Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 31

Sponsored Links

โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*PAGE 31*

Khalid yi tafiyar ka gida kaji”
Cewar Hajiya, bayan fitar yaron mik’ewa itama Hajiyar tayi ta wuce sama bata k’ara bi takan Meenal akan maganar ba dan ta k’uduri aniyar cewa bazata k’ara shiga maganar soyayyar su biyun ba, sai dai suga ta yanke hukunci kawai,

Daga kan minutes ya fara lissafi sai gashi mintunan suna ta wuce wa shiru ba Meenal ba labari, wayar shi ya d’auka ya fara kiranta sai dai yarinyar nan dan wula walan walakanci haka tayi kunnen uwar shegu da kiran nashi duk da cewa yana da tabbacin taga kiran,

Musty daya shigo gidan yanzun ne ya hango shi zaune sai faman latsa waya yakeyi,

“Baa’ba yadai me kakeyi anan zaune kai kad’ai kuma?”

Dogon tsaki AK yaja yana barbaza gashin kanshi,

“Ya dai ko mutuniyar ce ta tab’o mana kai?”
Musty ya k’ara tambaya,

“Wai haka kuke fama da yaran nan dama?
Da kyar fa na samu yaron dana aika cikin gidan nan akan ya kiramin ita amma wai sai cema yaron tayi ya fad’amin cewa tayi bacci alhalin kuma Hajiya tace ma yaron yace gata nan zuwa, kasan mintuna nawa na b’ata anan zaune ina jiran fitowar ta?”
Bai jira Musty ya amsa mishi ba yaci gaba da cewa,

“Kusan awana d’aya fa a wajen nan zaune na kira wayarta nasan kuma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba cewa taga kiran nawa kin d’auka dai tayi saboda ta raina ni”

“Calm down mana ya kake so ka b’ata ranka akan wannan d’an k’aramin damuwar,
Menene ma na wani b’ata ma kai lokacin dahar sai ka wani nemi yaron aike cikin gidan a sanda kake buk’atar ganin ta?
Gidan kune fa nan d’in kana kuma da damar da zaka iya shiga cikin shi a duk sanda kayi ra’ayi, oh wai nan dama kai kazo tad’ine kana jiran ta fito?”

Musty ya fad’a yana nuna AK din yana kuma mishi dariya,

“Zanci uban ka a wajen nan idan ka nemi matsamun kasani”

“Miye laifina ni kuma daga baka shawara, kawai ka tashi ka bita cikin gidan tunda yau mulki takeji bazata yarda ta fito ba, kuma ai mai nema baya fushi kuma yasin ko nine ita ina da saurayi a gida bazan yarda in fito hira a harabar gida duk Sauro su gama cizona a banza ba”
Gefen da AK d’in ke zaune shima Musty ya rab’a ya zauna,yana mai cigaba da cewa,

“Baa’ba sai kayi hakuri fa indai yan matan nan ne duk haka suke da shegen jan aji amma na lokaci ne kaci gaba da tara ta kawai indai rabon kace duk zaka fanshe in kaso a rana d’aya” ya k’arasa fad’a yana dafa kafadar AK din ya jinjina alamun tabbaci.

“Wai kai kasan cewa har yanzun yarinyar nan tak’i bani hankalin ta yanda ya dace,
Idan nayi nan sai tayi nan na rasa me take nufi dani, wai har cemin fa tayi wai ita ba aure ne a gabanta ba yanzun, to wai so take ta maida ni d’an iska in zuba ido ina kallon maza na mata layi daga nan har zuwa sanda taga dama kafin muyi auren?
Kana kallon dai yanda nike ta k’okarin canza kaina duka a kokarina na ganin na shawo kanta amma kasan me?
Har yanzun banga wani canji mai girma a tareda ita ba har yanzun kallon taubashi abokin wasan ta take min”
Ya k’arasa fad’a a dame sosai,

“Bana so in tauye tane shi yasa nike tabi a sannu ba tareda na gabatar da kaina a gaban manya ba, amma tunda hakan ta zab’a ni kuma bani da wani zab’i sai na aikata hakan, idan Allah yasa su Baba Usman su iso lafiya zanyi magana dashi kawai suje su nemar min auren ta idan yaso daga baya ma daidaita tunda haka ta zab’a”

“Hakan ma tunani ne mai kyau, nima naso inyi maka wannan maganar gara batun yaje gaban manya saboda idan hakan ya faru shine zata k’ara tabbatar da cewa da gaske kakeyi,
Yanzun dai kar kayi fushi tashi kaje ka sameta a sashen Hajiyan kuma idan kaje koda wasa karka nuna mata b’acin ranka”

“Musty yarinyar nan fa ta riga ta gama raina ni wallahi,”

“Ah ah ba raini bane su mata haka suke, hakan kuma da takeyi shike kara tabbatar da cewa tana da class dan haka karka damu kanka,
Kasan yan magana sukace Mai ganin abu daga nesa da tantama yake sai mutum ya matso kusa zai gano abunda ya dace,
Muje in taka maka”
Jawo hannun AK din yayi ya mik’ar dashi tsaye, haka suka jera suna tafe suna k’ara tattauna wa sai da yakai shi har bakin k’ofar falon kafin ya juya ya koma da baya zuwa side d’in Hajiya Jummai shi kuma AK ya shiga falon da Sallama.

Zaune a falon ya sameta wayarta ne rik’e a hannun ta wanda ta maida gaba d’aya hankalin ta akan wayar tana faman latsewa, da alama chatting takeyi kuma yasan baya wuce ace dasu Meelat take chat d’in,
Kwarai kamar yanda ya hasaso dasu take chatting domin tun bayan tashin Hajiya ta maida hankalin ta akan wayan saboda yau su dukan su suna online suna magana ne akan isowar da Moon zatayi Zaria jibi, hankalin ta ya d’auku akan hirar nasu dan haka gaba d’aya sai bata k’ara tunawa da batun AK daya aiko yaro kiranta ba,

Har ya isa inda take sam bataji motsin shigowar nashi ba gane hakan da yayi shi kuma sai ya koma ta bayan ta gefen kunnen ta yakai hannun shi ya tafa su da k’arfi
“Faff”
karar Sautin tafin hannun nashi suka shiga cikin kunnuwanta a bazata, sosai ta firgita wanda har hakan saida yayi sanadin data jefar da wayar dake hannun ta, tana shirin zurawa da gudu a cikin halin firgicin da take shi kuma ya rik’o kafad’un ta da hannun wanshi ya maida ta zaune,

“Ke dallah can matsoraciya kawai, wai me yasa kin cika tsoro ne? daga d’an tafa hannuwa shi kenan duk kin wani bi kin firgice kamar wacce tayi karo da kura ko wani abun da zai iya cutar da ita! Nine fa ba kowa ba”

Tureshi ta farayi tana kai mishi duka tako ina,
Tsalle d’aya yayi ya tsallako daga bayan kujerar da take ya dawo ta gabanta yana dariya,

“Nidai wallahi ka dauki alhakina, babu damar mutum ya zauna shiru indai kana gida sai ka sashi yayi surutu, waima Ina ruwan ka dani to?”

“Niko keda ruwa dake Darling da fari dai wana kama?”ya tambaya yana tsats tsareta da ido,

“To ni wani abu na maka da zaka kamani?”

“Oh da gaske baki san abinda yasa zan kamaki ba? To waye na turo yaro ya kiramin tace ma yaron ya koma yace min tayi bacci?
Shi baccin ai naga shi nazo na sameki kinayi, ba d’azun dama nace miki zanzo hira ba, mai yasa baki fitoba kika shanya ni a waje? wulakanci ne hakan da kikayi fa, amma dai ba komai na yafe miki karki k’arayin haka next time dan naji haushi sosai da kika shanya ni baki fito ba”
Ya fad’a a fizge bayan ya d’an kame fuskar shi kad’an,
Shiru tayi ba amsa,
Shima kuma sai yayi shiru da bakin shi daga karshe ma sai ya jinginar da kanshi a jikin kujerar kawai yaci gaba da binta da kallo kamar ya samu tv shi dai wallahi Allah ya sani baya jin zai tab’a iya gajiya da kallon ta, dan shi kad’ai yasan yanda yake ji aduk yanda ta kasance kusa dashi irin haka Allah dai yakai damo ga harawa, ko baici ba ai zaiyi burgima son rai wallahi,

Shifa bai iya kallo yana d’auke kaiba ah ah inzai kalleta kallon ga daga yake mata ita kuma sam ta kasa sabawa da hakan, da zarar ya fara kallon ta duk sai taji ta tsagu bazata samu kwanciyar hankali ba har sai ta dena jin nauyin idanun shi a jikin ta, dan haka ko yanzun bayan data d’auki wayarta kasa cigaba da chatting din tayi ko nasu chat din dake shigowa cikin wayarta kasa karanta su tayi a tsanake dan bata gane komai kuma, sunyi zaman a haka na tsayin lokaci baice mata komai ba sai kallo itama kuma ta kasa tanka mishi, gajiya tayi da zaman ta mik’e tana mikewa kuma shima ya mik’e tunda ta fara taka matakalan benen bata yarda ta juyoba domin tunda taji takun tafiyar shi a tare suke haurawa tasan bazai wuce yace zashi d’akin Hajiya ba,
Sai dai abunda bata sani ba shine ita dashi a tare suka kai cikin d’akin da yake matsayin nata yanzun a gidan, bata lura dashi ba kwata kwata dan haka koda ta shiga sai tayi tsaye a tsakar d’akin dafe da k’irjin ta tana sauke a jiyar zuciya a jejjere dan tun dazun bata samu damar shaqa ko sauke numfashi da kyau ba har saida ta shigo cikin d’akin,
Tunawa da tayi cewar bata kulle k’ofar d’akin bane hakan yasa ta juyawa da niyyar ta kulle k’ofar gudun karma idan ya fito daga d’akin Hajiyar yace zai lek’o nata, sai dai kuma tana juyawa taci karo dashi tsaye kik’am a gabanta hannayen shi goye ta baya yana binta da kallon nashi da yake mugun takurata,
Bud’e baki tayi da niyyar kwarara ihu sai shi kuma yayi azamar daura hannun shi manuniya a saman lab’b’anta,

“Shishshsh” yayi mata alamun tayi shiru da bakinta,
Ganin hakan ita kuma sai ta fara matsawa baya saboda kusancin dake tsakanin su yayi yawa sosai ta yanda har tana iya ganin yanda numfashin shi yake sauka a k’irjin shi dan rigar dake jikin shi duk da cewar bata kama shiba sam amma wuyar rigar yana da fad’i sosai kuma yadin rigar irin mai kwanciya ne a jiki, ga kuma gashin dake kwance lufluf akan k’irjin nashi da suka nuna kansu ta inda wuyan rigar ya sauka,
Kallo d’aya tama wajen a cikin kuskure tayi saurin d’auke kanta bata k’ara gigin kai idonta wajen ba ta ci gaba da matsawa baya,
Ganin tana yin baya shi kuma sai yaci gaba da binta tana matsawa yana binta har takai jikin wardrobe din d’akin ta jingine dashi,
K’ara matsowa yayi sai dai bai yarda ya matse mata waje da yawa ba sai yayi amfani da hannuwan shi ya dafe jikin wardrobe din ya zamana ya sanya ta a tsakiyar hannayen nashi,

Kankame jikin ta dake rawa sosai tayi bayan ta runtse idonta da kyar ta samu ta iya fusgo magana da karyayyar murya tace,

“Me.. Me… Me kakeyi, meee kakeyi haka dan Allah?
Mai maa kazooyi anan too?”

Murmushin mugunta yayi yana cigaba da kallon ta yace,

“Oh baki ma san abinda nazo yiba bayan nazo tad’i kin shanya ni a waje saboda rashin tsoron Allah kika k’i fitowa, na shigo har ciki kuma haka bakiji tausayina ba kika k’ara shareni daga k’arshe ma sai guduwa kikayi, na biyoki kuma kina tambayar mai nazo yi, to hira nazo muyi a cikin d’akin tunda anan kike so muyi hirar koh?”
Ya tambaya yana d’age mata girar shi,

“To aini dama nace maka bazan zo ba”

“To da bakizo ba bagashi ni dana matsu dason ganin naki nazo ba, ko bakiyi murna da zuwar nawa ba?”

Tura baki tayi kafin ta bashi amsa da cewa,

“To ai hira a k’ofar gida akeyi shine kai kuma ka Kama ka biyoni har cikin d’akin bacci na, anan ne zamuyi hirar ko koh so dai kakeyi Hajiya tazo ta ganka in shiga uku,
Mai zance mata idan ta sameka anan? Nidai dan Allah ka rufamin asiri ka tafi ba dan halina ba”

“Oh kunyan Hajiya kikeji bayan a gabanta na maimaita kalaman soyayya ta a gareki,
Idan ta tambaya zance mata nazo hira ne mana tunda a gabanta na aiko yaro kika ce acemin kinyi bacci,
Ni kuma bazan iya bacci ba tareda na ganki ba shi yasa na biyoki har nan”
Ya furta hakan babu alamun damuwa ko d’ar a tareda shi,

“To ai ka ganni tun a falo mai yasa baka tafi ba?”

“Ok saboda ba iya ganin naki ne ya kawoni ba zuwa nayi ki bani amsar da nike jiran ji daga gareki,
Shin kin amsa soyayyar tawa in aika nawa iyayen can gidan ku ko koh har yanzun baki gama nazarin da kikeyi a kaina ba?”

“To aini na fad’a maka ba yanzun zanyi aure ba”

“Ni kuma Ina mai tabbatar miki da cewa yanzun shine lokacin da nike buk’atar ki a cikin rayuwana dan haka rashin shirin ki bazai dakatar dani ba”

“Nidai dan Allah ka tafi to naji na yarda gobe zan baka amsar eh ko ah ah din da kake son ji,”

“Gobeee” ya furta yana hura mata iskan bakin shi akan fuskarta,

“Lallai bakya son in tafi indai har sai gobe ne bazan iya jira ba, kodai ki amsa ki furta min da bakin ki cewa kina sona ko kuma yau in kwana a cikin d’akin nan…. ”

Tun bai gama furta kalmar kwana a d’akin ba ta katse shi da cewa,

“Meee ๐Ÿ˜ณ “idanuwa a waje tana binshi da kallon tarin mamakin shi daya ke neman sa zuciyarta tsayawa daga aikin,

“Wai anan d’akin zaka kwanan?” Ta tambaya saboda ta k’arajin tabbaci daga bakin shi,

“Oh kina wasa dani koh kina ganin kamar bazan iya ba,
Ok to bari ki gani”
Kamo hannun ta yayi suka k’arasa k’ofar dakin dake bud’e har yanzun, da kafar shi yayi amfani wajen tura k’ofar ya rufe kafin ya murza key a jikin k’ofar,

Kuka take shirin fashe mishi dashi ganin da tayi da gaske ya kulle k’ofar d’akin,

K’arfi yasa ya juya ta kafin ya matsa gab da ita ya had’a bayan ta da k’irjin shi sai dai sam bai yarda ya matse taba,
Duk’o da kanshi yayi saboda tazarar tsayin dake tsakanin su, ya cusa kanshi a gefen wuyanta ba tareda ya kwantar ba, rawa jikin ta ya d’auka dan take taji wani zazzabin tsoro yana neman kamata kankame jikinta tayi sosai,

Bakin shi ya maida kusa da kunnen ta kafin murya can k’asa ya furta mata cewa,

“To yane Dr kin shirya amsar Soyayyar nawa kuwa? Ko har yanzun kina da ja”

Shiru tayi jikinta naci gaba da rawa,

“Kinsan dai in baki amsa ba ana zan kwana koh?”
Ya kara fad’a bayan yayi k’asa da muryar nashi sosai fiye da yanda yayi magana da ita a d’azun,

“Eh na shirya yanzun indai na baka amsa ai zaka tafi koh?”
Ta tambaya da muryar kuka dan Wallahi ita dai a tsorace take,kawai ya fice mata a cikin d’akin shi tafi muradi,

“To kice kina sona sai in tafi, kuma da shauk’i nike so kalaman su fito daga cikin bakin ki”

“To shikenan naji Ina sonka amma da sharad’in ba yanzun zamuyi aure ba”
Ta fad’a da shakakkiyar murya,

“Ban yarda dako wani sharad’i ba An mata, kuma ni ba haka nike son kalmomin su fito daga bakin kiba, haba ai ko kema kin san cewa sam baki furta kalaman naki da shauki yanda ya daceba, haka nike so inji kince, Abdul Khareem Ina sonka na kuma amince zan aureka mu rayu har k’arshen numfashi”
Ya jero kalaman a natse kuma a tsare yana kwaikwayon muryar ta,

“In kuma hakan bai miki ba bari in maimai ta miki nawa kalaman sai ke kuma ki bani amsa,”

A yanzun kam jingina ta yayi da jikin shi ya kuma ziro hannayen shi ya d’aura akan nata wanda suke cikin juna a dai dai cikin ta,

“Ameenat Ina sonki irin son da zuciya da gangar jikine kawai suka san adadin shi, dan Allah ki tausaya ki amshi soyayya ta, ki bani dama in gabatar da kaina a gidan ku matsayin mai neman auren ki, ni kuma nayi miki alkawarin cewa zan kula dake fiye da yanda zan kula da kaina zanci gaba da sonki har zuwa gushewata”

Yana maganan ne yana k’ara kan kameta a cikin jikin shi cike da shauk’i, hucin numfashin shi da kuma gashin gemun shi da yake gogar mata wuya sune abinda suka kassara ta ita kuma, sai dai duk yanda taso ta kwaci kanta hakan ya gagara saboda k’arfin su ba d’aya ba kuma ba rik’on wasa ya mata ba,

“Ki dena wahal da kanki bazan sakeki ba har sai kin bani amsa, kinyi shiru ke nike saurare fa ko baki so in tafi in barki kiyi bacci ne?”

“Ina so” ta fad’a da shakakkiyar muryar ta wacce tayi sanyi kalau,

“Uhumm to ki fad’amin mana”

“Ina,
Iii… Inaa sonnn.. kaaaa”

“Banji abinda kikace da kyau ba”

“Ai nace Ina son ka nidai ka sakeni haka ka matseni fa kuma ai d’azun nan nace maka bana son kana tab’ani…. ”

Bata kai karshen zancen ba yasa karfi ya matse ta ya d’aga ta sama ya fara juyi da ita a cikin d’akin,

Shi yana ihun murna ita kuma tana ihun kiran dan Allah ya sauketa tana ganin jiri, dan da gaske jirin take gani

“Dukan k’ofar d’akin hajiya keyi ta waje tana faman kiran sunan Meenal,

“Ke Meenal wani sabon shegen taka ne kuma zaki shiga d’aki ki rufe kina yima mutane iface iface, bazaki zo ki bud’e k’ofar nan ki gaya min ihun ubanme kikeyi ba”

Jiyo bugun k’ofar da Hajiya keyi ba kakkautawa ne yasa shi sauke ta bai tsaya bi ta kanta ba duk da cewa yana kallon sanda jiri ya kwashe ta ya watsar a kan gadon ta dake gefe,

Da sauri ya bud’e k’ofar d’akin yana budewa kuma ya janyo hannun Hajiya ya fara jujjuyata irin rawar nan da turawa keyi, ya farayi da ita sam bakin shi yak’i rufuwa tsabar farin cikin daya ke ciki,

Bige hannun shi hajiya tayi da karfi ta kumayi amfani da k’afarta ta take nashi kafar da karfin da allah ya bata,
Ta kuwa yi nasara dan Zafin bugun dana taka war su suka sanya shi cin burki na dole, a shagwabe ya kalleta,

“Hajiya bakiga Ina cikin farin ciki bane shine kike so ki b’ata min mood din da nike ciki mai dad’i,”

Jawo Hajiyar yayi ya rungume tsan tsan cike da murna yake cewa,

“Hajiya takwarar ki ta amsa tayin Soyayya na a yau, ta kuma yarda ta bani dama in tura iyayena a nemo min auren ta, shi yasa kikaga Ina ta murna Hajiya burin ki zai cika kwanan nan na ganin aure na”

Daure fuska sosai Hajiya tayi tana binshi da kallo sheqeqe ta bud’e baki tace,

“Shi soyayyar duk yafi k’arfin a bada amsar shi a ko Ina duk fad’in gidan nan har sai an shigo har cikin kuryar d’aki?,
Kenan da tace ace maka tayi bacci wanko naka kafafuwan kayi ka biyota har cikin d’aki saboda gaka rasa kunya, to fita maza fita mata daga d’aki kuma kar in k’ara ganin ka a cikin d’akin nan koda wasa,”

“Hajiya bafa abunda kike tunani bane, kema ai kin san bazanyi haka ba, kawai dai na kasa hakuri akan jan ajin da take min ne shi yasa na biyota har nan d’in kiyi hakuri,”

Hannun ta yaja sai da suka kai bakin kofa yaci burki, kafin ya juya yana kallon Meenal data cukuikuye kanta a k’asa ta had’a kai da gwuiwa a gefen gadon tun bayan shigowar hajiya d’akin,

“Dr good night ”
Ya fad’a yana aika mata da kiss din da yayi ma yatsun shi guda biyu ya nuna ta dashi, janye shi Hajiya tayi tana kai mishi bugu da mitan cewa bamashi da kunya a gaban idonta yake aikama jikarta kiss wato shi ga fitsararre sirikin zamani tana cigaba da mitan suka k’arasa fita daga d’akin tana cema Meenal ,

“Ki taso ki kulle k’ofar ki kuma dunga kulleta da key kina ji na fad’a miki karki yarda ki dunga kwanciya baki kulle kofa da makulli ba ”

Bata iya mik’ewa daga inda take ba har sai da ta tabbatar da cewa sun sauka k’asa kafin taje ta tura k’ofar d’akin ta rufe da key ta koma kan gado ta kwanta a rigingine tana kallon silin din dakin,
murmushi ne ya kwace mata sai tayi saurin kai hannu ta rufe fuskarta tana mai jin kunyar kanta da kanta,

Wai yau ita Meenal itace ta furta cewa tana son wani, harma ta bashi daman zuwa ya nemi a auren ta a wajen iyayen ta,
Sam batayi zaton cewa hakan zaizo mata da wurwuri ba, lallai AK ya shammace ta da yawa, ita da taci buri mai girma nayin rayuwar da take so ta yanda zata biya bashin Yarintan ta da aka dakushe mata, sai gashi tun ba’aje ko Ina ba da alamu burin nata dai bamai cika bane.

*UMMIEE CE*โœ๐Ÿผ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button