Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 26

Sponsored Links

โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ

*BOOK 2*

*PAGE 26*

Kusan raba dare tayi ba tareda ta iya rintsawa ba, kira ko ta kwatanta kiran shi sau adadin da bata iya lissafi ba, sai daga baya ta gane cewa da gangan nema ya kama tashi wayar ya kashe tunda dole yasan cewa zai sa zuciyar ta a shiga ukun da dole ta kirashin tunda ya sauka a online,
Wai ita Sarki keso!
Bai tsaya iya nan ba kuma har saida ya mata wayau yasa itama ta amayar da abunda ke cikin nata zuciyar duk da cewa ita koda ta rubuta mishi kalmar I LOVE YOU TOO,din ta tura tasan cewa kalmar daga k’asan zuciyar ta ta fito amma bawai da wani manufa ta tura hakan ba,
Wato su maza idan basu nuna ma mace ban bancin yawan shekaru, wayau, da kuma hankali ba basa samun nutsuwa,
Anya ma kuwa ba itace ta kwafsa ta yanda yayi saurin gane cewa itama son shi takeyi ba kuwa?
Ita yanzun duk ba wadannan ne damuwar ta ba irin yanda yace wai gobe zaizo gida ya kawo gaisuwa,
To idan Baba Usman ya tambayeta mai zata ce mishi?
Kai gaskiya fa tana cikin chakwakiyar da bata san wanda zai fidda taba, waye ma wanda ya kamata ta tunkara da wannan maganar wanda zai bata shawarar daya dace?
Meenal ce sai dai a yanzun kuma bata jin zata iya tunkarar Meenal din da wannan maganar dan har yanzun gani takeyi kamar taci amanar meenal din ne, to amma ai indai abun ya tabbata dole meenal din zata sani bai kamata kuma taji a bakin wani ba a dai yanda suke kamata yayi ace itace wacce zata sheda ma Meenal din komai dake faruwa to amma kuma ta yaya?
Shin fitowa fili zatayi tace mata,
Meenal tsohon mijinki wanda kuka rabu ya dawo wajena yana sona da aure ko da wani kalmar zatayi amfani wajen yi mata bayani,

Wallahi Allah ita dai Allah ya sani tana cikin tsaka mai wuya sosai kuwa ga abun murna ya samu amma kuma babu halin yin murnan,

Umman su da hawowarta saman kenan tazo d’aukar wani abunda ta manta bata d’auka a d’akin ta bane ta hango wutan d’akin Moon d’in a kunne,
A gogon wayarta ta kalla wanda ya nuna kusan 1 saura na dare, mamaki ne ya kamata domin tasa Moon din mawuyaci ne ka sameta a farke zuwa wannan lokacin dan ita da wuri take bacci bata dogon hira duk ranar da batayi baccin da wuri ba kuma to tabbas sai dai in suna da wani case mai mahimmanci, dan haka mai makon ta wuce dakin ta kamar yanda tayi niyya sai ta juya akalarta zuwa d’akin Moon din dan ta kashe mata wutan.

Da sallama ta shiga bayan ta tura kofar, tsayuwar cak tayi tana bin Moon d’in da kallo wacce ke kai kawo a cikin d’akin ta kasa zaune ta kasa tsaye mafita kawai take nema ta yanda koda maganar nan ya fita jama’a bazasu kalleta a matsayin maciyiya amanar da take son mijin daya saki yar uwarta ba, cikin yan awanin da basu kai uku ba duk ta firgice ta rasa nutsuwar ta,

“Lafiya kike kuwa? Maiya sameki kike farke har yanzun? Wannan kai da kawowan kuma da kikeyi shima na menene?”
Umman su ta jero mata tambayoyin bayan ta maida kofar d’akin ta kulle,

Da hanzari Moon din ta k’araso inda take tana isowa bata jira komai ba ta rungume ta,
Kukan tashin hankalin da take ta dannewa tun d’azun ne ya kwace mata ta fara rairashi ba kakkautawa,

“Ke wai miye haka? Ya abunda na tambayeki daban baki bani amsa ba kinzo kin kankameni kina min kuka!
So kike nima nawa hankalin ya tashi kamar yanda kika tada naki? Kiyi shiru kimin bayanin abunda yake faruwa da yasa kika kai har yanzun bakiyi bacci ba”

“Umma ina cikin matsala ban san da wani idon zan kalli mutune ba idan abun nan ya tabbata,
Mutane zasu dunga kallo na a matsayin maciyiya amanar da taso mijin yar uwarta”

Kamata Umman nasu tayi suka k’arasa bakin gado suka zauna jin kalaman dake fita daga bakin Moon din wadanda ita bata gane musu ba sam,
Sai da ta zaunar da ita kafin tasa hannun ta ta sharema Moon din hawayen ta kafin tace,

“Kiyi shiru da kukan nan haka kimin bayanin abunda ke faruwa yanda zan gane”

Wayarta Moon din ta d’auko ta shiga cikin chat dinta da Sarki hirar da suka gudanar a d’azun din ta nuna ma Umman nasu tun daga farko har karshe,

“To menene abun damuwa ko tashin hankali anan Maimoon dan wani namiji ya nuna yana sonki?
Yaune aka fara cewa ana sonki da zaki damu kanki ki d’aga hankalin ki nima ki d’aga min nawa hankalin, waneni shi d’in? ”

“Umma bazaki gane bane, domin ba kalmar son bane abin tashin hankali a wajena tunda ai ba akan shi na farajin kalmar ba, ah ah shida kalmar ta fito daga bakin shine tashin hankalin nawa a halin yanzun”

“Shi yasa nima ai na tambayeki wane ne shi din?”
Ummah ta k’ara tambaya a karo na biyu,

Sauke ajiyar zuciya mai nauyi Moon tayi kafin ta iya kallon fuskar Umman nasu ta bata amsa da cewa,

“Ya Sufyan Sarki Mijin da suka rabu da Meenal d’in Hajiya,
Shine wanda ya furta yana sona kuma wai aurena zaiyi gobe kuma yake son yazo yaga baba dan ya nemi izini a wajen shi ni ban san ya zanyi ba tun d’azun nike kiran wayan shi ya kashe wayar ban san ya zanyi ba”
Ta k’arasa fad’a da muryar koka kananan hawaye na Saukowa kan kumatun ta,

“Turk’ashi!
Shi mijin na Meenal ko ince tsohon mijin shine yace yana sonki?
To ma a ina kuka had’u ya akayi yasan ki ko dama kun saba dashi ne?
To shi bai san alak’ar dake tsakanin ki da ita Meenal din bane da zai wani zo yace son ki yakeyi ko koh dai salon ya b’ata zumuncin dake tsakanin ku, wannan ma ai ba maganar da ya kamata kunne ya saurara bane dan ana barin halas ko dan kunya inshi namiji ne bashi data ido aike mace ce duk da bawai hakan ya haramta bane amma kusancin yayi yawa, ke mema ya had’aki dashi?”

Kaf abunda ya faru tun daga ranar daya sha gaban ta da mota har zuwa yau Moon ta kwashe tass ta sheda ma Umman su,

“Maimoon kina son shine?”

Shiru Moon tayi kafin ta amsa da cewa,
“Nima ban san yanda zan kwatanta abun ba, amma nasan ina matuk’ar kokarin kame kaine akoda yaushe indai ina tareda shi,”

Riko hannun ta Umman tayi,
“Moon bazance karki soshi ba domin ban san ya kikeji akan shi ba, sai dai zan miki tuni ne akan zumuncin dake tsakanin ki da yar uwarki Meenal ki d’auka cewa kece kika rabu dashi sai kuma kwatsam kikaji cewa ya koma sonta duk da kawancen dake tsakanin ki da ita ya zakiji, kibar batun cewar da akayi babu abunda ya hada su na auratayya koma dai yayane ita d’in tayi zama na shekaru a matsayin matar shi dan haka koda bata nuna a fuska ba tabbas ba lallai bane hakan ya mata dad’i a cikin zuciyar ta, ni dake dukan mu mata ne kuma ciwon ya mace na d’iya mace ne abinda bazan so ya faru dani ba indai zumuncin dake tsakanina da wata na gaskiya ne shima bazan so ya faru a kanta ba dan haka ina mai baki shawara da kisan yanda zakiyi ki cire son shi a cikin zuciyar ki in ma kin fara son nashi,
In kuma babu soyayyar falillahil hamdu sannan karki yarda ki barshi yazo gidan nan a gobe kisan duk yanda zakiyi ki hana shi zuwa ganin abban ku dan su maza kusan tunanin su d’aya ne basu fiye damuwa da abun da ke iya zuwa ya dawo ba kinji dai na fad’a miki dan in hakan ya tabbata ban san da bakin da zan kare kaina wajen Hajiya ba dan haka babu ruwa na ki kuma kwanta kiyi bacci dare yayi”
Tana gama fad’in hakan ta fice daga d’akin bayan ta kashe ma Moon din haske,
Wannan dare dai sam baiyi ma Moon dadi ba domin sosai kalaman Umman su ya k’ara sanyaya mata jiki, kamar kuma yanda Umman nasu tace ta d’auki hakan a matsayin cewa a kanta ne abun ya faru itace ta rabu dashi sai ya koma yana neman yar uwarta ya ita zataji,
Gaba daya sai takejin ai in itace hakan ya faru da ita tofa tabbas bazata iya d’auka ba, to waima miyasa tun farko tayi saken da har ta bar zuciyar ta ta kusantu dashi har haka? Lallai ita soyayya batayi mata adalci ba me yasa?
Me yasa?
Me yasa? Zuciyar ta zata kamu da son shi.

Tsabar yanda tasa damuwa a ranta ne hakan yasa washe gari ta tashi da zazzafar zazzabin dako aiki bata iya fita ba dan sai da aka kira likita yazo har gida ya dubata,
Fad’a sosai umman su ta mata sai dai duk abunda ke faruwa Umman bata nuna ma Baba Usman komai ba,
Ita kuma Moon d’in duk da yanda take jin jiki haka tayi ta neman Sarki a waya amma bai kunna wayar shi ba gashi kuma ita ba sanin gidan shi tayi ba balle taje ta same shi,
Wajen da suke had’uwa kuma tasan ko zaije wajen sai yamma yau kuma batama da tabbacin cewa zai yarda su had’u tunda gashi yak’i kunna wayar shima, tana ta addu’a ko baba Usman zai fita gida amma sai gashi yau tunda gari ya waye bak’i kawai yake tayi wad’an nan na fita wasu ke shigowa kuma duk in bak’in sun shigo sai ta aika kannnen ta su dubo mata,
Daga ita har umman su babu wacce ta samu nutsuwar zuciya dukan su a tsorace suke.

****
A gefen Sarki ko lafiya kalau yayi bacci a wannan rana cike da farin cikin kololuwar da zuciya ce kad’ai zata gane hakan, a yau daya fitar dake abunda ke cikin zuciyar shi akan Moon sai yakeji kamar ai har anyi angama dan haka kamar yanda ya kudurta dole a goben zai isa ga Baba Usman dan haka kwana yayi yana shawara da zuciyar shi akan shine zaije ko koh wani ya kamata ya wakilta yaje mishi ne?
To wani wa zai wakilta?
Brig, Gen, zuciyar shi ta bashi amsa,
To amma idan yaje ma brig da maganar nan hakan bai zama cin fuska ba kuwa?
Yaushe yaushe ya rabu da Meenal harda zai fara neman wani auren ga kuma Teemah ba wani lafiya take dashi ba kullum fama takeyi da kanta, kuma shi brig din fa uban matan shine,
To amma idan bashi din ba ana ai bashi da wani shak’ik’in da zai tura, kuma koda Brig baiji maganar nan yanzun ba dole zaiji zuwa gaba dan haka gara ayi ta ta k’are kawai tun yanzun yasan cewa tunda brig namiji ne zai gane halin da yake ciki,
Da wannan shawarar daya yanke ya samu bacci kai d’adi ya d’auke shi,
Washe gari ko yana k’aryawa bayan ya gama abubuwan da zaiyi ya d’auki Boy yama Teemah sallama akan zasuje Barracks,
Sun tattauna sosai tsakanin shi da Brigadier abunda bai tab’ayi ba shine yau yayi wato zauna wa ya labarta shima irin zaman da sukayi da Teemah dama abubuwan daya faru harma da dalilin rabuwar su da Meenal harda hukuncin daya yanke na k’ara aure dama yarinyar da yake son auren,

Brigadier yayi fad’a sosai akan me yasa tsayin shekarun nan shi Sarki baizo ya shaida mishi irin rayuwar dake gudana a cikin gidan shiba, ranshi ya baci sosai dan haka bai b’ata lokaci ba shi da kanshi ya shirya bayan ya amshi adireshin gidan su Moon ya kira Aminan shi mutum biyu suka shirya suka tafi dad’i kamar ya sheqe Sarki dan baiyi zaton hakan zaizo mishi da sauk’i ba,

Su brigadier sun isa gidan su Moon a wannan rana sun kuma samu damar ganawa da Baba Usman,
Bayan gaisuwa sunsha hira sosai a tsakanin su domin ashe d’aya daga cikin abokan na Brigadier tsohon Abokin Baba Usman ne wanda suka dad’e basu had’u ba hasali ma dukan su basu san cewa gari d’aya suke zaune ba dan haka sai aka shiga hira da tuna baya irin na tsofaffin abokai kafin suka gangaro kan abunda ya kawo su gareshi, wato neman iri, anan ne shi brigadier ya gabatar da kanshi a matsayin uban Sarki a kudu kuma uban matan dashi Sarki d’in yake aure ya kuma k’ara dayi mishi fashin bak’i neman auren Moon din da suke so duk da kasancewar ta yar uwa wajen Meenal,

Da yike kasancewar su maza hakan bai wani dame suba sai dai Baba Usman ya sheda musu cewa shi dai shine uban Maimoon kawai amma neman auren ta da bada shi yana hannun d’an uwan shi Ahmad ne wanda a halin yanzun kuma baya k’asar yana zaune a Saudiya ne tare da nashi iyalan,
Jin hakan sai suka rok’e shi akan ko zai basu number din waliyin natan in yaso sai su neme shi suji ta bakin shi dan sufa da zafin su sukazo,
Hakan ce ta faru domin a nan falon Baba Usman ya kira Abba Ahmad sukayi magana su brigadier suka kawo maganar neman auren da suka zo,
Shi kuma ya shaida musu cewa suyi hakuri har ya shigo k’asar a sati mai zuwa dan neman auren yarshi yafi k’arfin ace ayi shi ta waya suyi hakuri har sai yazo sai ayi komai daya dace,
A haka suka rabu kowa cikin farin ciki,
Bayan brigadier ya koma ne ya kira Sarki ya sheda mishi yanda sukayi, shima dai yayi farin ciki da jin haka koba komai yana da hope akan samun Moon din tunda yanzun maganar taje gaban Manya dan shi dai zuwa yanzun yana jin cewa bazai iya b’ata wasu watan ni masu tsoho ba tareda ya mallaketa ba,
A ranar da wuri Moon ta k’arfafa jikin ta bayan zazzabin ya d’an saketa ta fita zuwa inda suke had’uwa da Sarki sai dai kuma abun takaici haka tayi ta zama har gabannin magrib Sarki bai zoba kuma bai kunna wayar shi ba, gajiya tayi ganin dare ya kunno kai ta taso haka nan ta dawo gida jikinta a sanyaye,

Da dare yayi koda Umma tama Baba Usman magana akan bak’in daya dungayi a yau d’in a zaton ta najin ko zaice mata Sarki yazo ko wani abun makamancin hakan sam bai d’auko mata hirar ba dan ce mata yayi abokanan kasuwancin shine kawai,
Shi kuma yak’i fad’a mata gaskiya ne dan yasan a matsayin ta na mace bai zama lallai tama abun kyakyawar fahimta ba, dan haka ya yanke hukuncin gara yayi shiru har sai Abba Ahmad ya shigo k’asar zasu yanke hukuncin sannan su san ta yanda zasu shawo kan Hajiya akan maganar dan nata rikicin yasan yana gaba akan na kowa,

Daga wayewar gari zuwa dare Moon ta aikama Sarki sako mara adadi tana rokon shi akan dan Allah karyace zaije ya samu Baba Usman akan maganar nan ita bazata iya auren mijin da suka rabu da yar uwarta ba, lokaci zuwa lokaci take dubawa ko ya dawo mata da amsar sakon nin ta amma babu wani motsi har aka kwana aka hantse,
Bashi ya kunna wayar shiba sai da aka kwana biyu koda ta dana maganar kawai sai ya nuna mata ba komai bazai je wajen Baba Usman din ba har sai sanda ita da kanta ta bashi dama,
Amma fa kullum safe rana dare baya gajiya da kiranta a waya kawai dan yaji muryar ta ya kuma tambayeta ya take,
Ita kuma Umma ganin Moon din ta sake kuma shima Baba Usman baice mata komai ba sai tati zaton ko Moon ta shawo kan Sarki ne ya hakura dan haka itama sai tayi watsi da komai ta dukufa dama Moon din addu’ar Allah ya fito mata da miji na gari tati auren ta ta huta zaman gidan ya isa haka.

A gefen AK ko tun bayan barin su Meenal Kaduna bai samu zama ba a kokarin shi na ganin ya kammala komai kafin ya wuce Zarian dan yanzun shirye shiryen bikin Musty shine abunda yake gaban su,
Tunda Meenal tabar garin basu k’arayin waya ba koya kirata haka wayar zatayi k’ara harta gaji ta yanke bazata d’auka ba,
Daya fahimci horashi take son yi ta nan gefen sai ya daina kira ya koma tura mata sakon ni, shi kanshi mamakin kanshi yakeyi ta yanda yake iya zama wajen tsara tausasan kalaman soyayya masu tsuma zuciya wadanda ke fitar da gaskiyar abin dake cikin zuciyar shi ya tura mata,
Ko wani safe rana dare da kallar sakon da yake tura mata masu zafi kuma komai yakeyi in lokacin tura sak’on yayi zai ajiye ne ya rubuta sai ya tura mata ya tabbatar sakon ya tafi kafin zaici gaba da al’amuran shi,

idan kuma yana son jin muryar Meenal d’in number d’in Sultana da yasa Musty ya amsa a hannun Meelat ya tura mishi yake kira,
Ita kuma sai ta ajiye wayar a kusa da Meenal tayi ta janta da hira bayan ta d’auki wayar haka zaiyi ta saurare har sai ya gamsu zai yanke wayar,
yawan jin muryar ta da yakeyi ta wayar Sultana ba kad’an ba yake rage mishi kewar ta duk da haka Allah Allah yakeyi ya iso Zaria tunda dai har yanzun bai san me nene gaskiyar abinda yake cikin zuciyar ta akan shiba,

To itama dai Hajiyar taku a gefen ta tun tanajin wani iri a duk sanda zata ga sak’on shi har ya zamana yanzun Allah Allah take taga sak’on nashi ya shigo wayarta dan ta samu inda zata lab’e ta karanta, tsaf ta haddace lokutan da yake turo mata sakon sai dai duk rok’on da yake mata akan ta amsa mishi wato ta maida mishi amsar sak’on nashi tak’iyin hakan zata dai karanta tana murmushi amma babu amsa,
Mutum biyu sune sukafi takura mata a rayuwarta yanzun na farko Salman wanda take ma kallon tabab’b’e tun daga ranar daya wanko k’afar shi yazo har gida ita ta d’auka wani abun arzikin zai fad’a mata amma wai gayen nan sai da ya karkace ya gyara tsayuwar shi kafin ya kalli tsabar idonta ya fad’a mata wai shi dai Salman shine yake sonta kuma ma abun bai tsaya nan ba harda wani ikirarin wai aurenta yake son yi abundai kamar a duniyar mahaukata wallahi,
To dai ai ko daga dawanau ya kwato ya fito ai bai kamata ita tana matsayin matar da yayan shi ya aura ya sake ba shi kuma yazo ba kunya ba tsoron Allah yace wai shima sonta yakeyi zai aureta,
Ita wallahi bata tab’a sanin cewa k’aton mahaukaci ta dad’e tana ma kallon mai hankali ba sai ranar dan rasa amsar da zata bashi ma tayi sai kawai ta juya ta shige cikin gida ta barshi a wajen yana kwala kiran sunan ta ko waigen shi batayi ba,
Tasan in tace ta bud’e baki tayi magana a lokacin tofa tabbas tana iya lailayo k’atoton zagin da zata d’ura mishi ko kuma ta sheqe fuskar shi da mari ko ya dawo hayyacin shi, koda ta fad’a ma Sultana abunda ya faru tsakanin ta da Salman din dariya kawai tayi kafin tace mata,

“Ai na fad’a miki dama cewa sonki yakeyi amma kikak’i yarda, wallahi in kikayi sake jan ajinki yasa kika k’i yarda ki amshi soyayyar AK tofa sai dai kiji ana shelar d’aurin auren ki a masallaci bayan an d’aura,
Muko mik’aki zamuyi mu fito muna fatan Allah ya kawo yan hud’u”

“Sultana kibar wannan maganar ki barni in fama mamakin abunda gayen nan yamin,
Waini zai kalla yace yana so wato so sukeyi shida yayan shi su mai dani kwallon wasa wato yayan ya saki shi kuma bari ya kunno min kai, insha Allah ni kuma duk ranar daya k’ara shawo kayan mayen shi yazo ya k’aramin hauka sai nayi tsalle na tsatso karfi kafin in kakkafta mishi mari”

Dariya sosai sultana take mata,

“To ki yarda mana kawai tunda dai shi AK kince bakya son shi… ”

Yanke ta tayi da cewa uban wa yace miki bana son shi,
Ko ban so da aure ba ai dai shi din dan uwana ne, kuma amsa soyayyar ne ban tashi ba tukun, kece baki san halin shiba na rantse miki da allah ina sakewa nace na yarda ina son shi tofa na shiga uku kenan bani ba k’ara shakar numfashi cikin kwanciyar hankali,
Kinga wancan ustazun yayan naki da kike ganin yana matsa mana? To yasin nashi kad’an ne ni kuma yanzun bana buk’atar kowa ya takura min, kuma ai nace musu ni ba yanzun zan k’arayin wani auren ba”

Wayarta data d’auki karar kira ne ya katse mata zancen bakin ta,

“Sultana kin san wake kira?”

“Waye”Sultana ta tambaya,

“Mutumin mu na ranar nan wanda muka had’u dashi a kofar doka”

Dariya sosai sultana ta fashe dashi tana cewa,

“Sister kiji tsoron Allah kibar mutumin nan tunda ba auren shi dai zakiyi ba shima da shegen naci nayi zaton ya dena kira ai!”

“Ki barshi kawai ai inya iya naci ni kuma nice maganin shi, kin san tun jiya yake nacin wai yana son zai gaishe da Mommy tunda na hana shi zuwa gida nace sai zuwa gaba tukun,
To tun jiyan yake kirana wai in bata waya ni karan hauka ne ya cijeni dazai had’asu tab’,
Wai kin ma san me?”

“Ah ah”

“Wai tambaya na yake nawa nake buk’ata kudin da zanyi hidimar biki,”
Dariya sosai Meenal ta fashe dashi kafin ta d’aura da cewa,,

“Kibar mugun wai ni zaima gatse harda wani cewa yaji shiru ban tura mishi da account number ba kona raina abunda zai bani ne, ni kuma tunani nike in tura ko in kyale shine to gashi dai kin gani sai faman kira yake tun d’azun”

“Kawo wayar ki gani, da fari dai ki fara tura mishi account number din, idan ya tafi sai ki kira shi kice mishi Mommyn bata kusa ne amma gata ni kuma zan gyara muryata irin ta manya sai inyi magana dashi a matsayin Mommy muci kudin banza wallahi”

“Allah dai yabar min ke My Namcy bari ki gani yanzun kuwa zamu gabatar da komai kamar yanda muka shirya”
Amsar wayar tayi ta fara tura mishi account number d’in sai da ta tabbatar da cewa ya isa tashi wayar kafin ta danna mishi kira,
Ita kuma Sultana tana gefe sai faman gyara murya take dan ko kad’an bata son su kwafsa, tsun tsune fa suka samu daga sama gasasshe dan haka ai suci rabon su kawai,

Din din din karar da wayar keyi kenan alamun dake nuna wayar na ringing tacan gefen,
Yanke wayar akayi cikin kankanin lokaci ya maido da kiran zuwa wayar Meenal d’in,

“Ke gashi yana kira wallahi” cewar Meenal tana nuna ma Sultana,

“To ki dauka mana kar kiran ya yanke kuma”

” Assalamu Alaikum hello” ta ambata bayan ta daga kiran sai ta danna wayar a speaker,

“Ameen Alaikis Salam Baby girl barka da war haka ya kike?”

“Ina lafiya Yallabai, dama nace bari in kirane in had’aku da Mommyn kamar yanda ka buk’ata”

“Ok ok aiko kin kyauta naji dad’i sosai ki bata wayar to”

“Ok Mommy gashi zaku gaisa”
Cewar Meenal tana tura ma Sultana wayar,
Gyara muryar ta Sultana tayi sosai ta yanda ya koma kamar na Babban mace ba kuma na tsoffi ba ta rik’e wayar a hannun ta tana cewa,

“Wanene kuma zaki had’ani dashi Yar Malam keda ko maganar samari bakya son ana miki a gidan nan wani kai sa’an ne wannan?”
Ta tambaya kamar irin bata san shi na cikin wayar yana jin me take cewa ba,

“Ni dai Mommy gaisawa kawai zakiyi dashi bance kice mishi komai ba atoh dan so nike sai mun k’ara shakuwa kafin in gabatar dashi kuma ke kad’aice ma yanzun zan had’aku”

“Haba Meenal ko baki fito fili kin fad’aba ai nasan kina son shi Allah yasa dai ya rik’e min ke da amana kema kiyi auren nan dai”
Sultana ta karasa fada kafin tace,

“Assalamu Alaikum”

“Ameen Alaikum Mama ina wuni”

“Lafiya lau d’an nan ya gida ya aiki da wajen iyayen ka dafatan duk kuna lafiya?”

“Lafiya lau Mama ya lafiyan jiki?”

“Alhamdulillah d’an nan ya rayuwa? Sannu kaji naji dad’i sosai wallahi Allah dai ya maka albarka yasa ka gama da iyayen ka lafiya, Allah yayo jagora kaji, nagode kwarai da gaske”

Shi kuma acan gefen shi amsa addu’ar nata yake tayi da “Ameen Ameen Mama nagode, ina dai ta rok’enta akan ta bani dama inzo gida in gabatar da kaina shi yasa nace ta baki wayar muyi magana ko zaki sa min baki ta amince”

“Ayah ayyah indai wannan ne ai karka wani damu kanka,
Tunda har ta had’ani da kai nasan ba k’aramin so take maka ba dan haka ka kwantar da hankalin ka abi komai a sannu dan nidai ka riga ka samu goyon baya daga gareni ban ganka ba amma sosai na yaba da hankalin ka”
Hira sosai Sultana tayi da shi a matsayin itace uwar Meenal kuma tayi na’am da soyayyar da yake ma yarta kafin su kayi sallama sai da ya fad’a mata cewa zai tura ma Meenal din sak’o yanzun sai ta siya mata goro,

Ita ko harda wani cewa “ayi haka d’an nan daga gaisuwa kuma sai ka fara dawainiya tun yanzun, to andai gode Allah ya k’ara bud’i”
Sosai ta dunga kwarara add’u’a shiko sai dadi yakeji irin a dole ya samu k’arbuwa a wajen uwar budurwa,

Bayan wayar ya koma hannun Meenal ne kuma ya k’ara tabbatar mata da cewa zai turo da sak’o dan Allah tayi k’ok’ari ta fita ta siyo ma Mommyn abunda tasan tana so wanda zai faranta mata rai,
Shi baya gari yanzun haka amma yana fatan idan ya dawo zaici arzikin da zata bari yazo ya kawo gaisuwar shi na musamman a wajen Mommy,

Lafiya lau sukayi sallama tana mishi godiya, suna yanke wayar ita da Sultana suka fara dariya kamar wasu tab’abb’u,

“Ke tashi fa muje in tayaki ki had’a kayan ki dan Wallahi yau ban k’ara kwana a gidan nan kafin wancan mahaukacin Salman d’in anjima ya k’ara dawowa,

“Ah zauna tukun muyi magana inji nawane nawa kason idan kud’in suka shigo mana”

“Dallah can ai dai kya bari harya turo kafin muyi kasafi”

Sultana ta bud’e baki zatayi magana kenan idonta ya hango mata Sheikh dake tsaye daga bakin kofa hankalin shi kachokam yana kansu,
Fuskewa tayi kamar bata ganshi ba ta d’auki wayar Meenal ta shiga da sauri ta goge number din mutumin daga jerin kira ta shiga cikin message ma ta goge message din da suka tura mishi na account number sai zufa take had’awa dan tasan yau su kuma sai ta Allah fatan ta dai allah yasa Sheikh baiji hirar su ba Allah yasa yanzun ne ya iso wajen bawai tun d’azun ba,

Ta yunkura zata bar wajen shi kuma ya k’araso fuskar nan kadaran kadahan bazaka iya tantance halin da yake ciki ba,

“Koma ki zauna”
Ya fad’a kai tsaye,
Sai lokacin Meenal ta d’aga kai ta kalle shi,

Zaman Sultana tayi kamar yanda ya buk’ata tana mik’a mishi gaisuwa bayan tayi kokarin boye tsoron dake cikin zuciyar ta,
Gaishe shi itama Meenal ta mik’a hannu zata d’auki wayar ta da Sultana ta turo mata yakai nashi hannun ya d’auki wayar kafin ya samu waje ya zauna,
Wayar bata da matakan tsaro dan haka kai tsaye call long ya fara dubawa sai dai ga mamaki babu wata number wanda akayi kira da ita yanzun dan number din dake wajen duka wad’anda aka amsa kira dasu ne tun na jiya ya gane hakan ne a sanda ya duba lokacin kiran,

“Dawa kuka gama magana a waya yanzun?”
Ya tambaya yana tsatstsare su da ido,

Shiru sukayi kafin Meenal ta d’ago kanta suka had’a ido da Sultana kafin ta maida duban ta kanshi ita din shima yake kallo.

“Uhumm ku nike saurara kuma karku sake kumin k’arya inba haka ba saina b’ata muku rai”

Yana rufe baki ko numfashin kirki bata bari ya sauke ba ta amsa mishi da cewa,

“Bazawari nane ya kira, ya buk’aci in had’ashi da Mommy ni kuma ban shirya gabatar dashi ma kowa ba shi yasa na had’ashi da sultana”
Ta fad’a irin ko a jikin ta, tunda yace kartayi mishi karya ai dama ko baice ba gaskiyar zata fad’a tunda dai tasan bashi da wuta ko aljannar da zai saka ta,
In ya iya takura ita tayi zama ma da wanda magana d’aya biyu zakiji yace “sai na zane miki jiki, saina mareki, sai na karya k’afarki”
Kuma har yanzun ya kasa aikata ko d’aya balle kuma shi Sheikh d’in.

Babu editing

*UMMIEE CE*โœ๐Ÿผ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button