Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 9

Sponsored Links

๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ
*~{{MY FAMILY}}~BOOK 2*
ยฉยฎ *UZ-2023.*

*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{Ummiee Zaria}~*โœ๐Ÿผ

,,, *Page 9*

Mai makon shi wanda suke magana da Meenal d’in ya biya kud’in kamar yanda ya buk’ata, ah ah sai gashi abokin tafiyar shi dake gefe shine ya matsa wajen biyan kud’in ya biya tun su Meenal basu gama nasu muhawaran ba,
Babu b’ata lokaci haka mutumin nan ya lale kud’ad’en kayan da suka siya tsaf ya biya kud’in,

Ita ko Meelat kallon Meenal kawai takeyi cike da mamaki,
Dan batun yau ba zadu iya cewa Meenal itace hatimin nasarar su dan ata dalilin ta sun dad’e suna cin yan kud’ad’e na samari tun kafin auren ta, bayan auren kuma da suka fara karatu duk wanda ya yunk’uro idan suka ce matar aure ne sai ya nemi lab’ewa a tsakanin ita Meelat d’in ko Maryam a haka zasuyi ta musu hidima har sai in sun gaji dasu sanemi hanyar sallama su salin alin,
Kai itafa idan ma tace batayi farin cikin mutuwar Meenal yasin k’arya takeyi sai dai kawai dan darajar dake cikin aure yafi k’arfin ace za’a nuna mad’aukakin farin ciki a fili bayan mutuwar shi,
Amma ba komai tasan cewa yanzun kam qawarta zata samu damar data rasa a shekarun baya na tsaya ta zab’ar ma kanta abokin rayuwar da take ganin ya dace da tsarin ta, hakan nema yasa take ganin wannan lokacin na musamman ne a awaken su da zasu kasance a tare dukan su babu wacce keda igiyar auren wani akan ta balle hakan ya musu shamaki akan wani abun,
To gashi tun daga yau da alama wasar zai fara, idan suka had’a ido sai Meelat d’in ta girgiza kai ita kuma Meenal k’asa kasa take binta da murmushi,

Tsaf aka had’e musu kayan da suka siya yaran shagon suka raka su dashi har mota ko Sallama Meenal bata yarda d’aya daga cikin su tama Ya Mashkur ba dan allah ma sheda ne cewa Allah Allah kawai takeyi akan suyi subar wajen kafin ya fito dan tasan mawuyaci ne idan Maryam ta fad’a ma mutanen sunan su na gaskiya dan haka sukeyi dama batun yau ba in suka had’u da samari irin haka to suna da inkiyar da suke kiran sunan junan su sab’anin ainihin sunayen su na gaskiya.

Har wani ajiyar zuciya ta sauke yayinda taga sun fito daga shagon salin alin ba tareda an samu matsala ba, shiko wancan mutumin da suka shigo tare da Maryam bakin shi ko gajiya bayayi da surutu, d’ayan dai da alama miskiline dan bai iya tanka musu ba sai bayan sun fito ne sannan ya matso inda suke,

“Sannu koh yan mata!”

“Yauwa sannu Maryam da Meelat suka amsa mishi dashi domin ita gwanar ko kallo bai isheta ba saima gaba da tayi abunta bayan ta kulle booth din motar ta da aka sa kayan da suka siyo, ta juya da niyar shiga motar kenan shi kuma ya tare ta da cewa,

“Yan mata nace ba!”
Ya fad’i hakan a yayinda yasha gabanta ya tare hanyar da zata wuce,
D’aga kai tayi batareda ta kalli fuskar shiba ta amsa mishi da cewa,

“Kace me? Oh na manta ban maka godiyar dawainiyar da kayi damu yanzun ba, mun gode fa Allah ya k’ara arziki ya jikan iyaye”

“Ameen nagode da addu’a duk da dai bawai nayi bane dan a gode min d’in ba,
Bama wannan ba shinko zan samu gimbiyar tad’an bani aron lokacin ta In ba damuwa ina son mud’an tattauna,”

Sai da tasa hannu ta gyara zaman gyalenta zuwa saman kai kafin ta bashi amsa da cewa,

“Yar uwata bata gaya maka cewa ina da aure bane hala?”

“Hakan dai tace min da farko kafin daga baya kuma sai ta fad’amin cewa tadai fad’ane kawai amma baki da aure,”
Ya k’arasa fad’a yana kureta da kallo,
Turo baki tayi ita kuma tana juya mishi baya

“Oh da gaske dai baki da auren kenan?”ya k’ara tambaya

“Injiwa yace maka? Nidai ai nace maka ina da aure koh”

“Yanda kikayin ne ya nuna min cewa da gaske d’in baki da aure, dan haka in babu damuwa ko zaki bani dama mu k’arasa zuwa gidan ku, dan gaskiya ina buk’atar magana dake kinga kuma dani dake duka ba girman mu bane mu tsaya muna hira a titi, shine nike ganin ko zaku mana jagora in yaso mu sai ku biyo ku a baya zuwa gidan ku ?
Dan yau nike son komawa Abuja bazan so kuma in wuce bamu tattauna ba gaskiya please ๐Ÿ™”

Kam buhu yau Allah ya had’ani da d’an anace daga taimako shine saboda tsabar maita wato bazai yarda mu rabu anan ba shine yake son lallai sai ya rakamu har gida,
jama’a ina ma laifin yace ta bashi number in yaso koma dai miye alakar ta tsaya a iya waya kawai in yaso sai ta bashi koda number din wayarta da ba kullum take amfani dashi ba,

“Kinyi shiru?”

“Umm umm to aini tsoro nikeji dan mu a gidan mu ba’a barin namiji zuwa wajen mace sai ya nemi izini kaga kuma ni karatu fa nikeyi a yanzun shi yasa ba’a barni na fara tsayuwa da kowa ba tukun”ta k’arasa fad’a tana wik’i wik’i da ido,

“To yanzun ya kenan?”

“Kayi hakuri sai dai muyi waya zuwa wani lokacin idan ka k’ara shigowa ni kuma zan san yanda zamuga juna koda a gidan d’aya daga cikin yayye nane, zaka iya zuwa ka sameni ai”

“Mai zai hana kuwa kin tab’a ganin inda mai nema yayi fushi ne?
Kafin nan dai bari in gabatar miki da kaina,
Suna na Al’ameen Adam Rano, bakano neni amma kuma mazaunin abuja”

“Allah sarki ni kuma suna na Zubaidat Ibrahim amma Ikram ake kirana, kamar yanda ka gani kuma ni d’in yar Zaria ce mazauniyar cikin ta kuma”

“To karmu b’ata muku lokaci ga wannan katina ne dan Allah kiyi kokari idan kun isa gida ki kirani,”
Ya fad’a bayan ya mik’a mata katin nashi ita kuma ta amsa,
Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke dan da alama ta tsira.

“Mu zamu wuce nagode da lokacin da kika bani”

“Ah haba Yallabai ai muke da godiya da dawainiyar da akayi damu”

Sai da ya rakata har bakin motar ta ya bud’e mata ta shiga ya kuma maida mata kofar ya rufe sannan sukayi sallama da su Meelat ita kuma taja motar sukayi gaba suka bar su anan wajen suna d’aga masu hannu,

Sai da sukayi nisa da sosai kafin dukan su suka fashe da dariya,

“Kun san abunda ake cema dakyar nasha yafi ace da kyar aka kamani? To wallahi shine ya faru yau, haka kawai mutumin nan zai wani ce wai zasu bimu a baya suga gida kamar wani body guide dina” ta fad’a ta tareda ta dena dariyar da takeyi ba

“Kai Beb wallahi baki da kyau, yanzun yanzun kin wanki mutanen nan kusan dubu d’ari biyu fa, wallahi shi yasa nike son fita dake zuwa waje irin wannan dan zuwan ki alkhairi ne, wai haka dama yace zasu bimu tab lallai ma?”

Jakarta dake gefe ta d’auka ta mik’ama Meelat
din
“duba cikin Jakar zakiga katin daya bani fito dashi kimin gutsi gutsi dashi ki watsa shi ta window”

“Ah haba dai kina nufin ko sau d’aya bazaki kirashi ba?”
Cewar Maryam itama tana dariya.

“Wai hala dai idanuwan ku sun samu matsalar da basa gani da kyau ne? Ku daganin wannan mutumin ai kun san mijin wasu ne wallahi dan tabbas da ganin idon shi bazai yarda ya zauna da mace d’aya a gidan shiba to niko inba bakin iyaye ke bina ba uban me zanyi dashi, mtwss dallah ni karku bani haushi ma”

“Eh ai baki da uban da zakiyi dashi amma kina da uwar da zakiyi da kud’in shi”
Maryam ta fada tana dariya,

“Aini ban tura mishi katin gayyata ba, idanuwan shi ne suka gano mishi ruwan da yayi zaton suna iyayi mishi wanka, bai san cewa wannan ruwan maliya bane in ya sake ya shiga bai zama dole ya fito a raye ba,ina fatan dai baki fada mishi ainihin suna na ba?”
Tayi tambayar tana kallon Maryam.

“Kina da wani sunan da yafi Zuwairat ne a duk lokacin da tarko ya kama kurciya dama?”
Itama ta tambaya tana dariya,

Dariya suka kara fashewa dashi,
“Kai Zubaida ashe baki manta sunan nawa ba?”
Inji Meenal.

“Ke wai ma da muka barki tare dasu me wancan yake fad’a miki?”

“Ah ah ai shi rakiya kawai yayi abokin ne ya gano abinda ya gano shine yasa suka biyo mu a baya, shi dai yace min sunan shi Auwal kuma wai d’an Malali ne a garin gomna (kd take nufi)”

Basu isa gidan hajiya ba sai da suka tsaya Meenal ta siya kajin da ta amshi kudin su a hannun Ya Mashkur,

Bayan ta faka motar nata a harabar gidan baya ta koma ta tambayi Isah,
“Mai Jama’a yana gida koya fita?”

“Ai Hajiya tun fitan da yayi na safe ina tabbatar miki da cewa har yanzun bai dawo ba, su Sadeeq ne kawai a gidan suma d’azun nan suka shigo”

Juyawa kawai tayi bayan ta gama sauraron abunda yake cewa domin su Meelat sunyi gaba zuwa Sashen na Hajiya dama,

Sai da sukayi shagalin cin kajin nan kafin suyi zaman ware kayayyakin kowacce ta d’auki nata suka cirema Moon da Aisha nasu, dan a gobe suke so su fara rabon ankon,

Suna cikin ware kayan ne kuma Allah yama Hajiya shigowa dan ta shiga wajen Dada Turai kakar Billyn Ya Sa’eed,

“Wa nake gani yau a gidan kamar Amaryar Mustafa na?”

Da dariya Meelat ta tareta tana cewa,

“Wallahi Hajiya kamar kin san cewa ke nike jira dama”

“To ai gani na dawo ya akayi ne hala”
Ta tambaya a sanda take zama a kan kujera,

“Hajiya yaushe za’a kwaso kayan Meenal na can gidan ne? In kuma ba’asa ranar kwasowan ba ki bani key dan Allah muje gidan nida Maryam mu d’ibo cikin kayan ta wad’anda bata dinka ba, mukai mata d’inki, ki kalli shigar da takeyi fa har yanzun Hajiya bayan ita din a yanzun da bata da aure kamata yayi ta canza kalar shigar ta,”

“Eh to kema kince wani abu dama so nayi in hayaniyar Sakin ya lafa sai insa a kwaso kayan, amma yanzun bari in d’auko muku mukullin sai kuje ku d’auko abunda kuke buk’ata din kafin a kwaso kayan”

“Yauwa Hajiya aiko mun gode, kinga ko ga kayan ankon ki kema na ware miki dan kema ai k’awar amarya ce”

Sun kai har bayan la’asar a gidan suna ci gaba da tattauna wa sai yamma liss Musty ya kwashe su ya mai da gida kafin su tafi kuma sai da Meelat ta amsa key d’in da tayi ma Hajiya magana aikai,

har lokacin kuma AK bai dawo ba dan tun Meenal na d’ar dar da tunanin haduwar su har ta sake taci gaba da harkokin ta,

A wannan ranar dai basu ba had’u da AK din ba dan da wuri ta haye sama ta kulle d’akin ta bata kara gigin Saukowa ba har dare, kuma ranar dashi dasu Sadeeq dukan su anan Sashen Hajiyar sukayi hirar dare,
Tunda baiga wulkin Meenal din ba yasan kunyar ganin shine ya hanata Saukowa dan haka sai kawai ya share shima,

*BAYAN KWANA HUDU*

A gefen Meenal sosai ta d’auki matakin hana kanta zama a falon Hajiya inko har zata zauna tofa saita tabbatar da cewa ta rufo kofar falon dana kitchen,
Anayin knocking kuma da bazata bud’e ba sai ta tambayi waye, inko har taji muryar AK ne tofa bazata bud’e mishi kofar ba juyawa zatayi ta koma d’aki idan kuma anyi katari Larai na kusa ita ke bud’e mishi kofar Yanzun,
Ya kuma yi tambaya akan dalilin menene yasa yanzun ba’a barin kofar a bud’e ?
Larai kuma ta fad’a mishi Hajiya k’arama ce ke kulle kofar,
Tun daga ranar ya gane cewa da biyu take kulle kofar kenan hakan na nufin cewa har yanzun kunyan had’uwa dashi takeyi,
Sai dai kuma gaskiya shi tana matuk’ar cutar dashi ta wannan hanyar, ita bata san cewa saboda itane yazo garin nan har ya kwana biyu ba amma haka nan ta tsiri hora shi da rashin ganin ta,
Kwana biyun nan kama kanshi fa kawai yakeyi akan rashin ganin ta dan ma yakan lab’e daga falon shi aduk sanda zata fita haka zaiyi ta kallon ta har saita fice, gashi gobe yake son yin tafiya zuwa Jos a kallah kuma zaiyi kusan sati baya nan,
A haka a babu yanda zaiyi din haka ya shirya washe gari yabar mata garin,
Yana tafiya ita kuma ta koma kan harkokin ta kamar yanda ta saba a baya,
Duk wannan abun a idon hajiya yake faruwa dan itama tasha tambayar dalilin da yasa meenal din take kulle mata kofar falo amma bata samu amsa gamsasshiya ba, sai dai kuma bata matsa mata ba ta kyaleta,
Yusuf kuma yakai ma Hajiya Ziyara na musamman a wani dare bayan ya tabbatar Meenal na cikin d’akin ta shi kuma Ak baya ma unguwar gaba d’aya a lokacin dan sun gama yanke hukunci shida su Musty aka cewa gara ya sanar da Hajiyan komai kawai tun yanzun kar in abu ya lalace a gaba tace dan me yasa basu sanar da ita tun da wuri ba,

To dai koma me suka tattauna zamuji shi zuwa gaba, ta amince ko ah ah nima dai ban sani ba, dan washe gari Yusuf din da AK suka wuce Jos Musty da Sadeeq kuma suka koma bakin aiki suma duk da dai yanzun Musty baya wani zama Sosai a Kaduna saboda hankalin shi dake kan ginin gidan da Meelat zata zauna a ciki da yaketa faman kokarin ganin ya kammala kafin lokacin bikin da kullum k’ara matsowa yakeyi,
Wannan kenan,

*BARI MU LEK’O SARKI*

Yauma kamar kullum tunda ya dawo daga wajen aikin daya kawo shi garin yake zaune a cikin d’akin shi na cikin barrack din da aka sauke su,
Zaune akan kujera mai mazaunin mutum d’aya ya mik’e duka k’afunshi sai ya daura su akan center table din daya jawo zuwa gaban shi kad’an,
Laptop ne a kan cinyar shi yana cigaba da duba hotunan gidajen da yayi magana da wani abokin shi dake can ZARIA ya turo mishi akan Maganar gidan da sukayi da Meenal cewa tana son ta siya ma Malam gida,
Domin bai baro garin ba a ranar sai da ya bada cigiya akan yana son gidan, kamar yanda yaba Salman umarnin kawo mata motar a ranar,
Tun zuwan shi bai samu zaman da zai duba hotunan ba duk da cewa abokin nashi yasha kiran shi dan yaji ko ya duba gidajen daya tura mishin domin duka a kasuwa suke,
Mamaki yake son bata dan haka sai ya yanke hukuncin turama Sa’eed hotunan Kawai akan ya taya shi zab’en gidan, sai da ya aika mishi hotunan kafin ya kirashi ya bashi umarnin son yake ya zab’a mishi d’aya a cikin gidajen daya tura mishin,
Rufe Laptop din yayi ya ajiye shi a gefe dan sai lokacin ne ya tuna da tonunan da Meenal din tace ta tura mishi a cikin wayar,
Dan haka sai ya d’auko wayar ya gyara zama bayan ya shiga cikin ma’ajiyar hotuna ya fara bincike,
Hotunan daya gani kusan kala 10 ne kuma dukan su na mutum d’aya ne sai guda biyun da sukayi ita da Meenal din ne hakan ya tabbatar mishi da cewa sune wanda meenal din ta tura mishi dan haka sai ya fara bin su d’aya bayan d’aya yana karema hotunan kallo,
Ya dad’e yana kallon hotunan bai iya furta komai ba sai kuma zuwa can yace,

“Meenal kenan wato saboda taga Teemah tana da d’an jiki kad’an shine yasa take son had’ani da wannan kenan?”

Eh kam gaskiya yarinyar cikin hoton tadan d’auki hankalin shi duk da a iya hoto ya ganta amma yana jin cewa zatayi dai dai da tsarin shi dan ya lurada cewa ta mallaki dukkan abunda yake buk’ata a wajen macen da zai zauna da ita a matsayin matar shi na aure, wato wayewa kyan fuska cikakken diri da wasu abubuwan wadanda shi ya barma kanshi sani,
A bayyane kuma ya k’ara furta cewa,
“Koma batayi ba ai dole in amsa haka da hannu bibbiyu ma kuwa tunda ta fito daga wajen abunda nike matuk’ar girmamawa a yanzun,
Inma batayin ba duk ni zan saita ta zuwa tsarin da nike muradin ta kasance min.

*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button