Sponsored Links
Hausa NovelsHausa Novels and Love StoriesKyalKyalin Kauna Hausa Novel

KyalKyalin Kauna 34

Sponsored Links

EPISODE 3️⃣3️⃣

Jama’a ina sababbin amare da matan aure dasuke so su koyi abubuwan da basusan da akwaisu daba, M shakur dinku is back again with another banging class na MATAN AURE dazan fara muku next month dazaran nagama wannan novel din na KYALKYALIN KAUNA💃💃💃

Classes namu asabar da lahadi ne na tsawon wata daya wato 4 good weekend classes kenan.
Ki shigo class dina lemme teach you how to catch your husband a hannu ba kayan mata ba magani tsabagen iyawa kawai da kwarewa a harkan oza room🥰
Registration is 1k
Chat me up idan kinason shiga wannan class din nawa.
wa.me/+2347012181461

Hannunta Hajiya takai da sauri tadaura kan kuncinta inda Maheer mara ta sosa dan she can’t believe Pablo just slapped her kafin tadago fuskanta tazubamai idanunta dasukai jajir suka cicciko da ruwa amman basu zuboba cikin wata kalan murya mai bala’in rauni tace “Pablo ni ka daga hannu ka mara because of yarinyar chan daka santa for just few days”? Sosai Maheer ke kallonta ranshi yayi masifaffen baci dahar jijiyoyin kanshi sun fito yadawo sak Pablo dinshi, zuciyanshi wani kalan tafarfasa yake na innanaha, cikin kakkausan murya yana kallonta right in the eye yace “duk randa kika sake attempting hurting that girl I will leave you forever Wallahi!” Yay rantsuwa mai kyau, wani mummunan faduwa gaban Hajiya yayi jin Maheer yagaya mata kalman zai rabu da ita har abada abinda bai taba fadamata ba all this years harda rantsuwanshi ba, dasauri tazare hannunta dagakan kuncinta takai dasauri zata tabashi wani kalan ihu yamata saida gidan ya amsa. “Don’t touch me! Don’t Maryam!” Chak ta tsayar da hannunta tana kallonshi kirjinta na racing, idanunshi sunyi jazur yace “don’t you dare touch me” yana maganan yajuya yafita daga dakin tareda bugo kofanta yafice sauka yayi kasa azuciye yayi waje dasauri Dan dake waje yabishi yace “Sir ina zaka bakasa riga ba” ko kallonshi Maheer baiyiba da sauri yake tafiya yawuce parking space wani power mahaukacin machine dashi kadaine pake awurin yahau ya kunna hamlet dake kan machine din yazare yawani jefar akasa saura kadan yasami Dan ya matsa da sauri yawani kalan tada machine din yayi hanyar gate dasauri sojan yabude mishi gate yafice Dan yabishi da kallo yana mamaki waya batamai rai haka, Oga nada bala’in fushi, bala’in fushi dazai iyaje yajima kanshi ciwo yanzu haka kuma anytime yake fushi he just wanna be alone baiso abishi idan ba kanaso fushin ya hauhawa bane don’t even follow him.

Yanda Maheer ke gudu zaka dauka yana kokarin kashe kanshi da gangan ne acikin dajin, kanshi kawai yadau chaji yarasa makemai dadi aduniya, he can’t get yarinyar commissioner nan out of his head, his mind his thoughts, this was problem dayake kokarin ya kawar aranshi abinda yasa yaje garden getting fresh air kenan, yana wajen sai fadomai take arai abinda yasa yataso yazo kenan all yasami Hajiya trying to drug the girl, kawai jiyayi kaman shi taje kokarin drugging, the way tarike hancin yarinyar yaji kaman nashi tarike, baitabajin ya tsani Hajiya for anything ba sai yau sabida yarinyar commissioner din nan, drugs are abubuwan dayake saidawa, su Nas waye waye har ita Hajiyan nasha but he never felt bad, baitabajin komi aranshi ba but why is he feeling this bad sabida Hajiya tayi kokarin bama that girl? Shi ko workers nasu sukai laifi saidai yasa akaisu amusu hukunci baijin yataba daga hannu yataba wani ba but yau all because of this girl ya mari Hajiya, and bazaiyi karyaba he wanted to do more dan at that point data kama hancin Yasmeen he wanted shima yazo yakama nata takasa numfashi harsai tai slumming to death but he couldn’t sabida Yasmeen dake wajen, why is he this angry sabida yarinyar nan, why is his heart going crazy sabida Hajiya try to hurt her, why why whyyyyyy”? Daidai machine nashi yaci karo dawani dutse dashi da machine din suka zube akasa saida hannunshi yaji ciwo amman ko ajikinshi sama ya kalla tareda kwala wani kalan ihu shikadai yace “what is wrong with me?” Ya tambayi kanshi, kafin ya lumshe idanunshi kawai yayi shiruuuu, yakai kusan 1hr kwance akasan wajen babu riga ajikinshi baidamu da wani abu yasameshi ba sannan yadan karkace yazaro wayanshi daga aljihunshi ya danna wayan takawo haske sannan ya shiga daddanna number yay dialing number saikuma dasauri ya katse kiran ya yarda wayan akasa yace “shit” kara wayan yashigayi hakan yasa yakalli wayan yaga number daya dialing ya katse ke kiranshi that means call din dayayi yariga yashiga kafin ya katse, kin daukan wayan yayi harta katse, sake kira akayi hakan yasa ahankali yamika hannunshi yadauki wayan yakai kunnenshi yayi shiru, daga ta dayan bangaren ma akai shiru, kusan 10min ahaka kafin Hamad wanda shine adayan bangaren yace “idan kasan ba magana zakayi ba akan me kabani beep mtsswwww” yay tsaki zai kashe wayan ahankali Maheer yakira sunanshi asanyaye. “Hamad” chak Hamad ya tsaya dan har kasan ranshi yaji yanda Maheer yakira sunanshi yasan yanada matsala something kokuma yace wani abu yafaru, da dan sauri Hamad yace “what is wrong with you Maheer”? Shiru Maheer yayi yakasa magana wayan na kunnenshi, ahankali Hamad yace “bazaka fadamin ba ko” dan shiru yayi kaman bayakan wayan kafin ahankali yace “come and get me” faduwa gaban Hamad yayi dasauri yace “Maheer kamin magana meya sameka? Eh, what happen to you kana ina?” Ahankali yace “I don’t know” sosai Hamad yarude baitabajin Maheer this soft ba sai yau dasauri yace “kasan mene just on ur location for me gani nan zuwa I will locate you” yana maganan ya katse wayan danna location nashi Maheer yayi yana kwance awurin.
Almost 30mins bayan wayan sannan Hamad ya iso daga nesa sosai yay parking BMW dinshi sannan yafito yana sanye ma da lab coat dan daga Hospital yake wayan a hannunshi yana kallo yana track Maheer a map sannan kaman daga sama ya hangoshi kwance akasa Machine agefenshi kwance ba riga wani kalan ihu yayi. “Maheer” da gudu yayi wajen tsugunnawa yayi gaban Maheer din da idanunshi ke lumshe yakai hannunshi saman fuskanshi yana duba numfashin shi yace “Maheer Maheer am here open you eyes, Meya sameka meya faru?” Bude idanunshi Maheer yayi ahankali yazubasu akan na Hamad dayayi kaman zaiyi kuka ahankali yace “take me home” gyadamai kai Hamad yayi dasauri ya tashi tareda taimakamai yadagashi daura hannunshi yayi akan kafadarshi yakarbi wayanshi yahada da nashi yasa a aljihu sannan suka fara tafiya har zuwa wajen mota sashi yayi cikin mota yarufe yadawo gefe ya kunna motan yaja sukabar dajin binibini yake tuki yana kallonshi harsukakai wani hadadden layi dakeda gidaje masu kyau, horn Hamad yayi wani mai gadi yazo yabude gate din suka shiga gidan, parking Hamad yayi gab da entrance na shiga falon sannan yafito yazagayo ta inda Maheer yake yabude kofa yakamo hannunshi yafito dashi, ahankali suke tafiya Hamad yabude kofan falon suka shiga ciki, wani tsoho ne magidanci zaune afalon gashinan fess fess dashi yana sanye da farin jallabiya da hula akanshi idanunshi sanye da bakin glass kur’ani a hannunshi gefenshi kuma wata doguwar sanda ne a tsaye, bude kofan kadai yaji yace “Hamad harka dawo daga asibitin? Lafiya daik…..” tsayarda maganan yayi yanadan hura hanci ahankali yace “dakai da waye Hamad?” Kallon Maheer da kaman baya hayyacinshi Hamad yayi ahankali yace “ni da Maheer ne Baba” dasauri mutumin ya mika hannunshi yadauki sandanshi tareda rufe Al’Quranin ya ijiye mazauninshi cikeda mamaki yace “Maheer!” Dasauri Hamad yace “eh amman baida lafiya bari na kaishi dakina Baba” yay magana yana fara tafiya Baba yabiyosu yana dogara sanda yace “Subhanallahi meya sameshi kuje ina biyeda ku” gyadamai kai Hamad yayi yawuce batare daya damu ba dan Baba babu abinda bayama kanshi dudda makaho ne shi, wani babban daki asama Hamad yabude dakin yahadu sosai yawuce gado da Maheer ya kwantar dashi, daidai Baba na shigowa dakin, Hamad yace “Baba bari na dauko kayan aiki” gyadamai kai Baba yayi yakarasa cikin dakin daidai bakin gadon ya zauna ya ijiye sandarshi taredakai hannunshi yashafa fuskan Maheer dawani kalan so da kauna yace “Maheer” bude idanunshi kadan Maheer yayi yakalli Baba kafin ya lumshesu back, addu’a Baba yashiga tofamai har Hamad yashigo ya tarar dasu ahaka bai hana Baba mai addu’a ba yawuce gefe yana treating ciwon dayaji a hannu jin jikinshi da zafi yahada allura yamai yakuma mai na bacci dan yasan kwata kwata Maheer baya bacci baa wani dade ba bacci yay awon gaba dashi.

Baba daya gama tofamai addu’a yace “yayi bacci”? Gyadamai kai Hamad yayi ahankali yace “eh” shiru Baba yayi saikuma yace “zo Hamad” tahowa Hamad yayi gaban Baba saikuma yazauna akasan gadon, ahankali Baba yakama kanshi ya kwantar da fuskan Hamad kan kafarshi yace “kada ka damu babu abinda zai sami dan uwanka kaji” gyadamai kai Hamad yayi daidai wasu hawaye masu zafi sun zubomai kawai ya kifa kanshi akafan Baba yana huci, bayanshi Baba ya bubbuga yace “kada kadamu kowa daka gani arayuwan nan da tasa kaddaran dudda haka baa yanke zato, ina mai tabbatar maka komi yakusan zuwa karshe, saukan Al Qur’ani da addu’a dakake sawa kusan duk sati sati anama Maheer bazaibi iska ba da yardan Allah, addu’an damuke mishi Allah zai karba, In sha Allah duka wannan halin zai zubarda shi very soon kaji” gyadamai kai Hamad yayi yadago kanshi tareda share fuskanshi tass yajuyo da kanshi yana kallon Maheer dake bacci ahankali yace “Baba ina matukar jin tausayin rayuwan Maheer sabida tun yana karami wahala yake an haifeshi a misery, koni dana taso dakai Baba baka iyamin komi sabida ciwon idanunka nasan gata da dadin iyaye but Maheer baisan menene soyayyan uwa ba kona Mahaifi, Baba bantaba sanin akwai iyayen dazasu iya wulakanta dan da sune suka haifesu da cikinsu ba sai akan Maheer, Baba sun kalli dansu as bad luck yaron gabaki daya yataso cikin kunci, damuwa da rashin walwala, su dafa abinci su hanashi akadoshi waj…….” Hannu Baba yadaura akan bakinshi yace “kadaina fadin magana mara dadi akan wayanda suka rigamu gidan gaskiya, kawai mucigaba da yima Maheer addu’a, Allah ubangiji ya shiryashi Allah yasa mai rabon rahaman ubangiji ne kaji” gyadamai kai Hamad yayi, ahankali Baba yatashi yace “bari naje idan yatashi kazo kafadamini” gyadamai kai Hamad yayi yana bama Baba stick dinshi karba yayi yawuce yafita daga dakin.

 

✨KK✨

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button