Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 14

Sponsored Links

Episode 14

A fusace jabair yanufi diyana, tana tsaye ko motsi batayiba kuma babu alamar tsoro ko kaɗa a face nata ” hannu Jabir ya ɗaga zai’kaiwa diyana bugu ” da sauri hiyana tarike hannun nasa ” a zafafe Yajuyo yaga waye yarike masa hannu, ganin hiyana che yasa ya watsa mata harara yana faɗin sakeni ” ita ma rai a bace tache wlh bazan sakekaba kafara buguna tukun nan kafin kabugi diyana ” fisge hannunsa yayi yasake ɗaga hannu zai mari diyana ” da sauri hiyana tashiga tsakanin’ su tana faɗin diyana kiwuche class naku ” diyana dake tsaye babu alamar tsoro a face ɗin ta tace babu inda zanje hiyana sai dai duk abun da zai’mana yamana tare ” ganin haka yasa jabir yajuya yabar wajen dan kuwa bazai iya bugun hiyana ba dan yana sonta itakuma bazata taɓa barin abugi diyana ba ” suna ganin jabir yatafi suka rungumi juna ” diyana nafaɗin wlh sauran kaɗan nayi fitsari a wandona dan tsoro, dayanzu jabir yabugeni da wan nan katakon hannun nasa ai nashi uku ” dariya hiyana tayi sosai san nan tace wlh ba kyaji diyana ae nima nakusa fitsarin saboda tsoro kawai dagewa nayi dan bazan iya ganin ya sauke wan nan jibgegen hannun nasa a jikinkiba ” dariya sukayi gaba ɗayansu san nan suka saki juna suka reke hannun’su chikin na juna suka nufi class,

KASAR SAUDIA

Tsaye yake gaban mirrow yana gyara gashin kansa sanye yake chikin wandon jeans Navy Blue da White t-shirt, bakaramin kyau kayan suka masaba sosai ya gyara gashin kan nan nasa ya tara ya ɗaure ta baya, yasake ɗaukan turare yafeshe jikinsa,ga sajen nan nasa kwanche a kan face nashi kamar wani balaɓe wayarsa ya ɗauka yafito wajen kai tsaye palon kasa yanufa, zaune yasamu yan uwan nasa gaba ɗayansu har dasu haidar, kallan DON yayi yafara magana ” zan fita inasan inje wani wajen ” da mamaki DON ya ɗago green eyes nashi yana kallan Aryan ya mai maita maganar zai fita inasan inje wani waje shiru yayi kamar mai tunani ” Aryan dai ido yazuba masa kawai yana kallan’sa ” zarginafa yafara tabbata a kanka Aryan chewar DON ” murmushi kaɗan Aryan yayi san nan yace au daman zargina kake ke nan ” yap zuchiyata na zargin wani abu ” matsowa Aryan yayi kusa da DON sosai san nan yafara magana karkabar zuchiyarka tana raya maka wani abu a kaina kasan dai wlh babu wani abun dazanyi batare da saninkaba yanzunma kasawu zanje kuma nasan bazuwa zakaiba konache muje, shiyasa banche mujeba nayi shirina na zuwa nikaɗai ” dogon numfashi DON yaja san nan ya jinjina kai yana faɗin ok to shike nan nayarda ba komai Allah ya tsare a dawo lfy yayi maganar yana kokarin mikewa kai tsaye stairs ɗin yanufa ” binshi da ido Aryan yayi har yakurewa ganinsa san nan ya dawo da kallansa kansu Khalid ” a nitse yache na wuche ” adawo lfy suka masa gaba ɗayansu ” san nan face yana amsawa da Amin
Mikewa Khalid yayi yana faɗin Yusuf muje Koh ” mikewa Yusuf ɗinma yayi zasu wuche waje sukaji Ahmad na faɗin wlh akoi abun da kuke shiryawa, wani harara Khalid ya wurgawa Ahmad batare da sunyi magana ba suka nufi hayar fita palon ” kallan Aiman Ahmad yayi yana faɗin tabbas yaya Yusuf da yaya Khalid suna shirya wani abun ” mikewa Aiman yayi yanufi staircase ɗin yana faɗin zanyi binchike a kansu ae zan samusu ido sosai yanzu ” mikewa Ahmad ma yayi yabi bayan Aiman ” dogon tsaki fahad yaja san nan yace wlh yaya Ahmad da Yaya Aiman kunchika gulma ni barima naje na gaida su ammi yayi maganar yana kokarin mikewa ” haidar da umar suna ganin fitar fahad suka kwashe da dariya kamar abun haɗin baki sai dasukayi mai isarsu, tukun nan suka tsagaita ” kasan me haidar da alama fa akoi dirama a gd nan wlh chewar umar ” jijjina kai haidar yayi yana faɗi babbama kuwa, amma naga alamar yau yaya Aryan nachikin farinchiki sosai bakamar jiyaba ” kai dai tashi muje mu gaidasu Abba inmunje ɗaki makarisa magana chewar umar a tare suka mike sukayi waje,

Mai martaba Ammi Ummi Aunty amarya zaune suke a nasu palon suna hira “Fahad yashigo da sallama” amsa masa sallamar sukayi yashigo chiki ya zauna saman sofa ya fara gaida iyayen nasu ” da fara’a suka masa ”

Ummi ta dubi mai martaba tace ranka yadaɗe wai yabatun komawar yaran nan bakin aikinsune ” shiru Abba ya ɗanyi kafin yace bayan zuba sai bayan naɗin sarauta ” eh hakanma yayi chewar Ammi ” aa baiyibakam gaskiya sukoma wajen aikinsu chewar Aunty amarya ” jinjina kai mai martaba yayi yana faɗi aa aini ba zaɓinku nanemaba bare kufara musu hukunchina kawai nayanke sai anyi naɗin sarauta ” calmly Fahad yafara magana Abba inasan zuwa Us ” da sauri Ammi ta ɗago tana kallansa zatayi magana mai martaba yarigata dachewa sai kayi aure tukun nan dan inbakiyi aureba bazaka sake fita Nigeria ba ” baƙaramin daɗi Ammi tajiba jin amsar mai martaba ” Fahad kuwa a razane yace Abba Aure fa kace ” eh aure a kache auren wani mugun abune Ummi tabashi amsa rai a bace ” bahaka bane Ummi bawai auren ne mugun abuba taya zanyi aure su DON basuyiba ” dogon numfashi mai martaba yaja san nan yace ae suma a nayin naɗin sarauta, zansa su sufito da mata dan ya isheni ganinku haka ” dariya Fahad ya kwashe dashi yana faɗin wayyo duniya wayaga DON da mata chab to wai suda ko yanmata basu taɓayiba ai na zasu samo matar ” Ammi tace kai banfa san iskanchi kasani ne dasu kake fitane ” ae Ammi infaɗamiki duk wanda yasan yaya Aryan yaya Prince yaya Yusuf yaya Khalid yaya Aiman yaya Ahmad yasan basuda budurwa kuma basu taba chewa ko chikin wasa sunasan wataba suda ko kalloma mace bata ishesuba ” tashi kafita mana a ɗaki chewar Ammi ” fahad zai sake magana sai sukaji sallamar Haidar da umar ” Abba yace yauwa kuzo nan kuma daga yanzu kuje kufara neman matar aure dan wlh bayan naɗin sarauta duk aurar daku zanyi na huta ” ɗaure fuska haidar yayi san nan yajuya yanufi hanyar fita yana faɗin inazuwa ” salati Aunty amarya tayi kana tace yanzu maganar auren ne tasa kajuya kafasa shigowa koh haidar ” haidar dai baibi ta kansuba yayi waje da sauri ” da sauri umar ma yajuya yabi bayansa ” mikewa Ummi tayi tana faɗin kai jama’a zama bai gammuba wayan nan yaran sai na danganasu da ɗakin kaba barima naje nafara musu addua tun da sassafen nan yara saikache wadda aljana ta aura, ” Mikewa Ammi tayi tace muje tare wlh sai mun haɗa da sallar darema dan abun nasu yafara wuche hankali ” mai martaba ma yamike yana faɗin muje tare dan nima naga alamar sai na haɗa da tawa adduar ” a tare suka nufi waje Aunty amarya kuwa tamike tanufi ɗaki ta haye gado ta kwanta ” baki buɗe fahad ke kallansu Abba har suka fice afili yace wai muza’awa tsayuwar dare harma da danganamu da kaba yanzu mai mukayi hmmmm baridai naje nafaɗawa DON halin da ake chiki yamike ya fito ya haye lifter yakoma sama

Da sallama yashiga ɗakin don kwachi yasameshi a kan makekiyar gadon sa yana latsa waya karisawa chikin ɗakin fahad yayi ya haye gadon ɗago kai DON yayi yana kallansa ” kwaɓe fuska fahad yayi kamar wadda ya taka kashi ” lfy kazo kana bata rai DON ya tambaya ” daman kamar jira Fahad yake a tambayesa nan take yafara faɗawa DON abun da yafaru a ɗakinsu Ummi yanzu ” dogon tsaki DON yaja yana faɗin to suyi tsayuwar asubama ba na dareba ni dallah tashi kabani waje na daukama wani abinne nine za’achewa na kawo mata aure niɗin never wlh babu aure a tsarin rayuwata ” da karfin guiwar fahad yamike yafito dan shi a tunaninsa DON zai watsa maganar auren

KANO STATE NIGERIA

Misalin karfe 4 na yamma suna zaune a palon Ammi hiyana na karatun qur’ani diyana na game a wayar Zahra ” Zahra kuma tana gyarawa amrat gashi ” lamrat kuma tana Assessment na English da a kabasu a school kawai sukaji diran motochi gidan jiniya kakeji ta ko ina ya karaɗe gidan ” diyana tamike tana faɗin kodai su Abba ne suka dawo ” aa basu bane chewar zahra ” hiyana zatayi magana ” Zahra tace kutsaya kutsaya naji kamar busan gidan sarautane hakan nanufin Aunty maryam ne tazo tab ” da sauri Hiyana ta ɗago tana kallan Zahra wacece Aunty Maryam hiyana ta tambaya tana kallon Zahra ” babban yarinyar Aunty amaryan che chewar Zahra ” tab wlh tun danaji yarinyar Aunty amarya che nasan muguwache irinsu yaya Aryan chewar diyana ” baki buɗe hiyana ke kallanta san nan tace ke diyana nikam taushe zakiyi hankaline haka a kachemiki ita muguwace ” da sauri zahra tace aa hiyana diyanafa batayi karyaba tabbas aunty maryam muguwace nabugawa ma a jarida ” lamrat tace to Aunty Zahra to daman ina Aunty maryam ɗin take ” tayi aure ne a gombe kinsan Aunty amarya yar sarkin gombe ne to yayan Aunty amarya shine yake rike da mulki yanzu yana da babban ɗa mai suna Mahmud to Mahmud ɗin ne mijin Aunty maryam shiyasa kukaji karan irin busar da akewa Abba idan zai fita ta ko ina ai mijin Aunty maryam ɗin shine yarima mai jiran gado ” to Aunty Zahra me tazoyi gidan nan yanzu chewar diyana ” itakam hiyana baki bude take kallan diyana tana tunani mutun da gidansu amma diyana ke tambayar me yakawota ” murmushi Zahra tayi san nan tace ai daman kowani sallah suna zuwa ammafa sai anyi sallah da kwana ɗaya suke zuwa ” to ai yanzu Sallah sauran kwana 10 meyasa tazo chewar diyana ” Zahra zatayi magana hiyana tarigata dacewa zaki iya zuwa ki tambayeta ai meyasa tazo ” mikewa Zahra tayi tana faɗin kuzo muje mumata sannu dazu kartace munajin zuwanta mun shareta ” mikewa sukayi gaba ɗayansu suka bi bayan zahra

Kai tsaye bangaren Aunty amarya suka nufa da sallama suka shiga wasu yan mata guda 3 suka samu da alama kuyangun Aunty maryam ne ” yanmatan suna ganin su Zahra suka fara gaidasu ” lfy kawai Zahra ta amsa musu dashi san nan kai tsaye ta wuche tanufi wani ɗaki ” su hiyana suka rufa mata baya ” sallama zahra tayi a bakin kofar kusan 5 mnt tukun nan a ka amsa tare da izinin shigowa ” diyana kam sotake kawai taga wan nan Aunty Maryam ɗin ” shiga chiki sukayi gaba ɗayansu zaune a gefen gado suka samu Aunty Maryam dukawa kasa zahra tayi tace sannu dazuwa Aunty Maryam ya hanya ” ganin Zahra ta duƙa yasa hiyana da lamrat da amrat suma suka ɗuƙa ” diyana kuwa tana tsaye ” ɗago kai Aunty Maryam tayi tana kallansu itama kamanninta ɗaya da Aiman sosai ” bata amsa sannu da Zahra tamataba sai daima tsawar data dagawasu diyana ke kuma wacece, wasu kazamai’ne Zahra kika kawomin ɗaki ” murya na rawa Zahra tafara magana yan uwa na ne yayan kawuna..” a fusache Aunty Maryam tace get out of my room ” da sauri Zahra tamike tarike hannun amrat tana faɗin kuzo muje, mikewa hiyana da lamrat ma sukayi suka nufi kofar fita, har sunkai kofa sai kuka juyo sukaga diyana a saye bata ko motsaba ” diyana kizo mutafi mana ” firgigit diyana tayi alamar dai tunani tashiga maganarsu che tadawo da ita daga duniyar tunani datashiga juyawa tayi tanufesu tana faɗin dan kinsamu munzo kaisheki zakiwani che mufita to wlh badan Zahra bama bazuwa zanyiba ” what ? Ke dan uban ki zo nan chewar Aunty Maryam ” ba musu diyana ta juya takoma wajen Aunty Maryam ɗin ” dago ido Aunty Maryam tayi ta kalli su zahra ai tunkan tayi magana Zahra taja amrat sukayi waje hiyana da lamrat suka rufa musu baya ”

dawo da kallanta kan diyana tayi from head to toe take kallan diyana, wayarta ta ɗauka ta danna kira jim kaɗan a ka daga kiran ” kushigo iya abun datache ke nan ta katse kiran ta ajiye wayar ” jim kaɗan saika wayan nan ƴanmatan dasuke palo zaune dazun sun shigo har ƙasa suka duƙa suna faɗin rankiya’daɗe kamu ” chikin izza danuna isa Aunty Maryam tafara magana kumike ku bugammin yarinyar nan ” diyana najin hakan ta watsa a guje tayi waje sukuma yan matan sukabi bayanta ” Ajiyar zuchiya Aunty Maryam ta sauke san nan tace ai ko ban tambayaba nasan kune Aunty amarya ke bani lbr kuma danku nazo gidan nan ubanku zakuchi wlh sai kungudu da kafarku kafinsu Abba su dawo

Diyana kuwa tana fita kai tsaye wajen security tanufa da gudu kai tsaye bayan shahram tanufa ta ɓuya yan matan na isowa suma tsaya chirkoh chirkoh ” shahram da bajin hausa yakeba sai tambayar diyana yake what happened itakuwa diyana ba wani turanchin kirki takejiba ” ganin yammatan suna kokarin kama diyana yasa shahram ɗaga musu hannu kana yachiro wayarsa yafara neman layin ogansa ” tsayuwa yan matan sukayi shiru sunasan zuwa sukama diyana subuga dan inbasu bugetaba Aunty Maryam zata hukuntasu gashi sukuma suna tsoron sojojin nan ga Shahram fuskarsa babu annuri ” shahram kuwa kiran layin Aryan yashiga yi wayar tanata ringing har sai da takusa tsinkewa tukun nan Aryan yayi picking call ɗin ” a nitse shahram yafara masa bayanin abun dake faruwa chikin harshen turanchi ” give har the phone abun da Aryan yache kawai ” da sauri Shahram yamikawa diyana wayar, hannu tasa ta amshi wayar tamanna a kunne tana faɗin hello ” ajiyar zuchiya Aryan ya sauke yana faɗin ae daman nasan ke’che dan duk gidan nan ba mai neman faɗa sai ke meya haɗaki dasu , suwaye nema ” murya na rawa tace wlh yaya Aryan babu abun dana musu kawai dan munje gaishe da Aunty Maryam ne sai tace wai mu kazamaine mufita mata a ɗaki shine nukuma nace dan tayi sa’a ma…. Bata karisa maganarba Aryan ya dakatar da ita dachewa ya isa haka bawa shahram wayar mika masa wayar diyana tayi bata san me suka tattau naba sai dai taji Shahram yace let’s go madam ” gaba tayi yabi bayanta sukazo suka wuche yammatan ” da sauri yammatan suka juya zasubi bayansu shahram ya dakamusu tsawa bashiri suka tsaya, har bangaren Ammi shahram ya kai diyana san nan yajuya yakoma bakin aikinsa ”
yan matan kuwa jiki na bari suka juya suka koma inda suka fito chike da zullumin hukunchin da Aunty Maryam zata musu dan basu bugi diyana ba da sallama suka Shiga ɗaki waya suka samu Aunty Maryam keyi duƙawa sukayi gaba ɗayansu a kan guiwowinsu suna jiran hukunchi ” bayan tagama wayarne ta ajiye wayar a gefenta afilli take faɗin bazanyi jayayya da kaiba Aryan amma kuma a chikin ruwan sanyi zan dafa yaran nan, dankuwa Aunty amarya bata sonsu suna sata baƙin chiki nikuma duk abun da zaisa Aunty amarya baƙin chiki bana sonshi, kuma dole na kawar mata dashi shiru ta ɗanyi san nan tadubi yanmatan tace kutashi kutafi , ” mamakine yaka masu mikewa sukayi suka bar ɗakin suka koma palo suka zauna

A bangaren diyana kuwa shahram na shigar ta ita ɓangaren Ammi ta kwasa da gudu tayi chikin palo kai tsaye ɗakinsu tanufa ba ko sallama tashige ” Zahra na ganinta tamike tana faɗin bata bugeki bakoh diyana ” dariya diyana tayi san nan tashiga basu lbr abun dayafaru ” ajiyar zuchiya hiyana ta sauke san nan tace kai Allah yayiwa yaya Aryan albarka kekuma sai ki kiyaye bakinki ” shiru diyana taɗanyi kamar mai tunani ” Zahra ta dafata tana faɗin to tunanin me kuma kike diyana ” dariya diyana tai san nan tache ina tunanin yau wache rana yaya Aryan yayi abun arziki ” tsaki hiyana taja san nan tace ni kunga tafiyata lokachin shirya abun ɓuɗa baki yayi tana kaiwa nan tafice ” mikewa su lamrat sukayi gaba ɗayansu s Yanzu wasan zai fara k

Pls more comments an share

 

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button