Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 20

Sponsored Links

 

……..tako ina mun dace da juna” takai qarshen maganar tasa ne hadi da fitar bugun zuciyarta,kaf tsayin rayuwarta wannan shine karo na farko data taba magana irin wannan da wani da namiji,kowanne lokaci suke qoqarin kawo kansu zuwa gareta,da furta kalaman da zasu sanya ta aminta dasu,sai gashi a wannan karon reshe ya juye da mujiya,dan mutan azare ya wargatsa mata record.

Murmushin gefen baki ya fitar,tako ina ta kuma kowacce fuska baiga dacewar da take magana a kanta ba,tana da wasu siffofi daya zuwa biyu da yake ra’ayin matar da zai aura ta mallaka,amma akwai kuma tarin abubuwa da nauyinsu ya haura muradin siffofin da suke tare da itan
“Bamu dace da juna ba” yayi maganar kanshi tsaye yana ajjiye mug din hannunsa idanuwansa a kanta
“Like how?”ta fada cike da mamakin yadda ya iya kallonta kanshi tsaye ya gaya mata hakan,babu wani kwane kwane ko kara
“Babu ta inda na hangi dacewarmu dake,alaqarmu ba zata taba bada wani abu me armashi ko kuma sakamako mai kyau ba…..dan taqadirin misali da nake ganin zaki fi fahimta dashi shine….ni dake din tamkar wasu halittu ne dake rayuwa bisa duniyoyi mababanta…..”saiya miqe tsaye yana duban agogonsa,akwai sauran mintunda suka kusa ashirin kafin akirayi sallar magariba
“Wannan itace tattaciyar gaskiya mara algus…..am sorry if i hurt you” daga haka ya soma takawa ya nufaci qafa fita,saita bishi da kallo ba tare da tasan meye abu na gaba daya dace ta aiwatar ba.

Cikin qididdigaggun sakannni ya bacewa ganinta,ta sauke jiyar zuciya tana janye idanunta,duk da cewa martani ta samu mara dadi daga gareshi,amma sai taji zuciyarta bataji haushinsa ba,saima burgeta da yayi,saita maida bayanta tana mai jingina da kujerar tana fitar da iska daga bakinta.

Koda ya fito din bai tsaya cikin gidan ba sai daya isa waje,hakanan ya samu kansa da yin tattaki cikin layukan unguwar tasu,iskar dake tafe da duhun magariba tana kadashi,duk shaqa daya da zai mata sai yaki ta fita ne da sauram guntuwar damuwa ko matsewar zuciya daya samu kansa a ciki,ya fahimci wannan duka plan din daddy ne,saidai babban abun tambayar,kamar mummy ma wannan karon tana goya masa baya.

Bukar mustapha,idan ya tuna dai dai,kamar shine mutumin da daddy ya shaida masa zaya bawa kamfaninsa babbar kwangilar da kamfanoni da dama suke farautar samunta,hakan na nufin zaiyine saboda diyarsa?,ko daddy nason ya amshi diyarsa a matsayin tukuici na kwangilar da zai sama masa?,wannan tunanin ya sanyashi ciro wayarsa da sauri,ya fara laluben number ezikwe.

Tun daga nesa idanuwanta da zuciyarta ke gaya mata shine,bata samu yaqinin haka ba sai da suka sake matsowa kusa dashi,samun kanta tayi da jan mayafin basma,wanda saura kadan ya zame daga kanta,tayi hanzarin dafeshi,ta kuma juyo a fusace cikin fada tace
“Bakya gani ne hala mubina zaki ciremin mayafi tsakiyar hanya”
“Sorry….. sorry don Allah,duba can da Allah,kamar me sanyi nake hangowa,mutumin afra” dubanta ta mayar wajen,ta koma ta kalli mubina
“Shine mana”
“Oh god” mubina ta fadi,duk yabi ta rude
“Meye kike haka mubina,kinyi hauka ne?”ta fada ganin yadda mubinan ke mazari,ta kuma tafi kanta tsaye,dakatawa tayi sanda taji abinda basma ta fada
“Sorry,wallahi rudewa nayi,kinsan tun ranar zuciyata bata huta da tunaninsa ba,duk sanda na fita kuma zuba ido nake ko zan dace”
“Hakane,amma kuma saiki sanya nutsuwa ko?”
“Yes” mubina ta fada tana daidaita numfashinta
“Muje to” ta fadi cikin dakiya da qwarin gwiwa,fatanta idan sunje wucewa ta gabansa ya ganta,har yayi qoqarin mata magana ma.

“A shirya dukka takaddun da suka dace,gobe zan shigo da sassafe,banason kowa yasan da shigowata,zan zauna mu rubuta takardar nema kwangilar nan”
“Amma sir…..ina cewa kana da hanya mai kyau da aka tabbatar maka da samun contract din…..akwai kamfanoni da yawa da suke a buqata,ko dazu munyi hirar da daniel,babbar kwangila ce,hakan yasa masu so sukayi yawa fiye da yadda ake buqata” ya fada da gurbataccen turancinsa,iska samir ya furzar
“Na sani,kawai kayi yadda nace din” yakai qarshen jimlar idanunsa na sauka akanta,bugun zuciyarta taji ya qaru fiye da dazu,sai tayi qoqarin aika masa da murmushi,saidai bisa rashin sa’a kansa taga ya dauke,babu wata alama data nuna ya taba sanin fuskarta a rayuwarsa,duk kuwa da cewa sun hada idanu dashi,har kuma suka gota bai waiwayi sashen da suke ba,bare ta sanya ran ya ganeta.

Kamar zata saki kuka sanda suka giftashin saita dakata tana duban basma
“Wannan wanne irin bad luck ne basma,kinga fa,kamar bai taba ganinmu ba”
“Komawa zakiyi kenan kiyi masa bayanin kanki?”kai ta kada alamun a’ah,tayi gaba zuciyarta na gaya mata abinda ya dace tayi,tunda dai har ta ganshi cikin unguwar,zuciyarta dama gangar jikinta na bata lallai tabbas nan ne unguwarsu,indai ko hakane to ta kwana gidan sauqi.

Bai dawo gidan ba sai wajen tara na dare,zuwa sannan baiga kiran kowa ba,wala’alla saboda kashe wayarshi da yayi ne,koda ya dawo sashensa ya wuce kai tsaye ba tare da ya nemi kowa ba,yayi relax saman sofa yana maida numfashi yaji an tura qofar dakin an shigo,yana daga kwancen ya wulga idanunsa bakin qofa,wanda yaga yana shogowar ciki ne yasa ya miqe sosai ya zauna,shigowar daddy bangarensa wani baqon al’amari ne,wanda baifi a qirge adadin lokutan daya taba shigowar ba.

“Barka da warhaka daddy” hannu ya daga masa,fuskarsa a dinke tsaf tamkar bai taba dariya ba
“Kai za’a yiwa barka da kuma sannu gaba daya,samir…..kayi qoqari kaga ka watsa min qasa a idanu,ka kuma nuna rashin muhimmancina kaji” daga haka bai qara ba ya juya abinsa ya fice,maganar data sanya samir din cikin tunani,ko meye dole yayi qoqari yabi dukka abinda daddyn yace har baqin su gama zamansu a rabu lafiya,indai har abinda jauhar ta fada daxun haka yake……to shine abu guda daya da baiga hanyar bullewarsa ko dai daituwarsa ba.

Hutawar da yayi niyyar yi ya fasa,saiya fidda kayan jikinsa ya shige toilet don ya watsa ruwa,ya wuce zuwa cikin gidan daddyn yaga gilmawarsa ko hakan zai sassauta zuciyarsa.

**********Sake riqe gyada me gishirin data siyo tayi da kyau sanda take tunkaro saronsu gabanta na dan faduwa,daga sanda auwalu ya dawo gifansu gaba daya ya zamana bata da wani sauran nutsuwa,duk sanda zata fita da dare koda yammaci cike da fargaba zata shiga,hakanan cikin fargaba zata fita.

Sai da tayi bismillah sannan ta saka qafarta soron,a hankali take tafiya cikin sanda kamar wadda ke taoron fadawa wani wawakeken rami,gabanta yayi wani mugun faduwa sanda taxo tsakiyar soron,hancinta ya fara jiyo qamshin wani abu me kama da ganyan taba.

Wani wawan ihu ta saki sanda taji an cafki hijabinta ta baya,ba tare da wani jinkiri ba ta fara kokawar qwace kanta,jin motsin tahowar mutane ya saketa ya koma lokon daya lafe,hakan ya bata damar fellawa da mugun gudu zuwa cikin gidan.

Karo sukayi da ummanta data fito da sassarfa,inna haule dake sashensa itama ta fito saboda ihun dataji din,jikin umman nata ta fada jikinta na wani irin rawa,hannu biyu umman tasa ta riqeta tana tambayarta lafiya?,muryarta na rawa kamar wadda aka watsawa ruwan qanqara ta hada kalmar
“Au….walu ne”
“Wanne auwalun?” Inna laure ta fada bayan ta gama daura zaninta wanda tayi daurin qirji dashi,wanda kusan aikinta kenam,a haka take kwana ta kuma wuni,shi yasa dukka zannuwanta suka kode suka nar rigunanta,ta kuma koma tana gyara daurin dankwalinta dake barazanar suncewa ya bayyana diddigeggen gashinta da kaltum ce dama marufar asirinsa,tunda kowa ta dauki gana dasu bayan karan tsanar data jima da dora musu tabar barin kaltum din tayi mata kitso.

“Auwalu nawa kika sani a gidan nan?”umma ta amsa mata cikin wani irin fushi dakr tashi saman fuskarta,ita kanta inna kauren sai data kalli inna sanda taji ta tofa tata,abinda batasanta dashi ba,duk da kuwa irun cin kashin da take mata cikin gidan
“Ke zuwaira,banason sharri,haka kawai ‘yarki taga wani abun daban za’a laqawa auwalu na,koma wanne dan jakar uban ta rakito bari na leqa na ganshi don ubashi zai jawa yarona bacin suna ba gaira babu dalili,baya duk sanya idanun da jama’ar qauyen nan suka masa” daga haka tayi hanyar soron bakadan bakadan,bata ko damu da yanayin suturar jikinta ba.

Umman na tsaye anan tabi laure da kallo,tana zuwa dai dai sanda auwalun ke zuqe sauran abun mayen dake hannunsa,salati tahau rafkawa
“Yanzu dama auwalu baka daina zuqe zuqen nan ba?,to don ubanka zoka wuce ka fice daga gidan nan,ba zaka jawomin magana ba bakin magauta,tattarawa zakayi ka koma inda ka fito,matuqar ba zaka daina abinda kakeyi ba”
“Habba….laure….yawa kike,nifa inason yarinyar nan,tayimin wallahi…..tun….ba yau ba,kuma keda iliya……duka kun sani”
“La’ilaha ilallahu….muhammadu ya rasaulullahi,to wallahi haihata haihata,maza ka fita”ta fada tana tankadashi zuwa waje da hannu bibbiyu har sai data tabbatar ya fice sannan ta dawo ciki.

Babu kunya babu tsoron Allah data dawo ta iskesu a wajen sai tayi mursisi,cikin muxuran borin kunya ta fara magana
“Ajawa yarinya kunya ehe…..banason aikin banza da wofi,shi yana qoqarin yakiceta amma ita tana liqe masa ina dalili?,to wallahi auwalu na dan gata kuma dan asali gaba da baya yafi qarfinta,babu abinda zaiyi da ita”
“Ke laure” inna ta kirata cikin kakkausar murya,cak ta tsaya tana mamakin yadda umman ta kirata
“Idan har ke kin manta abinda ya faru a baya ni din ban manta ba,duk wannan soki burutsun da tabarmar kunyar ba abinda ya shafeni dashi,abu daya nakeso shine,ki jawa danki kune,ki jawa danki kunne,ki jawa danki kunne,bazan dauki duk wani ganganci nasa tsageranci ko rashin kunya akan diyata ba,maganar gata da asali indai kaltume bata dashi to ita da auwalu duka sammakal suke,gata kuma babu gatan daya wuce na ubangiji,duk wani dan adam da zai baka gata to koma bayan gatan ubangiji ne,ki tilastashi yayi qoqarin kiyaye shiga hurumin diyata” ta dakata a nan,sannan ta kama hannun kaltum zuwa ciki ba tare da tabi takan inna laure kota damu da gyadar da tuni kaltum din ta watsar da ita ba cikin qasar dake wajen.

Iya fushin da kaltum yau ta gani a idanun ummanta abune da bata taba ganun makamancinsa ba ko sau daya,tabbas rayuwar auwalu cikin gidan kar barazana ce ga tata rayuwar,sai da umman ta danganeta da dakinta,sun jima zaune shuru babu wanda yace wani abu,a qalla kusa awa guda sanda sukaji muryar babansu yana doka sallama da wannan fusatacciyar muryar tasa,wanda babu abinda yake sawa ta rusuna bare kalaman cikinta su fita da taushi
“Kici gaba da kulawa da kuma takatsantsan,ki yawaita addu’a,daga yau kuma kada ki sake kwanciya baki kulle qofar dakinki ba” saita juya ta fice a hankali jikinta cikin matuqar sanyi…….

 

*********Jikinta take kakkabewa bayan ta gama yiwa wasu mata su biyu kitso,ta sanya tsintsiyar laushi ta share wajen tas,duk da cewa dan sumunti ne daya fara farfashewa,wanda dama iyakacinsa qofar dakunanasu,inda sukanyi shimfida su zauna,sauran duka qasa ne da yashi.

‘yar rumfar da suke dora abinci ta isa,ta shirya itace cikim qwarewa da gwanancewa ta kunna wuta,sannan ta cika tukunya da ruwa ta dora,kafin ta wuce ta daura alwalar sallar la’asar,yau cikin farinciki suke,saboda zuwan yakumbo indo,wadda ta taho musu da buhun shinkafa ‘yar hausa,harda kwalin taliya sukutum da guda,taliyar da idan sukaga babansu ya basu ita to babu yadda zaiyi ne,a haka ma baifi cikin wata biyu suci sau daya ba,saidai ‘yar murji ta hausa,itama idan ta samu. Ta hada musu da manja da man quli kowanne kwalba bibbiyu,haka take musu,lokaci baya lokaci takan yi musu irin wannan kyautar,ko ita ko kawu ado,ammafa saida su boye,su dinga diba da kadan da kadan suna dafawa,saboda matuqar babansu ya fahimci an kawo tofa babu sauran xaman lafiya a gidan,hakanan su da abincinsa sai bayan wani lokaci mai tsaho,koda wanda ta kawo.ya qare din,amma a yanxun da bai sani ba bakinsu alaikum,zai dauka buga bugar da suka saba sukayi suka dafa,idan yaga dama ya basu saisu tara zuwa lokacin da wanda suke dashi ya qare.

Sanda ta idar umman itama ta fito ta daura alwalar ta bada faralin sallah,lokacin kaltum na gaban tukunya tana sake iza wutar data hura,suna hira jifa jifa da umman,saidai ita umma har yau ranta babu dadi,tun daga lokacin da wancan abun ya faru,har yanzu ba’a sake take ba,tun daga ranar kullum tunaninta shine ta yaya zata baiwa diyarta tsaro da kariya har Allah ya kawo sanda zata bar gidan,tabbas da tana da inda zata kai kaltum din da zai zameta mata garkuwa daga barazanar gidan babu ko tantama zata haqura da zamanta a gabanta ta miqa ta can din.

Sallamar qaramar yarinyar da bata wuce shekara tara ba shi ya tsaida hirar tasu,daga umman har kaltum fuskarsu da fara’a suke kallon yarinyar,kaltum ce ta fara magana
“Hali dubu ‘yar gidan gwaggo habiba,yau an tuna damu?,ko gwaggon taki ce ta aikoki?” Dariya yarinyar ta saki tana gaida kaltum,sannan ta qarasa tabarmar umman tana gaisheta
“Cewa tayi nazo na gaya muku batajin dadi,wai ida n yaya kaltume bata komai tazo dan Allah ko yau ko gobe” girgixa kai kaltum tayi
“Dake za’a hada baki ko dubu?,to kwa gama qage qage ciwonku ku haqura” murmushi kawai ummansu tayi,tasa dama za’a rina,saboda tun zuwan habiba gidan na qarshe taga wasu canje canje daga gareta,tasan babu jimawa dama ciwo zai bayyana,kusan kwanaki bakwai kenan tana kasa kunnen jin hakan.

Ga mamakin kaltum sai taji ummansu da kanta tana cewa
“Kice mata zata zo in sha Allahu kinji ko?”
“To ummanmu” dubu ta fada kamar yadda taji habiban tana fada,yarinyar nata dariyar jin dadi ta fice yiwa uwar dakinta albishir.

“Ummanmu….kinsan fa banason zuwa wallahi,ni kunya nakeji,gidan qanwata ne fa” dubanta umman take,tausayinta yana ratsata,banda haka Allah ya shirya ai da yanzun itace adakinta ba habiba ba,saidai tsarin Allah kuma shine dai dai,tasan cewa kaltum din na kunyar zuwa,kodon surutu irin na jama’ar qauyen,duk da cewa ahalin yusufa basu da matsala,mutane ne masu karamci da dattako,har cigiyar babar yusufa take idan taji shurun kaltumen yayi yawa
“Na sani,amma ni kikeso naje naji matsalarta banda abinki kaltume?,kece fa ‘yar uwarta,ke kadai take da” shuru kaltum tayi tana gamsuwa da zancan umman,saboda hala bata sake cewa komai ba.

Bilal ne yayi sallama yana shigowa gidan,yayi futu futu da qasa kamar kullum,qoqari kawai yake ya cire gwabza gwabzan takalman qafarsa tare da neman wajen zama,kaltum ta dago taga firfita wutar da takeyi,idanunta ya kada yayi ja saboda hayaqi tana dubansa
“Sarkin nema,a ina ka sake samun wajen aiki kuma?” Sai daya kalli umma sannan ya sosa kansa
“Wajen aikin nan dai nawane?” Idanu kaltum ta zuba masa
“Wanne wajen aiki?,inda na hanaka zuwa?,bilalu bakajin magana?,baka tsoron mutanen nan su illataka?baka son lafiyarka ko?” Fuskarsa cike da alamun damuwa yace
“Ummanmu ce wallahi,ita tace na koma,ki tambayi xunnu,mutumin ne yayi cigiyata akace masa na daina zuwa,da kansa yazo Allah ranar bakya nan kin tafi tsangayar sarki yin kitso,yace na koma,yana da kirki mutumin,ya tambayeni amma nima dalibin makarantar ne ko?,da nace masa bana zuwa bakiga fadan daya ringa yimin ba,yace lallai idan aka gama gini dani za’a koma,zai siya min komai har uniform da litattafai,kuma nima daya yimin fadan sai naji yaya inason na koma,kullum saiya bani ragowar abincinsa,baki gani ba harda nama a ciki” idanu kaltum ta zuba masa,zuwa wani lokaci ta dauke idanunta ta maida kan ummansu,kallon data yi mata yasa ta gane umman tasan komai,kai ta jinjina mata,sannan ta soma magana
“Duk wani abu daka zama a duniya haquri shine jigo da yake maka jagora izuwa wannan matsayin,saurin fushi baya haifar da komai illa dana sani,sa’annan duk sanda wani yayi maka kuskure daga bisani ya dawo ya nuna maka cewa ya gane abinda ya aikata din ba dai dai bane,cikar dan adamtakar mutum shine ya yafe masa,gajen haquri….saurin fushi da saurin yanke hukunci basu da wani amfani arayuwarmu,ina fatan zaki dauki darasi” a hankali kaltum ta gyada kai,dukka maganganun ummansu tasan kan hanya suke,koda yaushe umman tasu burinta shine taga sun zama wasu nagartattun mutane.

Tana gaban murhun tana tunanin maganganun ummansu,har zuwa lokacin data kusa gama dahuwar shinkafar,bilal din ya qaraso wajen da take zaune yana roqarta ta kara masa ruwan zafi a wata silver idan ta gama girkin,saita yafitoshi da hannu,ya qaraso ya zauna dab da ita
“Don Allah kada kice na firfita miki wutar nan,Allah yunwa ta gama cinyeni abinci kawai nake buqata” harara ta jefeshi da ita,bilal din qwallo ne wajen ci,baya qoshi sam,dalilin da yasa ya shiga nema haiqa kenan,tun daga sanda ya budi idanu ya fuskanci gidan nasu ba wajene na ciyar da yaro ya qoshi ba,inda take godema Allah bai taba daukar kayan wani ba,saidai ya sadaukar da dukka qarfinsa ya nemi abinda zaici
“Kace mutumin zai siya maka komai?,wanne irin kudi ne dashi haka?” Dariya bilal yayi
“Babu wani kudi,shima kullum tare damu yake aiki,amma kamar abinda ake biyansa yafi namu yawa” kai ta jinjina tana mamaki,dama akwai ragowar mutane masu kyawun zuciya haka?….

 

 

21
D/z

*_littafin kudi ne, sharing dinsa tamkar xalinci ne a garemu,ki tuntubi wadan nan numbers din ki biya naki ki karanta cikin aminci_*

08184017082
Ko kuma
09134848107
_______________________________
*_INNA KAFAINAKAL MUSTAHZI’EEN_*👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽
________________________________

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button