Sponsored Links
Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 25

Sponsored Links

Page 25

Murmushi kadan ummu tayi,qarara ta hango kishin widad a idanun halima,ta rasa me yasa haliman ta kasa sabawa da hakan,sai ta gyara zama

“Mu dinma uwayenku da sanda aka aurar damu banajin munkai ya widad din,a gidan muka iya abubuwa,tun mun kwamacala har muka qware,yanzu gashi ba’a ce mune muka haifeku ba” kauda kanta anty halima tayi,tasan dama duk yadda takai bakai isa ka fadi wallen widad ko ka kusheta ga ummun ba.

Yau din tun qarfe takwas ta qudunduna a bargo cikin dakin ummu,bayan ta gama qarewa kayan data gani jibge a dakin ummun kallo,tun shekaran jiya taga ummun nata jibge kaya a dakin nata,itadai bata ce ga dalili ba,ta dan tura baki taja bargo abinta,bacci yau takeji da gaske,don ko sassan anty madina da aka cika ana hira yadda aka saba taqi zama,bugu da qari kuma yadda suketa faman kiranta da sunan amarya,wanda ta dauka duka tsokana ce irin tasu yau ta sauka a kanta suka tasota gaba,ita kuma bataso.

Fakare tayi tana jiran bacci ya iso,gefe daya tsoro tsoro takeji saboda ummun tana wajen dattijon mijinta,buda qofar dakin akayi a hankali,sai ta tada idonta tana kallon me shigowar ba tare data tashi ba,ummun ce,hannunta dauke da babbar baqar leda

“Yauwwa,gwara ma da bakiyi baccin ba,tashi” kai tsaye ta miqe din,don itama tanason yiwa.ummu tambayar

“Ummu…wai wannan kayan,na wanene duk sun cika miki daki?”

“Kayan aurenki ne” ta amsa mata gaba gadi tana kallon fuskar widad din,cike da fargabar yadda zata kalli zancan,kada ta watsa musu qasa a ido.

Idanun ta fitar,fuskarta babu wani emotion saina mamakin

“Aurena ummu?,duka wadan nan kayan?” Kai ta gyada mata

“Eh,harda wasu ma” ta fada tana bude mata ledar

“Wannan babanku yace ki zaba iya wadanda kikeso za’a dinka miki” da mamaki ta sake duban ummu

“Wai duka nawa ne?”

“Kadanma kika gani shalele ta,za’a kawo lefe a kawatuna duka naki” murmushi ya subucewa widad,kawai taji farincikin na kamata

“Harda kayan kwalliya ma irin nasu anty ramziyya?”

“Sosai,inajinma yafi nasu” ta fada tana murmushi ganin bata dauki zancan da zafi yadda ta saba ba,da wannan hirar ummun ta dinga hilatarta tana jaddada mata zancan auren,quruciya ta sanya widad din bata wani damu ba,saima cika da tayi da zumudin zuwan ranar da za’a kawo mata kayanta,wanda ummun tace mata sai ranar daurin aurenta.

********Wasa gaske saiga shirin biki nata kankama daga bangarensu widad,sam bata wani damu ko daga hankalinta ba,abinda ya baiwa kowa mamaki,yayin da wasu kuma hankalinsu ya kwanta ganin bata qi yadda ta saba ba,’yan adawa kuma fadi suke

“Shegiya dama da guntun wayonta,gashi tayi luff kamar ba ita taqi ‘yan uwanta har mutum biyu ba” oho,ita dai sabgar gabanta takeyi kawai,tana lissafin ranar da za’a kawo mata kayan kwalliya.

Daga bangaren su abbas kuwa maganar ta fara yawo,da yawa daga cikin dangi wadanda sukaci burin zuwan wannan rana,ranar da abbas zai qara aure labarin baije musu a dadi ba,wadanda suka jima suna addu’ar hajiyan ta sanyashi qara aure saboda halayen hafsa,duk sai gwiwarsu tayi sanyi,hajiyan ta musu ba zata,irin abbas din shi kowa ke kwadayin samu,saboda alamun wadata da aziqi dukka sun fara bayyana a tattare dashi.

Tabbas hajiyan tasan da wannan,shi yasa tayi musu wannan ba zatar,ta kuma zartar da wannan hukuncin,fatanta daya abbas din ya samu inuwar da zai huta,ya kuma samu sanyin idaniyarsa.

Har a sannan hafsat din bata da labari,gidanta ba gidan zuwan ‘yan uwan abbas bane,bama su kadai ba,hatta da nata dangin,saboda wata iriyar jarrababbiyar rowa da take da ita,muguwar sa’a ka taka idan kaje gidan ka samu tarbar pure water bare abinci,kusan anty ummee ce kawai ke samun wannan daga gareta,shi kuwa abbas,bayan ya ajjiye wa hajiya dukkan wani abu da yasan zata iya nema daga gareshi,komawa yayi kaduna,amma yace mata cikin satin daurin auren zaiyi qoqarin zuwa da wuri,da fatan alkhairi ta bishi,domin kuwa ita ya gama mata komai,sai fatan dacewa bisa niyyar alkhairin data nufaci rayuwarsa dashi.

************

Daga can tsakiyar ‘yan jaridar dake dauke da nau’ikan kayan aiki daban daban,ASP ABBAS SARKI ne tsaye,sanye da uniform din ‘yan sanda daga dace da structure na jikinsa,ya kuma yi masa kyau ainun,iya yadda yake tsayen kadai ya isa ya gaya maka cewa jajirtaccen police ne,wanda ya qware a aikinsa

“Wannan shine abinda ya faru a taqaice,we will let you know when the investigation is completed”. Sai ya zare hannunsa daga aljihu yana shirin wucewa,amma suka sake yunquro masa da tarin tulin tambayoyinsu,rasa wacce zai amsa yayi,saidai akwai wani cikinsu da yafi kowa matsa masa da tambayar

“Amma yallabai,labari ya iskemu cewa kai da kanka ka gudanar da wannan aikin,kuma kaine ka samu nasara cafko su,shin meye gaskiyar wannan al’amari?,don dama jama’a sun dade da saninka da kuma ficenka wajen gudanar da aiki?”

Wani miskilin murmushi yayi wanda yake cike da tarin gajiya,murmushin da har yau hafsa ta gaza gane irinsa har sai ya buda baki ya magantu,yasa hannu ya cire hular police din dake kansa mai zubin P-cap,cikin muryarsa mai zurfi da kwarjini ya fara amsa tambayar tasa,bayan tarin jama’ar dake wajen sunyi shuru suna jiran amsa

“Ko ni nayi wannan aiki,ko bani nayi ba nasara ce,nasarata kuwa nasarar dukka jami’an tsaro musamman na ‘yan sanda dake wannan qasar ne,muhimmin abu aci gaba da yi mana addu’a,fatan nasara” ya fada yana saluting nasu,sannan ya juya sa sassarfa ya shige ciki gudun kada su sake tsaidashi,sai wajen ya rude da muryoyinsu cikin farinciki kowanne na bawa kafar yada labaran nashi cikakken jawabi.

Tsaye yayi gaban table din office dinsa bayan ya ajjiye hular hannunsa a kai,saiya zare agogonsa ma ya dorashi saman hular,ya furzar da iska yana duba lokaci,ya riga yayi alqawarin barin Kaduna a yau zuwa bauchi,lokaci yanata quracewa ba tare da ya shaidawa hafsa komai ba,yanason ta fara ji daga bakinsa shi yasa ya hana kowa ya gaya masa,duk haukar da zatayi ta yita ta gama,yasan tabbas akwai case babba

Uwa uba kuma mai girma gwamnan bauchin yanason ganinsa,ya bashi appointment gobe da yammaci,zai sameshi gidan gonarsa,to dole tafiya ta kamashi a yau,saidai yana jin komai ma zaizo masa da sauqi da yardar Allah,tunda aikin da yake kwana ya kuma tashi dashi ya kammalashi,duka suspect dinsu suna hannu.

Wayarsa ya ciro da sirritaccen layinsa da ba kowa ya sanshi ba,ya kira wata number yayi confirming samun flight daga kaduna zuwa bauchi sannan ya aje wayar,ba kasafai ya fiya zirga zirga a jirgi ba,yafi ganewa yayi driving da kansa wani lokaci,yana tafe yana karantar hanya da inda tsaro yayi qaranci ko kuma inda komai yake tafiya dai dai,amma a yau din bashi da zabi illa yabi jirgin.

Taku biyu ya qara kamar zai fita,sai kuma ya fasa,ya sake daukar wayar yayi kira na sakanni ya ajjiye,ya shiga toilet ya kama ruwa sannan ya fito,ya duba dukka wani abu da yake da buqata cikin office din ya hada waje guda,bayan yayi wasu rubuce rubuce a wasu files sannan ya fito.

Daya daga cikin juniors dinsa ne yake driving nasa zuwa gida,yana a motar ya kira hafsat din don ya shaida mata tahowarsa,mimi ce ta fara daga wayar,sai data gama shirmenta sannan uwar ta karba wayar

“Kuna lafiya keda yaran?” Ya fadi don yasan zaiyi wuya ta fara tambayarsa lafiyarsa kota gaisheshi

“Lafiya qalau muke” ta amsa masa cikin ranta tana mamakin yadda ya sauko daga laifin data masa haka da wurwuri,duk da dama shi din bai cika riqo ba,amma a yadda taga ransa ya baci jikinta yayi sanyi,ta kuma aza zai mata hukunci mafi tsauri ne

“Am on my way to bauchi in sha Allah,two to three hours”

“Tooo….basai Friday ko Saturday ba?” Goshinsa ya murza kadan,ya salam,a nashi zaton tayi murna da yace zai dawo din ko?,amma saita buge da tuna masa ranar dawowarsa batayi ba?

“Na sani,inda muhimmin abu ne da zanyi a nan”

“Okay to,a taho mana da tsaraba”

“Yayi…..me zan samu?” Ta fahimci sarai me yake nufi,amma sai tayi kamar bata gane din ba

“Kamar me kenan?” Ta fada tana dan bata fuska,duk da ba ganinta yakeyi ba,zai dawo yanzu zai fara damunta da tsarabe tsarabensa.

“In so samu ne tuwo nakeso” tanason musa masa amma kuma batason bata saukowa da yayi daga fushin da yayi da ita ba tare data bashi haquri ba

“Xan qoqarta” ta fada cikin ranta tana jin ba zata iya yi ba

“Alright,saina qaraso” ya amsa ta ba tare da yaja doguwar hira da ita ba.

Bai wuce hutun awa yayi cikin gidan nasa ba,ya shirya ya wuce airport,gab da sallar isha’i cikin gidansa tayi masa, samuel ne yaje ya daukoshi ya ajeshi,ya shiga gidan nasa dauke da jakarsa,wata a hannu wata a kafada,sabida baya barin kowa da kowa ya shiga masa gida.

Yana shiga falon yanayinsa ya canza gaba daya,saboda qarancin tsafta da falon yake da,babu wani alamun qamshi ko qanqani da zaka iya ji daga falon,wala’alla ma idan ka taki mummunar sa’a hancinka ya iya shaqo maka qauri mara dadi dake ratsowa tun daga kitchen din dake falon zuwa hancinka.

Wannan ba baqon abu bane a wajensa,yayi fada yayi nasiha amma jiya iyau babu wani ci gaba,saidai yaci gaba da haquri kau da kai da nusashe ta,duk da hakan tana ganin kamar gazawarta yake gani,tunda dai tana iya nata bakin qoqarin a ganinta.

Yaran da suka garzayo suna masa oyoyo ya daure ya duqa ya rungumesu cikin jikinsa,ko daya babu wani kyakkyawan yanayi a tattare dasu suma,ita kuwa saita aje wayar hannunta tana dan sosa kai irin na marasa gaskiya,tare da qoqarin yi masa sannu da zuwa.

Amsawa yayi yana kallonta,wani hargitsatsen kaya ne a jikinta,atamfar dake jikinta ya soma gajiya da ganinta,idan zai iya tunawa da ita tazo gidan,kuma har yau ta gaza bada ita kyauta saboda tsabar baqar rowa,sau tari yakan tambayi kansa menene amfanin karatun da hafsa tayi?,tabbas da yasan haka zata ci gaba da kasancewa,baiga abinda zai sanya ya barta ci gaba da karatun ba,don wadan nan dabi’un nata babu wanda zai gani ya dauka yasan bihim a boko.

“Muje ku rakani na shirya” ya fada yana kada kan yaransa,saita bi bayansu da harara

“Agwagwa sarkin wanka” tafada,don tasan zuwa zaiyi ya hada ruwa ya musu wanka,ita duka ba wannan bane ya dameta,yadda dafa dukan shinkafar da tayi masa ta kama ta kuma yi qauri da kyau,ta yadda zata masa bayani take tunani,tasan halinsa,sarai baya wasa da cikinsa,ya baiwa abincinsa muhimmanci sosai.

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijer๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ

 

[2/21, 4:17 PM] It’s Queen Meenali๐Ÿ‘ธ๐Ÿป: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button