Sponsored Links
Hausa NovelsKyalKyalin Kauna Hausa Novel

KyalKyalin Kauna 90

Sponsored Links

[8/16, 2:59 PM] SAFIYYA: Kowa na kotun kallon Adamu yake daya shigo yana bama Ahmad wani flash drive.
Hamad da Malah kasa rufe baki sukayi, irin wait what is happening din nan?
Adamu kuma how? Sannin Maheer yasa Hamad yataba Malah yace
“kanina shegge ne”
murmushi Malah yayi yace “nagama tunani ta yanda yay making Adamu to come as a witness haka nakasa ganin way din”
murmushi Hamad yayi yanadan jin kwanciyan hankali yace “bari komi ya sarara zamu sani” kallo daya Maheer yama Adamu ya dauke kai, Adamu yawuce gaban kanta yaje ya tsaya yayi rantsuwa zai fadi gaskiya Ahmad yatashi yace “zaka iya gayama kotu waye kai” Anatse Adamu yace “sunana Adamu and inama Hajiya Maryam aiki tun ina shekaru 22 aduniya,
yau inada 45yrs aduniya, ni direban ta ne ina tukata nakaita ko’ina” nuna Maheer Ahmad yayi yace “waye shi awajen Hajiya”? Kallon Maheer Adamu yayi yace “ranan data dauko Maheer daga
kasan gada nina tukata,
nitake aikawa na dauko Hamad idan tabari yaga Maheer, agabana Maheer yataso hannunta tagayamana irin danta ne kaman adopting nashi tayi hakan nan,
dudda ba bangarenta muke kwana ba bani kadaiba kusan dukanmu ma’aikatan ta mukanji kukan Maheer tsakar dare yana kibari, banso, yakuri, kaza kaza dai idan tanama yaron abinda tasaba yi kusan duk daren duniya wani zubin harda safe ma”
kotu tai tsit anajin wannan al’amari babba na zina da yaro dan shekara takwas aduniya, anatse Adamu yace
“amman bamuda ikon cemata tadaina kota bari bamuda kudin fada da ita kuma bata bari kowa na zuwa wajen yaron,
10:35
idan zakaga Maheer sau dari to yana gefenta zaune yana kallon mutane da idanu baya magana, ita kemai komi dakuka sani hatta wanka”
yadanyi shiru Ahmad yayi murmushi yace “zaka iya zuwa ka zauna”
sannan yadauki flash yabada yace “ga evidence da Hajiya tayi confessing da kanta” daidai nan Obama shima yazo yabada footage din dahar an turo duk aka koma aka zauna na Obama aka fara playing gabaki dayan maganganun
Hajiya dasukayi da Maheer da komi jikin Baba yakara wani kalan sanyi,
sannan aka kunna flash din voice din Hajiya ne lokacin datake bama Adamu labari asiri tama Maheer wannan kara Yasmeen shigewa tayi karkashin benci tahau kuka Baba yama kasa cewa uppan kota fito kotai wani abu,
Ammi share hawaye takekawai su Baffa shima saida yashare kwalla su Yaya duka kuka, yan kotu kuka suke, fita Obama yayi yasa aka kira Adamu ya karbi address na Hajiya yakira aje ayi aressting nata sannan suka koma ciki.
Tass Alkali ya goge idanunshi anatse yace “Maheer kaga rayuwa!” Sannan yasa byro yashiga rubuce rubuce yabama wani abinda yarubuta aka saka a envelop aka fita dashi daga kotun sannan yayi gyaran murya yace
“abisa dogon bincike da shaidu kotu ta yanke shawaran bazata raba auren dake tsakanin Maheer da Fateema ba ahankali Maheer yasauke ijiyan zuciya nauyin da tuntuni zuciyanshi kemai ya
sauka gabaki daya, wani kalan sanyi Yasmeen taji azuciyanta tace Alhamdulillah,
anatse Alkali yace “bai kamata nazama emotional ba amman nadade banga case daya taba zuciyana ba irin na Maheer dan inada yara maza irinshi agidana”
Alkali yayi shiru yace “bazanma iya tunani ko kwatanta yarana ne sukai irin rayuwan nan da Maheer yayi ba”
Alkali yasake shiru yace “arayuwa bincike, sanin gaskiya nada kyau akowani al’amari kafin ayanke hukunci koka zagi mutum, so many people na wahala abisa laifin daba nasuba,
kuduba kugani kome Maheer yayi baya cikin hayyacinshi yayishi, matan nan tadaukoshi tadaura shi yamata,
Fateema itane abu nafarko daya soma dawo dashi layi kuma Allah ne yaturota rayuwanshi sabida tacire shi daga halin dayake ciki inda baiyi kidnapping nata ba dahar yau yanayin abinda yakeyi”
ijiyan zuciya Alkali yasauke ahankali yace “Maheer!” Ahankali Maheer yadago kanshi yakalli Alkali, nuna kanshi Alkali yayi yace
“you might grow up without a father without fatherly love amman yau agaban duka jama’an kotun nan zan sanar dakai kazama d’ana nazama mahaifinka!”
Allahu Akbar! Zokaji kabbara yanda yake tashi a kotun, Alkali yace “kuma I promise zanyi all I can to get you out of jail dan bakaine Pablo Escobar ba Maryam ce Aslin Pablo Escobar,
the first step was letter dana aika dashi yanzun nan nai requesting dakaina abude case naku ayi proper investigation dan YOU ARE INNOCENT MAHEER!”
Hawaye saukowa sukayi daga idanun Maheer yasauke kanshi kasa ahankali, Alkali yakalli mutanen dake kotu yace
“nariga nagama shari’ata all maganganun nan dakukaji inayi yanzu ina yinsu ne amatsayin mahaifi”
yay maganan yana maida kujeranshi baya yamike tsaye ahankali kowa yahau kallonshi ahankali yazo har gaban kujeran da Maheer ke zaune kusada lawyer shi Ahmad, Alkali yabude hannunshi yana kallon Maheer yace
“can I hug my son”?
Dago kanshi ahankali Maheer yayi yakalleshi baitabajin yanda yakeji ba yau kawai wani kalan tashi yayi ya rungume Alkali sai kuka ajikinshi haba kowa kwalla yake gogewa a kotun, har Ahmad, har Obama, hatta Adamu saida yay kwalla dudda deal yashigo dashi court din but all jama’an nan dashi kanshi Maheer din,
the atmosphere yasa yagane he’s wrong, he is a monster and in sha Allah daga yanzu ya chanza.
Hawaye saukowa sukayi daga idanun
Baba dawani kalan sauri yatashi yafice daga cikin kotun,
motanshi yabude yashiga yadaura
hannayenshi akan fuskanshi yafashe da kuka sosai yau kukan dayake yafi na ranan daya gano Pablo Yasmeen ta aura, baitabajin kalan guilt din nan dayakeji ba yau, komi dayama Maheer nadawomai fresh aranshi, dukan dayamai, mesa baiyi bincike ba? Maisa bai saurari Yasmeen kaman yanda
Ammi taroke shi yayi ba,
anya zai iya kallon MAHEER ever kuwa wayyo zuciyanshi, wayanshi yaciro
dasauri yamma IG text;
“Nayi kuskure akan case din Pablo
Escobar plssss ayi investigating afito da Maheer daga gidan yayi sannan zanyi withdrawing charges din danasa akanshi na kidnapping”…..
The whole Nigeria case din Maheer yadauka dan wasu dake kotu record the whole session an wasa a yanar gizo,
10:08
some reporters dasuka shigoma were live a IG secretary, some Twitter space wasu kuma tiktok live, internet is on fire, gwamnati sunfi kowa cin zagi wajen jama’a for abandoning yaron da aka haifa agidan yari ba tare da sun bama mahaifiyarshi tallafi ba, maza sun fi daukan case din sukasa agaban goshi suna Justice for Pablo dan ana yarda idan mata sunce maza sunyi raping nasu,
10:08
yanzu ga namiji dan uwansu evidence poro poro anyi raping nashi tun yana yaro abina gender su hakkin shi, justice fo Maheer, cus this is the first case na raping namiji da akayi that went viral,
10:09
case din Maheer yadawo the most talk about case a duniya gabaki daya not just Nigeria, kafin kace me mutane sunma Maheer creating go fund me account donating ake from every part of the world within few hours Maheer nada billions of Money aciki,Maheer yadawo wani kalan celebrity all news channels, gidan radio, jarida menene menene maganan shi ake, hotunan shi da akamai a kotu da video dan some people sunyi recording hearing din tundaga farko har karshe nata yawo a internet wayyooo wato Allah idan yatashi wankeka it takes just a blink of an eye kawai zakaga abu natafiya yanda yakamata ne kaman magic Allah kenan Al Azza Wajal!!
10:09
Lallashin Maheer Alkali yayi yace “I will get you out okay” gyadamai kai Maheer yayi su Obama suka wuce dashi Obama yahana asamai handcuff a hannu this time around, ko kallon side din da Yasmeen take tsaye Maheer baiyiba,
10:09
Yasmeen sai kallonshi take tana kuka tana gogewa da hijabi suna fitowa kotu irin mutanen dasuka gani saida sukaji tsoro kaman ranan salla sai hoton Maheer ake dauka ana kokarin mai interview yaki magana, aka sashi a mota aka wuce dashi.
10:09
Hannu Yasmeen Ammi tarike tace
“muje” rungume Ammi Yasmeen tayi sosai tana kuka haka dai suka taru suka fice da
10:10
ita amota suka sami Baba Ammi batacemai komiba sukasa Yasmeen tai zamanta abaya Farida tashiga gaba
Hajjo tazauna abaya sauran zasu shiga
10:10
motan Baffa Baba yakunna motan yaja sai kallon yanda Yasmeen ke kuka yake tacikin mirror yakasa magana kunyan yarinyar ma yakeji yanzu.
10:10
Sunyi nisa atafiya babu wanda ya iya lallashin Yasmeen a motan, dagowa tayi daga jikin Ammi tana rike cikinta tace “Ammi cikina”
10:10
kafin Ammi tamayi wani abu sai amai, arude Baba yayi parking yafito yana bude musu baya riketa Ammi tayi dudda tariga tayi aman amota amman tafito da ita haka tahauyi abakin titi kaganta saita baka tausayi babu komi ma acikinta amman sai aman take Ammi na bubbuga mata baya,
10:10
ruwa Baba yabasu ta kuskure baki
Ammi takamata zata maidata mota sai kawai tai luuuuu asume atsorace Ammi tariketa tace “Yasmeen Yasmeen” shima zuwa Baba yayi yace “Yasmeen ruwa suka watsa mata amman ko gezau, sata sukai amota Baba yaja motan sai asibiti aka karbeta akai emergency da ita.
10:11
Wata Dr takira Baba da Ammi tana murmushi tace “congratulations
Fateema na dauke da juna biyu” tai murmushi tace “tanada malaria zamu riketa anan mumata treatment kunsan
Malaria baida kyau ajikin mai ciki”
Gyadamata kai Baba yayi yace “tooh”
Dr tace “akawo mata kaya ta chanza dakuma abincin datakeso bakomi acikinta”
10:11
tashi Baba yayi kaman iska zai kwasheshi Ammi tabishi tace “muje na dauko mana kaya Farida da Hajjo saisu zauna da ita nadawo saika komar dasu gida” Gyadamata kai kawai
10:11
Baba yayi yawuce waje yana tafiya kaman fatalwa Ammi tabishi da kallo taje dakin da Yasmeen take dan yimisu sallama tanama bacci Yasmeen din sannan
10:11
tawuce tafita samin Baba tayi zaune acikin mota tashiga yaja motan sunyi tafiya mai nisa ya gangara gefen hanya yayi parking yajuyo yakalli Ammi dake kallonshi cikin wani kalan murya na tsantsan nadama yace “Maman Nana nayi kuskure babba”.
10:12
EPISODE
<YALKYALIN
Wani kalan kallonshi Ammi take kaman bazatai magana ba yace “I hope daga yanzu zaka gyara halinka,
10:12
shigowan Maheer rayuwan mu in the first place sabida Allah yanaso ka koyi darasi ne,
10:13
yanda kake dasu Yasmeen bashine zai tsaresu ba Allah shine ke tsare mana yaran mu, sannan kayi imani da kaddara kasan cewa hukunci ba ahannu ka yake ba a hannun Allah yake, Baba Nana kana claiming kanason yaranka but this case made me realize bama kasan menene soyayya ga yaro ba” Ammi tayi shiru tace “sa yaro amakaranta, supporting nashi a education, bashi ci da sha kadai bashine so ba, listening to yaranka is the first thing in nunama yaro so, listen to your kids, ka saurari views nasu, look at how suke ganin abun shine so, abinda yasa kaga suke sona kenan cus I listen to them and guide them,
10:13

baka tausayama diyarka ba Yasmeen, bakaji tausayin kukanta ba, nasan alokacin naji haushin abinda Maheer yamana na yaudaran mu but na tausayama Yasmeen sabida nasan menene so,
10:14

I saw yanda take mutuwan son yaron nan, na lallasheta na lallabata bakayi none of that ba saima dukanta dakayi,
10:14

sannan I hope ka koyi cewa taurinkai baya karan mutum da komi sai nadama da regret yasaka akunya”
10:14

Ammi tasake shiru chan tace “I hope ka koyi cewa shi tsana ba’a zafafa shi sabida makiyinka kan zama masoyinka kuma Mai cetonka, haka masoyinka kan zama makiyinka kuma makashin ka,
10:14

look at kalan dukan dakama yaron nan kaman bakada imani, koda yamaka laifi bakada right dazakama yaron nan baligi mutumin dake Auren diyarka irin wannan dukan yazakaji akama yaranka irin wannan dukan”?
10:14
Ammi tadanyi shiru ta share hawayenta tace “Maheer yamana laifi yayi kuskure but munama Allah laifin dayafi wannan ya yafemana, dudda abin nan dayayi ko alokacin saida nace Alhamdulillah koba komi yabiyota har gida ya aureta ta halas inda fa ya sacetane yatafi da ita batare daya aureta ba? Daya zamuyi”?
10:15
Ammi tasakeyin shiru tace “labarin
Maheer yatabani, after all kalan rayuwan nan dayayi he still have to face you kamai wulakanci da tijaran duniya walahira”
10:15
wani kalan ijiyan zuciya Baba yasauke muryanshi narawa yace “Maman Nana dan Allah kidaina fadin haka kinasa ina karajin tsanan kaina sosai” dasauri
Ammi tace “wh kaji tsanan kanka da kyau, u deserve much more guilt ma da wannan,
10:15
bakada kirki ko kadan Baban Nana, bakada kirki indai kan yaranka ne baka dagawa kowa kafa, nagida ma baka bari ba bare na waje rashin mutunci babi babi ka iya, and to top it all yaranma bakama iya musu soyayya yanda yakamata ba,
10:15
gabaki dayanka bahaggon mutum ne da bahaggon tunani, tunanin ka duka abaibai kaman ba musulmin kwarai ba” fashewa da kuka Baba yayi yace
“Nagane kuskurena wh wh Nagane
how do I correct my mistake now”?
Cikin kufilewa Ammi tace “kaika sani wih da nine Maheer sainayi zuciya na sakan maka diyarka saika jika kasha nagadai bada zinare aka kera Yasmeen dinba,
10:16
kadaiga nine Mahaifiyar Yasmeen ko amman wh idan Maheer zai saki
Yasmeen yanzu sainaji dadi sabida kaga ukuba da kalan halin da Yasmeen
10:16
zata shiga karasa kwanciyan hankali da natsuwa da sukuni sabida kasan gravity mistake din dakayi arayuwanka, yarinya na son yaro kadage saika raba Auren harda maka yaro a kotu”
10:16
girgixa mata kai Baba yayi yama kasa magana dan yasan dudda Ammi namai wankin soso da sabulu but gaskiya take fadi, Ammi tace “kuma namaka alkawari wh wih bazan shiga case din nan ba, zan kula da Yasmeen kodan cikin datake dauke dashi amman kaga harkan aurenta da Maheer billahillazi kaine daka batashi zaka gyarashi bazan shigaba,
10:17
yanda ka daukota ka lakadawa mijinta duka ka kwaso kayanta ka shirya correcting every one of your mistakes on your own bakada support din wih”
10:17
dasauri Baba yakalli Ammi yace “kada kimin haka bansan Yazanyi ba” Ammi tace “amman kasan yanda zakayi rashin mutunci da tijara ko? To haka zaka samo yanda zaka gyara komi, nidai tada mota muje namata girki agida”
10:17
ganin Ammi tahau sama kuma yanzu lallabata yake yasa yatada yana share fuskanshi.
Tun kafin sukai gidansu kalan mutanen dayagani akofar gidansu yan reports dasauransu saida suka firgita.
Protest ake akofar gidan Baba sun rirrike cardboard paper an rubuta free Maheer ajiki,
14:47
ana ganin motan Baba aka fara ihun Free Maheer! CP free Maheer! Cp Free Maheer, juya motan Baba yayi yabar anguwan.
14:48
Saidai suka sayama Yasmeen sababbin kaya a boutique sukasai abinci a eatery kiranshi IG yayi a office yace kazo office ina neman now yana dropping Ammi a asibiti yatafi headquarter.
14:48

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button