Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 11

Sponsored Links

Episode 11*

 

Mai martabane zaune a fada shida Aryan, Ahmad Khalid da’kuma Yusuf a nitse mai martaba yafara magana ” Aryan meyasa zaka mari diyana kanajin faɗan danayiwa safras fa ranan akan marin dayayiwa hiyana shine kaikuma kasake marin diyana koh wai bakuda tausayine nikam eh ” calmly Aryan yasoma magana kayi hakuri Abba wlh tabatamin raine sosai shiyasa ” nasani Aryan nasan halin diyana itakuma haka allah yayita hakuri zakurinkayi da ita ban hanaku kumusu faɗaba amma kurinka ragewa kuma bai’kamata kuɗora hannunku a jikinsuba bakuganin yanayin’sune, yanzu kaje kadubi fuskar diyana da kyau kagani shattin yatsunkane kwanche akai to na’menene hakan gaskiya bansan hakan karna karaji kuma karna kara gani ” inshaa allah Abba zan kiyaye chewar Aryan ” Khalid yace Abba yabatun zakkan nanfa ” eh kuna barwa ai kukula da komai ” Ahmad yamike yana faɗin aa Abba su yaya Khalid dai nikamma bari naje na dubo Aiman ” harara Yusuf ya watsawa Ahmad yana faɗin zakasani ne ai dakai da Aiman ɗin gaba daya wlh munkusayin maganinku a gidan nan ” Ahmad dai bai sake maganaba yafiche abunsa

Aryan yace Abba yabatun komawarmu England ne ” aikuda komawa kam to banacheba kabari ayi naɗin sarauta tukun nan sai inyi tunani akai chewar Abba ” mikewa Aryan yayi yana faɗin to shike nan Abba allah ya kaimu san nan yafiche daga fadan ” Khalid da Yusuf ma mikewa sukayi suka fito sunayiwa Abba sai anjima

Gabaɗaya family sun haɗu a palo dan chin abinchin dare amma banda don, dakuma yan matan Ammi subasu zoba , ” mai marbata yace waishin ina yan’matana’ne mesukeyi basu fitoba, ko dai daga buɗa baki shike nan bazasuchi abinchin dareba” Ammi zatayi magana sai sukajiyo sallamar’su nanfa kallo yadawo kansu banda Aryan da fahad kowa na palon kallansu yake, ”

diyana na sanye chikin dogon wando baki da rigansa zuwa guiwa pink colour still dai ba ɗan kwali a kanta ta zuba gashin nan har baya sai kwalli gashin yake nakinkirin dashi har tsakiyar bayanta, dan karamin bakin nan nata yasha janbaki pink ga blue eyes yasha kwalli ta gyara sagenta ga zarazaran gashim idanta, tasa high heel pink kalar rigarta

” hiyana ma dogon wando baki tasa sai riga sky blue zuwa guiwa ta ɗaure gashin Kanta, tayishi kamar donut ta yafa gyalen kayan akanta paki kalan wando dan bakin nan nata yasha ret janbaki tayi kyau sosai kamar kasacheta ga blue eyes yasha kwalli sai’yaƙara kyau sosai yana kyalli sajenta kwanche a gefen kumatun’ta gashin geranta kamar tayi caving tasa flat shoe sky blue kalar rigar

Zahra ma dogon wando baki tasa sai riga yellow tayafa gyalen kayan akanta shima bakine ɗan karamin bakin tan nan tasanya masa janbaki pink colour tayi kyau sosai itama daman zahra kama take da don sosai wan nan dalilinsaya suka zama kamar tagwaye da hiyana sai dai banbanchin kwayar ido dan zahra idanta bakine kamar nawa

Lamrat kuwa dogon riga baki tasa mai shegen kyau,
Tasa flat shoe fari, tayi rolling ɗin karamin farin gyale a kanta Zahra tamata make up sosai kamar wata balarabiya tazama

Amrat kuwa dogon wanto fari dasa sai yar farar t-shirt navy blue itama batasa ɗan kwaliba amma zahra tamata pakin na gashin a tsakiyar kanta tazuba jelar gashin a’ baya har tsakiyar bayanta booth navy blue tasa a kafarta

Yusuf ne yache wow my baby zo ” gaba ɗaya kallo yadawo kan Yusuf, a’ sukane Aryan yaɗago yana kallan Yusuf ɗin shi ko ajikinsa kallan su diyana ma yake baisanma jama’a na kallansaba ” bin inda Yusuf ɗin ke kallo Aryan yayi ” “Aryan kasa kawar da kannasa yayi daga kallanta ?

Karisawa wajen table ɗin sukayi sukayi kowa tasamu waje ta zauna lamrat zata zauna kusa da Ammi ” yusuf yache zo nan kizauna kusa dani my baby ” bamusu lamrat takoma kusa dashi ta zauna ” haidar da umar sai gulma suke kasa kasa ” Ammi da Ummi kam ko ajikinsu abinchinsu kawai sukechi ” Aunty amarya kuwa sai chika take tanata harararsu ” ɗaukoh fura ki damamin hiyana chewar mai marbata ” da sauri hiyana tamike tanufi kichin, kwarya ta ɗaukoh san nan ta daukoh fura, tanufi freig ta ɗauki ruba ɗaya na nono tajuya takoma palan mai martaba, da sallama tashigo palan ta dawo wajen zamanta ta zauna tafara dama furar

Sai’hira suke jefi jefi mai marbata yache banso a che muntafi umrah nan mun barkuba amma makaranta basu baku hutuba ” Ammi ne tache sai suje hajji kawai kokuma subari sai wata shekarar ” mai martaba zaiyi magana ” Ummi tace Fahad tashi ka kaiwa yayanku abinchi ” da sauri Fahad yamike yana faɗin ina abinchin ” yana kichin Ummi tabashi amsa , ” fichewa yayi daga palan

Bayan hiyana tagama dama furan tamikawa mai marbata ” karɓa yayi yana murmushi kana yace duk gidan nan hiyanata tafi kowa iya dama fura ” turo baki diyana tayi tana faɗin wlh nafita abun dama nina ko…. bata karisa maganaba sakamakon wani mugun kallan da Aryan yake wurga mata ” shiru tayi

Mai martabane kuwa sai kallansu yake yana murmushi yana farinchikin burinsa yafara chika aishi haka yakeso kodama hararanne Aryan kewa diyana daɗi zaiji dan daga harara sai kallan mutunchi ” Ammi che ta katse masa tunani dache ranka ya daɗe sai da safe ” hararar wasa mai marbata ya wuga mata kana yace inada magana dake ” to kawai Ammi tache ” jin mai marbata yace. yana da magana da Ammi yasa kowa yatashi suka fiche

Mai martaba yadubi Ammi yafara magana jiya Yusuf yasame damaganar akan Khalid da zahra, Khalid yafaɗawa Yusuf yanasan Zahra tun tana karama ina faɗamiki hakanne bawai dan kifaɗa mataba sai hakkinki a matsayin uwa da’kuma kisamata ido karkibari tawa Khalid kishiya, danni tun da Yusuf yafaɗamin nariga nabawa Khalid auren ta, kokina da wani abun faɗe ” ajiyar zuchiya Ammi tayi san nan tace, nikaina inakaunar Khalid nina renesa a hannuna yagirma babu halinsa da bansaniba bawani abun da zanche saidai inmusu fatan alkhairi kawai ” to masha allah Amma fa kinsan yau a ɗakin’ki nake amma kikechemin sai da safe koh ” murmushi Ammi tayi tana tace tubanake wlh nagajine a’zumin yau ɗin nan ya wahalar dani ” haryanzu dai lallanchinki bai raguba Aisha, to muje chiki namiki tausar koh ” mikewa Ammi tayi tana faɗin mujedai ninamaka ” dariya mai martaba yayi san nan yamike yabi bayanta sukayi chikin betroom

Karfe 10 na dare

Rike take da cup ɗin coffee tanufi bangaren Aryan jikinta sanye da kayan barchi riga da dogon wando pink colour still dai kanta babu ɗan kwali tafiya take tana kunkuni” ni wlh barchi nakeji nagaji saikayitaba mutun wahala dan mugunta ” da sallam tashigo palan baya palo kai tsaye ta wuche betroom ɗin ” kwanche yake akan makekiyar gadansa yana latsawaya jin shigowarta yasa ya ɗago kai yana kallanta ” sai turo baki take tana magana kasa kasa ” from head to toe ya karemata kallo san nan ya ɗauke kansa da sauri ” karisa shigowa chikin ɗakin tayi tazo gaban gadan ta duka san nan tace. Ina wuni yaya Aryan ” shiru yayi bai amsaba kuma bai motsaba ” itama shiru ta zauna har kusan 15 mnt, san nan tache yaya Aryan dan allah ka karɓi coffee ɗin mana wlh nagaji ” banzah Aryan yayi da ita kamar baiji metake faɗe ba shiru shiru baiyi maganaba ganin bai daniyar magana yasata tamike, tanufi indayake wai dan taga yayi barchine
Aji cup ɗin coffee ɗin tayi akan dan karamin table ɗin dake tsakiyar ɗakin san nan tanufi kan gado hawa gadan tayi taga idansa a lunshe , ta turo baki tana faɗin shine dan mugunta kabarni ina duke kan guiwowina har kafata namin zafi kaikuma kayi barchinka koh, to banyafe… Bata karisa maganarba taga ya waro manya manya ash eyes ɗin nan nashi akan fuskarta ” a’sukwane ta juya tana kokarin sauka gadan wani damka yayiwa gashin kanta wandayasa tadawo baya tafaɗa kan kirjinsa ” kware baki tayi zatayi ihu yasa hannu yarufe mata baki ” kasa kasa yace kina buɗemin baki ina harbinki da bindiga meya hauwar dake gadona yayi maganar tare da chire hannunsa daga bakinta ” murya na rawa tace dan allah yaya aryan kayi hakuri kasakemin gashina wlh zafi yakemin ” banche karna sake ganinki ba ɗankwali ba eh ” kayi hakuri zanrinka sawa chewar diyana tayi maganar chikin muryar kuka ” harchikin ransa yaji voice nata na karshe kayi hakuri zanrinka sawa a hankali yazame hannunsa daga kannata, yana faɗin to tashinmin ajiki ” da sauri tamike tana faɗin to ga coffee ɗin ” mikewa yayi shima kana yace bazanshaba ki mayar kije kisa ɗankwali saiki kawomin ” a shagwabe tace ayya dan allah kayi hakuri kasha allah gobe zan daura dan kwalin kafin nakawoma wlh yanzu nagaji kuma barchi nakeji ” kallanta yayi from head to toe san nan yache nikam, kekam kinada hankali kuwa kinsan chiwon kanki kuwa ” turo baki diyana tayi tana faɗin mekuma nasakeyi ” wlh azim idan kikasake fitowa a haka batare da hijabi ko kayan arziki ajikinkiba allah zakiyabawa aya zakinta ” binjikinta tayi da kallo achikin zuchiyarta tana tunanin to me laifin kayan nan tayi nisa chikin tunani taji ya daka mata tsawa ” wai badake nake magana bane nache kifitamin a ɗaki koh, da sauri tajuya tabar ɗakin binta yayi da kallo har tafita
san nan yamike yanufi inda ta ajiye coffee ɗin ya ɗauko cup ɗin yadawo gefen gadansa ya zauna yafara sha,

Bangaren diyana kuwa tana fita bangaren Aryan kai tsaye part nasu tanufa da sallama tashigo palan, da sauri taja burki tana faɗin ya yaya Yusuf kaima bakayi barchiba ” murmushi yusuf yayi yana faɗin eh ina hira da baby’s nawane suna koyamin fillanchi ” karisawa indasuke diyana tayi tana faɗin kema amrat hardake yau bakiyi barchiba sai kije school kiyita barchi a class koh ” lamrat tace ainikam ma yanzu zanje na kwanta ” zama diyana tayi kusa da Yusuf zatayi magana ” Yusuf yace kuje ku kwanta dare yayi kunsan akoi tashin asuba ga zuwa school yayi maganar yana mikewa yanufi hanyar fita ” suma mikewa sukayi suka wuche ɗaki

Karfe 4 dai dai na asuba gaba ɗayansu sun haɗu a palon mai martaba danyin sahur amma banda don abinchi sukechi chikin kwanchiyar hankali ” Ammi tache hiyana da Zahra kuchi abinchin nan dawuri ku’ɗauki na yayanku ku kaimasa zahra najin Ammi tache sukaiwa don abinchi tafasa kara sai da kowa na palan yaɗago yana kallanta ” lfy auta ta chewar Abba ” Zahra dai taki magana sai kukanta kawai take ” hiyana kam datariga da tasan me Zahra takewa kuka ko kallanta batayiba, su Ammi sunyi tambayar duniyar nan amma Zahra taki magana sai kuka take ” Aryan ne ya daka mata tsawa zakimana shirune kosaina babballaki a nan ” tsit tayi kamar ruwa yachita ”
Aunty amarya ne tamike tana faɗin kai umar kaje ka dauki abinchin yayan naku ka kaimasa kuma daga yau kai zaka rinƙa kai masa abinchi tana kaiwa nan tafiche tana tunanin aranta ai bazan taɓa barin yaran nan surinƙa kusantar samarin gidan nanba daga yau har ranar da gagarabadau zai musu aiki ido zan samusu sosai da sosai ɗakinta tawuche ta haye gado babu ko sallah takama barchi

Bangaren”su hiyana kuwa sunajin Aunty amarya tace umar yakai abinchin yayansu nantake suka fara murna sukamike a tare suna faɗin barimuje muyi sallah ” Ammi ta kalli hiyana chikin harchen fillanchi tace wani sallah kuma badai kina period ɗin kike sallah ba ” shiru hiyana tayi dan ita batama san idan a na period baa sallah ba ” ganin tayi shiru yasa Ammi ta dubi zahra tace kije ki koyamata abun daya dace tayi ” to kawai zahra ta amsa dashi san nan suka fiche

Mikewa Yusuf yayi yana faɗin gaskiya lokachi yayi dazan koyi fullanchi nima haba yanagama faɗin haka yayi waje ” Khalid ma yace tab aiko nima dole naje Zahra ta koyamin irin wan nan wariya daake nunamana kana yamike shima yayi waje ” dogon tsaki aiman yaja san nan yamike yafiche ” shidai Aryan zaune yake ahiru yana latsawaya har saida yafarajin kiraye kirayen sallah yamike yanufi bangarensa ” Ammi da Ummi ma suka fiche sukayi nasu bangaren danyin sallah ” palan yarage fahad haidar da Abba ” Abba yace wai kunyi arwala’ne kunfasan su safras sunafitowa zamuwuche masallahchi ” mikewa haidar yayi yana faɗin aa baridai naje nayi ” fahad ko chewa yayi nikam nayi Abba” ok kawai mai martaba ya amsa dashi
Shiru suka zauna har sauran matasan suka fito sukajera zuwa masallachi

Aɓan garen inna kuwa da sallama tashiga gidan su buba zaune tasameshi a tsakar gida ” buba na ganin inna yafara murmushi yana faɗin inna jamɓandu( inna ina wuni) ” lfy buba ya kafar taka ” da sauki inna” inna tache to allah yakara lfy ina innarka take ” tana garke tanabawa shanu ruwa da abinchi buba yabata amsa ” to barina dubota bata jira amsar buba tayi gaba abunta ” a garken shanun ta iskoh innar buba da sauri inna ta karisa wajenta tana faɗin albishir rinki yar uwa rabinjiki ” ɗago kai innar buba tayi tafara murmushi tana faɗin goro ” to kifito muje yau kuɗin sunchika dubu goma dai dai chewar inna ” da sauri innar buba ta ajiye sandar hannunta datake juyawa shanu ruwan gishiri tafito daga garken tana murmushi jerawa sukayi suka koma chikin gida innar buba ta ɗaukoh mayafi suka fiche

Wani ƙungurmin daji suka shiga tafiya suke har suka isawajen wani dutse ga hayaki nafitowa daga chikin kogon dutsen chikin kogon sukashiga ” wani kasurgumin bakin bokane awajen ga idon san nan jajawur duk yabi ya huhhuda hanchi yasa wasu karafuna gawani katan karfe mai raun dayasa a kunnensa bashida kyan gani ko kaɗan
Zama su inna sukayi kusa dashi ” zasu fara magana ke nan yayi wani mahaukachin dariya ha, ha, ha, da murya masa daɗin Ji yace aikin ku bazaiyuwu a chikin azumiba saboda duk an ɗaure mana mutanenmu amma kuje sai bayan sallah kudawo ha ha ha yana gama faɗan haka ya ɓache ɓat ” da sauri su inna suka mike suka fito inna tace to yanzu barinaje na ajiye kuɗin sai bayan sallah mudawo da haka suka kuche gida.

Kamar kullum yauma zaune suke a wajen chin abinchinsu na makaranta karatu boko hiyana take yaukam tun da bata da tsarki ” zahra da diyana da faria kuwa hirar wani film suke waishi love story English movie
Lamrat da amrat suna rubutu a takardunsu ”
Kamar daga sama sukajiyo muryan jabir yana faɗin ke hiyana zo mutafi ” ɗogo kai hiyana tayi a nitse tafara magana kayi hakuri jabir wlh yau banida lfy ne chikina namin chiwo ” to yakikesan nayi ke nan ga abokaina chan kowa budurwarsa tazo ni bandani ke nan ba zaiyiwuba i don’t care koma meke damunki, nidai kitashi mutafi ” kamar hiyana zatayi kuka haka tamike tanufeshi tana faɗin muje ” kallan uku 10 diyana tawa jabir kasa kasa tache mugu wlh sainayi maganinka ” kallanta zahra tayi san nan taja guntun tsaki ” jabir tunda yakira hiyana suka tafi basu dawoba har saida a katashi nanma saida diyana da zahra sukaje wajen dayake zama da abokan nasa sukache hiyana tazo sutafi mai ɗaukansu yazo ” jabir dayaji haka sai yache to taje zasu haɗu gobe ” jerawa sukayi suka nufi wajen da suke tsayuwa sujira motochin dake ɗaukansu ”

suna tsaye awajen sukaji magana daga bayansu ” gaba ɗayansu suka juya ” hiyana tace uncle Omar ina wuni ” da faraa a fuskanshi ya amsa san nan su Zahra suka gaidashi zaisake magana saiyaga motochin ɗaukansu yazo nanfa yamusu sallama yawuche ” sukuma suka shiga mota kamar yadda sukasaba hiyana Zahra diyana motarau ɗaya ” amrat da lamrat suma motarau ɗaya ” da gudun gaske motochin sukabar bakarantar” gudu suke sosai suna kan hanyane” zahra tace kinsanme hiyana ” girgiza’kai hiyana tai alamar aa ” uncle Omar fa wai san diyana yake chewar zahra ” kan uban chan niyakeso lallai kuwa yana ruwa wlh dannikam inba sojaba bazanyi aureba ” baki buɗe hiyana ke kallan diyana ” Zahra kuwa chewa tayi meyasa kikesan soja sojojifa mugayene ” eh ae a chikin sojanma mugun nakeso wanda zaiyimin maganin yaya Aryan kuma wanda yake da bindiga shima ” zahra tace to me yaya Aryan ɗin yayimaki haka dakike neman mugun soja yayi maki maganinsa ” to bashine kullun inna masa laifi saiyache zai ɗaukoh bindiga ya harbeni namutu kowa yahutaba ” aikuwa hiyana bata san sanda takwashe da dariyaba tana faɗin kai amma kuwa da yaya Aryan ya kyauta wlh ” Zahra kuwa chewa tayi dalla rabu da hiyana kinji faɗamin muguntar me yake miki ” bayan harbeni dayake chewa zaiyi saikuma jamin gashi da takuramin nasa ɗakwali dakuma kawo coffee kullun tayi maganar dai dai lokachin da motochinsu ke parking a parking space na chikin gida
Fitowa sukayi suka nufi chikin gida rike da hannun juna

Misalin karfe 4 na yamma gaba ɗaya yanmatan zaune suke a palon Ammi suna kallo hiyana kuma tana karawa lamrat karatun qur’ani gaba ɗayansu shiga iri ɗaya sukayi duguwar riga abaya dukkansu colour ɗaya baki ” Ammi ma nazaune a gefe tana gyarawa amrat jigidarta da Aunty farida ta saya musu to ya matseta sosai ” da sallama Khalid da yusuf suka shigo palan ” da gudu Zahra ta mike ta nufi Khalid,faɗawa kan kirjinsa tayi ta rungumesa sosai tana faɗin oyoyo yaya Khalid ” Yusuf ne yace my baby kema kizo kimin oyoyo mana ” da gudu lamrat ta mike tanufeshi hannu ya buɗe masa tafaɗa kirjinsa yana murmushi ” Ammi data tuno abun da mai martaba yafaɗa mata nachewar Khalid na san Zahra yasa da sauri tace ke zahra’u wai yaushe zaki girmane wlh idankika sake wan nan oyoyo zaki chi gidanku ” turo baki zahra tayi ” Khalid yasa hannu ya ɗan bugi bakin kana yace to wa’ake turowa bakin hannunta yarikoh suka koma kan kujera mai zaman mutun biyu

Yusuf ma rikoh hannun lamrat yayi suka koma kan doguwar sofan suka zauna ” hannu Yusuf yasa yana shafa kan lamrat yana faɗin my baby gashinkin nan kyau yakemin sosaifa ” baki buɗe Khalid ke kallan Yusuf, azuchiyarsa kuwa chewa yake amma Yusuf iskanchinka yawuche tunani anya kaima baka kamu da san yarinyar nanba kuwa ” afili kuwa chewa yayi ai gashin Zahra yafi nakowa kyau ” harara Yusuf ya wurga masa san nan yace yauwa Ammi nikam inasan intambayeki kullum mantawa nake ” Ammi tace. Tanbayi inajinka ” wai aina mukasamu kalolin idon mun nan ne pls ” Ammi tace au kache tarihi kakeson ji to gyra zama ” murmushi kawai yusuf yayi yazubawa Ammi ido

Kakanku wato mahaifiyar mai martaba itache asalin wanda takawowa family mu kalan idan nan kakanku namiji babban likitane aiki yakaishi Us, a chan yaje ya auro kakarku ta mace baturiyar Us, amma musulmache sunanta sarah to sarah itache mai ido light green irin naka kaida yayanku ” sarah kuwa mahaifiyar ta idonta ash ne mahaifintane mai light green ɗin ido shiyasa gaba ɗaya yayan sarah suka zama masu ido 2 colour wasu ash wasu green gashi abunkuma yabisu har kanku jikokinta, ” Khalid yace no wonder, shiyasa muke da kyau kamar yayan larabawa ashe ashe ” dariya Ammi tayi tana faɗin abun harda yabon kai ” Khalid zaiyi magana yusuf yache to ammi su hiyana fa ya akayi suka samu blue eyes

Ammi tace sukuma sungadone daga wajen kakanmu namiji kuma duk family mu ma sukaɗai sukayi saar samun blue eyes ɗin kakanmu namiji shi ɗan asalin kasar sudanne yazo nageria, a garin jimeta yola, yahadu da kakamu mace yana santa sosai iyayenta sukache bazasu bashi itaba, sai dai idan zai zauna a rugarasu haka yayarda ya auri kakanmu kuma suka zauna a ruga harsuka haifi babana, da kanwarsa ɗaya allah yayiwa kakanmu rasuwa, kakanmu mace kuwa babana yayi auri umma’ta Kuma duk a’ruga ɗaya suke kuma a chan suka zauna an haifenima bajimawa kakanmu tarasu itama, kanwar babana kuwa bayan an haifi kanina Ahmadu babansu hiyana ke nan itama tarasu daga nan babanmu ya ƙaura daga rugar chikin yola yakoma rugar jimeta, a nan mukachigaba da rayuwa
Rayuwar farinchiki muke sosai kanina da babana suje kiwo nikuma naje tallar nono a wajen tallar nono na haɗu da Mai martaba yabini har gida, da kyar babana yabasa aurena to na bayan aure ba jimawa innata tarasu, yarage saura baba da Ahmadu haka mukachi gaba da rayuwa bayardda mai martaba baiyi dasuba akan sudawo nan kano sunki har gida yasaya musu Amma sunki wai babu inda zasuje da waɗan nan uban shanaye babanmu yana da shanu dayawa kusan 700 ga awaki da raguna kaji da zabbi hakadai sukachigaba da zama a ruga
Kolokachin dana haifi yayanku sunki zuwa mota mai martaba yatura a ɗauko su amma sunki zuwa, babana ko yaki zuwane saboda niche yar fari Ahmadu kuma yaki zuwane saboda shine mai zuwa kiwon dabbobinmu kai intakaichemuku har babanmu yarasu Ahmadu yayi aure basu taba zuwa wajena ba saidai ninaje
Nidinma kunsan yanayin gidan nan sainafi shekara uku banjeba nanma saina matsa da kyar mai marbata yake barina, akoi lokachin dana ɗauki tsawon shekara 6 banje naduba Ahmadu ba a shakara ta 7 ɗinne nayita rokar mai martaba da kyar ya’yarda yabarni naje”
Danajene masamu fati matar Ahmadu ta haifi ƴaƴa har uku hiyana diyana dakuma lamrat san nan ga chikin na hudu ajikinta nasha mamaki sosai shine nachewa Ahmadu tunda yanzu bamuda iyaye yadawo kano kusa dani yaki yarda, wai inyadawo yazaiyi da dabbobinsa, nachemasa musayar yaki yarda wai bazai bar garin iyaye da kakanniba haka na hakura na kyalesa nasaya’ waya nabashi amma yaki karɓa wai baiso bayadda na iya haka nadawo na kyalesa
Sai danasake ɗaukan shekara 4 kafin nasake komawa kauye alokachin danaje nasamu mamansu hiyana tarasu wajen aihuwar amrat Ahmadu kuma ya auri habiba dan tachigaba da kulamasa da yara alokachinma saidana roki Ahmadu daya dawo kano amma yaki narokesa yabani hiyana da diyana nanma yaki ninasan halinsa da kafiya shine na kyalesa kuma tundaga wan nan lokachin dana dawo bansake zuwa kauyeba sai zuwan nan danayi na samu Ahmadu yarasu na daukoh su hiyana ” dogon numfashi yusuf yaja san nan yace. Tab lallai Ammi kina da hakuri sosai wlh allah dai yajikansu da rahma ” gaba ɗaya palon suka amsa da amin ” duba time yusuf yayi san nan yace. da Khalid muje koh mangariba ta kawo kai ” mikewa sukayi a tare yusuf narike da hannun lamrat sukayi wajen ” Ammi tace’wa su hiyana kutashi kuje kufara shirye shiryen kayan buɗa baki tare suma sukamike suka nufi palon kasa” Ammi ma tamike tayi ɗakinta

Misalin karfe 7 na dare gaba ɗaya family suna palo dan yin buɗa baki amma banda don abinchi sukechi chikin kwanchiyar hankali shiru ba mai magana saidai karan spoon ” diyana tace. Abba kasan me ” sai dakowa yaɗago yana kallanta da mamaki ” mai martaba kuwa chewa yayi aa diyana ta bansaniba sai kinfaɗa ” dariya diyana tayi tace wai uncle Omar na makarantar mune yace yana sona ” what chewar mai marbata ” a’sukwane Aryan yaɗago manya manyan idan nan nanshi yana kallanta a jafafe yabuɗe baki…..✍️✍️

 

Amin afuwa masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu more love

 

Pls more comments an share

*💫STAR LADY💫*

 

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*

 

 

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button