Dabi’ar Zuciya 26
“Kaiiiiiii…..nine ma shaidan din da kike korata?” Auwalu wanda yake tsaye gabanta cikin duhun daren da hasken farin wata ya ratsa,kuma cikin yanayin dake nuna a dan buge yake yayi maganar,take hantar cikinta ta kada,bata maganar da ya fada ba take,tana lalubar hanyar da zata gudu ne kawai,don ta dade da sanin tarayyarsu irin wannan ita da auwalun babu alkhairi a cikinta.
Duk da ta kadun,amma hakan bai hanata aro juriya da qarfin hali ba,ta durfafeshi zata wuce,saidai tuni ya sake shan gabanta,yana tangal tangal kamar zai fada kanta,hakan ya sanyata ja baya da sauri,cikin tangadi yace
“Waikeeee……bakisan irin son da nake miki ba?,Allah saina aureki,ko duk garin basa so,ni babu ruwana da wata laure…..ita take haukanta ita kadai” yafada yana watsa hannaye,haushi ya cika kaltum,ta baro wani takaicin taci karo da wani,don haka saita watsa masa harara
“Allah ya kiyaye na aureka,me zanyi da kai?,kaga ni ka matsamin hanya na wuce gida,dare yana dada yi” tayi maganar tana neman hanyar wucewa cike da jarumta.
Bata ankara ba yasa hannu ya fincikota baya ta hanyar riqe hijabinta,kafin ta daidaita nutsuwarta taji yana cewa
“To ai shikenan,kin ragemin wahala,tunda bakya sona bari kawai ayi shortcut a wuce wajen” yana kaiwa nan ya fara yunqurin jawota zuwa gareshi,tare da turata wani sakaye dake daura dasu.
Matuqar tashin hankali taji ya rufto mata,don bata manta wancan ranar da makamancin irim hakan ya kusa faruwa ba,saita fara turjewa tare da neman mafita da matsera,saidai babu kowa wajen,duk wasu suna gida,samarin da ‘yammatan kuma mafi yawansu suna dandali.
Gigicewa tayi sanda yaja hajibinta,qarar yagewarsa ta ratsa kunnuwanta,saiga hijabin ya dawo kafada,sassalkan gashinta data manta rabon data kitseshi ya bayyana,saboda rashin dankwali da bata daura ba,saita cukuikuye hijabin tana sakin tsumammen kuka.
“Saki hijabin mana masoyiyata…..nifa aurenki zanyi Allah….ko babu goro da alawa…..” Ya fada yana niyyar kai hannunsa jikinta ya zarw yagaggen hijabin data cukuikuye cikin jikinta,saidai kuma bai samu damar aikata hakan ba,saboda hambarar dashi da yaji anyi,yayi taga taga ya koma da baya ya fadi dabas a qasa,ya daga kai don ganin wanda yayi masa wannan aika aikar.
Samir ne tsaye yana hadiye yawu,Adams Apple dinsa daya bayyana sosai saman maqogoronsa yana ta sama da qasa,abu guda dake saurin nuna cikin fushi yake
“Kaiiiiii……. wallahi kaci sa’a bacci nakeji,da yau na nuna maka kurenka,amma dai……idan mukayi aure ko?,ba zakaci taliyar gidana ba” daga haka saiya koma ya maida kansa qas ya kwantar hankalinsa kwance,kamar wanda ya samu katifar cikin dakinsa.
Tun isowarsa wajen dama ya fuskanci a buge yake,banda haka garjejen qato kamar wannan yadda ya hangi abinda ke faruwa daga nesa,inda ace cikin hayyacinsa yake,mawuyacine ta iya daqileshi daga abinda yayi niyyar aikata mata.
Tsaye cak yayi yana jin yadda take kuka bayan ta dunqule a qasa da barkakken hijabinta,kallonta ya danyi sannan ya dauke kai,kwanaki qalilan da fara ganinsa da ita,amma yaga abubuwa da yawa kanannade da rayuwarta,’yar qanqanuwar rayuwar tata da bata kammala ginuwa ba,abun sai yaketa bashi mamaki,tare da ganinsa wani bambarakwai.
“Ki tashi ki nunan hanya na rakaki” yayi maganar yana dan qara taku kadan zuwa gaba,ba musu zumbur ta miqe,saboda gaba daya tsoro ya gama kassarata,rakiyar dama tafi buqata fiye da komai.
Waiwayowa yayi kadan kana ya dauke kansa yana dakatawa da tafiyae daya fara
“Kina iya tafiya ke kadai idan ba zaki iya shuru ba,bazamu tafi a haka ba a dauka nina miki wani abu” yayi maganar da dakakkiyar muryarsa dake nuna zallar abinda ake nufi da nutsuwa wanda ke tattare dashi.
Dole ya dinga cinye kukanta,har ta samu yatsagaita,a sannu a sannu suke tafe,tana dai biye dashi,har zuwa sanda suka kusa da qofar gidansu,sai taga yaja ya tsaya daga baya yana goye hannayensa
“Ki qarasa,ina hangoki daga nan” saita gyada kanta,cikin dasashshiyar muryar kuka tace
“Na gode” kansa yadan daga kadan,kana ya bita da kallo sanda take nufar qofar gidansu.
A rayuwa bai tsammaci yarinya mai shekaru kamarta zata iya fuskanta da daukar nauyin matsalolin rayuwa ba,sai gashi a yau ya gani zahiri.
Kiran wayarsa da akayi yasa ya dauke idanunsa daga kallonta,sanda take takawa da wani irin tattaki kamar na bawa farin shiga,wa da ke tsoron shiga qangin bautat da baisan zafa bulle masa ko akasin hakan,matsasttsen kuma siririn qugunta na sake bayyana muraran.
Idanunsa ya mayar kan wayar bayan ya zarota,Aamiru ne,fushi yake dashi,saboda haka ya katse kiran ya jefata aljihunsa,yana maida dubansa gareta,dai dai sanda take shigewa gidan gaba daya.
A qalla ta kusa minti biyar tsaye a soron tana qoqarin dai daita yanayinta da nutsuwarta,saboda batasan shiga da yanayi da zai sanya hankalin ummansu ya tashi,don ta tabbata ko yaya yanayinta ya sauya,tana da saurin gane hakan.
Sallama tayi cikin qoqarin son dai daita muryarta,ummansu ta amsa sannan taci gaba da shafa man da takeyi a jikinta,saboda iskar sanyi dake saurin busar mata da jiki,bilalu na zaune saman kujera ‘yar tsugono da kwano a gabansa yana cin abinci,danqararriyar dafa duka da sukayita tun kusan azahar,shinkafa mai tarin tsakuwa,wadda saida kaltum tayi tsaiwar gwamin jaki sannan ta samu nasarar gyarata,duk da haka baka kubuta ba,daga sanda ka fara cin abincin zuwa kowanne lokaci kana iya cin karo da tsakuwar da zata kashe maka haqora su kasa moruwa.
Bilal ne ya daga kai yana yiwa kaltum magana,saidai batajin zata iya tsaiwa ta biyewa shirmensa,hakan dai dai yake da ummansun ta gane yanayin data shigo cikin gidan dashi
“Kaina ke ciwo bilalu,kwanciya nakeson nayi” ta fada,sai umman ta bita da kallo,duk da ta shinshino damuwa cikin muryarta,amma ayau din bata matsa ba,saita bita da addu’ar
“Allah ya sawwaqe,ya bada lafiya”
Ta jima cure waje daya cikin shimfidarta tana fitar da qwalla,wai me yasa mutuncinsu da darajarsu ba komai bane wajen ‘yan uwansu,kowa da irin salon tozarcin da zaya zo dashi cikin rayuwarsu.
Ta dade a haka,tun tana jin motsin su umma sama sama harta dena ji sanda babansu ya shigo gidan,da alama kowa ya kama gabansa an bar masa filin tsakar gidan,kamar yadda ya zame musu jiki tsahon rayuwarsu,saboda koda shigowa yayi ya gansu zaune a tare waje guda,tofa bashi da aiki sai muzurai,da kuma fadin maganganu marasa dadi,yakance gulmarsa suka zauna sunayi ba wani abu ba,su da munafukar uwarsu.
********Yana tsaye daga a qofar gidan daya kasance masaukinsa ne cikin qauyen,sanye yanke da riga mai dogon hannu da wandonta,wanda suka fi kama da jessy,duk da ba jessy din bane,amma sun masa kyau sosai.
Hannunsa daya riqe da mug wanda ke cike da hot black tea,duk da cewa yafi sha’awar shan coffee amma baya tunanin xai sameshi a dan qauyen nan,dalilin da yasanya dole ya haqura yayi amfani da abinda ya samun.
Zamansa a qauyen yana masa dadi ta fuskoki daban daban,yana ganin yanayin rayuwa da dabi’u iri iri,a yanxun haka yadan saba da wasu daga cikinsu,yakan xauna da yammaci suyi hira dasu wani lokaci can qarshen layin da yake ciki.
“Barka da safiya sir” yaji am furta daga gefansa,koda bai waiwayo ba yasan waye,hakan yasa bai juya ba illa amsa masa da yayi yana ci gaba da kurbar tea dinsa
“Barka kadai,ka tashi lpy umar?”
“Lafiya lau og,jiya kuma saika tafi ka barni ba tare da nasan ka taho ba?”.
Dan qasa yayi da cup din yana sakin murmushin gefan baki
“Ina fatan ka fara irgen ranakun aurenku da yarinyar daka tsaida jiya”
Idanu umar ya fitar waje yana duban samir daya bashi baya
“Aure kuma sir?,ai ba aure zamuyi ba”
Murmusawa ya sake yi,da alama yau da ‘ya miskilanci ya tashi
“Koma yaya ne ka shirya,kaga gaba ka sake tsaidama wani yarinyarsa”
Cikin alamu na nuna damuwa yace
“Am sorry sir,kawai nima na dan gwada ne…..” Kadan samir ya waiwayo ya kalleshi,dariya na motsa masa kadan kadan cikin ransa,ya gane sarai abinda umar din yake nufi,kawai ya fada masa ne saboda kada shi ya zarme da yawa ya kuma zarma wata azo ana dogon turanci
“Kayi a hankali….kada daga zuwa aiki ka koma gida da mata” kansa yadan sosa,yana qiyasta yadda hakan zata faru yana murmushi
“Allah ya kiyaye sir…..za’a kula in sha Allah”
Baice dashi komai ba,saiya waiwayo yana miqa masa mug din hannunsa,yasa hannu ya karba ya juya zuwa cikin gida dashi.
Yana dab da shiga samir dake biye dashi yace
“Ka kiramin hannafi,kace mishi ina son ganinsa”
“Yes sir” umar din ya amsa suna shigewa gidan gaba dayansu.
Kamar jiran shigarsa ciki akeyi wayarsa ta dauki qara,ya soma lalube zuwa inda ya ajjiyeta,kafin yakai ga dagawa ta zama miscal,saiya shiga duba kiran daya rarrasa da safen,saboda barin wayarsa da yayi cikin gida.
Missed call ne guda tara,biyu daya na fauza,uku na salimat duka abokan aikinsa,wadanda suke son sanya kansu cikin rayuwarsa,rayuwarsa kuma baiga gurbin da zai basu ba komai qanqantarsa.
Kiran mummy da auta su suka biyo baya,sai jauhar wadda yakan manta da babinta ma gava daya,yayi dan qaramin murmushi ganin miscal din jawahir yana ci gaba da duba kiraye kirayen,yasan duk yadda akayi akwai abinda takeso ta gaya masa.
Miscal din salisu yaja hankalinsa daya gani barkatai sama dana sauran,kuma dukka kiransa yafi na kowa muhimmanci a wannan lokacin,don haka ya fasa kiran duk wanda yayi niyya,ya maida akalar kiran zuwa ga kiran salisu.
Saidai ko shiga batayi ba yunqurin kiran ya yanke,kiran jawahir ya danno kai,dole ya daga,saboda yasanta sarai yanzu saita masa mita,hakan nan ya daga yana kara wayar a kunnensa,bayan ya samu gefan katifa ya zauna yana miqe dogayen qafafuwansa.
“Yaayaa…kama manta damu ko?” Ta shigar da qorafinta cikin shagwabar data zame mata jiki
“Auta rigimar gangan,shekaran jiya mafa ina jin munyi waya ko?”
“Amma yaaya kace zaka kirani baka kuma kirani ba,nikam wannan karon inajin zan biyoka naga aikin daya riqe ka yaya a qauyen nan” murmushi ya qwace masa,har sai data jiyo sautinsa kadan,ya jujjuya idanunsa yana kallon irin dakin da yake ciki,shi kansa yayi mamakin yadda ya zauna a qauyen bai wani damu ba
“Wannan qauyen….ba zaki iya zama a cikinsa ba auta”
“Why yaya?,me yasa kai ka zauna,nima zan iya” fuskarsa a fadade da murmushi yace
“Akwai alot of funny here, amazing abubuwa da suka bambanta da gida,i assure you will enjoy it…..but,ba zaki iya zama ba,daddy ma bazai barki ba,baki gani nima yadda yake qalubalantata ba?”
“Amma yaaya…..”
“Ke mayya,ki haqura” ya tsinto muryar najwa ta cikij wayar tana fada cikin tsawa,da alamu da jawahir take,taji abinda suke tattaunawa ne
Shuru suka danyi dukansu,shi yana jin yadda tsawar ta ratso har cikin wayar da sukeyi
“Yaaya” jawahir ta fada a shagwabe,ranta kuma a dan bace
“Bata wayar” yace da ita kai tsaye,yanajin sanda ta miqa mata wayar ta amsa
“Yaya….barka da asuba” baibi takan gaisuwarta ba,don bayau ta fara irin wannan dabi’ar ba idan suna waya,yana iya jin yadda takan hantari jawahir din
“Kiyi dukka iya tunanin da zakiyi,ki samu abun fada min randa na qaraso gida kan dalilin da yasa kikewa auta hakaβ¦…bata wayar” cikin tsorata da sanyin jiki ta bude baki da niyyar baiwa kanta kariya,cikin tsawa tsawa yace
“Shut your mouth…..ki bata waya nace” hakanan badon taso ba ta miqawa jawahir wayar tana jifanta da harara,qasa qasa yadda bazaiji ba tace
“Munafukar Allah” batabi ta kanta ba ta amsa wayar tana maidawa kunnenta,daga can inda yake ya daga wayar daga kunnensa yana kallon screen din jin alamun kira yana shigowa,sai yaga salisu ne still,don haka yace da ita
“Auta….i will call you in the evening in sha Allan”
“Ok yaya” ta fadi tana katse kiran,yayin dashi kuma ya daga kiran salisun.
“Banza kawai asararriya,wallahi duk abinda kika sanya yayimin a kanki zan huceshi,kuma aishi din ba Allah bane,sai yazo din,idan yaso ya kulleni a kurkukun bayan duniya ya jefa maqullin teku,ko kuma ya zaremin raina” ta fadi zancan cikin son nuna bata damu ba,duk kuwa da yadda ranta ke cike da fargaba,don sunfi kowa sanin waye saraki idan ransa ya baci,jawahir bata ce komai da ita ba sai data miqe tsaye ta saita hanyar daki
“Oho dai,ke kika jiyo kuma,ni ba matsalata bace” da hanzari najwa ta yunqura zatabi bayan jawahir data qara wuta ta shige dakinta tana shirin kulle qofa,saidai kaifafan idanuwan mummy suka maidata suka zaunar,mummyn ta qaraso wajen,ba tare data zauna ba ta dubeta
“Ki dinga yawan tunawa da cewa,’yar uwarki ce da baki da kamarta kaf fadin duniya”
Ran najwa a bace tace
“Momy kina gani fa,yasa ta soma rainani” saida mommyn ta fara tafiya ta bata amsa
“Ke kika ja,tunda kika kasa riqe sandata domin ta yimiki jagorancin da bazaki fada kwata ba bare rami” shuru najwa tayi tana jujjuya zancan momy a ranta,saita miqe zumbur tabi bayanta,dai dai sanda daya daga cikin ma’aikatan gidan ta fito dauke da farantin data shiryo kayan ciye ciye a kai
“Ranki ya dade gashi an kawo”
“Koma dasu kitchen” najwan ta bata umarni tana ci gaba da tafiya sauri sauri zuwa dakin mommyn ba tare da tako juyo ya kalleta ba,saifa girgiza kai tana juyawa da uban farantin zuwa inda tasha wahalar shiryo kayan da sai da iyayenta suka zagu kamin ta gama lissafa mata dame dame takeso.
Cike da girmamawa ya gaidashi,sannan ya fara shigar masa da dalilin kiran,baqi gareshi,’yan qasar china dakeson zama dashi,an masa saqo ta email dinsa saidai basu samu respond ba,sai a sannan ya tuna cewa yabar system dinsa a gida wancan zuwan da yayi
“Am on my way jibi in sha Allah,ku shirya dukkan abinda ya dace,daga wannan karon ina saka ran zuwa daya xanyi na gama zuwa,zan bar ragowar aikin a hannun mutanen da aka amince dasu na dawo muci gaba da aiki,but….kada ka shaidawa kowa ranar dawowata”
“Yes sir,in sha Allah” daga haka sukayi sallama,dai dai lokacin daya ji muryar hannafi daga bakin qofa yana neman izinin shigowa.
Izinin yayi masa,hannafin ya shigo ya samu waje ya zauna yana gaidashi cikin girmamawa,ya amsa masa,suka dan tattauna kan batun gini,da abubuwan da za’a qara siyowa na kayan aiki,kusan komai akwai,langa langa kawai za’a dado bandir daya,suka lissafa abinda zai isa,ya bashi harda dori,saboda kusan da wuya yayi aike ya baiwa mutum kudin kai da kai.
Har hannafin ya miqe saiya tuna
“Nace a garin nan akwai teloli?” Murmushi hannafi yayi
“Yallabai akwaisu,amma kamar ba zasu dace da tsarinka ba” baibi takan zancansa ba yace
“Hijabai nakeso guda uku,daga nan zuwa anjima,zan samu?” Kai hannafi ya gyada
“Zaka samu sosai,yau kasuwar mafara take ci,ko a can saina gangara na siyo maka”
Baice komai ba,ya zaro wasu kudin ya miqa masa,hannafi yasa hannu biyu ya dafe sanna ya fice yana masa sallama.
A iya qaramin karatunta da tayi,da kuma dan wayewar data samu game da yanayin yadda karatu yake daga bakin nasuru,da kuma sanin data yiwa makarantar garin nasu,bata taba jin inda suka diba daliban J.s 3 aka tafi kaisu wani waje ba,koda na wuni daya bama bare akai ga kwana,sai gashi ita asiyan ta qirqiro qaryarta tayi mata fenti,iyayenta sun sanya hannu bibbiyu sun amsa.
“Allah ya kyauta” ta furta cikin zuciyarta,tare da tattare duk wani abu daya shafesu ya watsar gefe,abinda ta sani kawai shine,wanda baiji bari ba zaiji hoho.
Abu na farko data lura dashi kallo da wani lokaci akr binta dashi,idan ta hadu da wasu mutanen
“Akwai wata kenan” ta gayawa kanta,tasan dabi’a da halayen mutan qauyensu kaf,mutanene da basu raina abun magana,sun iya gila gutsiri tsoma da yanyana magana,don haka saita qara kama kanta,har ta isa gidan habiba.
Ta samu habiban jikinnnata da sauqi,laulayin nata ba wani mai zafi bane,kamar ta dauki kaltum ta goya,saboda ba qaramar sa’a bace zuwan kaltum gidanta,ta karba dambun tana murna,ta dibawa surukarta takai mata,baban ta amsa kuwa tana ta godiya,surukar arziqi kenan,wadda ta dauka habiba kamar ‘yar cikinta.
Sanda kaltum din tayi yunqurin tafiya hanata habiba tayi,ta tareta da hira,duk a yunqurinta na qata ragewa kaltum damuwa da debe kewa,don ganin farko tayi mata taga ta rame,hakanan babu zafin nan data santa dashi.
Duk da haka saida kaltum din ta yakice tace gida zata,ba hala habiba taso ba,amma bata sake matsa mata ba sukayi sallama,baya ta dauki hijabi guda biyu ta bata,hijabin da sai da akasha dambarwa kafin ta karba,har sai da babar yusufa tasaka baki,ta fita babar yusufan tana binta da kallo,cike da tausayinta,lallai inda ace tana da wani yaron bayan yusufanta,da sai ta sanyashi auren kaltum din,tana bata tausayi qwarai.
Kan hanyarta ta komawa gida ta yake shawarar leqawa gidansu lantana,a jikinta takejin akwai wata matsalar kuma,bata kuma fatan wata matsalar ta sake tunkarota a yadda take,tasan ba zata rasa jin abinda ke faruwa daga bakin lantana ba.
Ta tarar lantanar bata nan,innarta ta aiketa gidan yayarta,tace amma ta jima,don haka tana gab da dawowa,tayi tayi kaltum din ta jira amma tace a’ah zata gida,idan tazo a gaya mata.
Saidai tana fita qofar gida sukayi kacibus da lantana tana dawowa,fuskarta cike da fara’a da kuma ganin kaltum din agidansu tace da ita
“Wai….batan kai kikayi ko umma ce ta aikoki?”murmushi kaltum tayi da busashshiyar fuskarta
“Wajenki nazo kuma ban sameki ba” lantana tana qarasowa waje tace
“To ai gani na dawo,da tafiya zakiyi kenan ba zaki jira na dawo ba?” Ta fadi tana kama hannun kaltum zuwa cikin gidan
“Sauri nake wallahi,ban cewa ummanmu zan biyo ba”
“Idan kika ce mata nan kika biyo ba zata ce komai ba,ummanku da innata qawayene,inna laure ce tasa babanku yayi silar daina zuwansu gidajen juna da shegen kitsa gulma da munafuncinta…..inna na dawo” ta hade maganar tata da shaidawa innar tata dawowarta,tana jawa kaltum abun zama
“Yauwa….ashema kun hadu,yanzu nake shirin shaida miki ai tazo” inna data leqo daga daki ta fada
“Eh wallahi inna,a qofar gida mukayi karo” lantana ta amsa mata tana daukar kofin silba,ta ciko ruwa a randa tasha,sannan ta sake debo wani ta ajjiye gaban kaltum din sannan ta zauna tana dubanta
*_Assalamu alaikum masoya ‘yan cikin gidanmu na zafafa,fatan alkhairi a gareku tare da fatan dimbin nasara a rayuwarku,ina mai shaida muku cewa in sha Allahu nawa hutun xai kasance juma’a da asabar,saboda nawa jadawalin rayuwar nafi buqatar hutun juma’ar saboda shine nake da issue da itaππ,nasan in sha Allah hakan ba matsala bane,kunga zai kasance ranar washegarin randa ‘yan uwana zasu je hutu xaku samu guda daya da zai tayaku zama,ina fatan muna cikin wadanda xami rabauta da juma’ar,MUN GODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR_*
#TEAM ZAFAFABIYAR
ANA TAREβπΎβπΎβπΎ
27
D/Z
ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½
*Kada dai ku gaji,ga tashar dan uwanku,danku kuma qaninku SUDAIS tana buqatar gudunmawarku,shiga kawai zakuyi,ku dannan maballin SUBSCRIBE,ku kuma kunnawa yara ‘yan uwansa dake gida su dinga saurara don zaburar dasu suma*
*Jazakumullah bi ahsanil jazaaa*ππ½ππ½ππ½