Sponsored Links
Hausa NovelsSoldiers Family

Soldiers Family 33-34

Sponsored Links

Page 33&34

 

__”ya tada musu hankali sosai cikin sauri Maheer ya tallabo kanshi Yana fad’ar,  “me ya sameka?” Mama kuwa fad’awa tayi jikinshi tana kuka sosai kamar ranta zefita..

 

Maheer kuwa ganin yadda yake Aman jini idonshina k’arewa yasa ya gano gubace yaci cikin sauri ya,ajiyeshi zemik’e dan ya samu ya bashi taimakon gaggawa Amma Bello yarikeshi ba tare da sanin koshidin waye ba? ya rik’o hannun mama yasaka anashi ana fad’ar, “Amana na baka amanar wannan yarinya ka kulamin da rayuwarta Dan Allah karkabari ta shiga tashin hankali irin Wanda muka shiga arayuwa mahaifiyarta ta manyanta bazata iya kareta daga Sharrin masu sharriba bata da kowa aduniya daga Allah sai kai ayanzu karik’emun ita…”yana gama fad’ar hakan Rai yayi halinshi mama tayi kuka harta gode Allah daganan maheer ya gayawa maheerah amanar da mahaifin mama ya bashi atake ko tace, “wannan amanar tasuce su duka tabbas zasu zamema mama garkuwa tunda ga wannan lokacin suka mai da mama makusanciya agaresu komai basu boye Mata nacewa sud’in fa ba mutane bane Kuma mama Bata tab’a bawa eggo labarinsu ba sai dai Idan akayi Mata wani abun ko ranta yab’ace to kaitsaye zakaga alamar iska atare da,ita…Kuma duk abunda maheer da maheerah keyiwa mama familyn su sunsani domin suna Basu labarinta sosai..

 

 

Hakan gimbiya Halila tacigabada bawa abbe lbrn Mama tunda ga zuwan kawo ila gidansu da,abunda yafaru har sanadin fitowarsu da rasuwar eggo harkawo yanzu datake hannunsu..

 

Shiru abbe yad’an yi kamun yadubi Yan uwan nashi yace to kuji alak’ar dake tsakanin zaraah da way’annan bayin Allah.

 

Kana ya cigabada fad’ar, “bayan ta gama bani labarinta shine na buƙaci su bani  ita nizan rok’arta nasaka tayi karatu mai zurfin gaske yadda abbanta ke buri shinefa gimbiya halila tace Sam bazasuyi hakanba tinda Babu wata alak’a tajini Kuma Babu wani dalilinyin hakan bazasu yaddaba..nadaji hakan sai nace to Dan Allah inzasu amince su bani auren ta zannemawa Alyasat shine su kace basu ke da ikon aurar da ita ba dangin mahaifinta ne zasu kaini gun malam isah domin shi yanan daranshi se innema awurinshi…hakan kuwa akayi suka rakani har izuwa Nigeria garinsu abun mamaki tunda muka shiga garin bayan sunshe da cewa zaraah ce tadawo hakan mutane sukayita gudu ana fad’ar ga mayyanan tadawo.

 

Bayan munje gun malam isah shima dai daji abunda ke tafe damu yayi farin ciki sosai kuma shima ya k’ara jaddada Mana cewa ita wannan yarinya dazamu d’auka bakamar ko wacce yarinya bace musani marainiyace kuma nace ahannunmu ahakan dai Jalaludeen ya biyawa Alyasat sadaki bamu baro k’auyen ba sai da aka d’aura auren zaraah da Alyasat anan cikin masallacin marigayi Malam Mai lazimi.

 

Bayan mudawo zamu tafi da zaraah ne way’annan bayin Allah ke fad’ar, “ba wai basasan bani zaraah bane aa suna gudun abunda ka,iya faruwane duba da abunda ya faru Dani to ahakandai muka samu suka amincewa mukazazoda ita..!

 

kunji yadda akayi zaraah takasance matar Alyasat sauran abunda yafaru duk akan idon kowa yafaru bakwa buk’atar wani K’arin bayani..!

 

 

“”Tab d’ijam Allah annabi yayi gaskiya baka gama ji daganin abubuwan mamaki seranarda kabar duniya cewar Hajiya Suhaima…” “wannan hakan yake kam” dady yafad’a kana yace, “hak’ik’a munga tashin hankali Kuma munga abun mamaki daga jiya ko zuwa yau tabbas wannan yarinyar alkhairi ce agaremu bawai iya Alyasat ba domin saboda ita munsamu abunda dukiya ko matsayin yaranmu bai bamuba ba,abunda zamuyi Mata anan sai addu,a dafatar Allah yazaunar da ita lafiya ita da mijinta Kuma ya kauda fitina tsakaninsu”…kowa ya,amsa da ameen “domin dayawansu sunji dad’in wannan auren musamman samarin gidan dake ganin anmusu auren dole Amma Banda su Alyasat d’in.”

 

Abba ne shikuwa yabawa abbe labarin aurar da yaran maza da yayi ya k’ara da cewa sun d’auko wata hanyane wadda sukeso su B’ata Mana zuri,a hakan yasa na yanke wannan hukuncin…kallan duka Yaran gidan yayi kamun yace sabida hakan umurni ne wannan auren ba shawara ba Kuma insha Allah karshen wannan watan kowa zetare da matarsa Tinda kowa nada gida acikin stet d’innan har Alyasat datashi matar..

 

“”Masha Allah hakan yy gaskiya Allah yabasu zama lpy da zuri,atagari.. ameen ameen.

 

Ahakan taro ya watse ma sujin haushi naji masu Jin dad’i naji muhibbat kuwa kamarta kurma ihu dan bakin ciki gaskiya Yaya shareef ya cuceta ita da kesan auren Alyasat yanzu tak’are a shareef gaskiya dolene tad’auki mataki akan wannan Al amarin bazata yadda ba da wannan tinanin tanufi part d’insu.

 

 

Mama kuwa hajiya Suhaima ce ta kamata suka Mik’e tana fad’ar, “zomuje yata tareda kallon abbe tace. Yaya habeeb y’arka zanifa zata zauna wurina kafin sutashi tarewa… murmushi abbe yayi kamun yace shikenan Idan zata zauna aiba matsala..”ah ah bawata matsalar ma cewar hajiya suhaima suna barin perlon da kallo ammy tarakasu tanajin son yarinyar sosai har cikin ranta bataso suhaima tad’auketaba taso tazauna wurinta duk da cewa Bata jima da samun lafiya ba, Amma taso tayiwa yarinyar gyarana musamman kafin atashi kaita d’akinta..

 

 

*India*

 

Wata mushirikar tsohuwace keta faman zagaye awanj d’aki kaida ganin d’akin kasan natsafine domin Shi kanshi d’akin atsaface yake..cikin tashin hankali da tafasar zuciya tsohuwar Nan ke kallon b’arnarda su gimbiya Halila ke mata tunda kashe masu gadin ko wanne part dasukayi harshiga part d’in ammy har akazona habibbty cikin k’araji take cewa k’aryaneee k’aryaneee nace Baku isabaaaa senayi ajalinkuuuuu..!

 

 

 

 

*SOLDIERS FAMILY* na kud’i ne nera 500₦ kacal 👌 ga duk me buk’atar complete kuma 700₦ ne Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub’ar wannan number 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number 👉 08107819124

 

 

 

 

 

Autar Alheri ✍️

 

*S F*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button