Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 103-104

Sponsored Links

103 – 104*

 

Dakatar da drivern da zai kaisu airport sukayi aikuwa jikin mairo na 6ari tayi waje…fad’i take “Babace…wallahi babace allah sarki sun hanata ta shigone suka barta a rana”
“Take it easy dear ok”(kiyi a hankali kinji)
Jinjinawa oumman kai tayi kafin ta 6alle k’ofar tayi waje.suma suka bi bayanta.

Zuwa tayi gabda ita ta zauna “Baba an wuni lafiya? Ya sahan jikin?”
“Lafiya k’alou yarinyata
….allahu akbar kaga bak’in arab wainnan family kuna burgeni…Hajiya mairo nagode ko bakiyimun komaiba in d’aga darajata a wajen mutane,sanadiyyar ganina daku k’awayena mabarata sun daina hantarata.

Oumma ce tace su shiga motar su ayi maganar aciki ,don su su nihla sunce basu fitowa a wannan zafin ranar suna nasu d’ayar motan.

Sabon gaisuwa suka yi.kafin julayb ya waigo sosai ta gaba ,da kalar hausarshi mai kamada na gwarawa yasoma mata magana duk da itama muryan mairon ya d’an soma chanzawa amma kad’an.

“Baba zan wuce dake companyna na nan,zansa abaki share d’ina da nike dashi which nasan zai dauki nauyinku harda danginki inshaallah,dakuma gida a kurkusa…sannan inshaallah zan bar sallahun a fitar dake ko india ne ayi maki k’afafun roba yafi kinajan gindi ,allah yasa kaffarane”

Kuka ta kece dashi”allahu akbar daga aikatau ? Lallai allah na gode maka ,haduwa daku alkhairine…kuma na yarda da wannan duk wanda kake tare dashi karka wulakan tashi,don bakasan baiwar da ubangiji yayi masa ba,ko zai masa anan gaba mairo nagode…nagode😭”

Dakyar suka rarrasheta cikin sauri aukayi extending dinta akan komai ,kafin suka barta sukuma suka tafi

Daga airport jirginsu na tashi ba a wani rufe awanniba suka sauka a adamawa daganan suka wuce k’auyensu.

Gaban gidan kam cike take damkar da ‘yan gaisuwa…..

Sunyi murna da zuwansu kowa ya aza sunzo gaisuwane ,abunka da ranar ne uku

“Allah sarki gari ya gari tundaga makkatul mubaraka sukazo gaisuwan liman…Allahu akbar liman na allah gaisuwa harda larabawa ? Uhmuhum”
‘yan k’auyefa sun rude da murna haka yabisu yayi masu yayyafin naira a matsayin sadaka aiko mutane haka suke tuttud’owa harda mata….ka6akin abinci kam iri² aka dingi sauke masu harda masu sa mutum amai.

Tuni labari ya riski mama,hmmm hajiya mama kenan hajajju baitul lahi,mutam makkan da madina…banbadanci takesha bana wasaba,ta kafu tayi kudi a sabon gidanta yanzu ordern kayan dakin amare takeyi ga ‘yan aiki kowa na aikinsa…tayi k’ashar kashar tayi mulmul k’uruciya da kyawunta sun futo.

Sawa tayi aka je aka yo masu hadin lafiyayyun Abinci a wani hotel dake kusa dasu tunda bazai yiwu ayi masu girkiba kan su iso….part guda aka ware masu aka dad’a gyarasu akasa sababbin zannuwan gado da labulai koina ya dauki kamshi ,tayo wanka ta buga dandatsatsen leshi ta coge a kujera tana shirin tarban bakin alkhairi

Ba jimawa sai gasu aikuwa basu saki jikinsu ba sai sannan sunci abinci hankali kwance dukda dama bawani damuwa da abinci sukayiba sudai susha kayan ruwa ,yawwa.

Sun samu tarban karramci anyi gaishe gaishe haka take kiran ‘yan uwa suzo ga mairon ta da abokan arziki.
Omma da julayb hannunsu kam baya gajiya da mikawa…su nihla sun saki jiki sun jone da mairo suna cin karansu babu babbaka.

Mama da baba sunji. Dadin ganin ‘yarsu sunyiwa julayb godiya kamar mene.
Saida sukayi kwana biyar kafin suka dawo saudiyya ,bayan mairo ta kwashe kayan da take bukata na gidanta na lagos wanda bataso ta sadaukarwa ‘yan uwa da mabukata.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_✍️Oum Aphnan_
[3/14, 07:18] Bamalli✌️: *JRRB NMJ*

 

 

*Na…Oum Aphnan🌸*

 

*ALHERI WRITERS ASSO.🖊️*
*A.W.A*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button