Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 59-60

Sponsored Links

*59 – 60*

Washegari jumu’a su abbey suka kuma dawowa jejin ,da tarkacen su goro huhu² ,taburmi,cartoons ɗin drinks da ruwan roba ,sweets ,kwandunan dabino ,da sauransu suka lafto kayan mota guda aka jibge a gaban masallacin jumu’ar

Tuni labari ya fara trending a gari,shikuwa julayb bai shigoba sai gabda za’a ɗaura ,sai ga mota trela shaƙe da shanaye,anzo anjibge.

Cikin shigar nanyan kaya na zallar boyle fari ƙal ,ƴan ciki da malummalun,ya murza hula ƙiran tangaran ,kalan kwalliyar jikin rigar,sai ya saka baƙar takalmi ,yana tafe yuna bulbula ƙamshi na musamman,julayb ango cikin manyan kayan hausawa lolz.

Duk inda yabi ƴan ƙauyen kallon shi su keyi, taron ƴan jarida kuwa,dana gidajen t.v kamar an gayyace su

Ana sallame sallar jumu’ar aka shigo da kayan ɗaura auren a take aka ƙaddamar da ɗaura auren akan kuɗi miliyan guda.ana ɗaura auren aka zarce da rabon wainnan kayan dabinon dasu drinks da ruwan roba,zokaga layi zamusha ruwan roba🤩

Shikam julayb ,ana cewa an ɗaura ya shige mota ,kawai da ya rasa mai zaiyi saiya fashe da kuka harda sheshsheƙa shi wannan soyayyar ma dayike mata baisan kalan saba.
Wayarsa ya zaro ya soma kiran umma raudha, cikin ƙaraji ya ce “umma nikahtul annnn”
Baijira respond ɗintaba ya kashe haka yayi ta kiraye kuraye,kuma da ya shaida masu sai ya kashe ya kura wasu,kuma ko anyi calling back sai ace busy…

Saida ya gaji don kansa ,ya wurga wayar a mota ,ya fito,a take yasa ƴan kamfaninsa da suka zo masa ɗaurin aure dasu taru a rarrabawa dattawan garin shanayen da suka zo dashi. Kowa shanu da naira dubu goma.

Wohoho ,abun yayi exciting kowa ciki harda ƴan jarida,tuni gidajen tv suka shiga watsa wannan an amazing biki,yo multi billoniern balarabe dashiga surƙiƙin daji ,da auro bagidajiyar bafullatana ,talakan tilis kamar mairo batareda ƙyara ko hantara ba…saima rabon abun arziƙi da sukayiwa ƙauyen wanda ya toshe bakin kowa

Duk tsoffin anguwa kuwa faɗi suke “uhm uhm uhum ,allah in baka bamu ba kaba namu,allah karja bashemu aure irin na mairo shi ake kira da arzuƙa,jibi tuƙeƙen sa guda da ake shigiwa dashi gida gida…”

Yayinda wasu suke faɗin “ahab ,adai barsu ,zasu sha kallon abun mamaki ,wani aurene hakan ba mata sai maza mutum uku sai ango,lallai kwaɗayinsu zata yi kai,don kuwa tamkar sun saida ƴarsune kurum”

Wannan jita jitan shi ya fara zuwa kunnen mairo kafin ma tasan an ɗaura aure ,don haka duk ƙawayenta sa’ointa suka warwatse suka barta a gudan tiririshin da sukeyi.

Ƙunshe kanta tayi taringa rushewa da kuka ,fuskarta yayi jajir,ana haka tsoffi sukazo tafiya da ita ai mata wankan amarya, shikam julayb yina biye dasu shifa lallai sai ya ga anaryarsa.

Acan gida kuwa,mata na zaune da ƙaton turmi a tsakar gida ana jiran zuwan amarya

Suna shiga tana can ƙurya tana kuka, su bama su ankara ba,haka suka ɗagota suka fesa mata nono a fuskar suna aikin rangaɗa guɗa.

Jin ta sandare taƙi ko motsi yasa suka soma rarrashinta “”mairo aure bautar allah ne ,kiyi haƙuri haka duk mukayi muka zauna a gidajen mazanmu,yau kinga sai labari…”

Tun suna ganin abun kan auren ne har suka gane akwai matsala amma juyin duniya taƙi ko motsawa bare ta fito suje da ita.
wai lallai tafasa auren .juyin duniya an rasa yanda za ayi da ita.

Fitowa sukayi cikin fushi zasu koma gidan da sauri julayb yayi bayansu.
Tambayarsu yayi ko lafiya?
Nan suke shaida mashi abunda tace

A tsorace ya koma da baya ya shige gidan ,ƙwalla mata kira ya shigayi har muryan sa na dishewa.
Da gudu sukabi bayansa suna basa haƙuri,amma ina ko jinsu bayayi ya ringa shiga ɗaki² har ya hangota.

Yina zuwa bai wata² ba ya ɗagata cak,ya fito da ita sai mota
Cikin fararen kayan fulani ,anbi anmata murtuka²n kitson fulanin yina zabga warin man shanu,adole an ma gashin oiling ɗin ƴar gata.

Hannu da ƙafa ƙunshe da lallen gargajiya ƙafa da hannu tsohuwa ta faɗa taɓo.

Yina sakata ,ya figi motar da gudu suka bar garin ,dukda kwazazzaban da ya dinga cin karo dashi ga jijjigen bishiyoyi da sukasa aka sassare don asamu hanyar wucewa,amma sam bai damu ba har ya fito hanya ,daganan ya ɗauki hanyar airport da ita ,wanda nan ne kaɗai ya sani.

Yaje ana haranar kwasan pasinjar jirgin da zasuje abujane,amma ya roƙi abasa zai biya kuɗaɗen fasinjar su tafi harda ƙari.

Haƙurisuka basu suka ce nan da awa biyu wata jirgin zai zo.

Anan take suka ɗauki hanyar lagos ,few hour suka sauka ,ya ɗauki hayar taxi ya wuto dashi gidan saida ya gansa cikin compound ɗin shida mairon sa .
Sannan ya kira securityn da ya bari a can dasu abbey ,yace su je airport ɗin su ɗauko motarda ya bari ,shi ya wuto lagos.

 

 

 

 

 

Oum Aphnan✍️
[3/14, 07:06] Bamalli✌️: *Typing…✍️*

 

*JARABABBEN NAMIJI*

 

*Na…Oum Aphnan🌸*

________________________________

*ALHERI WRITERS ASSO.🖊️*

*A .W. A*

https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/

________________________________

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button