Dabi’ar Zuciya 21
A daren ranar suna zaune a tsakar gida saboda yanayin zafi,ummansu na qofar dakinta,haka babansu na nashi qofar dakin qarqashun rumafarsa ta bunu,yaci ya qoshi da abincin da bashi ya nemo ba,yana zaune kuma ya kunna radio gamida kasa idanunsa a tsakaninsu,yana neman wani dan qaramin dalilin da zai sanyashi ya bude faifan bala’insa,dole ce ta sanya kaltum itama zama qofar nata dakin,dukkaninsu ba’a sake suke ba,saboda zamansa a tsakaninsu babu abinda yake haifarwa sai da mara idanu,da zarar ya gansu a zaune tare zaice sun hada kai suna munafuncinsa ita da ‘yarsa,don haka matuqar yana nan din sun gwammace su raba wajen zama.
Addu’a kaltum take cikin ranta kada Allah ya shigo da bilalu,ta tabbatar idan har ya shigo din sai baban nasu ya samu abun fada.
Sallamar munzali ce ta ratso tsakar gidan,ya shigo hannunsa dauke da buhu,ummansu ta amsa masa tana miqewa ta zauna sosai daga jingina bayanta da tayi.
Fuska babu fara’a ya gaidata ta amsa masa cikin kulawa,idan da sabo ta saba da wannan halayya da dabi’a tasu,kai bakace itace ta rainesu ba a sanda mahaifiyarsu ta fita tabar gidan ba,sam babu wani halacci kara ko kunya a tsakaninsu,duk da cewa da wayonsu ta samesu,amma duk sauran hidima da yaro ke buqata kafin zamowarsa cikakken mutum ita ta dauki gabarar yi musu ita har zuwa sanda sukayi aure.
Ta gaban kaltum ya wuce,wadda take ta gaidashi yayi watsin tsiya da gaisuwarta,saima harara daya balla mata,ya qarasa gaban baban nasu,yaja kujerar mata ta tsuguno ya zauna akai ya soma gaidashi
“Ya akayi munxali?” Baice komai ba sai zazzage kayan dake cikin buhun da yayi,ya soma ware wasu gefe wasu kuma yana miqawa baban.
Sai daya ware jallabiya kala hudu,takalmi da agogo,da hular tashi ka fiya naci da kudi ‘yan dubu dubu guda hudu ya miqawa baban
“Gashinan inji innarmu tace a baka”
“Allahu akbar kabiran,hajjaju mutan saudiyya,ta dawo ne?” Ya fadi cikin wata madaukakiyar fara’a data baiwa kaltum mamaki,ta kuma sanyata kallon ummansu,saboda ita dai bata saba ganin hakan ba,saidai suna hada idanu ta dauke kanta,saima ta janyo wani dan abun hannu na duwatsu me kyau nata daya katse dazu taci gaba da gyarashi,kanta yana kallon qasa
“Bata dawo ba,ta dai yo aikene,ni da muzammilu da sani da muka ce mata muna son jari” ya fada yana jin haushin baban nasu can qasan ransa,saboda har yanzu bai manta yadda babar tasu tasha wahala hannunsa ba kafin ya saketa ta tsallake zuwa saudiyya neman kudi
“Ma sha Allahu,kai Allah ya saka da alheri”
“Wata shekarar take saka ran zuwa,zata tafi damu muyo umara”
“To madalla alhaji munzali,ince dai baku manta dani ba?” Sai daya miqe tsaye sannan ya bashi amsa,saboda ya soma gajiya da yadda yake fidda son zuciyarsa quru quru,baya ma tuna abinda shi ya aikata a baya
“Idan Allah ya kiraka kaima sai kaga ta biya maka ai”
“To Allah amin” ya fada yana jujjuya kayan hannunsa,wanda ba’a taba masa kyauta irin haka ba tunda yake.
Har munzalin ya gota kaltum saiya dawo da baya
“Ke kattume” ya kirayeta sa qarfi
“Na’am yaya” ta amsa tana daga kai da hanzari
“Rannan nazo nemanki ban sameki ba,bansan me kika yiwa fiddau ba,nayi nayi ta gayamin taqi,wallahi ki kuka da kanki duk randa ta shaidan naji rashin mutunci kikayi mata”
“Kaga yaya fa ba…..”
“Rufemin baki!” Ya dakata mata tsawa,sannan ya shura takalmansa yayi gaba abinsa,saita bishi da kallo,a lokacinne kuma baban nasu ya dira nasa
“Wani diban albarkar hala kika yi musu?,ke wai me yasa kike da daukar magana kamar ‘yar Allah ya bani?,to wallahi indai kuwa taba munzali ko ahalinsu kikayi nima ba qyaleki zanyi ba,shashasha mara lissafi,shi yasa qanwarki ta tafi dakin miji ta barki ke gododo a zaune” shuru tayi harya kammala jafa’insa ya koma kan murnar kayansa,yanata yada magana da habaici,kanzail ummansu batace masa ba,sai kaltum ta fara tattare shimfidarta jin ya koma kan umman tasu daya fuskanci bata da niyyar kulashi
“Wato saboda tsabaragen baqin hali da kishin banza,kin kasa yiwa uwar yaron nan godiya….a gabanki ya kawo kayan nan,kuma koda ya tafi ma kin gaza daga kai ki tayani murna” a hankali ta daga kanta ta dubeshi sau daya
“Allah ya sanya alheri,a kashe lafiya” daga haka ta maida haka ta maida kanta taci gaba da abinda takeyi,saidai duk da haka shi hakan baiyi masa ba,haka yaci gaba da qananun mitocinsa kafin ya tattara ya shige daki yana yiwa kayan boyo na musamman,tare da qiyasta sanda zai sanyasu.
*********Jawahir najwa da jauhar ne tsaye a farfajiyar gidan,sai saraki dake tsaye gefe guda sanye da wasu qananun kaya da sukayi masifar fitar da kyau da kuma kwarjininsa,hannunayensa gaba daya zube cikin aljihun wandonsa,ya zubawa motarsa a aka gama wankewa ana gogeta idanu.
Fita zasuyi zuwa gidan hajiya qarama,wanda mummy ce ta shirya fitar,da sunan yaje ya kaisu su gaidata,a gaban idanun daddy ne,don haka bashi data cewa,bama wannan ce damuwarsa ba,yadda yaji suna tsiro da zancan zuwa azare,abinda sam sam yakejin bada shi xa’ayi ba,zuwansa azare tare da jauhar kamar ya bada lasisin dake nuna amincewarsa da aurenta,saboda tafiyar zata zamana tamkar tattakine na nuna jauhar ga dangin mahaifinsa.
Horn ake saki a bakin gate din,wanda hakan yaja hankalin samir,saboda yadda ake danne horn din babu qaqqautawa,hannuwansa ya sauke yana duban gate din sanda malam salahu ke rawar jikin budewa,kauda kansa yayi sanda motar ta shigo,ba kowa bane sai fawwaz,don haka ya taka zuwa gaba,ya bude motar kafin ya qarasa gabanta,ta bada wata ‘yar qata ta security,hakan yaja hankalinsu jawahir suka matso suma sannan ya saka key ya bude.
Dakatawa yayi daga qoqarin shigar da yakeyi saboda jiyo muryar fawwaz cikin fada yana yiwa malam salahu fada,wanda a qalla ya kusa haifarshi idanma bai haifeshin ba,qafarsa daya zura cikin motar ya cire,yaja rigarsa qasa ya gyara ta sanna ya fara takawa zuwa inda suke tsayen
“……..dukka alamu sun nuna bakasan aikinka ba” kalmar qarshe da samir din yaji daga bakin fawwaz kenan,wanda ke tsaye gab da malam salahu,kamar me shirin gabza masa mari
“Baba” samir ya kira malam salahu cikin nutsuwa,waiwayowa yayi cike da girmamawa
“Na’am dana”
“Lafiya….meya faru?” Fuskar cike da alhini da alamun rashin jin dadin cin fuskar da fawwaz din ke yawan yi musu matuqar zai tako qafarsa cikin gidan ya shaida masa cewa,yana bayan gida yana fitsari ne sanda ya iso,kuma yana fitowa yazo ya bude masa,ya masa bayanin dalilin jinkirin nasa amma yace bai yarda ba.
Idanunsa samir ya dauke daga kan malam salahu zuwa kan fawwaz,wanda duba daya zaka masa ka hangi yanda ransa ya sosu dajin abinda fawwaz din yakeyi,idan bai manta ba shi akaran kansa wannan ba shine karon farko da fawwaz din ya aikata haka a gabansa ba,amma a yau din yakai maqurar da bazai iya qyaleshi ba
“Kayi haquri baba don Allah kaji?” Cewar samir da sassanyar muryarsa bayan ya maida.ganinsa ga malam salahu
“Babu komai dana,ba komai” ya amsa masa cikin nuna girmamawa yana cakude tafukan hannayensa waje daya,sannan ya motsa ya bar wajen,samir ya bishi da kallo cike da tausasawa.
“Ji mana” samir ya fadi sanda fawwaz ya gyara kwalar rigarsa yana shirin barin wajen zuwa cikin gida,dakatawa yayi fuskarsa a daure ya waiwayo yana duban samir din
“Kayi qoqari wannan ya zama karo na qarshe da irin haka zata sake faruwa takaninka da duk wani ma’aikaci na gidan nan,don mu muna girmamasu…..saboda daraja ta fifiko da tazarar shekaru da Allah ya bamu tsakaninmu dasu,banason na sake ji ko na sake gani,nan gidan akwai ɗa’a” ya qarashe maganar yana gyada kanshi,sannan ya taka zuwa wajen motarsa ya barshi a nan,cikin zuciyarsa yana jin zafi,saboda ya fuskanci maganarsa ta qarshe tamkar baqar magana yake gaya masa,gugar xana yake masa kenan?,qwafa yaja cikin ranshi yana fadin
“Idan kere na yawo,zabo na yawo…..” Yasa kai zuwa cikin gidan da sassarfa,samir dake qoqarin tada motar ya bishi da kallo,abubuwa masu tarin yawa suna kaiwa da kawowa cikin qwaqwalwarsa.
Tunda ya shiga motar ya zama tamakar kurma,duk yadda jauhar taso jansa da hira bata samu damar hakan ba,gwanine idan yaso miskilanci,duk da cewa bawai halayyarsa bace,hasalima mutum ne shi mai son ababen nishadi da abinda zai sanyashi dariya,saidai a wannan karon ya ari wata halayyar ta daban.
Jawahir da dama kusan tafi kowa sanin halayyarsa,tunda ta fahimta hakan bata sakoshi cikin zancansu ba ko sau daya,kusan magana daya biyu sai jauhar ta tambaya jawahir wani abu game da samir din,duk da yaqi bata hadin kai suyi hira yadda taso har suka kawo gidan hajiya qarama.
Da fara’a ta tarbesu,kamar yadda take da karrama baqo,duk da cewa mafadaciya ce,amma tayi gadon karamci da kuma dattako gami da halin qwarai.
Sosai jauhar ta sake cikin gidan,duk da cewa hajiya qarama bata ganeta ba,amma ta karbeta kamar yadda ta karbi su najwa,saida suka kebe da samir sannan ta samu sararin tambayarsa
“Saraki wannan fa?” Ajiyar zuciya ya sauke yana shafa fuskarsa har zuwa tsakiyar kansa,yama rasa makama da kuma ta yadda zai yiwa hajiya qaraman bayani
“Kayi magana mana,sai wani faman shafa gemu kake,ko labarinsa na tambayeka?” Ta fada tana hada fuska,saiya saki murmushi yana gyara zamansa
“Yadda kika ganta nima haka naganta hajiya,saidai ita yarinyar da bakinta ta gayamin manufar zuwansu shine a hada aurena nida ita….” Shuru hajiya qarama tayi tana nazari,a yau idan samir ya tashi aure tanajin babu wanda zai kaita farinciki,koda kuwa mahaifiyar data haifeshi ne,saidai tana tsoron daga inda aka qullo masa matara auren akeso a cusa masa ita,don ko sau daya bataji zancen daga bakin yayanta ba,to amma ba zata yanke hukunci da kai ba,don haka ta gyara zama tace dashi
“Waye gwanin hadin?” Hannunsa yadan jujjuya alamun shiga rudani
“To abundai gashinan hajiya,abinda na lura daddy da mommy dukka suna son abun” faduwa gabanta yayi,haka nan a take zuciyarta taji abun bai mata ba,ta yaya za’a kawo wa samir din matar aure,kuma wai da hadin gwiwar mommy a cikin lamarin,sannnan ta zauna tana ji tana gani?,ba zata lamunta ba
“Yanzu kai wannan mai zubin ruwan askin tayi maka kenan?” Dariya ce sosai ta qwace masa,ko banza idan yazo gidan hajiyan yana samun nishadi ko na minti kadan ne,hajiyar zuma ce,ga zaqi ga harbi,saidai tana da wani baban gurbi a zuciya da kuma rayuwarsa,qoqarin daidaita kansa yayi saboda harara da yaga tana jefa masa,sannan ya tattara kalaman da zai gaya mata
“To hajiya ni ya zanyi…..,gaba kura baya sayaki,kinsan sarai yadda muke ciki da Daddy,duk abinda zan aiwatar komai kyansa kawai gani yakeyi ina yine saboda na qalubalanci ra’ayinsa,tunda naqi siyasa sai yake ganin komai ma da zanyi bashi da wani muhimmanci ko fa’ida” tsaki hajiya qarama taja ta tabe baki
“Wanna duk makircin jidda ne bana wani ba…..to idanma kana so ka fiddata daga zuciyarka tuntuni,idan kuma bata ma shiga zuciyar ba to ka hutawa ranka” tana fadar maganar ta kama kanta hadi da shan mur,batajin har abada zata sake bawa jidda wata qofa komai qanqantarta,ta yadda koma a ina samir ya samo matar aure,amma zabin kansa da kansa,bawai zabin hadin gwiwa ba,koma ya zamana zabi daga bangarenta ita daya.
Wani sanyi yaji ya ratsa zuciyarsa,ya tabbatar mafita tazo masa,tunda hajiya qarama ta qyamaci abun to yana sanya rai babu shakka komai zai warware cikin sauqi,kuma koda laifinsa zaizo a cikin lamarin a wajen daddy,to zayazo ne da kaso mafi qanqanta.
A nan gidan ya barsu ya wuce green garden abinsa inda yayi zasu hadu da Ezekiel saboda hada takardun neman kwangila daga qarshe ma saiya turama jawahir tex kan idan sun gama abinda zasuyi su wuce gida ba yanzu zaya dawo ba.
Sannu a hankali take takawa cikin duhun magaribar,wanda ya mamaye ilahirin duniya gaba daya,ya kuma cakuda da sassanyar iskar dake nuna gabatowar lokacin sanyi kowanne lokaci.
Za’a iya cewa yawaitar duhu tafi a qauyen fiye da haske,saboda rashin wutar lantarki da basu da ita.
Iskar ke kadata daga hagunta zuwa damanta,a gajiye take tubus,ga wata bahaguwar yunwa data kwaso,kan hanyarta kenan ta komawa gida daga gidan inna,wanda matar qaninta ta haihu,ta kuma umarce taje ta yiwa mai jego kitson suna.
Da fari taqi zuwa,saida ummanta ta mata da gaske sannan ta shirya taje,saboda ranta ya baci sosai da yadda akaja baki akayi shuru,babu wanda ya shaidawa umman tasu haihuwar,saida tasu ta taso nason ayi musu kitso sannan aka nemeta,duk da kadaram kadaham suka karbeta,babu yabo babu fallasa,saidai bata yarda ko ruwan gidan ya shiga cikinta ba,bayan an gama abinci an dire mata,tace ta qoshi,daga haka inna tasa aka dauke ba’a qara mata tayi ko bi ta kanta kan taci din ba,haka ta nado yunwarta ta wuni guda tayo gida da ita.
Tana gab da isa gidansu ta hangi mutum jingine a qofar gidan nasu,ya harde hannunsa a qijri ya zubawa hanya idanu,da fari tayi tsammanin nasuru ne,saboda jiya ya dawo bayan kammala jarabawarsa,a yau kuma yace ta tsimayi zuwansa,saidai data matso kusa sosai sai taga bashi bane,don haka bata wani maida hankali kan ganin wanene ba ta tasamma wucewa zuwa soronsu.
“Ke kattume…..ke!”
Ta jiyo kiran kamar daga wata duniya ta daban,wanda hakan yadan razanata,ta waiwaya baya da sauri,sai taga yaya munzali ne,yana dosota tamkar zai tashi sama,sai qura yake tadawa kamar wanda ala bugawa kugen yaqi.
Cak ta tsaya tana dakonsa har ya qaraso,abu na farko data fara ji shine saukar wani lafiyayyen mari a kuncinta na hagu da dama,wanda hakan yasanya duk wata wuta ta jikinta daukewa,ta daina ganewa tsayin wasu sakanni kafin sadarwa jikinta zuwa kwanyarta ta dai daita,qara takeson saki amma kamar an riqe mata murya saboda tsananin zafi,kalamansa suka fara shiga kunnuwanta kamar saukar kibiya,wanda sai daya fara da manya manyan ashar sannan ya dora
“ashe ‘yar iska ce ke tantariya?,shegiya mara mutunci kawai,yau kuma ta kaina iskanci da fitsarar taki zata biyo?,to wallahi baki isa ba,don ni ba sa’anki bane”
wani irin ciwo kalamansa suka saukar mata a zuciya,batasan sanda hawaye ya sulmiyo mata ba,tafin hannunta biyu dafe da kuncinta,a sanyaye tace
“Me nayi maka yaya?” Shuri yakai mata da qafarsa,wanda badon tayi hanzarin ja da baya ba tabbas da taji jiki
“Ni kike ma tambaya?,ashe iskancinki yakai kije har gidana ki ciwa matata mutunci ki qala mata sharrin sata?,banda ita din mai hankali ce dakai zuciya nesa kikasan me hakan zai haifar muku?,don u*****rki ni baso nayi ta kamaki tayi miki mugun duka ba inga uban daya tsaya miki ba?”
Kalmar uwarta daya fada ita tafi komai bata mata rai,zuciyarta ta fara motsawa,bakinta ya gaza dannewa
“Uwata yaya?” Ta tambayeshi tana dubansa kai tsaye
“Eh uwarki an fada,ke mai uwa ko?,dama ance idan aka zageta bakya qyalewa,to a fada don u****rki don u***rki”
“Badai uwata ba wallahi,badai uwata ba”.
Gadan gadan ya yiwo kanta yana fadin
“Saidai tawa,sai tawa kike nufi?”.
Kafin tayi kowanne motsai har ya iso gareta,bata ankara ba yasa qafa ya kwasheta,sai gata warwas a qasa,qugunta ya bugu da qasa,wanda ya tilasta mata qwalla qara ba tare data shirya ba saboda tsananin azaba,bai jira komai ba ya soma kai mata wani irin duka tako ina,tamkar wani mahaukacin kare,abinda ya fara jan hankalin mutane dake nesa kadan dasu suka fara tasowa.
Dukanta yake kai kace Allah ne ya aikoshi,yayin data dinga kuka mai qarfi da ihun neman dauki saboda azabar irin dukan da yake mata kamar ya samu qato dan uwanshi,mutanen farko da suka soma isowa sukayi sukayi ya bari amma ya qiya idanunsa sun rufe,har sai da hijabin dake jikinta yayi nasa wuri,data miqe ya maidata ta hanyar duka,saida wasu suka qaru,Allah yasa akwai maqocinsu malam sule,wanda yana zuwa ya hankade munzalin
“Ashe baka da hankali munzali?” Malam sule ya fada cikin fushi,yayin da munxali ke haki yana kallon kaltum dake duqe a wajen tana rusa kuka,jikinta na kakkarwa.
“Shin wai mema tayi maka kake mata irin wannan dukan kamar Allah ya aikoka?”
“Ni zata nunawa iskanci da bariki?,ka barni na qara mata”
“Idan ka kuma kai hannunka a kanta sai ranka ya baci kaji na gaya maka” cewar malam sule yana nunashi da yatsa.
Dai dai nan bilal ya qaraso wajen,saboda labarin abinda ya faru da aka kai masa can inda suke kankarar rake,tutture mutane ya shiga yi har ya isa inda kaltum ke duqe
“Yaaya”ya fada yana dagota,saiya miqa hannu ya fara da dai daita mata hijabinta sannan ya kamata suka miqe tsaye.
Idanunsa cike fal da fushi ya dubi munzali
“Indai ka zalunceta Allah ya saka mata” maganar data sanya munzalin nufoshi cikin fusata,saidai tuni aka riqeshi aka hanashi tabashi,sanda yake riqe da kaltum dake takawa da qyar yace dashi
“Ni zaka yiwa rashin kunya?,zaka gane kuskurenka kaima” shidai bilalu baiko waiwayo ba bare ya saurareshi,hankalinsa naga ‘yar uwarsa dake takawa sannu sannu da qyar,hawayen ciwo da baqinciki na sauka kan fuskarta.