Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 24

Sponsored Links

โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{Ummiee Zaria}~*

*Page 24*

Yo Allah na tuba kai yanzun nan harma dan wata mace tace bata sonka har zaka wani d’aga hankali ka damu kanka bayan ba masoyan ka rasaba?… ”

“Hajiya bafa cewa tayi bata sona ba, kin san bai yuwuwa daga fad’a mata cewa ina sonta ta amsa min dai take a lokacin”

“Koma dai yayane kawai ka fita sabgarta taje can ta k’arata da yawarta ita tayi ma kanta dan nidai banga abunda ka rasa daga cikin abunda ake buk’atar samun mijin aure dashi ba tunda ko kaga bata amsa maka ba son kane batayi gara ma haka wallahi dan
Kaga ni dama gata naso in maka kana gani dai gashi nan abokan ka sai harama suke shi dama Yusufu tuni yayi muku fintinkau dan haka indai zakaji ta nawa gara kabar batun yarinyar nan kawai kazo ga wata matar Allah ya kawo na fidda maka ita ka aura,
Gata kuma yar gida sannan na yaba da nutsuwa da hankalin ta kaga idan ka auri wannan d’in ita waccen yarinyar da kace kana so d’in ko zuwa gabane in Allah yasa ta amince sai kayi ta biyu da ita ko ya kagani?,
Dan nidai dama bana maka sha’awar zama da mace d’aya wallahi,”

Yunk’urawa Meenal tayi da niyyar tashi tabar musu wajen, shi kuma yaja hannun ta dake rik’e cikin nashi ya maidata zaune ya kuma maida hannun nasu dake had’e kan cinyarta ya danne saboda ya hanata mik’ewar ,

“Ke kuma ina kike shirin zuwa? Ai gara ki zauna dan dama ina gamawa dashi kanki zan dawo atoh bawai na manta dake bane,
Nace har yanzun duk wannan uwar wankan da fesa turaren da kikeyi a kullum kafin ki fita kar dai kice min asarar ruwan wanka da sabulu kikeyi kullum?,
To ga dai lokaci yana ta tafiya amma har yanzun ban fara ganin manyan motoci suna jera min layi a kofar gidaba,
Anya kuwa Yar wajen Jidda ba amanata kike ciba kuwa wajen k’in kula samarin da suke nuna ra’ayin su a kanki?
Naga dai ko shekarun baya a lokacin da kike kwailar ki ma maza sun nuna maitar su a kanki yanzun kuma da kika koma tubarkhallah maka Allah sai inji shiru, to wai in baki basu damar zuwa gidanba ta ina zan iya tantance su wajen gano miki wanda ya cancanci auren ki a cikin su?”

AK ya katse Hajiyar da cewa..

“Hajiya, amma dai na roki arzikin ki akan abar maganar nan koh?
ba komai amma tunda kin matsa bari in fito miki a mutum!,
Ita dai yarinyar da kike magana a kanta koma wacece bana buk’atar ta a cikin rayuwata, akwai maza da yawa a waje wad’anda suka fini quality da komai ma da kike ganin ina dashi, ni kuma ina mata fatan Allah ya had’ata da d’aya daga cikin su wanda zai sota har zuwa k’arshen numfashin su,
Batun wai in fara auren ta ko wani zancen mata biyu da kike kawowa ina so ki soke shi in ma a mafarki kika gani ina tabbatar miki da cewa bazai tab’a tabbata ba domin bana da ra’ayin su,
Naga dai kema naki mijin dake kad’ai ya rayu har zuwa karshen rayuwar shi, suma kuma yaran daya haifa har yanzun kaf cikin su banga wanda yayi mace sama da d’aya ba, oh sai nine kike ganin nafi kowa a cikin jikokin ki da kike kiran min auren mata biyu, Hajiya so kike ranar kiyama in tashi da shanyayyen gefen jiki ko ya?
Kedai kin san cewa bazan tab’a iya adalci a tsakanin abunda na gani ina so da kuma wanda nayi alfarmar amsa saboda an cusa min ita ba,
Aure dai ina kike so kiga nayi?
To in hakan ne gata d’aya nike so kimin wajen tayani yak’in kwato abunda nike so d’in har zuwa sanda zai zama mallakina,
Yar gida wanda kika san halinta kuma kika yaba da tarbiyar ta kike min sha’awar aura koh?
To gata ayau a yanzun zan gabatar miki da ita batare da b’ata lokaci ba nidai na riga na gabatar da kaina a wajen ta, Ina son ta ina kuma fatan in mallaketa ta zame min matar rufin asiri,
Gata nan zaune a gaban ki dan haka sai ki yanke hukuncin daya dace domin da ita dani dukan mu tarbiyar kine babu wanda baki san halin shiba a cikin mu,”

Mikewa yayi tsaye sannan ya d’ago meenal d’in tsaye itama,
wacce zaune kawai take amma ji takeyi da da ace tana da wani layan zanan da zata latsa tayi b’atan dabo a wajen da tayi saboda tsaka mai wuyar da take ganin su biyun sun jefata a ciki, wannan ai ita akama turke wallahi.

“Meenal meet my grandma Hajiya ta itace gatana tun ban san kaina ba, duk wani matakin nasarar da nataka a rayuwata zuwa yanzun da gudun mawarta na same shi,
Ina fatan zaki kula min da ita fiye da yanda nike kula da duk abunda ya shafeta bayan auren mu?”

Hijjabin dake sanye a jikin Meenal d’in taja da duk’unkune kanta gaba d’aya a cikin shi saboda tsabar kunyar daya lullub’eta,

“Hajiya ga Ameenatu takwarar ki, zanyi amfani da wannan damar dana samu wajen gabatar miki da ita a matsayin macen da zuciyata ta zab’amin wacce nike fatan in k’arasa sauran rayuwata a tare da ita k’ark’ashin inuwar aure, Ina fatan zaki tayani yak’in neman amincewar ta akan maganar auren mu,
Domin kamar yanda na shaida miki ne, na riga na gabatar da takardar barar soyayyata a gareta amsar ta kawai nike da buk’atar ji a yanzun wanda shine zai bani kwarin gwuiwar takawa zuwa mataki na gaba wato gabatar da kaina a wajen iyayen ta a matsayin mane min auren ta,
Hajiya Ina sonta, so irin wanda ban tab’a zaton zanyi ma wata y’a mace shi ba,”

“Sadaqallahul Azeem! Allahu akbar ! Allahu akbar!
Allahu akbar,,,
Ashe ni Aminatu zanga wannan ranar a raye tun k’asa bai rufemin idon ganiba,
Oh oh Allah Sarki duniya… ”
Batakai k’arshen surutan da takeyi ba ta fara sheshek’a tana shirin fashe mishi da kuka,

Daga can cikin falon ko su Meelat da tun d’azun suka kashe kunne suna sauraron tattaunawar nasu, Sultana ce ta matso kusa saida ta k’arasa inda Hajiya take kafin ta tak’ark’are ta rangad’a gud’a uwa wacce ke taryar Amarya,

“Ayyiriri yirie yiriii yirrrriiieee dukan su suka had’u suna yarawa,
Hajiya dake sheshekar kuka basai gata itama ta biye musu suna rangad’a gud’ar atare dasu ba,

Da baya ya koma ya shige d’akin shi ya barsu a falon dan shifa tsakani da Allah ya manta cewa ba iya su bane kawai a gidan akwai wasu ukun a gefe tare dasu,
Sai dai ko kad’an baiji kunya ba shi a zuciyar shi ma dad’i yaji dan yasan suma zasu sa baki tunda a gaban su akai komai,
Suko yana shigewa suka zagaye Meenal d’in data d’uke kanta dake duk’un kune cikin hijjabi akan table din dinning d’in tak’i d’agowa balle su samu damar ganin yanayin fuskarta,
Basu damu da yanda tayin ba suka cigaba da tsokanarta da cewa,

“Allah yabar mana jikar Hajjaju sirikar Hajjaju, zaman ki lafiya tashin ki lafiya yar gaban goshin Malam…

Hajiya ce ta matso tana katsesu da cewa

“ku matsa ku bama sirikata waje karku samin ita a gaba da tsokana, yoni ina nasan cewa kanshi yake ma kiwo ashe!
Niko nike ta k’okarin yi mishi shishshigi, to ke Sultana kin daiji komai dan haka sai kija please ki rungumi sorry kiyi fatan Allah ya baki wanda ya fishi d’in kamar yanda shima ya rok’a miki, dan tunda ya iya kallon tsabar idona yace min ita yake so tofa bazai tab’a amsar naki soyayyar ba,
To amma Takwara haka ake rayuwa ayi ta abubuwa bani da labari ko dai da gaske bakyason shi d’in ne shi yasa kika kasa amsawa?
To bari kiji in baki shawara na gaskiya da gaske, dan ma karkice shid’in jikana ne shi yasa nike son taya shi yak’i ah ah wallahi ko d’aya dan kin sani duk wanda naga yana shirin yi miki dole akan auren wanda bakyaso sai inda k’arfina ya k’are,
Amma shi dai tsakani da Allah zan fad’a miki idan har kikayi saken daya kucce miki tofa ba lallai bane ki samu mafiyin shi ko kuma wanda ya kaishi,
Amma kinga in shine babu ta inda zanji fargaba dan na bashi auren ki domin dai dake dashi duka ina da iko daku kuma nasan bazai tab’a miki rik’on sakainar kashiba tunda yana sonki,
Na tabbata cewa yana sonki naki so na hak’ika tunda har ya iya gabatar dake a gaba na yanzun, bazance ki amince mishi dole ba,
Sai dai koda ace a yanzun bakya jin komai akan shi zan so ki bashi dama ko allah zaisa ki soshi d’in zuwa gaba, ni kuma na miki alkawarin inhar bakiji cewa kina son shi har cikin zuciyar kiba to bazan yarda kowa ya matsa miki cewa sai kin aure shi dole ba, wannan alkawarina ne kuma ku tayani sheda”
Ta k’arasa fad’a tana kallon su Maryam,

Insha Allahu kuwa zamuyi shedar ki Hajiyar mu, suka had’a baki wajen amsawa,

“To amma Hajiya ai Sultana tana son shi!”
Meenal ta fad’a batareda ta d’ago kanta ba,

“Ke Sister ni wallahi ba dagaske nike yiba inma dan abunda kikaji na fad’ama Hajiya jiyane to kisa ranki a inuwa Ya AK naki ne ke kad’ai, ina tayaki murna ubangiji Allah ya sanya alkhairi sai dai dan Allah karkija mana aji ki bada gari kawai musha biki a wuce wajen”

“Ni bazan auri mijin da tun baiyi auren farko ba kakar shi ke fad’in cewa tana mishi sha’awar auren mata biyu ba”
Ta k’ara fad’a tana juya kanta da har yanzun bata d’ago shi daga kan table d’in ba,

“Ah ah ha, Allah ya tsareni yi miki fatan zama da kishiya wallahi,
To dai koni da nike matsayin kakarki mijina har ya kwanta dama bai tab’a ambata min sunan kishiya a cikin gida ba,
Kuma dai har yanzun kina jin shima Yayan naki abinda yace dan suma dai nawa yaran babu mai kishiya a cikin su har yanzun, to wani mugun abun ne ni kuwa zaisa in so miki zama da kishiya yar nan!
Kwantar da hankali indai wancan ne Allah ya nufa zai zama mijin auren ki ina tabbatar miki da cewa kishiya sai dai ki gani a mak’ota ko baki lura da d’abi’un shi bane kaf nasara sun gamayin tasiri akan shi… ”

Meelat dake dariya ne ta katse Hajiyar da cewa,

“To Hajiya mai yasa wancan lokacin baki hana auren ta da Sarki ba bayan kun san yana da mata?”

“Yanzun yar nan har kya tambayeni dalilin wannan aure?
Yo shi wannan auren yana da dalilin da za’a danganta shi dashi ne bayan k’addara, ke dai ki bari kawai Allah dai yasa kaffara ne ya bata ladan zaman kuma, gashi dai tun ba’aje ko ina ba Allah ya mata canji na alkhairi ai ni wannan abu koshi uban gayyar bazai fini farin ciki ba allah dai ya kaimu lokaci,”

Da ameen dukan su suka amsa sunaci gaba dayi ma Meenal din tsiya,

Daga nan gidan AK unguwan dosa suka wuce kai tsaye domin sun Riga sun gama cinye lokaci a gidan dan basu suka fitoba sai karfe 10 saura sakamakon hirar daya d’auke musu hankali,
Hakan ne kuma ya shashantar da batun zuwa marafa dubo gidan AK da sukaso zuwa.

An gabatar da addu’ar kwana uku ga mamacin lafiya, tun daga nan kuma bak’in da suka zo saboda a gudanar da addu’a dasu suka fara juyawa suna komawa gidajen su, wad’ansu yan garine wasu kuma bak’i,
Yan zaria ma dai da yawan su sun koma Malam yayi magana akan komawar Raheenat gida idan yaso sai ta k’arasa wankan ta a can, amma kuma sai iyayen Mamacin wad’anda a gidan suke zaune suma suka rok’i alfarmar abarta a gidan har zuwa sanda zata gama wanka in yaso sai ta koma gidan tunda dai ita ba takabar mutuwar zatayi ba sakamakon haihuwar da tayi,
A haka aka rabu sai dai anbar mata Innar yara da kuma wata mace yayar Aunty Murja sune zasu zauna da ita yaranta biyu kuma dama Babban da mai bi mashi tun kafin rasuwar mijin nasu rik’on su ya koma hannun kanin mijin da matar shi da suke zaune a Abuja wad’anda Allah bai basu haihuwa ba,

A lokacin da duka ahalin suka fito da niyyar tafiya ne Meenal ta gabatar musu da sabuwar Motar ta da AK ya bata dan Farouq ne da yake ta ganin tana zirga zirga da motan a yayin zuwa gidan rasuwar yau ya gaji yake tambayar ta, ina ta samo d’anin mota,
Hajiya ce ta ceceta ta bashi amsa da cewa,
“Yayan ta ne ya bata ita tunda shi ya tara su da yawa baya hawa, sunyi mata Allah sanya alkhairi kafin suka kama hanyar komawa Zaria daga garin na Kaduna.

*BAYAN WASU KWANAKI*

Kamar yanda Sultana tace wajen Meenal zata sauka hakan ne ya faru domin sati d’aya kacal sukayi a unguwar Malamai family house shima dan kunyar da Meenal takeji na Hajiya ne yasa ta yanke hukuncin su sauka a can d’in ga kuma yan uwan su na kano da mutanen Abuja wad’anda suke gidan har yanzun basu koma ba,
Matan auren ne kawai Malam ya kora gidajen su washe garin ranar da suka dawo daga kadunan,
A kuma ranar da suka dawo Baba Adamu yayi amfani da wannan damar na had’uwar ahalin waje d’aya wajen had’a kan ahalin kwansu da kwarkwata ya k’ara ja musu kunne akan kulla da zumunci dan kar suga cewa basa gari d’aya suce zasu yarda zumuntan dake tsakanin su da sauran yan uwan su da suke zaune a wani wajen ya lalace, dukan su sunji dad’in wannan zaman domin anan suka k’ara sanin juna suka tantance wannan shine wane d’an wane yana zaune a waje kaza, sun kuma yanke hukuncin bud’e WhatsApp group wanda zasu cigaba da zumunci a ciki da tattauna abunda ya shafesu a cikin shi dan haka sai da sukayi exchanging numbers din junan su kowa ya ajiye number din dan uwan shi a wayar shi.

A kuma wannan zaman na kwanaki da Meenal tayi a gidan ne suka fara yar tsama da Yayan su Naseer wato yayan Sultana wanda kowa ke kira da Sheikh,
Abu na farko daya fara had’asu shine irin yanda tana malam yana nan nan dashi,
Magana d’aya biyu zaice a kira mishi Sheikh,
In dare yayi koda zataje cin abinci wajen Malam d’in kamar yanda suka saba a baya zata iske shi Sheikh din a hakimce a falon ko yana duba littafai ko kuma yana yin wani abun mai mahimmanci,
Tun ba’aje ko ina ba ta fahimci cewa ba k’aramin kusanci ne tsakanin Malam dashi Sheikh din ba dan haka tuni kishin ta ya motsa da gayya wani lokacin idan ta shigo falon taban shi zaune kuma malam baya nan sai tak’i gaishe shi tayi komawar ta, dan a farko in tazo ta kan zauna ta jira malam shi kuma na bakin ta da iyayen shi a wannan zaman zaiyi ta jefo mata tarin tambayoyin shi da basa k’arewa, abun haushin kuma bazai tab’a zama da kai kuyi hira dashi na minti goma da yaren hausa ba,
Ah ah magana d’aya biyu da kun fara dashi zai fara sako mata runkuma runkuman labarcin shi badan Allah yasa Malam yayi tsaye a kanta tun tana k’arama wajen ganin ta iya larabcin ba lallai da ba k’aramin kunya zata shaba,
To fisabilillahi larabcin nan dai tunda ba yaren da aka haifi mutum dashi bane ai sai ya tsaya a iya nashi yaren koh?
To shi da gaske so yake sai yakai k’arshen nata larabcin da take riritawa, to jama’a ita dake karatun likitanci yare nawa ake son ta rik’e ne?
Kuma dan wulakanci ko turanci kake mishi shi bazai tab’a amsa maka ba sai ma yayi uwar shegu dakai kamar bai san me kake cewa ba,
Da farko tayi zaton ko turancin ne bayaji sai daga baya data tambayi Sultana shine take ce mata wai ai Ya Sheikh yana jin yare sama da goma saboda k’asashen da yake karatu duk yanayin yaren su,
Ita kuma tun ranar sai ta kuduri aniyar cewa sai ta rama wallahi, dan haka koya mata magana da larabci ita kuma sai ta maida mishi da yaren hausa,
Daga baya sai ya tsiro musu da karatun safe dana dare,
Da zarar an idar da sallan asuba dana ishsha’i duka yaran gidan zasu taru a falon Malam ayi karatun,
Taso ta doje tak’i zuwa amma ba hali dan Mommy Hauwa da kanta take korata dan da ita ake karatun,
Amma wai duk yawan yaran gidan nan d’an bawan Allahn nan idan ya tashi jefo tambayan shi bazai jefa akan kowa ba sai a kanta ita marainiya wayon shi salon in bata amsa dai daiba yasa yara su rainata,
Dan haka dan dole ta zak’ulo littafan ta da suke karatun tare da baba malam a shekarun baya tana musu maraji’a gudun kar a samu bacin rana aji kunya,
Abu dai kamar wanda ya asirce ahalin gaba d’aya domin kowa zancen shi shine ya sheikh,
Ya sheikh kaza ya sheikh yayi kaza, dan haka kowa ma a gidan ya fara bata haushi,

Wata rana sun shigo gidan ita da Sultana daga gidan su Meelat suke domin tunda suka dawo suke cigaba da gudanar da shirye shiryen bikin su babu kama hannun yaro,
Har sun gota parking lot d’in gidan ta jawo Sultana suka dawo daga baya sakamakon Muryar Sheikh da taji cikin harshen turanci yana magana a waya,
Sun dade tsaye a wajen tana k’ara sauraren yanda yake fitar da lafiyayyen turancin yana kuma had’awa da wani yaren da bata san ko na wani k’asa bane,
Ita dai Sultana da taga tsayuwar bamai k’arewa bane gashi kuma ita fitsari ya matse ta kawai sai tayi wucewar ta ciki tabar Meenal d’in a wajen,

Nauyin ido yanaji ya mishi yawa ne yasa shi kuma ya yanke wayar ya juyo dan yaga waye a wajen,

“Me kikeyi anan?”
Ya tambaya da harshen larabci kamar yanda ya saba,
Ita kuma sai ta amsa mishi da turanci cewa,

“Kallon ka nikeyi mana ina kuma sauraron ka kana turanci bayan kuma ni kullum idan nayi maka magana da yaren nuna min kakeyi kamar bakajin me nake cewa”

Murmushi yayi kafin ya taso daga inda yake ya matso kusan ta sai da ya gota ta kafin yaci burki, bai juyoba ya amsa mata da cewa,

“Yaren turanci ba shine yaren da zamu tashi dashi bayan mutuwar muba, shi yasa sam baya burgeni”

“To amma kuma ai gashi nan naji ka iya sosai kanayi kamar a cikin su ka rayu!”

“Ke da kika iya kikeyi a cikin su kika rayu ne?”

“Ah ah ta bashi amsa tana girgiza kai,

“Ok niko kinga a cikin larabawa na rayu shi yasa na iya yaren su, kuma ko ba komai ai yaren shugaban annabawa ne koh?”

Yana gama fad’in hakan yayi gaba abinshi ya wuce ya barta a nan tsaye tana binshi da kallo cike da burgewa,

Malam daya shigo tun d’azun tsayuwar Sheikh din ya hanga a kusa da Meenal k’arasowan shi inda suke hakan yasa yaji duk abunda suka tattauna sai shima yaji Sheikh din ya k’ara daraja da kima mai girma a idon shi koba komai dai gashi duk tarin ilimin bokon da yake dashi hakan bai sa ya yarda yaren addinin shiba.

 

Wallahi babu editing kwana biyun nan rubutun kawai nikeyi, kuyi hakuri da mistakes

*Ummiee ce*โœ๐Ÿผ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button