Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 81-82

Sponsored Links

*81 – 82*

 

Su mairo an zama ‘yan school koyon karatu da rubutu ba kama hannun yaro a cewarta,gara tayi sauri ta iya kar dangin miji su rainata,wayarta kam shine komai nata duk abunda bata ganeba ,sai tayi voice record in ta dawo gida a k’ara koya mata.

Ga mai koyarda girki da kwalliyya kulum tana hanya darasin su 4-6pm ,din haka julayb kullum yina cikin kar6an samfarin girki masu dad’i da k’amshi ,yanzu kam yadaina k’yank’yaninta sakin ciki yakeyi yina cin duk abunda ta dafa ko ya iya ci ko bai iya ba…ga wasu arnan dressing da take koya ,yanzu julayb yasoma zama bindi kullum yina hanyar gida ,da safe Zasu fita tare,driver yasoma ajeta a makaranta kafin su wuce.

Da rana drivernta daya samar mata ,wanda yike mata aike da sauransu zai dawo da motarta yazo ya d’auketa…aikuwa tana shiga bata tsayawa ko cin abincin da masu aiki sukayi zatayo wankanta tayi sallah kafin ta hadawa kanta abinci da mijinta …saidai in tana mugun jin yunwane take cin na y’an aiki,amma julayb bata ta6a basa abincin ‘yan aikiba

Hmmm julayb hankalifa ya k’wanta har wani tozon wuya ya soma yi,to aure kwanciyar hankalin d’an adam,tunda ya gane tana girki da rana ya aske cin abincin waje…lokaci nayi zai garzayo gida…wata rana yazo ya tadda ita tasha wanka tana juya ukkku,tana jera abincin,wata karonma saiya taimaka mata suke k’arasawa…

Don haka tare suke cin abinci a fileti guda,yanzu kam tama saba bata iya cin abinci in bashi saidai snacks haka.

Yina d’ebo guntu da doguwar sha’awarsa topah gida yayi…itakuwa batajin k’yashin faranta masa a duk sanda yazo sa buk’atarsa…hmmm julayb kam ya sama kalar macen da yikeso,don shi mabuk’acine to kuma ga dukkan alamu haka mairon take,don d’aid’aikun dararene basu sex ,banda ‘yar kewaye da ake zagayowa yi darana…na safe kam wannan farillace ,don yace ba sex d’in da yakai na safe dad’i ga washe k’wak’walwa

Mairo kam wannan abu na mata sugar su k’wakuli juna ,suyi wanka tare su fita tare.

Yanzu satinsu uku kenan da aure ,amma ta zama wata hamshak’iya ,cikakkiyar matar aure ,abun alfahari da soyuwar ko wani d’a namiji.Tasan sirrin wanka da kwanciya da miji uwa uba ga girki da tsafta….julayb kam kullum cikin sambada mata albarka yikeyi…don wata zubin in ya kalleta sai yaga kamar ba wannan gidahumar ‘yar k’auyen da ya sani bace…wannan tafi kama da irin kosassun ‘ya’yan hutun nan da hutu danaira ya gama hudasu tuni…don inka had’u da mairo a hanya zaka rantse inkayi mata hausa bazata jikaba saidai ko wani yaran dabam ,kwata² ta rikid’e daga asalin kamanninta.

Akullum godewa anty jiddah takeyi,don itace tamkar matakalar da ta bata damar sanin yanda zata mallake zuciyar julayb ta hanyar sanin abunda yikeso,wanda bayi so and more.

Dukda acewarta soyayyar julayb ne ya washi mairo har yasa taji tana k’aunarta…to tunda tasan bazata samu julayb ba tunda itama saura ‘yan satuttukane yanzu haka auranta da anacen saurayinta,d’an ministan tsaro,dole ta koyawa matar julayb hilolin da zata jiyar dashi dad’i yanda bazai samu ko k’arzanen damuwa da itaba.

 

*****

Four weeks after

Mairo anfara gwagura turanci ,ta k’arfin tsiya don ko mutun yayi mata magana dahausa topah da turanci zaa maida masa,saidai ayi mata dariya a gyara mata tadai san ta k’aru.inko kaganta a gaban tv tana kallon channels na turanci zaka rantse wata nuguwar ‘yar bokone nan ko da k’yar take tsutsunta…saidai akwai tarin improvements

Ana haka bikin jidda ya kasance saura sati biyu,don haka mairo she’s fully busy…don ankon da sukayi su da amarya kurum sun haura biyar,banda gyaran amare da akai masu tare,kai harta ‘yan lik’e lik’en da ajayiwa hq d’in jiddan saida tasa akayiwa mairo ,jiki kam yasha halawa da wankan turare da ake masu..sai a satin biki takoma asalin busyn program tun saura kwana bakwai,kullum julayb namak’ale da matarsa kar ayi masa snatching itama in return tana mak’ale da mijinta kar wata tayi wuff dashi.

Tunda aka fara gyaran julayb basu d’an shafali junaba saboda period da takeyi ,dukda kwana uku tajeyi.
aikuwa jidda tace tayi prolonging kwanakin in yayi magana tace taba up ,kinga sai ki sama damarda maganin zai tsumu a jikinki ,sai bayan biki asha amarci.

Aikuwa haka tayi ,inyamatsa ai masa ‘yan dubaru yayi release a waje,inyayi magana ta marairece
“Baby nifa ina up,to ya zanyi nima kaina ina missing din lolipop d’ina ,amna bansan meyasa har yanzu nak’i gamawa ba kuma ba haka nake yiba”
“Kinaji kawaibari muje asibiti aduba mun ke sosai,kar matsala ta girma ina nan zaune”
“To amma mu bari sai bayan biki in bai tsaya ba sai a tafi tunda ba wani ciwo nike jiba”

Don dole ya k’yaleta
Biki kam anshashi ,kwana biyar akayi ana shagali a lagos kafin sukabi jirgi aka tafi abj akayi kwana biyu,aka sada amarya da gidanta dake cikin villa ,tun 4pm aka kaita ,saboda hali na covid angwaye sunsamu freedom😌

Aikuwa ana kaita julayb ya tasa k’eyar tasa amaryan sai gida.
A mugun gajuye kuwa sukaisa,don haka tunda sukayi sallah da wanka suke baccin gajiya .

 

 

 

 

Oum Aphnan
[3/14, 07:11] Bamalli✌️: *JARABABBEN NAMIJI*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button