana kwalawa jidda kira aiko tana isa dakin taci karo da abin goriba duk jidda ta watsar a tsakar dakin Ammi ta ce, “ohni ladingo ai dama na fadi nasan za’a rina tunda najiki shuru” washe baki jidda tayi ta ce, “ammi.! sadiq dake parlour ya qaraso yana dariya ya ce, “laa angel waya ce kiyi ma ammi 6ena? turo baki tayi ta ce “Daddy ba 6ana nake ba” ammi ta ce, “gidan ku kikayi ko? dariya jidda tayi ta boye bayan baban ta sadiq ya ce, “ammi bari mu qarasa part din Umma”
“toh shikenan saura can ma ki mata barnar” haqora jidda ta washe sannan sadiq yayi ma ammi sallama suka wuce part din Umma.

     Parlour ta kuma dawowa tare da kallan agogo ganin karfe 3:00pm yasa fatuha rau-rau da ido, tasan za’a rina tunda aka bar amanar ta a hannu sangami a iya tunanin ta ko wani gari suka kai su mom ya ci ace sun dawo gida, zama tayi saman one sitar can kuma sai ta tashi upstairs ta haura sama direct part din sadiq ta shige, a hankali ta murda handle din cikin sa’a kofar ta bude saboda a tunanin ta ya kulle part din, tana shiga sanyi da kamshi suka mamaye mata hanci lumshe ido tayi tare da mai da kofar parlour ta rufe bedroom dinshi  ta shige tana ta kalle-kalle wani album ta hango ya leqo ta qarqashin gado duqawa tayi ta jawo shi da hannun ta washe da baki ta bude album din, picture din sadiq ta fara cin karo da shi ya saki murmushi a picture din yasha kyau har ya gaji, cigaba tayi da ganin pics din album din wani guri ta ganshi da kausar wani gurin shi daya ganin yadda suke pictures din yasa fatuha ta dade tana kallon pictures din ko ba’a fada mata ba tasan maman jidda ce saboda suna kama da jidda ji tayi gabaki daya sun birge ta haka ta lallace tana kallon albums din kiran sallah la’asar ne ya sata qoqarin mai da album din har ta turashi qarqashin gado sai ta ji wani album din, jawo shi tayi tare da yin smile ta ce,, “bari na tafi da wannan idan na idar da sallah ya debe min kewa, tunda ni ka dai suka bari wato sun barni a gida duk abinda zai cinye ni ya cinye ni” downstairs ta dawo ta aje album din a parlour ita kuma ta koma bedroom ta dauro alwala.

   Da sallama su ka shiga part din umma, Umma na zaune tana kallo tana shan fruit a hankali da alama zaman ya mata dadi, cikin fara’a ta amsa sallamar su sadiq zaunawa yayi tare da gaisheta ta amsa jidda ko saman ciyar Umma tayi masauki umma ta ce, yan’mata baba” fari da ido jidda tayi ta ce “Na’am grandma”
“a’a waya koya maki fari da ido haka? dariya tayi ta ce “Aunty mana”
“wace Aunty? Ta bata amsa da cewa “Aunty fatuha mana”
“ah ni ban santa ba”
“kam aiko Aunty fatuha na da kirki sosai yanzu haka tana gida” murmushi Umma tayi tare da yi masu tayin fruits qasa sadiq ya sauko ya sha fruits din shi ya qoshi sannan ya haura upstairs cikin nutsuwa ya murda handle din kofar dakin majeed kwance saman bed ya hango majeed yana ta sharar bacci dan gutun tsaki ya ja tare da shiga daki fridge ya bude ya dau ruwa mai dan sanyi-sanyi sai da yazo saitin face din majid ya zuba a hannun sa ya shiga yayafa masa, firgigit majid ya miqe yana qoqarin tashi ganin sadiq yasa shi komawa ya zauna tare da zabga tsaki ya ce, “kai dai wallahi mugune in ban da mugunta ina bacci zaka sheqa min ruwa? harara sadiq ya aika masa ya ce, “yanzu lokacin bacci ne kana ganin la’asar ta wuce”
“mtss toh ina ruwan ka?
“da ruwa na” sadiq ya fada sannan ya zauna saman sofa, “wallahi big man baka kyauta min ba wallahi mafarkin wata hot baby nake kawai ka zo ka katse wa mutane jin dadi mtss tashi ka ban guri dan iska kawai,” dariya sadiq ya fashe da ita sakin baki  majid yayi yana mai kallon rainin wayau ya ce, “me haka wai,?
“ka ga kyale ni je kayi wanka first munyi magana,” ya ida zancan cikin dariyar shaqiyanci tsaki majid ya kuma ja sannan ya yaye blanket din jikin shi ya wuce bathroom ko 50 minutes bai yi ba ya fito sanye da bathrobe dressing mirror ya nufa ya shafe jikin shi da mai da sunyi 4 eye’s da sadiq sai ya aika masa harara shiko sadiq fuska yayi tare da jawo newspaper yana qarantawa sai da ya gama shirin shi tsaf sannan shima ya zauna saman sofa tare da qanqace ido yana kallon sadiq kamar zai masa masifa, dariya sadiq yayi tare da kuma daurewa duka majid ya shiga kai masa da pillow yana cewa, “d’an iskan banza sai wani kallo na kake kana dariya munafuki Allah ka dai ka san mafarkin uwar me kake kai ma, dadin abun ba kai na farau ba,” ya ida zancan yana harara sadiq smile sadiq yayi ya ce, “nina ce ma wani abun ne? wanka fa kawai na ce kayi? ko nace wani abu? ya ida zancan yana kare fuskar shi da newspaper yana dariya, sun dade sosai a family house ba su suka fara tunanin dawowa gida ba sai kusan 9:00pm lokacin jidda ma tayi bacci har farfajiyar gida suka rako su sannan sadiq ya ja mota suka bar gidan.

  fatuha ko  tana idar da sallah parlour ta dawo, ta cigaba ta kallon album tun bata jin tsoro har ta fara ji saboda duhu ya kunno kai kuka ta ci ta gaji tare da rakubewa jikin kojera rungume da album har bacci wahala ya kwashe ta, a parking space yayi parking dauke da jidda ya fito tare da yima motar key a hankali ya bude kofar parlour, ya qarewa parlour kallo tare da kunna haske parlour ya gwaraye ko ina cikin nutsuwa ya qaraso parlour  kallo daya yayi ma kujera da fatuha take kwance sannan ya wuce upstairs, bedroom ya shinfide jidda sannan ya shiga bathroom ya watsa ruwa yana fitowa jalabiya white yasa ya fita daga part din, saboda yana son shan coffee ya dawo downstairs inda ya bar fatuha nan take kwance har lokacin kare mata kallo ya shiga yi duka gashin kanta ya baje akan kujera, cinyarta bude yake kasancewar qaramar riga ce a jikin ta fuskar ta Sadiq ya qarewa kallo masha Allah yau ce rana ta farko da ya fara kallon fuskar fatuha dakyau eyes lashes din ta sunyi gadar-gadar kamar ansa mascara, tabe baki yayi yana qoqari shiga kitchen har ya kai bakin kofa ya dawo saboda album din da ya ganta rungume dashi, cikin zafi rai ya juyo ya ce, “fatuha..! cikin daka tsawa a razane ta tashi tsaye saboda yarda ta ji kiran da sadiq ya mata har cikin kwaryar kanta ta sakin album din qasa, dab da ita sadiq ya qaraso cikin zafin rai ya ce “Uban me kike min da album? Dan iskanci shine kika sakeshi kasa ko? a tsawace yayi maganar kuka fatuha ta saki saboda gabaki daya ya ruda ta mari ya wanke ta da shi lafiyaye ya ce, “open your mouth and talk to me,” kuka fatuha ta saki mai tsuma zuciya tare da yin magana cikin shashakar muryar ta ce “Dan girman Allah kayi hakuri me nayi maka ne mai kyau? koko amanar da mom ta baka ne tun yau zaka fara cinta” ta ida zancan tare da fashewa da kuka, ta cigaba da cewa, “bayan horan da kamin na barina a cikin makekyan gidanan bai ishe ka ba shine dan karfin hali harda mari na” 😭 kuka ta kuma saki tare rugawa da gudu bedroom.

   Sadiq ko amanar mom da yaji fatuha tace ne yasa jikin shi yin sanyi tare da daukar album din jiki ba qwari ya haura upstairs.

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★

http//mobile.Facebook.com./Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

51_52

Fatuha na shiga bedroom saman bed ta fada tare da sakin saban kuka tana cigaba da jerawa sadiq Allah ya isa da ace Allah ya isa na fitowa a jiki to da daran yau ba abinda zai hana shi fitowa ajikin sadiq, kuka ta ke mai tsuma zuciya har da shesheqa tana a jiyar zuciya, ita babban abinda ke damun ta koda ta zo masa muguntar sai ta kasa kuma ko tayi mai ramawa ya ke, lumshe idanuwanta tayi tare da sauke numfashi a hankali ta cigaba da jerawa sadiq alkaba’i a haka har bacci barawo ya sace ta.

Bangaran sadiq ko saman sofa ya zauna tare da ganin bai kyauta ma fatuha ba, lumshe ido yayi tare da ware su koma mai yayi mata ita ke san shiga gonarsa shiyasa shi kuma baya saurara mata da tasan yadda yake ji idan yaga albums dinan da ko fada mata akayi ta dauko su inda ya aje ba zatayi ba, iska ya busar mai zafi daga bakinsa bayan Ammi ta gama hada masa zafi ita kuma ta dagulamasa lusafi album din ya bude a hankali kamar mai jin tsoran wani abu ya shiga kallon pics din, ya dade yana kallon inda yake ganin mutuwar kausar ta dawo masa sabuwa har hawaye sai da ya zubar kamar ba soja ba, anan saman sofa bacci ya kwasheshi.

*Asuba ta gari*

Ko da ya tashi da asuba wanka ya sheqa sannan yasa jallabiya ya wuce masallaci, yana dawowa ya samu bacci mai cike da nutsuwa amma duk da haka qirjin shi namasa zafi saboda tsabar damuwa lumshe ido yayi tare da jan jidda jikin shi bacci ya kwashesu.

Fatuha ko da kuka ta tashi fuskar ta har tsami ta mata, saboda ba qaramin mari tasha hannun sadiq fuskar nan ta kunbura tayi sumtum kallon mirror tayi tare da fashewa da kuka fuskar tayi jawur har idonta sai da ya qara girma saboda tsabar kuka, toilet ta shiga tayi wanka tare da dauro alwala tana fitowa after dress tasa black tare da gabatar da sallah ko da ta idar da sallah kuka ta cigaba da rerawa sannan ta tashi jiki ba qwari ta murda handle din kofar tare da ficewa daga bedroom din direct part din sadiq ta shiga.
Duk da tana jin tsoro haka ta lalla6a ta murda handle din kofar bedroom zaune ta hango sadiq saman sofa yana danna laptop yana shan coffee cikin dari-dari ta qarasa shigowa tare da yin sallama, dago kai sadiq yayi ya qare mata kallo shi kan shi yasan bai kyauta ma fatuha ba ya 6ata mata baby face din ta, ra6ewa ta shiga yi dan tak take jira ta arce sunan ta ya kira cikin cool voice din shi gaban ta ne ya yanke ya fadi duk da yauce rana ta farko da mai kyau ya fara kiran sunan ta, sai taji duk duniya ba wanda ya iya fadi fatuha qara kiran suna ta yayi hakan yasa ta fara matsar kwalla tana yarfe hannu ta qarasa kusa da shi tare da tsugunnawa tana wasa da yantsun hannu ta idanuwanta taf da kwalla hannu yasa ya dago da habarta lumshi ido yayi tare da waresu gaskiya bai kyauta ma fatuha ba ji yadda ya mai da fuskarta, tausayi ta bashi sosai kuka ta shiga reramasa a tunanin ta wani mari zai qara zabga mata “shhhh.! ya ce mata cikin cool voice nashi shiru tayi tana matsar kwalla bedside drawer ya bude ya ciro magani a dan top sannan ya dawo sofa ya zauna tare da talabo mata fuskar matsar maganin yayi a hannu ya shiga shafa mata a face din ta kuka fatuha ta saka sai kace ya watsa mata ruwan zafi iskar bakin shi ya shiga hura mata mai sanyi lumshe idanuwan ta fatuha tayi, wani irin dadi taji dan tunda ta tashi da safe fuskar ke mata radadi sai yanzu da taji dama-dama, ware eye’s ball din ta tayi kan sadiq, tana kallonsa sadiq da ke qoqari dagowa goshin su ya hade ushhh ya ce, shagwabe fuska fatuha tayi tare da fara kuka sorry yace mata sannan ya sa hannu ya murza mata wajan dan karya kunbura har lokacin da ido fatu ke binsa komai sadiq yayi murgeta ta yake, sannan ya kyaleta tare da yi mata lallausan smile tashi tayi tana qoqarin daukar jidda su fita, fatuha yace juyowa tayi tana kallonsa ya ce, “shiga da ita toilet dina ki mata wankan” to ta ce masa sannan ta shige da jidda bathroom bin ta yayi da kallo tare da daukar newspaper.

Bayan ta wanke jidda tas suka fito washe da baki jidda ta gaisheshi, amsa mata yayi tare da yi mata peck jidda ta ce, “Aunty me ya sami fuskar ki” jidda ta fada a tsorace kallon sadiq fatuha tayi shima ita yake kallo sannan ya kauda kai murmushi fatuha ta qaqaro ta ce “Bigewa fa nayi jiya, aini fushi nake dake Jidda kika tafi kika barni ni kad’ai a gida to shine fa na bige gashi ba kyanan” raurau jidda tayi da ido ta ce “Sorry Aunty ba laifina bane laifin daddy ne” ta ida zancan tana nuna daddy da hannu daddy ta ce cikin shagwaba ya ce, “yes..! a taqaice yana kallon newspaper, “daddy please kar a qara barin Aunty a gida ita kad’ai, daddy kalli face din Aunty fa?” tana fadi tana ware ido juyowa sadiq yayi ya kalli jidda tare da lumshe ido angel kin fiye surutu please ki tsaya Aunty ta shirya ki kinga mun kusa maqara, sai da fatuha ta gama shafe jidda da mai sannan suka fita kai tsaye bedroom din ta ta dire jidda ta shirya ta cikin uniform din ta sannan ta ruqo hannu ta suka fito parlour dinner area suka zauna ta shiga bama jidda abinci tana feeding din ta sadiq ya qaraso dining area riqe da briefcase din shi kujera ya ja ya zauna, plate fatuha ta janyo ta fara saving din sadiq yau anci sa’a bai hana ta ba sai da ta gama zuba masa ta tura masa gabansa sannan ta hada masa tea a cup ya amsa ya fara sha zai kai chips din baki ya kalli fatuha da ke feeding din jidda, ya ce “Ke Bakiyin break din?” kallon shi fatuha tayi ta hadiye wani yawo dan bata san me yake nufi da hakan ba murmushi sadiq yayi ya ce, “yar kauye kawai kalaci nake nufi.! washe baki fatuha tayi ta ce “Aiyo zanci to”
“fara cin yanzu” murmushi tayi tana ci tana feeding din jidda a zuciyar ta ko mamakin canji sadiq take, shiko sadiq amanar Mom yake riqewa ba wai wani abun ba, fatu ko tana cin abincin tana satar kallon sadiq.

Bayan sun gama break har filin gida fatuha ta rako su da lunch box din jidda peck jidda ta mata tare da yi mata bye bye, fatuha na tsaye har suka fita daga harabar gida ta juyo ta dawo cikin gida kayan breakfast ta kwashe ta kai kitchen, a kitchen ta hadu da rabi’a na girki murmushi tayi tare da gaisheta amsa mata tayi cikin fara’a sannan ta aje kwanikan cikin zing ta wanke su tas rabi’a sai hannata take amma taki kusan tare sukayi komai na kitchen din sannan suka jera a dining area ,washe baki rabi’a tayi ta ce, “kai amma fa fatuha na gode dan ba dan ke ba da yanzu ina ta aiki wallahi” murmushi fatuha tayi tare da cewa, “ba komai wallahi”
“bari na zo na lalla6a na wuce gida” kala tausayi fatuha tayi ta ce, “Wai har zaki tafi ne?”
“eh wallahi,”
“yanzu ni ka dai za’a bari a gida nan kamar maya? ta ida zancan tana raurau da ido, Rabi’a ta ce, “yi hakuri kin ji fatuha akwai inda zani da ba inda zani dana taya ki hira amma akwai inda zani” murmushi fatuha tayi ta ce “Ba komai” bakin kofa ta raqota sannan ta koma parlour ta zauna tare da kunna kallo kitchen ta shiga ta gyara fruit sannan ta dawo parlour tana ci tana kallo har bacci ya kwashe ta.

Bangaran sadiq yana sauke jidda ya wuce office, ko da ya je office yayi aiki sosai karfe 2:00pm nayi ya fito yaje school din su Jidda ya dauko ta suka dawo office tare sai zuba masa surutu take kowa na office din ji yake da jidda, daka ganta hannun wannan sai ka ganta hannun wancan sai la’asar sadiq ya amshe ta suka wuce gida.

Fatuha ko kiran sallar la’asar ne ya tashe ta, wanka tayi tare da dauro alwala tana gama sallah parlour ta dawo tana lunch cuscus ne da miyar kwai take ci tana jin dadin abincin har wani lumshe ido take, sallamar su sadiq ce ta qatse mata cin abinci washe da baki ta kalli jidda rugowa jidda tayi ta fada jikin fatuha tana dariya cike da tsantsar Darin ciki itama fatuha dariya tayi tare da gaishe da sadiq ciki-ciki ya amsa kamar mai koyan magana sannan ya haura upstairs, fatuha ko saida ta cikawa jidda cikin ta da abinci sannan ta kai ta bedroom ta rage mata kaya sannan ta kaita toilet ta mata wanka sai da ta wanke ta tas sannan suka fito suna daririku, lotion ta shafa mata sannan ta sa mata gwon brown mai kyau tare da jan hannun ta suka dawo parlour, hango sadiq sukayi yana zaune a dining area yana lunch guri fatuha ta samu ta zauna jidda ko wajan daddy ta nufa tare da haye masa cinya tana masa surutu ta ce, “daddy.!
“yes angel.!
“daddy please muje shan ice cream please” ta fadi tana lagwabe kai ja mata hanci sadiq yayi ya ce “Wannan bakin naki kullun san zaqi yake” dariya tayi mai nuni tana cikin farinciki, ture plate din gaban shi yayi tare da aje jidda qasa qafa ta shiga bubuga masa ita aladule sai sun je shan ice cream yau yace mata “Ok Angel is ok daina kukan kije Aunty ta shirya ki ko” sannan ya haura sama yana last stairs jidda ta ce, “amma har da Aunty zamu tafi dan kar dodo ya ji mata ciwo” toh yace tare da bude kofar part din shi.

Shirya jidda tayi tsaf amma ita ta rasa kayan da zatasa, duk gwon din data janyo sai ta maida jidda rugawa ta yi parlour zaune ta sami sadiq cikin shirin shi na qananan kaya yasa red riga mai ratsin black mai dogwon hannu shirt sai wando black da takalmi yasha kyau har ya gaji sajan shi ya kwanta luf sai sheki yake sumar kansa tasha gyara jidda ta fada jikinsa ta ce, “daddy..! a dan shagwabe sadiq ya juyo alamar gajiya ya ce, “menene angel? lagwabe kai tayi ta ce, “daddy zo ka za6a ma Aunty dress ta rasa wanda zatasa” dan guntun tsaki sadiq ya ja ya ce “Angel me yasa kika fiye rigima?” um bata fuska tayi tana shirin yin kuka tana qoqarin sauka daga jikin sadiq hakan yasa sadiq tashi ba dan ya so ba bedroom din fatuha ya shiga tsaye ya ganta gaban drawer ta riqe qugu ga kaya baje a saman bed bakin kofa ya tsaya yana qarewa bayan ta kallo juyowa fatuha ta yi jin kamar ana binta da kallo ta bayanta su kayi 4 eye’s da sadiq dake binda da sexy eyes ball d’insa kauda kai tayi ta cigaba da abinda take a hankali ya qaraso wata gwon ya gani kawai ya jawo ba wai da ya lura da ita ba miqa mata yayi ya ce, “kisa wannan mu tafi” sannan yasa kai ya fice cikin 5 minute fatuha ta shirya cikin red gwon mai stones sai black veil tasa tare da murza hoda ta shafa lipstick wani irin kyau fatuha tayi komai na shape din ta ya bayana duk da ba wasu shekaru gare ta ba amma ita kanta tana mamakin girman jikinta kallo daya zaka mata kasan ta hadu tayi tamkar ba yar aiki ba takalmi tasa tare da feshe jikin ta da turare masu kamshi sannan ta yafa veil din ta, a hankali ta bude handle din kofar bedroom din parlour ta fito sadiq dake zaune saman two sitar ya lumshe ido, jidda na zaune gefe shi kamshin turaren fatuha ne yasa sa ware sexy eye’s ball din shi ya sauke su kanta wani irin kyau ta masa na ban mamaki sosai ya zage yana binda da idanusa ta6e baki yayi yace ashe wannan yarinyar nada kyau duk yana wannan zancan ne a zuci miqewa yayi tare da daukar car key suka fita, gaba jidda ta shiga fatuha na baya jidda sai zuba mata surutu take.

Sun sha yawo kamar me ice cream ko har sai da suka ture, fatuha ko baki har kunne dan dadi duk inda suka wuce sai an kalle su saboda sun sha kyau sun gaji munjibir park sadiq ya kai su zama yayi a resting chair yana kallon su, su fatuha wasa ko ba wanda basuyi ba, basu suka bar munjibir park ba sai yamma likis a gajiye suka dawo gida, fatuha ko dadi fal a zuciyar ta jidda ko saboda tsabar gajiya tayi bacci cikin mota.
hancin motarsa yasa cikin gida bayan mai gadi ya wangale get parking space yayi parking bala mai gadi sai washe hakkra yake daga masa hannu sadiq yayi tare da dai-daita parking din motar sannan ya kashe motar, kamar jira fatu take ta fito murfin motar gaba ta bude tana qoqarin d’aukar jidda shima sadiq ya turo kai da hannu yana qoqarin daukar jidda ji kake gwab sun qume kai “wash..! sadiq yace fatuha ma haka yadda sadiq yayi da fuska shi yaba fatuha dariya sai kace baby boy, dariya ta saki har ana ganin fararan haqoranta sosai take dariyar mai cike da birgewa, dariya da fatuha take sai ta qara mata kyau hakan yasa sadiq mutuwar tsaye yana kallon fatu yana qara ganin kyanta 6oyaye na bayana na ban mamaki, kallo da yake mata ne yasa ta tsagaita dariyar tare da daga masa gira hakan maido da sadiq saiti harara ya aika mata ya wani had’e rai ya ce, idan kin gama dariyar ki dauko ta mu shiga gida” dariyar da yake shirin zo mata ta guntse tare da daukar jidda.

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Salma mas’ud nadabo

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄

★we are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=,52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSFULANIWRITERSFORUM.com

53_54

          Sadiq na gaba tana biye dashi a baya, bakin bedroom din ta taci birki tana qoqarin bude kofar sadiq  ya juyo fuskarsa ba yabo ba falasa ya ce, “ina kuma zaki da ita bayan tayi bacci?
“uhm dama wanka zan mata” shafa sumar jidda yayi tare da cewa, “Ki samata night dress kawai saboda tayi nisan bacci” Allah ya taimake ta jidda ta ta6a fadin Kalmar shiyasa ta gane mai yake nufi, haurawa sama yayi ita kuma ta shige daki tare da kunna haskyan dakin shinfide jidda tayi sannan ta soma rage kaya jikinta, sai da ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito daure da qaramin towel cikin nutsuwa ta shafe jikin ta da mai tare da zura night dress din ta riga ce pink mai zanan cartons jikin rigar, rigar dai-dai gwiwa ta tsaya sai dan siririn hannun kamar na vest gashin ta ta sharce ya baje a gadon bayan ta, bayan ta gama shirya kanta ta shirya jidda cikin kayan bacci, sannan ta dauke ta a hankali take taka upstairs din saboda yau jidda ta qara nauyi cikin nutsuwa ta murda handle din kofar part din sadiq, parlour ba kowa sai sanyi AC dake tashi da kamshi direct kofar bedroom ta bude tsaye ta hango sadiq gaban dressing mirror yana goge sumar shi da qaramin towel sanye yake da bathrobe white hakan yasa ana ganin lallausan gashinshi na qafa kauda kai fatuha tayi, tare da yin sallama juyowa yayi ya qare mata kallo, mamaki gashin fatuha ke ba shi gashin har yaso ya mata yawa juyowa yayi ya cigaba da abin da yake shinfide jidda tayi tana qoqarin fita, lumshe ido sadiq yayi tare da ware su ya ce, “Fatuha..! juyowa tayi tana kallon shi can sai tayi qasa da eye’s ball’s din ta, ki hada min coffee toh tace tare da fita downstairs ta dawo tare da shiga kitchen ta hada masa coffee ta dawo, ko da ta dawo yana zaune a parlour yana kallon news aje masa tayi saman stool tare da ficewa, cikin nutsuwa ya shiga shan coffee yana kallon news amma sai dai ku san kallon news din kawai yake ba wai dan yana fahimta ba, kashe kayan kallOn yayi ya koma bedroom saman bed ya kwanta tare da janyo jidda jikin shi lumshe ido yayi ba wai dan yana jin baccin ba, saboda gaba ki daya kwanakin nan da tunanin kausar yake kwana.

   Tana shiga bedroom ta fada saman bed tare da yin addu’a bacci ko   minut 10 ba tayi ba bacci ya kwashe ta.

        Kiran sallah asuba ne ya tashe ta wanka tayi tare da dauro alwala tana fitowa uniform tasa tare da gabatar da sallah, sannan ta shafa mai ta fesa turare  parlour ta fito ko ina share kwal hakan ya tabatar mata da rabi’a ta zo, kitchen ta shiga washe da baki ta gaishe ta cikin fara’a ta amsa kasancewar yau Saturday shiyasa fatuha bata je part din sadiq da wuri ba, rabi’a ta shiga tayawa aiki doya suka fere suka dafa sannan suka yanka fatuha ta gyara albasa rabi’a ta fasa kwai  ta kade tare dasa albasa da percil da tonka sante da tafarnuwa da sauransu, fatuha  na kallo soya doyar da take,  rabi’a da taga fatuha ta iya suyar sai ta sakar mata ta shiga gyara fruit saboda za’ayi ma sadiq juices da su bayan ta gyara ta markada  ta juyo a  jug ta saka qanqara ta kai dining area kafin ta dawo fatuha ta kamala soya doyar ta juye a kula rabi’a shigowa tayi da murmushi ta ce,”Ah sannu da qoqari” murmushi fatuha tayi Rabi’a ta  ce, “ki kai kula dining ni bara na soya kwai” to fatuha tace tare da wanke hannu ta a zing ta dau kula ta wuce dining area, bayan ta aje kula ta dawo parlour ta kunna kallo arewa24  tana kallon gari ya waye washe da baki take kallon dan tana jin dadin shirin ganin goma ta gota yasa ta haura upstairs tana bude parlour zaune taga sadiq saman three sitar, idanuwan shi lumshe abin ya so ya dan bata mamaki saboda bai saba bacci a parlour ba sallama tayi sadiq da ke jingine kamar me bacci ya ware sexy eye’s ball’s din shi kan fatuha tare da amsawa kallonsa tayi ta ta6e baki tare da gaishe shi amsawa yayi kamar bai san magana fatuha ko shiga daki tayi amma sai dai yau tana ganin suku-suku da sadiq yayi, yayi yawa sai taga yayi kamar wadda bai samu bacci ba tabe baki ta yi ta ce, “ke Fatuha ina ruwan ki?” duk wannan zancan a zuci takeyin shi tada jidda tayi washe da baki jidda ta tashe tana cewa, “Aunty good morning? murmushi fatuha tayi tare da daukar ta ta kaita toilet ta mata wanka suka fito suna dariya tsane mata jiki tayi sannan ta shafa mata lotion kasancewar akwai wasu kayan ta a dakin shiyasa anan fatuha ta shirya ta, jeans n  t-shirt tasa mata rigar white sai jeans blue masha Allah tayi kyau sosai  fita tayi daga dakin tabar fatuha na gyara daki.

  Washe da baki ta fada jikin sadiq ta  ce, “daddy morning”
“morning too angel, how was ur night angel,”
“cool daddy n Ur’s daddy”
“The same” ya ida zancan yana mata peck jidda  ta  ce, “daddy..!
“yes sweet..!
“uhm me ya sami eye’s din ka sunyi ja,” lumshe ido yayi ya ce, “angel daddy ciwo ido yake,”
“sorry daddy, a kira uncle yakub ya duba ka please daddy,”
“na warke ai har ma nasa ma gani”
“sure daddy?
“yes  my  angle” peck ta masa cheeks tare da cewa, “daddy am Hungary,”
“ok ina Aunty ?
Aunty na busy now, OK muje nayi feeding naki ko sweetheart,” OK daddy daukar jidda yayi yana mata wasa tana dariya sai da suka qaraso dining area ya ja kujera ya zauna sannan ya d’aura jidda saman cinyarsa ya shiga saving din su sai da ya kamala ya fara feeding din jidda yana bata tana bashi cikin jin dadi.

       Bayan ta gama share bedroom din tas ta dawo parlour ta kwalwale shi tas, ta kunna Burne  a socket tare da sa turaran wuta tuni part din ya dau kamshi mai sanyi, gudun AC ta qara lumshe ido tayi tare da zama saman three sitar tana qarema dakin kallo, ita kanta part din ya mata kyau yadda ta gyara shi ji tayi kamar tayi bacci tashi tayi ta fita daga part din.

    A hankali take sakowa daga upstairs jidda dake saman cinyar daddy ta kwalawa fatuha kira, cikin jin dadi “Aunty..! wata irin juyowa fatuha tayi har sai da gashin kanta iska ta kad’a shi fari tayi da ido ta ce “A..!  Sadiq  dake  zaune  yana  kallon  fatu  tamkar  an  dasasa kashe  ma  jidda  ido  tayi  tana  sakowa ta  dage  mata  gira kujera  sadiq  ya  bi  ya  lafe  yana  bin  fatu  da  ido yarda  takeyi tamkar  da  shi  take, dariya jidda tayi ta ce, “Daddy ka ga yadda gashin Aunty yayi” lumshe ido yayi ya ware su kan fatuha yana qare mata kallo gani yake kamar idannuwan shi ke mai gizo kwanan kullun qara canza masa take kawar da zancan yayi ya cigaba da abinda yake,  saukowa jidda  tayi daga cinyar shi riqe da doya a hannun ta fad’a jikin fatuha ta  ce, “Aunty..!
“na’am.!
“bude bakin ki na baki yam” toh fatuha tace tare da bude dan qaramin bakinta ji tayi jidda ta bata ragowar doyar hannunta sadiq da ke zaune saman kujera dining yana kallon su ta qasan ido har mamakin yadda jidda ta saba da fatuha haka yake, ta6e baki yayi ya shanye ragowar tea din da yake sha ya miqe  ya wuce su ya haura upstairs fatuha ko dining tazo ta cika tunbin ta sannan taja jidda suka koma parlour suna cikin kallo rabi’a ta fito tare da yi masu sallama, har bakin gate suka rakata bala mai gadi sai tsiya yake ma jidda ita kuma sai turo baki take fatuha ko dariya abin ya bata janyo jidda tayi suka dawo cikin gida suka cigaba da kallo.

    Wani irin sanyi da kamshi ya doki hancin shi part din kwal kamar ba’a kwana ciki, wani irin sanyayan ajiyar zuciya ya saki tare da sakin handle din kofar, bedroom ya shiga nan ma wani irin lallausan smile ya saki komai ya mai yadda yake so take ya ji wani irin bacci na fizgarsa saman bed ya fada tare da sauke ajiyar zuciya bacci da baiyi jiya ba shi ya kwasheshi.

    Sun sha kallo har sun gaji  ba su suka bar parlour ba sai 1:30pm shima kiran sallah ne ya tashe su, alwala suka dauro sannan suka gabatar da sallah suna idarwa suka dawo parlour, ola ne yayi knocking din kofa fatuha ta tashi ta bude masa washe da baki ya kalle ta, cikin hausarsa mara fita ya ce, “madam sannu”
“yauwa.! fatuha tace “dama wannan malam min ne da ke koya maku karatu ne ya zo yanzu,” murmushi fatuha tayi ta ce, “malam ai ba da rana yake zuwa ba” ta fadi tana leqa waje ta  ce, “bari ina zuwa” daki ta shiga ta janyo  hijabin ta tare da daura zani saboda mini skrt ne jikin ta  sannan ta fito lokacin har ola ya koma bakin aikin shi malam na zaune saman tabirin mai gadi suna dan taba hira cikin nutsuwa fatuha ta qaraso tare da gaishe shi, murmushi yayi ya amsa ya  ce, “ah malama fatuha” murmushi kawai tayi  ya  ce, “kinga yau na zo tun 2:00pm wallahi ina da wata safga  anjima shine nace da naki zuwa gara na zo yanzu tunda kwana biyo ba muyi karatun ba” murmushi fatuha ta yi ta ce, “aiko dai malam mun gode bari na kira jidda” toh yace mata tare da tashi daga tebirin bala mai gadi ya koma inda suke gabatar da darasin, fatuha na shiga gida tasa mata hijabin ta suka fita.

    Cikin jin dadi suka gabarta da darasin su inda malam yayi masu qari tare da yi masu yan tanbayoyi suka bashi amsa sai da ya tabatar sun gane misalin karfe hudu ya sallame su, ya wuce akan cewa gobe karfe hudu zai zo insha Allah littafan su suka kwashe suka shiga gid, dama daure da alwala  fatuha take  sallah ta gabatar sannan ta cire zanin ta shiga wanka tana fitowa daure da towel ta tsane jikin ta tare da shafa jikin ta da lotion har ta dauko uniform din ta zata maida ta tabe baki, tunda na gama aiki ai sai na sa na gida dan ni na fara gajiya da su.! ta fadi tana turo baki wardrobe ta bude ta curo wata pink gwon mai dogwan hannu rigar  simple ce mai kyau tayi shape sosai tayi mata kyau rigar ita kanta sai da ta yaba rigar parlour ta dawo ta zauna, jidda na zaune tana kallon carton itama ta zauna tana kallon.

    Ring din wayar shi dake bedside drawer ne ya tasheshi dan guntun tsaki yaja tare da kai hannu ya dau wayar, ba tare da ya duba suna ba ya  ce, “hello.!  cikin alamar gajia ta daya bangaran a kayi dariya, sadiq tashi yayi zaune tare da saki guntun murmushi, ta  daya  bangaran  aka ce, “wallahi sadiq baka da kirki Allah yasa ma ka gane mai magana? yar dariya yayi tare da shafa sajan sa ya  ce, “ba Khaleed bane? dariya Khaleed yayi ya ce, “ashe dai kana gane mutane” dan guntun tsaki sadiq ya ja ya  ce, “ya za’ai na kasa gane muryar childhood friend dina,”
“ai ka kyauta ina majid ai ya fika zuminci,”
“haka dai kace”
“toh yau na leko Kano insha Allah zan shigo”
“toh shikenan sai ka zo idan ka zo ka kira ni” toh yace tare da yanke wayar agogwan dake manne a bangwan daki ya kalla ware sexy eye’s ball’s din shi yayi “ohno na kwanta ina ta bacci har 4 ya gota.! tashi yayi tare da yaye blanket din jikin shi toilet ya shige ya sheqa wanka yafito daure da qaramin towel a qugunsa, hannun shi riqe da qaramin towel yana tsane sumar kan shi yana cikin shafa lotion wayar shi ta fara ruri hannu ya sa ya dauka tare da karawa a kunne ta  daya  bangaran  aka  ce, “hello big man ganin a filin gidan ku” smile sadiq yayi ya ce, “are u serious,?
“yeah angayama kowa irin kane mara zuminci” dariya sadiq yayi  ya  ce, “kai friend nine fa”
“koma yane.!
“toh shikenan ganin zuwa” katse wayar yayi tare da zura jallabiya white ya fito daga part din shi ya wuce su fatuha a parlour suna ta karatun dan fatuha ta dake sai jidda ta koya mata karatun boko yanzu haka har ta iya ABCD.

      Yana fita farfajiyar gida ya hango Khaleed jingine jikin motarsa mai tsada kallo daya zaka masa kasan shima dan hutu ne, kuma gaye ne sanye yake da shada  tasha diki mai kyau Khaleed chocolate colour ne yana da saje daya kara bayanar da kyawunsa, yana da manyan ido murmushi ya saki ganin sadiq ya qara so fararan haqoran shi suka bayana cikin jin dadi sadiq ya qaraso tare da miqa masa hannu suka gaisa ya  ce,  “Ashe dama zan kara  ganinka a duniyar nan? murmushi  Sadiq yayi  ya  ce, “bagashi ba ai kai ma baka zama shiyasa”
“haka kuma dan last week ma na dawo daga London har muka hade da yaya jawad wajan shopping shi da matar shi har ya ke ce min sun kusa zuwa gida, jira kawai yake Aunty shukara da haihu su zo” murmushi Sadiq yayi ya ce, “haka ya fada min”  suna tattaunawa har suka qaraso kofar parlour cikin parlour suka shigo har yanzu su fatuha na nan inda ya bar su ,Sadiq ya ce  “Fatuha.! dagowa tayi ita da jidda tare da gaishe da Khaleed murmushi Khaleed yayi tare da amsawa yana bin fatuha da kallo Sadiq ya katse masa tunani da cewa “Fatuha ki kawo mana glass cup” ta ce masa toh tare da shigewa kitchen sadiq ya  ce, “jidda ga uncle.! Khaleed smile jidda tayi Khaleed murmushi yayi ya ce, “karka ce min angel ce ta girma haka”
“ita ce mana” zaro ido waje Khaleed yayi ya ce, “kai.! amma gaskiya mun yadda zuminci, come here angel” kusa da shi jidda ta matso kallon ta yayi tare da daukar ta suka haura upstairs sai tanbayar ta ya ke tana zuba masa surutu suna shi ga part din Sadiq saman two sitar Khaleed ya zauna tare da daura jidda a cinyar shi, sadiq kuma fridge din bedroom ya bude ya curo lemu ka masu sanyi ya kawo ma Khaleed lokacin yayi dai-dai da shigowar fatuha dauke da tray da cup’s amsa tray din Sadiq yayi tare da yi mata nuni da ta dau jidda, Khaleed sai bin fatuha da kallo ya ke kiran jidda tayi suka fita a tare tana fita Khaleed ya sauke ajiyar zuciya, yana kallon  Sadiq, Sadiq din ma kallon shi yake ya  ce, “big man ina kuka samo beautifully girl,”
“wake nan ya? fadi a taqaice
“wadda ta dau angel yanzu” murmushi Sadiq yayi ya ce “Fatuha she is my sister baka ga muna kama ba” ya fadi zancan yana cigaba da zuba ma Khaleed juice khaleed ya  ce, “amma ai nasan kai ne dan auta baka da wata sister” bashi glass cup yayi na lemo yana qara saki wani murmushin wanda iya karshi lips din shi ya  ce, “she is my consin sister yanzu ka gane ko” murmushi Khaleed yayi ya ce, “amma fa tana da kyau karka ce min Basma ce ta zama mai kyau haka” tanbayar Khaleed ta kusa fara kai Sadiq wuya amma sai ya maze ya ce, “ba ita ba ce wannan diyar sister mom ce”
“eyya.! shi kansa Sadiq yana mamaki karyar da ya zauna yana shunfuda ma Khaleed me  ke  damun  sa  haka toh me idan ya ce masa yar aiki ce, dan guntun saki ya ja a zuciyar shi  khaleed ya  katse  sa  da  cewa, “Sadiq mom fa?
“Mom ba ta nan sun tafi uk da Abba” OK hira suke sha sosai suna kallo.

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*www.Facebook.com/REALHAUSAFULANI WRITERS FORUM.com

55_56

       Hira suka sha sosai Sadiq da Khaleed, basu suka tashi ba saida suka fara jin kiran sallar magrib,    alwala suka dauro a tare suka fito domin tafiya masallaci, ko da suka iso parlour ba kowa Khaleed sai kalle-kalle yake ko zai ga fatuha, hakan yasa Sadiq ya masa nisa juyawar da Sadiq yayi yasa Khaleed daga kafa bayan an gabatar da sallah suka fito daga masallaci direct gida suka dawo, basu zame ko ina ba sai dining area Sadiq ne ya shiga saving nasu lafiyayan tuwan shinkafa miyar egushi taji kaji da naman rago kamshi sai tashi yake, turawa Khaleed na shi yayi sannan ya zuba na shi tare da zuba masu juice a cup’s, suna ci suna ta6a hira dan yau an hadu har basa gajiya da hira, bayan sun kamala suka dawo parlour da zama basu koma part din Sadiq ba wayar Sadiq dake aljihu ce ta shiga ruri hannu yasa cikin aljihu ya zaro ta sunnan da ya ganine manne a screen din ya sasa sakin smile, juyowa yayi ya kalli Khaleed ya ce, “gafa mutumin ka fa yake kira ni,” murmushi Khaleed yayi ya ce, “kamar yasan ina nan” daukar wayar yayi tare da karawa a kunne ta daya bangaran majid ya ce “Hello big man”
“Na’am.!
“kana gida?
“eh ina gida gani nan  tare da Khaleed,”
“eyya kace ma0sa ina gaishe shi”
“toh.!
“yauwa dama so nake ka raka ni wata dinner please,”
“dinner kuma? Sadiq ya maimai yana kwabe fuska  majid ya  ce, “ni dai ka rakani dan Allah nasan halin ka, yanzu ka fara min tsirfa”
“au tsirfa ma zan ma ko? toh ban zuwa,”
“haba kar muyi haka da kai mana please ka shirya kuma manya kaya zaka sa,”
“bazan saba zafi ya isheni”
“please kasa haba Sadiq nine fa”
“toh  naji.!  naji.! ya ce masa tare da katse wayar yana kallkn Khaleed ya  ce, “ka ji ni da majid wata kuma dinner zai kwashe ni muje taso muje mu shirye muje,”
“ni fa bana zuwa” harara Sadiq ya wurga ma Khaleed “lafiya.! Khaleed yace ya daure fuskar wasa “toh ai ji nayi ka ce baka zuwa”
“wallahi ko aiki na can na jira na shiyasa yanzu haka fa gudo ma aikin nayi”
“toh shikenan” part din Sadiq suka koma Sadiq ya shige bedroom tare da rage kayan jikin shi sannan ya shige toilet wanka ya sheqa ya fito daure da towel a jikin shi sai qaramin towel yana goge sumar shi lotion ya janyo ya shafa sannan ya bude wardrobe ya ciro dakakiyar shada shi brown tasha dinki da dark brown zare anmai irin dinkin nan na sarauta takalmin coffee colour yasa tuni ya fito yayi wani irin kyau, abinka da farar  fata  turare ya fesa mai kamshi da sanyin dadi tare da  manne agogwan shi silver sannan ya dawo parlour, khaleed dake saman two sitar  ya ce, “kai aboki na wannan sai kafi uban gayar kyau ai” smile Sadiq yayi ya ce “A hakan?
“eh mana”
“Cha6.!
“so kake yan’mata suyi rushing kenan dama har yanzu kaqi yima angel Mom,” smile Sadiq ya kuma yi ya ce “Nine Mom din jidda kuma nine daddy ta, so bata buqatar wata new Mom”
“haka dai kake cewa lokaci nanan zuwa da zaka watsar da  wannan tunanin haka, ni ko ina sis naka har yanzu ban qara sata a ido na ba? dago ido sadiq yayi yana nazari wace sis can kuma sai ya tuna qaqaro murmushi yayi ya ce, “wai me sister na ta tsare maka tunda kazo kake zancan ta”
“ah wallahi kawai yarinyar ta burge nine har na dan ji wani abu” kallon shi sadiq ya shiga yi kamar me neman wani abu a jikin shi can kuma sai yaja dan guntun saki ya  ce, “amma dai Khaleed wani abu ya shige ma kai ko? me za kayi da wa can yarinyar? yarinyar da ko 14 years bana tunanin ta kai, toh ka aure ta ka ji me? dariya Khaleed yayi  ya  ce, “wallahi aboki na baka kallon yarinyar nan wallahi irin sune idan suka ji kiwo kai kanka sai kayi mamakin abin da zaka gani”
“mtsss har ka fara samin headache wallahi” wayar sadiq da tayi rurice ta katse ma Khaleed zance daukar wayar yayi ta daya bangaran majid ya ce, “Gani nan cikin filin gida ka fito mu tafi” to yace masa tare da miqewa  Sadiq ya kalli Khaleed  ya  ce, “tashi mu tafi dan zumudin har yazo,” fita su kayi daga part din har sun kai bakin kofar fita sadiq ya ce “Ina zuwa”  parlour ya dawo tare da nufar dakin fatuha a hankali ya murda handle din kofar a zaune ya hango su fatuha saman daduma da alama yanzu suka idar da sallah, suna karatun AlQur’ani sallamar da yayi ne yasa fatuha aje Al Qur’anin tare da amsawa qarewa sadiq kallo fatuha tayi wani irin kyau ya mata kullun mai kyau qara kyau yake kauda idanuwan ta tayi, qarasowa dakin yayi jidda ta ruga ta fada jikinsa ta ce, “Daddy!
Na’am my angel.!
“daddy ina zaka? zan bika”
“angel ai yara basu zuwa” bata fuska jidda tayi tana shirin yin kuka tana dire-dire tana  cewa,  ni kam gaskiya daddy binka zanyi ban zama” langwabe kai sadiq yayi ya ce “Fatuha zo ki dauke ta” fatuha qarasowa tayi tana ma jidda murmushi ta ce, “yi hakuri kin ji jidda daddy nasan zuwa dake amma baya san dodo ya cinye ki  dodon yara yake ci” jidda ware idanuwa tayi tana kallon fatuha irin da gaske kike, sadiq ko wani irin dadi yaji yadda fatuha ke lalla6a jidda dan yasan idan ta kafa masa kuka har dinner fasa zuwa zai yi dan farin cikin jidda shine nashi, shafa kan jidda yayi ya ce, “kinji ko? ko mu tafin,” maqe qafa tayi ta fada jikin fatuha dariyar da ke san zuwa ma fatuha ta guntse shima haka Sadiq peck yama jidda sannan ya fice ya fito lokaci Khaleed da majid suna ta hira yana qarasowa majid ya aika masa harara tare da cewa “Tunda nace ka raka ni sai ka shanya ni mtss”
“oh haka nan zan bika banyi ma angel sallama ba ko? saima na fasa zuwa wallahi” hakuri majid ya bashi Khaleed dake gefe dariya yayi ya ce, “baku Gajiya da dirama wallahi har yanzu” murmushi su kayi tare da bude motocin su suka shige a tare da Khaleed suka bar unguwar.

    Sadiq na fita fatuha ta ja jidda toilet ta mata wanka itama tayi night dress suka sa tare da fitowa parlour, gidan yayi tsit ba alamar motsin mutane tsoro suka fara ji amma fatuha  daurewa take jidda kuka tasa mata ta ce  “Aunty”
“na’am jidda”
“Aunty ki zo muje part din daddy tsoro nake ji” shafa kanta fatuha tayi ta ce “Kiyi hakuri mu zauna anan” kuka jidda  ta fara rarewa fatuha hakan yasa fatuha daukar ta suka koma part din sadiq a parlour suka zauna fatuha ta kunna masu kayan kallo MBC 3 ta kai masu suka rashe suna kallon carton.

       suna isa wajan dinner  ke  da  wuya  kallo ya  koma  kan  su, wajen ya hadu   iyakar haduwa sun hadu duk wata mace dake wajan sai da ta yaba kyan su mata masu wayau a sace suka rinqa yaba kyan su marasa wayau ko har bin su sadiq suke, sadiq ko hade rai yayi kamar bai ta6a dariya  ba majid ko sai washe baki yake dama shi dan ina da yan’mata ne sunyi ciye-ciye da lashe-lashe majid sai da yayi kusan yan’mata biyar takaici ya hana sadiq magana  sai fuska da ya qara tsukewa kamar anmasa mutuwa, duk wadda ta zo tura kanta idan taga ba wasa a tare da sadiq sai ta ci birki ba su  suka bar wajan dinner ba sai 11:30pm lokaci sadiq har wajan ya fara hawa masa kai, ko da suka taho ba wanda yace ma wani qalla musanman majid ya san yana tankawa sadiq zai fara masa masifa dan yasan halinshi har harabar  gida majid ya saka hancin motar shi bala mai gadi sai daga masu hannu yake, tun kan majid ya ida parking sadiq yayi qoqarin fita dariya abin ya so ya ba majid amma baice komai ba yayi ribas ya fita yana shiga parlour ba kowa dama yayi tunanin haka saboda goma nayi jidda tayi nisan bacci bale kuma 11:30pm bedroom din fatuha ya bude a tunanin  shi suna ciki ganin ba kowa yayi tunanin suna part din shi haurawa yayi upstairs a hankali ya murda handle din kofar, TV ya iske nayi su tuni sunyi bacci, jidda ta dora kanta bisa cinyar fatuha, fatuha kuma ta jingina da kujera murmushi sadiq yayi tare da qarasawa ya kashe kayan kallon bedroom ya shige ya rage kayan jikinsa ya shige bathroom wanka ya sheqa ya fito sanye da bathrobe tsane jikin shi yayi da qaramin towel sannan ya zura night dress din shi parlour ya dawo har yanzu su fatuha bacci suke a hankali ya qaraso saman three sitar a hankali yasa hannu ya dau jidda bedroom ya kaita ya shinfideta parlour ya kuma dawowa, har yanzu fatuha bacci take a hankali sadiq ya kai hannu zai tashe ta sai kuma ya fasa gashin ta daya rufe mata fuska ya matsar tare da tsare  ta  da  ido yana qare mata kallo ya ga dai bacci take lumshe ido yayi tare da ware su, a hankali ya kai hannusa ya dauke ta aiko fatuha ta qara lafewa jikinsa tana sharar bacci yayi tunanin zai jita da nauyi amma sai yaji kamar ya dauki jidda a hankali ya sauke ta saman bed din shi ya ja masu blanket ita da jidda tare da qara masu gudun AC, sannan ya bude wardrobe ya ciro wani blanket din ya koma parlour ya kwanta saman three sitar ya dade kafin bacci ya dauke shi, zuwa can   bacci yayi awan gaba dashi.

   Yau su fatuha bacci har da munshari ansamu lafiyayan bed, duk da na dakin ta bana wasa bane amma duk haduwar shi bai kai na sadiq ba dan haka bacci tasha sosai ko da aka kira sallah asuba tana bacci, sadiq ne kadai ya tashi ya dauro alwala ya tafi masallaci, yana dawowa saman three sitar ya koma ya zauna tare da kunna kallo yana kallon new din safe cikin miqa fatuha ta tashi agogwa  dake manne jikin daki ta kalla kusan bakwai na safe ware ido tayi tana qoqarin tashi daga gadon da take, idanuwata ta ware sosai  tana bin dakin da kallo kwalla ta fara matsar wa tana fadin nashiga uku na lalace yau sangami zai kashe ni, wayo inna mu na bani qasan gadon ta zame tana rera kuka jira kawai take taji saukar aradu bayan ya gama kallon news din blanket din daya lullu6a da shi ya nade a hankali ya murda handle din kofar bedroom tsugunne ya hango fatuha bakin gado jin an bude kofa yasa fatuha zabura ta miqe, tana zarar ido yarfe hannu ta shiga yi dariya abin ya so bama sadiq daure fuska yayi ya bude wardrobe yasa  blanket din ciki, jikinfatuha ko sai rawa  yake  tana matsar kwalla tana yarfe hannu, ganin zai fita bai tanka mata ba ta ce , “tsakanina da Allah  ban san na shigo dakin nan ba Qur’an” ta fadi zancan tana matsar kwalla ta  cigaba  da  cewa, “wallahi iya kata parlour ban san ya na zo nan ba, dan girman Allah mai kyau kayi hakuri wallahi aljanune ke san jamin masifa,” sadiq da ya tsaya bakin kofa cak yana jin fatuha wata dariya ya gutse ya juyo fuska daure harara ya aika mata ya ce, “Kin ji na maki magana ne? kin min laifi kuma kin zo kina min kuka dukanki nayi  ko me? dama ai so kike ki kwata saman bed din saboda kina jin na zama sa’anki  toh kin kwanta kinji abinda nake ji ko, to saiki zo ki fita mtss” fatuha ko rantse-rantse ta shiga yi masa shiko yayi fuska kamar gaske ganin bai tanka mata ba yasa ta fita daga daki da gudu tana fita saman bed ya fada ya saki dariyar har mamakin tsoran fatuha yake ta iya rashin ji amma intaga an kamata yanzu ta fara kuka  gyara kwanciya yayi dama da kyar yayi bacci saboda bai saba bacci kujera ba.

Bangaran fatuha ko tana shiga daki ajiyar zuciya ta saki tare da shigewa toilet ta yi alwala.

    Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau  dadi gobe akasin haka, amma fadan da sukeyi da  sadiq ya ragu harkar shi  yake tayi nata, ta dage sosai jidda na koya mata karatun boko duk da itama din ba wani nisa tayi ba bangaran karatun ta na adini ba’a magana dan maida hankali take sosai, ga wani girma data qara dakyau yanzu haka su Jidda sun gama exam Aunty bilki sai matsama sadiq take ya  kawo jidda hutu tunda  su  Mom  basu  nan.

    Su Mom ko sun gama abin da ya kai su uk, amma Alhaji ya dage baza su dawo yanzu ba sai sun gama soyewar su sannan, aiko Mom bata masa gardama ba dan ita ba wanda take san faran ta ma rai kamar Alhaji.

     Sanye yake da blue shirt mai dogwan hannu, sai jeans sumar shi tasha gyara waya ce manne a kunnan shi da alama da Mom yake waya, sai shagwaba yake zuba mata sai da yazo  parlour sannan ya katse wayar tare da kwallawa fatuha kira, fatuha da yanzu ta fito daga wanka wata yar ficiciyar riga ta zura ta fito da gudu kallon ta yayi tare da kauda kai ya ce, “Kije ki hada ma jidda kayanta  a trolley” shagwabe fuska tayi tana kallon sadiq kamar zatayi kuka, kallon ta ya kuma yi sannan ya kauda kai yaga alamar idan ya biye mata ba inda zai kai jidda kuma shi gaskiya ba zasu tafi tare ba, idan suka tafi wazai gyara masa part din shi, bedroom fatuha shiga  sai da tayi kukan ta son ranta sannan ta cigaba da hada ma jidda kayan ta, jidda ko sai murna take zataje taga Jamal,  bayan ta gama hada mata kayan ta fito da trolley din  parlour sadiq na saman two sitar jidda na riqe da hannun fatuha daukar  trolley din yayi ya fida waje su fatuha na biye dashi a baya, cikin boot ya sa trolley din tare da kama hannu jidda, fatuha ko ji take kamar ta daura hannu a kai ta saki kuka idanuwan ta cike da kwalla taf, shigewa mota sukayi jidda sai daga mata hannu take har sai da motar su ta bar harabar gidan sannan ta shige gida da gudu ta fada saman three sitar ta saki kuka mai tsuma zuciya.

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com

57_58

Godiya ta musanman gare ku mosayan ❤ wannan novel ina jin dadi 💃🏼yadda kuke comments🤓 a kan wannan littafi hakan ya nuna min ana mugun tare 🤝🏽 wannan shafin naku ne.

      Sai da fatuha taci kuka ta gaji sannan ta tashi ta shige kitchen, ta bude fridge ta ciro fruit  ta wanke ta dawo parlour tana ci tana kallo har bacci barawo ya kwashe ta.

    A dai-dai bakin gate ya tsaya tare da yin horn shitu mai gadi ya taso ya bude masa gate, washe da baki ya shiga gaisheda sadiq, sannan sadiq ya sako hancin motar shi cikin gida Jamal dake filin gida yana ball ya saki murmushi ya biyo motar yana murna dai-dai ta parking din motar yayi a parking space tare da bude murfin motar tunkan ya budewa jidda motar, tayi sauri fitowa ta washe ma Jamal baki small dad Jamal yace tare da fadawa jikin sadiq murmushi Sadiq yayi tare da d’aga shi sama yana mashi wasa, dauke da shi ya shigo parlour tare da yin sallama Aunty bilki na saman three sitar zaune Hanan na saman one sitar cikin sallama sadiq yayi washe da baki Aunty bilki ta amsa tare wurga mai harara, sosa keya yayi tare da zama Hanan da ke, zaune a kujera ta gaisheshi a taqaice ya amsa mata tare da kallon Aunty bilki cikin wasa ta ce, dashi “Bari kallo na!, ta fadi tana qara aika masa harara dariya yayi ya ce, “Kai sister tunda na kawo ta ai sai ki huce”
“ban hucewa abinda sai da na dinga binka sannan ka kawo ta”
“to ayi min hakuri please” toh tace tana kwallawa baba larai kira ta kawowa sadiq kayan motsa baki dauke da tray ta fito cike da kayan motsa baki ta aje masa a gabansa tare da masa sannu da zuwa sannan ta juya ta koma bakin aikin ta, hira suka dinga zubawa shida  yar uwar shi suna cikin yin hirar Aliyu min jin Aunty bilki ya dawo shima zama yayi aka dasa sabuwar hira da shi, basu suka tashi ba saida suka fara jin kiran sallah magrib, alwala suka dauro sadiq da Aliyu  suka wuce masallaci Kasancewa Aunty bilki hutu take shiyasa ta cigaba da kallon ta.

     Sai da aka gabatar da sallah sannan suka dawo gida lokacin Aunty bilki ta shirya masu abinci a dining area, direct can suka wuce dining area Aunty bilki ta shiga saving nasu lafiyayan jallof  taji naman rago da kosulo cikin jin dadi suka cin abinci tare da taba hira bayan sun kamala cin abinci suka dawo parlour suna hira suna kallon news sai wajan karfe 10:00pm sadiq ya baro gidan Aunty bilki.

     Kiran sallah magrib ne ya tashe ta daga bacci bedroom ta shiga tare da shigewa toilet ta d’auro alwala ta gabatar da sallah bayan ta idar tayi zaune saman daduma tayi tsuru-tsuru wani irin tsoran gida take ji da wani fargaba, duk ji take gidan ya isheta tunanin rayuwar ta a kauye ita da fatsima ta shiga yi  har da yan hawayan ta ji take kamar ta rufe idanuwan ta ta ganta a kauyan wudil gabaki d’aya kewar su inna ta dame ta, jan jiki tayi ta hau saman bed bawai dan tana jin bacci ba blanket taja tayi lamo tana matsar kwalla.

      Bala mai gadi dake gyangyandi qara horn yasasa tashi firgigit wangale gate din yayi, yana washe baki qaraso da motar shi yayi dai-dai saitin bala mai gadi tare da zuge glass din window, murmushi yayi ya ce, “malam bala hala har ka fara bacci? murmushi bala mai gadi yayi ya ce, “Wallahi ko shi ke san dauke ni? saboda yar isakar da ake tana kadawa mai dadi sai kaji bacci na fizgar ka” murmushi Sadiq yayi tare da da ciro kudi idan yake ajewa acikin motar  yan’ dubu-dubu ko irgawa baiyi ba ya damkawa bala mai gadi tare jan motar, bala mai gadi jerawa sadiq Albarka ya shiga yi da fatan alheri sannan ya soke kudin shi aljihu yana yin parking ya kashe motar tare da jingi da kujerar motar ya lumshe idanuwan shi tare da ware su murfin motar ya bude, tare da samata key yana shigowa parlour haske ya kunna ya gwaraye parlour kallon parlour yayi ba kowa, kashe haskan yayi  a hankali ya qarasa bakin kofar dakin fatuha har zai murda handle din kofar sai ya fasa tare da ja baya ya wuce part din shi, fatuha ko duk wani motsi da sadiq yake a kunnanta take jin shin  lamo tayi kamar mai bacci haka ta dinga zare ido har bacci ya kwashe ta.

      Yana shiga bedroom toilet ya shige ya sheqa wanka ya fito, tsane jikin shi kawai yayi tare da zura kayan bacci yabi lafiyar bed ya kwanta.

     Kiran sallah ne ya tashi fatuha toilet ta shiga tare da yin wanka  tare da dauro alwala daure da towel tafito  Dan karamin towel na hannunta tana tsane jikin ta dashi,   shafe jikin tayi da lotion tana gamawa tabude wardrobe ta  ta janyo wasu riga da sket masu stone’s a jiki masu kyau   tana gama sasu ta dauko aftar dress ta aza bisa domin  gabatar da sallah tana idarwa ta koma  saman bed ta kwanta bacci ya qara kwasheta, ba ita ta tashi ba sai karfe bakwai kallon agogwan dake manne jikin daki tayi tare da yin miqa toilet ta shiga tayi brush ta fito tare da sharce sumarta ta kwanta a gadon bayan ta a hankali ta bude kofar daki ta zuro kai ta laleqa taga ba kowa fitowa tayi ta nufi dining area tana qaraso wa taga sadiq zaune cikin shirin shi na unform yasha kyau har ya gaji dago eye’s ball’s din yayi su kayi ido hudu da  fatu, kauda kai yayi ya cigaba da breakfast gaisheshi tayi ya amsa a taqaice qoqarin barin gun take har ta juya yace “Fatuha.! waigowa tayi hakan yasa iska ta hura gashin kan ta har ya shifi fuskar sadiq lumshe ido yayi tare da ware su a kanta itama din shi take kallo kauda kai yayi ya ce “Ki dawo kici abincin ki” washe baki tayi tare da jan kujera ta zauna saving din kanta tayi tare da janyo plate din gaban ta Sadiq kallon ta yake ta qasan ido hannun hagunta tasa ta gyara gashinta da iska ke yawo da shi ta zura hannun ta, cikin plate ta fara cin abincin, chips ne da farfesun kifi wani irin dadi ya mata sai kada kai take tana ci sadiq mamaki qazantar fatuha yake, cin abinci da hannu ko wankesu batayi ba kallon ta yake sosai dagowar da zatayi da kanta ta  kai wata lomar sukayi 4 eye’s murmushin karfin hali ta masa tana qoqarin boye hannu ta dan kwata-kwata ta manta yana wajan kauda kai yayi tare da daukar briefcase din shi kallon shi fatuha take tayi rau-rau da ido ko kallon ta baiyi ba yasa kai ya fice, ture plate din tayi take nan taji abincin ya gundire ta, kwashe kwanikan tayi ta kai kitchen a nan ta ci karo da rabi’a na aiki gaisheta tayi ta amsa cikin fara’a taya ta aiki fatuha ta shiga yi tun tana  hana ta har ta kyale ta, kusan tare sukayi komai na launch sannan suka jera a dining area bayan sun kamala fatuha ta shiga rokar rabi’a kar tatafi ta barta ita kad’ai aiko taci sa’a rabi’a ta tsaya taji dadin hakan sosai, dan haka ta wuce part din sadiq ta gyara shi tas ta dawo parlour suka cigaba da hira da rabi’a ko da aka kira sallah azahar  tare sukayi sannan su kaci abinci, sai kusan qarfe hudu rabi’a tayima fatuha sallama, fatuha bata ji dadi ba amma hakanan ta hakura ta zauna kiran sallah la’asar ne ya sata shiga bedroom ta shiga toilet tayi wanka tare da alwala saboda yau tasha aiki ba laifi wata hadadiyar riga da isket ta kuma sawa, hijabinta ta zura tayi sallah bayan ta gabatar da sallah ta cire hijabin ta dawo parlour, jin zaman parlour ya isheta ta yasa ta fita farfajiyar gida su ola da Sunday ne da sauran yaran sadiq suketa shawagi a gidan resting chair ta samu ta zauna tare da jingina da kanta ta lumshe ido wani iska ke kadawa mai dadi da sanyi, Sunday ne ya zuguro Emeka dake ta kallon fatuha har yana lashe baki ya  ce, “hey Emeka stop looking at her, mind ur business this girl past ur level  na Oga consin sister be that”
“I don’t now fa amma this girl na beautiful”
“Oh u no go stop looking at her I will tell  Oga”
“sorry Sunday haba kar muyi haka da kai”  Emeka ya fadi cikin hausar sa mara dadi Sunday ya  ce, “leave me alone” Sunday ya fada
“sorry lemme leave the place ma” Emeka tabirim bala mai gadi ya koma duk abun nan da sukeyi fatuha bata sani ba.

      Yau yasha aiki sosai wajan a office sai kusan yama likis sadiq ya nufo gida, yana zuwa bakin gate horn yayi bala mai gadi ya wangale masa gate ya kunno hanci motar shi, hango fatuha yayi harabar gidan  saman resting chair gashin ta ya bage kusan rabin qirjin ta duk waje suke domin riga da isket ne ajinta sun  dan matse ta sosai  dakyar take numfashi,  Emeka da ke gefan bala mai gadi sai kallon ta yake, yaransa sadiq yake  bi  da  kallo  wayanda  ke  harabar  gidan  kusan  rabin su  hankalinsu  na  kan  fatu,  take  farin  cikinsa  ya  d’auke lumshe ido sadiq yayi tare  da  ware  su yana ji wani  abu  mai  zafi  yana  masa  yawa mota ya  ja da karfi dai-dai parking space yayi parking ko dai-daita parking  baiyi ba ya fito cikin zafin rai fatuha dake kishingide ya nufa cikin zafi rai ya daka mata tsawa da  cewa, “me kike  a  waje  mai  ya  fito  dake? sadiq  ya  rintse  ido  yana  ta  masifa ganin  fatu  ta  tsare  shi  da ido  duk  ta  rud’e  sam  ta  kasa  gane  masifar  me  yake  mata mara  dalili  cike  da  masifa  sadiq  ya fisgota ba  shiri  tayi  masauki  bisa fafadar kirjinsa tana  sauke  numfashi  cike  da  tsoro  yanayin  sadiq  matse  mata  hannu  yayi sai  huci  yake   kamar  zai  hadiyi  zuciya  ya  mutu  saboda  masifa, ware ido tayi tare da saka masa kuka saboda  masifar  da  sadiq  yake  yayi  yawa janta  ya shigayi tana  rike  hannusa  tana  kuka  tana  cewa,  “mai  nayi  kuma  mai  kyau  Allah  banyi  komai  ba” ya cigaba da janta  cikin  zafin  rai  sai da ya zo parlour  yayi wurgi  da  ita saman kujera har sai da kanta ya bigi kujera kuka ta qara saki tana kallon sadiq dan bata san laifin data masa ba,  shima  d’in numfashi  yake  saukewa  cike  da  6acin rai cije  lips  yayi  yana  jin  wani  suya  a zuciyarsa  mara dalili, kallon ta yake ido cikin ido matsowa yayi daf da ita har tana jin saukar numfashinsa idanusa sun  kad’a  sunyi  jawur  rintse  ido  fatu  tayi  tana  kuka  mara  sauti hannu  yasa  ya matse mata fuska cikin daka tsawa yace “Uban waye yace ki fita waje haka? ya fadi a tsawa ce har cikin kanta sai da taji tsawar da sadiq ya mata runtse ido tayi tana girgiza kai tana kuka sakin fuskar yayi ya ja gashin kanta har saida ta saki qara tare da rushewa da wani sabon kuka cikin  daka  tsawa  sadiq ya  ce, “idan na qara ganin ki kin fita farfajiyar gidan nan baki sa hijabi ba sai na kona gashinan” ya ida zancan tare da matse mata fuska da karfi kuka ta kuma saki tana kallon sadiq wani irin tsanar shi na fizgar ta, lumshe ido tayi tana jin zafi da radadin, wani wawan tsaki sadiq ya ja tare da tura ta  ta bige da kujera sannan ya dau briefcase din shi ya haura sama da  sauri tamkar  zai  tashi  sama, kuka ta saki  mai ban tausayi.

     Yana shiga parlour shi ya wurgar da briefcase din shi ya zauna bisa kujera tare da lumshe ido, yana  sauke  ajiyar  zuciya wata zuciyar ta ce masa “Kai sadiq ina ruwan ka da harkata? idan ma tsirara zata dinga yawo me ruwan ka? runtse ido ya kuma yi” wata zuciyar tace masa “Ko dan saboda tarbiyar diyar ka ka taka mata birki? saboda duk abinda tayi shi jidda zata kwaikwaya?” duk wannan zancan a zuci yake kiran sallah magrib ne ya tasheshi bedroom ya shige ya rage kayan jikin shi agurguje yayi wanka, yana fitowa ko mai bai shafa ba ya zura jallabiya a hankali yake sauko wa daga upstairs, inda ya bar fatuha har yanzu nan take tana kuka jin alamar tafiya ya sata dago jajayan idanuwanta  ta kalli sadiq, sadiq ma kallon ta yayi  tare da aika mata harara ya ja  tsaki mtss ya fice, kuka ta kuma saki sannan ta ja jiki ta shige daki tana alwala tana kuka har ta gama, haka tafito ta zura abaya tana idar da sallah ta cigaba da lazumi   har sai da aka kira isha’i ta tashi tayi sannan ta ja jiki ta koma bed ta cigaba da raira kukanta kanta har ciwo yake mata amma dan jaraba takasa daina kukan.

  bashi ya dawo gida ba sai bayan sallah isha’i, yana shigowa parlour dining area ya wuce yana b’ude kulolin yaga alamar fatuha bata ci abinci ba dogon tsaki yaja tare da rufe kulolin, Kwala mata kira yashiga yi shiru ba’a amsa ba dan haka cikin nutsuwa ya nufi dakin fatuha ya murda handle din kofar can saman gado ya hango fatuha cikin cool voice din shi ya ce mata ” Yanzu dan iskanci
kina jina  kikayi   banza dani? tayi shiru bata tanka masa ba, rashin yayi mugun bacci dan haka ya daka mata wani uban  tsawa  wadda ta sata zabura ta sauko daga bed tare da fashewa da wani sabon  kuka😭, harara ya aika mata ya mata nuni da ta biyoshi, bin shi take har tana sarke kafa dining area ya isa itama taja ta tsaya ya  ce, “oya wuce kici abinci” a takaice tace masa ta koshi, wata tsawa ya kuma daka mata jiki na bari tana kuka ta fara zuba abincin dan kadan ta zuba, wani irin kallo sadiq ya wurga mata tare da yin magana cikin daure fuska “Haka kike zuba abinci eeeh?”  kuka tasa tana  mamakin  yarda  sadiq  ya  karanci  cin  abincin ta tare da cigaba da zuba abincin har ya kai bakin plate din, tana qoqarin qara zuba wani sadiq ya matse hannunta da karfi har sai da ta saki qara, saboda ya lura bata da niyar daina zuba abincin kuka ta  saki  tare  da  zaman  dole, juya abincin ta shigayi ta qasaci  sai kuka, cikin  murya mai sauti sadiq ya ce “Ko kiyi ma matune shuru! ko nasa alburushi  na bula maki kai kowama ya huta, kuma abincin karki ci ki bari na tashi tsaye Allah danne ki zanyi na dura maki har da plate din” cikin hawaye fatuha tashiga dura abinci har tana jin kamar zatayi amai amma sai da ta cinye shi tana gama ci tayi qoqari tashi cikin sauri sadiq dake saman kujera dining area ya lumshe ido kamar me jin bacci, har tayi nisa ya ce “Fatuha..! juyowa tayi tana kallon shi hawaya da ke maqale a idanuwan ta suka gangaro bisa kumatunta tayi  kala  tausayi  baby face  nata  yayi  jawur, wani irin yerr sadiq yaji ajikinsa   kallon  ta yashiga yi kamar yau yafara ganinta har wani  langwa6e kai  yake  yana  kankance  ida yakara Kiran ta akaro nabiyu   “Fatuha..! gaban tane ya yanke ya fadi kuka ta kuma saki tare da dawowa ta durqusa gaban shi tana rera wani saban kukan, a hankali sadiq ya kai lallausan hannun shi ya cigaba da gogema fatuha hawayan ta, lumshe ido tayi tare da ware su kan  sadiq dake  kallonta, yana gama goge mata hawayan  ya mata alama da  ta tafi har tayi gaba ya ruqo hannun ta  juyowa tayi da sauri idanu  ta  waje  tana  sauke  numfashi  da  sauri  da  sauri domin ita yanzu yafara bata tsoro,  langabar da kai yayi ya ce,    “Fatuha please kukan ya isa  haka”  kallon shi take shima din haka,     wasu sabin hawayan ne suka qara zubowa wani irin kallo sadiq ke bin ta dashi ya koma abin tausayi kamar bashi ba  hakan yasa fatuha hadiye wasu hawayen, smile yayi tare da sakin ta cikin sauri ta shige daki tare da fada wa saman  bed.
shima sadiq upstairs ya haura cike da farinciki dashi kansa mamakin haka yake….. Hmmm kayi bayani Sadiq😘.

Written by
salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★we are the beat★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*_Email_* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                   59_60

       Tun ranar da fatuha tasha maqara ta shiga wasan 6uya da sadiq, kwata-kwata bata bari su had’u dan ta lura aljanu gare shi, lol ko gyaran part nashi za tayi sai ta bari ya tafi office haka shima bangaran sadiq bai wani damu da rashin ganin na ta ba, saboda yasan lafiyar ta lau of cos yana ganin part nashi fes.

      Fatuha da rabi’a sun wani qara shaquwa musanman yanzu rabi’a bata tafiya gida sai 4, shiyasa fatuha ke dan jin dad’in gidan ita dai burin ta bai wuce ace su Mom sun dawo ba ko Jidda dan ta gaji da zaman kad’aici, ku san tare suke aikin ma yanzu dan fatuha yanzu ta fara gogewa da girke-girke dan yanzu kusan abinci gidan ita ke yin shi duk da rabi’a na hana ta.

      Misalin karfe goma na dare ya shigo gidan tsit ba motsin kowa, idan da sabo ya saba dama shi mutun ne ba mai son hayaniya ba part nashi ya wuce  tare da shigewa bathroom ya sheqa wanka, yana  fitowa ko mai bai shafa ba ya zura jallabiya white ba qaramin kyau ta masa ba, fitowa yayi daga part din na shi ya wuce main parlour direct dining area ya wuce abinci ya zuba dan kad’an shinkafa da miya ce tasha kayan had’i loma biyu zuwa uku yayi ya ture plate din dan kwata-kwata baya jin dad’in jikinsa gabaki daya, yayi missing din jidda bama ya ganewa yayi missing nata sai ya je bacci  zai ji bed din wayam sai dai yayata juyi har ya samu bacci ya dauke shi, gashi baya so ya je gidan Aunty bilki yasan yana zuwa zata ce Jidda ta kawo shi shiyasa yake hakura.
bangaran su Mom ko duk san da ya tanbayi ranar dawowar su sai Mom ta ce sai sun gama abinda suke.

         Jiki ba kwari ya koma part din shi,  wata irin fever yake ji sama-sama ga qirjin shi na masa zafi, magani ya cura daga bedside drawer  ya sha sannan ya kwata ta tare da rufe jikin shi da blanket.

         Asuba ta gari fatuha na tashi ta tsala wanka tare da gabatar da sallah, sannan ta koma bacci cike da kewar su inna, dan gabaki d’aya yanzu kauye take so ta koma, zama gidan yanzu ya fara hawar mata kai abu d’aya ke mata dadi yanzu shine idan malam ya zo koya mata karatu shima da sun gama ya tafi zata shigo gida kamar maya, gaskiya ta gaji da irin wannan rayuwar gashi kwanan ta lura mai kyau ko abinci baya ci, anya yana gidan ma kuwa ba ita kad’ai suka bari ba sannan ta ja dan guntun tsaki tare da gyara kwaciyar ta.

      Ba ita ta tashi ba sai kusan karfe 10:30 brush kawai tayi tare da gyara gashin kanta ya kwanta har gadon baya, sannan ta fito parlour sanye da gwon black mai kyau masha Allah fatuha tayi kyau ga wani haske da ta qara, gashi kullun yan matan ci bayana yake a jikinta.
Jin bata ji kamshi bane yasa gaban ta ya fadi leqawa kitchen tayi taga wayam ba rabi’a ba alama dan bata rai tayi ta dawo parlour tare da wucewa dining area, bude kulolin jiya ta fara yi jiya ma kusan ita kadai ta ci abincin dan guntun tsaki ta kuma ja tare da kwashe kayan ta wuce kitchen, gyara kitchen d’in ta shiga yi sai da kitchen din ya fita tas sannan ta d’aura ruwan zafi kan wuta ta fita sai da ta gama gyara ko ina sannan ta dawo kitchen, ta juye ruwan zafin cikin flacks  sannan ta soya kwai ta juye a plate ta rufe yan ciki ta fido a fridge suma ta wanke ta gyara ta d’aura a tukunya tare da gyara kayan miya ta zuba da k’yan kamshi tuni kitchen din ya gwaraye da k’amshi dad’i,  parlour ta fito tare da haurawa up stair’s a hankali ta murda handle din kofar part din sadiq wani irin sanyi da kamshi dadi suka doki hanci ta, lumshe ido tayi tare da ware su tana qarewa parlour kallo tsit parlour ba kowa, hakan ya tabatar mata da mai kyau ya tafi wajan aiki kofar bedroom ta nufa tare da bude ta a hankali  ta shiga dakin kamar yarda ta saba, sanyi AC ne kawai ke tashi sai kamshi kayan d’akin ta fara tatarewa duk da d’akin ba wani dati yayi ba blanket ta jawo zata linke sai taji anja, ware ido tayi waje tare da fara jin tsoro ko lafiya qara jan blanket din tayi taji anja dawowa tayi gaban bed din tayi tsaya a hankali ta kai hannu duk da zuciyar na dukan uku uku saboda tasan yau tuesday sadiq na zuwa office kuma baya kaiwa wannan lokacin bai fita ba, a hankali ta sa hannu ta fara yaye blanket din dai-dai fuskar sadiq taja ta tsaya Chak, saboda ba abinda sadiq yake sai rawar dari, a rude fatuha ta ce “Mai kyau me ya same ka? ta fadi bakin ta na rawa inbada rawar dari ba abinda ya ke sai hawayan fever dake bimasa fuska dan ko magana bai iyawa sai ma rintsa ido da yayi yana qoqari jawo blanket ya rufe jikin shi, riqe blanket din fatuha tayi tana  kallonsa  cike  da  tausayinsa har da yan  hawayanta tana  cewa, “mai kyau dan Allah me ke damu ka? hannuta  na  rawa  ta  kai hannuta tata6a goshin shin wani irin zafi taji rau take nan ta hau reramai kuka duk fever da ke jikin sadiq sai da fatuha ta dan bashi dariya, da  tausayi  ganin  yarda  take  damuwa  da  shi  sosai  duk da basa  wani  shan  inuwa  d’aya, yadda  ta rude sai ka ce yau ta fara ganin ana fever amma sai ya guntse dariyar tare da qara lumshe ido dan bai san ganin wannan kukan ko mutuwa yayi ai sai haka fita tayi daga d’aki ganin zaman bai fishe ta, tana zuwa bakin k’ofar fita suka ci qaro da ola shima zai shigo ya ji ko lafiya Oga bai fito ba, ganin fatuha na kuka yasa shi tsayawa tanbayar ta lafiya kora masa bayani kawai tayi sannan, shima ya haura sama part din sadiq wayar shi dake aljihu ya ciro ya kira doctor yakub sannan ya zauna saman sofa fatuha kuma na zaune kusa da sadiq tasa ruwan a ruba da towel tana dadana masa akai saboda jikin nashi ba qaramin zafi yayi ba cikin 15 minutes doctor ya qaraso gaishe shi fatuha tayi tare da matsa masa ya zauna, shi kuma ola ya fice, duba sadiq ya shiga yi  yan rubuce-rubuce yayi tare da gwada Bp din shi ya hau sosai kallon sa doctor yakub yayi tare da gwada kai ya curo allura zai  masa fatuha dake gefe sai ka ce  ita za ayima wa ritse ido tayi  tana  ji  tamkar  ita  doctor  zai  ma  allura dan ba abinda ta tsana kamar allura, bayan ya kamala duk abinda yake Dr yakub ya juyo cikin fara’a ya ce, “insha Allah anjima zai tashi kuma insha Allah fever zata sauka karki  damu anjima zanzo” fido magunguna doctor  yayi ya  ce, “dan Allah idan ya tashi ya samu yaci abinci dan babu alamar ya ci abinci, idan zan dawo zan dawo da ledar ruwa” to fatuha ta ce masa tare da masa godiya ta rakoshi har bakin kofa ta koma ciki, Ko da ta koma ciki, kitchen ta shige ta qarawa farfesunta dake wuta ruwa sannan ta koma part din Sadiq leqa fuskar  shi tayi ganin yana bacci yasata sakin ajiyar azuciya tare da ta6a goshinsa ta  ce, “Alhamdulillah zazza6in ya sauka” sannan ta rage gudun AC d’aki ta fara gyara part din.Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com-Real-Hausa-fulani-writers-forumRHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*_Email_*
realhausafulaniwritersforum@gmail. com

*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

61_62

       Sai da ta gama gyara part din tsaf sannan ta koma kitchen, lokacin har farfesun yayi ta juye a kula tare da plate ta zuba a  tray da bread a hankali take taka upstairs saboda ta cika tray din da kayan abinci, bakin kofa ta aje tray din sannan ta bude kofar ta shiga har cikin bedroom ta aje a stool qara leka fuskar sadiq tayi a qaro na biyu murmushi ta saki tare da zama gefan shi tana kallon yadda sajansa ya kwanta luf har mamakin kyau irin na sadiq take, sai dai yayi yar rama sannna fuskarsa tayi fayau dariya tayi ta ce “Ohni sangami ciwo yayi kamu kayi bulun buqwi tunda likita ya tsulama allura kaji zafi sai bacci kake, qila ma suma kayi saboda  zafi, kai  ma ka  ji  yarda naji  ranan yadda kayi bacci kamar ba masifafe ba, amma da ka warke zaka fara cika mana gida da tsuwa, na huta da masifar ka ko ta kwana biyu ce uhm bari na lalla6a naje nayi wanka a toilet din ka tunda kai ka zama gawar shanu dan tashin ka ba yanzu.

       Tashi fatuha tayi ta bude wardrobe ta ciro qaramin towel ta rage kayan jikinta tasa towel, duk wannan abun da fatuha ke duk a kunnan sadiq dan ya dade da tashi kawai dai yayi lamo ne, toilet din ta shige ta sheqa wanka ta fito ko da fito cikin sanda take tafiyar har ta qaraso gefe bed leqa fuskar sadiq tayi tana riqe da qaramin towel tana goge gashin kanta ta  ce, Allah sarki ba wan Allah sai bacci kake baka san wainar dana ke toyawa ba wai da zaka tashi dana sha masifa, yarfe gashin kanta tayi wanda hakan yasa ruwan gashin ya watso ma sadiq a fuska dan motsa ido yayi hakan yasa fatuha zaro ido tare da yin lamo tana zare ido tana yarfe hannu ganin ya juya ya gyara kwaciyar shi ya sata sakin a jiyar zuciya, baki dressing mirror din shi ta tsaya tana kallon mayukan dake baje akan dressing mirror  tsuru-tsuru tayi tana tunanin man da zata shafa can ta kai hannu kan wani mai na gashi kasancewa fatuha ba boko yasa ta d’auka ta fara shafawa sadiq dake kallon ta ta qasan ido sai dariya yake guntsewa, in taqaice maku duk wani mai dake saman dressing mirror sai fatu ta shafa dan taji ya mai kyau ya ke ji sannan ta fita daga d’akin, tana zuwa bedroom dinta kaya tasa sadiq dake d’aki dariya yayi sosai har da riqe ciki dan guntun saki ya ja tare da cewa “Yar kauye kawai..! Sannan ya tashi a hankali duk da har yanzu baya jin karfin jikinsa wanka yayi sannan ya fito yasa jallabiya ash mai kyau sannan ya gabatar da sallolin shi, yana idarwa  ya qara koma wa ya kwanta dan karfin hali kawai yake.

    Sket da riga tasa na atamfa mai ratsin dark green da coffee brown sai gyara gashin kanta da tayi tare da yin  ture ka ga tsiya dauri, sannan ta qara fesa turare rufe bedroom din tayi ta fito sannan ta haura upstairs direct bedroom din sadiq ta shige kwance ta gan shi amma sai dai wannan lokacin idanuwan shi biyu murmushi ta saki tare da qaraso wajan shi cikin sanyin murya ta ce “Mai kyau ya jiki?” lumshe ido yayi tare da ware su kan fatuha jim yayi yana qare mata kallo ba qaramin kyau tamasa ba musanman dan qaramin lips din ta pick kauda kai yayi tare da cewa, “da sauki.! ya lumshe ido smile ta kuma yi tare da jawo tray dake saman stool ta cigaba da saving nashi cikin nutsuwa kasancewa tasan bai cin abinci bane sosai, shiyasa ta zuba masa farfesun yan cikin kad’an ciki dan boll,

    Cikin sanyi murya ta kuma cewa “Mai kyau.! ware sexy eye’s ball’s din yayi ya qara sauke su kan lips din ta cikin shagwaba da sanyi murya ta ce, “Mai kyau dan Allah ka ci farfesun  nan ka ga likita yace ka ci abinci”   hade rai sadiq yayi tare da lumshe ido tare da yin magana cikin cool voice nashi ya ce “Bana jin yunwa fatuha” dan bata rai tayi tare da rausaya kai ta ce “Dan Allah kaga ko akauye idan bani lafiya idan banci abinci ba inna har dure take min, dan na samu lafiya ka ga yanzu Mom bata nan bale ama dure, dan Allah ka ci” ta ida zancan tana rausaya kai tana kallon sadiq dake kallon ta kamar qaramin yaro qara hade rai yayi ya ce “ba fa naci leave me alone pls” zaro ido fatuha tayi ta ce “Kai kasan wannan”  murmushi yayi wadda bai yi niya ba ya ce “Fatuha wai yaushe zaki waye?” dariya tayi ta ce “Sai ranar dana fara zuwa boko ka ga da jidda nan ita ke koyamin yanzu kuma tana gidan Aunty bilki” ta ida zancan tare da yin raurau da ido sadiq  ya  ce, “ai ta kusa dawowa kin ji, uhm to kina san karantun ne? bai ida rufe bakin shi ba Dr yakub ya shigo, cikin sallama tare wurgawa sadiq harara dake kwance gaisheshi fatuha tayi har qasa sannan ta dau boll din farfesun ta aje a tray tana qoqarin fita doctor  yakub ya  ce, “ah wai fita zakiyi da kin tsaya ai” murmushi fatuha tayi ta ce “Ina da abinyi ne a kitchen shiyasa”
“ok.! wannan abincin fa nawaye? kallon sadiq tayi dake ta faman aika mata harara tayi tsaye tare da sada kanta qasa, juyowa Dr yakub yayi su kayi ido hudu da sadiq “mtww haba captain me yasa kake haka ne please, wai bana sha fada ma ba ka rage damuwa ba uhm saboda tsabar damuwa  ka daurawa kanka hawan jini, me yasa kake abune kamar mara tawakali ai kowa ya sani duk me rai mamaci ne tunda kausar ta bar duniya ka daina walwala ka maida zuwa asibiti kamar zuwa kasuwa, haba captain ko dan lafiyar ka da matsayin ka ka hakura da wannan tunanin please,” lumshe ido sadiq yayi kamar yakub na magana da dutse tsaki Dr yakub yaja ya ce “To wannan abincin da kaqi ci  me hakan ke nufi?” ware ido yayi yana aika ma fatuha harara dan shi kwata-kwata baya buqatar wani abinci a cikin shi amma saboda tsabar naci irin na fatuha yanzu tasa sai ya ci abinci dan guntun tsaki yaja yana kallon yakub dake ta masifa yanzu “ka daure ka ci abinci ko nama alura ai dai ba saina fadama ila da alura kema mutun ba idan ba abinci ba” duk yadda ya so ya kauce ma qincin abinci sai da yakub ya takura masa ya sha farfesun kad’an  ba tare da bread ba ba laifi farfesun ya masa dadi duk da bakinsa ba test aje boll din yayi fatuha ta dau tray din ta fita alura Dr yakub ya masa tare da daura masa ledar ruwa saboda ya lura sadiq baya san cin abinci yana lafiyar ma yaci kadan bale yanzu.

     Dawowar fatuha ce tasa Dr miqewa ya ce “To ni zan wuce dan Allah ki kulla da cin abincin shi idan bai ci ba ki kira Aunty bilki ki fada mata ai yasan halin ta”  d’aga kai fatuha tayi sannan ta taimakamasa da daukar masa  briefcase din har sai da suka zo bakin kofa ta masa sallama ta rufe gidan bedroom din sadiq ta kuma.
Tana dawowa harara ya bita da shi sannan ya ja saki murguda masa baki itama tayi tare da zama saman sofa sanin  ba  zai  iya  tashi ba  yasa  fatu  haha sadiq  ya  ce, “keee wakike murgudawa baki? raurau da ido fatuha tayi ta ce “Bada kai nake ba”
“Dawa kike to? ya fada cikin sigar masifa “uhm ba da kai nake ba wallahi”
“mtww wallahi karki bari na tashi dan na tashi saina karairayaki, bama na hana ki yawo ba hijabi ba eh?
“amma ai a waje ka ce ba’a gida ba,”  tsaki ya  ja, mtww  sannan ya juya ya lumshe ido.Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best★

http/Mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=,H-R

*_Email_* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*_Facebook_*www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                   63_64

Juya bayan da sadiq yayi yasa fatuha jan dan guntun tsaki tare da kallon agogan dake maqale a bango kusan karfe 8:30 na dare, tashi tayi ta bar part din ta koma part din su tana shiga bedroom ta rage kayan jiki ta, ta  shiga toilet ta sheqa wanka ta fito daure da towel ko shafa mai ba tayi ba, ta bude wardrobe ta ciro kayan baccin ta riga da wando pink masu mayan flowers da zanan ya’yan cartoon, d’aure gashi kanta tayi da wata yar kibiya ta d’aure kai sannan ta fesa turara har zata kwanta sadiq ya fado mata a rai ta barshi a d’aki shi kad’ai, gashi baya da lafiya tashi tayi zubur zata fita sai kuma taci birki ta ce “Ko naje tijara zai mun dan ba mutunci gare shi ba, karma ya tsinka ni.! wata zuciyar tace haba fatuha duk rashin mutuncin mutu bai da lafiya ai dole ya shafa wa mutane lafiya riqe handle din kofar tayi kamar me na zari can kuma ta bude ta wuce part din sadiq  ta shiga dakin har yanzu bacci yake parlour ta dawo ta kuna kallo dan ba wani bacci take ji ba  cikin jin dadi take kallon arewa24 suna shirin tarkon kauna  gaba ki d’aya film din ya mata d’adi sosai sai da aka kamala film din misalin karfe 10:00 na dare sannan ta leqa dakin sadiq, bakin bed din ta tsaya tana qaremasa kallo a hankali ta kai hannu zata taba goshinsa amma ta kasa dunqule hannu tayi tana nazarin jikin nasa ganin ya motsa ya sata gyara tsayuwa tana kallon yanayinsa lumshe ido tayi a hankali ta kai hannu tata6a goshin sadiq ji tayi zafi rau kamar garwashi mamaki ne ya kamata da tsoro cikin rawar murya ta ce “Mai kyau?” shuru sadiq yayi saboda shi kad’ai yasan yadda yake jin fever na damu shi kneeldown fatuha tayi gaba gadon ta qara cewa, “mai kyau.! a qaro na biyu, bude sexy eye’s ball’s dinsa yayi a hankali yana kallon fatuha data fara matsar kwalla smile yayi ya ce cikin cool voice nashi “Menene fatuha? kin kasa bacci ne?” girgiza kai tayi alamar a’a “to menene? kallonsa fatuha ta kumayi ta ce “har  yanzu masasaran nan bata  sauka  ba  duk  da  likita  ya  duba  ka  tana matsama baka ji jikin ka da zafi ba? da a kauye ne da inna ta dafa ma magunguna kuma da kasha zaka warke, amma nan likita sai duba ka yake amma ka qi warkewa mai kyau, dan Allah ka daina tunani kaji shiyasa kaqi warkewa” ta fadi zancan tana zubar  da  hawaye kallon ta sadiq kawai yake yana mamaki irin tausayi na fatuha gabaki d’aya tabi ta rude tunda taga bai da lafiya lumshe ido yayi tare da warewa ya sauke so a kanta ya  ce, “insha Allah fatuha zan daina kinji” murmushi ta saki mai hade da kuka-kuka ta tashi ta shiga toilet din sadiq shi kuma ya bita da kallo ruwa ta d’ebo a babba boll na  roba tasa towel a ciki ta dawo d’akin har yanzu idanuwan sadiq na kan fatuha ko qif tawa bayayi, sai da ta qaraso gaban shi ya lumshe ido aje boll din tayi a gefen bedside drawer idanuwanta  taf  da  hawaye cikin nutsuwa ta shiga matse towel din a hankali ta nufo towel din goshin sadiq ta fara dadanna masa kamar yadda inna ke mata idan tana masasara,  ko ina na jikinsa take  bi inda ke bude tana danna masa towel din a hankali fever ta fara sauka shi kanshi Sadiq yaji dadin jikinsa sai dai dan dumin da jikin yayi bacci ne ya fara fisgar shi kafin ka ce me bacci ya kwashe shi, sai fatuha dake ta faman dannamasa towel.
A hankali ta fara gyangyadi dan ta fara jin bacci, sai bacci ya fisgeta sai firgigit ta tashi ta cigaba sai da bacci yaci karfin ta, ta fada fadadan qirjin sadiq bacci ya kwashe ta.

         Kiran sallah asuba ne ya tashi sadiq a hankali yake bude sexy eye’s ball’s din shi ya sauke su kan fatuha da ke bacci male-male a qirjinsa gashin kanta ya baje saman qirjinsa ta  kankame sa, matsar da gashin kanta yayi gefe yana qarema fuskar ta kallo, har mamaki wayau irin na fatuha yake gata qarama amma sai dai tana da halin manya, kasa  dauke  idanusa  yayi  kanta, yunqurin tashi yayi yaji ta motsa komawa yayi ya lumshe ido yayi  lamo kamar mai bacci.
tashi fatuha tayi tare da ware ido ganin  ta  jikin  sadiq  kwace a  zabure ta  mike  tsaye ta ce “Nashiga uku yaushe bacci ya kwashe ni? wayo Allah na da mai kyau ya tashi ya ganni dana bani” hannu ta kai goshin sadiq jin ba zafi yasata sakin ajiyar zuciya ta  furta, “Alhamdulillah jikin yayi sauki bari nayi sauri na d’auro alwala” part din ta bari ta wuce nasu.

      Alwala kawai ta dauro ta gabatar da sallah, bayan ta idar ta tsaya lazumi da bita qaratun ta saboda anjima da rana malam zai amsa.

     Fatuha na fita sadiq ya ware idanuwan shi tare da ta6e baki ya yunqura zai  tashi  yaji hannu shi yayi zafi, sai a lokacin ya tuna da ledar ruwan da aka qara masa har ruwan ya qare ga hannu ya kunbura, ya manta shaf bai cire ba yaye blanket din jikinsa yayi ya shiga bathroom sai da yayi wanka ya fito sanye da bathrobe da qaramin towel a hannu shi yana goge sumar shi da hannu daya, saboda  d’aya hannu namasa
zafi  sosai.

    Lokacin yayi dai-dai da turowar kofa waigowa yayi yana kallon kofar, fatuha dake bakin kofa itama shi take kallo tana  hamdallah  ganin  ya  warware kauda kai tayi tare da cewa, “ina kwana.! amsa mata yayi babu yabo babu falasa qoqarin fita take ya ce “Fatuha.! juyowa tayi tana kallon sadiq wanda shi ma ita yake kallo ya ce “thanks for the caring” murmushi fatuha ta saki duk da bata ji abinda yace karshe ba ta gane mai yake nufi da Kalmarsa ta farko  qarasa fita tayi shi kuma ya cigaba da aikin  gaban shi.

     Yau ma kamar jiya har yanzu rabi’a bata zoba har hankalin fatuha ya fara tashi da rashin  zuwan nata, shara tayi da wanke-wanke sannan ta fera dankali ta soya ta juye a kuloli tare da kwai sannan ta daura ruwan zafi ya tafasa ta juye kamar yadda rabi’a keyi, haka tayi har su ola sai da ta basu nasu, amma har yanzu lamarin rabi’a na bata mamaki zuba kayan abincin sadiq tayi a tray ta aje a dining area sannan ta shige bedroom ta cire kayan baccin dake jikinta ta shige bathroom tayi wanka tana fitowa mai ta shafa tasa material  red mai ratsin golding a jiki masha Allah fatuha ba qaramin kyau tayi ba, daure gashin kanta tayi da yar kibiyar soke gashi sannan ta fesa turare  mai kamshi sannan ta fito daga bedroom,

       Direct dining area ta wuce ta  dau tray din  kayan abinci sannan ta wuce part din Sadiq, a hankali ta tura kofar bedroom din kishingide ta ganshi saman bed yana sanye da riga da wando riga mai dogon hannu red mai ratsin black sai jeans blue ba qaramin kyau yayi ba, fuskar nan tashi tayi fayau cikin sallama fatuha ta shigo, amsa mata yayi a taqaice aje tray din tayi a stool,

      Sannan tace, “Mai kyau ya jiki ?” amsawa yayi cikin cool voice dinsa, “jiki da sauki fatuha”
“to Allah ya qaro sauki” sannan ta zauna saman sofa tana facing din sadiq wayarsa ce dake saman bedside drowe ta fara ruri hannu ya kai ya dauka sunan da ya gani jikin screen din wayar ya sasa smile,

   Daga daya bangaran Aunty bilki ta ce, “Hello baby, ya kake ?”
“lafiya lau Maman Hanan”
“ya naji voice naka wani iri?
“yanzu na ta shi daga bacci” ya fada a taqaice, murmushi tayi daga d’ayan bangaran ta  ce, “bari na baka jidda tun jiya  take matsamin tayi missing naka kai da fatuha” smile sadiq yayi wanda ya bayana fararan hakuran shi miqawa angel wayar Aunty bilki tayi ta  ce, “daddy.!
“yes my princess,”
“dadd I miss you”
“miss you more angel”
“daddy yaushe zaka zo d’auka na?
“sai end of this week angel”
“yeee daddy love u dadd ina Aunty fatuha?
“gata nan kusa dani”
“please daddy ka bata muyi magana I miss her”
“ok Angel lemme give her.

     Fatuha dake zaune saman sofa sai smile take saboda ta gane da jidda sadiq yake waya, saboda da ita kadai yake waya yana smile ko Mom miqa mata wayar yayi ta kara a kunne cike da jin dadi ta ce, “Jidda.!
“na’am Aunty” dan bata fuska fatuha tayi hakan ya  fito mata da sak yarintar ta ta  ce, “jidda haka ake ki tafi ki barni ni kadai a gida dan Allah ki dawo kin ji,”
“laaa Aunty baga daddy ba baya tayaki wasa? ai daddy ya iya wasa” dago ido tayi ta kalli sadiq da shima din ita yake kallo ta hadi wani yawu tace cikin zuciyar ta gaskiya jidda ba hankali ina ni ina wasa da sangami mtww Aunty da jidda ta ce ne ya maido da fatuha daga dogon tunanin da ta tafi sun dade sosai suna waya da jidda har mamaki fatuha take yadda suka dade kamar ba kudi ake dibaba.

      Miqawa sadiq wayar tayi tare da qoqarin bude kulolin abincin dake saman stool, saving nashi ta shiga yi chips n egg sai farfesun yan ciki dake ta zuba kamshi ni kaina ganin qoqarin fatuha nake dan yanzu baza ta wuce 14 years ba, bayan ta kamala saving din nashi ta miqamasa plate din hade da fork amsa yayi yana qoqarin daukar fork din da hannu amma ya kasa saboda hannusa yayi tsamin, daurewa yayi zaiyi ta maza ya ci da hannu kan dole amma ya kasa fatuha na lura da yadda yake matsawa kansa taimakamasa tayi ta amshi plate din sadiq ya bita da kallo debo chips din tayi ta kai masa baki duk da tana gudun tsinki na sadiq aiko taci za’a ba musu ya amsa haka ta cigaba da feeding din shi yana amsa har sai da chips din ya qare sannan fatuha ta saurara masa, shi  kansa  ya  ga  qoqarinsa  na  cinye  abincin  raban  daya  ci  abinci  kamar  haka  har  ya  manta, tana qoqarin qaromasa, zaro ido sadiq yayi waje ya ce, “fatuha wazai ci wannan?
“kai mana”
“lallai to wannan din dakyar na daure na  ci shima, anfada maki kowa irin kine acici” harara fatuha ta aika masa tana qoqarin tashi riqe hannu ta yayi ya ce, “sorry.!  Sororo fatu  tayi  ji  abin  sadiq  ya  ce,  murmushi ta saki sannan ta dau plate din chips din tana ci.

      Rayuwa na tafiya komai na gudu kwanakin da sadiq ya dauka yana rashin lafiya duk wata dawainiyarsa fatuha ce kulawa  fatu ke basa sosai  na  ban  mamaki, hakan yasa wata irin shaquwa ta shiga tsakanin su da sadiq a yanzu jin fatuha yake kamar qanwar shi hakama itama fatuha kusan yanzu kullun suna tare sai dai idan ya tafi aiki ko masallaci, yanzu sosai fatuha ke jin dadin gidan haka shima sadiq duk wani tunani da damuwa ya ragu ba kamar da ba, har wata yar qiba yayi saboda fatuha bata barinsa da yunwa ko  damuwa  duk  wani  farin  cikinsa  ya tattara  kan  fatu  kuma ya  kasa  gane  mai  hakan  ke  nufi, dan yanzu kusan ita ke  feeding din shi duk wani abinci tana bashi tana masa hira har ya cinye bai sani ba yanzu  sosai  captain  yake  dariya  har  kyakyatawa  kullun fatuha sai tasa sa dariya da labaran ta haka rabi’a ma ta dawo ta amshi aikin ta ashe itama fever tayi.

     Daririkun dake tashi  a dakin sadiq ,ya sani tura kofar kar ayi ban dani fatuha ce sanye da rigar sadiq ta uniform na wajan aiki ala dole sadiq take  kwaikwaya yarda yake  da dariya Sadiq ya saki  tare da matsowa kusa da ita ja mata hancin yayi tare da cewa “Fatuha baki ji ko?” dariya ta saki ta ce “Mai kyau ai haka kake yi idan kasa uniform” ta ida zancan tana qoqarin fita daga bedroom din riqe hannu ta yayi ya ce  “Anjima ki shirya zamu je dauko angel” tsale tayi tare da rungume sadiq tana dariya shima din rungume ta yayi yana smile dan sakin sadiq tayi ta ce “Wallahi da jidda bata nan gidan ba dadi”
“ko.!
“eh mana”
“ok oya kije ki shirya ki cire min kaya” bata fuska sadiq yayi ya ce, “2days dinnan kin fara rai nani Allah,” turo baki gaba fatuha tayi ta ce ” Yi hakuri” smile Sadiq yayi ya ce, “wannan bakin naki ya iya ba da hakuri kuma ya iya rashin jin” zame wa tayi daga jikin sadiq  ta fita tana saukowa downstairs ta hango baba jummai na shigowa da kaya niqi-niqi wani irin ihu ta saki ta ruga da gudu wajan ta ta rungume ta, sadiq da ke qoqarin shiga toilet ya fito da sauri ya rife part din shi chak ya tsaya a up stairs yana mamakin rashin hankali na fatuha guntun saki yaja ya juya, a  tunaninsa  wani  katon abune  ya  faru har  sai daya  rasa  nutsuwarsa  ta  wucin  gadi ajiyar  zuciya  ya  saki.
kallo baba jummai tabi fatuha da shi kirjinta  na  dukan  tara-tara tana mamakin rigar da ta gani jikin fatu  gashi ta wani  sauya  tayi  6ul6ul  wani miyau  ta  hadiya  makwat ta danyi murmushi  wanda iya Karshi le66anta  fatuha ta katse mata tunanin da cewa, “baba shikenan sai ki tafi ki barni  ni kadai a gida nan?
Baba  jummai  ta  ce, “dan Allah yi hakuri fatuha wallahi hidimomine suka min yawa kuma bada niyar dadewa naje ba, niyata nayi kwana biyu na dawo”
“toh shikenan bari nayi sauri nayi wanka dauko jidda zamuyi daga gidan Aunty bilki”  toh baba ta ce tana  kara  tsuma  da  danasanin  barin  fatu  gidan  basu  tafi  tare  ba  ashe jidda  ma  bata  nan  wani  abu  da  hadiya  mai  daci fatuha ta wuce bedroom baba jummai ta bita da kallon tuhuma Allah ya rufa asiri ta  furta  jiki  a mace sannan ta dau ledar tsarabar kayan miyan datayi ta shige kitchen.
Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*_Email_* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

65_66

Bayan ta tsala wanka ta shafe jikin ta da lotion mai kamshi da sanyi dadi, riga da sket tasa na atamfa mai ratsin pink green blue masha Allah kayan sun mata kyau, sai suka qara fitowa da haskyan ta daura dan kwali tayi ya zauna sosai a kanta, ta jawo green veil din ta sa sannan ta zura takalman ta black tare da fesa turare, bayan ta kamala ta fito daga bedroom parlour ba kowa sai kamshin girki baba jummai da ke ta tashi.

Part din sadiq ta wuce a hankali ta bude kofar parlour, ba kowa sai sanyi AC dake tashi cikin nutsuwa ta nufi bedroom ta burda handle din kofar tsaye ta hango sadiq gaban dressing mirror yana sanye da blue riga mai gajeran hannu sai blue jeans ya gyara sajan shi yayi luf-luf haka sumar kanshi ta kwanta yayi kyau sosai har ya gaji juyowa yayi su kayi ido hudu da fatuha kashe mata ido yayi ya ce, “kallon fa? murmushi tayi ta kauda kai tana qoqarin fita ya ce, “wallahi kika fita ban zuwa da ke” make kafada tayi tare da qarasa shigowa murmushi yayi ya ce, “Good girl” yana qoqarin saka mabalin rigar shi bayan ya kamala ya dauki car key dinsa da wayan shi dake bedside drawer ya nufo inda fatuha take ya ce, “inyee yan’mata ansha kyau ashe dai yan kauye sun iya gayu” dariya fatuha tayi ta rufe fuskar ta tana aika masu wani irin kallo tattausan murmushi yayi ya ce, “oya tashi mu tafi” a tare suka fito daga part din shi lokaci yayi dai-dai da fitowar rabi’a zata tafi gida kallo tabi so da shi tana mamaki yaushe sadiq ya fara wannan wasan chab ta furta, koma dai minene ai fatuha yarinya ce akan yan’matan dake masa layi kumama ko giyar wake yasha abinda take tunani ba shi bane dan babu abin sadiq zaiyi da fatu watsar da zancan tayi tare da yin gaba fatuha ce ta kira sunan ta, rabi’a waigowa tayi a dan tsorace tare da sakin murmushin da iyakar shi la66anta fatu ta ce, “har zaki tafi?
“eh wallahi na gama aiki na kuma dama gashi baba jummai ta dawo”
“toh ki gaida gida”
“gida zai ji” fatuha ta sakai ta fita.

Suna fitowa kallo ya koma kansu ola jiki na bari ya nufo sadiq har qasa ya gaisheshi Emeka da Sunday duk sai da suka kwashi gaisuwa, sannan ya bude murfin mota ya shige haka ma fatuha ya ja motar suka bar harabar gidan, cikin nutsuwa yake driven din waigowa yayi ya kalli fatuha da tarakufe guri daya ya ce “Fatuha.! Cikin tattausan muryarsa
ta ce, “na’am.!
“yau anfito bude ido ko? dan smile tayi ta ce, “tunda nazo birni wannan ce fitana na biyu”
“ai gara haka saboda bana son to much of yawo, uhm kina san karatu? saurin d’aga kai tayi sadiq ya ce, idan na saki school kina so” jinjina kai fatu tayi cike da farin ciki, “zaki iya karatu kina kulla da angel zaki iya? saurin d’aga kai tayi ga farin ciki shinfide a fuskarta ta ce, “insha Allah” murmushi sadiq ya saki mai taushi ya ce, “insha Allah zan saki kin ji,” lokacin yayi dai-dai da tsayawar motar su bakin geta din gidan Aunty bilki horn yayi mai gadi ya bude masu ya kunna hancin motarsa.

Dai-dai parking space yayi parking tare da kashe motar, fatuha ta 6ale murfin mota ta fito shima ya fito yana gaba fatuha na bayansa knocking din kofar sukayi baba larai ce ta bude masu washe da baki har qasa ta gaishe da su sannan ta basu hanya suka shigo, cikin sallama Aunty bilki da ke parlour zaune saman three sitar tana kallo washe da baki ta amsa tana cewa, “sannu da zuwa baby” saman two sitar ya zauna fatuha kuma ta zauna a qasa kusa da sadiq tare da gaishe da Aunty bilki, cikin fara’a ta amsa kwalawa baba larai kira tayi ta kawo masu kayan motsa baki aiko ko 5 minute batayi ba ta dawo riqe da tray cike da kayan motsa baki ta aje gaban Sadiq, kallon fatuha yayi dake zaune gefan shi a qasa tayi shuru itama shi din take kallo harara ya aika mata ya ce, “tashi ki zauna a kujera” Aunty bilki smile tayi ta ce, “aiko dai tayi zaune qasa abin ta, ni ban ma gane ta ba wallahi, naga ta girma sosai raban dana ganta tunda su mom suka tafi yau kusan 2month kenan, jiyama mukayi waya dasu Mom insha Allah ranar Friday zasu dawo tare da yaya jawad”
“aini fushi nake da su sun barni ni kad’ai a gida ai sun kyau”
“dama shagwabar ka ta ishemu ya kamata ka zo kayi aure haka naga har wata yar qiba kayi” fatuha dake zaune saman one sitar ce ta kalli sadiq shima ita yake kallo ji tayi gaban ta ya yanke ya fadi da furicin Aunty bilki kauda kai tayi tana jin jikita yayi mugun sanyi Kallon ta Aunty bilki tayi ta ce, “na aiki su Hanan ne amma yanzu kinga sun dawo” bata ida rufe bakin ta ba suka shigo da gudu angel ta fada jikin daddy murmushi Sadiq ya saki jidda ta ce, “daddy I miss you”
“miss you more angel” kissing d’in kumatunta yayi itama tayi masa Hanan cikin fara’a ta nufi fatuha Basma kuma na gefe tsaye tana satar kallon sadiq kasancewa ta zo hutu gidan Aunty bilki, gaishe da sadiq sukayi ya amsa a takaice sannan Hanan taja fatuha suka wuce dakin ta angel kuma na maqale da daddy.

Suna shiga d’akin Hanan Basma ta cire mayafin kanta ta fada saman bed, itama Hanan bed ta hau fatuha kuma ta zauna saman sofa Hanan ta ce, “laa fatuha baki zama saman bed”
“a’a barni a nan ma yayi wallahi”
Hanan ta ce, “Basma kinga wadda nake fada maki mai gashin nan” d’ago kai tayi ta kalli fatuha ta d’an yi smile ta ce, “sannu ki fa”
“yauwa” cewar fatuha hira suka shiga zubawa kasancewar duk sa’anin junane amma dai Basma ta dan girme su dan yanzu ita SS2 zata Hanan kuma SS1 kunsan a tare suke komai da Hanan da basma duk da Basma Aunty ce a wajan Hanan kuma ta d’an kirme mata sosai fatuha ta saki jikin ta amma sai dai tana dan d’ari-d’ari da Basma, kiran sallah magrib ne ya tashe su daga fira alwala suka dauro suka gabatar da sallah bayan sun idar angel ta shigo da gudu d’akin ta ce “Aunty fatuha daddy yace ki fito mu tafi?” to tace tare da yafa mayafin ta a tare suka fito da su Hanan parlour a tsaye suka tada sadiq Aunty bilki ce ta 6ata rai ta ce, “haba baby kabari kuyi dinner mana sai ku tafi”
“a’a gaskiya yau girkin baba jummai zanci I miss her food”
“oh ni ba kayi missing din nawa ba ko?
“ba haka bane sis so kike muyi barnan na gida ko?
“toh shikenan a gaida gida dan ko rakiyar banyi” langwabe kai sadiq yayi ya ce, “please kar muyi haka mana” harara wasa ta kaimasa sannan ta ja veil din ta dake saman kujera suka fito a tare hira suke sosai kamar karsu bari, bude murfin mota sadiq yayi angel ta shige gaba fatuha na baya sannan ya ja motar bai zame dasu ko ina ba sai shoprite shiga su kayi yayi masu siyaya sosai ice cream teddy’s duk ya kwaso kayan wasa kamar bai jin kudin ya cika boot da su sannan suka juyo gidan a gajiye likis.

Yana horn bala mai gadi ya bude masa geta yayi parking sannan yayi masu ola nuni da su kwaso kayan boot lokaci ma jidda tayi bacci, fatuha ce ta dauko ta suka shige gida upstairs sadiq ya haye fatuha ta shige bedroom kaya kawai ta cire ma jidda tasa mata na bacci, tana qoqarin cire nata akayi knocking din kofar zura hijabi tayi ta bude ola ne riqe da trolley din jidda da kayan wasanta, duk ya aje sannan ya mata sai da safe rufe kofar tayi ta rage kayan jikin ta, ta wuce toilet tayi wanka ta fito daure da towel tsane jikin ta ta yi ta shafa mai sannan tasa rigar baccin ta gown dai-dai gwiwa white n brown mai zanan cartoons, sannan ta saki gashin kanta tare da daukar jidda part din sadiq ta wuce da ita a parlour ta same shi yana kallon news kamar kullun, sanye da kayan baccinsa maroon riga da wando mai dogon hannu bedroom ta shige ta shinfidar da jidda sannan ta fito har ta fito yana nan yarda ta barshi a parlour har yanzu haka yake, qoqarin fita take ya ce, “fatuha ki kawo min dinner na nan” to ta ce masa sannan ta fita.

Direct dining area ta wuce ta zubo masa tuwan shinkafa miryar taushe tasha naman rago sai kamshi ke tashi, sannan ta wuce part nashi saman stool ta aje masa plate din zata fice riqo hannu ta Sadiq yayi tare da cewa “Fatuha waya bata makin rai tunda muka dawo na gabaki daya baki farin ciki? ko bros ya maki laifine?”
“laa Allah ba abinda kamin kawai na gajine yau munsha hira da su Hanan”
“toh naji amma ai ba kiyi dinner ba”
“bana jin yunwa ice cream din dana sha ya cika min ciki wallahi”
“ok tunda hakane na fasa kai ki school din” zaro ido waje fatuha tayi ta ce, “dan Allah kayi hakuri Allah zanci”
“tam oya zo zauna muci” zame hannu ta tayi daga ruqwan da sadiq ya mata ta zauna a qasa tare da jawo plate din gaban ta shima sadiq din zama qasa yayi cikin nutsuwa ta fara kai loma daya sannan ta debo ta kaima sadiq amsa yayi wata lomar ta debo ta kai masa baki hadawa yayi da yatsanta ya ciza yar qarasa ta saki tana yar fe hannu ta dariya sadiq ya saki, kuka ta fara masa tana kai masa bugun wasa riqe hannu yayi yana dariya ya rungumeta ya furta “sorry sis”can qasan maqoshi yana magana yana shafa bayan ta lamo tayi a fafad’an qirjinsa tana maida numfashi dago da fuskar ta yayi ya ce, “sis yau baki surutu kamar ankule maki baki, gashi kin bata min night dress da miya gaskiya ba zan yadda ba” ya fadi a dan shagwabe, kallansa fatuha tayi ta lumshe ido tare da cewa, “yi hakuri mai kyau bazan sake ba”
“good girl to fada min Fushin nan name to?
“uhm uhm dama ina so naje kauye ne kwana biyu wajan inna kafin na fara zuwa makaranta”
“wannan shine damuwar?
“eh.!
“ok karki damu insha Allah zan kai ki” zame jikin ta fatuha tayi daga na sadiq riqe habar ta Sadiq yayi ya ce, “fatuha ki dauke ni kamar yayan ki duk abinda ke damun ki ki fada mani na maki alqawarin samamaki farin ciki, kamar yadda kika samamin fatuha” murmushi ta saki wanda ya bayana fararan haqoran ta daukar plate din abinci tayi zata fita sadiq ya rako ta har kitchen ta aje plate din ta wanke hannu ta.

sai da ta zo bakin kofar shiga bedroom sadiq ya mata peck a goshi itama ta mashi a kumatu sannan ta shige bedroom shima ya haura upstairs.

***
Bayan kwana biyu haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda sadiq ke bawa fatuha da jidda kulawa sosai haka suma suna faran ta masa rai, wani bangare na daban yake jin fatu a ransa wanda baya iya fassara hakan, duk wanda yaga sadiq a yanzu yasan baya fama da wata matsala, sai wani kyau da yake ta qarawa.
bangaran karatun adini kuwa fatuha tayi nisa sosai tana mai da hankali, yadda ya kamata kuma a yanzu duk duniya bata da aboki ko qawa sama da captain shine uwar ta shine uban, ya riga ya zama wani 6angare a rayuwar bata bari yayi fushi da ita ko kad’an domin a duniya ba abinda ta tsana sama da fushin captain a kanta.
baba jummai ko duk yadda ta bigi cikin fatuha ta fada mata wani abu na daban, akan abinda take zargi bata samu ba, sai da kanta ta gane abinda take tunanin ba haka bane, zalla shaquwace kawai tsakanin sadiq da fatuha.

Dr yakub yafi kowa farinciki da canji sadiq har mamaki yake da hamdallah da sadiq yaji shawararsa ya canza lokaci daya.

Kwana biyu ko daya je wajan Ammi ma taji d’adi ganin canjinsa haka majid da kwana shi biyu da dawowa daga Lego’s anmasa transfer ya dawo kano da aikin, sosai sadiq yaji dad’in haka ko ba komai dan uwan shi ya dawo kusa da shi.

Kasancewa yau ta kama friday shirye-shiryan ake sosai na tarbar su Mom, yau zasu dawo Nigeria tare da yaya jawad haka Aunty bilki ta kwaso duka yaranta tazo dasu anata aiki.
fatuha na hango sanye da uniform din ta na yan’aiki wanda ta dade raban data sasu sun mata kyau sosai part din sadiq ta wuce riqe da cup na coffee ganin baya parlour yasa ta tura qofar d’akin yana tsaye gaban dressing mirror sanye da shada blue ta sha aiki da dark blue zare yana combing din gashi kansa, murmushi ya saki tare da qarasowa wajan fatuha amshe cup din yayi ya aje saman stool kallo tabi shi da shi dan yau ba qaramin kyau ya mata ba har mamakin kanta take da har yau ta kasa ganin wanda yafi sadiq kyau da komai har ma da kwarjini gashi kullun qara kyau yake, hura mata iskar da akayi ya sata ware manyan idanuwan ta tana kallon sadiq har cikin ranta take jinsa, smile yayi ya ce “Tunanin fa? kin hanani tunani amma ke gashi kinayi yanzu” far da ido fatu tayi ta ce, “bafa tunani nake ba”
“to mikikeyi bayan gashi na gani?
“uhm kayi kyau ne kawai” lallausan murmushi captain ya saki ya ce, “thanks ke ma kinyi kyau”
“a haka din?
“eh mana” cup ya dauka ya kai bakinsa ya wani lumshe ido ya ce, “hmmm lallai fatuha ta iya hada coffee gaskiya zani da ke” dariya tayi ta ce “Allah idan na biye ma sai mu kwana anan muna surutu”
“ko? tam shikenan tafi tunda tafiya zakiyi ni bana so kiyi aikin shiyasa nace akiramin ke, amma tunda kin fi so ki wahala shikenan tafi munma 6ata” langwabe kai fatuha tayi ta ce, “Kayi hakuri ka ga su Mom ne zasu dawo kaji”
“ok amma sai kin min peck ko kina tafiya” to tace tare da yi d’age ta masa peck a goshi sannan ta fice daga d’akin murmushi sadiq ya saki yana shafa goshinsa ya bita da kallo.

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best ★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

67_68

Da misalin karfe 1:00pm flight din su Mom ya sauka Nigeria lokacin har Sadiq ya Isa airport da yaransa kusan mota uku akayi ta tarbar su Mom da Abba a hankali suke saukowa daga matatakalar jirgin Mom na sanye da lace ash mai ratsin pink blue, Abba na sanye da shada brown tasha aiki da dark brown zare yaya jawad da Aunty shukura na baya suma sunsha shigar alfarma tana riqe da babyta, jawahir yana riqe da hannu babansa cikin fara’a suka qaraso gaban motocin.

Cikin sassarfa sadiq ya qarasa ya kai ma Mom hug, dan murmushi ta saki tare da rungume Abba ya murmusa ya ce, “baby wai yaushe zaka girma ne? dake gefe Mom yar dariya tayi 6ata fuska sadiq yayi irin na shagwaba tare da cewa “Danma banyi kuka ba kun tafi kun barni” yar dariya jawad yayi sannan yaran sadiq suka bude masu motocin suka shige.

A tare motocin suka kunno kai gida bala mai gadi ya wangale masu geta washe da baki yana daga masu hannu, dai-dai parking space motocin suka faka suka fara fitowa tun kafin su shigo gida yan gida suka fito kowa ka kalla kasan cike yake da farin ciki, haka jikokin a tare suka shige parlour su ola suka shige da kayan su ciki.

Murna wajan sadiq ba’a magana saboda dama yayi missing din Mom din shi dakuna suka shige matafiyan suka sheqa wanka, sai misalin karfe 3:00pm aka halara a dining area duk wanda ka kalla cikin farin ciki yake, cikin nutsuwa suke lunch din inda jawad da sadiq suke ta zuba hira Aunty bilki da shukura matar jawad, amma duk wannan hira ake hankalin sadiq na Kansas fatu kalle-kalle yake ya ga ta inda fatuha zata fito, abinci ne gabansa amma ya qasa ci saboda yanzu ya saba tare suke ci da fatuha ko tayi feeding din shi loma biyu zuwa uku yayi ya ture abincin.

Bangaran fatuha ko tunda ta kamala aiki cikin ta ke nukurkusa duke take a daki sai kuka take rairawa , qoqarin miqewa take ta kasa saboda cikin ba qaramin kullewa yayi ba bud’e kofar da a kayi yasa fatuha d’ago jajayan idanuwanta Hanan ce ta shigo cikin sauri ta qaraso wajan fatu ganin halin da take ciki ta ce, “fatuha meke damunki? ta fadi a dan tsorace kuka ta kuma saki tana riqe da marata, ganin ba abinda fatuha take cewa yasa Hanan fita lokacin kowa na parlour ana zuba hira Momi tace cikin rawar murya kowa ya waigo “Momi fatuha ba lafiya gata can kwance tana kuka wai cikin ta.! mikewa tsaye sadiq yayi har suna yar rige-rige da Aunty bilki haka Mom ta biyu bayan su suna shiga suma a durkushe suka same ta, sai kuka da take ta fama rairawa Aunty bilki ta matso kusa da ita tare da cewa “Fatuha menene ? cikin kuka-kuka ta ce “Ciki na Momi ”
“sorry tashi a kaiki asibiti kinji”
“bana iya tashi” ta fadi tana qara sakin saban kuka Aunty bilki ce ta taimaka mata ta tashi gabaki daya sket din ta ya baci da jini ashe aladace ta fara, “sannu kin ji Aunty bilki ta ce kallon Mom Aunty bilki tayi ta mata nuni da ta kori su sadiq waje aiko haka akayi aka tasa keyar su waje.

“Sannu kinji fatuha girmane ya zo kinji ba wani abu bane, yanzu shiga toilet ki wanke jikin ki sai kin fito na gwada maki yadda ake” d’aga kai fatuha tayi ta shige toilet a duduke Aunty bilki ta fita taba sadiq kudi ya siyo pad ya dawo kallo ya bita da shi tare da cewa, “ki bar kudin bari naje na siyo,” murmushi tayi ta maida kudin ta cikin handbag sannan sadiq ya fita ko minti 10 bai yi ba ya dawo ya miqa mata pad din, ta qara komawa lokacin fatuha ta fito duk yadda ake anfani da pad haka Aunty bilki ta gwada ma fatuha tare da bata yan shawarwari na gyara jikinta saboda yanzu ita ba yarinya bace, sosai ta ji dadin jikinta sannan ta bata magani tasha saman bed ta koma ta kwanta bacci ya sure ta Aunty bilki ta fita.

Basu suka bar parlour ba sai da akayi kiran sallah magrib yasa suka wuce masallaci, su kuma matan suka wuce part din Mom basu suka dawo ba sai bayan isha’i jawad ya wuce part din su sadiq ya shige gida, parlour ba kowa bedroom din fatuha ya wuce a hankali ya bud’e kofar kwance ya hango ta saman bed ta dunqule waje daya rife kofar yayi tare da qarasa shigowa, gaban bed din yayi kneeldown a hankali ya kai hannu yana shafa gashin kanta cike da begenta da tausayinta, a hankali ta ware idanuwan ta kan sadiq, kuka ta saka masa mai cike da shagwaba da yarinta, “shhh..! kukan ya Isa haka mana uhm” har lokacin sadiq na sakin tattausan murmushinsa yana shafa gashin kanta kamo hannusa fatu tayi tana qoqarin kai masa marata inda ke mata ciwo sauri kauda hannusa sadiq yayi tare da wayancewa dan ya lura har yanzu fatuha yarinyace shiyasa take haka a hankali ta furta, “mai kyau”
“na’am Sister” cikin wata kasalaliyar murya fatu ta ce, “Zai daina ciwo”
“eh mana gobe da kin tashi zaki ji kin warke kin ji sis” to ta ce masa tare da riqe hannusa tana wasa da su kamar an tsunkunesa ya tashi ya fita fatuha ta bishi da kallo.

Kitchen ya shige ya d’auko mata fresh milk mai sanyi ya dawo bedroom, har yanzu tana yadda ya bar ta tana bin sadiq da ido bata fresh milk din yayi ta kafa kai ta shaye sannan ya mata peck a lunatic tare da yi mata good night ya fice.

Kun san kwanan fatuha 4 tana period tayi wanka Mom ta gwada mata duk yadda ake.
haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi inda yanzu duk gidan ba wanda bai san shaquwar fatuha da sadiq ba, Mom ko in ban da dadi ba abinda take ji dan gani take fatuha alheri ce a rayuwar su, sannan sadiq ya sheda mata zai kai fatuha school kuma tayi na’am da zancan.

Harhad’a kayan ta dana jidda take a trolley saboda yau zasu je wudil, bakin fatu har kunne bayan ta gama had’a kayan tsaf a trolley ta wuce part din sadiq zaune a parlour ta samesa harara ya aika mata tare da kauda kai, dan 6ata fuska fatuha tayi tare da matsawa kusa da sadiq har yana jin saukar numfashinta mai fitar da sayayan kamshi ta ce, “mai kyau.! qara kauda kai yayi langwabe kai fatu tayi cikin siririyar muryarta ta ce, “yi hakuri idan nama laifi” ta miqe zata fita ruqo ta yayi tare da cewa, “shine dan zaki tafi gida shine ko ki leqo da safe? Lumshe ido fatu tayi ta ware su kan sadiq cike da kulawa ta ce, “yi hakuri, ka hada kayan naka?
“nope..!
“to na hada ma”
eh yace a taqaice d’akin ta shige ta hada masa nashi kayan cikin trolley ta fito da su dama shima ya shirya saboda tsabar zumudi ko break fatu ta kasayi haka Mom ta mata shatara na arziki har bakin mota ta rako su, acewarsu kwana biyu zasuyi su dawo saboda ankusa komawa school da sun dawo fatuha zata fara zuwa.

Sannan sadiq ya ja mota suka bar harabar gidan angel sai murna take tare da zuba masu surutu har bacci ya kwashe.

Ko 2 hours basuyi ba suka Isa wudil tunda suka iso fatuha ke bin kauyan da kallo, rayuwar ta da fatsima ta dawo mata sabuwa dai-dai kofar gidan su fatuha sadiq yayi parking har yanzu gidan nan yadda yake sai dai dan tsufa da ya fara sai yar kofar da akasa 6ale murfin mota fatu tayi cikin sauri ta shige gidan.

Inna na zaune saman kujera tayani gulma tana tankad’e, fatuha ta shigo da gudu tana cewa, “Inna..! Inna.! ta fada jikin ta cike zakuwa dagowa da ita inna tayi a dan tsorace washe baki tayi ganin fatuha binta inna tayi da ido dan dai fatuha na diyar ta da tace ba diyar ta bace, saboda girma da haske da ta qara bakin inna bud’e sallamar sadiq ce ta katse mata tunani ta ce, “kinga inna na bar mai kyau waje shida jidda” fita tayi tare da ba sadiq hakuri ta ruqo jidda suka shigo har qasa sadiq ya gaishe da inna, fatuha tayi ma inna bayani aiko inna hannu biyu-biyu ta amshe su dan ta yaba da hankalin sadiq jidda na gani inna ta samu kaka ta maqalewa inna, ta saki jikinta.
Da gudu fatuha ta fita daga gidan sadiq ya fita da ido bata zame ko ina ba sai gidan su fatsima, tana shiga ta shiga kwalla mata kira ba fatsima ba har Gwaggo a rude suka fito saboda jin muryar da suka dad’e suna kewa, da gudu fatsima ta fada cikin fatuha tare da sakin kukan farin ciki, murna wajan fatsima da fatu ba’a magana d’akin ta ja fatuha sai dai yanzu fatsima duk tayi sanyi nan take taba fatuha labari ranar daurin auranta mijin ya rasu, fatuha sai da ta tausaya mata sannan suka koma gida a tare lokacin inna har ta bama Sadiq masauki tare da kayan motsa baki jidda kuma na maqale da ita.

Kun san a tare suka wani da fatsima inda sadiq ke ta fushi fatuha ta barshi shi d’aya, basu suka rabu da fatsima ba sai gab da magrib lokacin Baffa ya dawo shima cike da farin cikin, inda ya dinga jan sadiq a jiki suna taba hira sama-sama, inna ta cika gabansa dafura da nono da tuwan dawa miyar kuka tasha manshanu, sosai sadiq ya saki jiki yaci abincin.

Misalin karfe 8:30pm bayan sun dawo daga masallaci sadiq ya wuce masaukinsa, bayan fatuha ta gama sa kayan bacci ta shirya jidda itama cikin nata sannan ta hada ma sadiq coffee kamar yadda ta saba a gida ta ja hannu angel suka wuce masaukinsa, da sallama ta d’aga labilan d’akin suka shigo, amsawa yayi a taqaice ta aje masa coffee ya amsa tare da aika mata harara wasa hannuwanta biyu tasa a kunne alamar bada hakuri tana rausaya kai d’an murmushi sadiq ya saki yana binta da kallo.
hira sukayi sama-sama inda angel ke ta zuba qiriniya har bacci ya kwashe ta, daukar ta fatuha tayi tana qoqarin fita sadiq ya mike ya masu peck tare da shafa kan angel dake kwance saman kafadar fatu, suka wuce d’akin fatuha.

*Washe gari*

Tunda safe fatuha ta tashi ta share tsakar gida tas, ta hura icce ta dora koko tare da dumama tuwan jiya, ta juye a kwanan samira tana qoqarin fitowa daga kitchen inna ta fito d’aga uwar d’aka washe da baki tana bin tsakar gida da kallo tana zancan zuci, alallai fatuha anyi hankali.! har qasa ta gaida inna ta amsa cikin fara’a sannan ta shige qurya ta fido jidda ta wanke ta tas ta shirya ta cikin jean n t-shirts masu kyau, sannan itama ta shige kewaye tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin riga da sket na lace red mai kyau sai yar hoda data murza da lipstick ba qaramin kyau tayi ba sannan ta dau kwanonin da tasama sadiq abinci ta nufi d’akin inna da ke surfa gero ta ce “Aiko dazu da sasafe tare suka fita da Baffan ki gona” murmushi fatuha ta saki ta ce, “shine baffa bai je dani ba ko? ta zun6oro baki tare da shigewa ciki ta aje masa abincin tana fitowa ta ci qaro da fatsima, washe da baki ta tarbeta kusan a tare su kayi kallaci sannan suka fita yawo ganin gari, duk inda fatuha ta wuce sai antanka da irin kyanda tayi da nutsuwar da ta qara haka aka rinqa layin zuwa ganin fatu ta zama balarabiya, haka ta dinga baje tsaraba tana rabawa fatsima ko tasha tsaraba kamar ba gobe.

Kwana su biyu a kauye inda yan kauye ke cewa fatuha ta zo da larabawa, itama ta zama balarabiya sun sha yawo da sadiq har rafi sai da ta kai shi, da gona mai gari inda suke satar mangwaro a da, sosai ya ji dad’in kauyan ba dan kad’an ba.

Fatuha ce riqe da trolley tana rusa kuka ita bata komawa, sai da inna tayi da gaske sannan ta shige mota sadiq yasa trolleys a boot tare da yima Baffa shatara na arziqi, duk yadda Baffa yaqi amsa haka sadiq ya matsa masa ya amsa, haka Baffa ya dinga samasa albarka fatsima har da yar kwallata sannan suka dau hanyar kano cike da kewa.

********** ********** ******

Akwana atashi ba wuya wajan sallah fatuha dai ta fara zuwa makaranta inda aka sata jss1 sosai take maida hankali kuma tana gane karatun gashi Alhamdulillah Allah ya zuba mata qoqari na ban mamaki, dan har tafi masu qoqarin ajin a yanzu a tare suke zuwa da jidda a yanzu jidda na primary 2 kusan duk makarantar su d’aya da su Hanan da Basma hakan ya qarasa suka shaqu duk inda kaga Hanan to zakaga Fatuha ko Basma sosai suke maida hankali akan karatunsu.

Kamar yadda aka saba tashin su misalin karfe 3:30pm driven yayi parking suka bale murfi motar suka fito a tare, sanye fatuha take da uniform din ta riga mai dagon hannu milk sai sket dark green dai-dai gwiwa sai dan qaramin hijab milk, jidda kuma biri da wando ne sai milk riga a ciki green a sama kallo d’aya zaka masu kasan sun gaji likis tun a parlour jidda ta fara wurgi da jakarta fatu ta ce, “oh no why this angel bari dai grandma ta fito ta zane ki.! sama nayi da ido ina tunanin wake wurgo wannan turancin kamar a mafarki ashe fatuha ce ohni salma😧, daukar bag din jidda tayi tana zun6oro baki ta kai bedroom dinta,

Har fatuha ta shiga bedroom ta fara cire mabalin rigar ta, ta tuna da ice cream din ta dake bedroom din sadiq cikin fridge da sauri ta fito ta haura upstairs, a hankali ta bude part din ta shige parlour ba kowa sai kamshi dake tashi, bedroom ta shige tare da nufar fridge, ganin Sadiq tsaye yana qoqarin cire rigar uniform dinsa ya sata cewa, “uncle..! waigowa yayi cikin smile ya qara kyau da kwarjini ya ce, “yes dear.!
“uhm ya naga ka dawo yau da wuri haka uncle?
“na gama aiki ne gobe da safe flight dina na zuwa london zai tashi zani wani course ne ba zata ya zo min, hada kayana na dawo yi” dan bata fuska tayi tare nufar fridge ta dau ice cream tana ta kunbure-kunbure ta fice Sadiq ya bita da kallo.

Vote
comment Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.CM

                      69_70

👏🏽Godiya gare ku mosayan ❤wannan novel, ina jin dad’in yarda kuke comments😍 ana mugun tare irin sosai din nan.🤸🏽‍♀🤸🏽‍♀

    wannan shafin naki ne Maimuna Lawal Allah ya bar zuminci har ya’ya da jikoki Ameen🤝

         Fatuha na shiga bedroom ta aje ice cream din saman bedside drawer dan gabaki d’aya ice cream din yafita ran ta, a duniya ba abinda ta tsana kamar mai kyau yayi nisa da ita, ita kanta har mamakin hakan take jiki ba qwari ta ida cire school uniform tare da shigewa bathroom ta sheqa wanka ta fito, bayan ta tsane jikin ta tabi da lotion mai kamshi tare da sanya black after dress din ta mai stone’s d’aure gashin kanta tayi kamar ganmo tare da murza yar hoda  da lipstick masha Allah fatuha ba qaramin kyau tayi ba, fitowa tayi daga bedroom din ta wuce na Mom cikin sallama ta shiga mom Na tsaye gaban dress mirror tana shiri da alama fita za tayi cikin fara’a ta amsa fatu ta ce, “Mom fita zakiyi ne?”
“eh wallahi zani gidan Ammi ne, dama yanzu nake cewa ko zaki raka ni? dan murmushi fatuha tayi itama tana san zuwa wajan Ammi din nan amma tunda ta zo sau biyu ta ta6a zuwa gashi tana san ganin Basma, amma Assignment ba zai bari ba gashi malam anjima zaizo ta  ce, “Mom kin manta yau wednesday,”
“oh haka fa na manta fa shaf next time munje”
“kuma wallahi Mom ina san zuwa Basma har ce min take bani da kirki bana zuwa,”
“ai ta fada duk zaryar da suke maki baki zuwa masu kema kin fara koyan halin uncle din naki,” dan smile fatuha ta saki mai cike da jin dad’i ita dai duk abinda za’a ce daga mai kyau yake so take ta  ce, “Mom ai baya san yawo uncle shiyasa”
“ke kuma sai  biye masa kike ko, zuminci fa abin wasa bane” Mom ta ida zancan tana daukar handbag din ta kusan a tare suka fito, angel na zaune a parlour tana kallon cartoon ganin grandma zata fita yasa ta tashi tana cewa, “grandma zan biki please”
“nope yau malam zaizo” zu6uro baki Angel  tayi gaba tana sanyin kuka ta  ce, “please grandma ki je dani,” fatu  ta  ce, “angel kiyi hakuri grandma ta je kin ji, muma ranar Friday mun tafi kinji.! d’aga kai jidda tayi ba dan taso ba,  har bakin mota suka raka ta suka juyo.

    A dai-dai bakin kofa suka ci qaro da sadiq yana sanye da 3 quarter black da white t-shirt da alama gym zashi, kauda kai fatuha ta yi ala dole fushi take da sadiq, smile yayi tare da d’aga angel sama yana mata wasa tana dariya ko kallon inda fatuha take bai yi ba saboda ya lura yau rigima take ji, ra6awa tayi ta gefansa zata wuce ta cika taf qiris take jira ta fashe, ruqo hannu ta yayi hakan yasa ta tsaya chak a wajan, ta kasa kwace hannu ta sai binsa da take da kallo, aje jidda yayi qasa yana aje ta kamar jira take tayi cikin gida da gudu, fisgo da fatuha yayi ta fado saman fafadan qirjinsa har tana jin bugun zuciyarsa lamo tayi a qirjin nasa idanu ta  lumshe, a hankali ya d’ago da habar ta yana kallon ta lumshe ido yayi tare da ware su kan fatuha cikin cool voice dinsa ya ce “Fushin na menene uhm? dan 6ata rai tayi tana qoqarin zamewa daga jikinsa tunda bai san fushin me take ba, dan matse ta yayi da karfi ta saki yar qara, ta fara matsar kwalla kamar  jira  take  tana  binsa  da  idanu  ta cikin  tattausar  murya  sadiq  ya  ce, “daga nace zanyi tafiya sai fushi fatuha 3 days fa kawai zanyi kin ji dear,” turo baki gaba tayi  ta  ce, “ni ba fushi nake ba”
“to me kike?
“ba komai”
“ok tunda ba fushi kike ba please ki had’a min kayana, na rasa kayan da zansaka kin riga kin shagwaba uncle da yawa,” d’an zunburo baki ta kuma yi maicike da shagwaba sadiq  ya  ce, “please karki ce bakiyi”
“zanyi mana”
“promise.!
“promise..!
“good girl”ya sakar  mata  peck  a  goshi ya fita.

    Bayan ta kamala hada masa kaya sannan ta kalli agogon dake manne a d’akin kusan karfe 4:30 sauri fitowa tayi daga part din ta wuce bedroom, d’auro alwala tayi tare da gabatar da sallah tana gamawa ta d’auko alQur’anin ta, saboda yau laraba, alqur’ani kawai suke yi tare da jawo hijab din jidda tun a parlour ta zura mata suka fita a tare, lokacin har malam ya zo karatu suka yi sosai inda malam ya masu qarin bayani akan hadisi, sai  gab da magrib suka shigo cikin gida, alwala kawai suka gabatar tare da yin sallah.
bayan ta idar ta tsaya yin lazumi sannan tayima jidda assignment tayi nata kiran sallah isha ne ya tashe su bayan sun gabatar suka fito parlour sukayi dinner sannan kowa ya wuce bedroom din shi saboda sun gaji likis.

        Asuba ta gari

      Sallah asuba fatuha tayi tare da yin wanka, mai kawai ta shafa tare da sa yar gown iya karta gwiwa sannan ta fito bedroom din jidda ta shiga tayi mata wanka tare da shirya ta cikin uniform sannan ta bar d’akin, kitchen ta shiga cikin sallama baba jummai nata jefa bafanke gaishe ta fatuha tayi cikin fara’a ta amsa sannan suka gaisa da rabi’a, bude fridge tayi ta fido yan cikin rago ta gyara ta d’aura kan wuta tare da zama tana taya su baba jummai aiki, sai hanata suke amma taqi sai da farfesun yayi ta juye a kola tare da hada coffee tasa a tray direct part din sadiq ta wuce.
a hankali ta murda kofar parlour ba kowa aje tray din tayi saman stool ta nufi bedroom, tsaye ta hango sadiq yana qoqarin saka necktie  sallama tayi tare da gaisheshi cikin fara’a ya amsa sannan ta qaraso ta amshi  necktie din tana samasa bayanta samasa ta kallesa da  murmushi  kwance  a fuskarta  ta  ce, “uncle you look so handsome” tare da masa peck shima peck ya mata tare da daukar suit dinsa black ya riqe a hannu, fatu  ta jawo trolley dinsa  suka fito parlour lokacin angel ta turo kofar tare da cewa “Daddy..! ta fada jikin sadiq hug nata yayi d’an shagwabe fuska angel tayi ta  ce, “daddy am going to miss you”
“me to angel.!
“amma daddy zaka min tsaraba teddys”
“yes angel.! washe baki tayi ta ce, “Aunty fatuha kema ki fadama daddy tsarabar da zaimaki” smile tayi tana  kallon  sadiq  kamar  yarda  yake  kallonta ta ce, “Duk abinda daddy yake so shi nake so yamin tsaraba” kallon ta sadiq yake mai cike da so da kauna sannan ya zauna saman one sitar tray ta jawo ta zuba masa farfesun a boll saboda sadiq mutun ne mai son farfesu shiyasa fatuha kullun sai ta masa dan ta faran ta masa, feeding din shi farfesun ta fara yana sha angel itama tana bashi haka suka dinga feeding din juna su cikin jin dadi happy family sannan suka fito tray din fatuha ta kai kitchen ta wuce bedroom tasa uniform tare da d’auko school bag dinta.

  Fitowar ta parlour yayi dai-dai da fitowar su Mom da Abba cikin nutsuwa ta gaishe su peck sadiq ya masu shida angel itama fatuha peck tayi ma Mom suka fice a tare mota d’aya suka shiga da sadiq driver na ja sai da aka zo school din su yayi parking, gaba ki daya idanunta sukayi rau-rau alamun zatayi kuka, suka bama sadiq hug suka fice yana kallon su har suka shige classes sannan driver ya ja mota sai airport.

Tunda sadiq ya tafi su angel suke missing nashi Mom har mamaki suke, bata ko yar rahanan sun daina idan kaga suna raha to sadiq ne ya kira waya, haka shima can cike yake da kewar su inda yake jin kamar wata yayi ba kwana uku ba.

    Akwana a tashi ba wuya wajan Allah yau kwana sadiq biyar kuma yaune ranar dawowar shi, zo ku ga murna wajan su fatuha sai zuba rawar kai ake Mom sai janta take dan yanzu fatuha ta tashi d’aga yar aiki dan tuni sadiq ya yan’tata duk wani abinci da sadiq ke so fatuha ita da kanta ta masa sannan ta jera a dining area.

     Bedroom ta shige tare da yin wanka, kaya ta fido  ta rasa wanda zata sa duk wanda ta fido sai ta maida can ta hango wata red gown me stone’s, aje ta tayi a gefe ta tsantsara kawalliya ba qaramin kyau tayi ba, sannan ta zura riga masha Allah indai maganar kyau ake fatuha ta kai, angel ce ta shigo da gudu itama sanye da gown pink ta ce “Aunty daddy ya dawo?” waigowa tayi tare da yin fari da ido cike  da  zakuwa suka fito a tare  shigowar sadiq parlour kenan su fatuha suka fito, kallo sadiq ya bisu da shi mai cike da so rugawa su kayi a tare suka rungume sadiq dariya ya saki kamar  yarda  suma suke  cike  da  farin  ciki  ya  ce, “zaku kadani.! Mom dake saukowa daga upstairs dariya ta saki ta ce “Sadiq kai da yaran ka kuna dirama wallahi” smile yayi tare da hug din Mom in taqaice maku duk wani girki da fatuha tayi sai da sadiq ya ci inda yake ta binta da kallo, ganin ta  kara  girma.

      Bayan ya hutu ya fido tsaraba yabama fatuha I phone 6 waya dadi da murna wajan fatuha ba’a magana jidda kuma Tap Apple mai shegyan kyau tare da new Teddy’s haka suka dinga zuba murna baki har kunne.

         *2years letter*

     Wata kyakyawar matashiyar budurwace da baza ta wuce 16 years ba ta rugo da gudu daga upstairs gudu take amma komai na jikin ta amsawa yake sanye take da 3 quarter pink sai riga white mai gajeran hannu tana  sakin  murmushi  mai  qara  fito  da  zalla  kyanta bangaje mutun da tayi ne ya sata tsayawa chak, cikin cool voice din ta ta ce “Sorry ..! tare da ra6awa ta gefansa ta wuce mutuwar tsaye majeed yayi yana binta da kallo jin  wani  abu  ya  harbi  zuciyarsa  lokaci  daya kafadarsa ya d’age tare da sakin killing smile yabi stair’s din da kallo, yana  ayana  yarda  ya  ganta wai gowa ya kuma yi ko zai ga yarinyar amma ba alamar mutum sauke  ajiyar  zuciya  yayi.
sama ya haura direct part din sadiq ya wuce a hankali ya murda handle din kofar ya shigo, sadiq na zaune saman three sitar yana kallon news cikin sallama ya qaraso amsa masa sallamar yayi tare da aika masa harara wasa ya  ce, “sai yau zaka nemeni dan raini senses? dariya majeed ya saki tare da cewa “Sorry” ya zauna yana  cewa, “ni dai yanzu ba wannan zancan ba wacece na gani yanzu kamar daga part din nan ta fito? gaban sadiq ne ya yanke ya fadi qaqaro murmushi karfin hali yayi ya ce “Fatuha ce” *(Ohni salma🤦‍♀ yaushe fatuha ta waye haka🙄lol)* ok majeed yace tare da cije lips dinsa  yana ayana  wasu abubuwa a ransa……hmmmm

Muje zuwa fan’s😘

Vote
Comment

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best ★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                 71_72

Ina matukar Godiya ga masoyan wannan novel, ina jin dad’in yadda kuke bani goyan baya wannan shafin naku ne duk masoyin CAPTAIN SADIQ*

      Ko da fatuha ta shiga bedroom wayar tace ta hau ruri dake bedside drawer, cikin fara’a ta d’auka saboda sunan dake maqale a screen din wato Hanan, daukar wayar tayi tare da kallon screen din kasancewar video call ne saman bed ta haye ta  ce, “Hey yan’mata ya kike?
“lafiya lau, wai yaushe zaki zo gida ne? ina so muje gidan Ammi birthday din Basma ya kusa?
“a ina za’ayi birthday din? inji fatuha
“kema kin san ba’a gida za’ayi ba”
“Chab aikin san halin uncle wallahi ba zai barni naje ba”
“nifa matsala ta dake kenan wallahi, ke komai uncle komai shi.! shi..!
“Eh naji din.!
“yanzu dai ki masa dubara sai muje”
“gaskiya ina tsoran fushinsa kin manta randa muka je birthday din haulat kenan?
“wallahi ban manta ba ina sane ras,”
“toh yayi kyau, amma fa zan shigo insha Allah”
“to shikenan ki gaishe min da angel”
“tam.! ta katse wayar tare da kwaciyarta tana  tuna kyakyawar  captain sadiq wadda  bata  gajiya  da  tozali  da  ita har  rana  mai  kamar  ta  yau  kankame pillow tare  da  lumshe  ido.

    Kamar yarda suka saba idan suka had’u haka suka dinga zuba hira tare da yin musu, dama sun saba baza su taba rabuwa ba, ba tare da sunyi musu ba, amma duk wannan hirar da suke majeed tunanin fatuha na maqale a ransa cike  da  begen  sake  tozali  da  ita  karo  na  biyu, kiran sallah magrib ne ya tashe su, d’auro alwala sukayi suka wuce masallaci.
Basu dawo gida ba sai bayan sallah isha, ko da suka dawo majeed bai shiga gidan ba daga waje ya tsaya tare da jan motarsa yana tunanin ta inda zai 6ulo domin  ya  kara  tozali  da  fatu  tattausan murmushi  ya  saki  yana  tuna  kyawuta mai  gusar  da  nutsuwar  wucin  gani, wannan  lokacin  sam  ba  zaiyi  wasa  da  damarsa  ba dan a gaskiya a shirye yake da ya aure ta kota halin kaka…….hmmm tofa..!

    Ko da sadiq ya shigo gidan Mom na zaune a parlour ita da angel suna kallo, kallon parlour sadiq yayi tare da cewa “Angel ina Aunty?
“tana bedroom Dady” ok yace sannan ya haura sama ko minutes 5 bai yi ba ya dawo parlour tare da wuce wa bedroom din fatuha, zaune take saman bed tana assignment da laptop tana sanye  da rigar bacci dai-dai gwiwa sai gashin kanta data nanad’e sa kamar ganmo.

        Bud’e kofar da akayi ne yasa ta d’aga eye’s ball’s din ta  saki  tattausan  murmushi ta ture laptop din dake  gabanta  tana qoqarin tashi, harara sadiq ya aika mata, tare da cewa, “Ina car Key’s dina?” zuburo baki tayi gaba sadiq  ya  cigaba  da  cewa, “wato kin rai nani ko? shine zan fita kika d’auke min car key’s kika boye”
“sorry uncle, bana so ka fita ne ka sha rana, kuma da ka fita ai da bakon ka bai same ka ba, am sorry.! tasa hannuwata biyu a kunne ta langwabe  kai  ta  ce, “Allah yaba ka  hakuri” matsowa sadiq yayi kusa da ita har tana jin saukar numfashinsa ja mata baki yayi har sai da ta saki yar qara, ta6e baki tayi tana shirin yin kuka cikin  wata  irin  murya can  kasan  makoshi  sadiq  ya  ce, “kul kika min kuka wallahi yau sai kin kwana kina kneeldown, kuma kin san zan iya, bani key’s dina,” bedside drawer ta bude tare da zaro key’s din ta miqa masa tana qoqarin komawa saman bed  jawo hannuta sadiq yayi yana qare mata kallo ba qaramin kyau ta masa ba, lumshe ido yayi tare da ware su a kanta murmushi fatuha ta saki mai cike da sakonni iri-iri wani langwabe kai  sadiq  yayi  yana  binta  da  kallon  qasan  ido  ya  ce, “rufe idanuwan ki kiga wani abu” cikin sauri da zakuwa fatu ta lumshe idanuwanta wani d’an kit ya fido tare da bude kit din ya  ce, “oya bud’e.! wata hadadiyar sarkar gold ce sai  sheki  take da  walwali kallo  daya  zaka  mata  kasan  ba  qaramar  sarqa  ba  ce  bude  baki  fatu  tayi  tana  kallon  sarqar wani irin ihu fatuha tasaki  tare da rungume sadiq, shima rungume ta yayi tare da kai hannu saman gashin kanta ya warware daurin data masa ya  kwanto  gadon  bayanta, cikin cool voice sadiq  ya ce can  kasan  maqoshi yarda  sai  fatu  zata iya  jinsa  cikin  rad’a ya  ce, “Gashin ki yafi kyau a haka..! smile tayi tare da dagowa daga fafad’an qirjinsa da murmushinta  mai  qara  mata  kyau ta juya masa baya tana facing din dressing mirror tare da matsar da gashin kanta gefe tana  kallon  sadiq  ta  cikin  mirror a  hankalin ya  kwance  sarqar lumshe  ido  fatu  tayi  tana  jin  yarda  hannu  sadiq  ke  yawo  a  dokin  wuyanta, samata sarkar yayi ya  tsare  ta  da  ido  ya  jin  farin  ciki jin  shuru  yasa fatu  ware  ido  ta  sauke  su  kan  sadiq  daya  daura  kansa  saman  kafadarta,  suna  kallon  juna  ta  cikin  mirror ba qaramin kyau sarkar ta mata ba da  murmushi ta juyo  tare da cewa, “Uncle na gode” murmushi sadiq yayi ya  ce, “nike da godiya fatuha yau kusan shekarana uku bana tunani, bana zuwa asibiti kin  zamar min  wani  bangare  na  rayuwata” murmushi ta saki tare da fita daga d’akin da  sauri.
tana Isowa parlour ta fad’a jikin Mom tana  cewa, “Mom kin ga sarkar da uncle ya siya min? murmushi moym tayi irin nasu na manya ta  ce, “amma dai gaskiya mun gode wannan kyau ta haka” lokacin yayi dai-dai da fitowar sadiq daga bedroom din fatuha, angel ce ta turo baki ta ce, “Daddy ni fa☹?” ja mata kumatu yayi tare da fido mata zube na gold ya sa mata murmushi ta saki ta  fada  jikin  sadiq  ta  ce, “love you daddy” tare da yimasa peck Mom  ta  ce, “lallai abin ma yar haka ce kenan? yaran ka kawai ka sani ni kuma ko oho” Mom ta fada, bayan Mom sadiq yaje tare da zuro kansa a wuyanta ya  ce, “sorry Mom next time siyayarki  ce  ke  kad’ai kin ji”  d’an smile Mom  tayi tare  da  shafa  sumar  kan  sadiq shima zagayowa yayi ya zauna sun dad’e suna hira sannan kowa ya wuce bedroom dinsa.

      Bangaran majeed ko cikin farin ciki ya koma gida, ko da umyma ta tanbayesa sai ce mata yayi ya kusa cika mata burin ta, murna ko har ba’a magana ko da ya koma d’akinsa da ya rintse ido fatuha yake gani tana  sakin  murmushinta  mai  tafiya  dashi haka ya dinga juyi saman bed har bacci barawo ya sace shi.

       *Asuba ta gari*

     Kasancewar yau weekend fatuha ta shiga kitchen tare da su baba jummai suna aikin suna zuba hira kunsan a tare suka gama komai, da misalin karfe 10:30 take tsaye gaban dining tana jera kayan abincin  cikin nutsuwa sallamar da kayi ne yasata dagowa tare da kallon kofar ta amsa a taqaice majeed ne, sanye cikin shada ash tasha aiki sai kamshi yake zubawa yana  fad’ad’a  murmushisa dining area ya nufo tare da yin smile fararan hakoran sa suka bayana. gyara murya yayi tare da cewa, “Dama ashe kyawawa na aiki? gaskiya kamata yayi ace warhaka kina can d’aki kwance kina bacci” d’agowa fatuha ta d’anyi a tunanin ta tuntuni ya shige ciki dan tasan kowaye a gidan saboda tasha ganin pics nashi dan murmushi ta saki cikin yauki ta ce, “Suwaye kyawawa anan? naga dai ni kad’ai ce”  ta ida zancan tana wai gawa  murmushi ya kuma saki a qaro na biyu ya  ce, “fatuha kenan duk inda wata kyakyawa take kin kai ai, idan ma baki sani ba to yau zan fad’a maki, wallahi kin hada duk wani abun da ake nema wajen wata y’a mace..! yar dariya ta saki ta  ce, “yau uncle da tsoka ka zo gidan nan ko? Ko  dai yau ranar tsokana ce? bata ida rufe bakin ta ba sadiq ya shigo sanye da kayan gym dinsa da alama daga gym ya dawo, tunda yaga fatuha da majeed tsaye gabaki daya annurin fuskarsa ya sauya kamar an aiko masa da mutuwa daurewa yayi ya qaqaro murmushi ya  ce, “my man da yaushe ka shigo?
“yanzu na shigo bama kowa parlour sai wannan kyakyawar dake ta faman aiki, ni fa a ganina ko kallonta kake ya isa ya kosar da mutun daga yunwa” wani irin kallo sadiq  ya wurga ma fatuha tare da bin kayan jikinta da kallo gown ce mai kyau sai dai ya matseta duk wata sura na jikinta ana gani, ganin kallon da sadiq ya mata yasa ta barin parlour ba shiri, majeed kuma ya bita da kallo har yana cewa, “har zaki gudu? ko tanka masa ba tayi ba ta shige bedroom, wai gowa yayi yana kallkn sadiq ko lura da irin canjin da fuskarsa sadiq tayi baiyi ba ya haura upstairs, sadiq ya biyo bayansa.
bayan sadiq yayi wanka ya shirya cikin qananan kaya daya saba sawa suka fito tare da majeed dining area suka nufa, lokacin kowa ya halara gaishe da su Mom sukayi a tare, tare da jan kojera suka zauna Mom  ta  ce, “a’a yau wanake gani a gidan nan  da  fara  safiya? dan murmushi majeed yayi yana sosa keya “lallai kam ka kyauta, amma dai wuni ka zo yi?
“eh mana Mom  ki sha kurimin ki Mom nama kusa kwaso  kayana na dawo nan da zama” ya ida zancan sa yana sunkuyar da kan sa kasa, dariya Mom da Abba sukayi sadiq ko ya cika fam kamar zai fashe, jawo plate fatuha tayi zatayi saving  sadiq kamar yadda ta saba, sai da ta gama samasa nashi zatayi saving  majeed ya fakaici idanuwan su ya riqe hannu  fatuha alamar kar ta zuba bata dau abin komai ba a tunaninta hutar da ita yake son yi, ta zauna ta fara cin abincin ta sadiq ne yayi saving majeed da kansa sannan suka fara break duk wata loma da majeed zai kai sai ya kai kallonsa kan fatuha idan sukayi ido hudu ya aika mata killing smile dinsa duk wannan abun a qwayar idanu sadiq, yake  faru sosai  ransa ke 6aci ganin  kamar  itama  fatu  na  maida  masa  da  martani lokaci  daya  annurinsa  ya  d’auke  abincin  ya  gundiresa, cikin bacin rai ya ture plate din dake  gabansa cike da masifa da zafin rai ya bar dining,  kallo su Mom suka  bishi da shi, fatuha ce tayi qoqarin tashi Mom ta ce, “Kyale shi ki cigaba da cin abincin ki, tunda kika ga haka ba qaramin abun  ke  damun  sa  ba”  d’aga kafada majeed yayi tare da cewa, “Indai sadiq ne ai ba yau ya saba haka ba, yanzu  ne  yayi  sauki” tunda sadiq ya bar dining fatuha ta rasa nutsuwar ta, tunda safe ta lura yake d’acin rai ta rasa dalili…hmm!

    Ko da ya shiga part dinsa a parlour ya zauna tare da lumshe ido wani irin bacin rai na damun shi, kuma  gashi ya rasa dalilin haka dafa shin da akayi ne yasashi ware eye’s ball’s dinsa fatuha ce tsaye da plate a hannu ta cikin cool voice ta ce “Uncle please kayi break koma waye ya 6ata ma rai kayi hakuri” ta ida zancan tare da zama tana miqa masa plate amsa yayi ya aje gefe yana kallon fatuha kamar me neman wani abu a fuskar ta can Kuma ya kauda kai tare da  cewa, “zanci kin ji tashi ki je bana san magana ne” ya fadi yana lumshe ido fita ta zo yi lokacin yayi dai-dai da shigowar majeed  bigewa su kayi da junan su, “ohshh..! majeed yace haka ma fatuha ta  ce tayi baya waigowa sadiq yayi yana kallon su wani miyau mai daci ya hadiya, dariya fatuha ta saki tare da cewa “Sorry uncle.! majeed ya ce, “tunda nazo gidan nan kike bige ni, har saida kika bige zuciya ta” zaro ido waje fatuha tayi tana dan kule bakinta ta ce “Kai uncle..! ba ruwana” ta fadi zancan tana ida fita duk  da  bata  gane  nufin  Majeed ba, ritse ido sadiq yayi tare da dunqule hannuwansa lokaci  daya  jijiyar  kansa  ta  taso yana mai da numfashi sama-sama majeed ne ya dafa shi lumshe ido yayi, a hankali yana jawo nutsuwarsa zagayowa yayi ya zauna yana  cewa, “big man ina tunanin ka daina zafin rannan naka ashe har yanzu kana yi, wai ma waya bata ma rai haka big man?
“kawai am not in the mood shiyasa”
“eyya sorry ko alura ce ta motso? ya fadi yana dariyar shaqiyanci pillow kujera sadiq ya wurga wa majeed  ya  ce, “wallahi ka rainani kai naka bai tashi ba sai nawa,” dariya  majeed ya  saki  ya  ce, “kasan me Ammi ta ce?
“a’a sai  ka  fadi”
“ta ce wallahi next meeting idan bamu fido mata ba wallahi auran dole zata mana, ni dai nayi mata very soon zaku santa, amma kai ban sani ba kana nan kana ruwan idon nan naka” dan ta6e baki sadiq yayi tare da cewa, “Ba wani ruwan ido har yanzu banga wadda ta dace dani bane shiyasa..!
“ko? za kayi bayani sanda Ammi zata kwasoma yar kauye,.! dariyar yake  sadiq yayi tare da d’aukar remote control…
Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM

73_74

this page is for you ummin mama

Sai bayan sallah isha majeed ya bar gidan su sadiq, bayan sadiq ya dawo party din shi ya wuce yana shiga yaci qaro da angel na kallo cartoon, murmushi ya saki tare da cewa, “my Angel? ya qaraso kusa da ita ya zauna peck ya mata a goshi angel ta ce, “daddy.!
“yes dear.!
“please gobe muje shan ice cream please daddy”
“sweetheart gobe ba time kin ga akwai work amma idan na dawo da wuri zamu je kijin angel”
“ok daddy, daddy yau a nan zan kwana” ta ida zancan ta cikin shagwaba dan ja mata hanci sadiq yayi tare da cewa, “Yanzu kin zama big girl fa? ko baki gani yanzu fa you are 9 years old ko baki sani ba? smile tayi ta ce “Haka kuma nima daddy zan zama kamar Aunty fatuha ko idan na girma?
“yes mana..! smile ta saki tare da yi masa peck a goshi ta ce, “good night daddy”
“night angel.

Fatuha ce tsaye gaban dressing mirror tana feshe jikinta da turare da alama shirin bacci take, dan kayan bacci ne a jikinta pink da ratsin green riga ce dai-dai gwiwa mai dan siririn hannu bayan ta kamala shirin ta, ta baza gashin ta har gadan bayanta. tsurawa dressing mirror ido tayi tana tuna lokaci da sadiq yasa mata sarka lumshi ido tayi tare da daura hannuta saman wuyanta tana tuna movement din da suka kasance da sadiq jiya dayake sa mata sarqar saurin ware ido tayi tare da cewa “you are very stupid fatuha..! tare da fita daga daki’n tana sakin tattausan murmushi.
bedroom din angel ta shiga lokacin har ta shirya cikin night dress din ta, tana kwace cikin blanket, a hankali fatuha qaraso kusa da ita ta zauna bakin gado tana shafa forehead din angel ware ido angel tayi kasancewa bacci bai dauke ta ba shafa gashin kanta fatuha tayi ta ce, “Angel bakiyi bacci ba?”
“uhm yanzu na dawo daga party din daddy”
“ok.! peck fatuha tayi mata tare da gyara mata blanket din ta kashe haskyan daki’n tare da rage gudun AC dakin ta fita.

Ko da fatuha ta fita kitchen ta shige ta had’a coffee ta daura cup din saman tray ta haura saman, a hankali tayi knocking din kofar, “come in.! aka ce hakan yasa fatuha bude kofar a hankali ta shigo, sanyi AC ke tashi da kamshi na musanman cikin fara’a ta qarasa shigowa sadiq na zaune saman three sitar sanye da night dress din shi blue masu taushi wando da riga, cikin nutsuwa ta samu guri ta zauna saman one sitar, miqa masa glass cup din tayi amsa yayi yana smile kurba biyu zuwa uku yayi tare da kallon fatuha ya ce, “kamar akwai magana a bakin ki” dan murmushi tayi tana wasa da yatsun hannu ta, “ina jin ki.!
“uncle dama-dama uhm gobe ina so naje family house ne ni da Hanan” wani irin miyau sadiq ya hade take nan coffee ya fita ransa, “waza taje gani family house ? ya fada cikin zuciyar sa qara hada rai yayi kamar an aiko masa da sakon mutuwa majeed ne ya fado masa a rai qara tsuke fuska yayi ya ce “Ban shirya ma zuwan ki family house ba” ya fadi a taqaice, “uncle…! d’aga mata hannu yayi ya ce “Yawon yayi yawa ina laifin kije gidan Aunty bilki, next time kin je can din” ya fadi a taqaice dan murmushi tayi wanda iya karshi la66anta, saboda bata san gardama da sadiq ko dan karya bata ransa ta ce, “Toh..! qoqarin fita ta take jiki ba qwari jawo ta sadiq yayi ta fado saman fafadan qirjinsa dariya fatuha ta saki tare da dan dukan qirjinsa cikin wasa, murmushi ya saki tare da d’ago da habarta ya ce “Na dauka kinyi fushi da uncle ne? dan 6ata fuska tayi tare da daura hannuta gefan fuskarsa tana kallon kamar yarda ya tsare ta da shanyayin idanusa ta ce, “bana fushi da uncle kuma ba zan fara ba..! Kuma dama can gidan Mami nayi niyar zuwa Hanan ce tace na tanbaye ka muje can” qarewa lips dinta kallo sadiq yake har ta kai aya yana jin wani sanyi na ratsa sa tunda daga d’an yatsan sa har zuwa kansa ya ce, “Ok.! zame jikinta daga na Sadiq tayi ta ce, “Uncle bari na tafi”
“ok har kin fara jin bacci ne na dauka hira kika zo taya ni” har lokacin hannu fatu na cikin na sadiq yana murzasu a hankali dan smile tayi wanda ya bayana fararan hakoran ta ta ce “Ba bacci nake ji ba kawai zan tafi ne saboda bana son dare yamin a nan ina jin tsora fita ni ka dai” d’aga gira sadiq yayi wanda ya kara bayana kyansa ya ce, “ok good night.! ya saki hannuta har ta kai bakin kofa ta jiyu ta ce “uncle zaka taya ni hira kafin bacci ya dauke ni?”
“yeah..!
“ok zan kira ka video call idan na je bedroom” dawowa tayi ta masa peck a goshi sannan ta fice daga part din.

Ko da ta koma bedroom laptop ta kunna, a bangaran sadiq ma haka kiran fatuha ya shigo laptop din sadiq dauk’a yayi yana kallon ta kamar tana gabansa, yana shan coffee yana kallonta suna magana surutu ta cigaba da zuba masa yana dariya, har cikinsa na kulewa haka itama sosai sukayi hira inda sadiq yake jin bacin ran dake damunsa ya tafi, har tayi bacci suna video call smile sadiq yayi ganin fatuha tayi bacci sannan shima ya kwanta, amma duk da haka ya kasa kashe laptop din kuma ya kasa kauda idanuwasa daga kanta yarasa dalilin da yasa inda yana tare da fatuha yake bata guri na musanman a zuciyarsa wasu abubuwan bai san yana yi ba idan suna tare so da yawa ya kan manta kansa idan yana tare da fatu, ita ka dai ce macan dake ganin murmushinsa fara’a shi da halinsa da wannan tunanin bacci ya dauke sadiq ba tare da ya kashe laptop ba.

*Asuba ta gari*

Addu’a cike a bakin ta tashi tana miqa d’auke, laptop din ta dake saman bed take qoqarin sadiq ta hango kwance yana bacci, mai cike da birgewa da jan hankali murmushi ta saki tana qare ma kyakyawar face nashi kallo hannu ta kai kan screen din laptop din tana shafawa can kuma ta janye hannuta, daukar laptop din tayi ta aje saman sofa yadda zata dinga hangosa duk abinda take, toilet ta shige ta watsa ruwa tare da dauro alwala daure da towel ta fito ko da ta fito lokacin sadiq shima ya tashi dan ba alamarsa ta cikin laptop din baya saman bed, cikin sauri ta shirya tare da gabatar da sallah sket din makarantar ta ta jawo tasa tana gama sawa ta zura rigata tana 6ale ma6alin riga ta, ta hango sadiq tsaye shima yana 6ale nashi dariya suka saki a tare ta ce, “morning uncle.!
“morning too dear, kin rigani tashi na riga ki shiryawa baki da sauri” dan turo baki fatuha tayi ta ce, “dama can ka tashi idan ba” yar dariya sadiq yayi ya ce, “kwarankwatsi ban tashi ba” fashe wa da dariya fatuha tayi saboda tasan tsokanarta sadiq yake da kalamanta na da kashe laptop din yayi domin ta qarasa shirya wa.

Kusan a tare suka fito lokacin angel har ta shirya cikin uniform din ta tana dining area ita da Mom da Abba cikn nutsuwa suka qaraso, gaishe da su Mom su kayi suka amsa a tare sannan suka ja kujera suka zauna saving din su fatuha tayi sannan suka fara break cikin jin dadi bayan sun kamala peck sukayi ma Mom, Abba ne ya ce, “lallai gidan nan ana gwada min banbanci jiya ina kallo Mom dinku kukayi ma peck, ni kuma ko oho ba komai zan rama” dariya sukayi su duka tare da ba Abba hakuri kusan a tare suka fito Mom ta rako su har bakin kofa yaran sadiq sai qamewa suke, shigewa motoci sukayi Abba ya shige nashi suka bar harabar gidan.

Sosai yau sun sha karatu har da test sai da sukayi na history sosai fatuha ke maida hankalin ita da kawayan ta, Nana da Zara sune kawayan ta na makaranta kuma yan’yan masu kudi ne masu ji da wayewa da yan matanci, fatuha ko tun tana jss2 ta zana JSSCE saboda qoqarin da hazaqa yanzu haka SS2 take Hanan na SS3 Basma kuma ta gama, Nana ce ta kalle ta bayan uncle ya fita daga class ta ce, “Niko fatuha ina wannan uncle din nan naki mai kyau?” kallon ta fatuha tayi tare da aika mata harara lokaci daya ta canza fuska kamar ba ita ba ta ce, “ina ruwan ki da uncle dina?
“laaa fatuha yaushe kika zama haka? inji Nana, Zara dake gafe ta ce, “Karki ga laifin ta wallahi ai dani ce fatuha da tuni na samawa kaina mafita wallahi”
“hmmm wai me kuke nufi ban fa gane wannan hausar taku ba? fatuha ta fada yar shewa Zara da Nana sukayi lokaci daya suka ce, “wallahi rainin hankalin nan namin dadi serious, to bari kiji ki zauna nan kwado ya maki kafa, wallahi dani na samu damar ki da tuni na dama wallahi” inji Nana.
“ku dai baku da aikin yi ni ina da, uncle matsayin yayana na d’aukesa ba komai ba”
“Allahu Akbar” su Zara suka hada baki wajan fada duka fatuha ta kaima Nana da Zara da littafin dake hannu ta.

***
Basma ce zaune ita da Umma tana taya ta kwalema a d’akin ta, pictures din sadiq ne ya fado hannuta kai ta dauka ta kurawa hotan ido tana kallon tana shafawa sam ta manta da Umma na wajan ta lula duniyar tunanin sadiq.
Umma ce ta ta6a ta firgigit ta dawo daga duniyar tunani duk ta daburce tana qoqarin aje hotan, dan murmushi Umma ta saki na su na manya ta ce, “yar auta me ke damun kine kwana biyu naga duk kin rame kin zabge kamar mara lafiya” hawayan dake maqale a idanuwan tane suka zubu tare da riqe hannu umma, tac e ” Umma na rasa me ke damuna tun zuwan da yaya sadiq yayi kwanaki na rasa meke damuna wallahi umma,😭 ina son yaya sadiq tun ba yanzu ba” ta ida zancan tare da rushewa da kuka ta ce, “ko kallo na bayayi..! lallashin ta Umma ta shigayi da cewa, “haba auta me abin kuka? share mata hawaye Umma tayi ta ce, “duk wata mace mai lafiya dole taso sadiq saboda ya tare duk abinda mata ke so Basma ban ga laifin ki ba, insha Allah zan taya ki da addu’a, idan sadiq alheri ne a gare ki Allah ya baki shi, idan ko haka ta faru sai nafi kowa farin ciki, kinga sai a hada da naki dana majeed tunda shima jiya yake fada min ya samu wadda yake so suna dai-dai tawa da ita” murmushi Basma ta saki tare da fita daga dakin da gudu cike da farin ciki Umma ta bita da kallo tayi murmushi irin nasu na manya.

*****
Misalin karfe 12:30pm suka tashi daga makaranta kasancewa yau friday angel na gefan ta suna jiran drive, hadadiyar motace baka ta faka gaban su fatuha kauda kai fatuha tayi kamar motar ba gaban su ta tsaya ba, saboda glass din motar tinted ne ko na ciki ba’a gani zuge glass din akayi hakan yasa angel washe baki tare da cewa “Second daddy?” majeed ne sanye cikin uniform din shi na aiki murmushi ya saki bale murfin motar angel tayi kamar tana jira ta shige gaishe shi fatuha tayi a taqaice tare da cewa, “angel fito kin san driver ne zai zo daukar mu” ta fada, murmushi majeed yayi ya ce “To ni zan d’auki kyankyawa yau na kai ta har gida dan tun dazu na kori driven, ni zan zama driver yau” dan zaro ido waje fatuha tayi ta ce “Sokake uncle ya mani fada ko?
“ah uncle ba zai maki fada ba ai yasan ni zan dauke ku, ni da shi ai duk daya ne ko baki sani ba? dan smile fatuha tayi wanda iyakar shi la66an ta ta bude murfin motar ta shiga cikin nutsuwa ya ja motar, yana driven yana kallon fatuha ta cikin mirror sai da ya zo dai-dai bakin geta yayi horn bala mai gadi ya bude masa geta parking yayi su fatuha suka fito tare da masa godiya sai da suka shige cikin gida yayi ribas ya fita.

Shiga office din majeed sadiq yayi amma wayam ba majeed dan ta6e baki yayi tare da fitowa daga office din, da khaleed ya ci karo wanda shigowarsa yanzu kenan cikin fara’a sadiq ya tarbesa khaleed ya ce, “Ah wai har yanzu majeed bai dawo ba?
“oh kama san da fita kenan”
“eh munyi waya nace masa zanzo shine yace min yaje daukar baby shin daga school..!
“baby.! sadiq ya maimaita ya ce, “bansan sanda majeed zaiyi hankali ba wallahi mtww” yaja Khaleed suka wuce office din shin.

Bayan sunyi lunch fatuha ta shirya tsaf cikin lace din ta yellow anmata dinkin bubu da lace din sosai kayan sun fidota da ita abunka da fara fata, dan kwalin ta ta daurasa hawan-hawan daurin ya zauna kamar gwagwaro janbaki ta shafa maroon da yar hoda kwalliya sosai ta zauna ta tsantsara veil din ta ta dauk’o white ta yafa masha Allah fatuha ba qaramin kyau ta zuba ba,

Tana fitowa parlour ta samu Mom da majeed sunata zuba hira yana sanye da blue shada tasha aiki, cikin zazakar muryata fatuha ta ce “Mom zan je gidan mami”
“to, shikenan ki gaishe min da su”
“zasu ji, “majeed ne yayi karaf ya ce, ” Tunda tafiya nima zanyi bari na aje ki a can”
“to! fatuha tace tare da yin gaba majeed yabi bayan ta shida kansa ya 6ale mata murfin mota ta zauna sannan ya bude ma kansa ya shiga,

Ko 20 minutes basu dauka ba suka Isa gidan Aunty bilki, inda majeed keta janta da surutu har ta dan saki jiki da shi yana yin horn mai gadi ya bude ya shigo da motarsa yayi parking, qoqarin fita daga motar take majeed ya ce “Baki ji ba,.! waigowa tayi sannan ya ce, “karfe nawa zaki koma gida?
“da yama” ta fada a taqaice.
“toh! shikenan zanzo daukar ki” Godiya ta masa tare da shigewa cikin gidan.

Da gudu Hanan ta rugo ta rungume ta tana cewa, “kai amma naji dad’i wallahi kin cika alqawari” gaishe da Mami tayi dake zaune parlour tana kallo sannan Hanan ta ja ta bedroom suka baje suna ta zuba hira cikin jin dadi kai ka ce yan’uwane yadda suke nuna ma juna so sai kusan yama likis majeed ya zo gidan Aunty bilki, inda ta dingq zuba masa shaqiyanci shida sadiq sun raina ta basu san zuwa gidan ta sai da dalili shi dai sosa keya kawai yake sannan suka bar gidan suka nufo gidan.

motar sadiq ce ta kunno kai cikin unguwarsu driver na ja, shi kuma yana baya, motar majeed ta wuce su gyaran murya sadiq yayi ya ce, “Wancan motar kamar ta majeed?
“yallabai ita ce ai dazu dana zo daukar fatuha, Hajiya tace min ai majeed ya kaita to qila sun dawo ne? Ras-ras kirjin sadiq ya bada wani qulolin bakin ciki ya tsayawa sadiq har yana jin ya qasa hadiye miyau.
kusan a tare suka shigo gidan sai da fatuha ta fito majeed shima ya fito murmushi fatuha ta saki tana ma majeed godiya, qoqarin bude kofar motar driver ya ke sadiq yayi magana cikin daka tsawa “karka bude.! ya fadi, shi kan shi driver sakatarere yayi da mamakin canji sadiq lokaci d’aya zaunawa sukayi a mota sadiq na hango fatuha da majeed, har tayi gaba ta dawo ta ce, “oh na manta wayana a mota” smile majeed yayi tare da bude motar ya curo wayar ya bata, tare da cewa, “gaskiya yadda na dako wayar nan ya kamata ki bani number ki” dan murmushi tayi ta ce, “uncle number ta?
“eh mana ko baza’a bani ba?
“zan baka mana” curo wayarsa yayi dake gaban aljihu ya bama fatuha ta rubuta maaa number ta sannan ya shige mota ya bar harabar gidan.

Yana fita sadiq ya bude murfin motarsa cikin zafi rai idanusa rufe da wani irin kishi mai tsanani wanda bai san yana da shi ba sai yau, shigar fatuha bedroom ke da wuya taji an banko kofar d’akinta cikin zafin rai waigowa tayi a dan tsorace tana kallon sadiq take bakin kofa idanusa sun rine da ja, gaban fatu ne ya yanke ya fadi da ganin yanayin sadiq ba tayi aune ba ya fisgota ya fizge wayar da dake hannu ta yayi wurgi da ita ta bigi bango ta dawo kasa a tarwatse ware ido fatuha tayi jikinta na rawa rike da bakin ta ban da rawa ba abinda jikinta yake tana ja da baya cike da tsoran yanayin sadiq tare da sakin kuka, manna ta sadiq yayi da bango ya koma mata kamar zaki idanuwashi sunyi jawur kamar garwashi cikin kakausar murya ya ce, “Waya baki izini fita gidan nan bada driver ba?” kuka fatuha ta kuma saki ko bakin magana ta rasa saboda tsawar da sadiq ya daka mata ganin bata da niyar bashi amsa yasa sadiq sakinta tare nufar kofar fita ya banka ta da karfi ya fita hata Mom dake part din ta sai da taji bugun kofar da sadiq yayi, zame wa fatuha tayi awurin tare da sakin kuka, koda sadiq ya shiga part nashi cili yayi da briefcase din shi saman three sitar ya zauna tare da lumshe ido yana maida numfashi sama-sama, ware idanuwan shi yayi saboda d’aya rintse fatuha da majeed ya yake gani shafa ganshin kansa yayi ya ce, “noooooo.!! Cikin d’aga murya……..

Vote

Comment
Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.co m/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_ speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM

                     75_76

      Sai da fatuha taci kuka ta gaji sannan taja jiki ta hau saman bed, tarasa dalilin da yasa mai kyau yake yin irin haka, kuka ta kuma rushewa da shi data tuna a irin yanayin data gansa, haka ta dinga raira kuka kiran sallah magrib yasata tashi jiki ba qwari, ta dauro alwala tare da gabatar da sallah zaune tayi bisa daduma abin tausayi ganin tunanin bai fishe ta yasa ta jawo AlQur’ani tana karantawa har aka kira sallah isha.
bayan ta idar da sallah ta ja jiki ta koma bed ta cigaba da raira kukanta abin tausayi turo kofar da akayi ne yasata miqewa tana kallon kofar, angel ce tsaye bakin kofar qarasowa tayi d’akin tare da hawa saman bed din ta ce ,”Aunty waya saki kuka? murmushi fatuha ta qaqaro wanda iya karshi la66an ta ta ce “Ido nane ke ciwo”
“sorry Aunty, ki fito parlour kuyi dinner naji shuru ne baki fito ba ke da daddy, shiyasa na biyo ki daddy dai yace ya koshi, ko kema kin koshi ne? ta fadi zancan tana kallon fatuha dan smile tayi ta ce, “ban qoshi ba ina nan zuwa naci komin dare” fita jidda tayi daga daki’n fatuha ta cigaba da raira kukanta har sai da kanta ya fara ciwo, ganin bame lallashin ta yasa tayi shuru tana sauke ajiyar zuciya bacci barawo ya sace ta.

     Bangaran sadiq  ban da juyi saman bed ba abinda yake yana tunanin  abinda  idonsa  ya  gane  masa, dakyar ya samu ya rintsa.

          ASUBA TA GARI

  Ko da fatuha ta tashi jiki ba qwari tayi sallah sannan ta qara komawa ta kwanta saboda kanta dake  mata ciwo, kuma taci sa’a yau weekend ba ita ta tashi ba sai karfe 11:30pm ware ido tayi tare da kallon agogan dake makale a bangon d’aki, cikin sauri ta mike ta shiga toilet ta watsa ruwa.
ko da ta fito mai kawai ta murza sai after dress data zura parlour ta fito ba kowa, dining area ta wuce ta bud’e kulolin dake jere wanjan, chpis ne da farfesun yan’ciki zubawa tayi a plate ta had’a ruwan tea sannan ta zauna, cike  da  kewar sadiq loma biyu zuwa uku tayi ta ture plate din dan kwata-kwata bata jin dad’in abincin.
Babban abinda ke daure mata kai ta rasa laifin da tayi, yanke shawarar zuwa bama sadiq hakuri tayi, duk da bata san laifin data masa ba dan bata iya jurewa wannan horan na  rashin  ganin  sa  da  saurara dad’ad’an kalamansa  masu  sa  nutsuwa  da  kwanciyar  hankali,  tashi tayi tare da kwashe kwanika ta kai kitchen sai da suka dan ta6a hira da su baba jummai sannan ta fito.

        Direct part din Sadiq ta wuce a hankali ta murda handle din kofar tare da shigowa cikin sallama zaune sadiq yake saman two sitar da laptop gabansa kallo d’aya zaka masa kasan baya  cikin  dad’in rai zaka  gane  akwai  abin da ke  damunsa fuskar nan  nasa babu annuri ya  koma  captain sadiq  na  da  sak bakin  fatu  na  rawa  ta  ce, “Uncle..!  dogo kai yayi ya kalli fatuha tare da lumshe ido ya kauda kai ya ce, “Just leave me alone” sadiq ya fada a tsiwace tare da tatara takadunsa dake gabansa da laptop dinsa ya shige bedroom tare da buga kofar da karfi, har  saida  fatu  ta  razana  da  yarda  ya  buga  kofar kafarta  kasa  daukar  gangar jikinta  yayi  saboda  tashin  hankali  na sauyawar  sadiq  lokaci  daya kuka fatuha ta saki tare da fita daga part din da gudu jin ta fita yasa sadiq jingina da kofar bedroom ya lumshe ido har  cikin  ransa  yake jin  sautin  kukanta, amma  kishi  ya  hana sa  saurara mata.

      Da gudu ta wuce Mom a parlour ta shige daki saman bed ta fada tare da sakin kuka maicinrai har  da  shesheqa, kuka taci ta gaji.
Mom dake parlour bin fatuha tayi da kallo tana mamakin mai ya hada su da  sadiq  haka, koma dai menene ai sun saba zasu shirya ne amma abin mamaki basa kai haka, kauda zancan Mom tayi tare da cigaba da kallon ta.
Duk yinin yau babu wanda yaci abinci cikin su, ban da kuka ba abinda fatu take, shi ko sadiq sai bak’in rai dayake fama da shi.

    Iskace mai sanyi da ke ta kad’awa da alama ruwa za’ayi saboda damuna data fara shigowa, qara cida ce kawai ke tashi bakin window sadiq ya tsaya a hankali ruwa ke saukowa kallon ruwan yake yanda yake saukowa da karfi, a wannan karan lumshe ido yayi tare da ware su, ya koma saman bed ya kwanta jikinsa  ba  dadi.
bangaran fatuha tunda aka fara ruwa ta lullu6e cikin blanket jikinta  yayi  rau  da  fever.

      Gabaki daya yini yau ba wanda yayi ma wani magana, cikin fatuha da sadiq, horan d’aki sukayi wa kansu ba tare da sun nemi abin sama bakin sallatin su ba, ba wai  kuma  basu  jin  yunwar  bane  a’a  abinci  ne  ba  zai  samu  mahali  ba, har bacci ya kwashe su.

           Washe  gari
Shiryawa yake cikin manyan kayansa kasancewar yau zasu je family meeting, fatuha ce ta fado masa a rai kawar da tunanin yayi dan har yanzu bai huce ba ko yana hucewa sai ya dawo daga meeting.
cikin Isa yake saukowa daga upstairs, lokacin har su Mom sun shirya suna parlour zaune suna jiran fitowar sadiq da fatuha ganin sadiq ya sako yasa Mom cewa, “angel kira Aunty mu wuce.!  ko da angel ta shiga d’akin kwance ta samu fatuha qudindine cikin blanket, fitowa tayi da sauri daga bedroom din ta ce, “Grandma Aunty bacci take”
“toh fa! amma ai fatuha bata kai haka tana bacci” shiga d’akin Mom tayi tare da qarasawa wajan bed din fatuha ta ce a hankali, a hankali fatuha ware idanuwan ta da suka yi nauyi saboda tsabar kuka, kallonta Mom tayi ta ce “Mike damun kin fatuha? dafe kai tayi ta  ce,  “Mom kai nane ke ciwo”
“eyya sorry dama meeting zamu tunda baki jin dad’i ki zauna kawai a gida” to kawai tace tare da shigewa blanket, sannan Mom ta fita ko da ta fita sadiq ta aika ma harara tare da ayana ma ranta idan sun dawo zatayima  tufkar hanci.

       Katafarin parlour su da aka ware danyi meeting suke zaune, tunda sadiq ya shigo gabansa ke yankewa yana fad’uwa yarasa dalilin hakan addu’a da ke  bakinsa ya furta dan samun nutsuwa, duk  kuma  ya damu  da  yanayin  daya  bar  fatu yafi  tunanin  harda  hakan  ya  hanasa  nutsuwa, majeed ne ya shigo tare da zama gefen sadiq ya  miqa masa hannu suka gaisa dakyar sadiq ke danne zuciyarsa kan majeed  da bata hakuri.
Alhaji Babba ne ya shigo sanye da babba riga tasha aiki sai sheqi kayan suke, da sallama ya shigo tare da zama a kujerarsa ta musanman wato kakan su sadiq, Ammi na gefansa na dama sauran jikoki da iyaye na gefe da yan uwa.
Taro ya fara budewa da addu’a sannan ya fara jawabin cikin nutsuwa ya  ce, ” ina  maku  barka  da  zuwa Allah yasa yarda  ku  ka zo  taron  nan  lafiya  mu  koma  gida lafiya, kuma  na  ji  dadin  yarda  kuke  zuwa  wannan taro na  qara dankon  zuminci kamar yarda kuka sani ko  wani  lokaci  muna  samun  alherai  da  yawa  bangaran  kasuwancin mu  ina  ma albishir da abubuwa da yawa na farin cikin a wannan shekara mun samu kimanin billioths of naire cikin ribar kasuwancin mu, mun talafawa gidan marayu da asibitoci  mun biyawa mutun 30 kujerun maka..! kabara wajan ya dauka tare da hamdallah.
Gyaran murya Alhaji yayi  ya ce,  “Kuma ga muhimiyar sanawar Majeed ya  samu matar da zai aura..! sadiq dake zaune saman kujera gabansa ya qara yankewa ya fadi ras-ras muryar Alhaji babba ce ta dawo masa dodan kunne, “Alhamdulillah  mun  nema an bamu saboda  karamci, ba kowa bace sai yar gidan ibrahim wanda yake ruqo fatuha..! har gidan iyayan ta muje munyi bincike ashe ma akwai sanaya a tsakanin mu kuma sun aminci sun bada haka ya  mana  dadi matuqa..!  wani irin gumi ne ya karyo ma sadiq maitsananin zafi take nan ya fara ji wutarsa na d’aukewa jikinsa  rawa  ya  d’auka  jin  kalaman  Alhaji  yake  tamkar  saukar  aradu, wani  irin  amo  kalaman  suke  masa  cikin brain, ba sadiq ba hata Mom sai da ta girgiza da wannan furucin, ita  dake qoqarin  furta  abinda  ke  ranta sai  gashi an masu shigar  sauri  da  karfi  kirjinta  ke  bugawa  tana  tunanin  halin  da  d’an  autanta  dilo  zai  shiga, wata kalmar ya qara jefowa a karo na biyu “sadiq kuma mun yanke shawarar bashi kanwarsa Basma amma da sharadi idan har ya kawo wadda yake so nan da sati daya kamin asa biki to za’a basa dama ya auri wadda yake so, Basma ma kuma ta hakura wannan shine hukuncin dana yanke.! sannan ya kalli baban Basma ya  ce, “Alhaji khabiru cika mana taro da addu’a..!

      Gabaki d’aya parlour juyawa sadiq yake dakyar ya samu ya miqe, jiri  na  neman  kadasa majeed ban da murna  ba  abin da yake  finally  yanzu  zai  samu  fatu  shawo  kanta  kawai  ya  rage masa, ko ta kan sadiq bai bi ba haka Basma baki har kunne tana  ganin shawo  kan  sadiq  ya  so ta  abu ne  mai  sauki  kamar  yarda  Umma ta  sheda  mata.
sadiq ne kadai da Mom basu farin ciki, sai Hanan da tashin  hankali  ya hanata  motsi  sanin  matsayin da  fatu  ta  aje  sadiq.
yana fitowa daga parlour parking space ya nufa cikin sauri ya bale murfin mota ya shiga, da gudu ya fisgi motar ya harba kan titi gudu yake tsulawa kamar zai tashi sama, ko  ganin  gabansa ba  yayi  saboda  tsanin  tashin  hankali  mara  musaltuwa,  fatu  da  majeed  abun  kamar  a  mafarki, yana isowa gida ya danna horn da  karfi  dan  sam  bai  san  mai  yake  ba, bala mai gadi na bude masa geta ya ce “Subhanilillah..! Saboda yadda sadiq ya shigo da motar da  mugun  gudu  kamar  zai  tashi  da  bala  mai  gadi.
ko daidaita parking ya kasa ya bale murfin motar ya fito, cikin sauri ya wuce part dinsa yana shiga ya zame bakin kofa tare da dafe kansa, jijiyar  kansa  duk  ta  taso  saboda  tsabar  tashin  hankali maganar Alhaji babba na dawo masa, cikin  dodan  kunne miqewa yayi ya shige bedroom saboda har yanzu bai dai na ganin jiri ba, gani  yake kamar  kunnasa  bai  ji  dai-dai ba  wani irin kuka sadiq ya saki mai tsuma zuciyar mai saurare kneeldown yayi a wurin bakinsa na  rawa  yana  furta, no..! No..! I cant believe abinda  kunne  na  ya  ji  noo..! fatali da kayan d’akin sadiq  yake kamar sabon kamu, duk  abinda  ya  dauka  ya  wurga sai  ya watse  ya  dawo  kasa sai da yayima d’akin fata-fata ya shiga toilet da kayan jikinsa sakar ma kansa shower yayi, maganganun Alhaji babba har yanzu  ke masa yawo a brain wata zuciyar ta ce “Wato jiya fatuha tabama majeed izinin turawa gidan su? Dama  fatu  ba  so  na  take  ba? Jikin  sadiq  na  rawa ya  furta  Kalaman bakinsa hadeye  kukan da yake yayi ba shiri ya fito sharkaf ya zauna kasan carpet bai damu da kayan dake jikinsa ba ya  takure  waje  daya.

      Bangaran fatuhu ko tunda su Mom suka fita gabanta ke faduwa, ta rasa dalilin haka ta rasa sukunin ta jin an bude kofar d’akin ya sata waigowa Mom ce tsaye bakin kofa murmushi fatuha ta saki wanda iya karshi la66anta ta  ce, “Mom har kun dawo da wuri haka? eh tace tana qoqarin danne damuwarta, ta  qarasa shigowa zama tayi kusa da fatuha cikin sanyi murya ta ce “Fatuha gobe da safe ki shirya zaki je wudil Baffa nasan ganin ki?” sannan ta tashi ta fita kallo fatuha tabi Mom da shi take nan jikinta ya haubari da tsoro-tsoro ko dai uncle ya kai qarata kauda zancan tayi tasan ma ba zanyi haka ba, amma zuciyarta na cike da tanbayoyi, ganin bata da amsa ta hakura.

      Ola sadiq ya kira a waya bugu d’aya zuwa biyu ya dauka, “ina san ganin ka” sadiq ya fada a taqaice.
ko da ola ya zo ganin watsin da akayima dakin sadiq ya tsorata kallon sadiq yayi da magana a bakinsa, ganin fuskar sadiq ba annuri yaja baki ya tsuke, nuni ya masa daya gyara d’akin shi kuma ya shingida saman sofa, yana  jin  wani  quna  da  suya  da  zuciyarsa  ke  masa hawaye daya na bin daya saman fuskarsa kamar ba soja ba,

      Gabaki d’aya gidan Alhaji Ibrahim ba wanda ya rintsa, daga angel sai Abba ne kawai suka samu bacci,
bangaran sadiq ban da kukan zuci ba abinda yake, fatuha kuwa tunanin me yasa Baffa ke neman take?  ko dai inna ce ta rasu? ba’a son fada mata girgiza kai kawai  tayi.

      Tunda safe fatuha ta tashi ta shirya cikin riga da sket dinta na atamfa yellow mai ratsin white a jiki masha Allah kayan sun hauta sai dai fuskarta tayi fayau, bayan ta kamala ta fito parlour cikin nutsuwa ta gaida Mom da Abba dake ta break angel na gefe itama ganin bata ga sadiq ba yasa gaban ta ya qara faduwa a karo na biyar jiki ba qwari ta zo ta hada tea kurba biyu zuwa uku ta aje Mom ce ta ce, “Fatuha har kin koshi?
“eh Mom dama idan zan yi tafiya bana wani cin abinci” to Mom tace, sannan ta qara da cewa, “ga driver nan zan had’a ku da shi idan ya kai ki yau zai maido ki, ki gaida mutun gida sannan idan kin isa ki kira ni ki fada min” lagwabe kai fatuha tayi ta ce, “Mom ai jiya wayar ta lallace”
“garin yaya?
“fadowa tayi daga saman dressing mirror ta dauke”
“eyya to bari na baki baby Nokia idan kin dawo a sake wata” to fatuha tace tare da shi ga daki ta dauko sim dinta, miqa mata wayar Mom tayi ta zura sim dinta ciki har ta kai bakin kofa ta dawo ta haurawa sama part din sadiq ta nufa a hankali ta murda handle din kofar taji kule gam tsoro ne ya kamata amma ba yadda ta iya haka ta dawo, tare da yima mom sallama angel ko sai rigama take sai tabi fatuha Mom ta hana.

     Shigewa mota tayi driver ya harba da su kan titi cikin dan qanqanin lokaci suka isa wudil, cikin kwatancan fatuha har driver ya kawo ta gida fitowa tayi a hankali tana qare ma gidan su kallo gabaki daya gidan ya canza a yadda ta san sa, mamaki ne ya bayana a fuskarta qarasa shiga tayi ciki da sallamah Inna dake  parlour ce ta fito da  murna tana yima fatuha maraba da zuwa duk da fatuha ba’a cikin jin dadi take ba bata yadda inna ta gane ba, parlour ta jata suka shiga har yanzu mamaki ne shinfide a fuskarta  tana  qarewa  gidan  na su  kallo  yarda  yayi  kyau ko  abirni  sai  haka ta ce cikin sanyin murya “inna waya gyara gidan nan? murmushi inna ta saki ta  ce, “yaron arziki sadiq wallahi shi ya mana abin arzikin nan, ya  canza  mana  gida ya  koma  kamar  aljanna  duniya” murmushi fatuha ta saki mai cike da jin dadi Baffa ne ya yaye labilan dakin ya shigo har qasa fatuha ta tsugunna ta gaisheshi amsa mata yayi a taqaice  sannan ya samu wuri ya zauna, itama fatuha qasa tayima kanta mazauni tana jiran jawabin Baffa gyaran murya Baffa yayi  da cewa, “Fatuha.!
Na’am Baffa.!
“Fatu nasan cewa na maki laifi amma kiyi hakuri ina fatan bazaki watsamin qasa a ido ba? ina fata bazaki bani kunya ba? duk wannan jawabin da Baffa keyi kan fatuha na qasa d’ago kai tayi ta ce, “insha Allah Baffa bazan baka kunya ba”
“yauwa diyar albarka, dama  nasan  baza  ki  watsamin  kasa  a  ido  ba, dama d’an uwan sadiq ne ya zo neman auran ki tare da iyayansa jiya daddare, mukanmu munyi mamaki da wannan zuwa fatuha ganin halacin da zura’a suka mana gashi nasan baban yaron hakan yasa na amince dan na lura yaron mai nutsuwa ne, Kuma dama neman auran budurwan anso iyayanta su za6a mata miji na gari da wannan nayi la’akari na za6a maki majeed a matsayin miji..! dagowa fatuha tayi a razane dan sai yanzu ta fahimci inda aka dosa   idanuwan ta taf da kwalla suka ciko  nan take hawaye suka fara anbaliya a fuskarta me yasa mai kyau zai mata irin wannan horan me yasa zai  mata  haka  dama  hukuncin  daya  dauka  kenan  dama  majeed  ne dalilin  fushin da mai  kyau  yake  da  ita  mai  yasa  bai  ji  ta  bakinta ba, fita tayi daga parlour da gudu ta fada dakin inna ta saki wani  irin kuka mai tsananin ban tausayi, inna ce ta dafa bayanta tana lallashinta cikin  tattausar murya, “haba fatuha bai kamata ki watsawa muta nan qasa a ido ba duk  halacin  da  suka  maki  banyi tunanin  haka  daga  gare  ki  ba, kuma  yaron  nan  kin  san  sa, kuma kowani mutun da qadarar dake zuwa masa fatuha idan dai majeed alkhairi ne a gare ki Allah ya tabatar ke  dai  na ki  addu’a  ne” haka inna ta dinga bitana tausar fatuha har ta samu tayi shuru tana sakin ajiyar zuciya, ko ruwa kasa sha fatuha tayi sai bayan sallah la’asar suka dau hanyar kano wayar tace dake cikin jaka taji qara message ya  shigo sai a lokacin ta tuna da Mom tace ta kira ta curo wayar tayi ta karanta message din kamar haka,

     Sister ina matukar farin cikin sanar dake yau buri na ya cika, mafarki na  ya  kusa zama  gaske, tun jiya nake qoqarin kiran ki wayar taki shiga ba wani albishir bane ila yaya sadiq ya kusa zama miji a gare ni, sannan ina taya ki murnar zama in-law a gidan mu cikin family din mu daga Basma your sister..

         Wani irin kuka fatuha ta saki mai cinrai ko qarasa karanta sakon ba tayi ba wayar ta fadi jikinta ban da bari ba abin da yake, ashuru driver ya juyo ya  ce, “haba fatuha komai yayi zafi maganin shi Allah bai kamata kina kuka irin haka ba , addu’a  ce  makamin  mumini..!  duk wannan magana da ashuru yake fatuha ba jin shi take ba kalmar sadiq yazama miji na kawai ke yawo cikin qwaqwalwarta har suka iso garin kano fatuha na sheka kuka kamar ranta zaifi ta, ko da ashuru yayi horn aka bude geta kafin ya tsaida motar ta bale murfin motar ta fita da gudu sadiq da yanzu ya ji qarar shigowar mota daga labila yayi tare da koma ya cigaba da zarya a bedroom.

           Da gudu fatuha ta haura sama ko kallon mutanan parlour batayi ba part din sadiq ta wuce Allah ya bata sa’a tana bude kofar ya bude, ganin bata gashin a parlour ba yasa ta shigewa bedroom da gudu.
fadawa tayi jikin sadiq dake  tsaye tare da sakin kuka mai cinrai, rintse ido sadiq yayi yana jin yadda fatuha ke sheqa kuka, sai  yanzu  ya  gane  ba  sa hannu  fatu  cikin  abinda  ya  faru cikin sarkewar harshe ta ce, “Uncle dan Allah karkamin haka wannan horan yamin nauyi wallahi bazan  iya dauka ba, kaji  mai  kyau..! my  uncle..! my  happiness..! dama ace mafarki nake abin da nake ji ba gaske bane..!  ta ida zancan   tare da sakin sabon kuka ta zame kasa…….

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn= H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERS FORUM.COM

77_78

Kuka fatuha ke rairawa kamar ranta zai fita,  gabaki d’aya jikinta rawa yake qafafuwan sadiq ta riqe cikin shashekar kuka ta ce, “Please uncle I beg you in the name of God a janye maganar auran nan, wallahi ban shirya yin aure ba yanzu ba, babu  abinda  ke  tsakanina  da  majeed i  swear.! taqara rushewa da wani sabon kuka har yanzu jikin fatuha 6ari yake bakinta na  rawa  ta  ce, “uncle ya zanyi da karatu na? bayan duk duniya ba abinda nake so sama da shi, wallahi uncle ba abinda ke tsakanina da majeed kaji..! ta qara sakin kuka mai cin rai ( ko ni salma sai da na matse kwalla😥) da kyar sadiq ya sai ta kansa ya  hade hawayan dake maqale a kwayar idanuwansa, juyawa yayi, ya d’ago fatuha tsaye dake durqushe tana kuka ya zaunar da ita zaman bed amma duk da haka ba daina kukan tayi ba jikinta  sai  rawa  yake  tana  faman  sauke  ajiyar  zuciya, fridge ya bude ya curo robar ruwa ya tsiyaya a cup ya miqa mata, kuka kawai take baji ba gani, aje cup din sadiq yayi saman bedside drawer ciki cool voice sadiq ya ce “Fatuha..! tsagaita kukanta mai  sauti tayi tana kallon sadiq hawaye  na  sulalo  mata, lallashin ta sadiq ya shigayi cikin sanyi murya ya ce, “Fatuha ina so ki sani ko kadan bani na maki haka ba dan me  zan  maki  haka  ba  tare  dana ji  ta  bakin ki  ba” daura hannusa yayi a fuskarta, haka itama fatuha ta daura nata saman hannusa tana sauke ajiyar zuciya, ya cigaba da cewa “Bayan na dau alqawarin samamaki farin ciki har qarshan rayuwar ki fatuha? dan meyasa zan rusa maki mafarkin ki da  alkwarin  dana  dauka? ina so ki kasance mai daukar qadara mai kyau da mara kyau, da anyi shawara dani fatuha ba abinda zai sa na amince a katse maki karatun ki, ko  a  baki  abinda  baki  so, ko yanzu nasan majeed zai barki kiyi karatu kinji, ki kasance me yima iyayan ki biyaya zaki ga ribar haka, kuma insha Allah zaki so majeed saboda majeed nada kyawawan hali kuma yana son ki zai baki duk wata kulawa, ba zai bari ki taba zubar da hawayan ki a kansa ba, na  tabbata yana  sonki  so  haqiqa ki daure ko so d’aya ne ki sama ranki son majeed ko dan yana dan uwa na..! wasu zafafan hawaye ne suka gangarowa fatuha tana bin sadiq da kallo, dan ko bakin magana ta rasa, dama  mai  kyau  bai  ta6a jin  sonta  ba  dama  ita  ke  haukarta, tunda  gashi  shawara  yake  bata  ta  so  wanin  sa.
sadiq ko ban da daurewa ba abinda yake dan numfashinsa neman yankewa yake, sai ya numfasa yake cigaba da maganar saboda zafi da quna da qirjinsa ke masa ganin  fatu  zatayi  nisa  da  shi, glass cup sadiq ya miqa ma fatuha da  ruwa  ciki amsa  tayi  jiki  mace ta kafa kai ta shanye ruwan a hankali taji sanyin ruwan na ratsata, shiru suka dauka na mintina ba wanda ya tanka, can sadiq ya ce, “Fatuha kimin promise baza ki tada hankalin ki ba” dakyar fatuha ta iya furta  to wasu hawayan suka sulalo, jiki ba qwari ta tashi tana qoqarin fita sadiq ya bita da kallo dan bai jin zai iya tsaida ta saboda ganin tama qara famamasa ciwo ne a ransa.

                Tana fita sadiq ya kafa rubar ruwan ya shanye yana maida numfashi tare da ganin wasu taurari namasa yawo.

      Tsayawa tayi bakin steps ta share hawayan ta dan bata san Mom ta gane cikin nutsuwa ta sako, tana  wasa  da  yatsun  hannuta Mom da fitowar daga kitchen kenan ita da baba jummai murmushi ta saki ta  ce, “ah fatuha har kin dawo? eh tace tana qoqarin hadiye hawayan idanuwan ta Mom ta  ce, “Ahamdulillah ya su inna?
“lafiya lau” ta ce, sannan Mom ta ce, “ina fata Baffa bai maki dole ba” d’aga kai fatu tayi  alamar a’a idanu  ta  taf da  hawaye tana  wasa  da  yatsun  hannuta baba jummai ce ta shafa fuskarta ta ce, “Alhamdulillah hajiya ni dai bani da abin cewa kun gama min komai a rayuwata” ta ida zancan tana matsar kwalla ta  cigaba  da  cewa, “daga kawo fatuha aiki sai gashi ta zama yar gida har zaku aura da ita hajiya na gode na gode, Allah ya bar zuminci” baba jummai ta fada tana share kwalla idanuwanta Mom  ta  ce, “haba baba ai duk mun zama d’aya ai fatuha ta cancanci abinda yafi haka, kamar  ‘ya take  waje  na” Mom  ta  fada  cikin  sanyin  murya  tana  mai  taya  sadiq  bakin  cikin  rashin  fatu duk  halin  da  yake  ciki  tana  sane  sarai, haka baba jummai ta dinga zuba Godiya sannan tasa kai ta fita, fatuha kuma ta shige bedroom  ko da shiga d’aki sana’ar ta fara wato kuka dan ya zamar mata jiki daga shekaran jiya zuwa yau,  bedside drawer ta bude ta ciro sarqar da sadiq ya bata tana kuka tana  zancan zuci, dama  duk  abin da sadiq  yake  mata  ba  so  bane  mai  yasa  captain  zai  mata  haka, bayan  ta  jima  tana  fama  da  sonsa  tun   kan tasan  me so tunda  tasa  kafarta gidan ta  kamu  da  son sa  amma sai gashi wani  sabon kuka ne  ya  kwacewa  fatu kuka  ta  ci sosai har ta gaji sannan bacci ya dauke ta.

      Bangaran Basma ban da murna ba abinda take daga  ta  kama  wannan  pillow  sai  ta  saki ta  Kama  wannan, tana  jujuyawa  cikin  dakinta  cike  da annushuwa, duk wasu qawayanta ta fesa masu zata auri handsome, har wani jin ta take a sama yanzu, zata  auri  captain.
majeed ko ya kira layin fatuha har ya gaji yanke shawarar zuwa gidan gobe yayi yaga sanyin idaniyansa, duk  da  cewa  yasan  ya  mata  katsalandan a ganin  sa  komai  zai  wuce, sannan ya juya ya gyara kwanciyarsa cike  da  kewarta.

      Washe gari
Kiran sallah ne ya tashi fatuha jiki ba qwari ta shiga toilet ta sheqa waka ta dauro alwala wani irin jiri ke dibar ta, saboda kukan da tasha jiya dakyar ta iya gabatar da sallah ta zura uniform dinta ta dauki school bag din ta ta fito,

        Ko da ta qaraso dining area Mom ce da Abba sai angel dake gefe cikin nutsuwa ta gaishe su kamar kullun taja kujera ta zauna, ruwan tea kawai ta iya hadawa tana sha kamar tana shan magani kamshin turaran daya  doki  hancinta ne  yasata dagowa sadiq ne cikin uniform dinsa yana riqe da briefcase dinsa, yasha kyau har ya gaji sai dai fuskarsa ba walwala angel ce ta gaishesa ya amsa  tare da yi mata peck, kallon shi fatuha take har ta kasa kauda idanuwanta haka shima sadiq ita yake kallo tuni idanuwan ta suka ciko da kwalla girgiza mata kai sadiq yayi alamar kar tayi kuka, yana murmushin  dayafi  kuka  ciwo lumshe ido tayi tare da qoqarin hadiye kukan da ke niyar kuboce mata, sallamar majeed ce ta doki dodon kunanta, ware ido tayi tana kallon kofar sanye yake da uniform dinsa shima sai sheqi yake yayi  kyau  har  ya  gaji, qarasowa yayi tare da gaishe da su Mom amsawa tayi cikin fara’a, tare da cewa, “ya su Umma?
“su Umma lafiya lau Mom” sadiq dake tsaye take fara’asa ta dauke daurewa yayi ya tataro nutsuwarsa ya saki murmushin karfin hali ya  ce, “my man yau kai ne da sasafe nan? Sosa keya majeed yayi tare da kallon fatuha kauda kai tayi ta cigaba da juya tea din dake  gabanta dan ba sha take ba.

        Haka sadiq ya dinga danne zuciyarsa, fatuha kuma haka ta gama juya tea din ta tashi tare da daukar school bag dinta, ta ja hannu jidda suka fice tare da yima Mom sai sun dawo, tana fita majeed yabi bayan ta haka shima sadiq kasancewar office zasu.

   Zata shiga mota majeed ya ce, “baki ji ba..! daure fuska fatuha tayi dan wata tsanar majeed take ji juyowa tayi a fusace dan ta gayamasa mara dadi hango sadiq tayi bakin mota da alama su yake kallo, kauda kai sadiq yayi yana wani jin suya a zuciyarsa da rad’ad’i bale murfin mota yayi ya shige, murmushi fatuha ta saki wanda iyakar shi la66an ta ta ce, “uncle majeed ina kwana” cikin zaquwa ya ce, “lafiya lau my love,” cikin sanyi murya ya ce “Fatuha!”
“na’am.! tace a taqaice dan dakyar take masa magana saboda tsanarsa da ke bin zuciyarta ya  ce, “nasan na maki laifi my love naje nayi abu bada sanin ki ba amma please kiyi hakuri” wasu sabin hawaye fatuha ta hade ta ce “Ba komai.! tana qoqarin bale murfin mota ta  tsinkayo  muryar  majeed “idan dai kin hakura please ki bini nayi dropping na ki? daure fuska fatuha tayi dan bata jin zata iya bin majeed a yanzu, lagwabe kai majeed yayi ya ce, “please ki bani dama duk da nasan bani da mazauni a zuciyar ki, musanman  dana  maki  karantsaye, amma dan Allah kiyi hakuri ki so ni koda kad’ane, tunda nataso ban ta6a samun yarinyar da ta kwanta min a rai ba kamarki ba, fatuha please ki bani dama na gwada maki soyayyar da nake maki” haka majeed ya dinga magiya dakyar ya samu fatuha ta shiga motar shima sai da jidda suka shige ya ja motar.

        Sadiq dake zaune cikin mota yana kallo su duk yadda suke, dakyar ya iya saita nutsuwarsa tabbas yasan duk ranar da fatuha ta zama malakin majeed ba abin da zai hana shi zama gawa, dakyar ya iya bude baki ya ce ma driver “ja mu  tafi.! ba musu yabi umarnin ogansa suka bar haraban gidan.
suna zuwa wajen aikin Sadiq ya 6ale murfin mota ya fito tare da daukar jakarsa, ahankali yake tafiya kamar kazar da kwai ya fashema aciki, duk inda ya wuce ma’aikata nata gaisheshi hannu kawai yake d’aga masu, domin jiyake bakinsa yayi masa nauyi, yana zuwa office dinsa yabude yashiga, yayi jifa da Briefcase dinsa ya zauna bisa kujera wani kuka ne ya ku6uce masa mai radadi da ciwo, jiyake duniyar nayi masa zafi, bai ta6a sanin yana kaunar fautuha ba sai yanzu da yake shirin rasata, na  har  abada Why majeed ! me yasa zakamin haka? me yasa kake neman rushemin farin ciki na? me yasa zakace kana son Fatuha alhalin nafika bukatarta a yanzu, na  fika  son ta why  majeed..!  da karfin tsiya ya daki teburin dake gabansa ya ce, “nooooo Fatuha tawace insha Allah, danni aka  halice ta” wani murmushin karfin hali sadiq yayi (da ni Salma nakasa gane ma’anar hakan)

        Majeed nayin parking a harabar makarantarsu Fatuha ta kama murfin motar zata bude, da sauri ya dana wani remote ya rufe koffofin motar, cike da tsiwa ta dubeshi suna hada ido dashi ta sunkuyar da  kai kasa, batasan meyasa majeed yake mata kwarjini  ba duk yanda taso yimasa rashin kunya suna hada ido zata nemi nutsuwarta ta rasa, murmushi majeed yayi ya ce, “Haba My love, ya za’ayi kifita kibar mijinki da tsananin tunanin ki? ya kamata ki fada min wata kalma da zai sani tunanin ki koda ina office ne please matata kada kice min a’a” takaicine ya lullu6e Fatuha, ban da iskanci gidan uban wa aka d’aura mana aure dashi da har zai kirani matarsa taja tsaki a ranta mtsss, a fili kuma ta ce “Please uncle kabarni natafi dan Allah” ta karasa maganar kamar zata masa kuka “Sorry my lovely zaki tafi amma dan Allah kiyi min murmushi ko zan samu nutsuwar zuciyata?” Fatuha ta ce a ranta “Dan iska shege mugu kawai Allah yasa zuciyar ka ya dawama da bakin ciki kamar yarda kake qoqarin sani, A fili kuma tayi murmushi da iyakarshi le6enta, majeed ya bud’e masu kofar da sauri ta fita tayi gaba, jidda na qoqarin binta majeed yaciro kudi masu yawa yaba jidda shi kansa baisan ko nawane ba tayi masa godiya tare da masa peck a kumatu ta tafi da gudu domin har Fatuha tayi mata nisa, shima majeed cike da farinciki ya bar harabar makarantar.

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

79_80

     Ko da fatuha  ta shiga class ba wani walwala, haka su Nana suka dinga tanbayar ta mai ke  damunta ta fada masu meke damun ta, amma firtaqi gaya masu damuwar ta, Nana ce ta ce, “fatuha kenan baki daukemu a matsayin qawayan ki ba ko wayanda  zamu  kashe  tare  mu  birne  tare ba? Shiyasa zaki boye mana abin da ke damun ki” Zara ce ta budi baki ta ce, “Kyale ta Nana ai dai mun san matsayin mu yanzu, bai  zama  dole  ta  fada  mana damuwarta  ba” Zara na qoqarin jan Nana subar seat, fatuha ta riqe Zara ta  ce, “please kuyi hakuri, zan fada maku damuwa ta.! ta ida zancan hawaye na sulalo mata, duk abin ya faru haka fatuha ta kwashe ta fada masu ta  karashe  zancan  da  cewa, “ina  son  captain  so  mai  tsanani  wanda  ke  tafiya  tare  da  bugun  numfashina  amma  sai  gashi  lokaci daya” kuka fatu  ta  saki mai  cin  rai ta  fada  jikin  Nana tana  gunjin  kuka, Zara taji haushi ba kadan ba haka  suka dinga bama fatuha hakuri tana raira kuka dakyar suka shawo kanta.

         Bangaran majeed ban da dad’i ba abinda yake ji, zuciyar shi fes take daya lumshe ido kyakyawar fuskar fatuha yake hagowa sai ya qara sakin smile, matsala sa  daya  da  fatu  ta  kasa  sakewa  da  shi.

      Jingine yake saman kujera office ya rasa sukuninsa, idanuwan shi na lumshe saboda nauyin da suka masa har wata masasara ke rufe shi ga wani  irin  zafi da qirjinsa ke masa, tamkar  an  daura  masa dutse  mai  nauyi a hankali ya ware sexy eye’s ball’s dinsa da suka rine sukayi jaa wayarsa dak’e ruri cikin aljinhunsa ya curo sabuwar number ce baro-baro a screen din, da kamar ba zai dauka ba sai ya daure ya dauka tare da karawa a kunne, daga  dayan  bangaran cikin zazakar muryata cikin yauki Basma ta masa sallama, amsawa yayi a taqaice tare da tanbayar, “wake magana? gyara kwanciyar tayi daga inda take tare da kankame wayar dan wani irin sanyi ke ratsata, dan gyaran murya tayi cike da shagwaba ta ce, “Yaya sadiq ni ce fa Basma..! ko number ta ashe baka da ita? ta ida zancan cikin shagwaba Sadiq dake kishingide saman kujera, ranshine ya qara suya dan shi duduniya ba macan dake birge shi ko bashi sha’awa kamar fatuha, ko wannan magana ma da take yi jiyake kamar tana watsa masa ruwan zafi,  tsuke fuska sadiq yayi kamar tana ganinsa ya ce, “Yanzu ina wani aiki ne letter mayi magana idan na dawo gida” bai jira cewarta ba ya katse wayar tare da yin wurgi da ita ta daki bango ta dawo watse ko ta kanta bai bi ba ya sa kai ya fice daga office din, domin idan ya cigaba da zama tabbas kwakwalwar shi da zuciyarsa suna iya bugawa.
bin wayar tayi da kallo tare da dan bata fuska, ta aje wayar ta kwanta.

    Ko da aka tashi su fatuha majeed ne ya zo daukar su, ganin shine yasa ta had’a gira sama data kasa dan ba abinda ta tsana kamar ganinsa, ba yadda ta so haka ta bale murfin motar ta shiga tare da gaishe shi, kallon ta yake mai cike da so da kauna, sannan ya ce “My love daga gani yau kin sha wuya da yawa? ina fata dai kina kulla min da kanki?” dan guntun tsaki fatuha ta ja ciki-ciki sannan ta ce a cikin zuciyar ta “Har wani kira kake na kulla ma da kaina mtww dan iska kawai” muryar  majeed ce ta doki dodan kunnan ta a karo na biyu ya ce, “My love! ko duk gajiyar ce tasa ko magana ba’a san yimin?” dan smile fatuha tayi wanda iyakar shi la66an ta ta ce “A’a” murmushi majeed yayi tare da cigaba da driven, haka ya dinga janta da surutu tana amsa masa sama-sama sannan ya wuce da su shoprite yayi masu siyaya ice cream da cake, jidda ko sai dadi take ji dan har yanzu bata san inda aka dosaba.

Suna kunna hancin motar su, suka ci karo da sadiq wanda shima dawowarsa kenan wani irin dogon numfashi sadiq yaja a duk lokacin da yaga majeed da fatuha, numfashinsa sai ya nemi ya dauke ko qirjinsa ya dinga masa zafi, dakyar ya iya d’aga kafarsa dan baya so ko fuskar su ya gani sun fito a tare, amma sai dai kash majeed ya riga ya kira sunan sa. lumshe ido yayi ya tsaya chak! sai da ya kwashe yan mintina sannan ya waigo tare da sakin smile din karfin hali, ta gabansa fatuha ta raba ta wuce jidda nata zuba masa surutu sannan itama ta shige, miqa mashi hannu majeed yayi suka gaisa ya  ce, “big man duk yau ban ganka a office ba”
“oh ina cikin office ina wani aiki ne gobe ma nake so na wuce Lagos”
“Lagos kuma? me zaka je yi lagos? cewar majeed
“zan je nayi 2week ne cikin ruwa na dawo”
“Eyya to Allah ya taimaka”
“Amin..! yana qoqarin shigewa majeed ya ce, “Baby..!
“yes..! ya ce a taqaice
“dama ina so muyi wata magana”
“ok mu shiga ciki” ok majeed yace tare da bin bayan sadiq suka shiga part din sadiq briefcase dinsa sadiq ya aje tare da rage kayan jikinsa ya shiga toilet, ya dade a toilet din baiyi wankan ba yana kukan bakin ciki sannan ya tashi yayi wanka, sanye da bathrobe ya fito da qaramin towel a hannusa yana goge jikinsa, majeed na zaune saman sofa shima tashi yayi ya shige toilet ya sheqa wanka ya fito ko da ya fito lokacin sadiq ya shirya cikin black 3 quarter  da white shirt mai gajeran hannu, yana zaune saman sofa idanuwansa lumshe, shiryawa majeed yayi a tsanake sannan ya bude wardrobe din sadiq ya ciro riga da wando riga blue sai dark blue jeans sannan ya bude fridge ya curo fresh milk ya tsiyaya a cups ya miqama sadiq ya amsa.
zama yayi kusa da sadiq ya ce, “Please ina so kamin taimako guda daya please?
“ok inajin ka indai baifi karfina..! murmushi majeed ya saki ya ce “Bai fi karfin ka ba”  gyara zama sadiq yayi yana sauraran majeed riqe hannusa majeed yayi cikin lagwabe kai ya  ce, “please baby kamin hanya fatuha ta so ni..! tsura masa ido sadiq yayi da idanuwansa da suka ciciko da kwala hadiye su yayi yana saurara majeed ya  cigaba  da  cewa, “baby ina  son  fatu wallahi ina sonta i  love  her  more than how  you  think, ban ta6a jin son wata  d’iya  mace ba kamarta ba, baby karkayi tunanin irin son da nake ma sauran yan’mata nake mata a’a son ta nake da gaske ba  da  wasa ba, idan har  na rasata zan iya rasa rai na ina  jin  sonta mai  yawa  sadiq  na  kamu  da  sonta  mara  musaltuwa  ina  manta  kai a  gabanta  ita  ce  bugun  zuciyata sadiq…!  majeed ya fada, da  sauri-sauri  numfashin  sadiq ke  gudu  zaune  yake tamkar  an  dasa  akwai yana bin majeed da ido kamar sakarai gabaki daya  jikin shi ya mutu sai zuciyarsa dake tsinkewa kamar zata fito waje dan  tashin  hankali, dan matse hannusa da majeed yayi ya sasa dawowa daga duniyar tunanin, smile ya saki yana  kallon majeed  ya  ce, “my man karka damu kaji d’an jama aji take amma nasan zata so ka kaji, kasan yadda mata suke amma nasan zata so ka  har ku dai-daita  babu  macan  da zata  same  ka  ta fasa kai  kasan  da haka, kana  da  abinda  kowace  ‘ya  mace  zata  so ka” murmushi majeed ya saki tare da kaima sadiq hug ya ce, da  gaske  Bros..!
“Eh mana.!
“Ka  tabbata  fatu  zata  so  ni?
“Sosai  ma..! hawaye dake  maqale  idon  sadiq  ne suka cigaba da anbaliya dan ko yasan ya rasa fatuha, dan baya fatan abinda zai samu majeed dan uwan shi abokinsa mai  son  farin  cikinsa bashi da aboki dan uwa saman da majeed, mai  yasa  ma  tun  farko  yake  kishin  d’an  uwan  nasa, lokaci yayi da ya kamata ya ba zuciyarsa hakuri jin majeed zai zame jikinsa yasa sadiq saurin share hawayansa tare da sai ta kansa murmushi suka sakar ma junan su, fira suka fara sama-sama kiran sallah magrib ne ya tashe su.

  1week letter

      Shirye-shiryan aketayi a family house, kasancewa yau za’a sa rana biki duk wanda ka kalla cikin farin ciki yake musanman Basma da majeed.
zaune suke cikin d’akin yan’mata sunata zuba hira muryar Basma kadai ke tashi fatuha na gefe tana matsar kwalla dan har yanzu gani take kamar wasa, kamar kuma  a mafarki tashi tayi ta fita daga d’akin ganin kayan da ake ta wucewa da sune yasa jikin fatuha qara sanyi.
fitowa tayi daga parlour hango qanan Baffa tayi su baba Barau  kasancewa  komai Abban sadiq  ya  ce zaiyi  tunda  fatu  hannusa  take, wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo mata yanzu ta tabbatar za’a samata rana da wanda bata so a matsayin miji kuka ne ya ci karfin ta, fita tayi daga gidan gabaki daya dan ko sanin inda zata ba tayi ba jefa  kafar  kawai  take  kan  titi, can baba jummai ta fado mata a rai keke napep ta tara ta shige  ta ce, a kaita gadan qaya” kasanwcewar gidan baba jummai kan titi yake bata wani sha wahala kwatantawa mai napep  gidan ba kukan da take yasa mai keke napap din bar mata kudin saboda ya tausaya mata.
ko sallama bata cika ba ta shige gidan, baba jummai dake qoqari fita, fatuha ce ta fada jikinta tare da sakin kuka kamar ranta zai fita, rud’ewa baba jummai tayi tana kallon ta baki sake tana  cewa, “ke  lafiyar  ki  ‘yan nan  wani  abune ya  faru? zaunar da ita saman kujera Baba  jummai  tayi tana qara tanbayar ta lafiya kuka take sosai, cikin shasheqar kuka ta ce, “Wallahi baba bana son majeed bana jin zan iya zaman aure da shi..! ta ida zancan tana rushewa da kuka, sallati baba jummai ta hauyi tare da tafi tana  cewa, “na shiga uku ni jummai , me nake ji haka fatuha sokike ki ja mana abin fade? kowa  yana  mana addu’a Allah  ya  rufa  mana  asirri ya  kai  ki  gidan  sutura, yanzu  kuma  ki  ce  ba  haka  ba, toh idan ba majeed ba wakike so? kuka ta kuma saki cikin shasheqar kuka bakin ta na rawa ta ce, “CAPTAIN SADIQ nake so Baba..! Baba idan na rasa sadiq mutuwa zanyi, ni  shi  nake  so” ta ida zancan tana kuka mai tsuma zuciya, zaro ido waje baba jummai tayi  ta  ce, “na shiga uku ni jummai..! rungume fatuha tayi tana lallashi dan ita kanta ta tausayama fatuha ita kanta taso ace da sadiq din za’ayi, amma ya zasuyi tunda shi bai ce yana so ba? d’ago da fatuha tayi tana share mata hawayan ta ta  ce, “kiyi hakuri fatuha kinji ki cigaba da addu’a Allah yana tare dake Allah zai dubi zuciyar ki ya baki mafi alheri fatuha, ki sama zuciyar ki sallama kinji” ajiyar zuciya kawai take saki tayi lamo a jikin baba jummai.

       ban da tari ba abinda yake har wani jiri yake gani, majeed dake gefansa sai sannu yake jera  masa, toilet ya shige da sauri yana cigaba da tarin gaban zing, yana  sauke  ajiyar  zuciya  saboda  galabaita kallon mirror dake manne jikin zing  yayi  jini da ya ganine gefan bakinsa  ya sashi zaro ido waje hannu ya kai ya ta6a ganin kamar jinine yasa gabansa ya yanke ya fadi, hawayan dake maqale a idanuwasa ne suka sulalo.
zamewa yayi a qasan toilet din yana mai da numfashi sama-sama kirjinsa  na  tsananta harbawa, miqewa yayi da sauri ya fito duk da yana jin jiri, majeed dake zaman jiran fitowarsa ne ya ta shi yana masa sannu ko amsa masa sadiq ya kasa, wardrobe ya bud’e ya jawo trolley ya fara zuba kayansa yana zubawa jiri na dibarsa ga tarin sai zuwa yake tare da jini amma duk wannan abun yaki yadda majeed ya gane sai da ya gama had’a kayan shi tsaf majeed na gefe tsaye riqesa yayi ya ce “Baby wai me ke faruwa ne? naga muna lafiya lau lokaci daya ka rude, me  ke  damun ka  ne? murmushi yayi ya ce “Karka damu tunawa nayi da flight dina na zuwa Lagos yau zai tashi kuma gashi saura 10 minutes ya tashi”
“ok muje nayi dropping naka”
“ka barshi kawai nayi ma driver magana ka ji” ok ya ce masa tare da yi masa peck  ya  ce, “safe trip..! sannan ya sa kai ya fita dakyar ya iya jan trolley ya fita waje yana tafiya yana tari tunkan ya qaraso ashuru driver ya bude masa murfin mota amsar trolley yayi yasa a boot sadiq yana shiga mota ya fara bale button din rigarsa saboda wani  irin zafi yake  ji  numfashinsa sai daukewa yake  yana dawowa, idanusa  sun  firfito  waje  sunyi  jawur  har  lokacin  yana  tarin  jini sai  dai yasa handkerchief yana toshe  bakinsa ko da ashuru driver ya shigo mota ja yayi suka bar harabar gidan.
Ta cikin mirror ya fara ganin halin da sadiq yake ciki a  firgice  ya  ce, “yallabai.! cikin galabaita sadiq ya iya furta, “kaini wajan Dr yakub.! da gudu ashuru ya fisgi mota sai asibitin doctor  yakub yana  driving  yana  waigen  sadiq.
Suna Isa asibiti driver  ya  faka mota sadiq ya 6ale murfin motar ya  fito duk da yana ganin jiri, numfashinsa na  barazanar  daukewa bibiyu  yake  ganin  mutane da  hanyar  ita  kanta office din Dr yakub ya nufa yana had’a  hanya.
bude kofar office  din  Dr  yakub  ke  da  wuya sadiq ya sulale sumame a wajan…🙆‍😰

  Muje zuwa fan’s

Vote
Comment Written by
salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We  are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                    81_82

            Mikewa Dr yakub yayi dan kawowa sadiq taimakon gaggawa. gabaki d’aya shima ya rud’e kwalawa nurses kira ya shiga yi da sauran ma aikatan asibitin, saboda  gabaki  daya ya  rikice, kafin kace me har an daura sadiq a gadon asibiti.
Ashuru driver da shigowar shi yanzu ya ga za’a  wuce  da  sadiq  emergency bin gadon yayi yana matsar kwalla, ba’a zame da sadiq ko ina ba sai emergency, ashura na ganin haka ya ci birki bakin kofar emergency yana zarya, yar wayar da ke aljihunsa ya zaro dan ya kira gida amma sai dai wayar ba chaji kuma bai iya tafiya ya bar sadiq a yanzu dan ana iya buqatar wani abu, haka ya dinga zarya bakin kofar gabaki daya ya rude hankali  sa a tashe.

          Haka baba jummai ta dinga lallashin fatuha sannan tayi shuru Baba jummai  ta  ce, “fatuha  tashi kiga mu koma tunda dai kin san aiki na can na jira na.! matsar kwalla ta fara cikin sanyin murya ta ce “Dan Allah Baba ki barni a nan wallahi bana san zuwa, bana son jin hayaniyar mutane, mudin na cigaba da ganin abinda ake a gida ina iya shiga wani hali” duk yadda baba jummai taso ta tafi da fatuha firtaqi ba yarda ta iya shiya ta barta ta tafi ko da baba jummai ta fita kuka fatuha ta dasa.

     Shewace ke tashi yadda kasan yaune daurin auran wajan  su  Basma, zuhura ce ta shigo da sauri ta fada jikin Basma tare da cewa “Ansa biki wata d’aya..! washe baki Basma tayi tare da jawo wayarta ta fara kiran sadiq duk wannan kira da take ba’a dauka ba, ta6e baki tayi tana  zancan zuci, “duk kayi ka gama aure dai sai munyi duk wulaqancin da kake zubamin bashi zai sa na daina son ka ba..! ta ida zancan zuci da jan d’an guntun tsaki, Hanan ce tashigo jiki a sanyaye Basma ce ta ce “Ke kuma lafiyar ki kuwa? Naga  duk  yau  baki  walwala..!
“wallahi tun d’azu nake neman fatuha a gidan nan narasa  inda ta shiga, shi  ne abun  duk  ya  dame  ni  ta  barni  ni  kadai, na kira wayarta yafi aqirga kashe”
“toh fa.! dazu dai tanan cikinmu har tace min kanta na ciwo na bata magani, namayi tunanin bacci tayi”
“ok qila ta koma gida, amma bari idan mun gama abinda muke sai muje ko?
“eh gaskiya” sannan Hanan tasa kai ta fita.

       Bangaran iyaye angama komai inda Mom ta yanke shawarar Basma ta koma can gidanta yadda za’a ji dadin kula da amaran, waje daya kuma kowa ya amince da shawara.

doctors ne kan sadiq dan ceto rayuwarsa, inda suka ci sa’a ciwo zuciyar bai dad’e da kamashi ba, daya sha magunguna yadda ya kamata zai warke sai da yamma likis aka fito da shi, Ashiru yabi bayan su aka ba sadiq d’aki, har lokacin sadiq na kwance yana bacci sai qarin jini dake masa wanda doctor yakub ya bada nashi, ashiru zama yayi d’aya daga cikin kujerin dakin sai da ya dan jima sannan ya wuce office din Dr, ko da ya shiga lokacin yakub ya fita ganin wasu marasa lafiyar hakan yasa wuce gida dan sanar masu  halin da sadiq yake ciki.

           A hankali yake ware sexy eye’s ball’s dinsa da suka masa nauyi, bude kofa akayi a ka shigo ba kowa bane sai Dr yakub qarasowa yayi bakin gadan ya  zauna  gefen gado a hankali ya kai hannu goshin sadiq har yanzu da zafi rau cikin sanyi murya Dr ya fara magana “Captain me yasa  kake wahalar da zuciyar ka da tunani tuntuni? nayi tunanin ka daina tunani amma yanzu ka dawo da shi sadiq, har kaja ma kanka ciwo zuciya” lumshe ido sadiq yayi kawai yana saurara Dr ya  cigaba  da  cewa, “na rasa wani irin tunani kake wannan sadiq? ciwo nan da kake gani yana iya jama ka rasa aikin ka sadiq, har ma  rayuwarka, da ace asibitin mu ka je ai da yanzu an farama shirin sallama ka wajan  aiki..! rike hannu sadiq yakub yayi  da sake cewa “Please ka fada min damuwar ka please sadiq? hawaye ne masu zafi daya ke bin daya a fuskar sadiq shi kan shi yakub ya firgita da yanayin da sadiq ya koma yanzu, cikin sanyin murya Dr ya ce “Tunda baka iya fada min ya kamata a gida a san damuwar ka..! ya fadi hakan yana qoqarin fita riqe hannunsa sadiq yayi tare da ware idanuwashi da suka zama ja ya ce, “Please karkamin haka Dr bana fata kowa yasan abinda ke damuna a yanzu, please kamin alqawarin baza ka fada ma kowa ba? zame hannunsa Dr yayi dan baya jin wannan karan zaiyi shuru, har ya kai bakin kofa sadiq ya ce “Dan Allah karka fadi please” ya ida zancan yana kuka mai cinrai  chak Dr yakub ya tsaya dan gabaki daya tausayin sadiq ya lullu6e sa  damuwar  sadiq  ta  zarce  na  da  a  yanzu dawowa yayi da sauri saboda tarin da sadiq  yake dan  basa taimako, allura samun hutu ya  masa, ya fita ko da ya shiga office ya kasa zaune ya kasa tsaye yana tunanin inda matsala sadiq take dan yanzu ya lura ko yasha maganin indai zai cigaba da tunanin da yake zai zama anyi ba ayi ba.

     Ko da  ashiru driver ya koma gida har yanzu basu dawo ba, suna family house juyawa zaiyi da motarsa ya wuce family house kenan, sai ga fatuha mai  keke napep ya ajeta ta fito suku-suku ba alamar walwala dan itama a tunanin ta sun dawo, Ashuru ne yayi  parking tare da qarasowa ida take gaishe shi tayi a taqaice tana qoqarin shigewa gida ya  ce, “fatuha.!
“Na’am” tace tare da waigowa ya ce, dama.. dama..!  gaban tane ya yanke ya fadi saboda yadda Ashurun ke magana kamar wanda yayi ma sarki qarya “me ya faru? ta fada a taqaice
“dama yallabai ne ba lafiya yanzu haka yana asibiti na zo fada maku ne kuma har yanzu basu dawo ba” zaro ido fatuha tayi da dafe da qirji tuni hawaye suka 6ale mata ta  ce, “me ya same shi? ta fada bakin ta na rawa, “muje ka kaini asibitin idan ka ajeni sai ka biya family house ka fada masu” da sauri ta shiga motar Ashuru ya ja sai asibiti.
suna Isa ta bale murfin motar Ashuru na gaba tana biye tana kuka suna Isa dakin ashuru ya juya fatuha ta shige ganin halin da sadiq yake ciki yasa fatuha sakin sabon kuka tare da qarasowa bakin gadon, a hankali ta kai hannuta saman kan sadiq hawayan na sulalo mata ruwan hawayan ta ne ya d’iga a saman idon sadiq, tana rasgar  kuka mara sauti a hankali ya fara ware idanuwasa sauke su kan fatuha data ci kuka har ta gaji ta  koma  tamkar sabuwar  mahaukaciya riqe hannu sadiq tayi ta ce “Uncle meke damun ka?” murmushi ya qaqaro wanda iya karshi la66ansa ya kai hannu saman fuskarta yana gogewa fatuha hawayanta lumshe ido  fatu  tayi tana  jin yarda  hannu  sadiq  ke  yawo da  hannusa saman  fuskarta  tana  sauke  numfashi  a  hankali, lumshe ido yayi tare da ware su ya ce, “My dear bana so ina ganin ki kina kuka kinji? ba wani abu bane ke damuna ba kawai fever ne saboda na daina ganin smile din ki” ya fadi zancan yana ja mata hanci smile fatuha ta saki mai had’e da kuka-kuka ta kai ma sadiq peck a goshi tana  bin  shi  da  idanuta.
Dr yakub da yanzu ya turo kofa ya shigo, ko sanin ya shigo basuyi ba, suna  ta  kallon  juna hannuwan su  sarke dana juna tsayawa yayi yana kallon su yana tunani, musanman yadda ya ga lokaci d’aya sadiq ya sauya, hannusa sadiq ya kai gashin kan fatu ya ta6a wanda ya leko waje ya ce, “fatuha.!
“Na’am” ta ce tana kallonsa cike da so da kauna ya  ce, “me yasa kika daina kulla da gashin kan ki? hawaye ne suka sulalo mata ta bud’e baki za tayi magana sadiq ya daura d’an yatsansa sama lips dinta ya  ce, “shhh.! a hankali ya kwance dankwalin kanta gashin ya baje a gadon bayanta ba wai wanke kan ne batayi ba a’a duk wasu mayuka masu sa gashin sheqi ta daina shafawa saboda ko lokacin hakan bata da shi, sadiq  ya  katse  mata  tunani da cewa, “har yanzu baki son majeed ko? kuka ta saki mai cin rai har da shesheqa, rintse ido sadiq yayi tare da shafa gefan face nata ya  ce, “kukan ya Isa haka mana bana so naga kina kuka kinji? d’aga masa kai kawai fatuha tayi tare da daura hannuta saman nashi bakin ta na  rawa ta ce, “Shikenan uncle yanzu Basma zaka aura? ta zama matar ka? angel ta zama diyarta ko? kuka ta kuma saki mai cin rai, lumshe ido sadiq yayi bakin ciki na cin sa smile yayi ya ce, “Nace fa ki daina kuka kuma angel diyarki ce ai” daga kai tayi ya ce, “good.! haka kuma nima naki ne? Jinjina  kai  fatu  tayi  wasu  hawayan  na  kora wasu  sadiq  ya  ce, “ko baki so na auri basma? idan baki so sai na fasa” ya fada yana smile.
“ba wai bana so bane uhm..! bata ida zancan ba Dr yakub yayi sallama dan ya lura sai su kwana suna hira gashi fira da ya ji suna yi kamar cike take da matsala da rudani idan ya fahimta kenan, da sauri ta daura dankwallin ta tare da gaishe da Dr alura ya ma sadiq tare da cewa, “wanake gani kamar fatuha? murmushi ta saki ta ce “Ni ce”
“gaskiya naga kin canza, ko duk amarcin ne? ya fada yana kallon face din sadiq take annurin sadiq ya fara daukewa haka fatuha dake zaune kusa da shi kawar da zancan yayi dama face nasu yake so ya karanta idan har ya gane suna son junan su, amma sai dai kowane wani da ban zai aura, insha Allah zai taya su da addu’ar cikar burin su idan  har  Alheri.

     Ko da Ashuru ya je gida ya fada kusan mota biyu sukayi ko 10 minutes basuyi ba suka iso asibiti, a lokaci fatuha na feeding sadiq abinci yana ci suna dariya dan ji yake gabaki daya kamar ya warke, turo qofar da akayi ne yasa su waigowa majeed ne ya fara shigowa turus yaja ya tsaya yana mamaki yaushe fatuha ta zo? haka Basma dake bayan shi da Umma da Mom, ashuru ne da shigowar su yanzu shi da su Abban ya fada masu yadda a kayi har ta zo dan sakin jikin majeed yayi amma har yanzu ya kasa kauda ido daga abinda ya gani, kishi ne ya lullu6e sa, fatu  kuwa duk kunya ce ta kamata aje plate din tayi tana qoqarin tashi, sadiq ya riqe hannuta yadda baza ta iya matsawa daga kusa da shi ba, dan bai iya hakuri da rashin ta kusa da shi yanzu kallonsa take tana masa alama daya sake ta amma yaqi sakinta, sai ma wasa dayake  da yatsun hannuta ganin ba yadda za tayi yasa ta hakura, tana sakar  masa  murmushi mai  cike  da  ma’anoni daban-daban Basma ko ta cika fam dan ita taso ace take kusa da shi ba fatuha ba.
shima majeed ba laifi ya dan shaka amma yaki yadda zuciyarsa ta fadi abinda take tunani sai ma watsar da zancan da yayi, shi ko sadiq yaqi sankin hannuta da sunyi ido biyu sai ya sakar mata lallausan murmushi, Mom da ke lura da yanayin su sai suka bata tausayi dan dai kar tayi magana ace gashi, da ba abinda zai sa tace a basa auran amma da tayi magana tasan abinda zai biyo baya.
ko da su Abba suka tanbayi Dr yakub me ke damun sadiq fever ya ce masu a taqaice .

     Kiran sallah magrib ne yasa Sadiq ya saki hannu fatuha dan ta dauro alwala lokacin har su Mom sun tafi, daga ita sai Basma sai majeed da shima yanzu ya wuce masallaci  tana Shiga toilet Basma ta matso ta zauna kusa da sadiq kasancewar ita hutu take ta  ce, “ya jikin?  cikin yauki da kisisina lumshi ido yayi ya  ce, “Da sauki”
“Allah ya baka lafiya sweetheart” miqewa tayi tana  kwarkwasa daniyar ta masa peck lokacin yayi dai-dai da fitowar fatuha daga toilet, bin gadon tayi da kallo ganin yarda Basma ta  wani  rankwafu  kamar  zata  sunbaci  sadiq a baki, wani irin kishi ne  ya  rufe  fatu wanda ita kanta bata san tana da shi ba.
juya mata baya sadiq yayi tare da cewa cikin cool voice, “Basma kai na na ciwo koya naji an tsayamin a kai nauyi yake min” ya fada yana kallon fatuha da saura qiris ta fashe tana  kallon su fita tayi daga d’akin da sauri ko da ta fita kuka ta saki mai ban tausayi, ta dade tana kuka sannan ta samu guri a wajen tayi sallah…
Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                    83_84

             Bayan ta idar da sallah tana qoqarin nade daduma majeed ya shigo lallausan murmushi ya sakarmata tare da qarasowa kusa da ita, duqar da kai tayi qasa tana wasa da carpet din hannu ta, a hankali majeed yasa hannu ya d’ago da fuskarta, kallon fuskar majeed yake cikin so da kauna, cikin sanyin murya ya ce, “My love me ya saki kuka?” kamar jira take ya tanbayeta ta fashe masa da saban kuka, rungume ta majeed yayi yana lallashinta ya samun daya daga cikin kujerin wajan suka zauna, daura  kanta yayi a kafadarsa yana shafa mata bayanta a hankali cikin sanyi murya ya ce “My love bana so naga kina kuka, idan kina kuka sai naji nima kamar nayi, meke damun ki? ki fada min koma menene zan samamaki indai zai saki farin ciki..! dagowa fatuha tayi ta kallesa, a cikin azuciyar ta ta ce “Ba komai zakamin ba, ila ka ce ka fasa aure na! ka barni da muradin raina da zabin zuciyata, abinda nake son gani safe rana dare wanda bana gajiya da ganinsa, wanda bana gajiya da saurarasa, wanda na  tsunduma  kogin  son sa  tun  kafin  na  san  menene  so..!  rushewa da sabon kuka fatu  tayi gabaki daya majeed rudewa yayi da yanayi fatuha, sai aikin lallashin ta yake dakyar ya samu ta daina kuka sai faman ajiyar zuciya da take, daura kanta yayi saman kafadarshi yana wasa da yan yatsun ta masu laushi  sun dau mintina suna a haka sannan fatuha ta zame kanta daga kafadarsa tana qoqarin tashi, d’ago fuskarta yayi yasa lallausan hannusa yana goge mata hawayan ta tare da yi mata peck a goshi runtse ido fatuha tayi tana jin wani irin suya da zuciyarta kema ta mai cike da tsanar majeed, hannunta ya riqe suka miqe a tare sannan ya amshi dadumar hannuta a hankali suka bude kofar d’akin suka shigo, har yanzu sadiq na kwance  amma ba bacci yake ba, Basma na gefansa  tana zuba masa iyayi yana saurara, shigowar su fatuha ce tasa shi d’an dagowa ya jingina idanuwasa ne suka sauka kan  hannun fatuha cikin na majeed, wani irin b’akin ciki ne ya taso masa tabbas wannan ba jinya aka zo ba zuwa akayi a qarasa shi, lumshe ido yayi dan baya iya jurewa ganin baki’n cikin, zame hannunta fatuha tayi tare da zama tana facing sadiq.

     Majeed qarasawa yayi wajan sadiq tare da shafa sumar kansa ya ce, “Baby.! bude idanu sadiq yayi tare da sakin murmushi riqe hannunsa majeed yayi ya zauna, ya aika ma sadiq harara wasa yayi tare da cewa, “Shine baka da lafiya kakasa fada min baby? wai me yasa kakemin haka? abu na damun ka baka fada min saboda  ban kai matsayin ba ko? ya fada yana lagwabe kai dan shagwabe, fuska sadiq yayi ya ce “Sorry banyi tunanin fever ya kai haka ba, nayi tunanin har sai naje Lagos nasha magani”
“uhm please next time karka sake haka,”
“tam.! yace tare da tsinkulin majeed  ganin  yarda ya  shiga  damuwa murmushi  ya  saki  ya  ce, “kaci abinci?
“no.!
“me yasa baka jin yunwa ne? so kake ciwo ya cigaba da riqe min kai ko? plate majeed ya jawo ya zuba abinci shinkafa da miya tasha naman rago  a hankali ya shiga feeding sadiq yana amsa cike da son dan uwa na shi yana ci yana jan shi da hira mai cike da nishadi, dariya sadiq yake can kuma yayi shuru yana bin majeed da kallo, sosai  jikinsa  yayi  sanyi, murmushi majeed yayi tare da aje plate ya ce “Kallan fa?” smile Sadiq yayi ya ce “Ba komai”  juyawa majeed yayi ya kalli fatuha ya ce “Sweetheart ku tashi  muje na saukeku gida” ok fatuha tace tare da tamiqewa, Basma ko peck ta ma sadiq tare da masa sai da safe ta fita, hadiyar zuciya ne kadai fatuha ba tayi ba sannan suka fice har sun kai bakin kofar mota, fatuha ta ce “Tayi mantuwa” da sauri ta koma dakin lokacin idanuwasa sadiq na lumshe.

A hankali fatuha ta qaraso ta shafa sumar kansa, bude ido yayi yana  kallon ta ya ce “Fatuha kin dawo ne ki kulla da uncle?” murmushi ta saki ta ce “Mantuwa nayi uhm”
“mekika manta? peck ta masa a goshi sannan ta ce “Kaga abinda na manta” smile sadiq ya saki tare da jawo ta ta fado saman qirjinsa har tana jin bugun zuciyar shi, sasanyar  ajiyar  zuciya  suka  saki  a tare suka lumshe  ido suka ware  su  kan  juna  su, lips din ta sadiq yabi da kallo a hankali ya daura finger dinsa saman lips din fatuha, kallon shi take me cike da kauna haka shima tafiyar tsutsa sadiq ya dingayi mata a lips lumshe  ido  fatu  tayi jikinta ya  mutu mudus lokaci daya tana  sauke  numfashi  a  hankali wanda ya  hadasa ma sadiq  mutuwar  jiki, yana  mai  cigaba da  yawo da  finger dinsa a lips dinta zuwa  dokin wuyanta riqe hannusa fatu tayi tare da d’an cizan shi dariya fatuha ta saki tana  masa  gwalo tana  wani  juya  ido, dan shagwabe fuska yayi ya koma kamar baby face yana  bin  fatu da  kallonsa mai  qara  tsundumata duniyar son sa cikin sanyi murya  fatu  ta  furta, “sorry..! ta riqe kunnanta, ja mata hanci sadiq yayi tare da yi mata peck a kumatu, fatu  na  jin yarda  karan  hancinsa  ke  gogar  kumatunta mai  cike  da  wani salo mai  tafiya  da  nutsuwa, dakyar  ta  iya  jawo  nutsuwar  ta  furta, “uhm uncle bari na tafi nabar mutane na jirana a waje” da sauri ta mike daga saman bed din zata fice riqe hannun ta sadiq yayi lumshe  ido fatu  tayi  tana  sauke  ajiyar  zuciya  da  sauri-sauri wasu hawaye  na  sulalo  mata, ta waigo ba  shiri tana  kallon sadiq dake binta da kallo itama shi take kallo ya kankance ido mai  cike  da  ma’anoni daban-daban zame  hannuta  tayi sannan tasa kai ta fita.
Tana fita taci qaro da majeed gabanta ne ya yanke ya fadi lokaci daya, ta dan da burce kallon ta kawai majeed yake ya  kasa kau da idon sa bai ce komai ba suka shige mota suka bar asibitin.

       Kwanan sadiq uku asibiti aka sallame shi, sosai ya samu kulawa wajan yan’uwan shi tare da soyayyar su, ya  murmure Alhamdulillah.
Zaune suke a dining area suna lunch har da Basma saboda yanzu ta dawo gidan da zama angel na gefe tana zubama sadiq shagwaba sai ya kai ta shan ice cream, Mom sai tsiya take mata, Basma ce ta kalli sadiq tare da jefa masa kallan so murmushi ya mata wanda iyakar shi la66an shi fatuha na zaune tana lura da hakan gabaki daya annurin ta ya dauke dan ji take ma abincin ya isheta, ture plate din tayi tare da tashi ta barwurin kallo sadiq ya bita da shi tana shiga bedroom ta fada saman bed tare da sakin kuka, sai da taci kuka ta gaji sannan ta bude bedside drawer wani album ta curo tana kallo pictures din tane ita da angel da sadiq tana kallo tana dariya da murmushi mai kuka. haka ta dinga kallan pictures din har bacci ya dauke ta.

     Bayan sun gama lunch suka koma parlour suna kallo Basma sai jan sadiq take da labari tun bai biya mata har ya dan fara sakar mata, amma duk bayan mintina sai ya kalli bedroom din fatuha sallamar majeed ce ta katse masa tunani, da sauri Basma ta qarasa wajan shi ta  ce, “bros  I miss you?
“miss u more sis”
“ya su Umma” ta fada
“suna nan lafiya lau,” dan bata fuska majeed yayi ya  ce, “matsala ta dake shegyan surutu ko bari bakiyi na huta kin fara tanbayata, haka zaki dinga yima sadiq? murmushi ta saki tare da rufe fuskarta ta6e baki sadiq yayi tare da kauda kai, qarasowa majeed yayi ya zauna kusa da sadiq suka gaisa, sannan ya ce, “ina my love? wani irin kishi ne ya rufe sadiq shuru yayi bai tanka ba Basma cikin zakuwa ta ce, “tana bedroom.! zunbur ya miqe ya shige a hankali ya bude kofar kwance ya hango ta saman bed smile yayi tare da qarasowa,  bacci take rungume da album a hankali yasa hannu ya zare album din ya bude album din yana  kallon picture dinta da sadiq ya fara gani, kanta na bisa kafadar sadiq suna dariya ya dade yana kallon picture din, sannan ya bude d’aya shafin ya gansu su uku cikin picture din suna shan ice cream haka majeed ya dinga bin pictures din yana kallo musanman in da yaga wanda fatuha da sadiq sukayi picture din har mamakin irin shaquwar da sukayi yake bai taba tunanin shaquwar su har ta kai haka ba, aje album din yayi yana qoqarin yaga sadiq bakin kofa fuskarsa a ha…
Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                       85_86

             Murmushi sadiq yayi tare da qarasowa ya dauki album din da majeed ya aje, ya bud’e sannan shima ya aje tare da kallon bed fatuha na kwance gashin kanta ya baje a bed, take kishi ya lullu6e sadiq qoqarin fita yake majeed shima ya miqe suka fita a tare, ko da suka fito Mom na zaune tana kallo Basma na gefe angel na assignment gaishe ta majeed yayi tare da yi mata peck cikin fara’a ta amsa tana tanbayarsa ya su Umma ya ce “Suna lafiya lau” sannan suka fita da sadiq.

     Basu zame ko ina ba sai family house, bangaran Ammi suka fara shiga da sallama suka shiga Ammi na zaune tana kallo washe da baki ta amsa tana  cewa, “A’a wanake gani?” ta fada tana gyara dankwalin kanta ta  ce, “dan tselankwa na dauk’a baka zuwa ai” zama su sadiq su kayi saman two sitar suna murmushi ta  ce,  “mai gida ai na dauka baka zuwa godiya? mu d’au zunkudediyar budurwa mu baka amma ko leqe? yar dariya sadiq yayi wanda iya karta la66ansa dan shi a gaskiya har mantawa yake da Basma a matsayin matar da zai aure ya ke, Ammi ce ta katse masu zance  da cewa, “bari na kawo maku fura,”
“to Ammi amma dai taji nono?
“ina ruwan ka da abinda zata ji? nifa dan mai gida nake badan kai ba, kai har gajiya nake da ganin ka wallahi” dariya majeed ya saki ya  ce “naji ba komai  ai danayi aure kin bar ganina wallahi,” wani miyau mai daci sadiq ya hadeye tare da kallon majeed ta qasan ido Ammi  ta  katse  masa tunani  da  cewa, “kai dai ka sani” sannan Ammi ta shige kitchen ta dauko masu fura a fridge tasha nono ta aje masu, sun sha sosai sannan suka dinga zuba fira suna cikin hira Alhaji babba ya shigo shima aka dasa da shi, sai kusan yama likis sannan suka wuce part din Umma inda umma ta dinga nan da sadiq dama can dan gaban goshin tane bale kuma yanzu da zai auri auta sai da suka sha fira sosai kiran sallah magrib ne ya tashe su dauro alwala su kayi suka wuce masallaci.

Bangaran su fatuha ko tana tashi wanka tayi, sannan ta shafa lotion mai kamshi ta zura after dress black ta mata kyau sosai sai dai tayi yar rama kad’an saboda tunani, parlour ta fito ta iske Basma na kallo cikin fara’a ta qaraso ta zauna kusa da ita, yar hira suka ta6a sama-sama sannan suka shige kitchen kusan a tare suke aikin, inda baba jummai ke ta bin fatuha da kallo saboda gabaki daya yanzu fatuha bata walwala ga wata yar rama da tayi, haka dai suka dinga aikin bayan sun kamala Basma da rabi’a suka kwashe kulolin suka kai dining area, a lokacin ne baba jummai ta ja fatuha gefe tana mata yar na siha kan tayi hakuri kar ta jama kanta ciwo ta  rage tunani, dan ta lura kwana biyu nan ko  abinci bata ci, kuka tasa mata lallashin ta baba ta dinga yi har ta samu tayi shuru tana qoqarin goge hawayanta Basma ta shigo kallon ta tayi ta ce, “Fatuha me ya saki kuka?” murmushi fatuha ta qakaro wanda iya karshi la66an ta ta ce, “Albasa ce ta shigar min ido”
“eyya sorry ke je ki wanke fuskar” to tace tare da fita daga kitchen din, ko da ta shiga toilet sana’ar ta cigaba wato kuka sai da tayi san ranta ta fito kaya ta canza tasa riga da skirt na atamfa ash mai ratsin pink masha Allah kayan sun mata kyau, sai dauri da tayi kasancewa hutu take ko sallah ba tayi ba.
fitowarta daga daki yayi dai-dai da shigowar su majeed mutuwar tsaye majeed yayi yana binta da kallo dan ba qaramin kyau ta masa ba, son ta  da  kaunarta  ne  ya  qara  lullu6e majeed, haka shima sadiq ji yake kamar yaje yayi hug nata saboda  ba  qaramin  kyau  ta  masa  ba cikin sauri-sauri majeed ya qarasa wajanta yana sakin smile ya ce, “My love kinyi kyau” murmushi fatuha tayi wanda iya karshi la66an ta sadiq na tsaye bakin kofa dan ko qarasowa ya kasa, kamar zai rungume ta majeed yayi yana magana can qasan  maqoshi yarda  futu  kad’ai  zata  iya ji “My love kullun qara kyau kike, ji nake kamar na jawo lokacin auran nan namu” sadiq dake gefe sai hadiyar bakin ciki yake dan har ya fara ganin jiri a hankali yake jefa kafarsa da bai san inda zai wurga ta ba, har ya samu ya haura upstairs tun kan ya Isa bedroom ya fara tari da bin bango ya isa toilet, tari kawai yake tare da jini zamewa yayi a qasan toilet yana mai da numfashi yana cire buttom  din rigarsa dan ya samu iska ya dau mintina goma yana a haka, a hankali ya ja jiki ya koma bedroom  kayan jikinsa ya rage yasa jallabiya ya bude bedside drowe ya ciro magani ya sha tare da shigewa blanket saboda fever dake damun shi a yanzu, lumshe ido yayi wasu hawaye masu zafi daya na bin daya.

      Sakin ta majeed yayi tare da yi mata peck a goshi kallon kofa tayi wayam ba sadiq ba alama, haka shima majeed, “oh sweetheart kin ga kin rudani da yawa ko sadiq na manta da shi” ya fada yana dan langwabe kai, fatuha da ta cika taf dan qiris take jira ta fashe daurewa kawai take ta ce, “Ai sai ka bishi..! ta fada tana qaqorin shigewa bedroom  hannun ta ya riqe yana  sakin murmushi ya dawo ya rungume ta ta baya rintse ido tayi tana jin wata tsanar shi cikin  rawar muryar ta ce “Majeed please ka bari? so kake su Mom su fito su ganmu haka? ta fada tana qoqarin kwace kanta majeed ya  ce, “uhm to me dan sun ganmu how many day’s ya rage ki zama tawa”
“naji duk da haka ai da kunya” fada  tana sa masa kuka sakin ta yayi yana bata hakuri ko sauraran shi ba tayi ba ta shige daki tare da fadawa saman bed ta saki kuka.

       Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wasu na farin ciki wasu na bakin ciki, inda ciwo keta cin sadiq dan yanzu sosai yake zubar da jini duk da yana shan magani da zai sa yaji sauki, amma abun sai gaba yake dan har ya fara fida rai da duniya.

      Cikin kayan ta na uniform take shiri duk da jikin ta ba kwari, bayan ta kamala ta fito su Mom na zaune suna break cikin nutsuwa ta gaishe su ta zauna ta jawo cup zata hada tea, kamshi turaran da ya doki hanci tane ya sata waigowa, sadiq ne sanye cikin  uniform dinsa masha Allah yayi kyau sai yar rama da yayi gaishe da Mom yayi tare da yi mata peck ya ja kujera ya zauna, cup fatuha ta jawo zata hada masa tea, da murmushi Basma ta mika hannuta amshi cup din dake hannu  fatu ta ce “Fatuha barshi kawai na hada masa da  kai  na, tunda ke kinga school zaku tafi karku makara” miqa mata cup din fatu tayi jiki ba kwari ta zauna tana juya nata tea din idanuwan ta taf da kwalla, taki yarda ta dago idanuwanta? kuma taki shan tea din, tana gama had’a tea din ta miqo wa sadiq yana miqa hannu zai amsa ya saki cup din ya fadi tea din ya bare a dining area dagowa fatuha tayi saboda tea din ya zuba, kallon sadiq take shima ita yake kallo lallausan murmushi ya sakar mata Basma da  duk  ta  rud’a ta  ce, “yaya sadiq tea din bai bata maka kaya ba ko?
“Eh Basma”
“ok bari na hada ma wani”
“barshi kawai nama koshi” dan 6ata fuska tayi, tana kallonsa ta ce “Yanzu baza ka ci komai ba? mom ce ta ce, “Kyale shi indai wannan ne ya saba da haka” to kawai Basma tace tare da fara tatare inda tea din ya zube.

        Kasancewar yau majeed be zo daukar fatuha ba yasa sadiq ne ya sauke su a makaranta, duk da ba wata magana sukayi ma juna ba amma hakan ba qaramin dadi ya masu ba, basuki su dawa ma a haka ba.

   2weeks letter

          Biki ya matso gadan-gadan yasa Mom ta samama amaran mai gyaran jiki, gyara suke sha sosai dan har sun fara murjewa da kyau da sheki dan yanzu Mom ko bari batayi su sadiq su  ga amaran.

       Tunda bikin ya matso kullun sadiq da fever yake kwana yana  tashi  duk  ya  wani  fige  ya  koma  Kala tausayi  kamar  ana  dibarsa ana  miya, gashi yaqi zuwa Dr yakub ya duba shi har yayi mita ya gaji, majeed  yayi  tanbayar  duniyar  nan  sadiq  ya  fada  masa  damuwarsa amma  fir yaki sai  dai  ya  ce, ba  komai.

        Majeed ne ya shigo bedroom din sadiq, sadiq na zaune saman sofa ya jingina ban da tunani ba abinda yake, dafa shin da majeed yayi ne ya sasa ya dago murmushi ya sakar masa sannan ya zauna, ya ce “Ga katin ka nan tun dazu nake kiran wayar ka bata shiga”
“na kashe wayar ne saboda bana son takura” sadiq ya fada “to ai shikenan yanzu dai ga katin daurin aura anjima zan amso na dinner” katin sadiq yabi da kallo sannan majeed ya sa kai ya fita yana fita sadiq jawo katin yana  kallo  wasu hawaye ne masu zafi suka zubo masa, a hankali ya fara daukar katin d’aya bayan d’aya yana yagawa yana kuka, haka ya dinga bin kati yana cewa, “shikenan fatuha kin zama ba tawa ba, me yasa nayi nauyin baki? na kasa fada maki abinda ke rai na, duk  laifi  nane  da  nayi  wasa  da  damata, har  na  bari  majeed  ya  rigani  furta maki  abinda  ke  rai  na, shikenan na  rasa  farin ciki na, fatuha bana iya rayuwa bada ke ba..! ya qara rushewa da saban kuka😭.

      Zaune suke a bedroom, Hanan ta shigo da katin bikin, ta miqa ma fatuha nata da Basma wani irin murmushi Basma ta saki ta ce,  “Yanzu ni zan auri yaya sadiq? finally buri  na  zai  cika” ta rungume katin tana jin dadi, angel da shigowar ta yanzu kenan amsar katin hannu fatuha tayi ganin ansa majeed baro-baro jikin kati kirjin angel  ya  bada  ras-ras kallon su angel ta shiga yi kamar  yau  ta  fara  ganin  su ta  aje  katin  ta  karo  d’ako  wani haka  dai  idonta  ke  gane  mata  Babanta  da  Basma fatu  da  majeed bakinta na  rawa ta ce, “dama.. Dam.. Aunty fatuha uncle majeed zaki aure..? Baki  ta  kama bata ida zancan ba ta fita daga dakin da gudu tana kuka.

    Bata zame ko ina ba sai part din sadiq tun a parlour take kwallawa sadiq kira “Daddy..! Daddy.! Daddy..! Sadiq da fitowarsa daga wanka kenan yaji irin kiran da angel ke masa da sauri ya fito parlour tsaye ya  ganta tana  hakki  tamkar  wace  tayi tsere idanu ta  sunyi jawur  tashin  hankali  ya  fito  6aro-6aro a fuskarta tana  jifan  sadiq  da  wani irin kallo mai  cike  da  tuhuma, kirjinsa  ne  ya  qara  harbawa takowa  yake tamkar  me  sand’a ganinta da kati rike a hannu watsar da katin angel tayi suka  watse a  qasa tana kuka da  karfi  ciki daga  murya ta  ce, “menene  wannan daddy menene..! Sadiq  daya  rikice  ganin  abinda  angel  take  jikinsa na rawa ya  dauka ya  kasa  furta koda  kalma daya  angel ta  ce, “Dama daddy ba kai zaka auri Aunty fatuha? Mai  yasa  zaku  min  haka, ni  zaku  rusawa  farin  ciki, wallahi daddy ba zan ta6a zama da wata a matsayin uwa ba idan ba fatuha..! ta ida zancan tare da zamewa a qasa tana kuka kamar ranta zai fita, mamaki ne ya lullu6e sadiq bai ta6a tunanin angel bata san yadda abun yake ba, a hankali ya  qaraso kusa da ita tare da d’aga ta ya rungume kuka take sosai ta ce “Daddy in dai kana son farin cikina ka fasa auranka da Aunty Basma ayi da fatuha..! idan ko baka so a daura da Aunty Basma”
“angel me yasa baki son Aunty ki Basma? ya fada zai qara bude baki ya qara magana angel ta  dago  daga  jikinsa  tana  jifansa  da  wani irin   kallo na mamaki ta ce “Daddy baka so na, duk  kai  ka  jawo, me  yasa  baka  aureta  ba  tuntuni  ba..! Sadiq  zai  jawo ta jikinsa da  karfi  ta ce, “Just leave me alone daddy don’t…! ta  zaro  ido waje tana  kallonsa ta fita da gudu daga part din har ta bangaje fatuha da ta biyo ta lokacin da ta fita da gudu daga bedroom din su, kallo sadiq tayi dake tsaye ya kame kansa idanusa  sunyi  jawur, hawaye ne suka cigaba da yima fatuha zarya itama juyawa tayi da gudu ta bar wurin, zamewa sadiq yayi a gurin ya zauna hawaye  na  gangaro  masa  da  gaskiyar  angel  laifin sa  ne  shi yayi  wasa da  damarsu tarin da yazo masa ba  shiri  ne ya sasa miqewa ya shige toilet da gudu jini kawai ke fita yana tarin wanke face din shi yayi ya jingina da bangon toilet.

      Angel na shiga dak’i ta fada saman bed ta saki kuka, fatuha ce ta shigo dak’i dagowa angel tayi cikin d’aga murya mai sauti ta ce “Just leave me alone, bana  son  ganin  ku  ke  da  Daddy..! ta buga kofar daki’n da karfi zamewa fatuha tayi baki’n kofar ta saki kuka me cin rai dakyar ta iya jan jiki ta koma bedroom dinta bakin window fatuha ta tsaya tana raira kuka.
a hankali iska ke kadawa kasancewar hadari ke akwai, a hankali ruwa ya fara sakowa mai cike da sanyi da karfi rufe window fatuha ta yi ta zame gefen gado ta cigaba da kuka, haka bangaran angel  ban da kuka ba abinda take, tana tuna irin rayuwar da su kayi a baya cikin ji dadi, haka shima sadiq rayuwar su yake tunawa a baya me cike da so da kwanciyar hankali, kuka fatuha ta Kuma saki tare da jawo picture din sadiq tana kallo tana tuno lokutan da yake yi mata fada farkon zuwan ta gidan, dariya take mai kuka-kuka ta daura hannu ta saman picture din ta ce “Mai kyau ina son ka.! tun bansan me so ba nake son ka amma sai gashi lokaci d’aya na rasaka, rashi  na har abada harma  da angel zan zauna da wanda zan koyawa kaina son sa” wani saban kuka ne ya kubuce mata.

       Haka suka wuni ranar cikin kunci. duk yadda su Hanan suka tanbayi fatuha mike damunta? sai tace masu headache ke damun ta, angel ko fir taqi cin abinci dan ko kofar daki’n taki budewa, fatuha tayi magana tayi magana har ta gaji part din sadiq ta shiga yana zaune a parlour ya jingina da bango.
a hankali fatuha ta qaraso gaban shi cikin muryar kuka ta ce, “Mai kyau.! bude ido yayi na kallon fatuha kamar wanda ya dade bai ganta ba ta  cigaba  da  cewa, “mai kyau dan Allah kayi ma angel magana ta ci wani abu tun safe ta rufe dak’i taqi fitowa? sai faman kuka take please ka mata magana” lumshe ido sadiq yayi ya ce, “Fatuha I don’t now how to do angel bazata saurare ni ba, sai dai idan zan bi abinda take so, kuma  ba  zaiyu  ba  bakin  alqalami  ya  bushe” kuka fatuha ta kuma sadiq d’ago ta sadiq yayi yana lallashita, sun dauki mintin 30 yana rungume da ita kanta ya dago yana kallon kyakyawar fuskarta ya kumbura ya ce  “Ina sonki Fatuha..!

        Ina kaunar ki ! tun ranar da kika shigo gidan nan Allah ya jarabce ni da sonki, a da Ina tunanin wasa ne a yanzu da nake shirin rasaki na gane cewa kece farin cikina, ke ce abin alfabarina, kevce annurin zuciyata, ban taba tsamani zan iya son wata diya mace ba, bayan rasuwar matata ba sai gashi Allah ya hadani da wacce idan na rasata ba makawa mutuwa zanyi, wallahi fatuha zan iya mutuwa idan kin zama malakin wanina, wayyo Allah na 😭 nayi zurfin ciki na kin bayanar miki da ke ce linzamin zuciyata, da ace wani ne ba majeed ba koda Zayn ransa komai nawa bazan bar masa ke ba, sai dai kash majeed ya wuce duk yanda kike tunani a wajena ina son majeed son da zan iya sadaukar masa da komai nawa ciki Kor har da ke, ya ida zancan sa hawaye na ciki ba da ambaliya a fuskar sa,  Majeed da tunda Sadiq yafara magana yake tsaye baki’n kofa basu lura dashi ba domin sunyi nitsa a duniyar su ta masoya, kamar gumki ya zama zufa ne ke fito masa a ko ina, wani irin jirine yake daukarsa ji yayi kamar ya kurma ihu domin a tunanin sa mafarki yake, dakyar da taimakon addu’a yabar wajen ko gabansa baya gani, yana zuwa falo ba kowa da sauri yayi waje.

     Fatuha Ko wani irin farin ciki ne ya kamata, takara shigewa jikin Sadiq , A cikin zuciyar ta ta ce “Ya Allah na gode maka, ashe bani kadai nake haukana ba, kuka ta fashe dashi da ta tuna cewa baki’n alkalami ya riga ya bushe daman Sadiq yasan bazata iya bashi amsa ba, dan haka ya kara rungume ta suka ci gaba da kukan su abin tausayi😢.

         Majeed Na shiga motar sa ya jata da karfin tsiya, da sauri mai gadin ya bud’e masa gate saura kad’an ma yabi ta kansa , ikon Allah bala maigadi yace domin abun yayi matukar bashi mamaki Allah ya kyauta yace yashiga dakin sa ya kuna redio yana saurare.

          Gudu majeed yake saman titi kamar zai tashi sama hawaye na bin fuskarsa , kuka yak’e sosai gashi kuma yana tuki na fitar h’ankali duk inda ya huce sai an bishi da kallo, yana shan kwana wata babban mota ta shiga gaban sa ji kake  kuuuuuuuuuuuuu😭🙆‍♀Innalillahi wa’inna ilaihi raji’una.

  Vote
Comment

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.CM

87_88

this page is for you Aunty Rahenat ina jin dadin yarda kike bani goyan baya tare da min good editing and every single person that always comment on this novel, I am in love with your comments

Firgigit sadiq yamike yana sauke ajiyar zuciya, ya jiqe sharkaf da zufa dakyar ya iya miqewa ya bude fridge ya tsiyayo ruwa cup yana sha. tarine ya sarkesa lokaci guda da gudu ya shige toilet yana aman jini dakyar ya saita kansa ya dawo saman bed yana furta duk addu’ar da ta zo bakinsa yana maida numfashi, bai taba mumuna mafarki irin haka ba, kuka ne ya kubuce masa dan baya fatan ranar da majeed zai rasa rayuwar sa saboda furucinsa a kan fatuha, wayarsa dake saman bedside drawer yayi saurin rarimowa ya fara kiran layin majeed kira biyu zuwa uku majeed ya dauka da alamama yayi nisan bacci ya furta, “Hello baby.! hamdallah sadiq yayi tare da sauke sanyayar ajiyar zuciya ya furta, “dama wani abu zan tanbaye ka tunda bacci kake shikenan..! sannan sadiq ya katse wayar tare da komawa toilet ya dauro alwala yana rokan Allah ya rage masa son fatuha a ran sa.

***
Kiran sallah asuba ne ya tashi fatuha alwala kawai ta daura ta gabatar da sallah, bayan ta idar ne ta wuce daki’n angel a hankali ta murda kofar taci sa’a ta bude cikin nutsuwa ta shigo angel da fitowar ta daga toilet kenan ta daure fuska kamkar bata ga fatu ba ta jawo hijabinta tatada sallah.
Bakin gado fatuha ta samu ta zauna tana jiran jidda ta idar da sallah, ko da ta idar bata kalli inda fatuha take ba sai ma qoqarin barmata dakin da take, riqe hannunta fatuha tayi cikin sanyi murya ta ce, “Angel fushi kike dani ko? shuru tayi kamar ba da ita fatuha take ba sai ma qoqari zame hannuta da take jin ta kasa zamewa ya sata sakin kuka tana cewa, “Ni ki sake min hannu ki kyale ni tunda baki son babana? kin zabi ki zauna da wani ba daddy na ba..! hawaye ne suka fara yima fatuha zarya tana girgiza ma jidda kai ta ce, “Angel ya za ayi nace bana son abban ki? please ki daina fushi dani.! fatuha ta fada tana shafa fuskar angel cire hannu fatu angel tayi ta ce, “Idan har kuna so na kuma kuna son farin cikina a cikin gidan nan to ku fasa auran da zakuyi daga ke har daddy..! ta fada cikin daga murya sannan ta fita ta barma fatuha dakin kuka fatuha ta saki tana furta, “na shiga uku wannan wani irin abune gabaki daya duniya ta mana kunci, ya Allah ka kawo mana mafita.! fatuha ta fada tare da tashi ta bar dakin.

Haka angel ta dinga fushi da su fatuha dan ko saurarasu ba tayi, duk abin yabi ya dame su idan anga angel na magana to da Mom take gashi ta daurawa Basma karan tsana, dan ko bari batayi ta ta6a abu itama ta ta6a. abin duk yabi ya damu Sadiq tun Basma bata dauka abun da zafi har abin ya fara 6ata mata rai ga uban na mata diyar na mata.

Yauma kamar kullun mai gyaran jikin ta zo, tana masu kurkur tabi ko ina na jikin su dashi da saqo, sannan ta hada masu zuma cokali 3 madara peak ta ruwa rabin gwangwani da white egg 3 da lemon tsami d’aya ta had’a ta buga su ta murje amaran dasu, ga wasu turaru ka masu kamshi da suke wanka da su na tsumin lale. tuni fatar su ta fara canza launi ga wani sheqi da suke abunka da fararan fata ko kaya suka cire kamshi suke.

Bangaran kayan ni’ima ba’a magana dan wasu Mom da kanta take had’a masu, na kaza dana tantabara gashi kullun sai an basu madara da zuma sun sha kayan fruit ko har turewa suke, su kansu sun san tsumin nayi masu dan sun ga canji sosai a jikinsu, Mom ce ta saki murmushi ta ce “Kai amma wannan gyaran yana yi sosai.n! ji yarda suka murje yaran nan ku ni da nake mace idan na ta6a fatar su biyo ni take ina jin dadi bale kuma angwayan” rufe fuskar su sukayi dan Mom ba qaramar kunya ta basu ba.
bayan a gama gyaran jikin Mom ta raka batul mai gyaran jikin har bakin motar ta sannan ta juyo ko da ta dawo cewa tayi, su fatuha su hada duk abinda suke buqata dan jibi za’a koma family housa a fara gudanar da biki.

Jikin fatuha ne yayi sanyi, dan yanzu har ta fara fidda tsamani ya zamar mata dole ta koyawa kanta son majeed, ko da ta shiga bedroom dinta kayan ta ta shiga hadawa tana sana’ar wato kuka sannan ta aje trolley dinta a gefe.

Bakin wani hadadan gida sadiq ya tsaya da motarsa horn yayi mai gad’i ya bude gate, ya kunna hancin motarsa gaishesa mai gadi’n yayi a taqaice sannan yayi parking din motar suka fito tare da majeed kallon gidan majeed yayi ya ce, “Big man gaskiya gidan nan na da kyau” murmushi sadiq yayi ya ce, “Taho mu Shiga” babu abinda ba’a zubaba na morewar rayuwa ba cikin gidan, iyakar haduwa gidan ya hadu, sai dai kash ba muradin ransa bace zata kasance da shi ba, a wannan gidan ba haka suka gama zagaya gidan sannan suka wuce gidan majeed masha Allah shima gidan iyakar haduwa ya hadu dan sun kashewa gida jan kudi bana wasa ba, bayan duk sun gama dubawa sadiq ya aje majeed a gida sannan shima ya nufo gidan su.

Da sallama ya shigo angel na parlour zaune tana kallo, ciki-ciki ta amsa sallamar tana qoqarin barin parlour jawo ta sadiq yayi ya langwabe kai ya ce, “Angel nasan sarai kin san ba kyau fushi da iyaye? me yasa kike fushi da daddy kin uhm? nasan nayi laifi amma ya kamata by now an yafe min” kuka ta samasa tana cewa “Ni daddy Aunty fatuha nake so?idan ka aureta ka gama min komai” d’ago da fuskar ta sadiq yayi ya ce, “Me yasa baki son Aunty Basma? tana fa sonki angel, tana maki’n duk abinda kike so, kuma Aunty ki ce ko ba komai?” bata rai tayi ta ce “Ni bana son ka aure ta ne that is all.! ni Aunty fatuha nake so..! fuuuu ta wuce sadiq tayi daki tsaye sadiq yayi yana mamakin irin kafewar jidda jikinsa yayi mugun sanyi, fatuha dake qoqarin fitowa daga kitchen tayi lamo tana jin duk abinda suke, haurawa sama sadiq yayi ya wuce part dinsa fatuha tana ganin haka sai ta bi bayan shi a hankali ta bude kofar dakin.
tsaye ta hango sadiq a hankali ta isa ta rungumesa ta baya wani irin yar sadiq ya ji tun daga kansa har d’an yatsan sa na kafa har itama fatuha din, juyo da ita sadiq yayi suna facing juna yana smile dan ja mata hanci yayi yana binta da wani irin kallo ba qaramin kyau tayi masa ba, a hankali ya kai mata peck a goshi yana jin wani sauyi sosai a jikin fatu, itama peck ta masa tare da zame jikinta ta zauna zaman sofa, biyota sadiq yayi tare da kneeldown a wajan yana kallon kyakyawar fuskar ta ya ce, “Fatuha kinyi kyau..! yar dariya tayi tare da rufe fuskar ta, murmushi sadiq yayi a hankali yasa hannu ya cire hannuta dake fuskarta hawaye ya gani suna mata zarya, langwabe kai sadiq yayi dan shima da zai samu dama da kukan zaiyi, tashi yayi ya zauna saman sofa kusa da ita jawo ta jikinsa yayi yana lallashinta cikin sanyin murya can kasan maqoshi, “Please fatuha ki daina kukan nan please bana so.! lamo tayi a fafad’an qirjinsa tana jin bugun zuciyarsa tana jin wani irin feeling na da ban wanda bata ta6a jinsa ba sai akan Sadiq shima din yau, shima haka yake ji a hankali take sauke ajiyar zuciya, d’ago da fuskar ta sadiq yayi yana bin ta da kallo mai cike da so, zuciyarsa sai bijuro masa da wasu abubuwa take zame jikinsa yayi tare da komawa saman bed ya zauna yana kallon fatuha, itama di’n shi take kallo tamkar yau suka fara ganin juna, kauda kai tayi tana wasa da yan yatsun hannunta, miqewa tayi tana qoqari tashi sadiq ya ruqo hannuta tare da jawo ta ta fada jikinsa lallausan murmushi ta saki tana kallon kwayar idonsa kamar yarda ya kafe la66anta da ido a hankali ya daura lips dinsa saman nata ya fara kissing nata sosai sadiq ya fita hayacinsa yana kissing fatu jikinsa har rawa yake, kasancewa fatuha tasha tsimi har ta gaji hakan yasa ta kasa hanasa itama d’in martani take maida masa tamkar zasu cinye juna su, sai da sukayi kissing juna su san ran su sannan suka saki juna, suna bin juna su da kallo suna sauke numfashi cikin cool voice sadiq ya ce “Fatuha..! lamo tayi tana jin shi dan har bata san abinda zai sa ta matsa kusa dashi, shafa gashin kanta ya shiga yi a hankali hakan ba qaramin dad’i yake ma fatuha ba, tana jin yarda hannu sadiq ke mata tafiyar tsutsa a dokin wuyanta can kamar an tsinkuli sadiq ya miqe yana tari da sauri ya shige toilet fatuha ta biyo bayan shi tun kafi ta iso ya kule toilet din da key, dan baya so taga halin da yake ciki, aman jini yake sosai ya dade a toilet din yana abu d’aya fatuha ko duk ta rude sai faman kiran suna sa take tana yan hawaye yana bude toilet ta fada jikinsa a rud’e tana created “Mai kyau me ke damun ka please ka fada min?” ta fada ta shafa masa gefen fuskarsa saman bed ya hau tare da jawo fatu ya ce, “Ba komai kawai na kware ne” haka fatuha ta dinga masa sannu sannan tasa kai ta fita.

Washe gari

Bayan fatuha tayi wanka ta shirya cikin lace dinta maroon mai kyau masha Allah tayi kyau har ta gaji, fatar jikinta sai sheqi take ko da ta fito parlour ba kowa bedroom din angel ta shiga kwance ta hango ta, d’an girgiza kai fatuha tayi tare da bud’e wardrobe ta tafido trolley jidda ta fara zuba mata kayan ta sai da ta gama zuba kayan tsaf ta aje trolley din tana qoqarin fita angel ta tashi ta ce, “Aunty.! cikin sanyin murya juyowa fatuha tayi tana kallon jidda idanuwan ta taf da kwalla da gudu jidda ta rugu ta rungume fatuha tare sakin kuka itama fatuha kamar jira take ta fara nata kukan ba mai lallashin wani sai da suka ci kuka son ransu sannan suka yi shuru suna sauke ajiyar zuciya a tare angel ce ta dago ta ce “Aunty shikenan yanzu bazaki auri daddy na ba? dan smile fatuha tayi tana goge hawayan idonta ta ce, “Angel bai kamata kina damun kanki ba kinji? idan kina son bina sai ki bini mu zauna tare” 6ata fuska angel tayi ta ce, “Aini nafi so na ganki da daddy bada kowa ba”
“Na sani angel, amma shima uncle majeed ai daddy kin ne, da shi da Abban ki duk daya ne, ko kin manta irin son da second daddy yake maki ne My angel Uhm” haka dai fatuha ta dinga lallashin angel sannan ta tafi.

Direct part din Sadiq ta wuce a hankali ta bude kofar part din ta shiga, parlour ba kowa sai kamshi dake tashi bedroom ta shiga kwance ta hango shi qudidine cikin blanket, a hankali ta qarasa zama tayi gefen bed din, a hankali ta fara janye blanket din tana kallon face din sadiq a hankali ta kai masa peck a goshisa, ware sexy eye’s ball’s dinsa yayi ya sauke su kan fatuha smile ya saki tare da juyawa ya gyara kwanciya dai-dai saitin kunan shi ta ce cikin cool voice din ta “Uncle ka tashi kowa ya gama shiryawa kai kadai ake jira” ware idanuwa yayi yana kallon ta jawo ta yayi ta fad’a saman fafadan qirjinsa ya ce, “Fatuha me yasa kike so ki katse min bacci, ko kun tafi zan iya biyo ku okey.! lamo tayi a qirjinsa ta ce, “Saboda na dinga kallon ka kafin muyi nisa da juna, shiyasa na tashe ka” ta fada idanuwan ta taf da kwalla tashi zaune sadiq yayi yana facing nata shima ji yake kamar yasa kuka, kawai daurewa yake shiyasa yake nuna mata rashin damuwarsa langwabe kai fatuha tayi ta ce, “Ka hada kayan ka ne?
“nope.!
“ok bari na hada ma”

Haka fatuha ta shiga hada ma sadiq kayansa yana kallkn ta saida ta gama hada kayan tsaf tabi daki’n da kallo, kuka ya kubuce mata saboda tunowa da rayuwa da sukayi a baya shikenan yanzu rayuwar ta zama tarihi kuka take sosai, har da durkushe shikenan son da takewa sadiq ya sha ruwa, dagota sadiq yayi ya jawota jikinsa yana lallashi a hankali ta fara magana, “Mai kyau me yasa mutum baya samun abinda ya ke so a lokaci da yake so? ta fada tana qara rushewa da kuka a hankali sadiq ya lallu6o lips din ta ya fara mata hot kiss wanda shi kanshi bai san yana hakan ba, har suka zube kasan carpet bai kyale ta ba har sai da ta tsaigaita kukan, tana sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ya sake ta yana maida numfashi, hada face nasu yayi guri guda yana magana can qasan makoshi mai kama da rad’a ya ce “Fatuha please ki dai kuka, dama shi rayuwa bai zama dole mu samu duk abin da muke so ba, muyi hakuri jarabawa ce daga Allah, insha Allah zai bamu sakamako mai kyau, dan haka muyi addu’a Allah yasa hakan shine mafi alheri a gare mu, kuma ki daina kukan haka saboda yana tadamin da hankali a duk sanda naji.! d’aga kai tayi tare da kauda kanta dan gabaki daya kunya ta lullu6e ta, tashi tayi ta fita da sauri daga bedroom din, ko da ta fita jingina tayi da kofar tana maida numfashi a hankali ta daura hannuta saman lips din ta, ji tayi kamar an yaye mata bakin cikin dake damun ta sannan ta fito da gudu d’aga part din haka shima bangaran sadiq haka yaji.

Bayan kowa ya gama hada kayan shi su ola suka wuce da su boot gabaki d’aya, jikinta fatuha susuku yayi, haka sukayi mota 5 fatuha ta dade tana kallon gidan sannan suka bar harabar gidan suka harbawa kan titi,

***
Bayan sun Isa family house dangi har sun fara cika, take jikin fatuha yayi sanyi dan tasan tabbas ta rabu da sadiq har abada, haka shima bangaran sadiq hakan yake ji a ransa.

Bayan sun dan huta kowa ya aje kayan shi inda ake ajewa, aka kira mai lale ta fara yima amaran lale kafin ka ce me qawayan amaran sun fara halara, Zara da Nana har sun zo sai rawar kai suke zubawa, sallamar da akayi ne yasa fatuha juyowa cikin fara’a, waza ta gani inba fatsima ba, da gudu ta ruga ta rungumeta cike da murna haka itama tuni dakin ya dau shewa duk da fatuha ba jin dad’i take ba, amma ganin fatsima ba qaramin dadi ya mata ba, hakan yasa ta fara walwala.

Bangaran Basma ma haka qawayan ta duk sun hadu yan gayu masu ji da kan su, sai shewa suke suna taya Basma murnar samun handsome kamar captain sadiq, sai pictures suke kamar ba gobe kowa ce ka duba face nata kasan cikin farin ciki take.

Angwayan ma friends nasu da suke qasashan waje har sun fara sauka, haka part din nasu ya cika taf da bakin gida dana ketare, duk wannan abun da ake sadiq na gefe ya zuba masu na mujiya kamar ba abinda ke damonsa, sun san halin miskilancin sa shiyasa ba kowa ya damu da hakan ba sai Dr yakub dake ta faman lura da shi dan yasan sarai ciwo ne ke cin sa kowani lokaci zai iya faduwa…

fan’s kuyi hakuri da wannan page din ba yawa, saboda ina school shiyasa, abubuwan sunyin yawa ga shirye-shiryan fara exam amma insha Allah gobe zan maku page mai yawa idan na samu dama

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                          89_90

                        Shirye-shirye suke sosai kasancewar yau ake kamu, da misalin karfe 4:00pm kowace ka gani shiryawa take cikin ashobe, Fatuha da ke zaune cikin toilet tana sana’ar kuka knocking din kofar da akayi ne ya sata miqewa tana share hawayanta, Hanan dake bakin kofar ta ce, “Fatuha ki fito me make up ta zo har an gama ma Basma ke kadai ake jira” to tace tare da yin sauri ta watsa ruwa ta fito.

                         Ko da ta fito shaharariyar me make up fandi ta zo fatuha kawai take zaman jira, tana  daure da towel ta fito ta zauna tana  shafe jikinta da mai, Aunty bilki ce ta shigo da kayan da zasu sa washe da baki ta aje kayan ta  ce, “a’a fatuha dama ba’a gama make up din ba” daga kai fatuha tayi Aunty bilki ta  cigaba  da  cewa, “ya kamata kuyi sauri ku shirya kar ku 6ata lokaci saboda da kun dawo zaku dinner” to tace sannan Aunty bilki tasa kai fa fice, a hankali fandi ta fara tsantsara mata make up kafin ka ce me fatuha ta fito wasu peak materials tasa gown mai stone’s masha Allah tasha kyau har ta gaji, kanta na  daure da head silver,  ita kanta me make up ta yaba da irin kyan da fatuha tayi, su fatsima ne suka shigo sanye da ashoben su ash atamfa mai ratsin peak suma sun sha head  kun san a tare suka fito da Basma kusan kaya colours daya suka sa har yan mata amaryar anko daya su kayi, motoci ne masu numfashi da tsada suka faka amaran suka shige ba a zame ko ina ba sai meenah event hadadan hall na party iyakar  haduwa hall din ya hadu, kuma ya qayatar kasancewar kamun na mata zala ne shiyasa ba ango ko daya sai yan’mata da iyaye, yan asharale ne suka fara buga ganga tuni hall ya dau sauti amaran zama su kayi ma zaunin su  aka fara gudanar da shagulgula, su fatsina da Nana da Zara fili suka shiga suna ta kwaso shoki haka suma qawayan Basma biki yayi biki sai dai muce Alhamdulillah .
Fatuha ko duk wannan bidirin da ake zuciyar ta naga muradin ranta, ji take kamar ta rushe da kuka kallon kowa take da ke farin ciki da walwala angel ta hango itama ba laifi ta saki jikin ta tana warwasawa.

                  Anci ansha inda aka raba turaru kan wuta da atamfofi masu tsada sosai, aka raba kaya kamar ba’a so, sai kunsan yamma liqis taro ya watse suka dawo gida.

                   Ko da suka dawo wanka amaran suka qara tare da dauro alwala suka gabarta da sallah magrib da isha, sannan amaran aka fara shirya su cikin wani wanka ni kai na har mamaki nake irin shirin da akayi ma bikin, lace suka sa blue mai ratsin dark blue mai shegen tsada ga make up da aka qara zuba masu sai kamshi suke, yan matan amaraya ko pink lace suka sa mai ratsin white  kowa ce tasha make up,  fatuha ko saboda tsabar kyau kasa gane ta kake, dan ba qaramin kyau tayi ba  kuma ga annuri da ya sauko mata na amarci, Basma ma ba’a barta a baya ba tayi kyau b sosai.

                   Shiryawa angwayan suke cikin  getzner shada blue tasha aiki da dark blue zare malin-malin, duk wannan shirin da sadiq keyi jinsa yayi suku-suku dan kwata-kwata baya tare da walwalarsa links yasa ma hannun rigarsa sannan ya daura agogo a tsintsiyar hannusa hublot ya zura takalminsa black mesarath tuni ya fito yana sheqi da wani irin kyau, sajan fuskarsa ya  kwanta luf-luf  ya  daura hula wadda  ta  dace  da  kayan gashin kansa ya leqo ta gefe-gefan hular feshe jikinsa yayi da turare masu kamshi da sanyi dadi kusan shigar su iri d’aya da majeed shima ba’a barshi baya ba dan yasha kyau har ya gaji, sai murmushi yake saki fararan haqoransa na bayana, aboka nan angwayan ma ba’a bar su a baya ba dan suma sunsha kyau ko wana su sai sheqi yake, Khaleed sai rawar kai yake zuba wa haka shima Dr yakub ba’a bar shi a baya gayu su kayi na sosai abun ka  da bikin manya.

                Cikin natsuwa suka fito suka shige  motocin su Benz black, haka  motocin masu zafi suka  harba kan titi dan dauko amaran kasancewar a hotel suka shirya, ko da suka iso amaran sun shirya tsaf motoci aka fara shiga kowace amarya ta shige motar angonta,

         Da murmushi majeed ya dubi fatuha da wani irin kallo mai cike da so da kauna, ba  qaramin kyau  ta  masa ba  ga  wani fitinan kamshinta  daya mamaye hancinsa mai kashe jiki, a hankali daura  hannusa  saman na fatu yana kallon lalan dake hannuta ja da baki yayi wani irin kyau ya ce, “My love lalan nan yayi kyau, bama shi kadai ba  harda ke  din ma” smile tayi wanda iya karshi la66anta  ta janye hannuta daga cikin na  majeed ta qara manewa karshan kofar tana tuna abin sonta.

                    Da kallo Sadiq yabi Basma ba laifi ta masa kyau, yau ce rana ta farko daya fara ganin kyanta ayanawa yayi a ransa, tunda ya ga Basma haka to ya fatuha zata kasance? wani irin kishi ne ya lullu6esa da qunar zuciya juyowar da yayi ne su kayi ido hudu da Basma smile ya sakar mata da kauda kai.

                   A dai-dai affcent center motocin suka faka lokacin har wasu sun halara tun daga bakin hall din kana jiyo irin sautin dake tashi, wajen ya hadu ba karya, kallo  daya  zaka masa  kasan  naira  tayi kuka wasu kujeru ne na  alfarma  a hall d’in wanda ko  ba’a  fada ba  zaka  gane  hall  din  na  d’an wane  da  wance  ne, jerawa yan’matan amaran sukayi masu ashobe, haka suma  abokan  angwayan suka  jera  reras masha Allah shigar ta su yayi kyau, amaran suka shiga tsakiya da angwayan Sadiq sai bin fatuha yake da kallo bugun zuciyarsa na daduwa, ta masa  wani  irin kyau ita kanta fatuha ta qasan ido take kallon sadiq tana jin wani irin kishinsa dan ba  qaramin kyau ya mata ba.
A natse suka shigo hall din, wajen ya gwarare da shewa da ihu, tuni aka canza salan kida da sauti majeed hannusa na maqale dana fatuha yadda ya shige mata kamar zai maida ta ciki, sadiq ya cika taf dan har ya fara jin kirjinsa na masa zafi duk  sanyi AC dake ratsa hall baya ji sai zafi  da  yake ji zufa na  karyo masa, kidin da  aka saki  sai  ya  qara  dagula  masa lusafi ya  fara  hanging jiri riqe hannu Basma yayi dan ba yadda zaiyi dan baya so ya bata ma qansa rai, ko bai so Basma  so  na aure ba yana sonta a matsayin ta na kanwar sa, sosai ya  damke  hannuta yana  sauke numfashi a hankali dake  neman kwace masa, ko da suka shiga gurin zama suka yi aka fara gudanar da shakali, can na hango su Aunty Rahenat anata kai kawo anzu shagali😜 ashe abin ba ita kadai ba ce har da yan Real Hausa fulani writers, can na hango Fulani da Aunty Rahama Nalele suna rabawa mutane kayan motsa baki, nima dai ba’a barni a baya ba dan na shiga a dama dani shoki kawai ake kwasowa.

          A hankali  majeed ya matso daf da kunan fatuha ya ce, “My love yanzu fa gobe kamar yanzu kin zama tawa ko? yana magana yana wasa da yan yatsunta Sadiq dake gefe yana kallon su bakin ciki na qara qumesa, dafe kirjinsa yayi domin yafara yi masa nauyi, zufa sai  karyo masa take tamkar wanda ke  bakin wuta a hankali ya miqe ya saci jiki ya bar guri tunda ya fito daga hall din jiri ke di barshi yana  had’a hanya yana  sauke  wani  irin numfashi mai  baraza na  da  rayuwarsa, ko gabansa baya gani dakyar ya iya isa inda akayi parking motarsa  ya daura hannusa kenan ya ji an riqe hannunsa, waigowa yayi su kayi 4 eye’s da Dr yakub girgiza kai Dr yakub yayi ya ce, sa…!! bai furta abinda yayi niya ba ida sadiq ya fado jikisa sumame, rudewa Dr yakub yayi ya  cewa, sadiq..! captain..!  ka ga sadiq tashi ka  ji kalle ni ka  bud’e ido karka mana haka, ka  gani  ko abinda  zurfin  cikin ka  zai  ja  mana karka barni aboki na ka  ji  captain.! kuka yakub yake  sosai  ya  rude  ya  rasa  abunyi daukar sadiq yayi cak yasa a mota ya bar harabar gurin da gudu..

           Duk  wannan bidirin da ake  ba  wanda  yasan halin  da  sadiq ke  ciki  sai  Dr yakub, MC ne  ya  fara cewa, “amarya da ango  su  fito  su  yanka cake ango ya ba  amaryarsa itama ta basa” saukowa sukayi a hankali  suka  tsaya majeed ya yanka cake d’in yaba fatuha a baki itama  ta  basa hall din ya dau ihu, sadiq aka kira da Basma amma ba ango ba alama haka MC ya dinga kira ango ganin abin kunyar dake shirin faruwa yasa Khaleed hawa a matsayin ango yaba Basma cake a matsayin sadiq tuni hall ya dau tafi, Basma iyakar cika ta cika bata taba jin bacin rai ba irin na yau, yaune ta tabbatar da sadiq bai sonta kuma ba zai taba sonta ba tunda har ya iya wulaqantata gaban bainar jama’a, idanuwan ta taf da qwalla, tana tausayawa kantada irin rayuwar da zatayi a gidan Sadiq, haka akayi taro kusan duk abinda ango zaiyi ma amarya Khaleed ne yayi ma Basma.

                Ko da fatuha ta juya bata ga sadiq ba tuni idanuwan ta suka kawo ruwa, dama shi take gani tana jin sanyi a ranta.

            Ko da Dr yakub yaja mota basu zame ko ina ba sai asibitinsa, suna shiga aka turo gadon daukar marasa lafiya  sadiq da yanzu idanuwansa sun fara budewa saboda  oxygen d’in dake  manne  a  hancinsa haka yake ganin asibitin na juya masa numfashinsa na sama-sama, Dr yakub kuwa  kuka  yake  sosai, emergency aka wuce da shi doctorsa sun dade a kansa Dr yakub ma kasa shiga  yayi sai zarya da yake a bakin kofar kusan 1 hour suka dauka sannan aka fito da sadiq manne da oxygen a hancinsa daki aka bashi tare da sa masa life sport machine sai qarin jini da ake masa, a hankali Dr yakub ya qaraso gaban gadon yayi kneeldown, hawaye ne ke masa zarya  a hankali ya kai hannusa ya shafa sumar kan Sadiq ya ce, “Friend why me yasa kake bama kanka punishment haka? why sadiq.! ya ida zancan hawaye masu zafi na gangaro masa wayara ce dake  ringing ciki aljihu ya curo tare da kallon suna dake maqale a screen din majeed, kashe wayar yayi gabaki daya tare da jawo wayar sadiq ya kashe sannan ya dau kayan sadiq da aka cire masa yaba daya daga cikin ma’aikatan  asubitin su wanke.

          Bayan ankamala dinner kowa ya dau hanyar zuwa masaukinsa majeed sai kiran layin sadiq yake, baya shiga dana Dr yakub, yana mamakin  abun ya  faru yau ya  rasa  mai  ke  damun  sadiq hakura  yayi da kiran tare da maida wayar aljihu.

                  Bangaran Basma ko kuka take sosai tare da taqaicin amincewa da auran sadiq, Khaleed sai bata hakuri yake tare da ganin rashin kyautawar sadiq ya rasa dalilin da zai mata irin wannan cin fuskar bayan tana qanwarsa kuma matar da zai aura, shi a ganinsa duk wanda ya samu Basma a matsayin mata ya mure, ya rasa me yasa sadiq ke nuna rashin ko in kulla a kanta, kuma  majeed  na  gani  ko  ba  komai  yasan  dole  zai  ji  haushin sadiq da wannan tunanin suka qaraso gida ko Godiya bata masa ba ta shige gida da sauri tare da tsananta kukanta.

      Motar su fatuha na fakawa majeed ya fara jero mata kalaman soyayya tare da jan ta  jikinsa, ganin zai wuce gona da iri yasa fatuha sakin kuka,  lallashin ta majeed ya shiga dan  kukan fatu na  d’aga masa  hankali yayi mata peck, ko saurara shi ba tayi ba ta bale murfin motar ta fita da sauri.

        Bangaran sadiq ko bashi ya tashi ba sai wajan 2:00am na dare  a hankali yake ware sexy eye’s ball’s dinsa da wani irin ishin ruwa ya tashi, Dr yakub da ko rintsawa baiyi ba ya miqe da sauri ya qaraso wajan shi cikin cool voice sadiq ya ce, “Ruwa..! da sauri Dr yakub ya bude fridge ya dauko rubar ruwa ya bashi ko da ya sha ruwan miqewa yayi yana qoqarin cire jini da ake qara masa riqe hannusa Dr yakub yayi ya ce, “Captain me kake shirin aikatawa? ya fada bakin shi na rawa kallonsa Sadiq yayi ya ce, “so nake na tafi gida bana so majeed ya gane bani da lafiya, na  san  yanzu  haka  Basma name fushi  dani, na  ruguza  mata  farin cikinta  saboda  rashin  hakuri  na” ya ida zancan yana cire qarin jinin wasu hawaye ne masu zafi suka zubu ma Dr yakub ya ce, “Sadiq wai me yasa kake so ka raya rayuwar wani ka bata taka? why sadiq? Dr yakub ya fada yana jijiga sadiq kuka sadiq ya saki tare da cewa “ka  dai kiran  majeed da  wani  d’an uwa nane kuma  na  jini, bazan ta6a bari majeed ya mutu saboda bakin ciki na ba, nafi son farin cikin majeed a kan na kowa a duniya, bani da d’an uwa sama da majeed, kasan  ko  ya  majeed  ya  ke  waje na  yana  so na yana  son  farin  cikina, tunda  da  nake  da  majeed  bai  ta6a nuna  min  abinda  yake  so  ba  kamar fatu  ba, ina  iya  ce ma  kan  fatu majeed  ya  san  me  so saboda haka ban taba bari saboda ni ya rasa rayuwarsa..! sadiq ya ida zancan yana kuka mai tsuma zuciyar mai saurare a hankali ya ida cire kayan asibiti dake  jikinsa yasa kayansa wayarsa ya dauka tare da kunna ta Dr yakub mutuwar tsaye yayi yana bin sadiq da kallo cikin  bacin  rai ya  ce, “kai  taka  rayuwar yaya  za’ayi  da  ita, kai  taka  zuciyar  ayi  yaya  da  ita? Sadiq  ka  fahimce  ni  kafi majeed  buqatar  fatu, kafi  majeed  son  ta, ka  duba  halin  da  kake  jefa  kanka, ka  falasa  abinda  ke  ranka  tun  kafin  gobe  fatu  ta zama  malakin majeed..! tabbas yanzu yasan me sadiq yake nufi so yake ya rasa rayuwarsa ya zamar masa dole ya kawo karshan abunan ko saurarashi sadiq bai yi ba saima car key daya dauka tare da fita yana ingisawa…..

Vote
Comment

Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘 REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                         91_92

                    A hankali yayi parking motarsa ya mata key, harabar gidan tsit ba motsin kowa sai motoci birjik kamar wajan saida mota, a hankali ya cigaba da takawa duk da yana jin jikinsa kuka-kuka ya fara ji sama-sama hakan ne ya sasa tsayawa tare da kallon agogo hannusa mamaki ne ya lullu6e sadiq a hankali ya fara bin inda kukan ke fita, fatuha ce zaune sama resting chair tana raira kuka, qarasowa yayi gabanta firgigit ta dago a tsorace ganin sadiq ne yasa  fatu mikewa tsaye ta ruga da gudu ta fada jikinsa ta qanqamesa tare da sakin wani irin kukan, rungume ta sosai sadiq yayi yana jin kukanta har cikin ransa tamkar shima ya fashe da kukan ko ya samu sauki cikin zuciyarsa daurewa kawai yake, d’ago fatu yayi suna kallon juna  jawo hannuta yayi suka zauna a hankali yake shafa bayanta ba wanda yace ma dan uwansa ko da kalma daya, sun dau kusan 5 minutes a haka fatuha ce ta dako tana kallon sadiq kamar yarda yake kallonta  cikin sanyin murya ta ce “Uncle.! ya naji jikin ka da zafi? dan smile sadiq yayi ya ce “Nima haka naji jikin nawa” kallonsa take cike da kallon tuhuma da tanbayoyi fal a zuciyarta ganin yarda ya rame ya zabge amma sai ta kasa magana komawa tayi saman fafadan qirjinsa tayi lamo tana sauke numfashi a hankali, kunsan a haka suka zauna har bacci ya dauke fatuha idanuwan sadiq biyu yana kallon fatuha har sai da ya fara jin kiran sallah asuba sannan ya tashe ta ya ce, “Dear tashi asuba tayi?” qarayin lamo fatu tayi jikin sadiq ta qanqamesa shafa gashin kanta yayi a hankali ya furta, “Fatuha..! a hankali ta ware eye’s ball’s din ta, ta ce, “Na’am.!
“tashi mu shiga gida asuba tayi” jiki ba qwari ta tashi har tayi gaba ta tsaya chak idanuta taf da kwalla da sauri ta waigo kusan lokaci daya suka waigo da sadiq suna kallon juna cikin murya mai matukar taushi fatu ta ce, “Yau ne zan rasa farin ciki na.! yaune mafarki na zai rushe, ina ma ace dogon bacci nake na farka ahalin yanzu” wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo mata ta ce, “Yanzu duk wata rayuwa da mukayi zata zama tarihi mai kyau? Numfasawa tayi saboda muryarta dake sarkewa ta furta, “ina ma fatan alheri Allah ya baku zaman lafiya da Basma.! tana ida zancan ta fashe da kuka mai ban tausayi ta juwa sadiq baya rungume ta sadiq yayi ta baya tamkar karamin yaro  hawaye na masa anbaliya cikin sarkewar harshe sadiq ya ce “Fatuha ki kasance mai biyaya a daki’n mijin ki kin ji, majeed na sonki please karki bari majeed yayi kuka dake dai-dai da rana daya, duk wanda yayi hakuri a rayuwa zai ga ribar haka..! ya ida zancan yana share hawayansa ya waigo da fatu suna facing juna yana  sakar ma fatuha lallausan murmushi dayafi kuka ciwo, suna kallon juna da sauri fatu ta shige cikin gida.

Duk inda ka wuce hada-hada ake da shagali abinci ke ta yawo da kayan motsa  baki, kaji ko har ture su ake da naman rago yan’matan amarya na zaune a daki, shirya fatuha ake saboda wudil za’a wuce da ita sai an daura aure aje dauko ta, tunda ake mata make up take kallon agogo tana irga mintinan da suka rage ta zama malakin majeed, hawaye ne taf a idanuwanta bayan angama make up din ta zura kayan ta atamfa mai ratsin green, pink, brown masha Allah kayan sun mata kyau tasha danqareriyar sarqa ta gold da yan hannu sai sheqi take,  Aunty bilki ce ta leqo ta ce, “Fatuha ku fito ga motocin da zasu kai mu wudil?” gaban tane ya yanke ya fadi dan har wani jiri take gani a haka su fatsima suka sata tsakiya aka lullu6eta aka kaita wajan su Mom sukayi sallama, anata guda har suka fito harabar gida, mota suka shige driver ya ja suka har ba kan titi.

                 Wanka angwayan kawai suke suna shiryawa Khaleed ne ya kalli sadiq ya aika masa harara tare da cewa, “Wai ina kaje jiya? bala masa harara sadiq yayi ya ce, “Ina ruwan ka da inda naje?  ka fiye sa ido, irin kune ana ruwa kuna irgawa” dariya majeed yayi ya ce, “Kai dai tashi kayi wanka kaji baby ko ni ban tanbaye ka ba sai shi, ga kayan ka can tun dazu na aje ma ina so yau ka kasance cikin farin ciki kamar  kowani ango.! majeed ya ida zancan yana zura kayansa a hankali sadiq ya miqe ya shiga toilet majeed  ya bishi da kallo tare da ida shiryawa, tunda sadiq ya shiga toilet yake kuka kamar qaramin yaro sai da yayi son ransa sannan yayi wanka ya fito.
ko daya fito Dr yakub ne kadai daki’n kallosa sadiq yayi tare da kauda kai ya cigaba goge jikinsa  da qaramin towel, sai da ya gama shafe jikinsa da lotion mai kamshi da sanyi dadi sannan Dr yakub ya balo magani ya miqawa sadiq dan bata fuska sadiq yayi yace “Wannan fa? daure fuska Dr yakub yayi ya ce, “Magani mana” bai ida rufe bakinsa ba aka turo kofa aka shigo, murmushi sadiq ya saki ganin ya jawad  qarasawa yayi ya rungume jawad zame jikisa yayi tare da bata fuska ya ce, “Sai yauma zaka zo? smile jawad yayi yana bin sadiq da kallo yarda ya zabge ya rame ya ce “Sorry baby tun jiya na zo kuma na zo nemanka aka ce baka nan, ya naga ka wani rame ka zabge kamar ana dibar ka ana miya ko duk hidimarce”dan lagwabe kai yayi yana murmushi ya furta, “Toh shikenan, bayan makara harda sheri, ina su Aunty shukura?
“tana wajan su Mom”
“ok.! Dakakiyar fara shada ya jawo white getzner  tasha aiki ta gaji malin-malin  su jawad ne suka taimaka masa ya shirya tuni ya fito yayi kyau masha Allah duk da ya rame idanusa sunyi ciki, bayan sun gama shiryawa suka fita

             Zaunawa sadiq yayi tare da kallon agogo dake manne a bangon daki,  karfe 1:30pm saura minti talatin a daura auran su, haka ya dinga dane zuciyarsa yana bata hakuri.

                       Suna isa wudil  gida ya dau gud’a baba jummai ta fito da sauri tana cewa “Ladingo amaryar fa ta iso” inna washe da baki ta bude masauki da su fatuha zasu sauka kusan tare suka shigo, Aunty bilki na riqe da ita masauki suka sauka nan aka fara jera masu kayan motsa baki, kama daga waina alkubus sinasir tuwan shinkafa da lafiyayin kaji da lemuka,  yan’matan amaryar ko alwala suka fara daurawa suna sallah kasancewa azahar tayi haka itama fatuha ta gabatar da sallah sannan suka zauna aka fara gudanar da biki.
gwaggo ce ta aiko a kira fatsima tashi tayi ta fita har Nana zata bita sai kuma ta dawo ta zauna, ko da fatsima ta isa gidan su shima cike yake da baqi, mamaki ne ya lullu6e fatsima babban abinda yafi daura mata kai har da dangin babanta, to ko suma bikin fatuha suka zo? watsar da zancan tayi tare da shigewa daki inda gwaggo take washe da baki gwaggo ta tarbi fatsima ta fara mata magana. (duk yarda naso naji me ake cewa na kasa ji, hakan yasa ni da Aunty Rahenat muka bar gun jiki a sabule lol.)

                 Duk inda ka waiga a cikin masallaci Sheikh Isyaka Rabi’u mosque ya cika da manyan mutune yan daurin auren, sadiq ne cikin din bin jama’a, a nata masa Allah ya sanya alheri duk wannan abu Dr yakub na lura da yanayin shi majeed ma sai murmushi yake saki daka ganshi kasan yana cikin farin ciki, haka shima Khaleed dan yasha kyau har ya gaji tamkar ango, gyara lasfika da kayine yasa gaban sadiq ya yanke ya fadi, kirjinsa ya bada dam zuciyarsa ta tsinke bugun zuciyarsa ya qaru rawa jikinsa ya dauka gudun jinin jikinsa ya qaru take wata irin zufa ta fara karyo masa bugun zuciyarsa na harbawa fat-fat dam-dam tamkar ana lugude cikin zuciyarsa, tabbas yasan ana daurawa ya zama gawa dishi-dishi ya fara gani yana ganin jiri maganar mutane na lunkuwa cikin dodan kunnasa da kwakwalwarsa, a hankali ya fara kutsawa cikin taron jama’a yana tafiya, yana  tari mai dauke da gudan ji tamkar kaki zufa ta jika shi sharkaf  a hankali yake takawa dan yanzu ya fara yin nisa da masallacin.

        Cikin masallaci ko MALAM JAURO   YA BADA  DIYARSA KAN  SADAKI NAIRA  DUBU DARI GA DAN  ALHAJI IBRAHIM WATO  SADIQ IBRAHIM,  MALAM ALIYU YA MIQA DIYARSA KAN NAIRA DUBU DARI WATO  FATSIMA ALIYU GA DAN ALHAJI KHABIR WATO ABDULMAJEED KHABIR, TARE DIYARSA BASMA YA MIQA TA GA DAN ALHAJI SANI WATO KHALEED KAN SADAKI NAIRA DUBU DARI  kowa na masallaci kallon-kallo aka koma mamaki ne ya lullu6e kowa.
sadiq wanda fitowarsa kenan majeed ya biyosa ya kwalla masa kira da cewa “Baby..! waigowa  yayi idanusa jawur ya galabaita sosai ya fita hayacinsa yana sauke numfashi a hankali tafe da zuciyarsa hawayan wahala na bin kumatunsa ya jike sharkaf da zufa zaro ido majeed yayi da karfi ya murfa, “sadiq..! dim sadiq ya durkushe a kasa duniyar na juya masa yana sauke numfashin wahala dakyar-dakyar ya sulale baya numfashi,  da gudu majeed ya qaraso tare da sakin kuka yana cewa “No..! no..! Baby karka min haka ka tashi ka ji baby.! Majeed na maganar yana dan dukan fuskar sadiq da ko motsi bayayi cikin matsanan cin kuka ya ce, ” in dai fatu ce na bar maka sadiq bana son ta Allah, duk laifi nane na kashe baby da kai na tashi ka ji baby kasan bama haka sadiqqq..! majeed ya koma tamkar zarare yana magana hawaye na masa zarya Dr yakub da kusan tare suka iso wurin daskarewa yayi tsaye ganin halin da sadiq yake cikin jikinsa rawa ya dauka kaf-kaf dan baya tunanin akwai sauran wani abu rai jikin sadiq su Baba da Abba dake cikin masallaci da alhaji babba jin yarda majeed yake kururuwar kiran sadiq suka fito da gudu liman ya rufa masu baya da yan daurin aure.
Dakyar Dr yakub ya samu damar bud’e baki yana tsiyayar hawaye ya ce “Ba kuka zamuyi ba, muyi sauri mu kai shi asibiti” jikin majeed na rawa ya dauki sadiq chak ya bud’e murfin mota yana kuka ganin ba zai iya tuqin ba yasa doctor yakub ya amshi car key din suka bar harabar masallaci da gudu su Abba suka rufa masu baya.
kuka majeed yake yana cewa “Ban taba tunanin abin ya kai haka ba? am so sorry sadiq ka yafemin, duk nine sila” sanbatu yake sosai a haka suka iso asibitin sai da aka wuce dashi emergency sannan majeed ya zame jikin bango tare da sakin kuka, wayarsa ya curo cikin aljihu ya danna number Umma bugu daya zuwa biyu ta dauka kuka majeed ya saki yana cewa “Umma saboda ni ina ji ina gani baby zai rasa ransa? Ya fadi hakan tare da sakin kuka ita kanta Umma kuka take dan labarin tuni ya cin masu ta tausayawa sadiq.

                            Kafin ka ce me, asibitin ya cika da yan’uwa, majeed na ganin Abba ya mike da sasarfa ya qarasa garesa ya fada jikinsa yana kuka kamar qaramin yaro ya ce, “Shikenan Abba bakin ciki na zai kashe baby, bazan ta6a yafewa kai na ba har sai sadiq ya tashi lafiya Abba ka ce su ceto rayuwar baby duk nine sila komai, na tafka babban kuskure nayi anfani da son da baby ke min na cutar da shi..! a hankali Abba ke shafa bayan shi tare da zaunar da shi d’aya d’aga ciki’n kujerin dake gurin, ajiyar zuciya kawai majeed ke saki cikin sanyin murya Abba ya ce, “Ba laifin ka bane majeed ka ji.! har da laifin sadiq da yayi nauyin baki ya kasa fad’a, da kansa yayi wasa da damar daya samu, hasali yarinyar nan kullun suna tare gida daya kusan komai nasa ita ce amma yayi zurfin ciki da nauyin baki? ko yanzu da kukayi  magana  aka sauya daurin auran? indai fatuha tace bata son sa dole ya sake ta” kuka majeed ya saki tare da cewa, “Abba da kunne na naji irin son da suke ma juna su, kamar yarda basu rintsa ba jiya, nima ban rintsa ba ina jin irin kalaman da suke fadawa juna, kuma dama na dade ina zargin akwai so tsakanin su amma baby yaki furtawa, tun ranar da aka sa bikin mu, sannan Dr yakub ya karamin bayani daran jiya, Abba dan Allah a taimaki rayuwar baby? ya ida zancan yana qara sakin kuka,  haka abba ya dinga lallashinsa har yayi shuru, Ammi ko sai kuka take tana share majina saboda tausayin sadiq, sai yanzu suka san abinda ke damun sadiq.

                 Duk iya bakin qoqarin likitoncin asibintin sun kasa duk da suna manya-manyan likitoci wayanda ake ji da su, sosai hankalin su ya tashi suka fara fidda rai da sadiq, da sauri suka fito daga emergency suka ba Abba shawara ya fidda sadiq waje kawai duk da can ma basu da tabbacin warakasa domin ya riga da ya zo ga6a, biza Abba yasa aka masa dan a fitar da shi waje saboda a wannan karan ciwon yayi tsanani, dan yafi buqatar a masa aiki gaggawa tahanyar samun qwararin likitoci.

                Su Baffa na isa wudil jiki bakwari sanin halin da suka bar sadiq ya sanar da su, Inna an daura auran fatuha, wani irin kuka fatuha ta saki dan yanzu ta tabatar da ta zama malakin majeed kuka take kamar ranta zai fita, lallashin ta su Aunty bilki suka shigayi dakyar aka samu fatuha ta shirya.
ko da ta shirya dakin Baffa aka kaita ya mata nasiha sosai duk wannan nasihar da Baffa ke ma fatuha  kuka take har da shesheqa abun gwanin ban tausayi, a haka aka tataro ta aka sata mota taci kuka sosai sai anjiyar zuciya da take ta saki, dan ko fatsima bata  nema ba.

                            Bangaran fatsima ko su gwaggo sun gyara ta sosai duk da bata jin son  majeed amma a yarda ya mata bayani da yarda su gwaggo suka mata hakan yasa ta fara jin son sa, dan tayima kanta alqawarin bashi farin ciki, haka suka shige motoci amaran aka harba da su kan titi ,

                         Tunda fatuha ta ga an iso kano ta qara sakin kuka mai cin rai, sosai take kuka kamar ranta zai fita, a yanzu kam kukan fatu ya fara d’agawa su Aunty bilki hankali dan ba kukan lafiya fatu take ba, suna isowa family house aka bude mata murfin mota fatu na fitowa ta yanke jiki ta fadi  luuuu  jikin Aunty  bilki sumamiya…

Vote
Comment

  Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄
★We are the best ★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFUROM.COM

                   93_94

       Daukar fatuha akayi chak aka maida ta mota aka ja suka bar harabar gidan Hanan sai  matsar kwalla take basu zame ko ina ba sai asibitin da aka kai sadiq, suna shiga lokaci majeed na qoqarin fita kamewa yayi yana bin su da kallo kamar gunki ganin halin da fatu ke ciki duk saboda shi, bin bayan su yayi wasu hawaye masu zafi na masa zarya duk wannan abun da ya faru saboda shine, shiga da fatuha emergency akayi.

             Bayan yan mintoci aka fito da fatu har lokacin bata farfado ba tana kwance amma Dr yace da sauki tashin hankali da tunanin ne ya haifar mata da yankewar jiki ta fadi, dakin da aka kwantar da sadiq aka kwantar da fatu   kafin anjima jirgin su ya tashi har yanzu kwance yake bai san halin da ake ciki ba

               A hankali fatuha ta fara ware idanuta wayanda suka mata nauyi tana bin dakin da kallo, yunqurin tashi tayi ta kasa dakyar ta iya miqewa zaune dafe da kanta dake tsanata sara mata tamkar zai rabe biyu, ta juyo ganin sadiq kwance  kefan ta ya dagawa fatu hankali yunkurin sauka daga saman gadon ta je wajan sadiq  ta kalli drip din dake  hannuta, hannuta tasa ta cire drip din dake hannuta tana kuka da sauri ta matsa kusa da sadiq kuka tasa ganin halin da yake ciki kuka take sosai tamkar ranta zaifi saboda tsanin firgita da halin da sadiq yake ciki a hankali ta fara cewa, “mai kyau meya same ka haka, karka tafi ka barni ka ji idan babu kai babu ni ka ji sadiq d’ina, ina son ka handsome I love you more than how you think please don’t leave me alone, na rokeka  nima mutuwa zanyi.! Sosai fatu ta rikice dan bata cikin hayacinta duk  tabi ta rude sai fama kuka take har sautin kukan ta ya fara fita waje Mom da shigowar su asibitin kenan suka shigo dakin dan duba jikin fatu dana sadiq.
kuka fatuha take tana mai cigaba da cewa, “mai kyau ka tashi wallahi na rasa ka mutuwa zanyi, Allah bana iya zaman aure da majeed please ka tashi, ni kai nake so kai ne farin ciki na ka ji sadiq” ta ida zancan tana kuka mai cin rai Mom ce ta jawo ta, ta rungume tana shafa bayan ta fatu na cewa, “Mom sadiq nake so Allah bana son majeed ku ce masa ya tashi karya tafi ya barni” kuka fatu ta kuma saki ta qanqame Mom “shhhh ya isa kukan haka fatuha, ki kwantar da hankalin ki kin ji indai mai kyau ne ya zama naki..! dagowa tayi tana kallon Mom da mamaki idanuta sunyin jawur lokaci daya kukan da take ya dauke tana jin kalaman Mom kamar ba dai-dai ta ji murmushi Momta sakar mata ta ce, “yes abinda kika ji haka ne,  yanzu ba kuka ya kamata kiyi ba kulla da mijin ki ya kamata kiyi idan kun dawo  kunji bayani gabaki daya” wani irin farin ciki ne ya lullu6e fatu wanda bata iya boyewa lallausan murmushi fatuha ta saki tana goge hawayanta da bayan hannuta ta qarasa bakin gadon sadiq tana dariya mai had’e da kuka tana cewa, “mai kyau kana jin abin da suke cewa wai da gaske na zama matarka, kayi sauri ka warke ka ji handsome.! majeed dake gefe smile ya mata yana daga mata gira wata irin kunya ce ta lullu6e fatu, sai yanzu ta tuna da su Mom da sauri ta miqe tana qoqarin ta fita daga dakin da gudu saboda tsabar kunya, Basma ce ta tare ta, “ina zaki je kibar mijin naki, ko kin mata kema baki da lafiya kina buqatar kulawa” waki-waki fatu tayi dan tama manta bata jin dadi, harara wasa ta aikawa Basma dan ta bata hanya ta wuce, gabaki daya dakin aka fashe da dariya, sunkunyar da kai fatu tayi.

            Khaleed dake gefe ne yaja Basma suka wuce gida dan ta samu hutu kafin anjima akaita dakinsa kusan a tare suka fito da majeed yana qoqarin bude mota, motar su ya jawad ta tsaya shida shukara suka fito tare da fatsima sai matsar kwalla take qarasawa majeed yayi tare da cewa, “haka ake sai ku fito min da mata ba tanbayar izini”  harara jawad ya aika masa  ya ce, “ka raina mutane ai matar taka zaka tanbaya mai yasa ta biyo masoya” ya kai masa duka ya goce yana dariya jawo fatsima yayi jikinsa ya rungume tsam cikin cool voice ya ce, “my wife me ya saki kuka haka kina so ki bata min kwalliyar ki” fatsima da tayi wiki-wiki tana raraba ido neman kwace kanta take dan rashin kunyar yan birni tafi karfinta kamar bai san mai ya kawo su asibitin ba, amma sai wani iskanci yake dan murmushi majeed yayi ya ja karan hancin fatsima washe baki fatsima tayi tare da rufe face nata (lol su fatsima anqaro wulaqanci😜)

          Bayan an gama shirya komai flight din su sadiq ya tashi sai London suna isa london babba asibiti suka sauka kusan amaran tare suka tafi, saboda suma honeymoon za suyi a chan Khaleed sai zuba ma Basma soyayya yake sai yanzu Basma ta gane me so yanzu ta san ta fara so ashe da ba so take ba, haka shima majeed sosai ya samu piece of mind har cikin ran sa yake jin son  fatsima  yana ta gwada mata so ita ko sai kunya yake bata,
ko da aka wuce da sadiq asibiti emergency suka wuce da shi saboda yana buqar aikin nan kusa fatuha ta kasa zaune ta kasa tsaye sai zarya take tana duk  addu’ar data zo bakin ta, fatima ce ta dafata ta ce, “fatuha ya kamata ko wani abu ne ki sama cikin ki, raban ki da abinci tun jiya insha Allah lafiya lau sadiq zai fito, da yardar Allah za’ayi aikin cikin sa’a kin ji” haka Basma da fatsima suka dinga bata baki sannan ta ci abinci, shima d’in d’an kadan ta ci bayan ta kamala cin abincin duk da ba wani ci tayi ba su fatsima suka mata sallama akan zasu wuce masaukin su, su huta anjima su dawo haka ko akayi fatuha ta dawo ta zauna haka shima majeed yana asibitin dan ba da shi suka koma masauki ba, sai kun san yamma likis aka fito da sadiq Alhamdulillah anyi aikin cikin sa’a tashi fatuha tayi tabi gadon da sadiq ke kai har aka bashi daki sannan doctor ya nemi ganin majeed, magunguna ya bashi tare da masa congrat ya ce, “an gama aiki lafiya kowani lokaci yana iya tashi sai dai yana buqatar kyakyawar kulawa jan ku,” bakin majeed har kunne hamdallah yayi da godewa Allah ko da ya dawo albishirin da yayi ma fatuha kenan, curo wayarsa yayi bugawa su Mom yayi masu albishir sannan suka shaidamasa suma gobe zasu iso fita yayi ya bar dakin tare da shaida ma fatuha tare zasu dawo da su Basma to ta ce masa ta shige toilet dan ta dauro alwala.

          Bayan ta gabatar da sallah tana qoqarin linke daduma sadiq ya fara motsawa kusa da shi ta matsa ta tsaya, tana qare masa kallon ba qaramin jiki sadiq yasha ba sosai tausayin mijin nata ya lullu6eta musanman idan ta tuna duk saboda ita ya shiga wannan halin, a hankali ya fara bude  idanusa ya sauke su kan fatuha kallon ta yake kamar wanda  bai taba ganin ta ba yana bin dakin da kallo, cikin sanyin murya ya ce, “zan sha ruwa! ruwa ta tsiyayo masa a glass cup ta taimaka masa ya d’an dago har lokacin bai dauke ido a kanta ba har ya kafa kai ya shanye ruwa  ya mika mata cup din ta aje sannan ta qara dawowa bakin gado tana murmushi lumshe ido sadiq yayi ya ware su cikin sanyin murya ya ce, “fatuha..!
“na’am.! ta ce tana qoqarin ta6a sumar kansa, riqe hannu ta yayi ya furta, “ina mijin ki me ya kawo kinan, ke fa yanzu matar aure ce..! bai ida rufe bakinsa majeed  da shigowarsa yanzu ya ce, “akwai wani mijin ne bayan ka..! ya ida zancan yana qarasowa gaban gadon, kallo sadiq ya bi majeed dashi mai cike da mamaki daga mai gira majeed yayi ya ce, “karfa kayi mamaki da kai aka daura aure badani ba, saboda kai ka cancanci zama da fatu bani ba, ni ga matata..! fatsima ce ta shigo tana smile Basma ta biyo bayan ta kanta na saman qafadar Khaleed mamaki ne ya lullu6e sadiq hawayan farin ciki na bin gefan fuskarsa Khaleed ya ce, “karfa kayi mamaki dama over taking kamin yanzu kuma na dau abita” ya ida zancan yana dariyar shaqiyanci yana mai cigaba da cewa, “ai sai ka miqe yanzu tunda an daura da fatuha” rufe fuska fatuha tayi tana qoqarin barin gun riqe hannuta sadiq yayi na tattausan murmushisa ya ce, “kun fiye sa ido” ya fada cikin cool voice saboda har yanzu bai jinsa yadda yake ba amma jin wannan labari ba qaramin dadi ya masa ba, zuciyarsa na kunshe da tanbaboyi fal ta yarda aka daura auransa da fatu sai kallon juna suke shi da fatuha, haka suka dinga raha suna bama Sadiq kulawa har ya fara jin ya warke, kiran sallah magrib ne yasa su ka fita tare da matan su dan su dauro alwala a masaukin su kasancewa masaukin ba nisa da asibiti, suna fita fatuha ta tashi tana qoqarin itama shiga toilet ta dauro alwala,  riqe hannuta sadiq yayi tare da jawo ta batayi masauki ba sai saman fadadan qirjinsa yana binta da kallonsa mai kashe mata jikin a hankali ya hada bakin su guri guda ya fara kissing nata sun dau mintina suna a haka, sannan ya sake ta ya hada face nasu guri daya yana wasa da yan yatsun hannuta suna sauke numfashi  a hankali, cikin taushin murya ya bude baki ya ce, “my wife..! smile fatuha tayi tare da lumshe ido cikin cool voice sadiq ya ce, “fatuha kina so na? Jinjina kai fatu tayi cike da kunya tana murmushi “bani da abinda zance sai dai na godema Allah daya bani ke, ban taba tunanin zan shiga wuni hali saboda  rashin ki ba, ina son ki fatu son dani kai na ban san wani irin so bane” hannu fatuha sadiq ya jawo tare da daurashi saitin zuciyarsa ya ce, “fatuha ke ce rayuwa ta idan babuke babu ni bana jin zan iya rayuwa babu ke,  I love you from the bottom of my heart.! ya ida zancan yana langwabe kai ya ce, “please ki ce kina so na please” ya ida zancan kamar qaramin yaro rungumesa fatuha tayi tana hawayan farin cikin zame jikin ta tayi tana qoqarin tashi riqe ta sadiq yayi ya ce, “baki ce komai ba” rufe fuska tayi tare da saurin shigewa toilet jingina tayi jikin kofar tana sauke ajiyar zuciya tana smile cike da farin ciki ta gabatar da alwala ta fito har ta fito sadiq na binta da kallo, ta gabatar da sallah tana idar wa majeed ya shigo da take away ya aje tare da shafa kan sadiq peck ya masa ya sakin lallausan murmushi ya ce, “please forgive me bros” lumshe ido sadiq yayi ya ce, “mention not ni ya kamata na gode maka” laqace masa hanci sadiq yayi dariya sukayi lokaci daya sannan majeed ya ce, “ai saika miqe ka warke tunda ga muradin ranka kusa da kai” ya ida zancan yana kashe ma sadiq ido duka sadiq ya kai masa na wasa ya goce tare da qarasowa saitin kunnansa ya mashi wata magana, dariya suka saki a tare majeed ya fita da sauri yana cewa, “mu dai asuba ta gari” dariya sadiq yake har da yar kwalla peck fatuha ta masa a forehead ta ce, “mai kyau mai ya fada ma haka har ya saka wannan dariyar” smile yayi  ya ce, “zaki sani amma not now amma very soon zaki ji” ya fada yana kashe mata ido murmushi tayi tare da jawo lafiyayan abinci ta fara feeding nashi yana amsa.

         Ko da majeed ya koma masaukin su fatsima na wanka cikin toilet daure da qaramin towel ta fito ganin shi zaune saman bed yasata yan noqe-noqe dakyar ta fara shirin duk kunya ta isheta shima rage kayan jikinsa yayi ya wuce toilet ya watsa ruwa tare da dauro alwala ya fito.

    Shiryawa tayi cikin pink night dress masu kyau masha Allah ta yi kyau sosai kuma kayan sun hauta, saman bed ta hau ta shige cikin blanket tayi lamo ko qala majeed bai ce mata ba shima ya shirya sai da ya gama shirin shi ya ce, “fatima.! a hankali ta dago ya ce, “mata tashi ki ci abinci” dan smile tayi ta ce, “Na koshi ai naci abinci a asibiti”
“ai wannan da ban ne dana asibiti, ki tashi mana” ya ida zancan yana langwabe kai ba musu fatima ta tashi zaune ta sauka daga saman gado ta zauna saman carpet kaza ce lafiyayan majeed ya bude tasha rumo ta gaji a hankali majeed, ya dinga feeding din fatima tana amsa sai da suka ci suka koshi sannan ya dauke komai ya bata umarni ta dauro alwala, brush tayi ta dauro alwala majeed  ya ja masu sallah raka’a biyu suka godewa Allah, bayan sun idar majeed ya kama kanta ya mata addu’a sannan ya dauke ta kamar baby sai kunya take ji ya daura ta saman bed kissing  nata ya fara cikin salo yana shinshinar kamshi turaran ta ganin zasu wuce gona da iri ya sani fita jiki a sabule har ina tuntu6e saboda harara da majeed ya wurgo min😒

       Ko da naje part din su Basma shima kulle yake jiki asabule na dawo parlour ina wurga ido😒

Written by
Salma mas’ud nadabo

     Edit by
Raheenat

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* Realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

95_96

this page is for you Aunty khadija Hamu nadabo tare da daukacin masoya wannan novel ina son ku irin sosai din nan❣❤🤸🏽‍♀

       Washe gari ko da fatuha ta gama wanka, taimakawa sadiq tayi ya tashi shima ya shiga toilet, sanye da towel ya fito yana goge jikinsa da qaramin towel, lallausan murmushi ya sakarwa fatuha dake zaune saman kujera a hankali ya qaraso kusa da ita ya sakar  mata peck lumshe ido tayi ta ware su  ta ce, “Uncle ina kwana? lakace mata hanci yayi ya ce, “Ina kwana sweetheart? rungume ta yayi a jikinsa tsam  suna jin bugun zuciyar junan su, lamo fatuha tayi a fafadan qirjinsa  ta ce, “Uncle.! dan 6ata fuska sadiq yayi ya ce, “Sweetheart bana san wannan sunan, ki ce wani suna mana kamar my love” kallonsa fatuha take cike da so ta ce, “to wani suna kake so nace?
“ki zabi wani suna mai dadi a part form uncle” smile tayi ta furta, “to habibi na.! smile sadiq ya saki da cewa, “please qara fada naji” maimaitawa tayi tana qoqarin zame jikin ta riqeta sadiq yayi ya ce, “Ina zaki baki shirya ni ba? zaro ido fatuha tayi waje ta rufe fuskarta, jawo ta ya kumayi jikinsa ya ce, “My love yau fa ke zaki min komai ko mai bana iya shafawa.! rufe ido fatuha tayi ta ce, “Uhm ni dai…! bata ida zancan ba ya hade bakin su waje daya yana mata french kiss me cike da salo tuni jikin fatuha ya fara mutuwa dan sakin ta yayi yana kallon ta, lumshe ido fatuha tayi a hankali ya hura mata iskar bakinsa mai sanyi ware ido tayi tana kallon sadiq ta jawo lotion ta fara bin ko ina na jikinsa tana shafa masa idanuta rufe riqe hannu ta sadiq yayi ya ce, “My love ni gaskiya na warke yau zamu koma gida? yar dariya fatuha tayi ta ta6a goshin sadiq ta ce, “har yanzu da sauran zazza6i, dariya sadiq ya saki yana cewa, ” in ba wani zazza6i jikina” yana mata cakulkuli tana gantsarewa tana dariya.

                Ko da na leqa masaukin su fatsima😂 zaune take saman bed tana tana sheqa kuka, majeed da yanzu ya fito daga wanka yana goge jikinsa da qaramin towel lagwabe kai majeed yayi ya qaraso bakin gado kusa da fatsima cikin cool voice ya ce “Please baby kiyi hakuri kukan ya isa haka mana my love, tun jiya kike abu daya har kin sama kanki ciwon kai” ya ida zancan yana jawo ta jikinsa zamewa tayi ta ce, “Ban qara yadda da kai wallahi? ta ida zancan tana qara rushewa da kuka, “ni ka matsa ka ban guri” smile majeed yayi da dagowa da face nata ya ce, “please my love kiyi hakuri bazan sake ba, kuma fa kowa da kika gani da haka ta fara, kuma har da ke kin fiye dadi da yawa shiyasa nayi baji ba gani, but am so sorry” ya ida zancan yana langwabe kai murgada masa baki  fatsima tayi tana qoqarin kwantawa ya ce, “Please ki tashi ki sha magani? bata musamasa ba ta miqe ta amshi magani tana gama sha ta koma ta kwanta shima yana gama shirinsa ya kwanta tare da jawota jikinsa.

           Kuka take har da shesheqa, Khaleed ne ya ce “Please sweetyna kiyi hakuri mana tun jiya fa kike kuka nan gashi har da safe please ki daura ki ci wani abu please, ko ruwan tea ne” kuka Basma ta kuma saki ta ce, “Ni ka kyaleni? ni da ka so ka kashe ni jiya.! ta ida zancan tana kuka lallashin ta Khaleed ya shiga yi dakyar ya samu ta sha ruwan tea sannan ya balo mata gani ta sha lol amare ansha jiki😂🤣 fatuha nan  tafe itama😂😜.

         Kiran sallah azahar ne ya tashe su daga bacci, majeed ya taimaka ma Fatima ta dauro alwala, shima yayi ya jasu sallah suna idarwa ya mata peck yana cewa “Sweety na bari naje asibiti na duba lafiyar sadiq? to tace masa tare da tashi itama zata bishi langwabe kai majeed yayi ya ce, “My love ki zauna gida ki samu hutu”  to ta ce tare da komawa ta kwanta.

          Yana fitowa ya hade da Khaleed shima zai fita, tare suka fice zuwa asibiti da sallama suka shigo lokacin fatuha na feeding sadiq lunch, murmushi ta saki ta gaishe su da tanbayar ina su fatsima suka amsa a takaice, kallon juna su kayi a tare su uku suka kashe ma juna ido, gyaran murya majeed yayi ya ce, “Suna gida suna sauke gajiyar tafiya” lol 😂” wata dariya sadiq ya guntse, sa kai tayi ta fita.

               Da misalin karfe 4:00pm jirgin su Mom ya sauka London basu zame ko ina ba sai asibiti, lokacin suma su fatima sun zo murna ba’a magana haka Mom ta dinga nan da su ita da Umma haka su Abba ba wani banbanci a tsaka nin su, sai tsantsan soyayya inda sadiq ya dage shi ya gaji da zaman asibiti, hakuri aka bashi da cewa sai ya warke sosai.

           Kwanan su Mom biyu aka sallami sadiq daga asibitin dan sosai jikinsa yayi kyau ya warware, tare suka dawo Nigeria da yamma likis driver’s d’in sadiq suka zo daukar airport da yaransa su ola suka dauke su sai gida, suna isa gida majeed ya dau fatima sai gida haka shima Khaleed.

                Angel tana ganin sun dawo  da albishir da gudu ta ruga ta rungume su dan sun gama mata komai a rayuwa na ganin cewa aunty fatu da daddy sun zama mata da miji, murna ba’a magana haka ta dinga rungume su tana masu peck kumatu da goshi ta basu chocolate saboda abin ya mata yarda take so, sadiq daga angel yayi yana jujuya ta duk da ta girma sam bai ji nauyinta ba,  Mom kuma ta haura upstairs ita da Abba ya rage daga fatuha sai sadiq itama dak’i ta wuce, sadiq kuma ya wuce masallaci sallah ta gabatar kana ta watsa ruwa, night dress dinta ta zura tana shafe jikinta da lotion a hankali taji an bude kofar dakin, waigowa tayi sukayi ido hudu da sadiq murmushi ta sakar masa tana cigaba da feshe jikinta da turare, a  hankali ya qaraso ya rungume ta ta baya yana shinshinar dokin wuyanta mai matukar kamshin turare mai sanyi dadi ni’imatacan kamshi, kamshin jikinta ba qaramin  fizgarsa yake ba, take nan jikinsa ya fara mutuwa haka itama fatu ta lumshe ido tana jin yarda karan hancin sadiq ke yawo a wuyanta can kasan makoshi  dai-dai saitin kunnan fatu sadiq ya furta  “My love..! yar fatu ta ji tun daga kanta har yan yatsunta saboda yanayin yarda sadiq ya furta kalmar har tana neman zubewa kasa sadiq ya qara qanqameta tsam tamkar zai maida ta ciki ya cigaba da cewa, “yau fa ba a nan gidan zamu kwana  ba? a gidan mu zamu kwana” 6ata fuska fatuha tayi tana qoqarin zame jikinta sadiq  ya rungumta sosai yana  kissing ko ina na jikinta tun daga wuyanta har kafadarta da hannuwanta tuni tayi laqwas. cikin wata kasalaliyar muyar sadiq ya ce “Kin taba ganin amarya tayi amarci a gidan su? so kike Mom ta kore mu ko? ya ida zancan yana daukar ta kamar baby lafewa tayi  a faffadan qirjinsa gashin kanta ya baje masa a faffadan  kirjinsa bai zame da ita ko ina ba sai gaban motarsa….

Lol har kun baza kunne …..Hhhhhh muje zuwa😂😜
Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                           97_98

          Suna isowa katafarin gidan su wanda yayi matukar tsaruwa sadiq yayi horn mai gadi ya wangale masu geta, ya shigo da motar sa ciki bayan sun gaisa da mai gadi, parking Sadiq yayi a parking space tare da zagayowa ya dauki fatuha kamar baby sai shagwaba take zuba masa.

        Bai dire ta ko ina sai bedroom dinsa, ya sakar mata peck a goshi sannan ya shige toilet, dakin fatuha tabi da kallo tana mamakin irin qayatuwar dakin da tsaruwar gidan, pictures din su na su uku ta hango manne a bangon dakin, sai wanda take ita  kadai da wanda su kayi tare da sadiq  suna dariya abin ba qaramin qayatarwa yayi ba.

           Sanye da bathrobe ya fito yana goge jikinsa da qaramin towel, gaban dressing mirror ya tsaya yana shafa ma jikinsa lotion mai kamshi kana ya feshe jikinsa da body spray mai kamshi da sanyin dadi, fatuha dake zaune saman bed sai qarewa halittarsa kallo take da qara ganin tsatsan kyan sadiq, lallai sadiq ya dace da akira shi da handsome, domin shi din mai kyau ne Allah yayi ma sadiq halita da zaka kalla ka kuma kalla domin bashi da makusa ko ta ina, a hankali ya qarasa wardrobe ya ciro night dress sababi white ya saka sannan ya juyo yana kallon  fatuha killing smile din shi ya mata tare da d’aga gira ya ce, “Wannan kallon fa my love? murmushi fatuha tayi tare da rufe face nata, dan ba qaramin kunya ta ji ba da sadiq ya gane tun dazu shi take bi da ido, murmushi yayi tare da fita, kitchen ya shiga ya dauko ledar kaza da juice masu sanyi sannan ya dawo bedroom.

        A hankali ya qaraso kusa da fatuha cikin cool voice ya ce, “My love tashi ki sama cikin ki wani abu kin ji, nasan ba kiyi wani dinner ba” tashi tayi suka dawo saman carpet sadiq ya bude kazar lafiyaya sai kamshi take zubawa da duminta ( d’aga gani zatayi dadi nima har sai da miyau na ya tsinke😋lol) a hankali ya shiga feeding fatu tana ci shima yana ci, sai daya tabbatar ta koshi sannan ya bata juice mai sanyi tasha.

          Bayan sun kamala ci sadiq ya dauketa  chak sai toilet, brush yake mata tana zuba masa shagwaba ala dole itama sai ta masa, haka shima ya bata brush da makilin ta mashi suka dauro alwala.
gabatar da sallah raka’a biyu sukayi suna mai godewa Allah da ya cika masu burin su, waigowa sadiq yayi ya dafa kan  fatuha ya mata addu’a sannan ya dauke ta kamar baby ya dire ta saman bed, jawo ta yayi jikinsa a hankali yake yawo da hannusa jikinta har ya qaraso bakin cibiyarta a hankali fatu ke sauke numfashi cakulkuli ya fara mata dariya take kyakyatawa sosai sai da yaga harwani shidewa takeyi saboda dariya shi yasa ya kyale ta, yana kallon face nata mirginawa yayi tare da lumshe ido yana jin wani irin farin cikin kasancewarsa da fatu inuwa daya matsayin mata da miji ware idanusa yayi yana kallon silin, a hankali fatuha ta mirgino ta rungume sadiq, ta lafe saman fafadan qirjinsa ta qanqamesa tana maida numfashi, hannu sadiq yasa ya kashe  fitilar d’akin, a hankali ya fara shafa ta yana yi mata tafiyar tsutsa wani irin d’adi fatuha take ji take nan jikin ta ya fara mutuwa saboda rikitattun sakonnin da sadiq yake aika mata,  kissing nata ya fara ko ta ko ina  a hankali ya lalubu lips nata ya tura harshan sa cikin bakinta cikin salo mai rikita lusafi ya fara mata french kiss  mai rikitarwa, yana sarafa ta cike da kwarewa sosai suka fita daga hayacin su. (ganin zasu lola  ya sani qoqarin fita ashe Aunty Raheenat na ra6e wai sai taga yadda za’a kashe arna😉 tasa keyar ta nayi  muka fice baki’n kofa muka tsaya , jin wata rikitata qara yasa ni tsale na koma parlour  Aunty Raheenat tace “Gobe akwai gashi😆”.

    Asuba ta gari

  Kuka fatuha take ta sheqawa, a hankali Sadiq ya miqa hannu ya dauke ta kuka ta kuma samasa tana mutsu-mutsu tana cewa “Ni ka kyale ni? cikin dashashiyar muryata zama sadiq yayi  ya sa hannu ya shafa kanta ya ce “Am sorry love..! kuka ta  saki saboda tuna  azabar da tasha, daukar ta kawai Sadiq yayi sai tsala-tsale take ya sake ta bai dire ta ko ina ba sai cikin ruwan dumi, miqewa tayi tana qoqarin fita ya mai data kuka ta saka masa ta ce, “Dama har yanzu mai kyau ba ka daina cin zali ba? Kuma wallahi yau gida zan kwana.! sadiq bai ce mata komai ba sai ma tausayi  da take bashi, dan ba qaramar dirza yayi  mata ba ko a hakan ba koshi yayi ba kawai ya tausaya mata ne, da kanshi ya mata wanka sannan ya fito ya barta tayi wankan tsarki, ko da ya fito bedsheet  ya cire ya canza wani tare da qara gyara dakin ko da fatuha ta gama wanka kuka ta qara saki saboda ta kasa fitowa, jin kukan yayi yawa yasa sadiq komawa toilet din zaune ya same ta, harara ta aika masa ta ce, “shikenan ka mai dani musaka” ta ida zancan tana rushewa da kuka, abin dariya yaso ya bama sadiq daukar ta yayi  sai saman bed, ya taimaka mata ta shirya ya zura mata hijab, shima a gurguje ya shige toilet yayi wanka yana fitowa jalabiya ya zura ya ja su sallah bayan sun idar  ya maida ta bed, a hankali ya jawo ta jikinsa ya rungume tsam tamkar ya maidata cikin dan so ya ce, “Fatuha Allah ya sa maki albarka bani da bakin da zan iya gode maki my wife, kin sani farin ciki mara musaltuwa kin kore min duk wata damuwa my love, naji dadi da kika kilace min kan ki har wannan lokaci, nayi maki alqawarin zan baki farin cikin har qarshan rayuwata fatuha” wani irin dadine ya lullu6e fatuha son mijinta na qara narke mata a zuciya, lamo tayi a jikinsa tana sauke numfashi a hankali  d’ago da face nata yayi ya sakar mata peck ya furta, “am sorry my wife, nasan na wahalar dake amma ai.! bai ida zancan ba fatuha ta hada bakin su guri guda tana masa french kiss, take ta qara rikitashi da salon ta ganin zai zarce tasa masa kuka, dariya yayi tare da ja mata hanci ya ce, “Matsoraciya kawai”
“naji din ba komai kuma gida zaka mai dani wallahi”
“lallai kam kwarankwatsi ba inda zaki” ya fada yana kallon fatuha, dariya suka saki a tare ya ce, “My love akwai drama” ya  ida zancan yana lakace mata hanci qara matse ta yayi suka shige blanket suka koma bacci.

          Basu tashi ba sai kusan shadaya,  a hankali sadiq ya zame jikinsa ya  shige toilet, ya qara hadawa fatuha ruwan dumi daukar ta ya dawo yayi ya kaita toilet yana dire ta ta bude ido tare da lumshe su, wata irin kunyar shi take ji a wannan lokacin, ruwan dadi ya mata taji dama-dama, sannan ya maidota bedroom shima ya koma yayi wanka ko da ya fito ta shirya cikin riga da sket na atamfa dinkin ya mata kyau sosai ga make up tasha lallausan smile Sadiq ya saki tare da qarasowa ya rungumeta ta baya ciki cool voice ya ce, “My love kinyi kyau” murmushi tayi ta ce, “Thanks love” lotion ta jawo tana shafa masa ita da kanta ta zaba masa kaya wani hadadan yadi mai tsada ta curo masa milk da ratsin brown mara kauri ya sha diki da dark brown zare taimaka masa tayi yasa, tuni suka fito sukayi kyau masha Allah, knocking din kofar da ake ne ya sa sadiq qoqarin fita kusan a tare suka fito da fatuha parlour ta bi da kallo wani irin kyau ya mata gidan kamar ba’a qasar Nigeria take ba dan yayi matukar tsaruwa.

     A hankali ya bude kofar baba jummai ce riqe da kuloli, murmushi sadiq ya saki tare da gaishe ta angel ce ta fada jikinsa ta rungumesa ta ce, “Daddy.! dariya sadiq ya saki ya ca6e ta, qarasa shigowa baba jummai tayi ta aje kulolin, fatuha qarasowa tayi ta gaida baba jummai ta amsa angel sakowa tayi daga jikin daddy ta rungume fatuha smile fatuha tayi ta ce, “I miss you angel” tare da yi mata peck a kumatu.

        Parlour angel ta dawo ta ce, “Daddy  kunna min kallo”   kunna mata yayi  shima ya zauna kusa da ita baba jummai ko jan fatuha daki tayi ta bata sakon Mom na kayan tsimi da turaru  ka  masu kamshi da tsada, Godiya fatuha ta dinga jera mata suka fito a tare, murmushi baba jummai tayi ta ce, “Jidda taso mu tafi ko? 6ata fuska fatuha da angel su kayi lokaci daya fatu ta ce, “A barta anan munyi missing nata ni da baban ta ko? ta fada tana kallon sadiq, murmushi yayi tare da daga mata gira yana jin dadi yadda fatuha ke gwada ma angel so da kauna, baba jumma sakin baki tayi ta ce, “ni da zuwa da yar rakiya ku da amshe min ita, to ai shikenan ni na wuce Allah ya bada zaman lafiya” har bakin kofa fatuha ta rako ta sannan ta dawo parlour hannu jidda ta janyo ta ce, “Zo muje kiyi break nasan ba kiyi ba” tashi su kayi a tare taja ma sadiq kujera ya zauna, sannan angel ta zauna, saving din su fatuha tayi a hankali sadiq ya fara feeding  fatuha itama tana feeding nashi da angel sai murna suke suna jin dadi cike da so da kauna ida sadiq ya zage yana gwada masu so

    Agurguje

              Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi,  fatuha ce tsaye gaban dressing mirror sanye da uniform kasancewar yanzu ta koma  school, yanzu haka tana SS3 kuma ita ce Head girl tana shirya sadiq cikin uniform nashi smile  yayi tare da yi mata peck ya ce, “I love you”
“love you more habibina” briefcase din sadiq ta dauka da school bag din ta suna  fitowa angel suka samu zaune saman dining area ta fara break gaishe su tayi tare da yi masu peck suma kujera suka ja suka fara break, bayan sun kamala fatuha ta kira yar tsohuwar mai aikinta ta ce ta kulla da gidan sannan karta dafa abinci sai ta dawo zata daura da kanta to tace mata tare da yi masu Allah ya kiyaye hanya, ta koma bakin aikinta, mota suka shige sadiq ya ja su bai sauke su ko ina ba sai harabar makaranta yana parking angel ta bude kofa ta fita fatuha na qoqarin fita ya riqe ta, murmushi ta saki a hankali ya jawo ta jikinsa yayi kissing na ta lumshe ido tayi ta ware su a kan sadiq ta ce, “Habibina zanyi missing naka?”
“nima haka my love,” Sannan fatuha ta bale murfin motar ta fita,

    Tana Shiga class su Zara suka dau shewa suna cewa, “kai Head girl kina wuta wallahi,” harara ta aika masu tana cewa, “wallahi na kusa maganin ku” yar shewa sukayi  tare da cewa, “lallai ma”  wata dariyar shaqiyanci Zara tayi ta ce “kwanan naga wani sheqi kike me sirin? littafin hannu ta fatuha ta gefa ma Zara dariya suka sa a tare suka ce, “zakiyi bayani wallahi” ganin uncle ya shigo yasa su nutsuwa aka cigaba da gabatar da darasi,  kasancewa yau juma’a karfe 12:30pm suka tashi drive ne ya zo daukar su  direct gida ya dire su.

         Wanka suka yi sannan fatuha ta shirya cikin 3 quarter pink da t-shirt  milk  ba qaramin kyau fatuha tayi ba, sai gashin kanta da ta sharce ya kwanto har gadon bayan ta fitowa tayi daga bedroom ta shiga kitchen, tuwon shinkafa ta daura miyar Egushi taji naman rago kamshi sai tashi yake sannan ta ahada juice din mangworo dan ba qaramin dadi yake mata ba, kwana biyu nan bayan ta kamala ta dawo dining ta jera sannan ta koma bed ta qara sheqa wanka ta fita ta shirya cikin gown din ta maroon mai stone’s dikin ya hauta sosai parking din gashi kanta tayi jin a shigone ya sata waigowa angel ce tsaye bakin kofa, murmushi tayi ta ce, “Mom kinyi kyau” murmushi fatuha tayi ta ce, “thank you my angel” langwabe kai angel tayi ta ce,  “Mom ina so naje gidan Mami yau ne birthday Jamal” smile fatuha tayi ta ce, “To shikenan amma sai kin fara lunch” dan shagwabe fuska tayi ta ce, “Please Mom kin san fa nice best friend tare zamuyi komai”
“ok naji ina zuwa” wata hadadiyar gown ta curo daga wardrobe tare da gift ta ce, “gashi wannan gown din taki ce ita zaki sa ki tafi” wani irin tsale angel tayi ta rungume fatuha tana mata peck ta ce, “thanks Mom.! Sannan ta zame jikin ta dariya fatuha tayi tare da lakace mata hanci ta ce, “Wannan  gift din kuma na Jamal ne” Godiya ta mata tare da rugawa daki ta shirya girgiza kai fatuha tayi ta cigaba da abinda take, rungumeta ta bayan da akayi yasa fatu lumshe ido  ta ce, “Habibi na” ajiyar zuciya sadiq ya saki ya ce, “My love gabaki daya make up din nan ta gigitani kinyi kyau” smile tayi tare da juyowa suna facing juna a hankali ya kai hannu ya warware parking din….

Written by
Salma mas’ud nadabo

     Edit by
Raheenat

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM

                           99_100

1 Month letter

   Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi, inda sadiq ya samu qarin girma dan yanzu haka abuja ya koma da aiki sai weekend yake dawowa kano, fatuha kuwa  shirye-shiryan SSCE suke angel kuma JSSCE, sosai suke samu kulawa wajan sadiq inda yake fifita son su dana kowa, ya ware masu guri na musanman a zuciyarsa haka itama fatuha sosai take bashi kulawa da nuna masa tsantsar soyayya.

    Bangaran su fatima majeed ya sama mata makaranta su fatuha ta fara tun daga jss1, sosai take maida hankali dan ganin taci ma burin ta.

        Basma kuwa Khaleed ya sama mata admission a BUK tana karanta english, sosai take samun kulawa wajan  Khaleed.

    Dr yakub kuwa soyayya suke zubawa tsakaninsa da  Hanan har manya sun shiga maganar.

      Yauma kamar kullun wainar flower take soyawa wadda kwana biyun nan ta zamar mata jiki, dan ko yini bata iyayi bata ci ba,  har wata yar kiba tayi da haske komai na jikin ta ya ciciko da ka ganta kasan tana jin dadi, hutu ya qara ratsata  rungume ta da akayi ne yasata sakin murmushi kasanewar ta san ba mai yin hakan sai sadiq, waigowa tayi tana kallon sadiq cike da so da kauna sadiq na sanye da kakinsa hannu sa na riqe da qugunta, kallonsa take cike da so ta ce, “Habibi na yaushe ka dawo? Light kiss sadiq ya sakar mata a lips ya ce, “Yanzu nan ji nayi bana iya hakuri rashin ganin ki har sati, gaskayi sweetheart daukarki zanyi mu koma tare, na fara gajiya da zama ni kadai ba mata kamar wani gauro” smile fatuha tayi ta ce, “Bari na kashe gas din nan to” kallon wainar yayi tare da cewa “Me kike da wannan abun? ci tace ataqaice tana qoqarin tura wani cikin bakin ta dan bata iya hakuri, bin ta da kallo sadiq yayi da cewa, “Yaushe kika fara cin wannan dear? d’aga kai sama tayi ta ce, “uhm na dan kwana biyu” ok yace tare da daukar ta suka haura upstairs cakulkuli ya shiga yi mata sai dariya take zubawa dan tsagaitawa yayi yana kallon face nata ya dire ta saman bed ya ce, “Ina Angel? shafa gefan face nashi Fatuha tayi ta ce, “Tana gida wajan  grandma dazu da baba jummai ta zo shine ta bita suka tafi” ok yace yana yawo da hannusa cikin rigarta yana qanqace ido mai cike da sakonni ya fara kiss nata ko ta ko ina kiss juna suke with immense feeling da dukan su suke da shi, yana aika mata da sakonin shi masu zafi haka ita fatuha ganin zasu lola duniyar ma aurata naja masu kofa na fice.

            A  tare suka shige toilet  sukayi wanka, dauke da ita sadiq ya fito yana mata cakulkuli tana dariya ta ce, “Habibina sokake ciki na ya qule ko? ta ida zancan tana mai da numfashi lakace mata hanci sadiq yayi ya dire ta saman sofa ya janyo lotion yana shafa mata itama tana shafa masa sannan suka shirya cikin jeans n t-shirts iri daya jeans blue rigar red da ratsin dark blue n white  wani irin kyau suka zuba masha Allah.

    Parlour suka fito a tare, suka wuce dining area lafiyayan chicken and vegetable stew tayi  da cuscus da miyar kwai , tun kafi sadiq ya fara ci ya lumshe ido saboda kamshi dadi dama gashi fatuha ba baya ba wajan iya abinci, saving nashi ta gama yi sannan ta  fara feeding nasa yana ci yana jin dadi gefe ga natural lemun kankana amsar cokalin yayi ya kai abinci baki fatu ta amsa tana ci zuciyar ta na tashi da gudu ta haura sama tana kakarin amai, binta sadiq yayi a baya toilet ta shige tana kwarara amai kamar zata amayo yan cikin ta gabaki d’aya sadiq ya rude sai tanbayar ta yake lafiya, wanke mata fuska yayi da kuskure mata baki ya d’auke lamo tayi a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya ba abinda ke mata dadi kamar turaran dake jikinsa kamar karya sauke ta, saman bed ya dire ta ya koma toilet ya wanke inda tayi aman, ya wanke toilet din ya fito gefan bed ya dawo ya zauna yana ta6a goshin ta ya ce, “sweetheart sannu” yauwa fatu tace cike da kasala, mirginowa tayi ta lafe jikinsa tana shinshinar kamshin turaransa tayi lamo, haka sadiq ya dinga jera mata sannu  wayarsa ya dauka dake saman bedside drawer ya kira Dr yakub ko mintin 10 ba’ayi ba yazo, sadiq ya masa iso har bedroom har lokacin fatu na kwance tana rawar dari tana qudindine cikin blanket, sannu Dr yakub ya mata kana ya mata yan gwaje-gwaje tanbayar ta yayi ya ce, “me dame ke damun ki kamar mai dame kike ji? cikin sanyin murya Fatuha ta ce, “Zazzabi ciwo kai da yawan tashin zuciya, tun ba yau ba” rubuce-rubuce Dr yakub yayi ya bata wata yar kwalba ya ce, Ta shiga toilet tayi fitsari a cikinta  ta kawo masa a hankali ta tashi ta shiga toilet sadiq dai na gefe sai sannu yake mata, ko 5 minutes batayi ba ta fito  amsar kwalbar yayi yasa cikin jakar aikin shi ita kuma Fatuha ta koma ta kwanta smile yayi yana kallon sadiq ya ce, “Insha Allah zata samu sauki indai abinda nake tunani ne sai dai muce Allah ya raba lafiya, amma for now sai mun fara yin test tukun” murmushi ne ya subuce ma sadiq  da fatan Allah yasa abinda shima yake tunanine .

         Har bakin mota ya raka Dr yakub sannan ya juyo gida, ko da ya dawo kwance ya same ta yadda ya barta, saman bed din shima ya hau tare da taba goshin ta cikin shagwaba ta ce, “Habibina”
“na’am sweetheart” lumshe ido tayi ta ce, “Zanci irin wannan abincin dana fara ci randa na zo birni” kallon ta sadiq ya shiga yi yau kusan shekara nawa shi yanzu aka tare shi da bindiga bai iya tuna me akayi ranar, cikin sanyin murya sadiq ya ce, “Sweetheart kiyi hakuri ki fadi wani abun, amma wannan bana iya tuna ko me akayi, ko kina iya tunawa sai a maki?  d’aga kai tayi ya ce “To fadi min”
“shinkafa da miya da kosulo da farfesun yan’ciki” to sadiq ya ce mata tare da yi mata peck ya fita,

      Kitchen ya shiga ya samu baba asabe na goge-goge gaishe ta yayi a taqaice ta amsa ya fada mata abinda zata ma fatuha to tace masa, jiki na bari ta fara aikin, shi kuma ya koma bedroom sai zuba masa rigima fatu take, ko da baba asabe ta gama ta kai dining area ta jera, dauko Fatuha sadiq yayi ya kawota dining ya daurata saman cinyarsa  ya fara saving nata a hankali ya nufo da cokalin bakin ta tunkan ya kai bakin ta zuciyarta ta fara tashi da  sauri ta miqe riqe ta sadiq yayi yana kuma tanbayar ta kafin ya ida magana ta wanke shi da amai  langwabe kai sadiq yayi ya ce, “Sorry my wife” kuka ta saka masa lallashita ya shiga yi  ya dauke ta suka koma bedroom bai dire ta ko ina ba sai cikin toilet, wanka su kayi a tare sannan yasa bathrobe ya nado Fatuha cikin towel sai kuka take masa yana lallashinta kwantar da ita yayi yana qoqari dauko lotion wayarsa ta hau ruri a hankali ya kai hannu ya dauka suna Dr yakub ne ya baiyana a jikin scream din cikin sauri ya dauka tare da karawa a kunne, “hello Dr yakub” daga dayan bangaran Dr yakub ya ce, “albishirin ka” dan tsaki sadiq yaja ya ce, “me kuma hakan ina fama da mara lafiya kana kirana ka min irin wannan kidding din”
“toh shikenan tunda baka son sanin maganin” dan smile sadiq yayi ya ce, “Goro.!
“yauwa ko kai fa amma fa sai ka bani Goran albishir”  to sadiq yace yana mai qaguwa yaji mai Dr yakub zaice dariyar shaqiyanci Dr yayi ya ce, “angon qauri kasha kamshi” Dr ya fada yana dariyar shaqiyanci ya ce, “congratulation madam na da juna biyu na wata 1,” wani irin lallausan murmushi sadiq ya saki ya ce “Wai da gaske kake?” ya ce, “eh mana,!
“gaskiya naji dadin wannan albishir,”
“toh nima a bani goran albishir dina” dariya sadiq ya saki tare da cewa, “na dau nauyin tafiyar ku zuwa honeymoon kowace qasa kuke so a duniya zan  baku kudin kashe wa” wata irin dariya Dr yakub ya fashe da ita ya ce, “Wai da gaske kake? ya ce, “eh mana ana daura maku aure da Hanan zaka ji alat”
“Aiko mun gode sosai anjima ka shigo ka amshi magungunata” to sadiq yace a takaice sukayi sallama ya kashe wayar juyowa sadiq yayi ya sakar wa fatuha da lallausan murmushi itama smile tayi lotion ya shafa mata tare da  samata kaya sannan shima ya shirya kallon ta yake cike da so ya daura hannusa saman cikin ta ya ce, “My love yanzu nan akwai baby na ko” kallon sa Fatuha take tace “Wani baby kuma? ya ce, “babyn mu mana da zaki haifa mana soon ni da angle” ganin yarda fatu tayi kicin-kicin da rai yasa sadiq cewa, “ko baki so ki haihune uhm” ya fada yana kallonta kuka ta saki ta tashi daga jikin sadiq ta ce, “Allah bana so yanzu ya zanyi da exam da ciki tun yanzu yana bani wahala bale kuma idan na fara exam ya zanyi da shi” kuka ta saki tana cewa, “Allah bana so  a cire min shi a kai kasuwa” jawo ta sadiq yayi jikinsa ya ce, “Fatuha yanzu jinina ne baki so? ya fada yana kallon ta “ni ban ce bana son jinin ka ba, amma ai matsamin zaiyi shikenan haka zan dinga  shiga cikin su Nana da ciki” ta ida zancan tana kuka ta cigaba da cewa, “kalli ka gani ko fa yau cikin ya hanani cin abinci, ya hanani duk wata walwala”
“yi hakuri Fatuha ai duk wannan abun na dan lokaci ne, zai daina” tsale tayi ta dire ita bata so sai dai a zubar har  ta kai ga ran sadiq ya fara baci qoqarin fita yake daga dakin ya ce, “ki shirya gobe a zubar da cikin, ni kuma na  auro wadda zata iya zama da ciki na koma a inane” kuka fatuha ta saki tana cewa, “Allah ba mai shigo min gida ni kadai ke da kai wallahi,” ta ida zancan tana qara sakin kuka, abinma dariya yaso ya ba ma sadiq ganin duk tabi ta rude yasa sadiq ya ce mata ya fasa amma sai idan zata zauna da cikin sa amincewa tayi ba shiri tare da juya masa baya tana qara sautin kukan ta.

       Jawo ta sadiq yayi yana lallashin ta ya ce, “ai na ce na fasa tunda kina so yanzu” lamo tayi a jikinsa cikin cool voice ya ce, “My love me zaki ci? cikin shagwaba ta ce, “Dan wake” bata fuska sadiq yayi ya ce, “gaskiya babyna ba zaici mai da yaji ba,” kuka ta fara shirin samasa ganin ba yadda zaiyi  haka ya fada ma baba asabe tayi mata dan wake ba laifi taci dan wakyan sosai da akayi har da side plate.

        Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda fatuha ke samun kulawa sai dai cikin tana mai laulayi ne sosai, kusan a tare suke laulayi da su fatima amma sai dai duk ta fiso wahala ga wani shegyan kwadayi da ya samata angel ko da taji Mom na da ciki murna ba’a magana Mom za tayi mata qani ko qanwa ta samu abokiyar fira.

      Shirye-shirye ake sosai na bikin Hanan dan yau duk kusan sun halara family house saboda yau ne za’ayi kamu, bayan sun gama exam din mathematics a school driver ya zo daukar fatuha bai zame da ita ko ina ba sai family house, a gajiye likis ta dawo yana sauke ta tashigo gida umma ce ta tare ta, ta  hada mata ruwan wanka ta shiga toilet ta fito kasancewar ansan yadda cikin ta yake farfesun kifi Mom ta mata mai dadi tana fitowa ta iske kayanta saman bed after dress ce ta zura sannan ta fito parlour tana fitowa ta samu su fatima suna ta kwasar  nasu farfesun, kwabe fuska fatu tayi tana kallon Mom da itama kallon ta take dariya daki’n ya dauka Mom ta jawo ta jikinta tare da bude mata kola ta fara feeding nata tana amsa sai janta suke ta fiye raki harara da dinga aika masu Mom ta ce, “taje tayi din kuma din ai kawai shuru kukeyi da baku rakin kuma raki ba’a sani sai ranar juyewa” ammi dariya tayi ta ce, “kai hauwa kina fama da surukan nan naki, kina shan drama” ya zanyi ammi, komai cikin walwala da jin dadi da soyayya suke dan sun samu gidan maza jan nasu ya zama kamar gidan iyayan su dan yanzu sunfi mazan ma samun qugun zama har qorafi mazan keyi saboda banbanci da ake masu anfifita matan a kansu musanman yanzu da suke da juna biyu..
Written by
Salma mas’ud nadabo

Edit by
Raheenat

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM

101_102

     Godiya ta musanman gare ku REAL-HAUSA-FULANI-WRITERS-FORUM wannan shafin naku ne, ana mugun tare irin   sosai din nan Allah ya bar zuminci Allah ya qara hada kanmu

          Qoqarin sa rigar ashobenta  take da mami ta dinka masu, amma sket din ya kasa shiga saboda hips dinta daya qaru, lagwabe kai tayi tana qara tura skirt din tana jin kamar tayi kuka jin an bude kofa ya sata waigowa sadiq ne ya shigo dakin, kuka ta fara rera masa tunkan ya qaraso gareta, qarasowa sadiq yayi da sauri ya dago da fuskar fatu da tayi shafe-shafe da hawaye ya ce, “My wife me ya saki kuka uhm? wani kukan ta qara saki ta ce, “Habibina ashobe na ya kasa shiga ta tun dazu nake jan sket din yaki shiga” ta ida zancan tana sa masa kuka jawo ta jikinsa yayi ya zaunar da ita saman bed ya ce, “Wannan ne matsalar?” d’aga kai tayi alama eh, “toh shikenan bani kayan na gani” amsar kayan sadiq yayi ya duba Allah ya taimakesa akwai space,  zaunawa yayi ya warware skirt din da rigar sannan ya miqa mata tasa maqale qafa tayi ita bata iya sa kayan hannu ta nauyi yake mata, lakace mata hanci sadiq yayi ya ce, “My love yau baby  na rigima ya saki ko? turo baki tayi gaba cike da shagwaba kiss nata sadiq ya fara ko ta ko ina ganin zai zarce yasa fatu samasa kuka, smile yayi ya ce, “sorry.! sannan yasa mata kayan shima shirya cikin manyan kaya sannan ya jata suka fito ko da suka fito lokacin su fatima sun shirya ita kadai suke jira ta fito, tana fitowa fatima ta ce, “Sai muje ko?  ta ida zancan tana aika mata harara wasa murguda mata baki fatu tayi sannan suka fice sadiq kuma ya wuce wajan angwayan saboda kamun ba maza.

          Suna shigewa mota fatima ta ce, “Ke haka ake? daga shiga sa kaya saiki maqale da miji”
“kam me kika daukan to nayi din” ta fada tana aika ma fatima hararar wasa Fatima ta ce, “abin da kike tunani” dariya suka kwashe da ita a tare Fatima ta ce, “wannan cikin kamar ya dawo maki da halin ki na baya” dariya fatu ta saki ta ce, “har kin sa na tuna san da muke zuwa gonar mai gari.! dariya suka kuma saki suna tuno yarintar su mai cike da drama  kallon juna suka yi tare da cewa, “Allah mun gode maka bamu ta6a tunanin ganin mu a haka ba, rayuwa kenan” rungume juna sukayi tare da  hade bakin su suka furta, “Allah ya bar mana zumincin mu har ya’ya da jikoki ameen Fatsima” harara ta aika ma fatu ta ce, “ke mijina ya hana fadin wannan suna,” dariya sukayi tare da cewa, “sannu mai miji” a haka suka isa wajan kamun  kasancewar sune manya-manyan qawayan amarya hada-hada kawai suke biki yayi biki su Zara da Nana ma sai da suka zo ansha biki sosai sai kusan yamma likis suka dawo, gidan mami suka wuce direct.

        Da sallama suka shigo angel dake zaune da friends nata ta qaraso ta rungume fatuha ta ce, “Mom a I miss you”
“miss you more dear, kin manta da mamanki tunda biki ya kama ko? to ai gashi nan ni na biyo ki bana iya hakuri kimin nisa” fatuha ta fada tana shafa kanta smile tayi  ta ce, “Nima haka Mom” ja mata hanci fatu tayi sannan ta koma cikin friends din ta.

          Shirye-shirye na zuwa dinner suke, cikin material lace green and black yan’matan amarya, amarya kuma ta shirya cikin black lace mai ratsin white, sosai sun fito sunyi kyau musanman da suka sha make up, cikin  motaci na gani na fada aka zo kwasar yan matan amarya, fatuha ko motar sadiq ta shige, lallausan murmushi sadiq ya sakar ma fatu ya kama  hannu ta yana murzawa a hankali cikin salo yana sakin murmushi yasha kyau har ya gaji yana sanye cikin shada milk tasha aikin hannu,  kamshin turaransa na fizgar fatu ya  ce, “My wife kinyi kyau masha Allah” smile fatuha tayi ta ce, “na gode hubi, kai ma kayi kyau har na ji kishi kar mu je yan mata su dinga kalle min kai” fatu ta fada tana d’an 6ata fuska yar dariya sadiq ya saki yace, “ni ba mai kallo na mijin mace daya daga fatu na rufe” murmushi ta sakar masa mai cike da sakonni sannan ya ja mota hannu sa daya na maqale dana fatuha.

              Hall ya cika maqil anata gudanar da biki, inda abun ya zama abin sha’awa da birgewa amarya da Ango sunyi kyau har sun gaji, kasancewar bikin masu hannu da shuni ne  manya-manyan ya’ya masu hali da masu fada aji sun halara, fatu da sadiq kam sun zama abin kallo dan sadiq baya iya boye irin son da yake ma fatuha koma a inane nuna mata so yake, sai nan yake da ita haka aka gudanar biki, ayi ciye-ciye da lashe-lashe  naira tayi kuka dan anyi barinta sai dai mu ce Allah ya bada zaman lafiya.

          Da misalin karfe 10:00pm taro ya watse sadiq ya wuce da fatuha gida, maqale qafa tayi ita baza ta koma gida ba ya maida ta gidan mami, cikin yan’mata amarya fir sadiq yaki saurarata haka ta cika taf kamar ta fashe, horn yayi mai gadi ya wangale geta ya kunna hancin motarsa cikin gida yayi parking a parking space, kashe motar yayi ya bude murfin motar fatuha ko zaune tayi tana qoqarin fara raira kuka Allah ya gani gidan Mami ta so kwana ba gida ba, zagayowa sadiq yayi ya 6ale mata murfin motar ganin fatu bata da niyar fitowa sadiq ya dauke ta kamar baby ya shiga da ita gida sai rigima take zuba masa har da kuka dakyar ya lallashi fatu ta saurara masu sukayi baccin dare.

   Washe gari

   Yau d’ibin mutane suka sheda daurin auran Dr yakub da Hanan    akan sadaki naira dubu dari, zuciyar Dr yakub fes sai washe baki yake da ka gansa kasan yana cikin farin ciki, ana kamala daura auran Dr yakub yaji alat a account dinsa kallon sadiq yayi tare da sakar masa murmushi sannan ya masa godiya,  bayan  kamala biki ango ya dauki amaryar sa sai airport inda Hanan ke ta zuba kuka.

            Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dad’i inda sadiq ke bama fatuha kulawa sosai, yanzu haka sun fara exam, alhamdulillah exam din ta zo mata da sauki, cikin ta ya dan fito.

     Murna suke sosai na ganin cewa yau sun gama paper, sosai fatuha ke jin dad’i a gaskiya bata da abinda zata ce ma mai kyau ya gama mata komai a rayuwa, ko da ta fito sadiq ne ya zo daukar ta, kasancewar Saturday ne ya zo weekend gida cike da farin ciki ta qarasa gaban motar ya 6ale mata murfin mota ta shiga, su Zara ko d’aga mata hannu su kayi tare da yimata alqawarin sai sun zo ranar suna.

       Kallon ta sadiq yake cike da so a hankali yake driving cikin nutsuwa har suka iso gida, shi da kansa ya bude mata murfin mota wata hadadiyar mota ta gani mai tsadar gaske sabuwa dal  Lexus toyota fake a harabar gidan su, kallon sadiq tayi ta ce, “Habibina munyi baqine?” d’aga mata kai yayi tare da janta suka shige ciki suna  shigowa parlour, parlour ya dauki sautin, “happy birthday to you fatuha” cike da farin ciki fatu ke bin su da kallo wasu kyalkyali suka fara zubowa a jikinta da flowers kallon sadiq take da mamaki peck ya sakar mata a goshi ya furta,  “happy birthday my wife🎂.!  jan hannuta yayi gaban cake shida angel dan kusan ita ta hada komai, sosai farin cikin fatu ya kasa 6oyuwa dan ba qaramin dadi ta ji ba sai smile fatuha take tare suka hada hannu suka yanka cake din, parlour ya dau tafi, gutsuro cake din sadiq yayi ya bata a baki itama ta amsa ta bashi sannan angel ta bata itama ta ba angel, pictures sukayi sosai yan’uwa da abokan arziqi suka bata gift da yawa, daukarta sadiq yayi cak ya maido ta harabar gida a je ta qasa yayi ya rungume ta, ta baya tana facing din motar dazu ya ce, “Rufe idanuwan ki love” lumshe ido fatuha tayi sadiq ya ce, ta bude tana budewa taga car key wani irin ihu fatu ta saki tana kallon car key kame da baki, juyowa tayi ta rungume sadiq tasa kukan farin cikin, shafa bayanta sadiq yake a hankali ya zame jikinsa yasa hannu ya goge mata hawayan dariya ta saki tare da sakar masa peck  ta ko ina tana cewa, “thank you hubi thank you.! dariya su majeed suka saki shi da fatima, murfi motar ta bude ta shiga yana mai tsananin farin ciki sannan ta kule motar suka dawo cikin gida sadiq ya mata alqawarin kafi ta fara zuwa university zai koya mata driven.

   Bayan kwana 2
***
Shirya kaya fatuha take cikin trolley a yanzu cikin ta zai kai 4 month, sadiq ne ya jawota jikinsa ya zaunar da ita shi ya cigaba da hada kayan, sai murna take kasancewar wudil zasu daga nan su wuce abuja, yima sadiq kwana biyu bayan ya gama hada kayan cikin trolley, ya ja trolley din zuwa parlour ya kiran Sunday, ya amshi kayan ya kai su boot sannan sadiq ya leqa bedroom din angel itama ta gama hada na ta kayan, smile tayi ta ce, Daddy.! ta masa peck ta miqa masa trolley dinta, amsa sadiq yayi ya ce, “Angel kin sa komai da kike buqata  ko? Dan karki manta wani abu” d’aga kai tayi ta ce, “Yes daddy”
“good girl idan zaki fito ki kashe AC da komai na bedroom din” ok tace tare da nufar AC zata kashe sadiq ya fita ya ba Sunday trolley jidda ya kai boot komai sun gama hadawa, sun shirya tsaf sai tafiya  fatuha na sanye cikin  atamfa dinkin bubu dinkin ya zauna ajikinta das ya mata kyau sosai cikinta ya fito,  kanta ya sha dauri wadda ya dace sosai ta fito matar manya da ita tana yafe da mayafin daya dace da kala kayanta, tayi kyau har ta gaji ta qara haske, rike da wayarta iPhone 6 Angel ta fito daga bedroom suna video call da Jamal tana sanye cikin lace riga da sket dan yanzu ta fara zama yan’mata kashe wayar tayi ta biyo bayan su Mom suka fita a tare, da kansa sadiq yaja motar, sai da suka fara zuwa gida, haka Mom ta hada masu tsaraba sosai ta masu Allah ya kiyaye hanya ita da Abba kana suka kama hanyar zuwa wudil.

        Da misalin karfe 2:00pm suka isa wudil cike da murna fatuha ta shige gida ita da angel, da gudu angel ta fada jikin inna dariya inna ta saki ta ce, “oyoyo mutanan birni sannu ku da zuwa, yau tafiyar harda yan’mata? kwabe fuska fatuha tayi ta ce, “Angel dan kin fini sauri ko shine kika rigani” dariya sukayi a tare sannan suka shige parlour haka inna ta dinga nan da su sadiq ko tunda ya sauke su ya wuce gidan gona wajan Baffa ya taya shi aiki sai hanasa Baffa yake acewarsa daga zuwansa baya fara da aiki ba, sai yamma liqis suka dawo.
gaishe da inna sadiq yayi sai zuba masa albarka take sannan ya wuce masaukinsa, wanka kawai yayi yana tsane jikinsa fatuha ta shigo da kulolin abinci ta aje masa sannan ta amshi towel din hannusa  tana goge masa jiki, jawota jikinsa sadiq yayi sosai yana facing nata cike da so a hankali ya kai hannu kan cikinta ya ce, “Ya babyna? smile fatuha tayi ta ce, “Yana cikin koshin lafiya”
“Are you sure? d’aga masa kai, rage tsawansa yayi dai-dai cikin fatu ya kasa kunne saitin cikinta yana murmushi saboda baby sai motsi yake peck yama cikin tare da miqewa  fatuha ta taimaka masa ya shirya kana tayi feeding nasa tuwo shinkafa miyar kuka tasha manshanu da naman rago sosai yaji dadin abincin.

      Angel ko tana wajan inna suna shan hira, Idan ta bugo wani shirman inna ta biye mata, dan inna jin take tamkar jikarta haka itama angel sakin jiki take da inna sosai.

         Qoqarin fita fatuha take Sadiq ya riqe ta ya langwabe kai  ya ce, “my love,” shafa gefan fuskarsa fatu tayi ta ce, “Na’am” shagwabe fuska sadiq yayi ya ce, “Please ki kwana anan?” zaro ido waje fatuha tayi ta ce, “Ta6 ba ruwana nama ji da wannan abin kunyar” ta nuna cikin ta dariya sadiq yayi ya hade goshin su waje guda ya ce, “Ai na halal ne ko kin manta?” lumshe ido tayi a hankali sadiq ya lallubu bakin ta yana kissing, sun dau lokaci mai tsaho suna tsotsanar la66an juna su sannan ya sake ta yana maida numfashi, smile fatuha tayi ta ce, “I love you”
“Love you more” kana fatu ta fice da sauri, barbaza sumar kansa sadiq yayi tare da furzar da iskar bakinsa mai sanyi ya furta, “always loving  you fatuha..! Sannan ya kwanta.

        Kwanan su fatuha biyu a wudil, ta zagaya gidajan yan uwa da abokan arziki, hada kayan su suke zasu wuce, fatuha ji take kamar karsu tafi haka dai ta gama hada kayan, inna sai sa masu albarka take tare da yi masu addu’a samun zaman lafiya mai daurewa, sadiq ko albishir ya masu daya biya masu kujera haji murna wajan fatuha ba’a magana, haka ta dinga zuba ma sadiq godiya haka su Baffa da inna sannan ya fido kudi masu yawa ya aje masu dakyar ya samu Baffa ya amsa, sannan itama fatuha ta baje masu tsaraba laces da atamfa da shada da ta siya masu sosai su inna sun ji dadi sannan suka dau hanyar abuja fatuha har da yar kwallanta ita da angel.

      Sai  dare suka iso abuja, katafarin gidan nasu ya hadu fadin tsaruwar gidan ma bata lokaci ne, dan yafi na kano ko ta ko ina, duk inda ka waiga a gidan yaran sadiq ne sojoji da yawa kamar a barak haka suka shigo da kayan su kasancewar sunci abinci a hanya, sallah kawai su kayi angel ta shige dakin da sadiq ya gwada mata a matsayin nata dakin ya hadu dan yafi nata na kano kyau nesa ba kusa ba.

         Haka suma dakin su fatuha ya hadu iya kar haduwa, har kauyanci sai da fatuha tayima sadiq dariya kawai yake mata saboda komai tayi birgeshi take.

     Washe gari

Bayan sun kamala komai sadiq kwashe su zuwa yawo, sosai sun sha yawo inda sadiq keta kula da fatuha yana bata kayan gina jiki wanda zasu taimaka mata ta haihu cikin koshin lafiya.

   3 month letters

     Sosai cikin fatuha ya girma dan har Mom ta ce sadiq ya maido ta kano, kasancewar tun hutun da suka tafi basu dawo ba, saboda cikin yanzu ya kai wata na takwas, ba yarda sadiq ya iya ya amsa da toh dan baya so tayi nisa da shi.

       Shi da kansa ya hada masu kaya  sannan ya kai masu boot itama fatuha ji take za tayi missing nashi, sannan suka dau hanyar kano, suna isa kano gidan Mom ya wuce da su lokacin itama fatima ta dawo  gida ita da Basma saboda Mom ta ce baza su je gida ba, a wajan ta zasu haihu har suyi arba’in, dadi ta ji ganin su sai damuwar ta ta ragu kwana sadiq daya ya juya abuja cike da kewar fatuha.

    Akwana a tashi ba wuya wajan Allah, su fatuha yau da naquda suka tashi majeed Mom ta kira a waya ta sheda masa halin da suke ciki, driver ya  wuce da su asibiti, labour room aka wuce da su, su uku sun dade suna naquda, sosai hankalin Mom dana Umma ya tashi su Abba na kwantar masu da hankali, ko da sadiq ya iso gari daga  airport asibiti kawai ya wuce yana isa lokacin yayi dai-dai da haihuwa fatuha ta sili6o baby boy din ta Fatima ma boy ta haifa, Basma baby girl masha Allah yaran masu kyau, musanman fatuha gabaki daya baby sadiq ya d’auko kamar yayi kaki ya aje haka suka dinga murna kankace me asibitin ya cika da yan uwa.

      A hankali sadiq ya qaraso bakin gadon da baby ke kwance yasa hannu ya daukesa yana kallo, “masha Allah.! Ya furta a hankali yana smile tare da kallon fatuha hannuta ya kama ya sakar mata light kiss a hannuta Sadiq ya ce, “Thank you my wife da kika bani wannan farin cikin”Angel ma murna ba’a magana kwana su d’aya aka sallame su family house aka wuce da su.

      Sosai suke samu kulawa tare da wanka da shan abubuwa masu gina jiki,  ranar suna anyi shagali ba dan k’adan ba, inda dan fatuha yaci sunan Abba Ibrahim ana kiransa da aslam,
D’an majeed yaci su baba khabir ana kiran shi da Walid, diyar Khaleed taci suna Khadija ana kiranta da Nana.

      Suna yayi suna inda aka dinga narka kudi kamar ba’a so, anyi ciye-ciye da lashe-lashe an raba sabeniyas sannan taro ya watse kowa ya tafi gida cike da farin ciki aka bar masu jego.

        sosai Mom ta zage tana gyaran ya’yan nata inda suke ta shan gyara  jikin da tsimi wani irin kyau da sheqi suke  zubawa, baby’s kuwa sunyi wayau gasu yan duma-duma saboda suna samun ruwan nono sosai kullan angel na maqale da Aslam sai fatuha zata bashi nono sannan angel ke bata shi, dan wani irin son duniya ta daura mashi, bata da  lokaci kowa sai na Aslam.

      Sanye da qaramin towel ta fito daga bathroom tana goge gashin kanta da qaramin towel, gaban dressing mirror ta tsaya tana shiryawa lotion ta jawo zata shafa, ta hango sadiq ta cikin mirror lallausan murmushi ta sakar masa a hankali ya qaraso ya rungumeta ta baya sanyayar ajiyar zuciya ya saki yana shinshinar kamshi jikinta lumshe ido fatuha tayi tana amsar sakonin sadiq, dan ba qaramin kewarsa tayi ba qoqarin zame towel di’n jikinta yake ta riqe tana kallonsa ta cikin mirror, lumshe shanyayun idnusa yayi ya ce, “Please..! yana qoqarin zame hannuta dake saman towel din kasa magana fatu tayi har sadiq ya samu nasara zame towel din rintse ido tayi tare da waigowa ta shige jikinsa, daukar ta cak yayi ya daura saman bed ya fara aika mata sakonni da zafi-zafi lokaci daya suka fice hayacin su, gani zasu lula yasa na silale na fice.

        Shiryawa take cikin atamfa riga da sket cike da shagwaba ta ce, “Habibina gaskiya ka tashi ka fita bana so Mom ta zo ta gan ka, tana ganin ka zata gane” ta ida zancan tana parking  gashin kanta smile sadiq yayi  ya rungumeta sosai ta baya can kasan makoshi ya ce, “Uhm my love baza ta gane komai ba kinji”
“da gaske” daga mata kai sadiq yayi alamar eh tare da ciro wasu takadu daga aljihusa ya miqamata, wani irin tsale fatuha tayi ta qanqanme sadiq dan murna ba komai  bane yasata farin cikin ba sai admission na north west university data gani.

      Da sauri fatuha ta fita tana kwalawa Mom kira, fitowa tayi daga kitchen ta ce, “na’am fatuha” fadawa tayi jikin Mom tare da nuna mata admission murna Mom ta tayata tare da yima sadiq godiya sosa keya yayi angel itama fitowa tayi riqe da Aslam amsarsa sadiq yayi yana mashi wasa, haka su fatima suka dinga taya fatuha murna.

    3  years letters

      Sosai fatuha ke maida hankali a karatun ta tana karanta law yanzu haka tana level 2, Aslam yayi wayau sosai dan har tafiya yana yi ba ida baya zuwa zai kai  2years ga surutu  tsiya komai ya gani sai ya tanka, angel kuma na SS2 an fara zama yan’mata sosai.

       Yauma kamar kullun a  gajiye ta dawo daga makaranta tun safe taje school sai 5:00pm suka gama lectures, a gajiye likis ta dawo gida ga wata irin kasala dake damunta, Aslam ne ya sako daga jikin baba asabe rugo da gudu ya fada jikin fatuha, daga shi sama tayi tana chabesa yana dariya  zaunawa tayi saman three sitar tare da gaida baba asabe amsawa tayi atakaice ta shige kitchen Aslam zama yayi saman cinyar ta yana zuba mata surutu, cakulkuli ta shiga yi masa yana dariya tsagaitawa tayi ta ce “Ina yaya?, daga kai yayi cikin tsamin murya ya ce, “yaya na bacci” ok fatuha tace tare da tashi ta shige bedroom bata zame ko ina ba sai toilet ta sheqa wanka ta fito  ta gabatar da salolin da ake bin ta, turo kofar da akayi ne ya sata smile angel ce tsaye bakin kofar sanye da jean  n t-shirt ta ce, “mom sannu da zuwa,”
“yauwa” fatuha tace qarasowa tayi ta ce, “Mom  ki zo muyi lunch tun dazu na dawo daga school naqi cin komai sai kin dawo,” murmushi fatuha tayi ta ce ” Karki qara barin kanki da yunwa kinji angel? d’aga kai tayi ta ce,  “ai nasha fresh milk”
“ok muje” dining area suka wuce  lafiyayan doya ce da miya tasha kaji da naman rago sai kamshi ke tashi sosai fatuha taci abincin dan wani irin san doya take kwanan kusan kullun sai ta ci ga wani iri ci da take yanzu kamar runbu da san bacci har mamaki kanta take, bayan su kamala cin abinci suka dawo parlour suna kallo  Aslam sai wasa yake da kayan parlour komai ya gani abin wasa ne da an hanasa sai kuka yace zai fada ma daddy, yanzu ma haka 6ana yake fatuha jawo hannuwansa ta hada biyu tana masa fada kuka ya sa mata kamar ta daura masa wuka sadiq da shigowarsa yanzu kenan harara ya aika ma fatuha ya qaraso ya dauki Aslam ya wuce da shi bedroom nasa, ta6e baki  fatuha tayi tare da bin bayansa ko kallon ta baiyi ba sai ma wasa da yake ma Aslam yana dariya miqa hannu tayi ya bata Aslam ya wurga mata harara  ya ce, “Baki shi zanyi ki ida kasheshi ko me? ya  ida zancan yana qara rungume Aslam dariya fatuha tayi ta ce “Dama ka bani shi saboda yanzu zai fara daura ma headache, yaron nan baya ji sam”
“hmm  zakiyi bayani na kama ki kina dukar min d’a” jawo ta Sadiq yayi ta fada saman bed yana kai mata naushin wasa shi da Aslam dariya take sosai rungume sadiq tayi a hankali yake shafa bayan ta ya ce, “I miss you love” zame jikin ta tayi tare da kashe masa ido ta dauki Aslam ta maida shi parlour kana ta dawo taimaka ma sadiq  ya rage kayansa suka shige toilet maqale da juna suka fito suna shan soyayya.

     4 Years letter

      Wata kyayakwar yarinya ce wadda baza ta wuce  4 years  ba ta shigo parlour tana kuka ta fada jikin sadiq dake zaune saman three siter yana karanta newspaper idanusa manne  da farin glass yana sanye cikin  English wears ya qara kyau ya murje hutu ya zauna masa ya qara girma, cikin shasheqar kuka ta ce, “Daddy ka ga yaya Aslam ya amshe min baby wasa na ko” daukar ta sadiq yayi yana lallashita ya ce, “sorry little Mom, rabu da shi zan siya maki sabi okey” fatuha da fitowar daga kitchen kenan jin kukan little Mom, tana sanye cikin green lace tasha kyau har ta gaji ta ce, “Wai me yasa Aslam baya jin magana ne, duk wani neman fita ya iya? zai shigo gidan ya same ni ai sorry dear” yar yarinyar dake jiki sadiq sunan ta kausar amma suna kiran ta da little Mom saboda sunan margayiya kausar aka saka mata sosai fatuha ke ji da ita saboda ita da kanta tasa sadiq yasa sunan, yanzu haka sun koma abuja da zama fatuha ta gama karatun ta aiki take angel kuma na university.

          Kasancewar lokacin lunch yayi kowa ya halara dining area suna lunch suna dariya, sadiq ne ya curo wayarsa dake cikin aljihu yace selfy su duka suka matso tare da saki murmushi happy family life.

           Tamatubihamdulillah

  A nan na kawo karshan wannan littafi nawa mai suna captain sadiq, ina mai miqa godiya ga dinbin masoyan wannan littafi.

  Abinda muka fada dai-dai da wanda bamu fada dai-dai ba Allah ya yafe  mana.

   Ina godiya irin sosai din nan ga Aunty  Raheenat da ta bani goyan baya wajan rubuta wannan labarin tare damin good editing dan ya qayatar da masoya wannan novel,  ina miqa godiya ta irin sosai din nan muna mugun tare.

    Gamai buqatar littafi na ga number ta kamar haka 07063683025

Gargadi: Ni Salma Mas’ud Nadabo ban amince kowa yayi anfani da littafina Captain Sadiq tako wacce Siga ba, duk wadda tayi\Kayi na bar mutum da rabill izati dan haka a kiyaye.

Taku har kullun salma mas’ud nadabo
Pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button