Sponsored Links
Captain Kabeer Hausa NovelHausa Novels and Love Stories

Captain Kabeer Hausa Novel

Sponsored Links

*CAPTAIN KABEER*

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including  your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

بسم الله الرحمن الرحيم
*RUBUTAWA*

*HASSY SOJA  ce*✍🏻

*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

“`BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI  JIN’KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN“`

*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA  YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA’DI*

*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎

*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE  AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

🅿️1️⃣%5️⃣

*________________*🖊️
Wata tsaleleyar budurwa ce kwan ce take tana kuka sosai kamar ranta zai fita ta rike mararta tana juye juye ta dafe marar ta da har ta fara fita hayancin ta.

Shigowar wata Hajiya  ce ya sanya ta hankalin ta ya dawo gurinta tace “shalele na lfy klau kike kuwa meya ke damunki?.

Kuke take jikinta har rawa yake saboda azabar da take sha nuna mata take tana girgiza mata kai.

Da sauri ta karaso gurin tace tace “ko ciwon marar ne”!?.

Daga mata kai tayi tana kuka sosai kamar ranta zai fita.

Dauko waya tayi ta kira doctor sai gashi yazo yayi mata allura sannan yace “gaskiya Hajiya ya kamata ace kunyi mata Aure saboda irin wannan period yana bukatar Namiji kusa da ita.

Shiru tayi na dan wani lokaci sannan tace “to doctor insha Allah dama zamuyi magana da Alhaji idan ya dawo Nigeria insha Allah.

Jin jina kan sa yayi yayi gaba abun sa.

*America*

Wani soja ne zaune yana kallon ruwa Amman tunani yake ina zai sanya rayuwar sa ne  wato Capital kabeer fari tass kamar balarane shi ba dogo ba kuma shi ba gajere ba babu abun da ya tsana duniya kamar tuwon dawa ko na shinkafa  abun da yake so kamar shinkafa da wake da lemon juice da yanboll yana mutuwar son su kayan sanyawa kuwa black and fari da yellow da green.

Mota kuwa fara da black sosai yake hawansu bana son yawan surutu baya son kazanta baya son shishigi ko kadan.

Baya dariya ko murmshi ko dogon surutu sai mahaifiyar sa ita kawai ce ka ganin dariyar sa da surutun sa gashi sarkin shagwaba mahaifin sa ya rasu tun lokacin yana karamin sosai ya barmasu dukiya mai yawa sosai.

Babu abun da ya tsana duniya sama da Aure baya son maganar Aure ko kadan bayaa kula yan mata da yawa yan mata na son sa Amman be basu fuska ba .

Dafashi akayi sannan Abba  yace”Captain kb lafiya Qlau kake kuwa”!?.

Ajiyar zuciya yayi sannan ya mik’e tsaye yana kallon gefen sa yace “ku shirya zamuje Nigeria yau ko da dare yayi sannan ya wuce office din sa.

Dama Abba ya san halin abokin sa baya magana da kowa koda shawara ce bayayi da shi ko fuska baya saki bale wata shawara.

Cikin mintin kadan suka gyara har jirgein Nigeria sun samu d’aya yazo ya fada masa lokacin ya gama hada kayan sa sannan yace “to duk abun da kuke bukata ku dauka saboda ba zamu dawo kasan ba sai muje wata kasa wuce wa yayi ba tare da ya kalle inda suke ba.

Cikin dan kankani lokaci suka shiga cikin  jirgein Nigeria ahankali ahankali ya iso filin jirge sai da ya dauki mintina 30 sannan ya fito cikin ransa yace “Alhamdulillah nadawo k’asata.

Da gudu wani soja yazo Sir ana waya dago  idanuwan sa yayi ya Mike masa  hannu koda ya duba wayar sunan my life mom ya gani dan murmshi yayi sannan  yace “Assalamu Alaikum my life mom.

Zaune take tana kallon tv falon kuwa kamshi turaren wuta yake murmshi tayi tace “Amin wa, Alaikum sallama Naam my son har kun iso kenan ko”!?.

Langwabe kansa yayi yace “Eh yanzun dai ina hanya ne zakije insha Allah.

Ta fahimci akwai masu kallon sa sai tayi murmshi tace “to Allah ya kawo mani kai lafiya sai ta kashe wayar ta.

Bude masa kofar motar akayi sannan ya shiga ciki ya Zauna yana kallon gefen sa driver ya shiga ya fara jan motar ahankali sai da ya kai bak’in titi sannan ya sharara   gudu sai cikin Unguwar masu kudi mai cike da mutane dai dai wani hadaden gida ne yayi hon da sauri mai gadi yazo ya bude masu jin jina kan sa yayi yace “Alhamdulillah oga yadawo gari.

Sulalawa yayi cikin gidan dai dai lokacin yan aikin gidan suna tsaye shi kawai suke jiran fitowar sa Captain kb kuwa ya dauki tsawani mintina 30 Zaune cikin motar da sauri wani soja yazo ya bude masa kofar motar kafarsa ya fara saukowa.

Wow masha Allah Allah yayi halita gaskiya oga kb ya hadu sosai.

Fitowa yayi daga cikin motar kallon gidan yayi sannan ya sanya kai ya wuce cikin gidan.

Koda ya shiga falon kamshin turaren sa ne ya game falon shine ya tabbar mata da cewar d’anta  yadawo jiyowa tayi tana murmshi.

Da gudu yazo ya rungume ta sosai yace “miss you my life mom.

Mommy tayi murmshi cikin jin dadi tace “miss You my son dafatan kadawo lafiya!? .

Kwantawa yayi saman kujera yace “to Alhamdulillah Amman dai na gaji sosai wallahi bari dai na watsa ruwa sannan.

“To madallah Allah yayi maka Albarka.

“Amin ya Allah”

A hankali ta fara bude idanuwanta kai masha Allah Allah yayi halita gaskiya wannan gurin kallon dakin take sannan tayi ajiyar zuciya tace “Allah na gode maka da kabani lafiya.

Hajiya tace “sannu ya jikin naki ne yanzun”!?.

Tashi Zaune tayi tace “Alhamdulillah naji sauki sosai.

Cikin tausayawa tace “yanzun babu wata matsalar komai dai ko”!?.

Daga mata kai tayi tana kallon sama Amman bata ce komai ba ajiyar zuciya tayi tace “Hajiyar mu anjima zanje gurin mommy na dan Allah..

Tabe baki tayi tana kallon ta sannan tace “salon Kabeeru yadawo ku kama fada ko”!?…

Cikin jin haushin sunan da ta fada tace “wai ke Hajiya ni ina ruwa na da shi ni fa gurin mommy zanje fa dan Allah ki daina hada ni da shi dan mugun ne wallahi…

Dariya Hajiya tayi tace “to Allah ya sauwaka yanzun dai daga ke har shi baku zaman lafiya!?…

Turo baki tayi tana kallon gefen ta ……..

*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*

🅿️1️⃣1️⃣%1️⃣5️⃣

*________________*🖊️
Turo baki tayi tana kallon gefen ta saboda haushi maganar take duk abun da take Hajiya  na kallon ta sai tayi murmshin manya tace “to shalelen na adawo lafiya ki gaidan mani da mommyn ta ki.

Mik’ewa tsaye tayi sannan tace “amm kuma kice zan shigo insha Allah sannan ta fita daga cikin dakin tana mamakin irin halin su girgiza kanta tayi.

Tsalle tsalle take saman  gado saboda da farin ciki da take ciki tunda Hajiya ta aminci to yanzun zataje gidan mommy dama tayi kewarta da sauri ta sauko daga saman gado Jakarta da mayafin ta dauko fitowa tayi daga cikin dakin doguwar riga ce tasari green ajikinta saukowa tayi daga saman bene Zaune ta iske Hajiya tana kallon sunnah tv kamshin turaren tane ya game falon shine ya tabbar mata da cewar khadeejah ta fito.

Karasowa gurin tayi tana Murmshi tace “Hajiya na shirya sai nadawo ko”!?.

Kallon ta tayi tace “shalele na kin dauko key dinki ne”!?.

Murmshi tayi tace “eh yana cikin Jakata ne mota green zan hawa kinji Hajiya”!?.

Kallona take tace “uhm to menene na tambaya na ai na kine ko tafi Allah ya tsare.

Amin ya Allah shiyasa nake kara sonki Hajiya ta sai nadawo bye bye da sauri fita daga cikin falon koda ta fito sai ta ga mai gadi ya gama goge motar ta kallon sa take sannan tace ” Baba mai gadi har kagama ne”!?.

Washe baki yayi yace “wallahi kuwa y’ata Allah dai ya kaiki lafiya.

Dubu biyu ta Mike masa tace “to gashi kasai goro ko”?.

Amsa yayi yana sanya mata Albarka bude kofar motar tayi ta shiga ciki ta rufe sulalewa tayi da gudu tana fita daga cikin gidan sai ta kuna wa’kar  Husaini danko.

Zazzaune suke cikin falon da mommy da baba mai aiki kallon ta mommy tayi tace “Amma hajara kin sani danki yadawo ne”!?.

Washe baki tayi tana kallon mommy tace ” A’a  yaushe yadawo kin san lokacin na tafi gida ne”.

“Ok babu damuwa kin sani baya son hayani ne shiyasa.

Baba mai aiki tace “wallahi kuwa ai Allah dai ya bashi mata tagari.

Cikin jin dadi tace “”Amin ya Allah nagode sosai yanzun dai akwai kin gama aikin ne”!?.

Baba tace “eh Hajiya ai tunda zu na gama aiki na.

Horn tayi da gudu mai gadi yazo ya bude ganin hadadar mota green ya gani shigowa cikin gidan tayi dai dai kofar shiga cikin gidan tayi parking ma, aikanta gidanan kowa ya saki baki yana kallon yaga waye acikin motar shalelen kuwa sai da ta gama gyarawa sannan ta bude motar idanuwant sanye take da glass fitowa tayi daga cikin motar gaba d’aya kowa yace wow gaskiya gurin nan Allah yayi halita Allah yayi mata kyau sosai cikin ranta tace”o ni khadee to su wannan kallo haka sai kace tv girgiza kanta tayi tace “Allah ya kyauta.

Da gudu mai gadi yazo yace “A’a yar India yaushe kika dawo “!?.

Dariya maganar sa ta bata sai dai tayi murmshi tace “to  wa ya  fada maka tafiya nayi babu inda naji kaji sarkin tambaya.

Wuce tayi ta shiga cikin gida,  cikin falon ta shigo lokacin Mommy tana magana da Baba kamshin turaren taji ya daki hanci su da sauri mommy suka jiyo kallon ta suke.

Cikin shagwaba tace “Uhm uhm uhm mommy na kin manta da ni ko”!?.

Dariya tayi sannan ta bude mata hannuwa tace “karaso mana Auta ta takaina.

Da gudu tazo ta rungume mommy tace “miss you my mom nayi kewarki sosai.

Ita ta kara rungume ta sosai tace “nima Kullum sai nace wai ina Auta ta tashiga ne”.

Dariya Baba tayi tace “ikon Allah wannan soyayyar taku akwai ban sha,awa kuwa bari dai na tashi naje gida ko.

Tashi Zaune tayi tace “Alhamdulillah  yau gani ga mommy na sai abun da nace nake so ko”!?.

Kwantar da ita tayi saman kafafuwan ta tana dariya tace “sosai ma kuwa sai abun da kike so Auta ya Hajiya dafatan dai kuna lafiya da ko”!?.

Gyara kwanciya tayi tace ” wallahi nayi ciwo kwana biyu mommy ko magana bana iyayi.

Cikin damuwa sosai tace “har yanzun ciwon marar ne”!?.

Daga mata kai tayi ta lumshe idanuwanta.

Kamshin turaren sa ne ya game falon shine ya tabbar mata da cewar ya fito dagowa tayi tana murmshi tace ” Aa my son har ka fito kenan”!?.

Gaban ta yace rasss wani irin tsoro ne da tashin hankali  tashige ta  rufe idanuwanta tayi Amman tana jin muryar sa.

Be ma kula da wata kwan ce ba yace “washiii na gaji sosai wallahi my love  mom aiki akwai wahala sosai fa.

Cikin kulawa tace ” ayyah sorry my son ai dole akwai gajiya sosai.

Motsi yake ji kusa da shi da sauri ya duba ya ganin sai yaga mutum kwan ce saman kafafuwan mommy zaro manya manya idanuwan sa yayi yace “keeeeeee cikin tsawa.

Tashi Zaune tayi tana masa  kallon tsana yatsane fuska tayi.

Mommy tace “A’a  my son daga zuwan  yarinya sai taya mata da hankali “!?.

Cikin bacin rai yace “Haba my love  mom ya zaki bari wannan kazamar yarinya nan ta kwanata  saman kafafuwan ki saboda rainin hankali”!?.

Murguda masa baki tayi tace “to sannu sarkin tsafta kaji ni fa wallahi bana son shishigi fa.

Girgiza kanta mommy tayi tace “Auta ta ina zuwa Mik’ewa tsaye ta ta wuce ciki Captain kb da khadeejah  kallon tsana suke ma junan su.

Bayan minta gama shabiyar Mik’ewa tsaye tayi sannan zata wuce yace “keeeee baki iya gaisuwa bane”!?.

Dariya maganar sa taba tace “Allah ko kai ko kunya bakaji ba mtsss ni ko mutum ban gani ba bale kace wai ban gaida kai ba.

Wata irin tsawa ya daka mata idanuwan sa sukayi jajaru yace “ni sa,an ki ne da zaki fada masa magana son ranki”!?.

Ta tsorota sosai Amman sai ta dake tace ” nayi din ina ruwanka da ni ne daga zuwa na zaka fara mani matsifa mtsss wuce wa tayi part din mommy.

Mutuwar tsaye yayi yana tunani kalar rainin da tayi masa cikin zafin rai yace” yasin Sai na dauki mataki akanki…………

🅿️1️⃣6️⃣%2️⃣0️⃣

*________________*🖊️

          Mutuwar tsaye yayi yana tunani kalar rainin da tayi masa cikin zafin rai yace “yasin Sai na dauki mataki akanki Zaunawa yayi saman kujera Amman ya kasa natsuwa Mik’ewa tsaye yayi ya fita daga cikin falon.

Khadeejah kuwa koda tashi cikin dakin bata ga mommy motsin ruwa tajiya shi ya tabbar mata da tana toilet Zaunawa saman bakin gado tayi tana tunani cikin ranta tace”o ni  khadee to  wai meyasa duk lokaci da nazo gurin mommy sai na hadu da wannan mugun mutum himm yasin ba zan dauki  wula’kanci ba,

Fitowa mommy tayi cikin toilet tana goge ruwan wanka sannan tayi ajiyar zuciya tace “Auta ta lafiya kikazo kikayi Zaune ke d’aya ina dan uwanki ne”!?.

Dagowa tayi tana kallon mommy wasu abubuwan suna mata yawo acikin zuciyar ta tace “ya fita ne.

Murmshin manya tayi tace “ko kin san bana son kuna fada ko”!?

Shiru shalele tayi saboda haushi yake bata bata ce komai ba Amman azuciyar ta tace “yasin duk abun da yayi mani sai na rama.

Shiru yayi yawa sai ta dafata tace “Auta ta lafiya Qlau kike kuwa”!?.

Murmshi tayi tace “lafiya Qlau mommy na ina tunani wani abu ne shiyasa.

Bata ce komai ba ta dauko turare ta feshe jikinta da shi tace “Amman daddyn ki yadawo ne”!?.

Kwanta saman gado tayi tace “A’a ina tunani sai wani sati zai dawo.

“Ok babu damuwa bari na barki kiyi bacci ko”!?.

Shalele tace “to mommy na” rufe idanuwanta tayi ahankali ahankali har bacci yayi gaba da ita.

Fitowa mommy tayi falon sai bata ga captain kb ba zama tayi saman kujera tace “to ko ina ya shiga ne oho” kallon tv take.

Captain kb ne Zaune bariki yana aiki Amman hankalin sa na ga tunani irin matakin da zai dauka  akan khadee shiru yayi sai ya cire wayar sa ya kira mommy lokacin kuwa tana lazumi ne ringing din wayar ta taji ya sai ta duba sunan my son ta gani dauka tayi tace “my son lafiya tunda zu baka dawo gida ba”!?.

Ajiyar zuciya yayi yace “ki kwantar da hankalin ki my love mom ina gurin aiki ne”.

Ajiyar zuciya tayi tace “sai yanzun hankalina ya kwanta fa to kadawo gida kaci abinci.

Yatsane fuska yayi sannan yace “abinci kuma ni fa bana cin kazantar yarinyar nan fa”.

Mamaki da al,jabi ya rufe ta tace “my son gidan ku wai kai yaushe zakayi hankali ne kanwar ka ce fa”.

Shiru na dan wani lokaci sannan yace “to shike nan my love mom zan dawo Amman zuwa anjima.

Murmshi tayi tace “yauwa dan albarka sai kazo.

Kashe wayar tayi tana mamakin irin halin su girgiza kanta ta cigaba lazumi lokacin sallah la,asar yayi tashi tayi ta shiga cikin dakin ta tashe da khadeejah sai ta sameta Zaune tana lazumi sallama tayi tace “au ashe ma har kintashi”!?.

Shafa addu,a tayi sannan tace “ai tunda zu na tashi daga bacci mommy”.

Murmshi tayi tace ” to shike nan babu damuwa dama zuwa nayi nagani ko kintashi baccin.

Murmshi tayi tace “na tashi tunda zu yauwa kuma Hajiya tace tana gaishe da ke zan koma gida yanzun saboda gobe muna da lechers insha Allah”.

Mommy bata ji dadin maganar ba taso ta kwana anan sai tace “haba dai Auta ta bazaki bar sai gobe ki tafi gida ba kin sani inason ki zauna atare da ni fa”.

Ita ma bata ji dadi ba tace “am sorry mommy na insha Allah zan dawo na kwana biyu atare da ke kinji ko”!?.

Ajiyar zuciya tayi sannan tace ” to Allah   ya kaimu lokacin lafiya.

“Amin ya Allah ina tunani ko zuwa jibi ko gobe zan dawo kinji kada ki damu dan Allah cewar khadeejah tana kallon ta”

Murmshi tayi tace “babu damuwa Allah ya kaimu yanzun tashi muje sai ki hada kayan marmari sai ki tafi da su ko”!?

Dariya shalele tayi tace “mommy na kenan ki bar su zan dawo na ci abu kawai.

Mik’ewa tsaye tayi sannan suka fito daga cikin dakin koda suka fito waje dai dai gurin motar ta ta tsaye sai ga Captain kb ya shigo cikin gidan lokaci mommy na tsaye tana magana da khadeejah parking yayi sannan ya fito hango khadeejah yayi tana kokarin shiga cikin motar ta daure fuska yayi kamar be taba dariya ba karaso gurin mommy yayi yace “my love mom lafiya kikayi tsaye nan gurin”!?.

Baki ta saki tana kallon sa sannan tace “my son baka ga kanwarka zata wuce gida ba “!?.

Yatsine fuska yayi yace “my love mom kin san  abubuwa sun mani yawa sosai ne shiyasa ban kula da ita ba”.

Jiyowa tayi suka hada ido ta watsa masa harara sannan tace ” Mommy na sai nadawo sannan tashiga cikin motar ta rufe mai gadi yazo ya bude mata fita tayi daga cikin gidan.

Bayan ta fita daga cikin gidan sai mommy ta jiyo tana kallon sa tace “my son wallahi abun da kukeyi bashi da kyau sosai fa dan Allah ku gyara zaman ku please.

Captain kb yace “o, o my love mom kin san halin yarinyar nan bata jin magana ne Amman zamu gyara insha Allah acikin zuciyar sa kuwa yace “sai na koya mata hankali kuwa afili kuwa sai yayi mata murmshi.

Mommy ta shiga gaba sannan ya tsaya wayar sa ce ya cire ya kira wani yace “kana jina yanzun nan ta fito daga  cikin gidan fa ku shirya.

Kamar suna gaban sa yace “to sir shirye muke.

Gudu take shararawa sai ta hango mutum kwan ce saman titi da sauri tayi parking tace “to wannan bawan Allah lafiya ko ya mutu ne”!? Waya dauko ta kira Hajiya ta fada mata sannan ta kashe wayar ta.

Fitowa tayi sai ta duba ko ina babu mutane  tace “ko lafiya babu mutanen  da zasu taimaka masa karaso gurin tayi tana kallon sa cikin tausayawa tace “sannu bawan Allah bari na kira doctor ta dauko waya kenan ta jiya sai ta gani mutane  sun zagayeta sai dariya mugunta suke mata tana kallon gabanta tayi sai taga mutum tsaye yana dariya gabanta yace rasss wani irin tsoro da tashin hankali sunka bayana a fuskar ta baki na rawa tace “dan Allah ku  su waye daga ina cikin tashin hankali take tambayar su”!?.

D’aya daga cikin su ya hada ido da yan uwan sa da sauri yazo ya shaka mata kokin sulalewa tayi kasa da gudu suka tura ta cikin mota suka gudu da ita.

Mommy na Zaunawa saman kujera taji gabanta yace rasss wani irin tashin hankali tazo mata da sauri tace “my son kira mani Auta ta yazon dan Allah please.

Kallon ta yake sannan yace “my love mom lafiya kike kuwa yanzun fa ta fita daga cikin gidan fa”.

Kai dan ubanka ka kira mani ita yasin akwai matsala sosai.

Hankalin sa ya tashi sosai be taba jin mommy ta zage sa ba sai yanzun wayar sa ya dauko yace “my love mom bani da number ta bani wayarki.

Da sauri ta mik’e masa ya kira ta yana jin tana ringing bata dauka ba kallon mommy yayi yace “bata dauka ba.

Mommy tace ” *innalillahi wa inna ilaihir raji un* dan Allah kira mani Hajiya yanzun.

Hajiya na Zaune Amman bata jin dadi ringing din wayar ta taji sai ta dauko ta duba sunan yaro na ta gani gaban ta na faduwa sai ta dauka  tace” Assalamu Alaikum yaro na ya kuke”!?.

Yace “Ummi na yarinyar nan tadawo gida ne”!?.

Jiki na rawa Hajiya tace ” A’a  bata dawo ba kuma ta kira tana tace ta hango wani mutum kwan ce saman titi daga nan bamu kara magana ba”.

Captain kb yace ” *innalillahi wa inna ilaihir raji un* sun sace ta wallahi.

Zaro idanuwan sukayi kamar Hajiya na gabansa sannan tace “anan sace ta kuma”!?.

Mommy tace “anan sace ta kuma sai ta fadi kasa some……….

*TOPA*

*ANA WATA GA WATA ANAN SACE KHADEEJAH KUMA CAPTAIN KB YACE GATANA TA FITO KUMA YAZO YACE ANAN SACE TA*🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔

*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

🅿️2️⃣1️⃣%2️⃣5️⃣

*________________*🖊️

           Mommy tace “anan sace ta kuma sai ta fadi kasa some hankalin Captain kb yayi dubun tashi sosai da gudu ya bude frejint ya dauko ruwa masu sanyi yazo gurin da mommy take kwan ce ya fesa mata bata tashi ba sai da ya kara sannan tayi ajiyar zuciya tace ” *innalillahi  wa inna ilaihir raji un*  Allah kana gani Allah kada kabari acutar da ita wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata.

Ajiyar zuciya yayi sannan yace “sannu my love mom bari nazo ko”?.

Daga masa kai tayi tana kuka bakin ciki fita yayi da sauri koda ya samu guri ya tsaya wayar sa ce ya cire ya kira yaron sa lokacin hankalin su atashe.

Dauka yayi yace “Am sorry Sir wallahi bamu sameta ba da,alamar sace ta akayi saboda ga dankunnanta akasa.

Dafe kansa yayi yace ” *innalillahi wa inna ilaihir raji un* to yanzun menene mafita kusan dole anemota ko yanzun ma haka my love mom tana cikin damuwa sosai fa.

Cikin tausayawa yace “insha Allah za, aganta ku cigaba da addu,a.

A bangaren khadeejah kuwa.

Yau kwana biyar da sace Khadeejah tunda aka sace ta har yanzun bata tashi daga bacci ba wani mutum ne ya shigo cikin dakin da ruwan sanyi dai dai inda take kwan ce ya watsa mata ruwan sanyi wata uwar firgita da tayi da sauri ta mik’e zaune jikinta sai rawa yake sannu ahankali ahankali ta bude baki tace “wai dan Allah menayi maku ne idan akwai abun da kuka bukata to ku fada mani takara she maganar cikin kuka da bakin ciki.

Wani mugun kallo ya bita da shi yace “ga abinci nan idan kina bukata kuma kada ki kuskura bakin ki ya furta fita daga cikin gidan.

Zaro idanuwanta tayi cikin tashin hankali kuka ta kara fashewa da shi ga wani kafurar yunwa da take ji.

Turo mata abinci yayi sannan ya fita daga cikin dakin kuka take mai ban tausaya sosai tana gani ya rufe dakin gaba d’aya.

A bangaren Hajiya kuwa.

Damuwa tayi mata yawa sosai har ciwon zuciya ya kamata a yau ne Alhaji muntaka wato Baban Khadeejah koda ya shigo cikin gidan sai yaji duk hankalin sa be kwana ba karasawa yayi gidan  koda ya shiga cikin falon sallama yayi tunda ya shigo cikin be ji motsin kowa ba hankalin sa be kwana ba da sauri ya kara sa cikin dakin  koda ya shiga ciki sai Hajiya ce  ya hango kwan ce da alamar bata da lafiya.

Da sauri ya karaso kusa da Hajiya yace ” Subhanalillah Hajiya lafiya meya ke damunki ne”!?.

Bude idanuwanta tayi tana kallon sa sai ta fashe da kuka sosai hankalin Alhaji yayi dubun tashi sosai yace ” Hajiya ko baki da lafiya ne”!?.

Runtsi idanuwanta tayi saboda kuka yaci karfinta girgiza kan sa yayi yace “Am sorry kiyi hakuri  ki fada mani abun da yake faruwa kinji “!?.

Ajiyar zuciya take ahankali ahankali sai da tayi shiru sannan ta bude baki tace “Alhaji an sace Shalelen ka”!?.

Wata zufa ce ta karke masa duk Ac da akwai Amman be hana zufa ta zubo masa ba yace “an sace ta kuma yaushe haka ya faru  bani da labari”!?.

Muryar ta na rawa tace “yau kwana biyar kenan nima ban sani ba sai da yaro na ya fada mani yanzun haka suna ahanyar zuwa gidan nan bata rufe baki ba.

Bakin su dauke da sallama shigowa cikin falon sukayi kowa yana cikin damuwa sosai part din Hajiya suka wuce ciki koda suka karaso Alhaji ne Zaune ya buga tagumi karasowa su mommy sukayi zaunawa kusa da Hajiya tayi shi kuma ya zauna saman kujera yace “Daddy barka da zuwa dafatan kadawo lafiya”!?.

Ajiyar zuciya yayi yace ” *innalillahi wa inna ilaihir raji un*  yanzun kai yaro na har yau babu labarinta ne”!?.

Cikin damuwar da su daddy sukayi yace “har yanzun dai daddy babu labarin ta Amman insha Allah za,aganta mu cigaba da addu,a.

Hankalin Alhaji yayi dubun tashi sosai yace ” to shike nan Allah ya baya muna ita.

Baki suka hada guri d’aya suka ce “Amin ya Allah.

Haka rayuwa ke tafiya gudu gudu sauri sauri yau Khadeejah watan ta biyu da sace ta su Hajiya sun bar ma Allah komai kullum cikin Addu,oi suke yau kwanan Captain kb biyar da koma wa America saboda Ana neman su da gagawa shiyasa ya koma Amman har yanzun ana neman Khadeejah sojoji kuwa ko ina an zuba su saboda nemanta.

A bangaren khadeejah kuwa.

Kwan ce take tana bacci ahankali ahankali ta fara bude idanuwanta koda ta bude su sai ta wani saurayi Zaune saman kujera ya daura kafa d’aya saman d’aya yana kallon ta yana murmshi.

Da sauri ta tashi Zaune tana kallon sa da mamaki sosai cikin ranta tace “kamar Suleiman”!?.

Bude baki tayi tana kallon sa tace “Suleiman dama kana raye”!?…………..

*GA ALKAWARIN KU*😂😂😂😂😂😂

*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*

🧑🏻‍✈️ *CAPTAIN KABEER* 🧑🏻‍✈️

🅿️2️⃣6️⃣%3️⃣0️⃣

*________________*🖊️

        Bude baki tayi tana kallon sa tace “Suleiman dama kana raye “!?.

Dariya yayi sosai sannan yace “kwari ma kuwa masoyiyata ai dama ban tunda ba ya zama za,ayi na mutu na bar masoyiyata ai bazai taba yuyuwaba ya karshe magana yana kallon ta.

Cikin da mamaki take kallon sa tace ”  kamar ya ban gane ba”!?.

Gyara zama yayi yace “ai bazaki gane ba tunda har yayanki ya wula’kanta ni saboda ke saboda da haka yanzun za,a daura maki Aure da ni shike nan  kuma”.

Cikin tashin hankali tace “dan girman Allah ka rufa mani asiri wallahi ban tashi Aure ba yanzun kaji ka fadi duk abun da kake so daddy na zai baka”.

‘Kwal,’kyale da dariya yayi sosai sannan yace ” au kin dauka zanyi rabuwa da ke ne to bari kiji akan ki zan iya kashe kowa saboda ke,  ke bar kiji ko mahaifina zanyi kashewa akan ki dan haka ki sanya ma zuciyar ki ruwan sanyi.

Kuka take sosai kamar ranta zai fita saboda tashin hankali har zazabi yaso ma rufe ta muryar ta na rawa tace “Suleiman dan Allah ka rufa mani asiri wallahi ba zan iya Auren ka ba”.

Cikin bacin rai ya mik’e tsaye yace “wallahi tallahi ko mutuwa zakiyi sai na Aure ki dogon tsaki yaji ya fita daga cikin dakin da karfin gaskiya ya rufe kofar dakin.

Kuka take sosai babu mai lallashin ta har jikinta ya fara rawar sanyi zazabi mai zafi ya rufe ta.

Captain kb ne Zaune office yana rubuce rubuce sako ne ya shigo cikin wayar sa duba yayi sabuwar number ce ya gani koda ya bude sai yaga _HIMM NA SANI DOLE KAYI MAMAKIN GANIN SAKO NA TO BA, A ABUN MAMAKI BANE NI NE NA DAUKE KHADEEJAH RABIN RAINA DAN HAKA ZAN AURE NAN DA SATI D’AYA IDAN HAR KA ISA TO KADA KATAR DA AUREN MU NI SULEIMAN BY_ tashi tsaye  yayi yana maimata sakon yace “lallai Suleiman kai dan iska ne da sauri ya kira daddy lokacin yana Zaune falo kusa da Hajiya ringing din wayar sa yaji daukowa yayi sai yaga yaro na  yace “yaro na ya aiki”!?.

“Alhamdulillah daddy yanzun dai abun da yake faruwa shine yaron nan da na kora wanda yake zuwa gurin ta Ashe shine ya dauke ta kuma yace zai Aure ta nan da sati d’aya to kaji sakon da ya turo mani yanzun haka ma”.

Cikin tashin hankali daddy yace ” *innalillahi wa inna ilaihir raji un*  yanzun dama shine ya sace ta Hajiya dake Zaune sai da ta zabura tana kallon sa ya cigaba cewa to yanzun menene mafita kasan dole sai an sanya sojoji ko”!?.

Kwari ma kuwa yanzun dai shine zan turo maka da number sannan zan turo ma yaro na da suke tsaron garin nan sai ayi bincike agano inda yake “.

Ajiyar zuciya yayi sannan yace “to Allah ya taimake mu ya bamu sa,ar kama sa”.

Amin ya Allah suka ce.

Kashe wayar sa yayi sannan ya kalle Hajiya da take kallon sa tace “ganta ne Alhaji “!?.

Gyara zama yayi sannan yace “yaron da ya sace Shalele na shine Suleiman din na da yake zuwa gurin ta”.

Zaro ido tayi tace “Suleiman kuma d’an dan Alhaji musa mai gidaje “!?.

Kwari ma kuwa dan haka ki cigaba da addu,a insha Allah sai naganta kinji ko”!?.

Ni fa shiyasa ban yarda da shi ba saboda daga gan sa bashi da tarbiya wallahi.

*A bangaren Captain kb kuwa*

Turo ma yaron sa number yayi sannan ya kirasa ya fada masa komai da komai cikin girmamawa yace “insha Allah zamuyi bakin kokarin mu.

Kashe wayar sa yayi yana murmshin gefen baki sannan ya zauna saman kujera ya daura kafa d’aya saman d’aya yana tunani irin wulakancin da zasuyi masa idan suka kama sa.

Bayan kwana biyu da faruwar haka bincike ake sosai har gidan su anji aturo wata dattijor mata ko za,a dace sai dai taji labarin yana kaduna hotel yana hutawa ana take ta kira su ta sanar dasu duk abun da yake faruwa.

*A bangaren khadeejah kuwa*.

Zaune take kamar kullum addu,a take Allah ya fitar da ita cikin wannan dakin bude kofar dakin akayi wani katun mutune ya shigo cikin fuskar sa babu fari,a kaya ne a hannu sa ya jifa mata yace “ki sanya wannan kayan saboda yau ne za,a daura maki Aure da oga kuma kada ki kuskura bakin ki furta bazaki saka ba.

sannan ya fita daga cikin dakin kuka ta kara fashewa da shi sosai haka ta dauki kayan tana kuka ta sanya su duk da tana cikin damuwa sosai be hana fito da kyauwanta ba daure gashinta tayi da ribos bayan ta kamalah sai tayi ta kama zagayar dakin tana addu,a gajiya tayi da yawa guri ta samu sai ta zauna bata fi mintina biyar ba da zaunawa kasa ba sai wani ya shigo cikin dakin fuskar sa rufe karasowa kusa da ita yayi da sauri ta mik’e tsaye tace ” bawan Allah lafiya”!? Tana zaro ido.

Bude mata fuskar sa yayi yace “Amma kiyi hakuri dan Allah nazo ne zan taimaka maki saboda kina bani tausaye yanzun ma haka babu wanda ya san halin da muke ciki”.

Captain kb ne hankalin sa ya tashi sosai kira waya yake yace “Dan Allah kuyi sauri yau za,a daura masu Aure fa.

Cikin girma mawa yace “Sir yanzun haka muna saman hanyar zuwa inda yake kuma ba a hotel yake ba yana cikin daji zamuyi kokari insha Allah.

Jin jina kansa yayi yace ” good ” sannan ya kashe wayar sa kiran daddy ne ya shigo cikin wayar sa da sauri ya dauka yace “daddy antashi lafiya”!?.

Alhamdulillah yanzun dai muna saman hanyar zuwa inda yake insha Allah ki cigaba da addu,a Allah ya sa mudace.

Amin ya Allah Allah ya taimake mu ya sa mudace.

Gudu suke shararawa saman titi Khadeejah kuwa ajiyar zuciya tayi tana goge hawayen da suke zubo mata sannan yace “ki natsu sosai ki biyo baya na sai na nuna maki hanyar fita daga gidan nan.

Murmshi tayi ta biyo bayan sa sai ya leka sannan yace “karaso haka suka cigaba da sauri sauri har Allah ya taimake su ya kawo bakin get sannan yace “to kanwata kada ki tsaya ko ina idan kika mik’e sosai akwai titi na sani Allah zai haka ki da nagari ya kaiki gida.

Murmshi tayi saboda farin ciki sosai tace “na……. go…. de….. Sosai Allah ya saka maka da alkhairi.

Amin yace sannan ya jiya ya koma cikin gidan.

Khadeejah kuwa gudu take sosai sai da tayi nisa sosai sannan ta zauna tana ajiyar zuciya tace ” Allah sarki Hajiya ta da mommy na da daddy na nasani kuna cikin tashin hankali kuka taci ta koshe sannan ta goge tace ” yau insha Allah sai gida.

Lokacin motocin sojoji sun shigo cikin daji da sauri suka fito cikin moton Alhaji kuwa yana nan Zaune yana kallon su  zagaye gidan suka sannan suka shiga cikin gidan halben bindiga suke sosai.

Hankali mutane gidan ya tashi sosai koda Suleiman ya bude daki sai yaga babu kowa aciki hankali sa yayi dubun tashi sosai kira mutane gidan yayi gashi hankalin su tashe ciki bacin rai yace “uban waye ya bude ma masoyiyata ta kofar dakin nan ta gudu.

Kowa sai cewa yake bashi bane  cikin tashin hankali kuka ya fashe da shi bindiga ya dauko yace “wallahi zan kashe kugaba d’ayan ku be rufe baki ba sai aka ta’ka masu bindigogi soja  d’aya shiga cikin dakin kayanta ya gani daukowa yayi yace”Sir ku dube kayanta.

Ogan su ya kalle sa yace “ina ka buye muna ita ka fito da ita kafin mu tafi da ku ya karshe magana cikin tsawa yana kallon sa “.

Kuka yake kamar wani karamin yaro yace “ta gudu wallahi.

Mik’ewa tsaye tayi ta cigaba da tafiya jiki babu kwari sosai haka cigaba tafiya bakin  titi ta hango da sauri ta kara gurin ta gaji sosai sai nishi take tafiya take har ta iso bakin titi zata tsalaka bakin titi dai dai wata babbar mota tazo wuce wa ta buge ta Khadeejah ta fadi kasa some kanta ya buge kasa sai jini yake zuba sosai………….

🅿️3️⃣1️⃣%3️⃣5️⃣

*________________*🖊️

         Mik’e wa tsaye tayi ta cigaba da tafiya jiki babu kwari sosai haka cigaba tafiya bakin titi ta hango da sauri ta kara gurin ta gaji sosai sai nishi take tafiya take har ta iso bakin titi zata tsalaka bakin titi dai dai wata babbar mota tazo wuce wa ta buge ta Khadeejah ta fadi kasa some kanta ya buge kasa sai jini yake zuba sosai..

Dai dai wannan lokacin Hajiya na Zaune taji gaban ta yace dumm dumm dumm jikinta ya soma rawa tace ” *innalillahi wa inna ilaihir raji un*  waya ta bude ta kira Alhaji lokacin hankalin su atashe kira ringing din wayar sa yaji daukowa yayi duba sai yaga sunan Mommyn Shalele da sauri ya dauka yace “Hajiya”.

Baki na rawa tace “Alhaji kun ganta ne”!?.

Ajiyar zuciya yayi sannan yace “Am sorry Hajiya bata gida yace ta gudu.

Kuka ta kara fashewa da shi tace “wallahi Alhaji jikina ya bani tana cikin matsala wallahi gabana faduwa kawai yake ta kara she maganar cikin kuka.

Cikin tausayawa yace ” A’a ki daina fadar haka insha Allah tana cikin koshin lafiya.

Wallahi Alhaji jikina ya bani akwai matsala kuka ta kara fashewa da shi.

Runtse idanuwan sa yayi yace ” *innalillahi wa inna ilaihir raji un*  Allah kayi muna maganin abun da bamu iya ma kanmu ya Allah kasa y’ata tana cikin koshin lafiya.

Kashe wayar yayi yace “inshaAllah za,aganta.

Hajiya kuwa kuka take sosai sannan ta tuna da mommy da sauri ta kira ta lokacin mommy na Zaune ta buga tagumi ringing din wayar ta taji sai ta duba sunan Hajiya taga cikin sauri ta dauka tace “Hajiya an ganta ne”!?.

Kuka take sosai muryar ta na rawa tace “Ba,a  ganta ba wai ta gudu ta kara she maganar cikin kuka.

*Innalillahi wa inna ilaihir raji un* to yanzun menene mafita  Hajiya”!?.

Wallahi ina ji ajikina tana cikin matsala sosai  wallahi mommyn KABEER.

Ajiyar zuciya tayi hawaye na zubo mata  tace “zamu cigaba da addu,a insha Allah za,aganta kuma wannan dan iska yaro wallahi sai my son ya masa hukunci sosai yanzun dai kin san baki da lafiya ko”!?.

Ajiyar zuciya take ahankali ahankali tace “Eh mana kuma zamu cigaba da addu,a shi kuma wallahi yarda ya sanya mu kuka shima haka uwayen sa zasuyi.

Hakane Allah ya bayana muna ita.

Amin ya Allah.

Da sauri drivern yaja burki parking yayi ya bude motar ya fito masha Allah dan saurayi  ne shima yar uwar sa ta fito cikin motar cikin tashin hankali d’aya ya aza hannuwa saman kai yace “na shiga ukku na  Ameera kashe yar India.

Kuka ta fashe da shi da sauri suka Kara sa gurin kwan ce take cikin jini sosai durkusawa tayi tana kallon ta tace “Yaya Taheer mu dauke muje da ita Asibity mana aduba muna ita.

Cikin kankana lokaci ya dauke ta ya rungume ƴar India cikin mota ya sanya ta sannan yace “Ameera ki shi muje Asibityn.

Da sauri ta mik’e tashiga cikin mota ai kuwa ya ba mota wuta gudu yake shararawa saman titi Allah dai ya kai su lafiya da sauri mai gadi ya bude masu sannan ya shigo cikin asibity parking yayi yana kokarin bude motar sai ga wasu nurse sunzo wuce da sauri Ameera fito daga cikin motar tace “dan girman Allah ku taimaka muna ga wata marar lafiya mun kawo.

Karaso gurin sukayi  da sauri sauri ya taimaka masu aka shiga da ita Emergency taimakon gagawa kayi mata Taheer da Ameera hankalin su tashe kallon sa tayi tace “gaskiya ya kamata mu fadawa Mami abun da yake faruwa.

Ciro wayar sa yayi ya kira Mami lokacin tana zaune palo tana karatun jarida ringing din wayar ta taji sai ta duba sunan Taheer ta gani cikin ranta tace “ko lafiya ko dai har sun dawo ne ” kiran ya katse kara shigo yayi karo na biyu sannan ta dauka tayi tace “har kun dawo ne”!?.

Cikin tashin hankali yace “Mami wallahi muna cikin tashin hankali wata yar India ce na buge ta da mota yanzun haka muna asibity ya kara she maganar cikin kuka.

Sakin jaridar hannunta tayi tana maimata *innalillahi wa inna ilaihir raji un* to  yanzun da sauki ko”!?.

Zayayi magana sai ga doctor ya fito daga emergency ameera tace “doctor ya jikinta”!?.

Cire glass din sa yayi yace “Am sorry  gaskiya ta samu matsala saboda kanta ya bugu kasa koda ta tashi bazata gane yan uwanta ba sai ta dauki dan wani lokaci kafin ta dawo normal.

Zaro idanuwan sukayi yace “doctor yanzun kana nufin tayi losing din memory ta”!?.

Kwari ma kuwa sai yanzun bacci take saboda nayi mata allurar bacci zaku iya shiga cikin dakin   ku ganta Amma ban da hayaniya please ya karashe magana yana tafiya.

Mami kuwa duk abun da aka fada acikin kunnuwanta tace ” Allah sarki yar mutane Allah ya baki lafiya zamu cigaba da kulawa da ke insha Allah.

Koda suka shiga cikin dakin kwan ce tana bacci alamar tana jin ciwo ajikinta zaunawa kusa da ita Ameera tayi tana kallon ta tace “Yaya Taheer kaje gida sai ka gyara sannan kazo da Mami saboda hankalin ta ya kwanta.

Ajiyar zuciya yayi sannan yace “insha Allah bar naje gida daga nan zamu muyo mata shopping.

“Yauwa na sani Mami ya tayo muna abinci kuma akwai nama na da na,aje sa kazo mani da shi dan Allah tana kallon sa.

Jiyowa yayi yace “insha Allah sai nadawo sannan ya fita daga cikin dakin….

Kallon ta take sosai tace “ikon Allah dama India wa na zuwa Nigeria Allah mai iko.

*A bangaren captain kb kuwa*

Duk abun da yake faruwa yaron sa ya fada masa komai da komai yace “wallahi tallahi ko mutuwa zai yi to sai dai ya mutu Amma maganar hakuri  babu ta  inaso kazo mani da shi  america yau yau dina bana so ku bata mani lokaci .

Cikin gamsuwa yace “ok Sir insha Allah yau yau zamu shigo da shi.

Kashe wayar yayi yace “baka san waye Captain kb ba Amma yau zaka gane waye ni lelo yake saman kujera ya daura kafa d’aya saman d’aya.

*A bangaren khadeejah kuwa*.

Taheer ne da Mami cikin mota tafiya suke sosai shopping sukayi  sannan suka dawo asibity parking yayi yana kallon Mami.

Budewa tayi tace “muje mana kayi Zaune.

Fitowa yayi daga cikin motar kullon abinci ne ya dauko dai dai kofar dakin yayi tsaye yace “gashi nan Mami bar na amsa waya.

Amsar abincin tayi tace “to shike nan babu damuwa shiga cikin dakin tayi har yanzun bata falka ba daga bacci ba Zaune ta same Ameera tayi tagumi sallamar Mami tajiya.

Amsa sallama tayi tace “Sannu da zuwa Mami bar na baki guri ki zauna.

Kallon yarinyar take sosai tana jin son yarinyar har cikin ranta tace “Allah sarki yarinyar kykkyyawa ce Allah ya baki lafiya zamu cigaba da kulawa da ke.

Zaunawa saman kujera tayi karfe 4:00pm  ta fara bude idanuwanta kallon dakin take sosai Ameera ce ta da ke Zaune ta lura da tashin ta da sauri tace “Mami ta bude idanuwanta.

Mami tace “sannu baiwar Allah ya jikin naki”!?.

Da sauri ta mik’e zaune jikinta sai rawa yake sosai tana zaro ido direwa tayi saman gado tana girgiza kan ta tana kuka  bude kofar dakin akayi Taheer ne ya shigo cikin dakin da sallama.

Dagowa tayi tana kallon sa da gudu taje ta rungume sa tana kuka sosai.

Zaro idanuwan sukayi yace “Mami lafiya dai”!?.

Kallon kallo suke tace “ta tsorota ne shiyasa tana ta tashi daga bacci.

Rike sa tayi sosai tana kuka hankali sa yayi dubun tashi sosai yace ” menene”!?.

Nuna masa take su Mami da ke tsaye  kallon su,  su Mami suke da ita da Ameera Mami ta fahimci wannan abu tace “tana tsoron mu ne kai ne zaka nuna mata abubuwa saboda yanzun kai ne ta sani tana karashe maganar tana kallon ta cikin tausayawa.

Rike mata hannu yayi yace “insha Allah  Mami zo mu Zauna yana nuna mata wuri zama.

Rike take da shi sosai kada ya gudu ya barta  zaunar da ita yayi saman gado yayi sannan shi ma ya zauna saman kujera.

Dariya Ameera ta kwal, ‘kyale da ita  sosai tace ” Yaya Taheer yanzun ka zama mai raino hhhh.

Kallon ta yayi da alamar tambaya.

Tace “Yaya Taheer ko da gurin aiki zakaje to tare zakuje kuwa.

Mami tace “kwari ma kuwa kullum sai ka nuna mata abubuwa..

Kallon ta yana murmshi yace “insha Allah Allah ya bamu ladar taimako …

Amin ya Allah suka ce.

Kallon su take Amma bata gane komai ba gashi tana jin yunwa tace “ni dai wallahy yunwa nake ji..

Zaro ido sukayi da mamaki da al,jabi Ameera tace “kai ke  dama ba  haushiya ce……..

*TO MASOYAN CAPTAIN KABEER GASHI NAN DAI ALLAH YA BANI IKON NAYI MAKU POSTING YAU DA MASU KIRA NA DA MASU MANI MAGANA TA PC NAGODE SOSAI DA SOYAYYAR DA KUKE MANI*😘😘😘😘😘😘😘💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA DAK KASASHIN WAJE WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

🅿️3️⃣6️⃣%4️⃣0️⃣

*_________________*🖊️

         Zaro ido sukayi da mamaki da al,jabi Ameera tace “kai ke dama ba haushiya ce”!? 🤔

Kallon su tayi sai ta fashe da kuka sosai jikinta har rawa yake saboda yunwa da sauri yace “to ya isa zaki ci abinci ko”!?.

Share hawayen da suka zubo mata tayi tace “ai tunda zu nake jin yunwa”.

Ayyah sorry sister kinji ko”!? Cewar Ameera da ke Zaune kusa da Mami.

Abinci ya zuba mata cikin pelta kallon ta yayi sannan yace “Alhamdulillah gashi nan har sai kin koshi.

Amsa tayi jikinta har rawa yake hannu baka hannu akushi har sai da ta kusan cinye wa sannan ta turo masa pelta tace “na koshi yanzun.

Cikin jin dadi Mami tace “to Alhamdulillah yanzun dai babu abun da yake damunki?.

Kallon Mami tayi tana magana mai makun tayi magana sai ta shareta tana kwan ce saman kafadar Taheer shi kuma latsar waya yake doctor ne ya shigo cikin dakin kallon su yayi sannan yace “Alhamdulillah yanzun bata da wata matsalar komai dai to masha Allah meka masa takarda yayi yace “wannan ta sallamar tane sai maganin da zaku siya mata kullum ta sha Allah ya bata lafiya.

Amin amin suka ce hada kayan sanyawa su sukayi sannan Ameera  tace “to muje ko Yaya Taheer.

Mik’ewa sukayi sannan suka fita daga cikin dakin hannun sa rike da hannun khadeejah tafiya suke dai dai motar sa suka tsaya bude kofar motar tayi tace “Yaya Taheer ka bude mata ta zauna gaba.

Daga kan sa yayi ya turo wayar sa cikin aljihu sannan ya bude mata yace “to shiga ciki ki zauna ko”.

Kallon sa tayi tace ” A nan zan zauna”!?.

“Eh mana”

Shiga cikin motar tayi sannan shima ya zagaya ya shiga ciki su Mami kuwa dama sun dade da shiga cikin motar fita yayi daga cikin Asibity gudu yake shararawa har ya iso bakin get din gidan su masha Allah gidan irin masu hali ne babu karya ya hadu sosai.

Horn yayi wa mai gadi da gudu yazo ya bude masa get shigo cikin gidan yayi cikin gareji yayi parking sannan suka fito daga cikin motar cikin gidan suka shiga acikin palon kuwa zazaunawa saman kujera sukayi ya Zauna saman kujera d’aya kusa da shi ta zauna ta rike sa sosai.

Dariya Ameera kayi kasa kasa tace “Yaya Taheer kana da aiki gabanka yasin kuwa”.

Yace “to ya zanyi dole na rike ta Amma insha Allah zan rika nuna mata abubuwa.

Mami tayi murmshi tace “wannan gaskiya ne yauwa ka kira Amina kuwa”!?.

Shiru yayi sannan yace “A’a Mami inaso sai zani gida sai na fada mata saboda kin san bakin kishi gareta wallahi.

Cikin tausayawa tace “hakane gaskiya Allah dai ya rabaku lafiya.

Ameera tace “Himm ai wallahi kishi har na hauka take da shi kai ni dai ba yar uwar sa ba to bata yarda mace ta rabe sa ba Allah dai ya kyauta.

_*Asalin labarin*_

Alhaji muntaka shine Babba sai  Mommy ita ce Auta adakin su da Alhaji buzu da Hajiya dakin su guda Auren zumunci akayi masu Alhaji muntaka ya Auri Hajiya shi kuma Alhaji buzu ya Auri mommy rana d’aya akayi bikin su kwana atashi babu wuya gurin Allah ya shekara goma da Auran su Mommy ce ta haifi shin talelen jariri yaro ranar suna ya ci sunan sa KABEER haka suka cigaba da rainon kb har ya kai shekara tara ciwo ciki yayi sanadin rasuwar sa kowa ya shiga cikin damuwa da tashin hankali suka shiga  bayan rasuwar mahaifin Kabeer  sannan aka haife jaririya fara ce sosai Allah yayi mata kyau sosai ranar sunan yarinyar taci Sunan KHADEEJAH haka suka cigaba da raino.

Har wani shekaru goma kb yana karatu kasar India.

Khadee kuwa tana kusa da gida lokacin ta kara girma haka ita ma aka sanya ta school sosai take karatu.

Bayan wasu Shekaru abubuwa sun faru har da shiga Aikin soja da kb yayi cikin ikon Allah samu CAPTAIN KABEER gida kuwa suna cikin farin ciki sosai komai yana tafiya dai dai.

Khadeejah kuwa ta grima dan yanzun shekarar ta goma sha biyar aduniya  har ta gama second school yanzun tajona jami,a ta tafi gurin Shopping ta shiga cikin shagon turaren wuta turaren jiki da coconut milk siyaya mai yawa tayi tazo acire kudi sai akace “hello sauraniyar ta dafata dai kina lafiya”?  Da sauri najiyo ina kallon sa murmshi yayi yace “yes ni dai Sunan SULEIMAN ni  ka d’aya ne ga mahaifina kuma bani da mommy dan ta dade da mutuwa kuma muna da dukiya sosai  so dafatan zaki soni”!?.

Baki na saki ina kallon sa ya bani da dariya sosai dai na share kawai nace “am sorry ni bana kowa number bale kai daga zuwanka”.

Da sauri yace “haba dai beauty kada kiyi mun haka mana ok to nawa zan baki ki bani number ki”!?.

Khadee tace “bana bukatar Namiji kusa da ni tana fadar haka da sauri ta fita daga cikin shagon motar ta shiga ta rufe da sauri tabar gurin.

Biyar ta yayi daga baya dai dai get din gidan su yayi parking  kallon sa yace “yes na gano gidan nan ai kuwa kullum sai nazo gidan gurinki kuwa tafiyar sa yayi lokacin.

kullum sai Suleiman yazo gurin ta tun bata fitowa har takai tana fitowa tana fada da shi saboda haushi yake bata ranar ta zaune sai kiran Mommy ya shigo wayar ta dauko tayi ta dauka tace “Assalamu Alaikum barka mu da yamma mommy na “.

Cikin jin dadi mommy tace ” Amin wa,Alaikum sallama barka dai Auta ta yaushe, zaki shigo ne”!?.

Dama inason zuwa nayi sati biyu gurinki bari na gyara yanzun zan shigo insha Allah.

To shike nan babu damuwa Allah ya kawo ki lafiya cewar mommy.

Amin amin kashe wayar tayi da gudu ta shiga cikin dakin Hajiya lokaci Zaune take tana kallon da sallama ta shigo cikin dakin.

Amsa mata sallama tayi tace “au  ashe ma har kintashi”!?.

Yatsine fuska tayi sannan tace “Eh wallahi Hajiya ina son gudu yau hijira zanyi”.

Kallon ta take tace “uhm to shike nan babu damuwa yau zaki guje mu kenan ko”!?.

Murmshi tayi tace”laaaa ba haka bane Hajiya  sai nadawo da gudu ta fita daga cikin dakin.

Koda ta shigo cikin falon mommy lokacin tana cin naman kaza da hollandia yoghurt da sallama ta shigo.

Dagowa mommy tayi cikin farin ciki tace “A’a Ashe da gaske Auta ta take to shike nan karaso gurin ki ci ragin Mommyn ki”.

Murmshi tayi tace “sannu da hutawa mommy na dama kwana biyu kullum sai nayi mafarkin ki wallahi zaunawa tayi kusa da mommy.

Ayyah to gani Auta dafatan dai Hajiya tana lafiya da Yaya na”!?.

Lafiya Qlau cewar khadeejah.

A yau ne *CAPTAIN KABEER* zai dawo Nigeria gyara gyaran gida ake khadeejah kuwa ko da ta fito cikin dakin sai ta hango mommy zaune ta ci kwaliya kamar ba ita ba kamshin turaren ta ne ya game falon shine ya tabbar mata da cewar Auta ta ta fito   lokaci waya take da kawayen ta tana cewa “haba dai best yanzun dai yaushe zaki shigo ne”!?.

Karaso gurin tayi tana kallon mommy tace “best zamuyi magana anjima insha Allah.

“Good morning mommy na”.

Mommy tayi murmshi tace “my Auta morning kin tashi lafiya”!?.

Khadeejah tace “Alhamdulillah naga sai gyaran gida ake yi lafiya”!?.

Murmshi tayi tace “Yayanki zai dawo Nigeria yau din nan insha Allah.

Gabanta yace rasss wani fargaba ya shigeta gabanta  yace dumm dumm jikinta ya soma rawa tace “yau kuma mommy na “!?.

Kallon ta mommy tayi tace “Auta ta lafiya kike kuwa”!?.

Waskewa tayi tace “lafiya Qlau mommy na ina tunani wani abu ne shiyasa.

Mommy dai tace “Himm to Allah ya sa zatayi magana kenan sai kira Waya ya shigo lokacin mommy ta duba sunan my son ta gani dauka tayi tace “missyou my son.

Captain kb yace “miss you my love mom dafatan kina lafiya”?.

Lafiya Qlau har kun iso kenan ko”!? cewar mommy.

dariya  yayi  yace “Eh wallahi gani nan cin mota ne ok mommy mun iso bakin get.

Kashe wayar tayi tace “tashi muje Yayan ki ya iso.

Mik’ewa mukayi jikinta babu kwari haka suka fito waje motoci suka shigo cikin gidan dai dai inda mommy take tsaye sukayi parking.

Kusan mintina 30 sannan ya fito daga cikin motar kallon gidan yayi sannan karaso gurin mommy yace “miss you my love mom.

Bude masa hannunwa tayi tace “missyou my son rungume sa tayi cikin jin dadi sosai.

Hada ido yayi da Khadeejah ta watsa masa harara sannan tayi magana kasa kasa  tace ” dube sa dan Allah sai kace karamin yaro mtss.

Sakin mommy yayi yace “my love mom wannan yarinyar fa yana mata mugun kallo.

Juyawa tayi tace “Au kanwarka ce fa Auta ta ce har kamanta da ita ne”!?.

Dafe kansa yayi yace “ok ke baki iya gaisuwa bane”!?.

Wuce cikin gidan mommy tayi tana murmshi jin dadi yau d’anta yadawo gida.

Dariya tayi masa sosai sannan ta daure fuska tace “ban iya ba gaisuwa ni ko mutum ban gani ba bale na gaishe da shi .

Karasowa gurin yayi dai dai numfashin sa yana tafiya tare da nata yace “yaushe kika iya rashin kunya ne”!?.

Jikinta yaso ma rawa tace “mallam meye haka wai kake nufi ne”!?.

Karasowa yayi kamar zai rungume ta yace “abun da kike nufe shi ne ke damunki ne?  arayuwa dole ki bani girma na fa.

Jikinta har rawa yake sosai tace “ni dai babu abun da nake nufi ka bani guri na ce”.

Murmshin gefen bakin sa yayi yace ” kada ki kuskura na ganki da wani mutum ko saurayi dan baki isa Aure ba saboda ban tashi maki Aure ba yanzun  sannan yayi gaba abun sa.

Baki saki tana kallon sa hawayen bakin ciki suka zubo mata da sauri ta goge hawayen koda ta dago sojoji ne tsaye cikin gidan da sauri ta wuce cikin gidan.

Daki tashige ta rufe ta fashe da kuka sosai kamar ranta zai fita.

Bayan ya shiga cikin dakin sa wanka yayi sannan ya fito ya sanya farar jalabiya sannan ya fito falo Zaune ya hango mommy Amma bega khadeejah ba tabe baki yayi ya karaso gurin mommy ya Zauna saman kujera yace “washii na gaji sosai wallahi.

Cikin kulawa tace ” ai dole yanzun dai kaci abinci.

Ajiyar zuciya yayi sannan yace “ina wannan yarinyar tazo ta zuba mani abinci.

Kallon sa mommy tayi sannan kwala mata kira tayi  tace “Auta ta kizo ina falo.

Khadeejah kuwa tana daki taci kuka sosai har ta koshi toilet tashiga ta wanke fuskar ta sannan ta fito kiran mommy ne ya shigo cikin waya bata dauka ba sai dai ta fito falo hango shi tayi Zaune yana latsar wayar sa karaso gurin tayi tana kallon mommy tace “gani mommy na

Mommy tace “yauwa Auta ta ki zuba ma Yayan ki abinci ina zuwa tashi tayi ta wuce cikin dakin.

Jitayi kamar takama dukan sa saboda bakin ciki da takaici kamar ta hade zuciyar ta ta mutu saboda haushi.

Pelta ta dauko ta cika masa abinci sannan ta ajiye gaban sa ta mike tsaye zata wuce sai taji muryar sa yace “ke gidanku haka ake ba mutum abinci halama nayi maki kada da irin ki ne”!?.

Kallon ta jifa masa tace ” ai ga alamome nan nagani tunda baka da hannuwa da zaka ci abinci.

Kallon ta yayi yace “ke wasa nake da ke ne  to maza ki dauke abinci nan ki cinye sa.

Murguda masa baki tayi tace “sannu sarkin huta  to ba zan ci ba ko nayi maka kama da mai jin yunwa ne”.

Wata irin tsawa ya daka mata idanuwan sa sukayi jajaru yace “zo nan”.

Jikinta yaso ma rawa tace “Allah sai dai ka kashe ni Amma bazan zo ba.

Mik’ewa tsaye yayi da gudu khadeejah ta shige daki ta rufe tana ajiyar zuciya tana mamakin irin halin na.

Shi kuma mamakin rashin kunyar ta yake dogon tsaki yaji.

Wata rana Captain kb yazo gaida Hajiya sai yaga mutum tsaye bakin get parking yayi sannan ya fito yana kallon sa yace “kai daga ina”!?.

Washe baki Suleiman yayi yace “nazo gurin matar da zan Aura”..

Tsawa ya daka masa yace “Babu wata matar ka anan daga yau duk sannan na kara ganinka sai na karya maka kafafuwa kaji ko”?.

Cikin rawa jiki yace “dan Allah kayi hakuri wallahi ba zan iya rayuwa babu  ita ba.

Kiran sojoji yayi yace “kun ga wannan dan iskan yaro duk ranan da yakara zuwa gidan ko sai nayi maganinku afusace ya shigo cikin gidan..

Yace “wallahi sai na dauki fansa.

*Dawowa labari*

*A bangaren Captain kabeer kuwa*

Zaune yake yana aiki ga laptop turo kofar office din kayi be dago idanuwansa ba ya cigaba da aikin sa.

Sir gashi tare muke da shi cewar wani soja.

Kashe laptop din sa yayi sannan ya mik’e tsaye ya fito waje sojan yana biye da shi.

Durkushi yake kasa yana kuka sosai har da majina idanuwan sa sunyi kumburi sosai.

Kallo d’aya yayi masa ya dauke idanuwan sa gurin yace “ku kai sa gidan horo.

Dagowa yayi ya kalli fuskar Captain kb babu rahama yace “dan  Allah oga kayi hakuri wallahi ba zan kara ba dauke ta ba.

Ko inda yake be kalla ba juyawa yayi ya koma cikin office  haka suka dauke sa suka tafi da shi gidan maza………….

*To masoyan CAPTAIN KABEER gashi nazo nayi maku posting din asha karatu lfy*
😁😁😁😁😁😁

🅿️4️⃣1️⃣%4️⃣5️⃣

*_________________*🖊️

         Ko inda yake be kalla ba juyawa yayi ya koma cikin office ya cigaba da aikin sa haka suka dauke sa suka tafi da shi gidan maza.

Kuka yake yana magiya Amma basu saurara masa ba cikin gidan suka shiga da shi mutane ya gani kamar bayi aikin wahala kawai suke babu Wanda ya damu da su can gefen wani ya hango an dukan sa kamar jaki hankalin sa ya tashi sosai yace ” dan Allah ku taimake ni zanyi fitsari”!?.

Wani katun soja ne yazo da bulalar sa katuwa yace “oga aiki zayayi ne”!?.

Sojan yace “eh shine wanda ya sace kanwar Sir”.

Zaro ido sukayi da mamaki da al,jabi katun sojan yace “kutttt kace nama ne gasashi ai kuwa zaka ci ubanka zamu koya masa hankali.

Jikin sa ya soma rawa yace “kuyi hakuri wallahi shairin shed’an ne”!?.

Sojan yace “yanzun sai shed’an ya taimake ka tunda da sani nai ku wuce da shi kawai “sannan ya juya ya fita daga cikin gidan mazan.

Watsa masa dorinar yayi sai da ya fadi kasa some ruwa masu sanyi ya watsa masa ajiyar zuciya Suleiman yayi yace “Ashe mafarki ne nake”.

Can yaji ance ba mafarki ne kake ba fa.

Zaro ido yayi shi har ga Allah ya dauka mafarki ne yake kuka yake jikin sa na rawa yace “dan girman Allah oga kayi hakuri bazan kara ba.

Kara watsa masa yayi sai da yasaki firsari a wandon sa da gudu ya shiga cikin gurin dai dai gurin dutsi yayi tsaye yana kuka har da majina yaji an ce “kalle wannan dutsin kagan shi ko”!?

Daga kai yayi yace “eh na gashi”.

Dariya yayi sosai sannan yace “shi ne zakayi aiki gurin inaso ka fasa mani shi gaba d’aya da kagama shike nan ka gama da wannan aikin.

Shiru yayi cikin ransa yace “yanzun shike nan nazama dan wahala sanadin Khadeejah gashi ban iya aiki ba kuma gashi an ce da nagama wannan shike nan afili kuwa yace “yanzun da nagama wannan shike nan gida zan koma”!?.

Daure fuskar sa yayi yace “yaushe nayi da kai haka to aiki yanzun ka sanya hannu kuma kana murnar zuwa gida salon kacigaba da iskan ci ko to ba yanzun ba wuce ka cigaba da aiki yaro.

Kuka yake sosai idanuwan sa har sunyi kumburi haka ya karasa gurin jikinsa babu kwari sosai guduma ya dauka kamar ya fadi saboda nauyi.

Captain kb kuwa Zaune yake yana kallon su duk abun da suke yana gani murmshin gefen bakin sa yayi yace “Am sorry yaro ka shigo hannu” video ya turo ma su mommy da daddy.

*A bangaren su Mommy kuwa*

Zaune take sai taji wani sako ya shigo cikin wayar ta taji sai ta duba sunan my son tagani video ne tagani tana budewa wahalar da Suleiman yake sha ita tagani dariya mommy tayi tace “wannan shine dai da kai kiran daddy ya shigo cikin wayar ta dauka tayi tace “Yayana kaga abun da ya dace da shi ko”!?.

Gyara zama yayi sannan yace “wallahi kuwa abun yayi kyau sosai ai Hajiya tana kallon sai tayi dariya tace “Allah ya kara masa.

Labari suka cigaba da yi abubuwa suka mata ayi masa sannan sukayi sallama.

Hajiya kuwa share hawayen ta tayi tace “Allah sarki y’ata ko tana cikin wane hali Allah ne masa Allah ya sa tana cikin koshin lafiya.

Kwantawa tayi saman gado sai bacci yayi gaba da ita.

Koda daddy ya shigo bacci ya sameta tana yi cikin tausayawa yace “insha Allah y’ar ki zatadawo maki nada badadewa ba in Allah ya yarda” sannan ya fita daga cikin daki.

*A bangaren khadeejah kuwa*

Yanzun ta fara sakin jikinta da su Mami yau ma kamar kullum Zaune take tana kallon tv da sallama Taheer ya shigo cikin falon Ameera ce sai Khadeejah kallon sa Ameera tayi tace “Yaya Taheer ina kwana”.

Kallon ta yayi yace “Ashe kuna cikin falon lafiya klau ina Mami”!?.

Tana ciki bari nakira ta cewar Ameera.

Zaunewa yayi Saman kujera ya daura kansa yace ” yar India yau babu magana”!?.

Turo baki tayi tace “to ba tunda kashigo nake maka sannu da da zuwa Amma ko kallona bakayi ba.

Tashi Zaune yayi yana kallon ta yace “haba dai kanwata kodai kinyo fada da Auntyn ki ne”!?.

Muryar Ameera yajiya tace”himm waye zai kara zuwa gidan ka ai wallahi mu da gidan ka ko ba yanzun ba.

Kallon su yake sosai lokacin Mami ta shigo cikin falon tace “A’a  Taheer yanzun ka shigo tana kokarin zaunawa kusa da ita.

Yace “eh wallahi wai me yake faruwa ne kanwata fushi take da ni”!?.

Tabe baki Mami tayi sannan tace “matar ka bata fada maka wani abu ba ne”!?.

Girgiza mata kai yayi yace “eh babu abun da ta fada mani kawai dai na sameta tana ta bakar masifa Amma ban tambaye ta ba.

Himm wai meya sa Amina bata da hankali ne su Ameera ne suka je gidan ka zagi kala kala take ma baiwar Allah nan wai wallahi sai ta kashe ta duk sannan ta ganku tare da ita.

Dafe goshin sa yayi sosai sannan yace ” *innalillahi wa inna ilaihir raji un* wai yaushe zata rage haukar kishi ne haukar ta zata hanani nayi Aure ko yayi wallahi Mami da ina da wata budurwa da sai na Aure ta nagaji da haukar Amina wallahi.

Cikin kulawa Mami tace “hakane Allah ya baka ta gari ko nima inaso naga jikoki na wallahi.

Ameera tace “ga yar India nan aka Aure ta.

Da sauri Mami tace “A’a kada ayi haka saboda baku sani ba ko tana da Aure sannan ke Ameera kada ki sake wannan maganar dan Allah.

Ajiyar zuciya Taheer yayi yace “wallahi kuwa nima abun da nake tunani kullum sai nayi tunani ko tana da Aure gashi inason sosai har cikin raina.

Kallon su Khadeejah take Amma bata gane komai ba tace “wai lafiya kuke kuwa naga kun shiga cikin damuwa ne”!?.

Kallon soyaya yake aika mata da shi da sauri ta dauke idanuwanta gurin.

Mami tace “wallahi kuwa Yayan ki ne yana cikin matsala sosai saboda matar sa bata barin sa  yayi Aure ko budurwa bata yarda ta rabesa ba.

Khadeejah tace “to Allah ya sauwaka Allah ya shige masa gaba.

Gaba d’aya suka ce” Amin ya Allah.

*A bangaren Daddy kuwa*

Mommy da Hajiya Zaune gurin d’aya gyara zama daddy yayi yace “to Alhamdulillah yanzun ke Hajiya ina mai baki hakuri akan abun da zan yanke.

Kallon sa suka kowa yana son yaji abun da zai fada.

Hajiya ta kalle mommy tace “Alhaji kayi magana mana ka sanya mu cikin duhu fa ko ba gaskiya ba”!?.

Mommy tace “wannan gaskiya ne Yaya kayi muna bayani.

Gyara murya yayi yace “Abu na farko shine mu dauke wannan abun amatsayin kadara.

Jin jina kai sukayi suka ce “wannan haka yake.

“Sannan kun ga yanzun bamu san inda Shalele take ba Amma ina tunani tana cikin koshin lafiya.

“Hakane insha Allah muna tunani haka”.

Jin jina kai yayi yace “masha Allah abu na gaba shine inaso na hada Shalele da yarona Auren Zumunci kamar yarda akayi muna inda tadawo sai afada mata nasani zasu muna biyaya insha Allah.

Wasu hawayen farin ciki ne suka zubo masu mommy da Hajiya da sauri mommy tace “Allahu akbar yanzun dai  ka nufin da Auta ta da my son zasuyi Aure kenan.

“Kwari ma kuwa cewar daddy.

Share hawayen ta Hajiya tayi tace “to kuna gani zasu amince kuwa saboda nagani basu shan inuwa d’aya”!?.

Mommy tace “nima dai abun da nake tunani kenan kullum ciki fada kamar kaji”.

Daddy yace “zasu shirya ai saboda babu wanda zai kalle su insha Allah sai munyi alfahari da wannan Aure.

Hajiya tace “to yanzun menene mafita”!?.

Daddy yace “cikin wannan watanin za,ayi Aure saboda da haka kada ku fadawa kowa sai biki na sauran kwana biyu ko d’aya.

Wani irin farin ciki sosai ya mamaye zuciyar su mommy da Hajiya………

*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE

*COMMENT AND SHAR*

🅿️4️⃣6️⃣%5️⃣0️⃣

*_________________*🖊️

         Wani irin farin ciki sosai ya mamaye zuciyar su mommy da Hajiya mommy kuwa tace “to Alhamdulillah gaskiya naji dadi wannan hadin yayi sosai.

Daddy yace “to yanzun shike nan sai ku fara shirye shirye zuwa wani sati inaso ku kamala shirye shirye kayan lefe ba sai anyi ba.

Zaro ido mommy tayi tace “A’a gaskiya dole sai nayi mata ba dangarci Yaya Auta ta tawa haba daidan Allah .

Dariya Hajiya tayi tace “to  shike nan kasan y’ar ta ce shiyasa take son ayi mata yanzun dai shike nan Allah ya shige muna gaba.

Amin ya Allah suka ce”

*A bangaren khadeejah kuwa*

Yanzun komai yana tafiya lafiya klau alhamdulillah Mami kuwa Zaune take falo tana kallon tv da sallama Taheer ne ya shigo hannun sa rike da leda mai zane.

        Amsa sallama tayi tace “A’a Taheer  shigowa dare kake”!?.

Karasowa kusa da ita yayi yace “ina wuni Mami wallahi kuwa wai shopping nayi wa kanwata.

Murmshi tayi tace “Allah sarki gaskiya ka kyauta sosai Allah shiye albarka.

Amin ya Allah shiru yayi na dan wani lokaci sannan yace “wai suna ina ne”!?.

Kallon sa tayi ta fahimci wannan abun sai tace “suna daki yanzun ina ganin ko bacci suke ko labari.

Mikewa yayi yace “gashi nan Mami idan sun tashi zan wuce gida sai da safe”.

Allah ya bamu alkhairi.

Fita yayi daga cikin falon acikin zuciyar sa duk be ji dadi ba saboda beyi tozali da kykkyyawa fuskar ta ba dai dai gurin mota yayi tsaye waya ya ciro ya kira Ameera lokacin Zaune suke suna labari abubuwa na rayuwa.

Ringing din wayar ta taji sai ta duba sunan Yaya Taheer ta gani murmshi tayi tace “A’a Yaya Taheer bakayi bacci ba”!?.

Cikin kulawa yace “wallahi kuwa na kasa yanzun na fita daga cikin gidan fa gashi ban ganta ba.

Dariya sosai sannan tace “matar ka  fa tana gida baka gudun tazo da wuka tace zata kashe ku”!?.

Dogon tsaki yaja yace “ni dai yanzun ki bar wannan maganar ina gimbiya ta”!?.

Khadeejah kuwa kwan ce take ta lumshi idanuwan ta tana jin su wani irin haushin sa take ji Amma bata nuna ba.

Ameera tace “kwan ce fa ina tunani tayi bacci.

Cikin jin haushi yace “haka zakiyi mun ko to shike nan babu damuwa nagode.

A’a kayi hakuri Yaya Taheer wallahi Allah da gaske nake to shike nan bar na tashe da ita.

Gyara kwan ce tayi tana saurara su Amma bata yarda ta gane idonta biyu ba.

Taheer yace “yauwa my kanwata mike mata wayar muryar ta kawai nake son ji.

Y’ar India ki tashi Yaya Taheer yana son magana da ke”.

Uhm uhm bacci fa nake ki ce masa ya bari sai da safe dan Allah.

Yana jin abun da ta fada masa be ji dadi ba haka yayi sallama da Ameera ya kashe wayar sa ya shiga cikin mota ya bar gidan.

Dukanta Ameera tayi da sauri Khadeejah ta tashi Zaune tana matsar ido tace “wai ke lafiya kika dake ni”!?.

Cikin jin haushi tace “wallahi baki kyauta wa  Yaya Taheer wallahi.

Kallon ta tayi tace “Allah  sarki to meya faru matar sa ta korosa ne”!?.

Tsaki taji tace “yanzun fisabillah yazo dan ya ganki be samu ganinki ba kuma ya kira waya kince wai bacci kike gaskiya ban ji dadi ba har yayi fushi wallahi .

Shiru tayi tana saurara ta ajiyar zuciya tayi sannan tace “to yanzun yakike so nayi ne”!?.

Ameera tace “yauwa  kiran sa zakiyi ki bashi hakuri shike nan.

Khadeejah kallon ta kawai take ita har ga Allah bata son wani abu ya shiga tsakanin su Amma bata sani ba tace “to shike nan babu damuwa kira sa.

Cikin jin dadi ta kira Taheer lokacin yayi parking zai shiga gida kiran Ameera ne ya shigo cikin wayar sa duba yayi sannan ya dauka yace “Ameera lafiya dai ko”!?.

Ameera tace “to kayi hakuri gashi tace na kira ka”.

Ajiyar zuciya Taheer yayi yace “yanzun kuma to bata wayar”.

Mika mata wayar tayi sannan ta amsa sallama tayi masa tace “ina yini”.

Ajiyar zuciya Taheer yayi yace “lafiya klau madam nazo gidan akace bacci kike “!?.

Uhm bacci nake lokacin tana hararar wayar.

Taheer yace “wallahi soyayyar ki ta shige mani zuciya kina so na kuwa”!?.

Shiru tayi masa tana wasa da yatsan hannunta hamma tayi tace “Yaya Taheer ina godiya sosai da kulawar ka sai da safe kashe wayar ta sannan ta mika mata tace “to shike nan hankalin ki ya kwanta”!?.

Dariya tayi sannan  tace “matar nan kina burge ni da yawa fa kwantawa tayi kusa da ita bacci yayi gaba da su.

Kallon wayar yayi yana mamaki kunyar Khadeejah yace “uhm nasani kunyata kike ji shiyasa da kin furta.

*A bangaren Suleiman kuwa*

Suleiman ne Zaune duk ya rame yayi bakin wahala sanadin Khadeejah gashi yaci bakar wahala Soja ne yazo da bulalar sa katuwa yace “kai yaro zaman mekake yi ne gurin nan”!?.

Bakin sa na rawa yace “oga na gama aiki na ne shiyasa.

Sojan yace “”kutttt ubanka yace da kagama ka zauna”!?.

Girgiza kan sa yayi yace “A’a oga wallahi bayana kamar zai cire “.

Zai dake sa ne sai wani ya shigo gurin yace “dakata Sir yace muzo da shi yanzun.

Tsawa ya daka masa yace “maza wuce oga yana son ganka.

Fitowa sukayi gurin sai da sukayi tafiya me nisa sosai sannan dai dai office din Captain kb sukayi tsaye d’aya daga cikin su ya shiga cikin gurin sa.

Captain kb kuwa Zaune yake kamar kullum yana kallon su shigowa soja yayi yace “Sir gashi nan munzo da shi.

Daga kansa yayi yace ” ku shigo da shi.

Da sauri ya fita sai gashi sun shigo da shi kallon office din yake tunda yake be taba ganin irin wannan office din ba sai yau koda ya dago idanuwan sa sai cikin na Captain kb.

Captain kb kuwa ya daura kafa d’aya saman d’aya fuskar sa babu rahama murmshin gefen bakin sa yayi yace ” yanzun ka gane ni”!?.

Jikin sa na rawa yace “eh wallahi kai ne kace kada na kara zuwa gidan ku.

Jin jina kai yayi yace “masha Allah hakane to meyasa ka sace kanwata kuma”!?.

Bakin sa na rawa yace “dan girman Allah kayi hakuri wallahi shairin shed’an kuma da son zuciya lokacin inasonta ne”.

Kallon sa captain kb yake sosai yace “yanzun kuma baka sonta kenan”!?.

Daga kansa yayi yace ” eh na daina sonta kadara ce dama.

Zaro ido yayi yace “dama idan mutum yace yana son yarinya kuma ana daina son mutum”!?.

Dariya wani Soja yayi yace “Sir hauka dai soyayya ai ba,a daina soyayya inda har mutum yace yana sonka.

Jin jina kai yayi yace ” hakane to kenan har yanzun kana sonta “!?.

Girgiza kansa yayi yace ” A’a wallahi bana sonta.

Shiru yayi sannan yace “Ashe mafarki soyayya na karya ne tunda kai matsoraci ne.

Ina ma kasamu number na cikin tsawa yake magana  yana kallon sa.

Jikin sa rawa kawai yake sosai yace “wallahi zan fadi gaskiya cikin wayar Khadeejah na dauke ta.

Mamaki da al,jabi yake kallon sa to ina Khadeejah ta samu number ta  to ko da yake lokacin da yakirata tana makaranta ne babu Wanda zai amsa masa tambayar sa shiru yayi kallon sa.

Suleiman kuwa har ya fara sakin firsari a wandon sa.

Inaso zuwa gobe mu koma Nigeria cewar Captain kb.

Ok Sir an  gama insha Allah.

*A bangaren khadeejah kuwa*

Yau watan ta biyu da zuwa gidan su Mami kowa ya dauko wanka kamar wanda zasuje gidan biki.

Ameera tace “Mami yau fa fita zamuyi gidan maryam zakuje.

Baki ta rike tana kallon su tace “to shike nan a kula sosai dan Allah.

Insha Allah Mami cewar Khadeejah rike hannuwa sukayi sallama sukayiwa Mami sannan suka tafi daga cikin gida.

Tafiya suke sosai Ameera ce tana waya da kawarta sai Khadeejah tace “dan girman Allah ki ajiye wayar nan har mu dawo.

Kashe wayar tayi tace “matar nan wallahi kina da matsala sosai fa.

Tabe baki Khadeejah tayi tana hararar ta.

Taheer ne ya shigo cikin gidan da sallama Mami ce ya iske Zaune tana kallon tv da sallama.

Amsa masa tayi tace “Taheer ya gidan”!?.

Taheer yace “lafiya klau Mami ina su Ameera ne”!?.

Wallahi su fita makota yanzun gidan su maryam.

Zaro ido yayi yace “gidan su maryam kuma yanzun kuma sai da su fita”!?.

Kallon sa Mami tace “wai kai lafiya klau kake kuwa”!?.

Taheer ya gyara zama yace “lafiya klau Mami kawai dai bana son suna zuwa yawo fa.

Murmshin manya tayi tace “to masha Allah haka yana da kyau ka kula da su Allah yayi albarka.

“Amin ya Allah  Taheer yace.

Tsalakar titi sukayi wani gidane suka shiga da sallama gaishe gaishe sukayi sannan suka fito Ameera ce ta tsaya baya Khadeejah kuwa tazo tsalakar titi sai wata mota tazo da gudu bata kula da motar ba kawai ta buge ta Khadeejah ta fadi kasa some  cikin jini.

Wani irin ihu Ameera tayi da gudu tazo gurinta rungume ta tana kuka……….

*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*

🧑🏻‍✈️ *CAPTAIN KABEER* 🧑🏻‍✈️

*RUBUTAWA*

*HASSY SOJA  ce*✍🏻

*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

“`BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI  JIN’KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN“`

*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA  YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA’DI*

*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎

*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

🅿️5️⃣1️⃣%5️⃣5️⃣

*_________________*🖊️

         Wani irin ihu Ameera tayi da gudu tazo gurin ya rungume khadeejatu tayi tana kuka tana girgiza ta tace ” yar India kada ki mutu ki bar ni.

Babu numfashi atare da khadeejatu kamar wanda tar mutu da sauri driver  yazo yace “tashi muje asibity kada ta mutu.

Jikinta na rawa ta tashi tsaye tace “to muje dan Allah.

Daukar ta yayi ya sanya ta cikin motar itama Ameera ta zagaye sai Babbar Asibity garin Emergency aka shiga da ita Ameera da mai mota kuwa suna atsaye waya ta dauko ta kira su Mami lokacin suna zaune da ita da Taheer.

Rigging din wayar ta Mami tajiya da sauri ta duba sai taga sunan Ameera tagani daukowa tayi tace “Ameera lafiya har yanzun baku dawawo ba”!?.

Cikin kuka Ameera tace “Mami muna Asibity yanzun.

Cikin tashin hankali Mami tace “Ameera naji kina kuka kamar harda Asibity kika fada”!?.

Eh Mami wani mai mota ne ya buge y’ar India yanzun haka muna asibity cewar Ameera tana share hawaye.

Kallon Taheer tayi tace “tashi muje akwai matsala an buge yarinyar nan fa.

Zaro ido yayi cikin tashi hankali yace “abun bugeta kuma yaushe a wane guri duka yayi wannan tambayar jikin sa na rawa”!?.

Tashi sukayi sannan fitowa waje gurin motoci d’aya  suka shiga da gudu ya fita daga cikin gidan sai asibity cikin asibity yayi parking yayi sannan suka fito emergency suka nufa hango Ameera zaune da wani mutum ne ya sanya suka nufa gurin Ameera  ce da sauri ta mik’e tazo gurin tace “har kun iso”!?.

Mami tace ” Eh tana wane dakin  ne yanzun”!?.

Tana emergency ne yanzun bata rufe baki ba sai ga doctor yazo da sauri suka kara gurin Taheer yace “doctor ya jikinta”!?.

Kallon su yayi yace “kune kuka kawu wannan yarinyar ko”!?.

Mami tace “eh mune doctor yayi jikin na ta”!?.

Doctor yace “ku same ni office yanzun” sannan ya wuce da sauri office daga baya suka bisa shiga cikin office din suka da Mami da Taheer ne suka zauna saman kujera da Ameera da mai mota sukayi tsaye.

Ajiyar zuciya doctor   yayi sannan yace “Alhamdulillah kun san lokacin da kuka zo mani da ita ko to yanzun hankalinta yadawo normal  komai nata ya dawo  sanadin bugewar da motar tayi mata.

Ajiyar Mami tayi cikin farin ciki Ameera bakin ta be rufuwa saboda jin dadi tace “Alhamdulillah yanzun zamu iya ganinta doctor”!?.

Jin jina kansa yayi yace “Eh hakane saboda yanzun dai tana bukatar hutawa Amma zaku iya ganinta.

Da gudu Taheer da Ameera suka wuce Mami tana beye da su cikin dakin suka shiga da sallama kwan ce tana bacci da alamar ta dan bugu Amman ba sosai ba.

Mami ta kalle Ameera da ke zaune tana kallon khadeejatu tace “ya kamata kije gida ki dauko abinci.

To kawai tace sai mik’e ta fita daga cikin dakin sai gida.

Misalin karfe 3:45pm khadeejatu ta fara bude ido dafe kanta tayi tace “washiii Allah na daddy na Hajiya kuna ina ne .

Da sauri Mami da Taheer tace ” sannu yarinya”!?.

Kallon su take ahankali ahankali ta tashi zaune ta dafe kanta cikin ranta tace “topa wannan fa daga ina”!?.

Murmshi Taheer yayi yace “kanwata ya jiki”!?.

Zaro ido tayi tace “bawan Allah daga ina fa dan Allah ku su waye”!?.

Kallon ta yayi yace “zamuyi magana Amman sai kin samu sauki.

Muryar ta na rawa tace “ni fa lafiya na klau dan Allah ku su waye kuyi mani bayani tana zaro ido.

Mami ta kwantar mata da hankali tace “bari doctor yazo ya sallame ki sai muje gida sannan mu baki labari.

Shiru tayi tana son ta tuna su abubuwa Amman takasa dafe kanta tayi sosai.

Doctor ne yashigo yayi rubuce rubucen sa sannan ya duba ta ya bata sallama wuce sukayi gida.

Bayan sati d’aya da dawowar Khadeejah gidan kullum sai tayi mafarki Hajiya tana son ganta kusa da ita.

Hankalin kowa ya tashi saboda Khadeejah hankalin ta ba kwan ce yake ba kullum sai tayi kuka idan ta tuna da abubuwan da suka faru da ita.

*A bangaren Su Mommy da Hajiya kuwa*

Kullum sai Hajiya tayi mafarkin Khadeejah gashi kullum  gabanta sai faduwa yake sosai ta rasa abun da yake damunta.

Shirye shirye suke biki saura kwana ɗaya Zazzune suke saman kujera daddy ne ya shigo da sallama

Mommy tace “A’a Yaya har kadawo yaushe kadawo”!?.

Zaunawa  yayi yace “jiya nadawo sannan magana gidan da zasu zauna G. R. A  zasu zauna koma na sanya acikin gidan.

Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar su mommy da Hajiya mommy kuwa tace “to  Alhamdulillah gaskiya naji dadi wannan maganar sannan kuma kayan lefe suna daki jiya kawata tadawo Dubai.

Jin jina kai yayi yace “Masha Allah shike nan koma yazo da sauki ko”!?.

Eh mana Alhamdulillah.

*A bangaren khadeejah kuwa*

Bayan sun koma gida labari suka bata komai da komai kuka take sosai tace “tana son komawa gida gobe.

Mami tace “to shike nan babu damuwa Allah ya kaimu Amma naso kin kara samun sauƙi wallahi amma babu komai ai Allah kai mu .

Kowa yace amin ya Allah Ameera ce tace “gaskiya har naso naga gari ya waye wlh.

Taheer ya hararar ta yace “ke ko bakin ki da shegen surutu ko yanzun dai zan koma gida saboda dare yayi sai zuwa karfe takwai zamuje kano insha Allah.

Sallama Taheer yayi masu sannan ya fita daga cikin gida.

Daki su koma da khadeejatu da Ameera daki ɗaya suke kwana Mami kuwa sai ta wuce dakin ta saboda dare yayi.

Da asuba kuwa ko da suka tashi gaban Khadeejah yake faduwa  sosai runtse idanuwan ta take tana “maimata  *Innalillah wa inna ilaihir raji un* wai meya ke faru da ni ne.

Ameera kuwa tana lura da motsin ta duba ta tayi tace “Allah sarki sister meya ke damunki ne haka”!?.

Zata shiga toilet tace “bari nayi alwala yanzun” shiga cikin toilet tayi tayi fitsari sai taga period yazo mata haka ta wanke jikinta sannan ta fito rayuwata bata jin walwah.

Zaune saman salaya ta isko Ameera kwantawa tayi tace “ke dai bari kawai yasin gaba na yake faduwa sosai ban san meya ke faruwa ba.

Ajiyar zuciya Ameera tayi sannan tace “ina tunani saboda zaki koma gida ne shiyasa.

Lumshe idanuwan ta tayi tana tunane abubuwa marar sa kan gado.

Washe gari gida ya dauke hidimar biki mutane sun ciki gidan maza da mata su mommy kuwa an sha wanka daddy yazo ya kira su yace “karfe 12:00 za,a daura Auren fa.

Mommy tace “to shike nan Allah ya nuna muna lafiya yanzun karfe 11:48 am fa.

Hajiya ce ta fito cikin falon acikin zuciyar ta tanajin wani irin farin ciki sosai tace “A’a mommyn Shalele ya akayi ne”!?.

Lafiya klau alhamdulillah za,a daura Aure karfe 12:00 pm fa shine Yaya yazo ya fada mani cewar mommy.

Misalin karfe 12:00 pm masallaci ya ciki da mutane liman yace “AN DAURE AUREN CAPTAIN KABEER DA AMARYAR SA KHADEEJAH AKAN SAKI DUBU DARI BIYAR laƙadan ba, ajalan ba.

Allahu akbar kowa sai kabara yake sosai daddy kuwa bakin sa be rufuwa  saboda farin ciki sosai.

Dai dai wannan lokacin  Captain kb sai gaban sa yake faduwa sosai be san meyasa ba hankalin sa ya koma gida Nigeria kiran wani Soja yayi sannan yace “yau fa zamuje gida Nigeria maza maza ahada komai.

Ok Sir an gama cewar sojan fita yayi ya fadawa kowa ne soja na take sukayi airport

Kiran Captain kb yayi ya sanar da shi komai da sauri ya kira sauran yaron har da Suleiman suka wuce airport cikin jirge suka wuce  ƙasa Nigeria.

Misalin karfe biyu dai dai Captain kb suka iso bakin get mutane ya gani sun sha manya kaya wasu suna cin abinci kallon driver yayi yace “ko lafiya ake wannan zaman”!?.

Horn yayi da gudu mai gadi ya bude masu get shigowa cikin gida sukayi.

Da sauri driver yay parking sojoji ne suka fito daga cikin motar dai dai motar  Captain kb Soja yazo ya bude masa kofar kusan mintina 5 yana zaune cikin motar gaban sa sai faduwa yake da sauri sauri runtse idanuwan sa yayi sannan ya fito daga cikin motar.

Ƴan mata ne ya gani kowa ce da wayar ta tana photo kala kala ɗaya daga cikin ƴan mata hango Captian kb tace”kai ga ango can fa yadawo.

Da sauri ƴan mata suka zagaje sa sai guɗa

Gugu Taheer yake shararawa saman titi har suka shigo cikin garin kano gudu yake sosai wata unguwa ce ta masu kudi tace “shiga ciki kawai.

Taheer yace “to shike nan babu damuwa.

Gaban ta sai faduwa yake da sauri sauri dafe gabanta tayi tana karato addu,oi. sannan ta fara samun sauki dai dai kofar get din gidan su yayi parking yace “mun iso fa kanwata.

Ajiyar zuciya tayi sannan tace “ina zuwa dan Allah “fitowa tayi cikin motar karasawa tayi tana kwankwasawa tayi mai gadi ya bude kofar shiga cikin gidan zaro ido yayi bakin sa na rawa yace “Ha……. jiy… aaaa… aaaa ke ce kowa”!?.

Murmshi tayi tace “Nice Baba mai gadi.

Jin jina kai da mamaki da al,jabi yace “Hajiya ai tana gidan su Captain kb yau sati ukku kenan yana washe baki.

Gabanta yace rasss da sauri tace “gidan su mommy kuma ok babu damuwa bari naji can da gudu tajuya bude kofar motar tayi ta shiga ta zauna tace “muje gidan mommy na yanzun Hajiya na can.

Kallon ta su Mami suke babu Wanda yace komai haka yaja motar tana nuna masa hanyar unguwar.

Mamaki da al,jabi Captain kb da Suleiman da sauran sojojin suke da sauri ya wuce cikin gidan.

Su mommy ne Zaune saman kujera falo  kamshin turaren Captain kb tajiya shine ya tabbar mata da cewar ya shigo cikin falon acikin zuciyar tayi tana kallon kofar.

Bakin sa dauke da sallama yana karasowa cikin falon mommy da Hajiya da sauran baƙin da  sukazo gidan biki miƙewa tsaya suka da sauri ya karaso ya rungume mommy yace “miss you my love mom.

Murmshi tayi tace “A’a  my son babu sanarwa sai kawai muganka”!?.

Hajiya tace “A’a yarona har ka iso babu sanarwa ko”!?.

Murmshi yayi yace “am sorry Hajiya ta wallahi kawai dai hankalina ne ya kasa kwan ce shiyasa nace nayi maku zuwan bazata.

Zaunawa yayi kusa da mommy rike masa hannuwa tayi tana kallon sa tace “hakane Allah yayi maka albarka.

Amin amin.

Shiru yayi na dan wani lokaci sannan yace ” my love mom lafiya dai na ga gidan ya cika da mutane”!?.

Zatayi magana kenan kawai sai sukaga mutum ya shigo yayi tsaye yana kuka.

Gaban Hajiya yace rasss jikinta na rawa tace”Sha….. Leeee….. Leeeee na ke ce kuwa ko , ko dai gizone Allah ya sa ba gizo bane.

Da gudu Khadeejah tazo ta rungume Hajiya tana kuka jikinta har rawa yake saboda farin ciki tace “Nice Hajiya ta ni ce wallahi taba jikina ki gani”.

Girgiza kanta tayi tana kukan farin ciki da sauri   mommy  tazo ta rungume khadeejatu tana kukan farin ciki  tace “Allah sarki y’ata Ashe zamu kara ganinki “!?.

Sakin Hajiya tayi da sauri Khadeejah ta rungume mommy tana kuka tace ” Ashe zan kara ganku mommy na dama sai da kike ce kada na tafi Ashe kadara ce zata fada mani.

Kallon su yake cikin tausayawa yace “Khadeejah”.

Da sauri ta dago idanuwan ta duba sa tabbas Yayanta ne bazata manta wannan muryar ba tace “Na’am Yaya Captain kb “hawaye na zubo mata.

Su Mami ne suka shigo cikin falon da sallama…..

*Dan Allah kuyi hakuri da wannan afuwa Afuwa ina  busy  ne  shiyasa  Amma na kusa gamawa insha Allah*🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*

🧑🏻‍✈️ *CAPTAIN KABEER*🧑🏻‍✈️

*RUBUTAWA*

*HASSY SOJA  ce*✍🏻

*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

“`BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI  JIN’KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN“`

*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA  YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA’DI*

*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎

*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

🅿️6️⃣1️⃣%6️⃣5️⃣

*_________________*🖊️

         Suleiman kuwa hawaye ne suka zubo masa cikin ransa yace “da yanzun ni ne na Aure ta shike nan  yanzun son zuciya ya rufe mani ido.
Zaunawa daddy yayi saman kujera sai ya daure khadeejat saman cinyarsa yace “to Alhamdulillah yanzun dai komai yayi dai dai Allah yayi muna jagora.

Suka ce amin ya Allah.

Khadeejat tace “my sister muje part dina mu kwanta.

Ameera tace ” OK babu damuwa” miƙewa tsaye tayi sannan suka wuce part din khadeejat key ta dauko saman taga sannan ta bude dakin kamshi turaren wuta mai dadi dakin yake sosai shiga cikin dakin sukayi ajiyar zuciya Ameera tayi tace “masha Allah gaskiya dakin akwai kamshi mai dadi.

Murmshi khadeejat tayi  tana kokarin zama saman gado tace”uhm ko wannan gidan fa ba na mu bane gidan mu nace inda na fara shiga.

Zaro ido Ameera tayi tace “kamar ya fa”!?.

Ajiyar zuciya khadeejat tayi tace “wannan gidan su Captain kb ne fa mahaina sa shine Yayan Hajiya ta ita kuma mommy   daddy na shine Yayanta Aure zumunci akayi masu.

Rike baki Ameera tayi sannan tace “ikon Allah ke ki ce ke ma Aure zumunci ne akayi maku gaskiya Aure su mommy da daddy da Hajiya abun sha,awa yasin to yanzun  yakike kiran sunan mahainsa”?.

Murmshi nayi nace ” Abba ai ko shi be san mahainsa ba bale ni.

ok tin yana karami kenan ko “!? .

nace “yes ke bari na kwana naji mararta ta fara ciwo.

Subhanalillah to yanzun menene zaki sha ya daina ciwo.

Kasa magana tayi saboda yanzun ciwon ta taso mata sosai jikinta har rawa yake sosai kuka ta fashe da shi tana juye juya da sauri Ameera ta fito daga cikin dakin falo ta nufa hankalin ta tashe.

Lokacin sallah yayi daddy yace ” ku tashi muje masallaci lokacin sallah magrba yayi fa.

Taheer da Suleiman da daddy suka fita daga cikin falon sai masallaci saboda lokacin sallah yayi.

Mommy da Hajiya da Mami sun miƙe kenan sai ga Ameera tashigo cikin falon tace Hajiya Khadeejah bata da lafiya.

Cikin tashin hankali suka wuce dakin da sauri koda suka shiga da gudu kwan ce take tana kuka tana yarfe da hannu da Hajiya da mommy suka karasa gurin ta rungume mommy tayi tace “Auta ta ciwon marar ne ko”!?.

Runtse idanuwan ta tayi tana kuka jikinta rawa yake sosai kiran daddy Hajiya tayi ta fada masa Khadeejah bata da lafiya ko minti biyar beye ba sai gashi yashigo cikin dakin da sallama karasowa yayi yace ” kun kira mijinta ne”!?.

Hajiya tace “A’a kamar shima baya da lafiya fa.

Shiru yayi sannan ya ciro wayar sa ya kira Captain kb lokacin kwan ce yake yana rawar sanyi ko gani bayayi sosai saboda zazzabi mai zafi ne dauka yayi muryar sa na rawa yace “Naam daddy .

Daddy yace “baka da lafiya ne”!?.

Eh daddy zazzabi mai zafi ne ya rufe ni yanzun haka ina kwan ce daki.

Subhanalillah to yanzun gashi itama Shalele bata da lafiya bari na kira doctor yazo ya duba ku.

Kashe wayar yayi sannan ya kira doctor mintina 30sai gashi yashigo cikin dakin da sallama karasowa yayi yace “gani Alhaji.

Khadeejah har ta fara fita hayacinta saboda azaba allura doctor yayi mata sannan yace “gaskiya Ina baku shawara kuyi ma ƴar ku Aure idan har kuna son ta daina ciwo nan.

Murmshi daddy yayi yace “ai tana da Aure yanzun dai ga mijinta can kwan ce bashi da lafiya.

Doctor yace “Masha Allah Allah ya basu zaman lafiya gaskiya ina tayaku murna sosai.

Fita sukayi daga cikin dakin wuce wa part din  Captain kb lokacin kwan ce yake saman gado yana rawar sanyi shigowa cikin dakin da sallama suka sannan ya duba sa yayi masa allura har da ta bacci sai ya dauke sa.

Ajiyar  zuciya daddy yayi yace “Alhamdulillah yanzun dai komai zama normal ko”!?.

Doctor yace “insha Allah hannu ya bashi sukayi musabiha.

Khadeejah kuwa bacci take sosai sai Ameera tace “wai mommy haka take fama da shi ko lokacin da muna tare da ita tana yin sa sosai.

Hakane muna godiya sosai Allah ya saka maku da alkhairi cewar su mommy da Hajiya.

Bayan kwana biyu.

Su mommy da Hajiya da Mami ne Zaune saman kujera suna labari sai ga daddy yashigo cikin falon da sallama.

Amsa sallama sannu da zuwa sukayi masa.

Zaunawa yayi saman kujera yace “wai yaran nan suke”!?.

Mommy tace “suna daki”.

Daddy yace “gaskiya ya kamata KABEER ya dauke matar sa ya tafi da ita gida nagaji da zaman da sukayi cikin gidan nan fa ciro wayar sa yayi ya kira captain kb sannan ya kashe ya kira Khadeejah sannan ya kashe wayar sa.

Shigowa Captain kb yayi da sallama karasowa yayi yace “barka ku da hutawa Hajiya.

Murmshi Hajiya tayi tace “yauwa  yarona dafatan kaji sauki sosai.

Zaunawa yayi saman kujera yace “Alhamdulillah Hajiya.

Sallama Khadeejah tayi tace ” ina kwana ku su Mommy”zauna tayi kusa da mommy .

lafiya klau muke ya jikin na ki”!?.

Alhamdulillah Hajiya cewar Khadeejah .

Gyara murya daddy yayi yace “Alhamdulillah  KABEER  ka dauki matar ka ku tafi gidan ku na G. R. A ga key nan.

Da sauri Khadeejah ta dago idanuwan ta duba daddy tace “daddy tun yanzun dan Allah kayi hakuri bata karasa ba ya daga mata hannu.

Daddy yace “Aa ƴ’ata  bana son musu da ke ni dai Allah ya baku zaman lafiya kiyi masa biyaya duk abun da yace kiyi to kada kiyi musu kiyi abun da yace kinaji ko”!?.

Hawaye ne suka zubo mata ga kumatu kuka ta fashe da shi da sauri ta rungume Hajiya, rungume ta Hajiya tayi tace “kiyi hakuri wannan shine mafi alkhairi da ke yanzun kin zama babbar mace da kin haihu to kin zama uwa kiyi ma mijinki biyaya ki bisa sauda kafa dan Allah kada ki yarda wani yaji sirin ku da ke da mijin ki tashi ku tafi Allah ya baku zaman lafiya.

Tashi tayi tazo gurin mommy ita ma ta rungume ta tana bu buga bayanta tace “kiyi hakuri Auta ta wannan shine gatan ki yanzun ke ba budurwa bace kin zama matar wani wato matar Aure nasanki da tarbiyar mai kyau sosai Allah ya albarkar ce Auren ku.

Tashi yayi ya amsa key sannan yace ” muna godiya sosai Allah ya saka maku da alkhairi tashi muje.

Kuka take sosai kamar ranta zai fita daƙwari ta sufa fita tare bude mata mota yayi saman ta shiga tana kuka zagayawa yayi ya shiga sannan yaja motar suka fita daga cikin gidan gudu yake sharawa saman titi kukanta har cikin ransa tsawa ya daka mata yace “dan Allah gafar can ki rufe mani baki kin cika mani kunne da baƙan kukan tsiya mtsss.

Dago jajan idanuwanta tayi tana hararar sa tace “to ina ruwan ka da ni ai wallahi an cuce ni da aka hadi ni da kai mugun kawai kuka ya subuce mata.

Parking yayi gefen titi saboda takaici yace “yasin idan baki rufe mani baki ba sai dai ki fitar mani daga mota.

Ko sauraren sa batayi ba haka tacigaba da kuka sannan tace “wallahi baka isa ba ai ba motar ka bace da zaka ce na fita.

Murmshin mugunta yayi yace “haka kika ce ko”!?.

Eh din wai ina ruwan ka da ni ne mtsss.

Gudu yake shararawa saman titi unguwar G. R. A suka shigo dai dai wani hadaden gida ne mai feenti gree  horn yayi da gudu mai gadi ya bude masa shigowa cikin gidan yayi cikin gareji yayi parking sannan ya fito daga cikin motar ko da ta duba ya fita daga cikin motar sannan tace wallahi sai na kuya maka hankali fito tayi cikin gidan tashiga tundaga can ta hango sa zai shiga daki karasowa tayi ta duba gefen dakin green feenti dakin da gudu ta ture sa ta shiga ciki baƙin kofar dakin ta tsaya tace “wannan daki nawa ni kaje ka duba wan can”sannan ta rufe kofa.

Baki ya saki yana kallon ta da mamaki gefe d’aya ya kalla sai ya ga feenti fari da baki ne yace “Alhamdulillah kamar daddy ya sani wan can shine nawa karasawa yayi ya shiga cikin cire kayan jikin sa yayi sannan ya shiga toilet watsa ruwa yayi sannan ya fito daure da towel yana goge ruwan jikin sa jalabiyar sa fari ce ya sanya sannan ya kwanta bacci yayi gaba da sh.

khadeejah kuwa kwan ce take tana kallon sama tana ajiyar zuciya saboda kukan da tasha yau bacci yayi gaba da ita.

Misalin karfe 4:47 pm sannan ta farka tashi tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa sannan ta fito bedroom ta bude ta dauko Abaya yellow ta sanya sannan ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi sosai duk da batayi kwaliya ba tayi kyau sosai sannan ta fito daki saukowa tayi daga saman bene  cikin falon ta karasa gaban ta yace dumm dumm hango shi tayi zaune saman kujera yana kallon tv BBC kamshin turaren ta ne ya dake hancin sa da sauri ya juya suna hada ido ya dauke idanuwan sa ya cigaba da kallon sa.

Karasowa tayi cikin falon zuciyar ta na bugawa da sauri sauri runtse idanuwan ta tayi sannan ta karasa gurin  kujera  tayi kujera d’aya ce sai zauna tana kallon gefen windo.

Captain kb ya daure fuska yace “ke ki saurareni da kyau sosai kada ki ce ban fada maki ba to daga yau zaki rinka gyara mani daki na sannan kuma ke zaki rinka yin mopping    sannan kuma girki kullum da safe da rana da dare kuma bana son ƙazata ko kaɗan sannan kuma bana cin tuwo ko wane irin ne sai shinkafa  da wake.

Sakin baki tayi tana kallon sa sai da ya gama fada sannan tace “ikon Allah yanzun kana nufe duk wannan uban aikin nice zanyi sa”!?.

Wani mugun kallo ya aika mata da shi…….

*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*

🧑🏻‍✈️ *CAPTAIN KABEER*🧑🏻‍✈️

*RUBUTAWA*

*HASSY SOJA  ce*✍🏻

*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

“`BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI  JIN’KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN“`

*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA  YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA’DI*

*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎

*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

🅿️5️⃣6️⃣%6️⃣0️⃣

*_________________*🖊️
Su Mami ne suka shigo cikin falon da sallama, sallamar Mami ce ya sanya kowa ya juya yana kallon su.

Khadeejah ce tace “ku karaso ciki mana Mami.

Karasowa sukayi sannan suka fara gaishe gaishe zaunawa saman kujera su Mami da Ameera da Taheer sukayi shiru sukayi.

Hajiya ce ta dauko wayar ta ta kira daddy tana gama fada masa ko minti biyar beyi ba sai gashi ya shigo cikin falon da farin ciki sosai kallon falon yayi sai yaga ciki da mutane da gudu Khadeejah taje ta rungume daddy tana kukan farin ciki tace “Daddy na gani nan nayi kewarka Ashe zan kara ganinka “!?.

Rungume khadeejatu yayi sosai sannan yace “Allah sarki y’ata Ashe kina kusa da mu Alhamdulillah Allah kai ne abun godiya.

Su Mami da Ameera da Taheer da Suleiman  hawayen tausaye suke basu taba ganin irin wannan kulawar ba sai ga Khadeejah.

Jawo hannuta yayi yace “muje mu Zauna ko”!?.

Daga masa kai tayi sannan sukaje suka Zauna saman kujera d’aya  daddy ne yace “Alhamdulillah Allah shine abun godiya Mommyn Shalele kin ga yarki tadawo ko “!?.

Cikin murna suka “Eh gashi nan tazo tare da wandin da suka taimaka mata.

Sai yanzun ya kula da Captain kb Zaune kusa da Hajiya mamaki da al,jabi ya kamashi yace “ikon Allah  kai yarona yaushe kadawo”!?.

Murmshin gefen bakin sa yayi yace “daddy nima yanzun nadawo ma, ƙasa ne.

Daddy yace ” ina barawon y’ata ne ko yana can kun baro ne”!?.

Khadeejah kuwa jikinta sai rawa yake sosai saboda taji an ce wanda ya sace ta  sai taga Suleiman ya mik’e tsaye tace “Suleiman waya kawo ka gidan mu har cikin falon.

Suleiman kuwa jikin sa ya soma rawa yataso durkusawa yayi gaban su mommy da daddy  Hajiya  yace “kuyi hakuri dan Allah  wallahi shairin shed’an da son zuciya yana kuka.

Mommy tace “to shike nan Allah ya yafe mu baki d’aya.

Suka ce” Amin ya Allah.

Suleiman kuwa kuka yake sosai kamar wani karamin yaro tashi yayi yazo gaban Khadeejah, Khadeejah kuwa gaban ta sai faduwa yake rike hannuwa daddy tayi sosai tana kuka Suleiman yace “dan girman Allah Khadeejah kiyi hakuri ki yafe mani sanadin ki na sha wahalar da bantaba tunane zan sha ba ki yafe mani.

Runtse idanuwan ta tayi tace “Allah  ya kara maka kai bacewa kayi ba sai ka Aure ni ko mutuwa zanyi ba to yanzun gashi nan an koya maka hankali.

Ameera tace “Himm ikon Allah dama kai ne kayi sanadin bugewar y’ar India tabba yasin da na sani da nayi maka ila kuwa tana hararar sa.

Suleiman kuwa kallon Ameera yake sai yaji kamar ya kama dukanta saboda haushi.

Khadeejah tace “dan girman Allah ni dai ka tashi bana son ganka.

Murmshi daddy yayi yace “A’a bazayi haka ba shike nan kice kinyafe masa tunda ya tuba.

Turo baki tayi tana bu buga kafafuwanta tace “ni dai Uhm uhm uhm uhm uhm uhm uhm uhm uhm  bazanyi ba saboda wata rana zai dawo.

Daure fuska Captain kb yayi yace “ke baki da hankali ne kina gaban mutane zakiyi muna abun da kika saba ko”!?.

Turo baki tayi tana hararar sa ƙasa ƙasa tace “Allah ya kara masa.

Dariya mommy tayi tace “A’a fa Auta ta ban sanki da haka ba fa.

Turo baki tayi tace “to  shike nan Allah ya yafe muna baki d’aya.

Dariya Hajiya tayi tace ” ikon Allah  wato sai da mommyn ki tayi magana sannan ikon Allah wannan soyayya haka.

Tabe baki Captain kb yayi yace “ai dama nasani halin ta wai ita Shalele wallahi mommy ke zaki lallata ta da shagwaba mtsss ace mutum ya girma be san ya girma ba.

Murguda masa baki tayi tace “eh din ina ruwanka da ni daga zuwa na sai masifa nima ai nayi masifar tana hararar sa.

Kallon su kowa yake sosai da mamaki.
Captain kb  yace “ai shiyasa nace maki baki da hankali yarinya kina abu sai kace wata Babba kuma ni Yayanki ne dole ki bani girma na.

Tabe baki tayi tana hararar sa tace “tabba Allah ya sauwaka ni fa yanzun na wuce da saninka dube sai dan Allah wai ko mata baya da ita hhhh.

Cikin jin haushi yace “haka  ne to ai ke ma baki isa Aure ba kin gani ko mun zama d’aya gwarowa kawai.

Dariya Hajiya da mommy sukayi Hajiya tace ” sannu ku Tum and jerry  kun dawo kenan kowa ya nuna halin sa ku wai dan Allah ko kunyar mutane bakuje ba”!?.

Su har Allah sun manta da akwai mutane acikin falon wata kunyar ta kama Captain kb da khadeejat kamar su shige cikin ƙasa sun kuyar da kan sa yayi yace “Am sorry Hajiya na manta ne.
Dariya suka bushe da ita saboda abun ya basu dariya sosai.

Daddy ne ya gyara murya yace “A’a  babu wani idanuwan ku sun riga sun rufe da masifa ne yanzun dama akwai magana mai muhimmaci kowa ya saurane da kyau.

Kowa yayi su gaban Khadeejah yake faduwa sosai da sauri sauri Captain kb kuwa gaban sa yake faduwa da sauri sauri *Innalillah wa inna ilaihir raji un* shine abun da suka maimata wa.
Khadeejah cewar daddy.

Gaban ta yace rasss tunda take da daddy be taba kiran sunata ba sai yau topa Yau magana ce mai muhimmaci zai fada mani bakin ta na rawa tace “Naam daddy.

KABEER cewar daddy.

Gaban sa yace dumm dumm yace “Naam daddy.
Daddy yace “ni waye agurinka”!?.

Sunkuyar da ƙasa yayi yace “kai Mahaifina ne.

Ajiyar zuciya daddy yayi yace “to  ina leman wata alfarma agurinka.

Kallon daddy yayi yace “daddy babu wata alfarma da zaka ne ma aguri na narasa baka ni dai kawai daddyka fada mani wallahi Allah ko wuta kace na fada zan fada.

Jin jina kansa yayi yace “to Alhamdulillah”sai ya kalle Khadeejah yace “Khadeejah ni waye agurinki”!?.

Bakin ta na rawa tace “kai mahaifina ne Daddy.

Ajiyar zuciya daddy yayi yace”inda har ni mahaifinki ne to kuma ki dauke ni mahaifinki to na yanke maku hukunci da ke da Yayanki na Daure maku Aure ya din nan.

Dafe kirjinta tayi hawaye na zubo mata bakin ta na rawa tace “Dan Allah daddy kada kace wannan mugun ka Aure mani ni dai ko mai gadi ka Aure mani zan Aure sa Amma dan Allah kaje maganar Aure na da *CAPTAIN KABEER* daddy kara fashewa da kuka tayi jikinta na rawa.

Idanuwan Captain kb sukayi jajaye sosai har zazzabi ya soma rufe sa yace “Daddy dan Allah kayi hakuri tunda bata son zama da ni.

Girgiza kai daddy yayi yace “ke Khadeejah Ashe ban isa da ke ba Ashe akwai abun da zan fada ki nuna mani ban isa da ke ba to shike nan tunda haka kika ce kai kuma KABEER na riga na yanke maku hukunci tunda kayi mani biyaya Allah yayi maka albarka futt ya wuce part din sa.

Tashi Captain kb yayi jikinsa babu kwari sosai fita yayi daga cikin falon kansa kamar ya rabe gida biyu part din sa ya wuce.

Kuka Khadeejah take sosai ta sauri ta mik’e taje gurin Hajiya tace “Hajiya kina jin abun da daddy yace ko kuka take sosai.

Rungume khadeejat tayi tana bu buga bayanta tace “”A’a Shalele na ban san ki da rashin kunya ba kin san daddyn ki be taba ɓata maki rai ba fa kuma ki tuna tun sanda kira jaririya har kika girma duk abun da kike so to shine akeyi agida to yanzun bazaki duba kiyi masa biyaya ba”!?.

Dagowa tayi tana share hawayen da ke zubo mata tace “wallahi na hakura zanyi masa biyaya idan har zai ji dadi sosai farin cikin sa shine nawa bar na bashi hakuri.

Murmshi Hajiya tayi tace “Yauwa Allah yayi maki albarka.

Wuce part din daddy tayi  can ta hango sa zaune saman kujera yayi shiru yana tunani da Sallama tashigo cikin dakin jikinta babu kwari gurin sa ta karasa ta durkusa ƙasa tace “dan Allah daddy na kayi hakuri ka daina fushi da ni ni na aminci da da Auren sa zanyi maka biyaya idan har zai sanya ka farin ciki kuma daddy ko wuka kace na dauko na yanke kai na zanyi bale Aure.

Murmshi yayi yace “ni ai bana fushi da ƴata ina alfahari da tarbiyar ki dan haka babu komai Allah yayi maki albarka.

khadeejat tace “Amin ya Allah daddy na to kayi dariya mana cikin shagwaba take cewa.

Dariya sannan suka fito falo yana rike da hannun ƴata suna labari suna dariya.

Su mommy kuwa ba karamin farin ciki sukayi ba Taheer kuwa kamar ya hade zuciyar sa ya mutu saboda baƙin ciki da takaici Ameera ma bata ji dadi ba Amma cikin ranta tace “Allah ya baka wata Yaya Taheer.

Suleiman kuwa wasu hawaye ne suka zubo masa cikin ransa yace “da yanzun  ni ne na Aure ta shike nan…. …

*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*

‍🧑🏻‍✈️ *CAPTAIN KABEER*🧑🏻‍✈️

*RUBUTAWA*

*HASSY SOJA  ce*✍🏻

*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

“`BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI  JIN’KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN“`

*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA  YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA’DI*

*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎

*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA DA ƘASASHIN WAJE WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

🅿️6️⃣6️⃣%7️⃣0️⃣

*_________________*🖊️

         Wani mugun kallo ya aika mata da shi yace “wasa nakeyi da ke ni ko na taba wasa da ke to bar kiji wannan gidan ba gidan hutawa bane aiki dole kiyi sa kuma ko da wasa kika fadawa su mommy da Hajiya wallahi sai na kakarya maki kafafuwa na cire maki hauru.

Kuma sannan na bindige ki shike nan ki mutu babu ruwa na afusace ya fita daga cikin falon sai masallaci saboda lokacin sallah azzhur yayi kuka Khadeejah ta fashe da shi tashi tayi ta shiga kitchen kayan tagani green masu kyau sosai tsaye tayi tana kallon su komai ya buge ta.

Buhuhuwa shinkafa tagani da taliya da wake da indomie komai akwai kuna gs tayi ta daura ruwa acikin tukunya sannan ta rufe wake ta debu ta gyara sosai sannan ta wanke sa ta zuba wanken cikin ruwan kanwa tazuba ciki da maggi minti biyar sai tukunya ta tafasa shinkafa ta wanke ta zuba sannan ta rufe fitowa tayi tana tunani ina zataga yaji dawowa kitchen tayi sai ta bude wata loka can ta hango sa daukowa tayi tace “yauwa bar na gyara yajin kafin nagama girki.

Taushi da maguguna da kayan kamshi daka shi tayi sosai sannan ta zube sa cikin yar ruba ko da ta duba shinkafa tayi sannan ta dauke ta zuba mai guda sannan ta soya bayan ta kamala ta kashe gs sannan ta zuba shnkafa da wake cikin kula ta rufe dauko kular tayi ta kawo masa falo ta ajiye sa kowa ma kitchen tayi ta dauko yaji da mai suma ta kawo falo ta ajiye masa.

Dakin sa ta wuce ta gyara sosai sannan ta fito daga cikin dakin zata wuce part din ta sallamar sa tajiya amsa masa tayi Amman bata kalle sa ba dakin ta ta wuce ta gyara sosai sannan ta shiga toilet ta watsa ruwa sannan ta fito da daure da towel  tana goge ruwan jikinta riga da wando ta sanya sannan ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi sosai duk da batayi kwaliya ba tayi kyau sosai sannan tayi kwan ceyar ta daki tana tunani duniya.

Captain kb kuwa koda ya shigo cikin falon kamshin turaren wuta mai dadi yake falon zaunawa saman kujera yayi yace “washii bar na kira Hamza ko yaushe zamu koma.

Koda ya duba sai taga kular abinci da kwai da kayan miya da yaji da mai kallon kayan yayi sosai tabe bakin sa yayi ya kira hamza  yace ”  hello yaushe zamu koma america”!?.

Hamza yace “Sir kai da kayi Aure ka bar kagama cin amarci sannan.

Cikin bacin rai yace “wai kai hamza yaushe na fara wasa da kai ne”!?.

Hamza yace “Sorry Sir bazan sake ba insha Allah.

Kashe wayar sa yayi yana kallon tv BB kwala mata kira yayi yace “ke yarinya kina ina ne”!?.

Kwan ce take tana kallon sama kiranta taji anayi da sauri ta fito daga cikin dakin ko dankwali babu saman kanta karasowa tayi ta duba gefen ta bata komai ba har zata juya sai taji yace “wai ke bada ke nake ba ne “!?.

Hango sa tayi zaune saman kujera ya daure kafa d’aya saman daya fuskar sa babu rahama karasowa tayi tace “gani.

Captain kb yayi kamar be ganta ba sai da tayi mintina 30sai yace “kina nufe me”!?.

Cikin rashin fahimta tace “kamar ya fa”!?.

Harara ya aika mata da ita yace “ban sani ba wai ke yaushe zakiyi hankali ne wai”!?.

Turo masa baki tayi tana kallon kasa kasa tana hararar sa tace “ni wallahi ina da hankali na”!?.

Duk abun da take yana kallon ta ta gefen idonsa murmshi yayi yace “sannunki  da hararar ta kinji”.

Da sauri Khadeejah ta dago idanuwan ta dube sa tace “yaushe kuma na harare ka”!?

Karya zanyi maki kenan ni dai kizo ki zuba mani abinci.

Jiki babu kwari haka ta durkusa kasa ta zuba masa abinci ta mike masa sannan ta zuba masa lemon juice tace “to gashi nan” har ta mike zata wuce sai taji yace “kina nufe ni zan cinye wannan abinci ko yaya”!?.

Bata fuska tayi tace “ni fa na koshi wallahi kuma ai kai kace na zuba maka”!?.

Tsawa ya daka mata yace “zauna ki fara ci saboda kada ki zuba mani guba naci na mutu maza ci abinci nan”ya daure fuska.

Jikinta har rawa yake sosai kuka ta fashe da shi tana cin abinci kamar tana cin magani luma biyu tayi dakar da sauri ta mike da gudu ta wuce dakin ta tana kuka binta yayi da kallon ya tabe baki ya cigaba da cin abincin sa.

*A bangaren Suleiman kuwa*

Koda  ya koma gida daddyn sa kawai ya isko kuka yake sosai yace “daddy Ashe akwai abunda zani nema na rasa samun sa Ashe duk abun da nake ba dai dai bane to yanzun na gane gaskiya.

Kallon sa daddyn sa yayi sannan yace “my son ina kashiga cikin duniyar nan munyi nemanka amma bamu samu labarin ka ba.

Labari ya fara bashi tun daga farko har karshe yace “yanzun nayi nadama kuma insha Allah bazan kara ba.

Cikin jin dadi daddyn sa yace “Alhamdulillah Allah mungode maka da kagane gaskiya to yanzun sai kane ma matar da zaka Aure shike nan nima son naga jikana.

Share hawayen sa yayi yace “insha Allah kacigaba da yi mani addu,oi Allah ya bani tagari.

Amin ya Allah cewar daddy.

kwana biyu da faruwa haka kwan ce yake saman gado yana bacci mafarki Ameera yake suna zaune gefen ruwa suna soyayya har da Aure da sauri ya tashi zaune yana mamakin mafarkin sa dafe kansa yayi yace “Alhamdulillah yanzun dai ita zan koma wa Allah ya sa ta soni.

Tashi yayi ya shirya cikin manya kaya kamar wanda za, a daure wa Aure ya sha kyau sosai fitowa yayi falo daddy ne ya iske zaune yana karatun jarida gaishe da shi yayi sannan  yace “daddy zan shiga cikin gari.

Washe baki yayi yana jin dadi yaron sa ya shiryu yace “Alhamdulillah Allah ya taimaka ya sa adace.

Amin ya Allah cewar Suleiman.

Fita yayi daga cikin falon sai gurin da motoci ya dauke d’aya daga cikin motoci ya shiga ya fita daga cikin gida.

*A bangaren Taheer da Ameera kuwa*

Bayan sun koma gida komai yana tafiya lafiya klau kullum sai Ameera tayi waya da Khadeejah da kuma kawarta maryam har tace zata shigo.

Zazzune suke saman kujera da Mami da Ameera kallon ta Mami tayi tace “wai lafiya kwana biyu da ke da Yayan ki sai ahankali wai me yake faruwa ne”!?.

Ajiyar zuciya Ameera tayi tace “ni kai wallahi Mami ban sani ba kawai kwana biyu bana jin dadi ne shi kuma Yaya Taheer rashin Khadeejah ne wallahi yana sonta sosai.

Shiru Mami tayi na dan wani lokaci sannan tace ” to Allah ya sauwake.

Da sallama ya shigo cikin falon zaunawa saman kujera yayi yace “Mami lafiya dai ko”!?.

Ajiyar zuciya tayi tace “wallahi ina tausaya maka ne Amma insha Allah zaka samu mata tagari.

Murmshi yayi yace “babu komai ai Mami ni na bar ma Allah komai.

Cikin jin dadi tace “Alhamdulillah yanzun naji dadi haka Allah ya kawo.

Sallamar wata yar budurwa ce ta shigo cikin falon tana murmshi Ameera da ke zaune gefe muryar da tajiya ne da sauri ta dube kofar zaro ido tayi tace “Maryam yau ke ci gidan na mu da gudu taje ta rungume ta.

Cikin kunya tace “wallahi kuwa sake ni mu gaisa da Mami karasowa tayi tace “ina wuni Mami”!?.

Murmshi Mami tayi tace “lafiya klau ya gida naku ina Mamar ki”!?.

Sunkuyar da kanta tayi tace “suna lafiya tace ai gaishe da ku.

Muna amsa wa sosai.

Yaya Taheer ina yini cewar Maryam.

Baki ya saki yana kallon ta sai da Ameera tace “Yaya Taheer an gaishe da kai fa.

Murmshi yace “Alhamdulillah su mommy na lafiya dai ko”!?.

Cikin jin kunya tace “lafiya klau Yayan mu”tashi tayi suka wuce daki da ita da Ameera.

Kallon Mami yayi yace “wallahi ni dai yarinyar nan tayi mani sosai Mami.

Murmshi Mami tayi tace “to Alhamdulillah Allah ya tabbar muna da alkhairi.

Kiran wayar sa yayi yana duba wa sai ya  ga sunan Suleiman dauka yayi yace “ya akayi ne dan uwa” da yake yanzun sun zama yan uwa.

Yana tuƙi yace  “ina saman hanya fa zan shigo gari”.

Da sauri Taheer yace “Haba dai kai dan uwa kace yau zamuyi babban bako”!?.

Dariya yayi sosai yace “insha Allah sai nazo ina kanwata masifafa”!?.

Dariya Taheer yayi yace “Ai kuwa kai da ita kun zama toom and jerry fa Allah daga ina sai gidan ka.

Kashe wayar sa yayi yana dariya yana tuƙin sa.

Kallon Mami yayi yace “ɗan ki yana saman hanya zai shigo.

Kai masha Allah abu yayi kyau Allah ya kawo shi lafiya…………….

*TOPA SULEIMAN YA FADI TARKON SOYAYYAR AMEERA TAHEER KUWA SHIMA DAI YA FADA TARKON SOYAYYAR MARYAM KO YA ABUN ZAYA KASAN CE*🤔🤔🤔🤔🤔    🤣🤣🤣🤣🤣🤣

*KU CIGABA DA BIBIYA TA DA SAMUN AMSA WANNAN TAMBAYOYIN*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*

🧑🏻‍✈️ *CAPTAIN KABEER*🧑🏻‍✈️

*RUBUTAWA*

*HASSY SOJA  ce*✍🏻

*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

“`BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI  JIN’KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN“`

*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA  YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA’DI*

*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎

*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

🅿️7️⃣1️⃣%7️⃣5️⃣

*_________________*🖊️

         Kai masha Allah abu yayi kyau sosai Allah ya kawo shi lafiya cewar Mami da take murmshi.

Amin ya Allah dama kwana biyu yana kira yace mani zai shigo sai dai yanzun Allah yayi zuwa nai.

Jin jina kai Mami tayi tace “haka ne Allah dai ya kawo muna shi lafiya.

A bangaren Suleiman kuwa yanzun ya shigo kaduna kuka kawai yake shararawa saman tit cikin i unguwar tudun wada  ya shigo  kiran wayar Taheer yayi yace “ina shigo cikin tudun wada fa.

Ok babu damuwa gani nan fitowa kaji rani yanzun cewar Taheer.

Kashe wayar  sa yayi yana jiran sa ko mintina biyar beye ba sai gashi ya isko gurin da yake ya fada masa motar da shigo Taheer yace “kaga gida can fa kai kullum sai na fada maka”!?

Hararar sa Suleiman yayi yace “ban sani ba tuƙin motar yayi dai dai get din gidan sai yayi  horn da sauri mai gadi ya bude masa shigowa cikin gidan yayi samu guri yayi sannan yayi parking kashe motar yayi bude masa kofar motar Taheer yayi yace “to fito mana Mami na jiranka.

Fitowa yayi daga cikin motar yana murmshi sannan ya bashi hannu sukayi musabiha.

Cikin gidan suka wuce da shigowa cikin falon yayi da sallama Taheer yana dariya yace “uhm Mami ga surukin kinan ya iso.

Da sauri Suleiman yake kallon Taheer da mamaki yace “kamar ya fa”!?.

Murmshi Mami tayi tace “Suleiman sannu da zuwa ansha hanya ko”!?.

Sosa kai yayi da key din sa yace ” Yauwa Mommy na same ku lafiya”!?.

Lafiya klau ya daddyn naka yana klau ko”!?.

Yace “a gaishe ku.

Muna amsa tashi ka zauna mana.

Saman kujera ya zauna yana watsa da key din sa yayi kusan mintina 30 sannan  yace “wai har yanzun banga Ameera ba ko ta fita ne”!?.

Dariya Taheer yayi yace “Alhamdulillah yanzun gashi nan ya fada da bakin sa.

Kallon sa yayi yace “Himm ba haka bane to wai ma ko haka ya akayi ne”!?.

Dariya Mami tayi tace “ni indai Ameera ina tana son shi ai shike nan sai ayi yar gida kawai.

Duk kunya ta kasa shi yace “wasa nakeyi fa Mami.

Ai ko da gaske kake yi mun baka shike nan cewar Taheer yana murmshi kwala ma Ameera kira yayi.

Zaune suke suna labari kira ta tayi anayi shi ya sanya ta tace “ina zuwa dan Allah kiyi hakuri Yaya Taheer na kira na”.

Murmshi maryam tayi tace “wai ni ai yanzun gida zani je fa”.

Bata fuska tayi tace “ni  dai gaskiya ba yanzun ba bar nadawo”da sauri ta fito daga cikin daki tana murmshi hango su Mami da Yaya Taheer tayi sai taga wani hadaden saurayi zaune karasowa tayi tace “gani.

Kallon sa yayi sannan yace “uhm ga Yayan ki nan yazo yace duk yau be ganki ba.

Kallon sa tayi  sannan ta zauna kusa da Mami tace”Yaya Taheer waye dan Allah.

Suleiman yace “ni ne mana ko baki gani ne ba ne”!?.

Harara ta watsa masa tace “Au dama kai ne kazo”tabe baki tayi tana kallon sa kasa kasa tana hararar sa.

*A bangaren Khadeejah kuwa*

washe gari da rana shinkafa da wake ta girka masa lokacin yana aiki sai da ya kamala sannan ya fito daga cikin dakin falo ya nufa wata hadader kula ce ya gani karasowa yayi gurin Khadeejah kuwa tana kwan ce saman kujera  tana kallon tv kamshin turaren captain kb tajiya shine zuciyar ta take bugawa da sauri sauri *Innalillah wa inna ilaihir raji un* cikin ranta tace “wai meya ke faru da ni ne mtsss.

Da sauri Captain kb ya daure fuska yace “ke tashi zaune”.

Turo masa baki tayi tana kallon kasa kasa tana hararar sa tace “ni wallahi nagaji yanzun fa na gama gyaran daki da girki fa.

Watsa mata mugun kallo yace ” wasa nake da ke ne tashi zaune nace”cikin masifa.

Tashi zaune tayi idanuwan ta sun cika da hawaye sai gan gara suke.

Tabe baki yayi sannan ya zauna saman kujera ya daure kafa d’aya saman daya fuskar sa babu rahama  yace “zuba mani abinci naci”.

Shiru tayi masa tana wasa da yatsinta wata irin tsawa ya daka mata sai ta tashi zata gudu saboda tsoro sai zaro ido tayi tace”to” durkusa kasa ta zuba masa lemon juice sannan ta zuba masa shinkafa da wake ta mike masa.

Binta yayi da mugun kallo yace “me kike nufe da ni ne halama ce maki akayi ni rago ne da zaki ta dirka mani wake da shinkafa to bashi nake so ba ki tashi maza da sauri ki daura mani yan ball.

Kuka ta fashe da shi sosai tace “haba dan Allah kayi hakuri bata karasa ba ya daga mata hannu yace “bashi nace kiyi ba dole yan ball zakiyi mani dan har kina son zaman lafiya a cikin gidan kuwa kuma sannan wannan abinci ke zaki cinye sa” yana gama fadar haka yayi kwan ce yar sa saman kujera ya lumshe idanuwan sa.

jiki babu kwari haka ta mik’e ta wuce kitchen ta daura masa abincin da yake so tana kuka tana girki kusan mintina 50 sannan ta fito da kula acikin kitchen kawo masa tayi tace “gashi nan nagama.

Shiru yayi mata kamar mai bacci haka yayi mata sai da ya ga alamun tagaji har ta fara kuka sannan yace” uhm  saman kai na zaki ajiye sa ko yayi bude idanuwan sa yayi yana kallon tv.

Jikinta rawa yake sosai gashi kanta yana ciwo sosai sannan ta ajiye masa abinci har ta mike zata wuce sai taji yace “kina nufe ni zan zuba mani abinci ko yaya”!?.

     Dawowa tayi ta zuba masa yan ball sannan tace “gashi nan”.

tashi zaune yayi yace “ci na gani kin san dole sai da haka kada ki zuba mani guba naci na mutu maza ci abinci nan”yana daure fuska.

Dafe kanta tayi tace “na koshi wallahi”.

Murmshin mugunta yayi yace “ko ki ci ka nayi maki dure da kai na.

Tana jin yace haka da sauri ta sanya hannunta ciki tana ci tana yatsinar fuska tace “to na koshi fa”!

Kallon ta yayi yace “haka ake cin abinci ne”!?.

Tashi tayi tana hawaye tace “to ai na koshi ne”.

kallon ta yayi sama da kasa  yace “ke banson iskan ci zauna ki ci abinci so kike ace bani ci da ke kenan”!?..

Idanuwan ta suka ciki da hawaye tace “to ai na koshi wallahi kuma ai bana jin yunwa”.

Tabe baki yayi ya cigaba da cin abincin sa hankali kwan ce ita kuma Khadeejah wuce daki tayi saboda kanta yana mata ciwo koda ta shiga fadawa tayi saman gado tana kuka mai cin rai sai da zazzabi ya fara rufe ta sannan tayi shiru har bacci ya dauke ta.

*A bangaren Suleiman da Ameera kuwa*

Zaune yake yana kallon ta da mamaki yace “Ameera.

Har cikin ranta taji kiran suna ta yatsin fuska tayi tace “gani fa”.

Gyara zama yayi sosai  da yake  babu kowa cikin falon  yace”kin ga yanzun na gyara halayena ya kamata ki bani dama na nuna maki soyayya da kauna”.

Zaro ido tayi tace “tabba Allah ya sauwake ni ba zanyi soyayya da mugu ba gaskiy.

Dan marairaice mata yayi yace “haba Ameera sai ka ce ba musulmaba kada ki manta bawa yana ma Allah laifi kuma sannan ya roƙisa kuma yayafe masa dan Allah kiyi hakuri ko khadeejah da nayi wa wannan abun, shairin sheɗan ne kuma ta yafe mani ya kamata ace kin yafe mani ke ma”.

Shiru ta na dan wani lokaci sannan tace ” to shike nan babu damuwa Allah ya yafe muna baki d’aya…..

Amin ya Allah cewar Suleiman.

*A bangaren Taheer kuwa*

Zaune yake cikin motar da shi da Maryam kallon ta yayi yace “Maryam na san zakiyi mamaki jin abun da zan fada to ba abun mamaki bane alkhairi ne yazo da ni.

Sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da hannunta tace “to Allah ya sa muji alkhairi.

Murmshi yayi yace “Amin ya Allah   Inason ki kuma so bana wasa ba kuma ni Auren ki zanyi nasani kina da wani saurayi Amma.

Da sauri Maryam  ta kalle Taheer cikin idanuwan sa taga hango irin son da yake mata ajiyar zuciya tayi  tace “Alhamdulillah dama nima ina jiran wannan rana da zaka furta mani so kuma ni amince dari bisa dari .

Taheer yace “Alhamdulillah Ashe akwai ranar da zaki aminci mani wai halama dama kina so na ne”!?.

Rufe fuska tayi tana dariya tace “eh mana ko kana mamaki ne”……..

*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*

‍🧑🏻‍✈️ *CAPTAIN KABEER*🧑🏻‍✈️

*RUBUTAWA*

*HASSY SOJA  ce*✍🏻

*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

“`BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI  JIN’KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN“`

*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA  YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA’DI*

*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎

*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE A AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*LAST PAGE*🔚🔚🔚🔚

🅿️7️⃣6️⃣%8️⃣0️⃣

*_________________*🖊️

         Rufe fuska tayi tana dariya tace “eh mana ko kana mamaki ne”!?.

Murmshi yayi sannan yace “kwari ma kuwa dole nayi mamaki mana.

Himm ai ba abun mamaki bane alkhairi ne saboda lokacin da Ameera suke zuwa gurina babu abun da ban sani ba game da kai Yaya Taheer wallahi ni tun lokacin da naganka na kamu da sonka Amma sai dai kashi wata tarigani.

Jin jina kai yayi yace “to  meyasa baki fada mani kina sona ba”!?.

Dariya Maryam tayi tace “Haba dai nace inasonka kuma tabba ai bazan iya fada maka ba saboda mu mata muna da al, kunya fa nace ni fa ko cewa nayi wallahi ko soyayyar zata kashe ni to ban fada wa kowa ba sai sirin zuciya ta .

Dariya yayi sosai sannan yace “gaskiya Ina Ashe ina matata kusa da ni Allah sarki yanzun sai nayi ta biyu da ke”.

Cikin shagwaba tace “ni uhm uhm uhm uhm uhm uhm Allah bazan zauna da kishiya.

Zaro ido yayi yace ” kina nufen bazaki Aureni ba kenan ko”!? .

Da sauri Maryam kallon sa tace “ni wallahi ba haka nace ba ni fa nafi son na zauna da ni da mijina mu sha soyayya fa”da sauri ta rufe fuska tana dariya.

Taheer yace “Alhamdulillah Alhamdulillah yanzun nasamu mata Allah ya nuna muna lokaci lafiya mu sha soyayyar mu.

A bangaren Suleiman kuwa yanzun komai yana tafiya  dai dai Ameera ta amince da soyayyar sa wata irin soyayya yake nuna mata sosai yanzun Auren su saura kwana biyu biki.

*A bangaren Khadeejah kuwa*

ko ina da ko ina ta gyara sosai sannan kuma girki kullum sai ta canza kalar abinci yau ma ta gama girki kusan mintina 50 tana zaune falo tana chat da Ameera kamshin turaren captain kb tajiya shine zuciyar ta take bugawa da sauri sauri cikin kafin hali tacigaba da chat  voice Ameera tayi mata  tace “Amarya kina kamshi wai Yaya Captain kb ne ko ya koma America”!?.

Zaunawa yayi saman kujera ya daure kafa d’aya saman daya fuskar sa babu rahama yana kallon tv Amma duk abun da take yana kallon ta ta gefen idonsa itama sai tayi mata voice tace “wallahi lafiya klau muke yana gari be koma ya su Mami da Yaya Taheer “!?.

Koda ta dago idanuwan ta sai cikin nashi da sauri  ta daura idanuwanta ta cigaba da chat Captain kb yace “ke zubo mani coffee zan sha.

To kawai taci da shi sannan ta tashi ta wuce kitchen coffee ta hadu masa sannan ta fito daga cikin kitchen falo ta nufa a hankali koda ta karaso guri tace “gashi” ta mika masa kenan ya dago hannu Ashe be amsa ba kawai ta saki coffee ya zube mata kafafuwa sai kofin ya fashe kasa ihu ta saki ta fadi kasa tana kuka sosai hankalin sa ya tashi sosai yace “Subhanalillah sannu da sauri ya dauko ruwan sanya yazo ya zuba mata yana goge mata kafafuwanta yana mata sannu kallon sa take hawaye na zubo mata ga kumatu kuka ta fashe da shi sosai tace “wayyo Allah na wayyo Mommy wayyo Hajiya wayyo daddy wayyo kafafuwa na kuka take sosai.

Har cikin ransa yake ji yace “Am sorry Khadeejah kina iya tafiya”!?.

Kuka tana girgiza masa kai duk ya rude da sauri ya dauketa kamar ya dauke jaririya rontsin idanuwan ta tayi ta turo kanta cikin kirjin sa shiga cikin dakin ta yayi saman gado ya daura ta yana mata sannu sannan yace “Am sorry mekike so yanzun”!?.

Girgiza masa kai tayi tana hawaye tace “to ai na koshi wallahi”.

Murmshi yayi yace “sannunki kinji Allah ya sauwake bari na kira doctor yazo ya duba k ko da allura ce sai yayi maki”.

Kara fashewa da kuka tayi tace “ni dai wallahi bana son allura.

Shiru yayi sannan ya juya ya fita daga cikin dakin falo ya nufa ya zauna saman kujera ya lumshe idanuwan sa sannan ya kira d’aya daga cikin sojojin sa ya turo masa kudi yayo masa shopping .

binsa tayi da kallo sai da ya fita daga cikin dakin sannan tayi ajiyar zuciya tana gyara kwan ce tana jin radadi konewar da tayi mintina 30sai gashi yashigo cikin dakin da sallama hannun sa rike da leda mai zane sai ya rasa me zai ce mata kawai  yace “Amma Khadeejah tashi ki sha wannan sannan ya juya ya fita daga cikin daki tashi zaune tayi tana tunani wai yaushe Yaya captain kb ne ya canza ta lura kwana biyu ya canza ko lafiya oho jawo ledar tayi sannan ta bude ayaba da lemo ne acikin da apple sai madara koma wa tayi ta kwanta bacci yayi gaba da ita.

Misalin 3:39 sannan ta falka daga bacci ruwa ta watsa sannan ta gyara cikinta sosai sannan ta dauko rida da skit na atamfa mai ratsin ja da baki kayan sunyi mata kyau sosai sannan ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi sosai duk da batayi kwaliya ba tayi kyau sosai sannan fito daga cikin dakin falo ta nufa a hankalin  kujera ta biyu ta zauna lokacin babu kowa cikin falon ya fita wayar ta dauko saman d’ayar kujera duba chat din da suke da Ameera tayi voice biyu taga misalin karfe 12:00 pm kun nawa tayi tana sauraro tace ” Khadeejah yau saura kwana biyu biki na da Yaya Taheer dan Allah ki shigo please my sister.

Da sauri ta kira ta lokacin Ameera tana zaune da kawayen ta rigging din wayar ta tajiya da sauri ta duba suna my sister tagani dauka tayi tace “my sister dazu nayi maki magana fa.

Ajiyar zuciya khadeejah tayi tace”wai da gaske kike ko wasa”!?.

Ameera tace “wallahi da gaske nake da ni da Yaya Taheer fa sai dai kin zo dan Allah ki fadawa Yaya captain kb please.

To shike nan babu damuwa Allah ya kawo shi lafiya cewar Khadeejah.

Amin ya Allah yayi tafiya ne”!?.

Wallahi ban sani ba kawai ban gan shi ba bata rufe baki ba sai gashi ya shigo cikin falon da sallama.

To gashi nan ma ya shigo cikin falon ina tunani daga masallaci ya fito.

Dariya Ameera tayi sannan tace “ikon  Allah ke bazaki tashi kije ki tarbesa ba topa dama haka kuke soyayyar.

Dogon tsaki tayi tace “ban son iskan ci fa to sai anjima kawai.

Da sauri Ameera tace “Afuwa my sister sai kinzo.

Kashe wayar ta tayi tana bata fuska karasowa yayi gurin Khadeejah yace “ya jikin”!?.

Dago idanuwan ta dube sa tace “Alhamdulillah naji sauki”.

Zaunawa yayi saman kujera yace “Masha Allah Allah ya tsare gaba.

Amin tace da shi daga nan babu Wanda yace komai haka suka cigaba da zauna tunani take ta ina zata fara tace “Amma dan Allah inaso zanje biki”!?.

Be kalle ta ba Amma yana jin Abun da take fada shiru yayi sannan yace “ke da baki da lafiya zaki ce wai zakije biki to bikin waye”!?.

Idanuwan ta suka ciki da hawaye tace “to ai biki Ameera ne zan tafi.

Kallon ta yayi sama da kasa yace “wai ke yaushe zakiyi hankali ne wai”!?.

Kuka ta fashe da shi sosai tace “haba danAllah kayi hakuri kabari naji daga shi bazan kara zuwa ko ina ba.

Share ta yayi yana jin kukanta har cikin ransa yace “dan Allah kiyi mani shiru please zaki sanya mani ciwon kai.

Da gudu ta wuce dakin ta tana kuka kamar ranta zai fita har bacci ya dauke ta.

Dafe kansa yayi yace “wallahi wannan yarinyar zata sanya mani ciwon ka ko dan taga ni ina tausaya mata ne mtsss aikin banza kawai.

Sai bayan isha’i sannan ya shigo cikin falon Amma be ganta ba sai sai ya fara tunani fushi take da shi fa sannan ya wuce dakin ta koda ya shiga cikin dakin zaune take tayi tagumi da sallama karasowa yayi gurin Khadeejah yace “to shike nan babu damuwa yaushe ne biki.

Da sauri Khadeejah ta dago idanuwan ta dube sa tace “gobe nake so na tafi saura kwana biyu bikin.

Ok babu damuwa Allah ya kaimu Amma kwana biyu kawai zakiyi saboda nima tafiya zanyi.

Da sauri ta rungume sa tace”ina godiya sosai Yaya captain kb Allah ya saka da alkhairi.

Zaro ido yayi yace “”Amin ya Allah to sakeni.

Da sauri ta sake sa wata kunya ce ta kamata girgiza kai yayi yace “to ki hada kayanki da wuri saboda driver zai kai ki.

To shike nan babu damuwa yana fita daga dakin ihu tayi cikin farin ciki tana tsalle tsalle saman gado tace”uhm  yau zanyi kwana farin ciki”, saukowa tayi saman gado ta dauko akwati kala biyar ta zuba ciki sannan ta rufe.

Washe gari tunda asuba tayi wanka ta gyara sannan tayi masa lafiyayin abinci mai rai da lafiya ta ajiye masa saman dani table wani Soja ne ya shigo cikin falon yace “madam idan kin gyara ki fito muna jiranki.

Kallon sa tayi tace “ok shiga cikin ka dauko akwai na.

ok madam akwatin ta ya dauko sannan ya fito daga falon ita kuma Khadeejah wuce dakin sa da sallama lokacin zaune yake da kayan sojoji yana aiki amsa mata sallama yayi ya cigaba da aikin sa.

Karasowa tayi tace “Yaya captain kb ina kwana”!?.

Lafiya klau har kin gama gyara wa ne”!?.

Eh mana gashi nan har afita da kayana.

Kudi ya dauko yan ban duri ban duri yace “gashi nan kiyi masu tsaraba.

Amsa tayi tace “nagode sosai Allah ya biya”har tajuya sai taji muryar yace” Amma ina tunani daga bari dai kawai ki zauna cikin shiri kawai Allah ya tsare.

Amin ya Allah sannan ta fita daga cikin dakin waje ta nufa koda ta shiga cikin motar sai garin kaduna.

A bangaren Ameera kuwa gobe ne za,a daura masu Aure gida ya ciki  da mutane misalin karfe 2:00pm sai wayar Ameera ta fara rigging da sauri ki dauka tace ” har kin iso ne”!?.

Khadeejah kuwa tace “eh gamu nan cikin gidan mana.

gudu Ameera ta fito daga cikin dakin ta fito waje mota black  ta gani da sauri ta karasowa gurin ta bude mata mota tace welcome back my sister dafatan kinzo lafiya”!?

Murmshi Khadeejah tayi tace ” uhm Amarya zamani lafiya klau alhamdulillah.

Wani soja ne ya fito daga cikin  motar yace “ina kwana Hajiya”!?.

Murmshi Ameera tayi tace “Alhamdulillah Amma muje daga cikin mana.

Mai gadi yazo nan cewar Ameera.

Da sauri yazo yace” gani Hajiya.

Yauwa wannan sojan da shi da driver zaka nuna ma dakin baki kaji ko sannan suka wuce cikin gidan.

Bayan sun shiga cikin falon sannan aka biyo ta da akwatin ta kawar Ameera ta amsa akwati aka shiga da shi cikin dakin bayan Khadeejah ta gaishe da Mami sannan suka koma daki zaune sukayi Ameera tace “Allah  mai iko yau gashi kin zo biki na.

Dariya Khadeejah tayi tace ” uhm wannan waye sace zuciyar ki haka ne”!?.

Ajiyar zuciya tayi sannan tace “wallahi nima kai na banyi tunani zanyi Aure yanzun ba ko da yake komai na Allah ne ( littafin Ummu ihsan) kin san ko waye”!?.

Gyara zama Khadeejah tayi tace ” Aa sai kin fada.

Bakuwa bane face Suleiman kuma wanda kika sani cewar Ameera tana kallon khadeejah.

Zaro ido tayi tace”Suleiman kuma wanda ya sace ni”!?.

Kwari ma kuwa Khadeejah kin san bazanyi maki karya ba ko wallahi su Mami da Yaya Taheer suka sanya ni gaba shiyasa.

Ajiyar zuciya khadeejah tayi tace “ikon Allah to Allah ya bada zaman lafiya.

Amin ya Allah.

Rigging din wayar ta tajiya da sauri ta duba suna my husband taga ni dauka tayi da sallama.

Ajiyar zuciya yayi yace “wai ke ina kika shiga ne ina kiranki Amma baki dauka ba.

Shiru tayi tana sauraro sa tace “ni wallahi ban gani ba fa kuma wayata na cikin Jakata.

To shike nan babu damuwa ina tunani gobe za mu zan shigo daga nan zamu wuce America fa kada ki ce ban fada maki ba to.

Zaro ido tayi tace”gobe kuma to Amma ba dani zaka ba ko”!?.

Daure fuska yayi kamar yana ganta yace “Tare zamu kuma mommy tace mu tafi tare dan haka ki shirya “zatayi magana ya kashe wayar sa.

Kallon ta Ameera tayi tace “lafiya dai ko”!?.

Dafe kanta tayi tace “wai gobe America zamuje wallahi kada kigani irin wahalar da yake bani.

Zaro ido Ameera tayi tace “haba dan Allah wai da gaske “!?.

Wallahi kuwa kuma wallahi inda na kalle cikin idanuwan sa soyayya ta ce zallah  acikin idanuwan sa fa.

Ajiyar zuciya Ameera tayi tace “Alhamdulillah ai ko yanzun ya sani kina da farin jini kuma yana kishinki dan haka ina baki shawara ki rungume mijinki wallahi kada ki bar wata tashigo maki cikin gida.

Shawararori ta bata masu kyau sosai gashi dare yayi sosai can kuma sai gashi ya kara kiran ta kamar bazata dauka ba sai ta dauka.

Ajiyar zuciya yayi yace “bakiyi bacci ba”!?.

Gyara kwan ce tayi tace “eh banyi ba”!?.

To meyasa baki yi bacci ba ko tunane kike”!?.

Tunani kuma tunani waye zanyi ni fa bana tunani kowa fa tana murmshin mugunta tacigaba da cewar “sai dai ban sani ba ko akwai wanda yake tunani na”!?.

Cikin ransa yace “wato bata ma kewata bale  tunani na mtsss aikin banza kawai.

Sai da safe ya kashe wayar sa.

Dariya tayi sosai sannan tace “Alhamdulillah kashigo hannu” tana tunani daga nan har bacci yayi gaba da ita.

Washe gari da rana aka daura Auren Ameera da Suleiman da Taheer da Maryam bayan an daura Aure aka kai amare gidan mazaje su nace Allah ya bada zaman lafiya.

Washe gari da safe Khadeejah tana zaune cikin motar sai airport koda suka isa Captain kb yana jiran su fitowa tayi daga cikin motar wuce wa sukayi suka shiga cikin jirgi sai America.

bayan sun isa america lafiya gida suka wuce kowa ya gaji wanka yayi sannan ita tashi ta watsa ruwa sannan ta fito kayan taga saman gado kallon kayan tayi tace “ikon Allah yau kuma himm bazan baka haƙinka ba sai gobe sanyawa tayi sannan ta kwanta tana hutawa.

Captain kb kuwa koda ya shigo cikin dakin kwan ya sameta tunda taji kamshin turaren sa da sauri ta rufe ido kamar mai bacci.

Zaunawa saman gado yayi yana kallon ta yace “Alhamdulillah Allah nagode maka da kabani kanwa amtsayin matata ta sunnah Alhamdulillah”kwanta wa yayi ya rungume ta yace “uhm my baby ai nasani idonki biyu dan haka yau ce ranar farin ciki mu da ni da ke.

Bude idanuwan ta tace “uhm uhm uhm uhm uhm uhm to ai ni gan girma ba.

Dariya maganar ta tabashi yace “ai yanzun zaki girma kuma idan baki bani haƙina,  ba da ke da Allah.

Hawaye ne suka zubo mata ga kumatu kuka ta fashe da shi tace “ai ba sona kake ba cutata ce kawai zakayi.

Lashe mata hawaye yayi yace “Aa ni ina sonki tun kina karama nake da burin na Aure ki kuma gashi kuma lokacin da kika girma baki jin magana sai rashin kunya.

Turo masa  baki tayi tana kuka tace “to ai ni ban sani ba kuma nima inasonka tunda na fara ganka shiyasa ma nake zuwa gurin mommy saboda na rinka ganka.

Cikin da mamaki ya tashi zaune yana kallon ta yace “da gaske kike “.

Kara rungume sa tayi tace “eh mana.

Nima haka duk ranan da na shigo gari dole sai na ganki hankali na zai kwana akwai lokacin da na dawo america wallahi kin Zama babbar mace to a lokacin hankalina ne ya tashi sosai kada wani ya Aure mani ke Ashe ke tawa ce ina tunani kin amanta abun da nace maki ko.

Gyara kwan ceya tayi saman kirijinsa tace “Himm lokacin da kace wai baka tashi mani Aure kuma duk rana da kaganin da wani saurayi sai ka karyani wallahi nayi kuka sosai daga baya kuma sai nayi dariya.

Dariya sukayi sosai sannan Yace “I love you my wife ina alfahari da ke.

I love you my husband ina kaunarka sosai………

*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALLAH NA GODE MAKA DA KABANI IKON KAMALA LETTAFI MAI SUNA  (CAPTAIN KABEER)  LAFIYA*

*INA ROKON ALLAH YA YAFE MANI KORAKORAN DA NAYI ACIKIN WANNAN LABARI*

*SAI MUN HADA CIKIN SABON BOOK DIN NA MAI SUNA…….*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including  your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

بسم الله الرحمن الرحيم

*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button