Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 66

Sponsored Links

66

Kamar yadda ya zame mata al’ada,duk sanda ya fita aiki kafin ya dawo ta kammala komai da tasan zai iya buqata,kama daga tsaftar gidanta dama gwanace,zuwa kwalliya wanda shima wannan ba sabon abu bane a wajenta,har abinci da ruwan wankan da zai iya buqata.

Yau dinma haka ta fito zuwa falon nata daya wadata da qamshi,tayi kyau cikin wata fitinanniyar mai zubin straight gown,saidai tsahonta iyakarsa qauri,ta daure kanta da band kalar kayan,sai qamshi da sheqi gashinta yake.

Wayar jawahir take amsawa,suna magana ne kan wasu taruruka da sukayi order wadanda suka iso,suna hannun jawahir din,tace zuwa gobem idan ta samu ya samir din ya barta,zata leqo ta karba,idan kuma yaqi ta aiko koda yaron gidanta ne,don samir din wani mugun boyonta yake,kishinta yake kamar me,hatta da abokansa bai yarda ya shigo dasu gidan ba,musamman idan kaima ba da iyalinka kake ba,yafi ganewa su gama sabgarsu da kai a office,idan ta kama zakazo gida kuma ku tsaya daga daya daga cikin falukan da aka tanada daga can wajen saboda baqi,ki wajen shan iska dake cikin gidan.

Wayarta ta jona charge sannan ta dawo ta zauna saman kujera,idanunta kan tv tana niyyar sauya tasha,saboda nan din news sukeyi.

Kamar da wasa aka nuno wani mummunan hatsari daya faru daga kano zuwa kaduna,saiga fuskar hajiya shuwa ta bayyana,hannu da qafa sun fashe babu kyan gani,daga gefanta kuma fawwaz ne,wanda ko motsi ma baya iyayi.

Maimaita sunan Allah take tana girmama girmansa isa da buwayarsa,duk da bata musu wani farin sani ba amma abun ya tabata,ta canza tasha tana rayawa a ranta,wala’alla sauran haqqin mutane dake bisa wuyansu ne ya musu haka.

Tana jin tsaiwar motarsa ta daga kai ta kalli agogo,murmushi ya subuce saman fuskarta,baya saba lokaci,ta godewa Allah da ya bata mijin da bai iya yawon dare ba,bai kuma san zaman majalisa ba,daga gurin aikinsa sai masallaci sai gidan,idanma zaya fitan to tare zasu su dawo,idan kuma ya fita shi kadai,to momma ko daddy,ko hajiya qarama keson ganinsa,da ya gama kuma zai dawo gidansa,itace abokiyar hirarsa,itace abokiyar sirrinsa,da ita kadai yake hira yaji ya gamsu,a yanzu takarbe wani kason matsayi mafi girma na amirun,kamar yadda jawahir ta karbe na samir din a wajen amiru.

Bata iya barinsa ya tsaya jiranta tazo bude masa qofa,don haka kamar ko yaushe yana zuwa yake shigowa,tana kuma tsaye tana jiran gama shigowarsa,saidai wannan karon kafin ta maida qofa ta rufe ya sureta yana juyi da ita,ta qanqameshi saboda yadda yake hajijiyar da ita,ya dakata ya sauketa yana qare mata kallo daga sama har qasa.

Hakan yayi mata dadi sosai,bai taba ganin wani abu tattare da ita ba tare daya yaba ba,ita kuma abinda ke qara mata qaimi da zaburar da ita wajen ganin tayi dukkan abinda tasan zata burgeshi,don haka saita fara juyi a gabansa,yaga ko ina kenan gaba da baya

“Wayyo haske na,zaki kasheni da raina….wannan kwalliyar na siyeta…..akwai biya mai daraja da zan miki…..saidai kafin sannan,na manta banyi sallama ba” da murmushi ta bishi,baya yadda ya shigo ya zauna baiyi sallama ba,saboda duk magidancin daya aikata hakan,a ranar shaidanun da suka biyoshi sun samu wajen kwana da kuma inda zasu ci abinci,amma matuqar ya yiwa iyalinsa sallama,to zasu dakata,su gayawa junansu cewa a yau dai cikin gidan basu da abinci basu da wajen kwana.

“Amincin Alla ya tabbata a gareki ‘yar aljanna” da wani qawataccen murmushi take takawa har inda yake tsaye,ta miqa hannu ta amshi jakar hannunsa,tabar masa envelop din kawai

“Amincin Allah ya tabbata a gareka dan aljanna” saiya tako ya shigo falon,ya sake jawota gareshi,sannan ya miqa mata envelope din hannunsa,ya mata signer akan ta buda.

Wani tsalle ta saki da qaramin ihu ta daneshi sosai bayan ta gama dubawa,sai kuma hawaye ya balle mata

“Ashe da gaske mafarkina zai tabbata?,ashe zan iya zama qwararriyar artch?”

“Definitely…..” Ya amsa mata cikin bata qwarin gwiwa,saita rasa bakin magana,ta kifa kanta a qirjinsa ta sanya masa kuka.

Wata makaranta ce ta musamman ya samar mata a wajen qasar nan,wadda babu ta biyunsu a universities da suke da qwararrun malaman dake koya course din,private uni ce,mai tsadar gaske,wadda bata taba kawota cikin kanta ba.

Sulalewa tayi qasa saman gwiwoyinta zata fara gode masa,sai ya dakatar da ita,ya dagata yana cewa

“Wannan godiyar marowata ce,ba kalar godiyar da nakeso ba kenan”

Cikin murya me sautin kuka tace

“Ka fadi kome kakeso,zan sadaukar maka dashi” matsawa yayi jikinta ya saka bakinsa a kunneta ya rada mata wani abu.

Wani dan ihu ta saki na jin kunya,tana fidda idanunta waje,ta juya da sassarfa ta wuce zuwa dakinsu,yana dariya shima ya rufa mata baya,yana jinta can cikin bargonsa.

*******Babban dakin taro ne wanda ya cika maqil da jama’a,saidai kuma duk da yawan jama’ar hakan bai hana wajen zama cikin tsari da doka ba,kowanne mutum na zaune a mazauninsa,hakanan kowa ya bada hankali kam stage din da ake gudanar da taron.

Kallo daya zaka yiwa wajen ka fuskanci taron yafi kama da taron yaye dalibai,fararen fata sunfi yawa kamar yadda yake qasarsu ne,sai tsilli tsillin baqar fata,wadanda sukunin rayuwa da huwace ta ubangiji qaddararsu ta zartar da yin karatunsu cikin jami’ar.

Taro ne da akayishi saboda miqawa daliban da suka kammala karatu a jami’ar wasu watanni da suka shude shaidar zama cikakkun artchecture,wadanda zasu iya aiki da kowanne kamfani a fadin duniya,sannan kuma an yarda da ingancinsu da kuma qwarewa da gwanancewarsu,bayan sun gabatar da jarabawa ta musamman.

Cikin lanqwasashen harshensa baturen ya kira sunan
“Ummu_kulsum ahmad” da wani irin sauti na rashin cikakkiyar hausa.

Shuru wajen ya dauka,kowa na dakon fitowar dalibar data ciri tuta,ta kuma zo a sahun farko.

Nima da kaina sai dana waiga sanda na fara jin takun takalmi cikin nutsuwa da aji,can na hangi wata mace chocolate color skin,sanye da lallausar atamfar England ruwan sararin samaniya da torches na ash a jiki da dark orange,dinkin riga me dogon hannu da plain zani,ta nannade jikinta da laffaya ta alfarma itama ruwan sararin samaniya.

Daurin da tayi ya sake qawata fuskarta matuqa da gaske,saboda yaddda ta kawo daurin goshi,ta kuma nannade gashinta samfurin nannadewar doughnut ta baya daga qasan daurinta.

Wuyanta sanye yake da wata siririyar sarqar gold me kama da chine na sarqa,saidai kuma akwai wasu qananun qulalai a jiki,iri daya da dan kunnen kunnenta abun hannu da kuma zoben dake yatsanta,kyawawan sexy eyes dinta saye cikin farin gilashi,wanda zaka iya ganin qwayar idanun nata tar,sosai Glass din ya qara qawata mata adon ya kuma qara mata kwarjini.

Daga qafarta kuma highshoes ne,wanda yadan qara mata tsaho kadan,daga baya da bayansa ana daureshi da wasu irin igoyoyi masu kyau,wanda suka dace doguwar qafarta,jikinta na bada wani ni’imtaccen qamshin humrori na jiki dana gashi da kuma turaren kaya duka na kamfanin YERWA INCENSE AND MORE,qamshi me nutsar da zukata da sai ka kusantota sannan zakaji tashinsa.

Daga gefanta kuwa the giant saraki ne saqale da hannayenta,murjajjen matashi,wanda ilimi hankali nutsuwa suka jiqashi,gefe kuma sassanyan kyau wanda baiyi yawan da zaka ganshi yana doso ka ba,saidai kuma baiwar kwarjini da Allah ya bashi,wanda ke firgita zukatan mata da sanyasu daka.

Sanye yake cikin wasu suit da sukayi shige da color din kayan jikin rayuwarsa UMMUKULSUM,sun dace shima da jikinsa,kamar don shi aka samar dasu.

Har yanzun yana nan da tsahon nan nasa,don kuwa….duk da takalma masu tsinin da kulsum ahmad ta sanya iyakacinta tsahonta har kanta kafadarsa.

Sake maimaita kiran suna kulsum din akayi,dai dai lokacin da suke qarasowa wajen,yaci gaba da riqe hannunta har suka hau saman step din,ta qarasa ta karbi certificate din,saidai tana karba ta miqawa samir,sai mai gabatarwa ya bata abun magana.

Cikin tsaftataccen turanci da sai ka dauka dashi aka haifeta a bakinta ta fara magana

“Wannan shaidar tashi ce….domin kuwa shine yafi cancanta ya kuma fi dacewa da ita…..” Sai ta daga kai tana dubansa cikin ido

“Mijina….aljannata….rayuwata,kuma duniyata gaba daya,na gode karo na babu adadi cikin rayuwata” tana kaiwa nan ta miqa abun maganar ga mc,saidai kafin takai ga juyowa har tafi ya karade wajen,saboda yadda suka burge kowa,ya kama hannunta ya hade cikin nasa sannan suka fara saukowa cikin nutsuwar da zata bayyana maka yana matuqar ji da ita cikin rayuwarsa,kuma wani sashe ce me girma a tattare dashi.

Ganin yadda dakin taron ke sake yamutsewa da mutane kala kala,da kuma manyan kamfanoni daketa kawo mata invitation letter suna gayyatarta zuwa kamfanoninsui,sai ya janye abarsa,sai daya bude mata side dinta ta shiga kamar yadda ya saba duk sanda zasu fita ko zasu dawo tare,sannan shima ya shiga ya tada motar.

Ta gefan idanunta taketa satar kallonsa,a karo na qarshe ya kamata,sai yayi caraf ya kama hannunta da hannunsa guda daya,ya damqe cikin tafin hannunsa.

Murmushi suka saki lokaci guda,sai ta kwantar da kanta a kafadarsa

“Am proud of you the giant saraki” murmushi ya fitar me sauti,ya saki hannunta ya kama hancinta yadan matsa,ta saki qaramar qara

“Zaka ciremin hancina…..salon ka sani na koma mummuna,kaje ka auro wata ni ina gefe?” Murmushi ya sake saki,cikin yanayin da zai nuna maka yana cikin zallar nishadi yace

“Ko yaya ummukulsum dita take ina sonta a haka,zan kuma ci gaba da sonta,babu wani abu a duniya da zai tsaidani daga soyayyar da nake mata……ita din rayuwata ce,ta bani rayuwa ta kuma tabbatar da rayuwar tawa cikin farinciki…..mace ta biyu mafi daraja a wajena” idanunta ta lumshe tana jin farinciki na ratsata,wannan sunan na sanyata taji kanta ya fashe a duk sanda ya furta mata shi,mace ta biyu mafi daraja cikin rayuwarsa,sai ta qara lafewa a kafadarsa,tana ta sakin murmushi,farinciki na cika zuciyarta.

Gidan da suke bashi da nisa da inda aka gudanar da taron,don haka cikin mituna biyar suka isa,ya bude mata qofa ta fito,sannan ya taka mata gar qofar gidan,ya sanya key ya bude mata ta shiga

“Bakici komai ba na sani,saboda zumudin tafiya wajen taro,ki shiga,zanje yanzu na samo mana abinda zamu ci” sai yadan ranqwafo yayi kissing forehead dinta sannan yaja da baya ya rufe mata qofar.

Idanunta ta lumshe tana sakin nannauyar ajiyar zuciya me hade da murmushi,ta koma da bata ta fada saman daya daga cikin kujerun dan madaidaicin falon,har yanzu bataga miji kamar nata ba,sam batayi kuskure ko daya ba idan tace mijinta yafi na kowa,tun daga aurensu da samir kawo yanzu shekaru bakwai kenan…..farinciki ne yake shigowa cikin rayuwarta daki daki gami da tarin alkhairai,kamar yadda yayi alqawari,tun gabanin ta gama karatunta ta kuma samu shaidar kammalawar ya bunqasa sunanta,tayi shuhura a duniyar zane,zane kama daga wanda idanu zasu iya gani,da kuma zane na ilimi,kama daga zanen na planning din gida ma’aikata kamfanunuwa makarantu xuwa gidaje,da designs da za’a yiwa atamfofi zuwa laces da sauransu,ba zata iya tuna irin alkhairin data samu a rayuwarta ba sanadin zane,wanda kome ta zama din samir shine jagoranta,wanda yayi ruqo da hannuwanta daga duhu izuwa haske.

Zumbur ta miqe,a daren yau ta shirya faranta masa fiye da yadda yake hasashen zaya samu daga gareta,zata maida wannan daren na musamman,zai kuma shiga cikin jerin darare masu tsada daraja da kuma tarihi cikin rayuwarsu.

Kayan jikinta ta fidda,baya ta duba agogo,gab ake da sallar isha’i,saboda dama taron daga yammaci aka farashi zuwa dare,ta daura farin towel yalwatacce,sannan ta daure kanta da wani,sabida batason ruwa ya taba gashin ba tare da samir ya mori gyaran da tayi masa a daxun da safe ba,idan hakan ta faru,sai take ganin tamkar tayi asarar kudinta ne,ko sau daya bata bari tayi wani ado ko kwalliya ba tare da samie ya zama mutum na farko da zai gani ba.

Ta jima tana wanke jikinta kamar wadda ra jima dayin wankan,bayan ta cika ruwan wankan da turarukan wanka masu sumar da tunani da hankali sannan ta fito.

Tana fitowar wayarta na tsuwwa,data duba sai taga jawahir ce,wadda tayi serving number din tata a yanzu da maman yara,saboda duk sanda samir ya kwasheta yawo wani waje ita suke barwa yaran ta hada da yaranta ta riqe har su dawo,shi din samir wani abu Allah yayi masa,tafiya koda ta sati daya ne bai iya tafiya ba tare da kulsum din tasa ba,momma tace ita abun ya isheta,ba za’a yita mata jele da yara ba,su din dai da sukaga zasu iya sai sun dawo,Allah raka taki gona,ummanmu kuma ta goyi bayan momma,wani lokaci shima amirun idan ya tashi nashi abun sai hajiya qarama momma ko ummanmu s karbesu,hakan ya sanya yaran suka shaqu sosai da kakanninsu.

Murmushi tayi ta daga video call din da take mata,ta maqale wayar yadda zata ganta sosai,ta amsa wayar bayan ta janyo mai ta fara shafawa.

Sai data fara da yiwa kulsum da samir tsiya kamar yadda suka saba koda yaushe sannan ta dora

“Kozu ku karbi yaran nan,muma zamu tafi namu honey moon din” dariya sosai ta kulsum ta saki

“Sharrin da zakiyi mana kenan?”
“Eh mana,jiya har sun fara maganarku wallahi,jiya da mukayi magana da ummanmu bakiga fadan da tayi ba,wai takardar meye da itama sai an mata wannan takakkar an karbota”

“Tayi haquri,an karbo certificate dazu,abinda ya rage mana tahowa,kuma ina tunanin a satin nan zamu taho”

“Ya daifi gaskiya” ta fada tana hararta,dariya kulsum ta sakeyi

“Lallabani yarinya,idan ba haka ba kamar a kunnen yayanki abinda kikamin”

“An gaya miki yanzu ina tsoro?,nima fa ina da me taremin din nan,kawai kara muke muku ni da hubby na,amma tunda abu ‘yar hakan…..”

Qarar bude qofar dakin da jawahir taji ya sanya ta saurin katse maganar da takeyi,don ta tabbatar saraki ne ya shigo,ta goce tana dariya,ta jonasu da yaransu.

Kyawawan twins guda biyu,identical twins ma kuwa,masu kama da mahaifinsu sak,irin jinin professor rashid,wanda a idanu zaka basu shekara takwas,saidai shekararsu biyar biyar kacal,bayan auren iyayensu da shekara biyu Allah ya albarkacesu da samunsu.

A hankali ya qaraso bayanta sanda take magana da yaran,tunda ya shigo tayi matuqar daukar hankalinsa,saboda wani qyalli da kyau da fatarta ta qarayi.

Dab da bayanta ya tsaya,ya dora habarsa saman kanta,kasancewar ya fita tsaho,murna ta kama yaran kamar su shigo ta wayar.

Taso zamewa ta qarasa shirinta,saboda tasan hirarsa da yaransa bame qarewa bace,amma ya hanata,ko yaya tayi gefe zata goce sai ya tarota,daga qarshe da qafafunta suka gaji da tsaiwa tilas ta sulale a jikinsa ta kwanta,tana ta murmushi tana sauraren hirarsu,har sai da wayar jawahir din ta saka low battery sannan aka haqura,ya dangwala yatsansa ya kashe kiran,saiya maida hankalinsa kanta.

Dagota yayi gaba daya ya dorata saman madubin yana fuskantarta,itama idanunta saman fuskarsa,ido daya ta kashe masa tana murmushi,saiya kama kumatunta yaja

“Yau akwai jan magana kenan” wannan shine salon furucin da sukewa juna a irin wannan lokacin,kai ta gyada sannan tace

“Amma yaran nan fa…..”

“I know,nima nayi kewarsu,naso ki rakani kallon wasan polo,but na fasa,ina buqatar jin dumin yarana…..sai me kuma?” Kafadunta duka ta kada

“Babu”

“Ni kuma akwai”

“Yes sir….ina saurarenka”

“Me yasa kikayi rejecting duk wata gayyata ta daukarki aiki da manyan kamfanoni suka miqo gareki? Bayan kina da right nayin mu’amala da kowa ta fannin zanenki” Qawataccen murmushin daya sake narka masa zuciya ta saki,sannan tamiqa santala santalan hannayenta ta dorasu saman kafadarsa,ta sake matsowa dashi sosai dab da ita,har ya zamana suna musayar numfashi

“Kaine baban kamfani na,kaine arziqi na,kaine kuma jarina……a yanzu bazan iya aiki qarqashin kowa ba sai kai,saboda babu wani abu da nake da buqatarsa a duniya da ban samu ba…..hakanan duk abinda zan buqata a gaba nasan da cewa zan sameshi IN SHA ALLAH,sabida ina tare da jarumin namiji,mijin da yafi na kowa” dire maganarta yayi daidai da daukarta caraf daga saman madubin yayi gado da ita,salon yadda take masa maganar salone da bazai iya kaucewa tarkonta ko haquri da ita ba.

*_TO NIDAI DAGA NAN NA FICE NA BASU WAJE,KUMA ANAN LITTAFIN DABI’AR ZUCIYA YA DAKATA,KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MANA,YA BAMU LADAN DAKE CIKI_*

*_DABI’AR ZUCIYA ce son rai_*

*_DABI’AR ZUCIYA ce son kai_*

*_duk kuma wanda ya biye ma wadan nan abubuwan yana tare da nadama da dana sani,kana da iko da damar da zaka iya DABI’ANTAR DA ZUCIYARKA KAN KYAKKYAWAN AIKI,qarfi bawai a jiki kawai yake ba,a’ah qarfi yana ga mutumin dake iya mallaka da kuma sarrafa zuciyarsa_*

*_Annabi S A W yana cewa akwai wata tsoka jikin mutum,idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan ta baci kuma dukkan jiki ya baci,yace ku saurara itace ZUCIYA,ALLAH YA BAMU TSARKIN ZUCIYA_*🀲🏽🀲🏽

*_BAZAN RUFE BA SAI NA MIQA GODIYA GA ‘YAN AMANAR ZAFAFA,WANDA BASA GAJIYA DA SIYAN LITTAFINMU,ALQAWARIN ALLAH YAKAI MUKU A KODA YAUSHE,ALLAH YA SADAMU DA ALKHAIRI,YA KUMA SAKE HADAMU A WANI SABON KAFCEN NA GABA IN SHA ALLAH_*

*_DUK INDA AKAGA WANI KUSKURE,TO AJIZANCI NE IRIN NA DAM ADAM,WANDA YAKE TARA BAI CIKA GOMA BA_*

*_FA SUBHANAKALLAHUMMA WA BI HAMDIKA,ASHAHADU AN LA’ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA’A TUBU ILAIKA_*🀲🏽🀲🏽🀲🏽🀲🏽🀲🏽

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button