Sponsored Links
Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 21

Sponsored Links

Page 21

Sai da suka gama cin abincin ma sannan uncle muhsin ya shigo,ya zauna suka gaisheshi,widad ta miqe zata tattara kwanukan uncle muhsin yace

“Dawo widad muyi magana,nujood debe kwanukan ke da musaddiq” da zumudinta ta dawo ta zauna,tana tunanin labarin tafiya gida zaiyi mata

“Widadun ummu” uncle muhsin ya fada yana murmushi

“Na’am uncle” ta amsa masa itama ta amsa masa murmushin,tun da tana son uncle muhsin sosai,kasancewar yana saya daga cikin jama’ar da suke nuna mata qauna da kulawa

“Akwai wani abokina,sunanshi abbas,yacemin yana son yarinya mai hankali da nutsuwa zai aura,nasan widad dina nada hankali da nutsuwa,ina kuma alfahari da ita,wannan yasa nace masa yazo ya ganki kema ki ganshi” gabanta ne yadan fadi,saita dan rage fara’a kadan,uncle muhsin din ya karanci haka,don haka yayi murmushi

“Kada ki damu,indai kika ganshi baiyi miki ba shikenan,babu wanda zai takura miki kinji ko?” Kai ta gyada

“To uncle”

“Yauwa,Allah yayi albarka widad”

“Ameen uncle” ta amsa masa tana miqewa,jikinta yayi wani irin mutuwa,kamar zata daki sai kuma ta fasa tabi bayan nujood data tsaya a kitchen.

Wanke wanke ta samu tana shirin yi,saita tsaya gefenta nujood din ta waiwayo

“Menene?,na dauka zan ganki kina tsalle zaki gida,ko abban cewa yayi an fasa tafiyar?” Kanta ta girgiza

“Wai wani abokinsa ne zaizo gobe ya ganni yanason yayi aure” murmushi nujood tayi

“Ke wanne irin farinjini ne dake,amma abokin abba?,na sassan abokansa,wa yace miki?” Idanunta tadan juya alamar tunani na wasu sakanni sannan da sauri tace

“Wai abbas”

“What?” Nujood ta fada tana ajjiye plate din hannunta

“Wai uncle abbas abba yake nufi?”

“Oho,inajin shi dinne ko?” Ruqunqume widad nujood tayi,tana dan ihun murna

“Wayyo widad,don Allah kada kice baki sonshi, uncle abbas yayi mugun haduwa,saima idan yasa uniform din nan nasa,ga miskilanci ga tsafta ga gayu,idan yazo gidan nan har ya tafi qamshin turarensa yana nan,don Allah kice kin yarda” ture nujood widad tayi tana tura baki

“Dalla malama,ni ba wani nan,na barmiki ke ki cewa uncle kina so” dariya sosai nujood ta qyalqyale da shi tana cewa

“Ni ai babana ne,banda haka ni abba zai bawa,tunda kika ga bai bashi ba kuwa babana ne din” ita dai widad bata sake cewa komai ba,sai ta hau saman kantan kitchen din ta zauna,tana sauraren nujood nata bata labarin uncle abbas din.

Musaddiq ne ya shigo yayi kiran widad bayan kaman awa daya,yace tazo hajjaa nason magana da ita,ta sauko.tabi bayansa.

A bedroom dinta ta sameta tana daga wasu kaya

“Shigo mana widad” hajjaa ta fada ganin widad din ta dan rab’e,qarasa shigowar tayi,hajjan ta dan tsokanarta kan kayan tafiya kano take hada mata,don ta samu ta sake sosai tayi maganar da ta sanya aka kirata din dominta,ganin ta sake din sai tace da ita

“Kinji abinda abbanku ya fada ko?” Kai ta gyada mata ba tare da ta amsa mata ba

“Karki damu,abbas nada matuqar kirki,sannan shi din dan hajiya ne,hajiya dai wadda kuka zauna gidanta wancan satin” maganar data fada na cewa dan hajiyan ne ya sanyata sakin jikinta sosai,cikin dabara hajjaa keta janta da zance har ta saki jikinta,sai a sannan ta sallameta.

Da yamma lis ta kama widad din duk rashin son kitso irin nata ta sake wanke mata kai,tana ta qi tana turjewa,sai data sanya su musaddiq suka dinga yi mata dariya ,tare da waqar me kukan kitso sannan ta nutsu,ta raba kanta tayi mata manyan kalaba da suka jelarsu masu tsaho zubo gefe da gefan fuskarta,saura kuma suka sauka a bayanta,kasancewar ba kasafai ta fiya kitso ba saboda qin da take masa,sai kalbar ta haska fuskarta tayi mata kyau sosai,hajjaa ta qawata qarshen kowacce jela da duwatsun kitso masu yawa da suka qarawa kalbar kyau suka taimaka kuma ta kwanta mata sosai a fuskar da bayanta.

Itakam widad gaba daya murnar tafiya gida ya sanya ma bata damu ko ya dauki batun zuwan abbas da muhimmanci ba,siyayyar da uncle muhsin yayi mata taketa shiryawa abinta,tana ta zancensu Aafiya da sauran ‘yan uwanta,da wannan batun ta kwanta bacci.

************Washegari a gida yayi breakfast wajen hajiya,ya kuma shaida mata yau din suraj zai rakashi gidan muhsin din.

Har cikin zuciya da ruhinta take jin farinciki,tayi addu’a sosai tare da fatan samun dacewa da albarka mai yawa cikin lamarin.

Sai Azhar ya wuce gida bayan yayi salla a nan,yana komawa bacci ya kwanta,bai farka ba sai gab da la’asar,tun bai tashi daga kan gadonsa ba ya janyo waya yana sake lalubar number hafsa,saidai yau din ma har tayi ringing ta gama bata dauka ba,a qa’ida idan yayima mutun kira daya baya qarawa,amma wannan karon ita din sai daya kira sau uku bata dauka ba,sai ya maida wayar ya ajjiye ransa yana baci,ya miqe ya shiga toilet ya daura alwala ya wuce masallaci.

Yana dawowa dakin kira na shigowa wayar tasa,suraj ne yana dagawa ya soma zolayarsa

“Sabon ango,Allah dai yasa ka shirya” ido ya lumshe yadan saki murmushi,surja badai zolaya ba

“Haba duk zumudin na meye?,bayan la’asar fa mukayi dakai,kuma yanzun nan ma aka gama sallar” dariya suraj din yayi

“Na qagu ne naga wacce mai sa’ar ce zata sake samunka,bama ni kadai ba,kaga zainab a nan ita kanta so take naje na dawo na gaya mata wacece”

“Ita da hafsat kuwa”

“To sai me?,kayi qoqari ka shirya,gani nan fitowa,abinci kawai zanci”

“Saika qaraso” ya fada yana katse wayar,dole ya fidda hular da ya sanya ya aje,ya shiga bandaki ya don yin wanka.

Yana tsaye yana tsane ruwan da yayi lumm cikin gargasar jikinsa yana duban madubi,karo na barkatai ya sake kallon wayarsa yana tuna adadin wayar da ya yiwa hafsat din bata dauka ba,sai ya jinjina kai yana qiyasta yadda zai fita daga bauchi jibi da sassafe zuwa kaduna.

Ya gama shirinsa tsaf yana gaban mudubi yana kallon kansa,hannunsa riqe da hularsa yana karyata,yana jin wani banbarakwai,wai yau shine a karo na biyu zashi zance,zancen ma wajen wadda baisan wacece ba,ya dora hularsa sannan ya dauki sassanyan turarensa dake fallasashi a duk inda ya shiga ya feshe jikinsa dashi.

Kiran suraj da ya shigo ya shaida masa isowarshi,saiya kara wayar a kunne ya tallafeta da kafadarsa saboda takalman da yake sanyawa a qafarsa bayan ya zauna kan dressing chair yana fadin

“Ka qaraso ciki mana”

“A’ah,ina cikin mota fito kawai” bai musa masa ba,ya zame wayar ya qarasa sanya wasu rufaffun takalma masu kyau da asalin tsada da wasu sake fidda shigarsa,ya dauki wayar ya mayar aljihu ya dauki keys din gidan suma ya saka sannan ya fito.

“Kai mutumina,kamar yau ne zan rakaka wajen maman mimi?” Harara ya watsa masa bayan ya rufo murfin motar sannan yace

“Kunna mota mu wuce,so nake muyi mu dawo,ina da wani uzuri”

“Yanzu kuwa yallabai” ya fadi yana dariya,sai ya tada motar suka wuce.

Suraj nata jansa da hira amma shi hankalinsa ya rabu kashi kashi,dubansa yayi sanda yaga yana qoqarin parking qofar wani qaramin mall

“Bari mudan samo abinda za’a kai mata,ai bama shiga hannu rabbana ba”

“Share kawai suraj mu tafi please”

“A’ah,nikam ba za’ayi haka dani ba,ko banza fa ta zama matarka,tunda an riga an tambaya an kuma baka” maganar sai yaji tayi masa nauyi,bace komai ba har suraj din ya fice,bai kuma dade ba ya dawo da tarin alawoyi da chocolates masu tsada da dadi,ya ajjiye ledar ya kunna motar sukaci gaba da tafiya.

~~~~~

“Kai,tubarkalla ma sha Allah,diyata din nan badai kyau ba” hajjaa ta fada bayan ta gama shirya widad,cikin wata sabuwar dark blue din super vilisco,dinkin doguwar riga,ta fidda jelar kalbarta tayi ta fito ta qasan daurin dankwalin data yi mata,ya zauna das a kanta,sannan ta bata siririn mayafi da ya dace da atamfar.

Murmushi widad kawai keyi tana kallon kanta a cikin mudubin,badan badan ba da sai tace bata taba ganin tayi kyau haka ba,ummu ta tabo daa,bata iya zama tayi mata wadan nan qyale qyalen,saidai ko yaushe zaka samu widad din fes cikin tsananin tsafta da kuma sutturu masu tsada,saidai ita da kanta take zama tayi kwalliyarta wansa a wajensu Aafiya da yayyansu su ramziyya take kwaikwaya,ko latifa da take mutuniyarta ita dinma bawai ta yanzu bace,ba wani iyawa tayi sosai ba,amma da yake hajjaan gwanar ado ce,a yau din ta qawata widad din sosai,har abun yayi mata dadi ya kuma burgeta ita kanta,farincikin yadda taga tayi kyau yasa bata jin wani fargaba ko bacin ran zuwan baqon,Allah Allah ma take yazo ya tafi tazo hajjaa tayi mata hotuna masu kyau ta turawa daya daga cikin ‘yan gidansu su nunawa ummunta kafin ta isa gida.

Musaddiq ne ya shigo dauke da ball a hannunsa yana gayawa hajjaa ga uncle abbas nan

“Bude musu setting room,ka kunna ac kadan kada tayi yawa,sai kazo kakai musu ruwa” da to ya amsa ya juya yana ficewa.

Sai da hajjaa ta tabbatar an kai komai sannan taja hannun widad ta zaunar da ita

“Na sanki da hankali da nutsuwa,to ki qaro wata a kai,idan kin shiga ki gaishesu kinji?”

“Tom” ta fada tana gyada kai,sai hajjaa ta kira nujood,ta sanyata ta saka hijab tace ta raka widad,har sun fita ta kirayeta

“Karki ce zaki zauna,nasan halinku da shirme,kina rakata kuna gaisawa ki dawo ciki”

“To” tace tana ficewa,suka rankaya kuwa ita da widad din zuwa setting room.

Setting room din yabi da kallo,duk da ba baqonsa bane,don yawanci idan yazo a nan suke zama da muhsin din,kamar bazai zauna ba,haka kawai ya samu kansa da qaguwa na ganin wacece,wayarsa da aka kira ya duba kuma yaga ogansa ne ya sanyashi zama dole,don suna da wani irin respect na ga gaba dasu,ya fara amsa wayar cikin nutsuwa da kuma girmamawa.

Suna cikin yin sallama da ogan nasa yaji suraj ya dan taboshi,sai ya maida dubansa ga suraj din don,signal yayi masa da ido yana masa nuni da hanyar shigowa setting room din,ya qarqare wayar yana ajjiyeta gefansa,sannan ya maida dubansa ga inda suraj din ke masa nuni.

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
[2/18, 12:43 PM] It’s Queen MeenaliπŸ‘ΈπŸ»: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button