Sponsored Links
Gidan Aunty Book 1Hausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 64

Sponsored Links

BOOK 1

Page 64

Not edited

Gabaki d’aya ranar king farincikin da ya keci ya kasa boyuwa da kansa ya kara dubawa ya tabbatar da cikin , begama farin cikin ba tahee ta bijiro masa da yan wakenta, yace zai kira ayi mata tace shi take so yayi mata, sabida farin cikin ta yau king akaro na farko da zai girka abincin Inba coffee ba da kansa, komai da komai saida tahee ta futo masa dashi gabaki d’aya ya bata kitchen din da floor hatta lallausan gashin kansa saida yasan da zuwan king kitchen, yanayi yana nishi, ita dai tahee sai faman dariya take masa, wajan sa dan waken ma da ya sa daya zai ce mata zai hutu wai ya dauka da daddai da daddai ake dafa dan waken, ga wata uban kuka da ya cika a cikin dan waken , yayi gore shar dashi, yana kammalawa tace masa saura tumatun da albasa, tunda ya fara yanka albasa yake lumshe idanuwansa sabida yajinta, da ya tashi yanka ta , gida shida ya rabata , wai haka turawa suke cin albasa, batace masa komai ba ya soya ma ta dakko yajin ta, da kyar ta yarda ya zuba mata yajin ganin uban yajin da take kokarin tunawa, tana saka dan waken abakin ta zaro idanuwanta, kallanta yayi cikin damuwa zai janye plate din “ karki ya cutar mun dake bari ko order sai muyi”, duk da uban kukan da ya cika mata murmushi ta sakar masa kafun ta furta “ yayi dadi, shine kake mun wayo ka iya girki ko”, kallanta yayi haryanxu yana kokarin dauke plate din , kukan shagwaba ta saka masa gabaki d’aya ya susuce sai faman sannu yake mata, ko da zasu kwanta ma duk motsi daya in tayi sai ya tanbayeta me yake damunta, sosai ya shiga lallashinta har bacci ya dauketa. Kallan flat tummy dinta yai kafun ya kai bakinshi ya sumbata, harta tahee dake bacci sai da ta motsa, gyara mata kwanciyar yayi kafun yayo alwala, sosai yayi nafila ya nuna wa Allah godiyarsa.

WASHE GARI

Yau weekend , tunda tahee ta farka yake tarairayarta harta abinci shike bata da kansa, ita dai sai dai tayi masa dariya wani irin Kaunar cikin na kara shiga ranta, karfe 8:30 ya shiryata, duk yanda taso dojewa saida king yasa ta shirya, yau da kansa yayi driving dinta har zuwa asibitinsa, kowa mamakine ya kamasa ganin king na driving da kansa, abunda ya fi daukan hankali kowa yanda ya rike wa tahee hannu har zuwa office dinta, sai a lokacin ya cire mata facemask din daya sa mata a mota, dakanshi ya duba lapiyan cikin , kafun ayi mata scanning, cikin wata d’aya da kwana uku, yana ganin result din wani murmushi ne ya kamasa “ so am not that bad “ ya furta a cikin zuciyar, wani murmushin ya kuma saki, be dade a office din ba ya dauke sai faman shaqwaba take masa , yawo ya zaga da ita shima bayan ya saka facemask sosai yayi mata siyayya ko me yaga ya burgeshi zai dakko mata, naira tayi kuka tun tana ce masa sun isa har tayi shiru da bakinta. Suna gomawa gida ganin yanda take rike bayanta ne yasa yayi saurin rikota “ meke damunki” kanta ta dan girgiza masa “ babu komai “, kin tabbata ,murmushin jin dadi ta saki kafun ta furta “ na tabbata “, daukanta yayi gabaki d’ayanta , wani wanka suka karayi atare kafun ya matsa mata jikinta, hakan da yayi mata kuwa ba karamin dadi taji har bacci ya dauketa, rage Ac dakin yayi kafun ya saka mata me dumi, fuskar sa cike da annuri ya nufi part din abeey , jinsa yake kamar a wata duniyar, Daidai lokacin da ya shiga falon abeey shima a lokacin abeey ya fito daka wani kofa, kallan fuskar king da take d’auke da annashuwa yayi, kafun ya tanbayi ba asi king ya karasa ya rungeme abeey din ajinka, kamar a mafarki haka abeey yaji dan an dau tsawan lokaci king yayi masa haka , cikin sanyayyar murya king ya furta “ finally abeey, akhii dina zai dawo, I will get another moha” dago da fuskarsa abeeey yayi alamun bai gane ba, “ she’s pregnant “ king ya furta ko kunya babu, a bazata abeey yaji saukar magana kafun ya fara bin king da kallan tuhuma, dariyar da ya kara fito da kyansa yayi har dimples dinsa na lotsawa na duka sides din yayi, cikin karyayyar murya abeey ya furta “ finally my real king is back, Allah na gode maka da ka nuna mun ranar da king dina ya dawo yanda yake, I’m so very happy son, I will become a grandfather now, oh my god, Allah ya sauke ta lapiya , Allah ya bata lapiya “, sosai abeey yayi wa tahee addua wani irin farin ciki na cika zuciyar abeey, jiyar fitar da zaiyi ya fasa ma hakan ya koma ya zauna, number mahma yayi dialing, king na ganin haka yayi saurin barin part din.

A part din dada ma yana shiga be dade ba ya fito duk yanda take tsokanarsa, yau kwata kwata be maida mata da martani ba gabaki d’aya hankalinsa na kan babyn sa da ya bari, part din ummey ya nufa, waya ya tarar da ita tanayi, be damuba gaisheka kawai yayi ya bar part din. Yana shiga part din ammey ya tarar da ita tana cin gasash shiyar kazar da taji kayan hadi, gaishe da ita yayi ganin yanda fuskarsa ta cika da annuri ne yasa ta kallesa da murmushi dauke a fuskarta, “ Son Anya wannan farinciki haka , ko dai akwai albishir me dadi”, gashin kansa ya taba a duniya in akwai me saurin gane yanayinsa abayan ammey yake , Daidai lokacin da take saka naman kazar abakinta tayi saukar muryarsa” she’s pregnant ammey”, wani irin kwarewa me shegen zafi ammey tayi a makogwaranta sai faman tari take, da Sauri king ya zuba mata ruwa ya bata , saida tarin ya lafa mata sosai kafun ta kallesa , “WACECE take da ciki son”, a hankali ya furta “your daughter “ , yanxu kam kwarewar da ammeey tayi ya fi Wanda tayi na farko sosai, dakyar tarin ya tsagaita mata, ta soma nunfashi a hankali, ganin yanayin da ta shiga ne yasa ya ajje mata naman da take ci ya gara shafa mata bayanta hartaji nunfashinta na daidaita, kallansa tayi murna sosai d’auke a fuskarta “ finally my son will be a father , and I will be a grandma , oh my god, congratulations son dina “ ta fada tana rungumeshi, shima rungumetan yayi yana kara jin wani irin farinciki na mamaye ransa, tanbayarsa wata nawa cikin ammey tayi, be damuba ya fada mata, wani irin farinciki yagani a fuskarta sosai harya so Bashi mamaki, har Ammeey ta fara lissafin siyayyar da za saka yi wa baby, shidai nasa murmushine , ya dan jima a part din ammey kafun ya bar part din, yana barin part din wani irin ball abbey tayi da plate din Kazan ta da ya sata bare wa, bata zauna a falon ba tanufi dakin ta cikin sauri.

Yana fita ya hadu da kabeer da haroon, cikin ladabi suka gaishe da king, abunda ya basu mamaki ganin yanda ya amsa musu cikin sakewa ba tare da ya dauke fuska kamar yanda ya saba ba. Be kara wani minute din ba ya nufi part dinsa. Bin bayansa da kallo su haroon sukai, “bro kaga kuwa abunda nagani, yau yaya king ne ke amsa mana gaisuwa babu hade rai, “ cewar haroon, “ Nima dai abunda ya bani mamaki , amma in tayi tsami ai zamuji, Yaushe zamuje ganin amarya “, kallan baka da hankali haroon ya bishi dashi, “ da alama jikinka tsami yake , ka kwana biyu baka sha mari ba “, dariyar iskanci kabeer ya sakin kafun ya cewa haroon “ Yaushe zamuje part din ammey , yau tun safe ban ganta ba”, banza haroon yayi dashi yayi wucewarsa , shima kabeer din bin bayan haroon yayi suka cigaba da tafiya daman part din ummey zasu .

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
ABUJA

MAITAMA

Babban gida ne katan gaske da ya gaji da haduwa, babban gate din gidan aka bude lokacin da wata mota fara ta shiga cikin gidan ,Daidai parking space mamallakin motar yayi parting kafun ya bude motar, ba kowa bane ya fito face Khaleed dake sanye da bakin suit a jikinsa, wayace kare a fuskarsa da alama waya yake , direct inda entrance din gidan yake ya nufa , knocking biyu aka bude masa komar, karo yaci da zahra lokacin da take bude masa kofar, wayo idanuwa tayi kafun ta saki kara tana rungumeshi “ yaya Khaleed oyoyo, nayi missing dinka “ Daidai lokacin da yake gama wayar , banbareta yayi a jikinsa kafun ya dungure mata kanta “ ke har yanxu wai bazaki girma ba , daddy da oumma zance su aurar dake ko na fadawa Hajiya kin isa aure duk kin cika mana gida “, sakar baki zarah tayi tana kallansa , kafun tayi magana wata hamshakiyar mata ta fito daka wata kofa jikinta sanye da purple din material , sosai kayan suka haska kyakkyawar fatarta duk da ashekaru bazata wuce shakara 43 zuwa 44 ba , da sauri Khaleed ya karasa wajan ta kafun ya rungumeta, “ nayi kewarki oumma ,kullum sai nayi mafarkin abincin ki, da sauri na juya dan ganin wacce yake kira da oumma , sosai nayi mamakin ganin oumma ganin yanda hutu ya kwanta a jikinta ga wani irin masifaffen kyau da ta karayi sak buzuwa abunta, cikin nutsuwa ta sakar masa murmushin da dimple dinta sak irin na tahee lo’bawa “ Nima nayi kewar ka son, yanxu dai kaje kayi wanka kafun kaci abinci “, toh oumma ya fada tare da kallan zahra, da Sauri ta matso wajan “ oumma kinga ko , yaya Khaleed ya dawo yanxu kin dena sona daman yanxu dady kawai ke sona , hajiya ma ta dena sona “, hancinta oumma taja “ waya isa ya taba mun Autaras dina Kema kinsan wasa nake masa sabida ya dawo ne “, dariyar jin dadi kuwa zahra ta saki kafun su shiga kitchen ita da oumma, dakansu suka hada musu lunch, zahra ta nufi dinning tana shirya musu abincin, ita kuma oumma wani tray ta dauka ta nufi wata kofa , knocking din kofar tayi kafun a bata izinin shigowa , wata matace zaune akan wani lallausan carfet duk da manyanta ya gama fito wa a jikinta, murmushi ta sakar wa oumma “ sannu maryama , Allah yayi miki albarka , bakya gajiya da d’a wai niya “, murmushi oumma ta saki ba tare da tace mata komai, akan lallausan carfet din ta ajje mata abincin Daidai lokacin da Khaleed yake shigowa madaidaicin falo urn bakin shi d’auke da sallama, “ hajiya me rankarfe , kiyi aure mu huta” da kuwa wacce yakira da hajiya tayi masa , “ saidai kaine zakayi Auran dan jakar uba, aika dawo zamu dora , bari uban naka ya dawo da kai da waccen ya galalalliyar yazo yayi muku aure , Kai invaka da mata akwai wata yarinyar Dije yar kawar kawata ce da mukayi mutumci amma san yarinyar kamar zararriya, nasan Itace maganinka, ita kuma waccan yaga lalliyar a bata shu’aibu me wanki”, kamar mutumin arziki khaleed ya karaso inda take kafarta da ta mike ta fara yiwa tausa cikin kashe murya ya soma mata dadin baki “ Haba hajiyar mu me yayi zafi haka ,kinsan ba a shiga tsakanin mu dake ko, Indai mata ce zankawo miki ba da dadewa ba , kisha kuruminki”, ta bile baki tayi “oho maka “, kallan oumma dake faman sakin murmushi yayi,”oumma kisa baki mana “ dariya oumma ta saka tana mikewa “kunfi kusa Nidea ba ruwana , hajiya a huta lapiya “, itama hajiya murmushi ta sakar mata “ ala huta gajiya maryama,nagode “, kafun oumma ta fita daga parlourn.

Tana fitowa ta tarar da dady da zarah,jakar da ya ajje ya dauka kafin tayi masa Sannu da zuwa , zarah na ganin oumma ta nufi part din hajiya itama , kallanta dady yayi, “Amarsu wannan kyau haka kamar yau ce aka shafa lapiya , kullum sai wani kara kyau kike kamar ba yarinya ba,” kunya kalaman dady suka bata , bata san lokacin da ta dara ba kafun tayi wuce warta part Dinsu, shima bin bayan nata yayi lokacin har ta hada masa ruwa tana kokarin fitowa “ Ah ah me kike nufi , yau fa amaryace zatayi mun wanka gaskiya inasan jin dumin matata nifa ba gwauro bane “Innalillahi oumma ta fara nanatawa aranta , yau taga abunda ya fi karfinta, dady kuwa ko ajikinsa yazo zai rike oumma kuwa tayi saurin Zillewa sai da taje bakin kofa kafun ta sakar masa wani murmushi da ya kusa kifar dashi “ kiyi wanka , bari naje na hada maka lunch dinka “ bata bari ya kuma cewa komai ba tayi ficewarta, dariyar dattako Alhaji kabeer yayi “ maryam badai kunya ba “, yana gama maganar zucin sa ya shige bandaki.

FLASH BACK

Abunda ya faru, tun lokacin da dady da su zarah suka nema alfarmar oumma ta zauna , gabaki d’aya tundaga lokacin wani irin shakuwa ce ta ban mamaki ta shiga tsakanin ta dasu zarah , duk da a yawancin lokuta gaisuwace take hada ta da dady, sati daya da faruwar haka dady ya yanko musu ticker zuwa abuja , inda yake rayuwa da mamansa, koda hajiya fatima taji labarin maryam itama sosai oumma tashiga ranta musamman yanda taga su zarah na kaunarta har hakan ya so bata mamaki.itama oumma gabaki d’aya ta fawwala lawa Allah lamuranta, a kullum ba ta gajiya wajan yiwa ya’yanta addua, har yanxu bata fidda Saran watarana zata gansu ba. Kwasam wata ranar litinin dady ya bijurowa hajiya cewar yanasan ya auri maryam sai su cigaba da kula dasu zarah kafun aga tahee da ya bata duk da haryanxu ana kan dubosa,itama hajiya sosai taji dadin maganar dakanta ta kira oumma akan auranta da dady yakeso yayi, rasa abun cewa oumma tayi ganin yanda dady yake satar kallanta yana jiran amsarta, a gefe guda ma hajiya na Rokan Allah kar maryam tace ah ah , wata iriyar kunyace ta kama oumma ganin yanda suke binta da kallo, a hankali ta furta “ Allah ya tabbatar da Alkairi”, ba hajiya ba hatta dady saida ya saki ajiyar zuciya, bakaramun dadi hajiya tajiba harda dan kukanta Aushe da raban zata kara ganin auren kabeerunta. A bangaran oumma kuwa har kuka sai da tayi ranar ganin yanda zarah da Khaleed suka nuna farincikinsu.wata iriyar soyayya dady yake nunawa oumma ko kunyar su Khaleed da hajiya bayayi, tun tana jin nauyin yadda yake nuna mata soyayya har ta soma bashi martani, sati biyu da hajiya taga abun nasa na musamman ne tasa aka daura musu aure da oumma .

BACK TO STORY

A dinning oumma tayi serving Dinsu abinci gabaki dayan su, ko wanne da annashuwa a kan fuskarsa,”yy khaleed har yanxu baka bani tsarabar bafa sai jamun rai kake”, kallanta yayi kafin ya kai wainar masa bakinsa, saida ya tabbatar ya cinye kafun ya soma magana , “ Na fasa , kin bi kin adda Beni kamar kin aikeni”, kamar zatayi kuka ta furta “shikenan “ ta mike da niyar tafiya, daga dady har oumma babu Wanda ya tanka musu, saida yagama cin abincin sa tsaf kafun ya zuba wani a plate , kallanshi oumma tayi alamun karin bayani” zan kaiwa autane, in tayi fushi dani ai babu zaman lapiya , yanxu sai tasa dady ya koreni”,gabaki d’aya dariya suka saki jin kalaman sa , yana barin wajan shima dady ya kalli oumma , “yanxu saura aikin lada , kin bawa kowa abinci a baki ban dani”, da Sauri oumma ta mike , dady yayi saurin rike hannunta , waigawa oumma tayi gudun kar wani ya gansu “ dan Allah kasakar mun hannuna kar wani yashigo”, shikenan zauna ki baki a baki , ba musu kuwa oumma ta fara bashi, befi spoon biyar ba ta gudu falourn hajiya .

( Soyayya bata tsufa, dady ka bani kunya 😂😂).

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

A tsaye ya tarar da ita tana gyara dakinsa , da Sauri ya karasa ya karbi towel dinta “ banaso ki bari” sakin baki tayi tana kallansa yau taga ikon Allah “ ka bani gyara fa nake “ a maimakon ya bata kamata yayi ya zaunar da ita kafun ya taba cikinta, “karna kara gani kinyi wani aikin , okay “lapiya ta fa kalau, shima amsa ya bata “ eh na sani ai , common me zakici” bata dade da Shan complex ba “ na koshi” me kika ci!? , itama amsa ta bashi da complex, girgiza mata kai yayi “ it’s not a food, zo muje kici wani abincin”, zanyi amai idan naci kabari anjima kaji,” be kuma ce mata komai ba sai cikinta da yake shafawa a hankali har yanxu jinsa yake kamar a mafarki, itama lafewa tayi a jikinsa sabida yanda take jin dadin yanda yake shafa mata cikin.

Yinin ranar gabaki d’aya tare da tahee yayi shi, hatta abinci da kansa yake bata,ita kuma sai faman narke masa take. Da daddare ma lokacin da zasu kwanta sai faman shagwaba take masa hakan da take kuwa ba karamun zautar dashi yake ba musamman breast dinta da suka cika masa ido ga wani girma da yaga sun karayi masa, be san lokacin da ya fincike rigar jikinta ba ta ynda zai ga breast din da kyau. Ga baki d’aya ta birki ta masa tunanin, hatta lokacin da zai kusanceta jiyayi ta canza masa, kara susucewa king yayi gudun karya ji mata ciwo ne yasa yake binta a hankali sai faman surutai yake yi.
GIDAN AUNTY

MSS LEE
07041879581

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button