Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 48

Sponsored Links

48
D/Z

Kwanakin da suka biyo baya ta maida hankalinta ne sosai ga jarrabawar da take gabanta,cikin ikon Allah kuma sai ta dinga zuwa mata da sauqi sosai kamar yadda jawahir ta gaya mata,sai abun yayi mata dadi qwarai a ranta.

Tafiya azare ta kama,kuma dukka kowa yayi amannar zuwa,har mummy da hajiya qarama bata damu da taje ko kar taje ba,sai gashi kamar ma tafi kowa damuwa da tafiyar,tun kafin ta isa garin kuma ta aika da tata gudummawar mai tsokar gaske ga bangaren gidansu amarya data ango,kamar dai yadda ta saba hidima kan jiki kan qarfi duk sanda wani sha’ani ya tashi daga dangin professor.

A satin da za’a tafi a zaren professor ya tako gidan da kansa wajen hajiya qarama,da alama kuma zuwan yana da alaqa da maganar auren samir da kuma bikin azaren.

Kaltum kusan itake kula da duk wani baqo da hajiya qaraman zatayi,tunda taji tace yaya rashid zaizo kaltum tayi abinci da abun sha na musamman saboda professor din,hatta hajiya qaraman bata sani ba,sai da yazo sannan taga kaltum din nata shirya masa kalolin abinci

“Kina wajen hajiya kenan?” Professor ya fada bayan ya gama amsa kasuwar kaltum dake duqe,hajiya ce ta karbi xancan ma tun kafin kaltum din tace komai

“Wallahi yaya,nace ina kuka samo haziqar yarinya haka,bason jiki ba ganda babu qyuya,na dade banji mutumin da naji dadin xama dashi ba kamar yarinyar nan” kada kai professor yayi,shi kansa yana yaba yadda yarinyar ke hidima da kowa cikin,duk da ba zama yake sosai ba amma yana lura da hakan,karon farko da zuciyarsa tayi sanyi da wuri kan wani abu da samir yayi gaban kansa ya aiwatar dashi ba tare da yarjewarsa ba

“Ki koma daki ki huta hakanan kinji,kya samu damar duba karatunki,zasu qarasa aikin”cewar hajiya qarama,tunda daya daga cikin masu aikinta ta dawo,dayar kuma ta kawo wadda zata riqe mata aikin kafin ta dawo. Kai ta gyada tana shigewa ciki.

Hira sukayi sosa irin ta zumunci ita da dan uwan nata,wanda dama duk sanda irin hakan ta faru yakan jima a gidanta,akwai shaquwa da qauna sosai tsakaninsa da hajiya qamar,daga qarshe ta fadi abinda take ganin ya kamata ya bayar kan hidimar bikin,ta kuma shaida masa ranar da ita zata tafi

“Ke kuma sai yaushe zaki tura taki gudunmawar hajjaju,naga jidda wannan karon ta rigaki bayarwa” ya fada yana saka hannunsa a aljihun babbar rigarsa yana ciro kudi.

Baki ta tabe tana duban wani barin

“Dama haka takeso ace,tayi qoqari,amma ni bana abu don a fada ko kuma saboda gasa,Allah sarki raihana…….har batason ace tayi wani aikin alkhairi,takan ce tayine saboda Allah,kuma shi take bida ya mata sakayya”

Wani kallo ya yiwa hajiya qaraman,tayi zaton abunda ya saba shi zaiyi a yanzun ma,saidai ga sabanin tunaninta sai taga ya dauke kai ba tare da yace komai ba,yaci gaba da irga kudaden daya debo din.

Miqewa yayi yana ajjiye mata kudin

“Wannan ki riqe a hannunki,nasun kuma zan saka a tura musu su cire ta banki” baki ta sake tabewa

“An gode,Allah ya qara arziqi ya rabaka da sharrin maqiya da munafukai” ya saba da jin wannan addu’ar daga bakinta,itama kuma tasan cewa an kawo qarshen hirar shi yasa daya miqe ma yana mata sallama ma bata damu ba.

Da kaltum hajiya qarama taso tafiya azaren,saidai kuma abun yazo da akasi,don randa xasu tafin ita da yaranta guda uku da jikokinta shida ranar kaltum din tana da sauran jarabawa guda uku,hakan yasa dole hajiyan ta barta suka wuce ita da yaran,da kuma jawahir banda najwa da ita tace sai ana ya jibi daurin aure zata je,ba zata iya zuwa azare ayi sati ba tana da schedules da yawa.

Jin cewa samir bazai samu tafiya ba sai ana ya gobe daurin aure tace ta zauna nan gidanta tunda masu aikinta suna nan,ya taho mata da kaltum din itama taga jama’a.

Hakan ya yiwa kaltum din,saidai jawahir bataso hakan ba

“Don Allah idan kin gama exams kafin ranar ki gayamin,Allah zan yankar miki ticket da kudina ki taho bauchi a ranar” murmushi kawai tayi mata,itakam banda ma hajiya nason taje da babu abinda zata,zatafi farinciki ace qauyen dinya akace taje,taje ta gano ummanta,don a yanzu bata da burin daya wuce haka.

Su amiru kuwa washegarin randa su hajiya suka tafi shima yabi bayansu,saboda akwai abota sosai tsakaninsa da angon fiye da samir,don yafi samir ma zuwa azare,hakan yasa professor ya sakashi ya tattaro ya dawo gidan hajiyan,saboda yace kada a bar mata gidan babu wani babba namiji sai masu aiki,dama kuma yana da niyyar hakan,saboda gyara daya bayar ayima sassansa,har mummy na tsokanarsa gyaran me?,shi daya kusa tafiya yabar gidan gaba daya?.

Ko daya kaltum batasan yana gidan ba,don ba shigowa ciki yake ba,iyakarsa sassan da suke zama yawancin lokuta shi da amiru idan suna gidan,hakanan da safe yake ficewa sai dare yake shigowa bayan ya gama sabgoginsa.

Yau tunda ta tashi takejin mararta babu dadi sosai,duk kuwa da cewa tun sanda ta gama shanye magungunanta dama takejin wani iri a mararta,amma na yau yafi na kullum,a haka ta samu ta rarrafa taje makaranta ta dawo,sai tayi lamo tun la’asar a bargo tana karatun novel tare da daukan darusa masu yawa,saboda jarrabawa biyu suka rage musu,kuma dukkansu masu sauqi ne,bata da wata matsala ko fargaba akansu,hankalinta kuma na rabuwa kashi biyu,saboda yadda mararta ke sake daurewa.

Bata tashi ba saida akayi sallar magariba,tayi alwala tayi salla,ta zauna saman abun salla kamar yadda ta saba kullum tsakanin magariba da ishaa,saboda lokacine na amsa addu’a,lazumi take a lokacin,idan ta gama kuma ta duqufa da addu’o’i kan ingantar rayuwarta data iyayenta.

Bata tashi ba saida tayi sallar isha’i,daga nan tayi bandaki tayi wanka da brush,kamar yadda yanzu ta sabarwa kanta ya zame mata jiki,ta tsane jikinta tayi oiling gashinta ta hadeshi waje guda tayi masa tufka daya sannan ta dauki wasu riga da wando milk colour masu taushi da kauri da hajiya qarama ra bata su,cikin wasu ragowar tsarabarta zuwanta saudiyya da professor ya kaita shekara biyu baya ranar ta dauko jakar ta gansu a ciki.

Tsaiwa tayi tana kallon kanta yadda kayan suka karbeta,ita kanta a yanzu takan jima tana kallon kanta yadda ta sauya lokaci daya,tasan mutane da yawa idan akace musu wanna kattumen da suka sani ce saisun qaryata kafin su yarda ita dince,abu daya ne yake daqila mata farincikinta,idan ta tuna ummanta da kuma habi,ko a wanne hali suke ciki?,ko habi ta haife abinda yake cikinta?,ko ummanta ta warke?,uwa uba kuma idan ta tuna ko zata karade duniya ba zataga dan uwa rabin jiki bilalunta ba,ita dashi sai a lahira,sai taji hawaye sun sauko mata,dukkan wata walwala tata da jin dadinta sun kau.

Yau a sanyaye ta koma ta zauna,ta jima a haka tana nazari,kafin ta sanya hannu ta shafi mararta dake sake qulle mata,wunin yau bataci wani abun azo a gani ba,abincinta na rana dana dare tasan duk suna kitchen din a ajjiye,kuma ko yanzu bata jin cin komai,bata da matsalar dafa ko cin abinda takeso,kamar yadda kowanne cikin masu aikin gidan hajiyan batayi masa shamaki da cin abinda ranshi keso ba ta hanyar data dace,babu almubazzaranci babu barna ko ha’inci,tana da kyauta da kyautatawa dukkan wanda ya zauna tare da ita,itakam.kaltum ba zata iya lissafa adadin kyautatawar hajiyan gareta ba,ko diyar data haifa a cikinta iyakar abinda zatayi mata kenan.

Komawa tayi ta sake kwanciya tana jawo littafin tana cije labba,wala’alla ko zuwa anjima zata iya jin yunwa ta tashi ta nemi abincin.

Yau da wuri ya dawo,don a nan unguwar ma yayi sallar magariba kana ya shigo gida bayan yadan tsaya wajen masu gadi sun dan taba hirar da bata fi minti biyar ba,duj da cewa ba jimawa yake wajensu ba,amma hakan yana musu mugun dadi,ta yadda baya qyamatarsu,ko kuma nuna banbamci ko fifikon dake tsakaninsu.

Yana fidda kayan jikinsa yana kiran wayar jawahir,yana sone yaji ina yarinyar take,saboda akwai siyayyar da yakeson mata,ya dade yana son mata wasu ‘yan siye siye,saboda ko babu komai tunda har agiyarsa ta hau kanta to dukka sharuddan kulawa yahau kansa a musulunce,to amma baisani ba ko tare suka tafi dasu jawahir din,don baisan taqamaimen ranar da xasu gama jarrabawar ba.

Bugu biyu jawahir din ta daga,da qorafi ta fara kamar kullum

“Yaya,ban tabajin azare ba dadi ba irin wannan karon,don Allah yaya kaida kaltum ko taho sooner” murmushin daya qawata fuskarshi ya qara mata kyau ya saki sanda yake zare tie din wuyansa

“Mr qorafi,babu gaisuwa,babu jin ya nake sai qorafi”

“Am sorry yaya”saita fara gaidashi ya amsa mata,yana tambayarta azaren tana bashi amsa,tare da bashi labarin yadda aketa tsara bikin,saboda an dade ba’ayi biki ba a familyn sai yanzu,sannan kuma ma auren zumunci ne tsakanin angon da amaryar.

Yana da jumurin sarare,abinda yasa alaqarsu da jawahir keda tsaho da kuma nisa,yasan cewa tana da sauqin kai kamar yadda take da surutu,amma banda daddynsu duk cikin gidan babu mai iya bata attention dinsa yadda takeso,shi yasa yake jumurin biye mata.

A handsfree ya saka wayar,har ya gama shanye yoghurt din daya tsiyayo,zuwa sannan ya soma cire socks dinsa saboda wanka da yakeson yi,ya gama jin cewa kaltum din na cikin gidan,saboda haka yayiwa jawahir bayanin zai shiga wanka,ya katse wayar,ya dauki qaramin towel ya shige bathroom din.

A hankali ta ajjiye littafin hannun nata,ta miqe ta zauna sosai kafin ta janyo dankwalinta me santsi ta daura akanta.

Tunani tayi ta fara samun ruwan dumi sosai tasha ko ruwan lipton ko xata samu sauqin cramping din da mararta keyi,don taga walida qawarta idan tana ciwon mara shi take sha,kuma cikin ikon Allah tana samun relief.

Kitchen ta isa kai tsaye,ta samu daya daga cikin masu aikin ta kammala komai,tana daukar cooler din tata abincin,wanda indai ta dauki cooler din ta shiga dakinta kuma saida safe,saboda tana da saurin bacci ne.

Dukkansu tsakanin kaltum dasu girmamawa ce ga junansu,da dan murmushin qarfin hali kaltum tace

“Har kwanciya baba?” Dariya ta danyi

“Tome zan zauna yi,gida babu kowa hajiyarmu bata nan,ai saida safe kawai kaltume….am…..amma ga abincinki nan tun na rana fa banga kinci ba” fuska tadan motsa kadan

“Yau banajin dadin jikina ne baba shi yasa” cikin fuskar alhini tace

“Ashsha….Allah ya sawwaqe,to ko za’a sanya hasanu(yaron gidan) ya yiwa yallabai samir magana ko dan qaramin dakin shan magani kije?” Kai ta kada tana mamakin dama yana gidan,rabonta da ganinsa tun ranar nan,ranar data tsaye mata a rai,take kuma yawan tuna abubuwan da suka faru a ranar

“Ruwan dumi xansha yanzu,ina kuma saka ran zanji dadin jikina”

“To….to Allah ya qara afuwa” da haka sukayi sallama,baba ta fice da flask din abincinta.

Tana tsaye ruwan ya tafasa,ta dauko cup ta juye ta dawo falo.

Tana daga tsaye take surbarsa saboda tana ganin kamar zaifi tsarga mata,tana gab da shanyewa taji motsi kamar an buda qofar falon,saita waiwaya a hankali tana dan jin tsoro ya kamata,duk da tasan cewa gidan cike yake da tsaro,babu wani abu da zai gifto su har nan.

A hankali yake takowa cikin parlour din,idanuwansa zube kam wayar hannunsa da yake amsa kiran dake shigowa,wanda handsfree ya sanya mata.

Yayi wani sassanyan kyau cikin wasu yellow din Kaya da sukayi matuqar fitar da sigar kyans da kwarjininsa.

Idanu suka hada shida ita,nauyin daya zuba ciki nata idanun ta hanyar nutsa nashi idanun cikin nata ya sanya ta janye kallonta,yayin da shi kuma yaci gaba da kallon nata yana ci gaba da amsa wayar.

Kamar kowane lokaci da zai dora idonsa akanta,zuciyarsa ta soma masa lissafe lissafe a kanta,baisan yana mata kallon from head to toe ba sam,koda wani ya fada zai iya qaryatawa,maganar amiru ta soma dawo mishi akan canzawarta,tabbas hakane,shima ya gani,ya hango abubuwa masu tarin yawa,kayan jikinta sunyi matuqar amsarta da haskata,baisan yaushe chocolate colour skin ta fara masa kyau a idanuwansa ba,murya can qasa yace

“Bye” yana katse wayar tare da sokata a aljihunsa,har yanzun kaltum dake tsaye yake kallo,wanda taci gaba da tsaiwar ne saboda a ganinta sam bai kyautu ta ganshi ba ta kuma wuce,duk da yadda takejinta a takure saboda kayan jikinta,wanda suka bayyana albarkatun qirjinta qwarai,don ta dauka daya daga cikin brasier din da jawahir ta sako mata cikin kayan.

“Ina yini” ta fada da zazzaqar muryarta ba tare data juyo ba,sautin ya tafi a hankali cikin kunnensa,yadan rage girman idanuwansa kadan

“Kina lafiya?”

“Alhamdulillah” ta amsa shi still ba tare data juyo ba,hakan ya bashi mamaki,tsaiwar me take ta bashi baya haka?,idanunsa saman hips dinta na wasu sakanni,saiya dauke kai,yana sake matsawa zuwa inda take tsayen,yana jin a ransa kamar akwai wani abu da take boyewa batason ya gani ne.

Koda ya qarasa din sai da yayi dana sanin zuwan,tsigar jikinsa ne ta dinga zubawa,ya dauke idanunsa ta hanyar daukan remote yana lalubar tashar da akace masa yau zasu sanya wasan polo live daga Amsterdam lokaci daya kuma yana bata umarnin

“Ki dauko hijabinki kizo muje” babu musu a tsakaninsu,ko wanne ciwo takeji a jikinta ba zata iya masa jayayya ba,don haka ta ajjiye cup din hannun nata da sauri ta juya ta nufi daki,duk da haka sai daya dan bita da kallo kafin ya sake janye idanun nasa yana sakin ajiyar zuciya.

Bata jima ba ta fito ta hijabin sallarta har qasa,ta sameshi ya bawa tv attention,da alamu yana jin dadin kallon,saita saci kallon tvn don ganin me yake kallo haka,a iya dan zamanta dasu ta karanci yana son doki da wasan dokin ma gaba daya,duk da haka haka ya ajjiye remote din ya miqe ta bishi a baya.

Kamar kowanne lokaci shuru ne ya musu rakiya har zuwa makeken kantin zamani,wanda yake maqare da dukka nau’in kayan amfani.

Yadda suke haba haba dashi ya tabbatar mata ba qaramin customer bane,kuma ba qaramin jin dadin zuwansa suke ba da alama,kujera ya samu nan ya zauna,yace ta shiga ta zabi dukkan abinda taga tana so,sai tayi saroro,saboda sam bata taba zuwa ita daya ba,yawanci da jawahir suke zuwa,daga bisani ta fara takawa a hankali a tana duddubawa har tayi nesa da wajen da yake zaunen.

Tayi nisa sosai cikin babban kantin amma haka taketa shawagi,ta kasa zaben wani abun azo a gani,saboda kome tayi niyyar dauka sai tayi tunanin me tsada ne,ta qyale kada taje a lafta masa kudi,saboda nan din ta fuskanci komai nasu kudi ne tsububu a cikinsa.

“Hey baby” taji an fada daga bayanta,saita waiwaya da hanzari,suka hada idanu dashi yana jifanta da murmushi,matashin saurayine wanda a qiyasce bazai wuce shekara ashirin da biyar ba,sanye da qananun kaya,hannunsa riqe da wayarsa,yana da kyau dai dai misali,hakanan kana kallonsa kasan dan gayu ne

“Bari na tayaki zaben,na fuskanci tun dazu kike yawo kin kasa daukan komai” kafin tace wani abu ya karbi dan kwandon hannunta,ya fara duba kayan mata na amfani yana jefawa a kwandon,yana kuma dan janta da hira ta yadda zata saki jikinta dashi.

Sannu a hankali ya fara cika kwandon da kayyakin amfanin mata,saita ci gaba da binsa a baya,duk da cewa amsar kowacce tambaya tasa daga eh sai a’ah.

Sun kusa qarshen layin da suke ciki,kamar ance ta daga idanu ta hangi samir a tsaye daga qarshen line din kayan turaruka,dukka hannayensa zube a aljihun wandonsa,ya kum tsaya qyam ya raba qafafunsa kamar wani soja,babu digon annuri a saman fuskar tasa,sai idanuwa daya kafesu dashi ita da saurayin……..

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button