Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 53-54

Sponsored Links

*53 – 54*

“Babansu wannan mutumin zaka bawa ƴa da bamusan usulinsa ba?”
“Ai almuslim akhul muslim ,ke yasan asalin naki ƴan ne,da yasota tsakani da allah?”
“Yo ai auren hushe sha’awa zaiyi daga zaran ya gama da ita kuwa ,sakko maka ƴanka zaiyi kaga kasamu abin faɗi a ƙauye ankawo maka ƙaramar bazawara an ajiye”

Cikin kuka julayb ya waigo ,lulun idonsa sunyi jajir “Mama kisoni don allah ,kamar yanda zakiso ƴarki mairo nikuma nayi maki alƙawarin samuna ɗa na halak ,me riƙe amana tsakani da allah…barama ku gani” wayarsa yaje da gudu ya ɗauka ya kira abbansa,itakam ta ɓangaren mama tsuke baki tayi don ita ba alaman sassautowa a tare da ita.

Mairo kam jirine yike kwasanta sakamakon raɗaɗin ciwon da ya dawo mata gabaɗaya ,can gefe ta koma ,ta riƙe ƙafan katakam tana kuka maras sauti,so kojin gaddamarsu ma batayi.

Cikin dasashiyar murya ya gaisheda baban nasa kafin ya cigaba da yimasa bayani da turanci, bayan yasa wayar a handafree

“Abbey Nasama mata zanyi aure a inda nike,amma yarinyar ƴar talakawa ne,kuma ma mai aikina ne,abbey ta taimakeni dayawa a baya,bayan kowa ya zambaceni ya juyamun baya,abbey ba abunda zanyi in biyata sai auranta. Gashi ina fama da reproductive health problem…(sosa ƙeya yayi kamar yina kallonsa,a gabansa) abbey ina buƙatar assistance,to amma iyayenta sunƙi yarda kai comfirming masu zaku nema mun auranta plz…dont think is a provocations,gama likitana zai maka bayani,kuma yinajin turanci zai fassara masu maganarmu nu dakai”

“Da farko dai julayb ba abunda zance sai alhamdulillah,don ni a kullum ba babban burina da addu”ata sai allah ya baka macen ƙwarai da zata soka tsakani da allah ,ku so juna don ku gina rayuwa mai tsafta…hmmmm julayb nasan abunda ke faruwa da rayuwarka tun farkon balaganka kawo yau,dukda abubuwan da kake aiwatarwa,allah ya sani ina taking measures na gyara saidai ummanka ita take restricting ɗina da son zuciyarta ,wai ita ɗanta na garine,and inaso kasani sanda nazo nigeria naji labarin abunda kake aikatawa har yaso ƙazanta,kuma nasan ka kwana tareda mace a ranar ,dukda ban nuna maka ba,amma nacigaba da bin ka da addu’a…kuma duk iftila’an da suka dinga faruwa dakai da masaniyata ,sannan naji daɗin hakan ,so duk abunda likitan ka zai faɗamun is just like mere repeatations,so…ja shaidawa iyayen matanka zamuzo nan da kwana biyar masu zuwa da yardan allah…dukda nasan basa fahimtana kamar yanda ja faɗamun ,inaso kai doctor ka miƙa masu saƙon godiyata,kafin mu iso…kaikuma likita nagode da taimakon da ka bani na ganin yarona ya shiryu,allah yayi albarka ya baka ƴaƴa nagari masu tarbiyya na gode…yaro expect our coming as scheduled”
“Thank you dad ,must to jubilate,my regard to kowa da kowa kafin in kawo masu amarya”
Dariya yayi kafin sukayi sallama suka rabu.

Nan likitan ya shaida masu komai ,harda saƙon godiyan abba
Dukda maman bata yarda ba,a tubaninta zasu yi masu halin ƴan bokone dole ta haƙura don taga mijin nata yasoma ɗaukan zafi da ita.

******

“To ai saikizo mutafi ko tunda burinki ya cika ƴar kanki?”
“Go where? Don allah ku zauna anan tareda mairo har a ɗaura auren ,akwai part dayawa a cikin gidannan wanda ko gani na ma bazakuna yiba”
“A’ah bazan zauna gida ɗaya da surukina ba,kuma dole yau mu koma mu shaidawa dangi ,sha’anin aure ba wasaba”
“Shikenan ku ɗaga mun ƙafa zuwa yamma zan sa anemo muku flight da zai kaiku ,don naji baba mai shara ta taɓa shadamun garinku da nisa”
Jinjina kai kurum tayi ,dondai batasan meye flight ɗinba.suja ja kayansu suka fita.

Corner ɗinda mairon take ya nufa,anan ya risketa tayi zufa sharkaf sai kuka take hannu riƙe da ciwo

“Subhanallah,likita zo kaga ni” yafaɗa tareda janyota daga wajen. Da sauri ya cire hannunsa akanta yina faɗin “sorry ɗan taka ki fito ok?”
Miƙewa tayi amma ta kasa ɗaga ƙafa sakamakon kwailewan da yayi gashi yasoma fushi ya tashi

Ganin haka ya kauda kai ,cak ya ɗagata ya kawota tsakiyar falon ya dire.

Murmushi likitan yayi ,kafin ya ƙaraso ya saka gwuiwoyinsa a ƙasa yina duba ,ciwon

“Sai anyi dresaing ciwon ,kuma ta samu luxation(gocewar ƙashi) a yatsan nan”

“Ooops to abata special care,amma a hankali kasan she’s my soul mate in taji zafi sharing zugin zamuyi”
“Ohk sir julayb,babban ango🤪”
“Tsokanata ma kakeyi ko? Yes i mean it” yafaɗa with a serious tune

Ɗagata yayi ya maida kan kujera ya rungumota kafin ya saƙalo masa ƙafan ta ƙasa
Cuno baki gaba tayi ,tana tuttureshi

“Uhm ni ka bari ,ka sakeni”
“Sorry baby,zaa duba ciwonkine banson ki gani bare ki damu

“To naji nidai cikani bazan kallaba”
Murmushi yayi kafin ya saketa.

Aikuwa likitan na saka gauze da ruwan wankin ciwon da ya haɗa ta fasa ihu ,ta janye ƙafanta
Tana lailayawa tana daɗa kuka

Dubara yayi mata yayi farat ya cafki ƙafan ya sauke ƙasa ,ya maida ta ƙasan cinyanta kafin ya rungumeta tsantsan,yanda bazata iya motsiba.

Daurewa tayi tana squeezing fuska har aja wawwanke,sai kuma aikin wato gyaran gocewan

Yina taɓan wajen ta canyara kuka,wanda har iyayenta dake waje saida sukaji,aikuwa a sukwane suka yo ɗakin.

Yina ganin zata basu matsala kawai sai ya maida bakinsa cikin nata ya rufe ,yina aika mata da saƙonda bai shirya bata a yanzu ba.

Mutsu² takeyi ,tanason yin magana babu hali ,har ta ɗan natsu ,inda wani abu yaringa fizgarta,da yadanne kaso 80 na jin zafin,tuni ta sona manta inda take.

Tayi luuuu ta saki jiki ,a jikinsa .
Shikuwa likita yashiga aikinsa safely.

Cikin tsere² iyayenta suka shigo,turus sukayi ganin abunda ke faruwa ,da sauri sukayi baya suka koma da sauri

“Uhmuhum sha’anin balaraben mutum…sha’aninsa sai a barsa”

“Eh aifa in ya ƙaƙule maka ƴarka duk zaku gane maga yanda zai auretan,ni garama kawai ayi auran nan nan kusa in huta da zullumi”

“To banda abunki baki ganin gyaran ciwon da kika ji mata akeyi? In bai kula da itaba,da yanzu bata hargitsa gidan nan da kuka ba?”

“Ku dai kuka juyota ,ni ina ruwana”

 

 

Oum Aphnan
[3/14, 07:03] Bamalli✌️: *Typing…✍️*

 

*JARABABBEN NAMIJI*

 

*Na…Oum Aphnan🌸*

________________________________

*ALHERI WRITERS ASSO.🖊️*

*A .W. A*

https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/

________________________________

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button