Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 47

Sponsored Links

47
D/Z

A gaba ta zauna kamar yadda tsarinsa yake,suna shiga motar jauhar na kiransa a waya,saiya hada wayar da speaker din motar yana amsa wayar.

Duk yadda taso dauke hankalinta daga hirar tasu hakan ya gagareta,saita samu kanta da bibiyar duk wata hira da jauhar din ke masa,shi kuma yana qoqarin amsata,wanda kana jin yadda yake amsawar dauriya kawai yakeyi da qoqarin tursasawa kansa,don hirarma batayi tsaho ba yace mata

“Am on my way to office,i will call you when I’m back”

“Ok honey,byeeee” ta fada da wani baby voice da take amfani dashi wajen ganin taja hankalinsa.

Shuru ne yaci gaba da wanzuwa,wanda mintunan da suka qara basu wuce biyar ba ya tsaida motar bakin makaranta,ta dauki jakarta ta fita tana cewa

“Na gode” ta maida murfin ta rufe bayan tabar masa sauran qamshin turaren data durfafa a yanzu.

Yana motsa motar zuwa gaba yana hangen sanda ta shige makarantar ta madubi,saiya dauke idonsa ya maida hankalinsa sosai ga tuqinsa,yana qoqarin daga wayar amiru data shigo.

Shaida masa yayi yana nan dawowa da yammacin yau,amma zai dan zauna gidan hajiya qaraman kafin ya qaraso nan gida,yaji dadin dawowar tasa wannan karon da wuri,sabida amirun shi daya ne amini ga samir,wanda yake iya tattauna matsala ko damuwarsa dashi,hakanan yakan samu courage na aiki a duk sanda amirun ke cikin kamfani,saidai dole wani lokaci akan rashi a kusa,sabida shike kula da dukiyar da mahaifinsa ya rasu ya barmusu shida ‘yan uwansa mata biyu dake aure a wata qasar.

Yau din tana aiki tana duba novel din,don da qagu taga qarshensa,sosai labarin yake dibanta gami da tafiya da ita,batasan sam haka soyayya take ba sai yanzu,batasan haka rayuwar auren masoya take ba sai data karanta littafin,saita tsinci kanta tana hasaso kanta da gina rayuwar soyayya irin ta cikin littafin,amma kuma dawa?,a yiwa kanta tambayar data katse dukka zaran tunaninta.

Idan ta dauko soyayyar da tayi a qauye sai taga ashe badan badamarsu kawai sukeyi,basusan meye ma ainihin soyayyar ba,kawai wani abu suke mai kama da wasan kwaikwayo.

Zamantakewar aure a karkararsu kuwa dama ta jima da sanin cewa ana yinta ne illegally ,abubuwan dake faruwa kwata kwata basuyi kama da zaman aure ba.

Ita kadai a kitchen tana aikin abinci tana sakin murmushi a duk sanda ta tuna da labaran novel din,sun sanyata nishadi ba kadan ba,abinda kuma ya jawo mata delay kenan,tayi nawar gama girkin da takeyi,har akayi kiran sallar magariba.

Ajjiyewa tayi taje tayi sallar sannan ta dawo tana duba abinda ya rage din,a hankali tanayi tana duba sabon novel din data karbo din.

Bakwai na dare motar tayi parking a parking lot na gidan,zaratan samarin guda biyu suka fito daga cikin motar,fuskokinsu wasai,suna taba hira har suka qaraso qawataccen parlour din hajja.

Tana daga zaune taji sallamarsu,murmushi ya wadata a fuskarta,farincki ya cika zuciyarta,ta bisu da kallo tana musu fatan dacewa da samun mataye na gari,a yanzu babban burinta shine taga dukkaninsu sunyi aure,sabida tsakanin ita da yayan nata yara maza biyune rak dasu,sai mata,ita uku shi biyu,tana fatan wadan nan da Allah ya basu yaci gaba da albarkacesu,su kuma tara musu zuri’a me dumbin yawa.

Waje suka samu suka zauna cikin nuna mata kulawa,amiru ya zamo ya gaidata yana mata sannu da jiki,yayin da samir shima ke sake mata sannu kamar ba daxu yabar gidan ba.

Hira suka fara tabawa kadan kadan,wadda ta shafu tafiyar tasa,da kuma abubuwan da suka faru bayan bashi nan.

Karo na kusan hudu wayar samir tayi tsuwwa yasa hannu yayi rejecting kamar yadda yakeyi tun dazu,hajiya qarama ta dubeshi

“Ka daga mana ba kiranka akeyi ba?” Saiya jinjina kai

“Barsu hajiya,idan na gama komai zan kira” maganar amiru ta katse zancan

“Nifa tunda na shigo nakejin qamshin girki hajiya,kuma anmin fuska,a amatsayina na baqo yaci ace an tarbeni da wani kyakkyawan girki nan” kallonsa tayi ta tabe baki

“Idan abun bai maka dadi ba kayi zuciya ka kawomin mata qarshen watan nan,ni dama na gaji da ganinku wallahi a gabana,shi wannan kamae bashi da idanu saida aka zaba masa mata,wadda har yanzu nikam ban gama yarda da ingancinta ba,kai kuma har yanzu shuru,to gwanda gwanda shi da kai ma” gyara zamansa yayi sosai yana duban hajiyan

“Wato hajiya kada ki damu,tana qarasa NYSC zan gabatar miki da ita in sha Allah” baki ta sake tabewa

“Zuwa yaushe kenan?”

“Nan da wasu ‘yan watanni ne,tana dawowa” kai ta dauke haushi yana cikata,badon sanin halin yaran zamani ba,da tuni kowanne ta zaba masa mata sun aurar dashi an huta,to amma ita kanta tana adawa da auren dole

“Data gama abincin da tuni ta kawo,amma yanzu ma nasan tana dab da gamawa” ta amsa musu,sai samir ya miqe,don da gasken shikam yunwa yakeji,wunin yau banda baqin coffee babu abinda ke cikinsa,sai cake guda biyu

“Bari na samo wani abun”

“Yauwa mutumina,ka hado dani please” hara rarsa yayi

“Idan ka matsu kaje ka dauka da kanka,yaron gidanka ne ni?” Dariya ya saki

“Ban isa ba,ataimaka min” bai sake ce masa komai ba ya wuce cikin kitchen din.

Bai lura da ita ba sai daya isa cikin kitchen din daga bakin qofa,saiya dakata a hankali da tafiyar da yakeyi din,tana tsaye riqe da littafin tana karantawa,fuskarta na fitar da wani murmushi dake nuna nishadin da zuciyarta ke ciki.

Sanye take da daya daga cikin kayan da jawahir ta bata,high tummy skert me wata belt a jikinsa me fadi wadda gabanta ke dauke da tambarin kamfanin DG daya bayyana asirin shafaffen cikinta,daga baya kuma mazaunai da qugunta da suka fara bajewa suka bayyana,sai long sleeves t.shirt turtle neck wadda ta dace da kalar peach din skert din me adon green,dan kwalin kanta shima peach ne me santsi sosai,wanda ya hadu da santsin gashinta ya hana dankwalin zama yadda ya kamata,hakan yasa ya zame daga kanta ba tare data sani ba.

Fuskarta yabi da kallo,fatarta data koma chocolate colour ta haska sosai cikin peach color kayan data sanya,daga gaban goshinta gashin kanta ya kwanta sosai ya sauka zuwa kafadunta.

Wani motsi yaji zuciyarsa nayi,yabita da kallo sanda ta furta

“Yes,anzo wajen” qasa qasa bada wani qarfi ba,saboda laushi da zaqin murya da Allah ya bata daya dade da sani tun a qauyen dinya,saita kife littafin,ta tafi ta juya miyarta ta kuma dan dana.

Fararen idanunta da suka qara girma da gaske ta dinga rarrabawa bayan ta gama dandanar miyar taji da sauran tsami,saita ajjiye ludayin,ta matsa gaba kadan gaban wata locker ta jikin bango dake sama,inda hajiya ta nuna mata nan suke ajjiye kanwa koda akwai buqatar amfani da ita,tasa hannunta ta bude locker tana fatan Allah yasa tsahonta yakai,saboda ta kere mata sosai.

Hannunta ta sanya ta laluba sosai,saidai bataju komai ba,saboda gwangwanayen sun shige can ciki,don haka ta duba hagu da damanta ko akwai abinda zata taka takai saidai babu,abinda yasa ta fara yin dage kenan tana tana ta zura hannu amma a banza.

Murmushi ya qwace masa saboda yadda yaga tana yin dagen,gami da tsalle duka,ya sauke hannayensa daya rungume a qirji,ya fara takawa a hankali zuwa inda take tsayen.

Ko kusa ko alama bataji wani alama na shigowa mutum ba ko qarasowarsa inda take,sabida socks ne kawai a qafarsa,sai dumin tsaiwar mutum da kuma jinginarsa data ji a bayanta,kamar anyi huggin nata ta baya kenan,saidai babu hannunsa guda daya daya tabata illa ya miqa hannunsa cikin locker yana qoqarin dauko mata abinda ta kasa daukowar.

Da fari ta tsorata,harma ta juyo da sauri,bugun zuciyarta na sake qaruwa gabanta na faduwa,saidai suna hada idanu sai komai kwance mata,tsoron yayi nasa waje,sai kunya nauyi da gudun zuciyarta wadda taci gaba da harbawa cikin qirjinta da sauri da sauri.

Sosai idanunsa suka mata wani irin tasiri,kamar yadda yaji dumin jikinta da tudun bayanta a lokaci guda suna wani ratsashi tare da saukar da wani yanayi a jikinsa,kusan lokaci daya suka sauke idanuwansu,ita ya sauk su qasa tana kallon tiles din kitchen din,shi kuma ya mayar cikin locker din ya fara sauke mata gwangwanayen ciki da daya da daya,kamar wanda cutar kasala ta kama,lokaci guda qamshin man datayi oiling kanta dashi ya cakuda da turaren jikinta yana shige masa hanci.

Sai daya sauke mata dukka gwangwanayen sannan yaja baya a hankali yana jingina bayansa da kantar kitchen din

“Zabi saina mayar,ko kuma nabar miki su duka?” Ba zata iya amsawa ba saboda yadda jikinta ke dan rawa rawa,ita kadai tasan feeling din daya haifarwa jikinta,irin abinda bata taba jin ya motsa cikin jikinta ba.

Da idanunsa ya kafeta sanda take budawa tana duba wanne ne kanwa ke a ciki,yabi hannayenta da kallo wanda ada basu da wani kaurin kirki,amma a yanzu sun ciko sosai,idanunsa suka sauka kan wani abun hannu guda uku dake daure a tsintsiyar hannunta,na dutsune irin dutsen shirin nan shigen na fulani,saidai wadan nan wasu irin masu garai garai da sheqi ne,butter colour ne masu dan girma circle shape.

Rubutune a dutsen tsakiya daya kaso hangowa,ya zuba idanu sosai amma bai gane me aka rubuta ba,har zuwa sanda tace

“Na gama” da siririyar muryarta,ya qarasa a hankali,saiya kama tsintsiyar hannunta,wanda hakan ya sanyata daga idanu ta dubeshi da sauri,sai taga dutsen yake kallo wanda aka rubuta i’m in love da qananun baqaqen rubutu.

Dazu dazu ta siya abun hannun a makaranta,an jima ana saidashi,duk da yadda kuma ‘yan ajinsu keta siya bata taba marmarin siya ba,saboda akwai mai sunan samari a jiki da yawa,kowa yana siyan me sunan saurayinsa ne,sai dazu da aka kawo wadan nam design din sukayi mata saita dauka.

Yana gama karantawa ya dago suka hada idanu,tayi saurin dauke idonta tana jin bugun zuciyarta na sake ninkuwa fiye da da,wani irin maganadisu idanunsa ke dashi,ta dade da ganin haka,tun ranar daya tsaidata zai shigar da haladu wajenta,abinda ya janyo a sannan ta kasa maida masa maganganun da tayi niyya kenan.

Ya lura wanu nauyinsa da kuma kawaici take masa,sai yaqi sakin hannun nata,yaci gaba da kallon abun hannun,a hankali ya sakar mata hannun sannan ya fara diban containers din yana maidawa,hakan ya bata damar yin gaba da sauri ta jiqa kanwar,ta matsa gaban tukunyar ta bude ta zuba,ta juya miyar ta tattabatar komai yayi,saita kasa juyowa sanoda tana da tabbacin yana cikin kitchen din,baisan shi mugun nauyinsa takeji bane?,tanason ta qarasa aikinta ne tabar kitchen din,amma wanzuwarsa a nan ya hanata ci gaba da yin komai.

Littafinta na saman freezer din da zai dauki abu,bai kula ba ya bude sai littafin ya fado qasa,ya sunkuya a hankali ya dagashi,zai gyara mata alamar data saka na shaidar inda ta tsaya,saiya buda shafin,idanunsa ya sauka a inda ta saka alamar.

Layi hudu ne,amma suna dauke da wasu zafafan kalaman soyayya,da alama sun jima suna dakon soyayyar junansu,sai ranar jarumin ciki yake bayyanawa jarumar soyayar da yake mata.

Alamarta ya maida mata,ya rufe littafin ya dora mata a gefanta,sannan ya bude freezer din ya dauko fresh milk da basuyi sanyi sosai ba,yana da buqatar daukan cups,saidai kuma tana tsaye a wajen,hakan ya sakashi takawa,ya sake tsaiwa dab da bayanta,dyk da kusancun baikai na daxun ba amma saida numfashinta ya dauke na wucin gadi.

Dai dai sanda ya miqa hannu ta gefan wuyanta zai dauka cup din ya jefa mata tambayar data sanyata diriricewa

“Waya koya miki karanta litattafan soyayya?,bakisan koya maka soyayya suke ba?,ko kin shirya yinta a yanzun?” Kalmomin daya gaya mata kenan da suka shige deep inside her da wani irin sound me nauyin amo.

Tambayar tayi mata tsauri da yawa,hakanan batasan kalar amsar da zata bashi ba,saita zabi yin shuru

“Yaka dade ne,am starving fa,fuska kawai nayi” suka tsinci murya amiru tsakiyar kitchen din,abinda yasa samir ya janye baya a hankali hannayensa dauke da kofunan,ya dubi amiru wanda idanunsa suka hango masa kaltum dake tsaye bakin tukunya,taqi kuma juyowa

“Gasunan acici,ka fado waje babu sallama”

“Don zan shigo kitchen sai nayi sallama?,wanne sabon salo ne kuma hakan?” Ya amsa masa tana matsawa gaba tare da gocewa gefen saraki daya tsaya a gabansa ya kare masa abinda yakeson ganin

“Ashe mana,dole mu zauna da yunwa ashe jawahir ke girki” ya fada da salon tsokana irin wadda sukewa juna lokaci zuwa lokaci shi da jawahir din.

Dole ta juyo saboda batason yacu gaba da dauka jawahir din ce

“Ina yini” ta fada tana sake takurewa waje daya,tare da Allah wadan rashin fitowa da mayafinta da batayi ba

“Oh, sorry…….ashe ba ita bace,kamar kaltum ko?” Ya fada yana nunata da yatsa,saita daga kanta kawai

“Ma sha Allah,lafiya lau” ya amsa yana juyawa,saiya hangi samir tuni yayi gaba yama kusa ficewa daga kitchen din,don haka ya juya yabi bayansa,bakinsa fal da maganganu.

Tunda ya fito samir din ya karanci maganganu ne fal bakin amirun,don haka yaqi bashi damar cewa komai ma,ya maida hankalinsa ga hajiya qarama dake masa bayanin tanason suje azare qarshen watan nan,fada take musu sosai shi da amiru

“Dukkanku zuba muku idanu ai nayi,naji wanda zai fara maganar zuwa a cikinku amma ba’a samu ba,wasa wasa so kuke gaba daya a watsar da zuwa azare,bayan kunfi kowa sannin ammi tana da rai,kai koda bata da rai hakan bame yuwuwa bane,to ku shiga taitayinku da kyau na gaya muku,tunda shi yayan yana kallonku ya qyaleku,saboda haka ku shirya…..bikin salis za’ayi da farida,kuma dukkaninsu ‘yan uwanku ne auren zumunci ne,saboda haka zuwa ya kamaku,kowanne ya kammala uzurinsa kafin sannan,ashirin da biyar ga wata nakeso mu wuce dukka harda su jawahir da najwa,uwarsu kuma idan taga zataje taje,wannan ba matsalata bace” can qasan rashi samir ke sakin murmushi yana kurbar fresh milk dinsa,har kwanan gobe dai hajiya qarama ba zata sauya ba,bai taba ganin wani abu data riqa ta kuma qi jininsa irin mummy jidda ba,taqi gaya masa dalili,kuma shima ya kasa ganowa,abu daya ya fahimta,tanayin komai ne akansa da mahaifiyarsa,mahaifiyar data gudu ta barshi,ta zabi ta shiga duniya ta barshi.

Jin zuciyarsa ta fara quntata da wannan tunanin yasa ya janyowa hajiyan wata hirar,tunani ne dake sanyashi yanzu yanzu ya burkice,shi yasa ba kasafai yake barin kansa yinsa ba.

Babu jimawa kaltum ta fito ya shirya komai,saidai wannan karon gaba daya jikinta lullube yake da wani cotton mayafi mai kyau baqi,ta gama shirya komai ta matso wajen hajiya qarama tana rusunawa

“Hajiya an gama” addu’a tayi mata sosai cikin kulawa da yabawa,har zuwa sanda kaltum din ta wuce daki bakin hajiya qarama baiyi shuru ba yaba mata take,mutum ce ita da bata raina ko manta alkhairi komai qanqantarsa

“Saraki…..wannan yarinyar….wankan engine akayi mata ne?,kasan rabona da ganinta kwana uku bayan zuwanta garin nan?”

“Wa ya sani ne?” Ya bashi amsa yana miqewa zuwa dining inda hajiya qarama ke kiran suzo ga abincin suci

“Anya kuwa kana kallonta da kyau samir?,kaga yadda ta canza? black skin din nan ta koma wani beautiful chocolate color?,ba sirantaka,komai nata moderate,baka gani ba wai?”

“Ban sani ba!,ba aikina bane wannan observation din, shut up your mouth kaci abinci malam” ya fada masa yana tsareshi da ido

Kai ya dauke ya fara zuba abincin,saidai bai iya yin shurun ba

“Saifa na fada malam,anya ba akwai abinda ka gano ba a sannan kayimin wuff ka amsha aurenta ba?” Haushi ya cika samir,ya rasa me zaiwa amiru ya huce,dama tun asali ya sanshi,mutum ne da yasa ainihin diri da halittar mace,aka haka yake da zabe zabe da ruwan idanu,a nan halinsu ya saba,kuma akan wannan suke fada,saiya dauka wani qaton saving spoon ya jefi amirun dashi,Allah yasa ua goce,don ba shakka daya sameshi saiyaji babu dadi

Kallonsu hajiya qarama data qaraso wajen kawai tayi ta tabe baki

“Har yau ku bakusan kun girma ba kenan” zuwanta ya yanke maganar,saidai duk sanda suka hada idanu da amiru saiya karanci maganar bata isheshi ba kenan.

Har suka gama cin abincin suka gama hirarsu bata sake fitowa ba,daga qarshe dai yadda amiru yaso kwana gidan bai yiwu ba,saboda daddy daya kira yanason ganinsu,dole tare suka tafi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button