Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 20

Sponsored Links

Episode 20*

 

A fusache DON yamike ya ɗaga yatsu biyar zai zabga mata mari green eyes nashi ya sauƙa a kan face ɗin Aryan dake zaune ya zuba musu ash eyes nashi ” da sauri Ammi tace karka kuskura ka kai hannunka jikinta takarisa maganar a fusache”a hankali DON ya sauke hannun’sa sai huchi yake tamka wani zaki, bai karisa sauke hannun’sa ba, yaga Aryan ya miƙe ya ɗauke Aunty Maryam dawani gigitachen mari yasake kara mata ta ɗayan gefen kumatun a fusache yayi kanta daniyar bugunta ” da sauri DON ya rikesa yana faɗin NO Aryan NO idan kace zaka bugeta a yanayin dakake’n nan wlh zaka iya kasheta ” Prince kasake kasakeni nacema Aryan yayi maganar chikin tsawa da zafin rai ” bazan sake kaba Aryan kadawo chikin hayyachin’ka mana kasan me kakesan aika tawa kuwa ” Aryan idon’sa ya rufe chikin tsawa yake magana Safras nache kasakeni koh “DON yalura Aryan baya chikin hayya’chensa, dan kuwa baitaba kiransa da Safras ba sai dai yace DON kokuma prince dan haka sai yayi kokarin jansa sutafi ɗaki ” Aunty Maryam kuwa rungume Aunty amarya tayi tana kuka ” Ammi tamatso kusa da Aunty amarya tana faɗin kiyi hakuri Maryam ” chikin kuka Aunty Maryam ke faɗin munafuka ina ruwanki dani duk bake kika haddasa fitinarba ” wani kukan kura Aryan yayi ya kwache daga rikon da DON yamasa yanufeta gadan gadan fiskarnar tasa gaba ɗaya ta sauya idon’sa sun ƙaɗa sunyi jaa sai huchi yake jijiyoyin kan nan nasa duk sun miƙe gadan gadan ya tun kareta kamar wani mayinwachin zaki ” aguje kannen nasu sukabar palon, yarage iyayen nasu sai Aunty farida Khalid da kuma yusuf Aiman da Ahmad ma sun gudu dan sun san hali Aunty salma Aunty mardiya ma duk sungudu ” harɗe hannu a kirji DON yayi a zuchiyar’sa yana faɗin awan nan karon kam bazan hanaka ba Aryan dan kuwa ta tsallake iyakarta ka bugeta kai ɗin zaifi domin ni innace zan bugeta tofa sai dai a ɗau gawarta shiyasa tun ɗazun nake kokarin danne zuchiyata karta haura

Aunty Maryam ganin Aryan ya nufota gadan gadan ne yasa ta zame jikinta daga na Aunty amarya zata gudu “wani damƙa Aryan yawa wuyar’ta, ta baya yajata ya bugata da jikin table,ya sake damkoh wuyar’ta yana kokarin kai mata wani bugun” ganin Aryan na kokarin kisan kai yasa Aunty farida ta nufesa da gudu ” a fusace yaɗaga hannu zai ‘kaiwa Aunty Maryam bugu a fuska da sauri Aunty farida ta kama hannun ta baya ” azuchiye yajuyo yana faɗin kasakeni DON tun bandawo kankaba ganin Aunty farida che ta rikesa yasa ya sassauta murya,pls pls Aunty farida sau ɗayan nan kawai ki kyaleni na hukunta Maryam, tun batayi aure ba takewa su Ammi wan nan rashin kunyar, dan Allah yau kubarni na dawo da ita kan hanya ”

Aryan idan kasake ɗaura hannunka a jikin Maryam dasu nan duka ban yafemaka ba chewar Aunty amarya tayi maganar rai a bace, “runtse ido Aryan yayi ya kwache hannun’sa daga chikin na Aunty farida zuchiyar’sa na tafasa yajuya a fusace yanufi hanyar fita daga palon ” Abba dake tsaye a bakin kofa tun ɗazun yana kallan’su yakasa shigowa yasa hannu ya tare Aryan yana kallan fuskar’sa” juya mukoma chiki chiwar Abba, gaba ɗaya jama’a dake chikin falon suka juyo suna Abba ” a nitse Aryan yajuya ya koma ya zauna a kan kujeran table ɗin ” Abba bi bayan’sa da kansa ya buɗe robar ruwan faro mai sanyi ya zuba a glass cup yamiƙawa Aryan ” ba musu ya karɓa ya sha” ku zauna gaba ɗayan ku Abba yabasu umarni rai a bace ” zama sukayi a kan kujerun” tashi kema ki zauna chewar Abba yayi maganar yana nuna Aunty Maryam dake kwanche kasa tana kuka, da kyar tamike ta zauna a kan kujeran itama kusa da Aunty amarya, ga shatin yatsun Aryan biyar a kan kunchinta gefe dukka biyu “A nitse Abba yafara magana abu biyu zuwa uku nakesan faɗa a nan kubani hankalin’ku ta farko nan umarni’ne ba shawara ba duk wan da yayi laifi a gd yazama dole a hukuntashi dan haka hajara kijanye kalamanki nachewa kar Aryan yasake,taɓa Maryam yazama dole intayi laifi sumata hukunchi,duk datake babba a kansu intayi ba dai dai ba zasu mata hukunchi, na biyu wan nan maganar ta mutu daga nan ” na uku ke Maryam wlh kinji na rantse ko ko kallan banza kika sake yiwa yaran nan to ban yafe’miki ba, ba ruwanki dasu tunda bazuwa ɓan’garen’ku sukeba, ya karisa maganar chikin faɗa,sai dayaja, kutashi kuje kuyi sallah lokachin sallar issha yayi ” da sauri Aryan ya miƙe daman kamar a kan kaya yake dan baisan ganin Aunty Maryam, miƙe’wa DON ma yayi da sauri yabi bayan’sa, dan yaje ya taushesa, yadaɗe baiga Aryan a irin wan nan bacin ranba “Khalid da Yusuf ma suka mike sukabi bayan’su DON ” Aunty farida takama han’nun Aunty Maryam sukayi waje,”Ammi da Ummi ma suka mike a tare ” Abba yace Aisha keda hajara ku zauna zanyi magana daku,”Ummi najin haka tayi waje” Ummi nafita

A nitse chikin sanyin murya Abba yafara magana,” ke Hajara banace kijanye maganar dakikayi tsaka’nin Aryan da Maryam ba,banji kinche komaiba ” na janye Aunty amarya tafaɗa tana ɗaure fuska ” to tashi kije kiyi alwala kiyi sallah,”mikewa tayi tana kunkuni tafice daga palon
sai da Aunty amarya tafice san nan Abba yadawo da kallan’sa kan Ammi yafara magana, idan yaran nan sunyi sallah kisa diyana ta kaiwa Aryan coffee kinji ” to amma ranka shi daɗe kagafa ran’shi a ɓache kuma kusan diyana’ce ta hadda’sa masa ɓachin ran, idan taje bazai bugeta ba kuwa Ammi ta karisa maganar kamar zatayi kuka ” Abba yace aa Aisha bantaɓa magama kimin musu ba komai nace to kawai kike chewa yanzu’ma to kawai nakesan kice kuma ki isar wa diyana da sakoh na, ya karisa maganar yana kokarin mikewa a chikin zuchiyar’sa kuwa yana faɗin ae diyana ce kawai zata iyasa Aryan ya saukoh domin kuwa duk wani motsi na ƴa’ƴana ba wan da ban sani’ba duk wani abun da Aryan keyi ina sane dashi yanzu haka ba abun dayake bukata daya wuce yaga fuskar’ta da wan nan tunanin yashiga ɗaki, ” Ammi kuwa jiki ba kwari ta miƙe tafice daga palon tanufi ɓan’garen’ta

Ammi na fita palon Abba kai tsaye,ɗakin’su diyana tanufa, da sallama tashiga ” kwanche suka su uku a kan gadon’su hiyana diyana Zahra, su amrat sun koma ɗakin’su ” suna ganin Ammi suka miƙe zaune,karisa shigo chiki Ammi tayi a bakin gadan ta zauna tasa hannu dafa hiyana tana faɗin sannu koh, Allah ya baki lfy ” hiyana tace amin, Ammi ina wuni ” murmushi Ammi tayi kafin tace lfy kunyi sallar issha’ne “aa bamuyi ba chiwar diyana ” to kutashi kuyi sallah zansa a kawo muku a’bunchi kuchi sai ku kwanta ku huta koh ” har suna haɗa baki wajen chewa to Ammi a tare suka miƙe,
Ammi ma tamiƙewa tayi tanufi hanyar fita, har ta kai bakin kofa kuma sai tajuyo ta dubi diyana, ke diyana idan kinyi sallah kikai’wa yayan’ku Aryan coffee ” kaiii Ammi tsoran’sa fa nake ji kar naje ya bugeni ” aa diyana bazai bugeki ba kiyi sallah kije ki haɗa masa da sauri ” to Ammi amma zanyi wanka tukun nan ” to koma me zakiyi dai kiyi dawuri ki kai masa takai karshen maganar tana mai fichewa daga ɗakin

Toilet diyana tashiga tayi wanka a gurguje ta ɗauro alwala tafito, tana fita Zahra tashiga itama danyin wanka,” shifiɗa dardu’ma diyana tayi ta ɗaura zani tasa hijab, kawai tatada sallah,”tana sallame, sallar tayi adduar, ta sosai tashafa ta mike zata naɗe, daddumar ” hiyana tace aa kibarmin zanyi Sallah” to kawai tace tanufi gaban mirrow ” diyana mezakiyi hiyana ta tambaya tana taɓe baki ” kwalliya,mana me zanyi,kuma ” kwalliya da daddare to Allah ya shirya’ki ” Ameen to tun da addua che diyana tafaɗa tana kokarin shafa foundation a fuska ” light make up tayi a face nata ta ammafa bakamin kyau tayiba, jan baki pink colour tasa a ɗan karamin bakin nan nata, sai kallan kanta take,a mirrow “Zahra dake zaune bakin gado tana jiran diyana ta matsa, awajen mirrow, itama tazo tashafa’mai,” tace kai diyana kinyi kyau har kingaji da kyau dan Allah kije, kisa kaya kikai’wa yaya Aryan coffee sa karyazo ɗakin nan ya same’mu ” dariya diyana tayi tana faɗin, Allah Aunty Zahra nayi kyau ” eh mana sosaima yanzu dai jekisa kaya,” da farinchiki a face ɗinta tajuya tanufi sip ɗin kayan’su doguwar rigar da Aunty farida ta kawo musu ta ɗau koh, zatasa ke nan ” Zahra tace diyana yakamata kisa bra kafin kisa rigar nan zaifi zama maki da kyauu dan kinga yana da igiya inba bra, aka ɗaure igiyar baya kyau ” yauwa Aunty Zahra idan dai zanyi kyau kawai kisamin diyana tafaɗa tana murna ” shiru Zahra tayi tana tunanin wai ita’kam diyana inazata kai kyau’ne, duk wan nan kyan da Allah yamata, bai isheta’ba take neman kari, duk wani abun da kacewa diyana zai ƙara mata kyau tofa koda abun bai mataba sai tayi amfani dashi itadai kawai taji anche taƙara kyau, Zahra tayi nisa chikin tunani bata an’karaba kawai sai taji ” diyana na taɓata Aunty Zahra kisamin abubuwan bra ɗin ” to juya nasa miki ” juyawa diyana tayi zahra tasa mata karfen bra ɗin ” hiyana dai baki ta taɓe tana ganin ikon god” komawa diyana tayi gaban sip ɗin ta ɗauki rigarta tasa, ta ɗaura igiyar rigar tayi kyau sosai ta ɗauki mayafin rigar ta rufa akanta tanufi wajen shoe rack nasu high heel blue kalar rigar ta ɗauƙa tasa tanufi waje kwas,kwas,kwas, abunta ”
baki buɗe hiyana ke kallan diyana har tafita ajiyar zuchiya ta sauke ta dawo da kallanta kan Zahra”Aunty Zahra kinsan me ” Zahra tace aa bansaniba hiyana am sai kin faɗa ” wlh inaga nan gaba kasuwa kwalliya gaba ɗaya za a’ɗaukowa diyana ” dariya Zahra tayi tana faɗin eh gaskiya kam naga alama nima ” hiyana zatayi magana sukaji kwas,kwas,kwas, ” ba ko sallam diyana tashigo da sauri gaban mirrow takoma ta ɗauki kwal’bar turare hunrar da Aunty farida ta bata ta shafa a jikinta dan Aunty farida ta faɗa mata indai batasa turare bazatayi kyau ba da sauri ta ajiye kwal’bar tanufi waje ” su dai su hiyana sunga abun dayafi karfin’su ” miƙewa hiyana tayi daga kan daddumar takoma kan gado ta kwanta ” zahra Kuma ta ɗauki hijabin’ta tasa tatada sallah

A gurguje ta haɗa masa coffee ta ɗauka tanufi ɓangaren’sa da sallama tashiga palon babu kowa kai tsaye tanufi betroom ɗin sallama tayi a bakin kofa, bata jira an amsa’ba kawai tashige chiki ” kwanche yake a katafaren gadonsa idonsa a lumshe farin singlet da short ne kawai a jikinsa asalin kirar’sa na jaruman maza ya bayyana ga wani gashi baki kwanche a chin yoyin’sa har zuwa kafofin’sa damtsen hannun’san nan kuwa kamar zasu fashe saboda karfi ” kan ɗan karamin table na chikin ɗakin ta ajuye coffee ɗin tanufi bakin gadon, zama tayi kusa dashi a nitse da cool voice kamar mai raɗa tafara kiran sunansa, tana ɗan bubbuga hannun’sa yaya Aryan, yaya Aryan katashi na kawoma coffee karyayi sanyi ” slowly yafara ware ash eyes nashi wanda suka chanza zuwa launin jaa, sauke idan nashi yayi a kan face ɗin ta, ƙara waresu sosai yayi yana kallan’ta ” diyana sai data tsorata ganin yadda idonsa suka chanza launi” mikewa tayi zata gudu ” hannu yasa da sauri ya riƙo hannun’ta, ya jata baya, ta koma ta zauna” kallanta yake sosai, nan take yaji wani sanyi na ratsa zuchiyar’sa wani farinchiki yaji, jiyake wani bakon yanayi na ziyartar zuchiyar’sa” turo ɗan bakin nan nata tayi kamar biro a shagwaɓe tafara magana yaya Aryan kayi hakuri kaji dan Allah karka bugeni, ta karisa maganar kamar zatayi kuka “shiru yayi yana kallan’ta, yakasa magana almost 10 mnt suna zaune haka yanata kallan’ta,kamar yamai data cikin’sa yakeji”turo baki diyana tasakeyi tana faɗin yaya Aryan dan Allah fa nace kayi hakuri ba dan niba” ɗan firgita yayi yadawo daga duniyar tunanin dayashiga” calmly yafara magana baki iya gaisuwa bane kuma wayace kiyi kwalli da daddaren nan” kayi hakuri to, ina wuni tafaɗa tana kun bura kumatu” sakin hannunta yayi tare da mikewa zaune ” itama ganin yasaketa tamiƙe tana kokarin tafiya ” ina zakije ya tambaya yana kallan’ta from head to toe ” ɗaki zanje ” nace kitafine ” aa kayi hakuri “to dawo nan ki zauna yayi naganar yana nuna mata drawer kefen gadon ” saman drawer taje ta zauna tana fiskantar kofar toilet
“juyo nan ki kalleni magana zanyi dake, a nitse ta juyo tana fuskantar’sa,ganin itayake kallo yasa tayi ƙasa da kanta tana murza yan yatsun hannun’ta ” dawo da kallan’sa yayi kan hannun’ta sosai yake yakara waro idan’sa yana kallo lallenta, ba’ƙaremin kyau lallen yayi masaba ” wayamiki wan nan abin yayi maganar yana nuna lallen nata ” laaa Aunty farida ta kaimu a kamana mana kuma kasanme takawo min kayan kwalliya dayawa” zuba mata ido yayi yana kallan yadda take murmushi take magana a zuchiyar’sa yace thank God nima nasaya kayan kwalliyar
afili kuwa yace baki bani amsa taba nace wayace kiyi kalliya da daddaren nan” nan take ta ɓata fuska ta daina murmushi ta turo baki tana faɗin yaya Aryan baa kwalliya da da’ddare’ne “anayi mana kuma kinyi kyau sosai kawai dai nine banasan kirinƙayi ” nan take kuma tafara murmushi tace laaaa yaya Aryan da gaske nayi kyau ta tambaya ” girgiza kai kawai yayi ya zuba mata ido yana kallan yadda take dariyar azuchiyar’sa yake faɗin kekam komai kikayi kyau yake maki inkina dariya ki ƙara idan kina murnushi makura che ke, kai ko kuka kike kyau yake miki ” katse mishi tunani tayi dachewa yaya Aryan intafine” girgiza mata kai yayi alamar aa “kallansa tayi sosai sai kuma tace laaaa Yaya Aryan kayi rashin lfy ne” me kikagani yayi maganar da ɗan mamaki a face nashi ” ae Naga karame’ne tafaɗa tana kara kallan’sa sosai ” yayi mamakin sosai da jin abun da tace,a zuchiyar’sa yake faɗin wow intelligent girl,tabbas ni kai na nasan na rame amma bawan daya gane hakan ko DON damuke tare bai gane hakan ba sai ke wow,

Ajiyar chiya ya sauke ya ya juyo da idansa yayi kanta yaga itama shi take kallo,” sai yace aa banyi rashin lfy, jeki kawomin coffee ɗin karyayi sanyi ” da sauri ta mike tanufi inada ta ajiye coffee ɗin ta ɗaukoh,ta dawo tamiƙa masa ” ansa yayi yana faɗin to zauna muyi magana” zama tayi a inda tatashi ta zuba masa ido tana kallan,yadda yake shan coffee ɗin,”yaya Aryan kasan me” ɗago ido Aryan yayi yana kallanta batare dayayi magana’ba ” tachigaba dacewa Allah yaya Aryan kana kama da wan da yayi film ɗin Bahubali, nan Amma fa kafishi kyau, yama sunan shi, taƙarisa maganar tana ɗaga kai kamar mai tunani” da mamaki yake kallanta yana tunani wae daman yarinyar nan tana kallan mutane ne, murmushi kaɗan yayi yace nima bansan sunan shi ba ae ” to zan tanbayi Aunty Zahra sunan shi sai nazo nafaɗama ” batare da ya amsa mataba yace tashi kije ki ɗaukoh min trolley ɗin chan yayi maganar yana nuna mata inda trolley yake da hannun’sa ” da sauri ta miƙe tanufi wajen tayi tunanin trolley bai da nauyi, sai tasa hannu ɗaya zata ɗauka amma sai taji a’kasin hakan dan kuwa ko motsa trolley ta kasa, shi kuwa Aryan ya zuba mata ido yana kallan’ta
Dad dagewa tayi da iya karfin ta ta jawo trolley baya baya tayi tafaɗi trolley ya faɗo mata a kan kafa kara ta fasa mai sauti ” a sukwane Aryan ya ajiye cup ɗin hannunsa ya ya miƙe ya nufuta hannu ɗaya yasa ya ɗaga trolley ya ajiye a kan gado, ya dawo kusa da ita ya duƙa yasa hannu ya kama kafar nata yana faɗin, menene abun kuka kuma, ” yaya Aryan wlh da zafi tafaɗa chikin muryan kuka” a haka kike chewa zaki auri soja matan sojoji fa jarumai ne ” turo baki tayi ga hawaye na zuba a kunchin’ta chikin shagwaɓa tace Allah yaya Aryan nima jaruma’ce ” zuba mata ido yayi yana kallan yadda take Magana gwanin burgewa, hannu ya kai kan fuskar’ta zai share mata hawayen sai dayaji wani shock saboda laushin da tsasin fatar ta, da sauri ya janye hannun’sa baya yamiƙe tsaye yana faɗin to tashi kizo ki karɓi tsaraba yayi maganr yana hawa kan gadon’sa ” a sha’gwaɓe tace wayyo Allah yaya Aryan Allah bazan iya tashiba “a sukwane Aryan ya juyo yana kallan’ta, dan yadda tayi maganar, ” a hankali kamar bayasan buɗe bakin nasa yace ki daina kukan nan ko gashi nan ae kina ɓata kwalliyar’ki ” da sauri tasa hannu ta goge hawayen tana faɗin yaya Aryan kwalliyar ya bacine ” dariyace ta kubche masa dan yadda tayi maganar,”bai bachiba yabata amsa yana murmushi ” da kyar tamike tanufi kan drawer tana ɗingisa kafa ta zauna “hayewa gadan yayi yajawo trolley ya ɓuɗe, wasu ma tsakaitan jakun kuna guda uku yachiro, daga chikin trolley ɗin, ya juyo ya dubeta yafara magana,”wan nan farin tsarabar kine a chiki, wayan nan bakake biyun kuma kibawa’su Zahra “da sauri tamiƙe ta haye kadon itama ta jawo jakunkunan tana faɗin Yaya Aryan har da kayan kwalliya”kallan’ta kawai yake yadda take zumuɗi, da farinchiki, bai ma san sanda yace, daman farinchikin da dariyar ki kawai nake burin, gani “sai jin diyana yayi tana faɗin to Yaya Aryan dariyana yana da kyau’ne ” firgigit yayi yana kallan’ta kwashesu kije ɗaki kiɓuɗe a chan” to kawai tace san nan ta saukoh daga dagon tasa hannu tajawo jakunan amma takasa ɗauka sunyi nauyi bazata iya ɗauka dukkaba” ido yazuba mata yana kallan’ta” turo baki tayi zatayi kuka ” da sauri yace aa karkimin kuka ki ɗauka mana ɗai ɗai ae bawanda yace dole ki haɗa’su koh ” nasu Zahra ta ɗauka ta bar nata zataje ta dawo suma da kyar ta iya ɗauka gakuma high heel a kafarta
har tafita kallanta Aryan yake, wani ajiyar zuchiya ya sauke yamike yanufi toilet dan yin wanka

lokachin da diyana ta dawo ta ɗauki ɗayan jaka’r Aryan na toilet yana wanka bai fitoba ɗaukar jakar tayi yajuya har takai bakin kofa saikuma tajuyo ta ɗaga murya yaya Aryan sai da safe tana gama faɗin hakan tayi waje, ko data’dawo ɗakin’su su Zahra har sun buɗe jaka’r nasu tsarabar dogayen riguna’ne masu kyau da perfumes masu kanshi da tsada sai murna suke, zama tayi a bakin gado itama tafara kokarin buɗe nata jakar amma sai’taga nata jaka’r an sawa zip ɗin kwa’ɗo, tayi tayi yaki,ɓuɗuwa sai ta ɗauki jakar tanufi sip dashi tana faɗin sai da safe na kaiwa yaya Aryan ya buɗemin,ajiye jakar tayi,tachire kayan jikinta ta ɗaura towel tashi toilet tayi wank atazo gurguje tasa kayan barchi tanufi kichin ta haɗa coffee tasha tadawo ɗaki ta haye gadon’ta nan take barchi awon gaba da ita

Yau tun asuba ake shirye shiryen walima da naɗin sarauta ” Ammi tasha kwalliya da wata ɗankarekiyar,shadda tasha aikin har kasa Blue colour tasa wasu shaggun sarkan da abun hannu na gold mai shegen tsada ta ɗaukoh wani ɗankareriyar al’khaiba baki anmasa kwalliya da wasu suwasu mai kyalli fari tasaka a jikinta kai kace yar shekara 20 sosai kyanta yasake bayyana,”wayar’ta ta ɗauka tafa kiran layin Zahra, kira ɗaya Zahra ta ɗaga tare da faɗin hello Ammi” Ammi tace kuzo gaba ɗayan’ku kusameni a ɗaki tana gama faɗin hakan ta katse kiran, ta zauna a kan gado tare da ajiye wayar’ta a kusa da ita

Da sallama su Zahra suka shigo sunsha kwalliya sosai riga da sket na atamfa Zahra hiyana diyana sukasa,”amrat da lamrat kuma duguwar riga, karisa shiga chiki ɗakin sukayi ” Ammi tace aa harkun shirya ne” har suna haɗe baki wajen chewa eh “ae ba wan nan kayan zaku saba Zahra’u tashi ki buɗe drawer kayana ki ɗaukoh muku kwalin kayan da zakusa, sai ku koma ɗaki ku chanza ” da sauri Zahra tamiƙe ta ɗaukoh musu sarine irin na indiyawa, kwali biyar kowa da kalan nasa ” Zahra baki,hiyana pink, diyana blue,lamrat jaa,amrat maroon” da zumuɗi diyana ta ansa nara tana faɗin Aunty zahra irin kayan danake ganin indiyawa suna sawa a TV nan ne ” Zahra tace eh shine” to ae Aunty Zahra ban iya sawaba tayi maganar kamar zatayi kuka ” dariya Zahra tayi tace to muje na koya miki” da fara’a diyana tamiƙe har suna haɗe baki wajen chewa Ammi mungoɗe

Dakin su suka koma Zahra tafara nuna musu yadda ake sawa wow kayan yamusu kyau sosai da sosai hiyana da amrat nasu najaa a kasa sosai dan yafi tsawon’su
yau make up sosai sukayi dukkan’su baƙaramin kyau sukayiba, hiyana kamar ita tayi kanta yau asalin kyanta ya bayyana datayi make up, Zahra sai santin kyan hiyana take har ita kanta diyana sai da tayaba kyan da hiyana,tayi” Zahra tace kai kuzo mutafi fada dan nasan yanzu gaba ɗaya an haɗu awajen kar ayi bamu kuyi sauri tayi maganar tana kokarin fita ɗakin ” da sauri suka bi bayan’ta

Yau fada chike yake tab da jama’a baki dayawa sunzo dan naɗa sabon sarki da za’ayi Abba yasha kwalliya irin na sarakuna sosai yayi kyau yana zaune a kan kujerar sarauta Ummi Ammi Aunty amarya suna gefensa ga wasu kugeru a gefe dama da a ka jera wanda su Khalid, Aiman, Ahmad, Yusuf, Fahad, Haidar umar Aunty farida Aunty salma Aunty, mardiya, Aunty, Maryam, ne zaune awajen, “kujerun gefen hagu kuma manya manyan saraku daga sassa daban daban na Nigeria da ma makwabtar kasashe irinsu niger,Cameron, Ghana,chadi, da dai sauran’su , ga manya manyan yan siyasa a gefe guda ” DON da Aryan ne kawai basa wajen, fada yayi tsit kamar babu mutane a chiki kowa yayi shiru suna jiran juran jawabin Abba

Da sallama ɗauke a bakinsu suka shigo fadan, gaba ɗaya jamar waje suka ɗago suna kallan’su kamar wasu taurari sai wal’wali da kyalli suke ” gaban Abba sukaje suka duka hiyana’ce tafara ɗagawa Abba gaisuwa “yusuf sai kallon lamrat yake yakasa ɗauke idonsa haka shima Khalid sai kallan Zahra’n sa yake ” da fara’a Abba ya amsa gaisuwar tasu ya ɗora dacewa kutashi kuje kuzauna kusa dasu farida, to sukache tare da miƙewa suka nufi wajen’su Aunty farida ” diyana kije ki kiramin Aryan ke kuma hiyana kije ki kiramin Safras Abba yafaɗa yana ɗaure fuska dan Aryan da DON sun ɓata masa rai tun dazun ake juran’su amma shiru” da sauri diyana ta juya ta fita, itakuma hiyana tafiya take kamar wadda kwai yafashewa,a chiki kamar zatayi kuka tafito daga fada ta nufi chikin gd

A hankali ta tura kofar ɓangaren nasa tashiga, sallama tayi a palon, kasa babu kowa kamar zatayi kuka ta shigo chikin palon babu kowa, a nitse ta haura stair ɗin tsayuwa tayi a bakin kofar betroom ɗin tanata doka sallama amma shiru shiru almost 20 mnt bataji wani motsi’ba, a hankali ta hannu ta tura kofar tashiga, tana shiga taji kofar yayi kara alamar ya rufe kanshi juyawa tayi tana bin ɗakin da kallo wani katafaren gadone mai girma da kyau yana shinfiɗe da betshit na alfarma Sky Blue ga wani haɗaddɗen sofa guda ɗaya a gefe sai wasu tagwayen kofofi da alama ɗaya kofar toilet ne ɗayan kuma kofar shan iskane,

shiru ta tsaya tana tunanin,kuɗin da aka kashe a ɗakin nan jin karar buɗe kofa yasa tayi saurin kai kallanta wajen zubawa kofar ido tayi dan taga wanene zai fito ” DON ne yafito ɗaure da towel a kugun’sa ga jikinsa da ruwa da alama wanka yayi ” wani kara hiyana tayi wadda yasashi juyowa a sukwane dan baiyi zatan da mutun a ɗakin’ba ” juyowar dayayi bakaramin rikitata yayi ba a guje ta juya taruɗe tama rasa ina zata nufa kawai sai tanufi kofar bangaren hagu tunda taga kofar a buɗe yake tana fita tayi rashin sa’a ta taka sarin’ta dake jaaa a kasa ta kai kai ta tafi kasan bene kallamar shahada kawai take dan tasan mutuwa zatayi..✍️✍️

Tanbaya a nan shin hiyana zata faɗi kasan benen nan kuwa? Shin intafaɗa zata rayu kuwa? ko’ko kar ku manta bene hawa ɗaya tafaɗo daga sama kudai sai mun haɗu

 

More comments pls 🙏🙏

*💫STAR LADY💫*

 

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button