Sponsored Links
Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 24

Sponsored Links

Page 24

Kai kawo ya dinga yi cikin dakin,ransa na masa suya,me zaiyi ya huce takaicin hafsa?,yasan dai tabbas bazai qyaleta ba,anzo gabar da dole ya koya mata lesson kamar yadda yasha fada.

Idanunsa suka sauka akan wayarsa,sai ya jawota da hanzari ya fara kiran layin hajiya,bugu biyu ta daga

“Abbas ya akayi?” Ta tambayeshi da mamaki,ganin bai wani jima da barin gidan ba,qoqarin dai daita muryarsa yayi,don bayason ta fuskanci akwai wata matsala ne ta tashi hankalinta

“Lafiya lau hajiya,cewa nayi zai yiwu a gabatar da neman auren cikin satin nan?” Kai ta jinjina cike da mamaki,anya babu walakin goro a miya?

“Eh to,saidai na nema kawunnanka naji”

“Idan zaiyuwu hajiya kawai ayi,na shirya” tana saurin gano damuwa da kuma fushinsa,yadda yayi maganar a jikinta taji akwai damuwa,amma zata tambayeshi a hankali

“Shikenan,zanyi magana dasu,duk yadda ake ciki zaka ji”

“To hajiya na gode,gobe da yamma zan wuce,zan shigo ta nan kafin na wuce din in sha Allah”

“To ba damuwa,Allah yakai mana rai” daga haka sukayi sallama.

Cikin mamaki take sauke wayar,saidai kuma ta samu kanta da sakin murmushi tare da fadin

“Alhamdulillah” zuciyarta na gaya mata wataqila akwai alkhairi mai tarin yawa a abun,shi yasa Allah ya kawo komai a kurkusa haka ya sauqaqe matsala da damuwa.

“Tofa,ta samu kenan hajiya?” Faccalarta da suke tare a falon,ita da yayar abbas din mai suna mabruka suna hira ta fadi,wayar ta ajjiye gefe tana cewa

“Aure ne ya tasowa danki” da mamaki ta kalleta

“D’ana,wa kenan?”

“Abbas mana” kallonta sukayi gaba daya cike da mamaki,abbas din da kowa yasan dabi’arsa,mutumin da ko auren hafsa dinma kamar bazaiyi ba saboda tsabar I don’t care manner irin nashi da rashin baiwa lamarin soyayya muhimmanci?

“Abbas din yaushe har yaga wata yanaso?” Faccalar tata da yara ke kira da gwaggwo fanteka ta fada

“Tayani tambaya gwaggwo,na dauka ma bashir ko yaya sa’id zata ce,ko kuma Sunusi” kai ta girgiza tana murmushi

“Abbas ne” kai suka jinjina su duka,mabruka tace

“Ya cancanci ya qara aure dama tuni,wannan rayuwar da akeyi a gidansa bata da ma’ana sam,naga qoqarinsa ma,ganin baida wannan ra’ayin yasa ban taba tuntubarshi da maganar ba,ga ‘yammata nan cike a dangi,ya zabi wata ya qara ko zai samu sassauci,haba abun na hafsa yayi yawa” kai gwaggwo ta gyada itama

“Gaskiya dai,yammata kyawawa fa gasunan masu hankali,ita wannan din a ina ya samota?,cikin yan uwansa ne?,amma banji batun ba sai yanzu?” Gwaggwo ta fada cike da son jin wace?,tana fata ya zamana cikin yaranta ne,duk da tasan zaiyi wuya,don inda cikin nasu ne da tuni ta fahimta,amma rabonta da abbas a gidan tun sanda tayi wata rashin lafiya ya shiga ya dubata

“Ba cikin dangi bane,wata yarinya ce diya take a wajen muhsin abokinsa,dukkanku ai nasan kunsan muhsin?” Ta fada tana kallon fuskokinsu, gwaggwo da tuni fuskarta ta sauya tace

“Qwarai kuwa” sai hajiya ta dora

“Yarinya ce ma,amma nutsuwarta da hankalinta ya bani abbas din xai samu nutsuwa a gidansa,zai kuma ce ayi ayi,a bari a bari”

“Turqashi” gwaggo fanteka ta fada ba tare da tasan kalmar ta fita a bakinta ba,wani bacin rau na motsa mata,yaron da dukkan alamu suke nuna zaiyi arziqi cikin dangin nasu,taketa qulafucin ganin ta samu ta jogana diyarta,lokaci daya hajiyan ta wargaza fatanta da burinta ta dauko wata bare ta maqala masa?.

“Banda abun hajiya ruqayya,gida bata qoshi ba za’a baiwa dawa?,gamu da yaran yammata duka sun tasa saiki dauko bare ki bashi?,duk da itama hafsan akwai alaqa amma ai baiyi alaqar sa da yaran kawunnansa ba ko?” Gwaggo fanteka ta fada tana dora murmushin yaqe kan fuskarta

“Gaskiya nima wannan tunanin yazo min” mabruka ta fada tana gyada kai, murmushi hajiya tayi

“Auren dangantakar ai bai amfana komai ba gwaggwo,gwara a gwada baren ko a nan za’a dace ko?” Kai ta kawar tana tabe baki,bacin rai iya bacin rai yana cikata,wanann babbar dama haka za’ayi asararta?,suna ji suna gani

“Da dai kin sake tunani gaskiya,duk yadda bare yake da dadi ai baikai dadin dan uwa ba”

“Hakane” ta amsa mata a taqaice,tasan halin gwaggwon da mita,ita kuma dama can bamaison dogon magana bace,gwggwon na daya daga cikin masu kushe aikin dan sanda a sanda abbas ya samu aikin

“Dan sanda?,me na sama yaci ballantana ya baiwa na qasa?,kayan cin hanci da rashawa” wannan shine abinda taji tana fada sanda hajiyan taje gidan da kanta tana shaidawa kawunsa mijin gwaggwon cewa ya samu aikin,tun daga matakin constable saai yanzun da daukaka ta fara zuwa masa ake kwadayin hada zuri’a da ita?,duk haqurinta da kawaicinta ita din ba mahaukaciya bace.

Hirar duka saita fita akan gwaggwo fanteka ta zama mara dadi,don haka bata jima ba ta miqe ta yiwa hajiyan sallama ta fice.

*WIDAD*

Sanda ta bude ido ta ganta qofar gidansu sai taga kamar wasa,kasa jira tayi drivern da uncle muhsin ya daukar mata shata har qofar gida ya fidda mata kayanta,ta sauka daga nan ta nufi gate din da gudu gudunta,ji take kamar zata bude ido ta ganta ta koma bauchi.

Cikin sa’a kuwa tana buda gate din ummun ta hanga tsaye a farfajiyar gidan ita da kawunnanta,sanye da atamfa da kuma hijabi,hannunta riqe da carbi,da alama salla ta idar suka tasota,akwai zancan da sukeyi.

“Ummunaaa” ta fada da qarfi sannan ta kwasa da gudunta,ta isa gabanta ta fada jikinta tana ruqungumeta.

Sai da ummun tayi taga taga zata fadi kawu ya tareta

“Ashsha,ashsha,zata kada mana uwa” sai ta saki dariya tana sakin ummun suka miqe tsaye dai dai ummun itama tana dariya idanunta akan fuskar widad din,kamar fa shekara bata ganta ba.

“Ke dawa?,yanzu kike tafe?” Ummu ta fadi tana dubanta

“Ni kadai yanzu yanzu na qaraso”

“Iyeee,muhsin din barmin ke yayi ke kadai kika kamo hanya?,tabdijan ,zamu hadu dashi kuwa”kafin ta qarashe drivern uncle muhsin din ya shigo da jakankunanta,suka gaisa yace zai koma,ummu tace a’ah sai yaci abinci,suka wuce ciki ita da widad tace taje ta kawo masa abincin,su kawu kuma suka fice bayan an bashi wajen zama anan farfajiyar gidan.

Zuwa wani lokaci sai ga sassan ummu ya dan cika da sauran yaran gidan,su Aafiya rafi’ah fareesa da sauran wadanda suke shekaru kusan daya,sun baibayeta tana ta basu labarin bauchi.

“Kano fa tafi dadi Allah” ta fada daga qarshe tana yamutsa fuska,dariya sukayi mata

“Daga baya kenan,bayan kin gama kwanakinki” dariya tayi tana cewa

“Da gaske nake muku,bari kuga” sai ta wuce daki ta janyo jakarta,ta fidda jakar ledar kayan makeup din da hajjaa ta damqa mata tace inji abbas,tunda ta taho kayan suke daukan hankalinta,komai na ciki ya burgeta ya kuma yi mata kyau,harda takalmi me tsini irin nasu basma da aka sako musu a lefe,tayita maitar takalmin sai basman ta jefa mata harara

“Ba baki zanyi bafa,kiyi addu’a kema Allah ya kawo me siya miki” fushi tayi tana tura baki tabar gurin,sai gashi ta sameshi sama ta ka,bayan shi harda mayafi da hand bag qarama mai matuqar kyau,a nan ta zazzage musu kayan,suka dinga santinsu,daga baya ta daukarwa kowa wani abun daga cikin kayan kwalliyar.

*************

Kwana biyu a tsakani tana kitchen tana cin abinci suna hira da latifa,ta ajjiye warmer din data zuba abincin alhaji a ciki tana cewa

“Ashe dan bauchi kika samo mana kuma” kallonta tayi tana ci gaba da cin abincinta,don ita har ga Alla ma ta manta da wani batu

“Dan bauchi?”

“Eh mana,naji abba mahmudu yazo suna zancan da alhaji ai”

“Auho,wai abokin uncle muhsin”

“Shifa” sai widad din tayi shuru kawai,don batasan me zatace ba,itadai ba sanin soyayya tayi ba bare ta tantance tana sonsa ko bata sonshi,kawai dai taji bata damu ba bata takura ba kamar sands ake zancan mahfood da ma’aruf.

Sosai ummu ta dinga juya zancan bayan da mahaifin widad ya zartar da cewa an bawa abbas widad don,amma bata taba kawo cewa zasu nema aurenta a nan kusa ba haka,taji abun sosai a ranta,a yadda ta lura kuma shi mahmudu din a shirye yake da auren diyarsa,tasan watarana komai tsahon zaman da zatayi da qaunar da takewa widad su rabu dole ta aurar da ita,so a yanzun bataga nata hurumin da zata hanashi bada auren ‘yarsa ba,tunda dukkan bincike da shaidu sun tabbatar da nagartar me neman auren kamar yadda musulunci yayi umarni.

Amma babban abun shine,kishiya daya tabbata widad din nada ita,ta yaya yarinya kamar widad din zata iya fuskantar abu me wahala da zafi kamar kishi?,bata sani ba,saidai tana fatan ko mai zaizo da sauqi fiye da yadda suke zata.

Kwanan widad din biyu da dawowa maneman auren abbas din suka iso kano qarqashin jagorancin uncle muhsin,sunga karamci irin na kanawa,duk da cewa su din ba kanawa bane usul,amma tunda an haifi ‘ya’ya da jikokinta suna amsa wannan sunan.

Cikin girma da mutunci gami da karamci suka gabatar da neman auren abbas ga widad din,aka sake jaddada basu,suka nema alfarmar karbar kudin aurensu harda sadaki,take alhaji yasa aka karba komai,suka karbi roqonsu na daurin auren sati mai zuwa.

A ranar zancan auren widad ya fara yawo a dangi,abinka da family house,kowa idan yaji zai gayawa na kusa dashi,bugu da qari widad din ‘yar gatan ummu,mai masoya da kuma tarin abokan adawa.

“Uhmmm,sunje sun zaba mata miji ba,ai dama wannan yadda akaci buri a kanta nasan sai me abun hannu zasu bata” wannan shine abinda wasu suka dinga fada,musamman da suka samu labarin muqamin da ya riqe a gwamnatin bauchin,da kuma wanda yake kai yanzu,gani sukeyi uncle muhsin ya dauketa ne dama kawai don ya aikata hakan.

Ita kuwa sam batasan ma me akeyi ba,don har ta koma islamiyya,wadda tun tafiyarta qaunar makarantar bata bar ranta ba,sanda ta koma din sai ta samu basu wani tsere mata ba,tunda ta dora daga inda ta tsaya a bauchin.

**********Karfe shida saura na yamma suka iso gidan ita da Aafiya rafi’ah da widad din,bayan tasowarsu daga islamiyyar,gab da zasu shiga gate din gidan Aafiya ta kalleta

“Nifa zancan bikinki naji ummanmu tana yi,wai nan da sati daya”

“Nifa abinda yake hadani dake tsokanarki” widad ta fada tana watsa ragowar alawar data siya cikin jakarta

“Wallahi nima haka naji,don kafin mu tafi islamiyya naji umma tana waya a karbo atamfofi akai mana wajen mai dinki”

“Mahaukata,sai kuyi ai” widad din ta fada tana yin gaba abinta tana dan waqenta.

Bata ma tsayasu ba ta zarce sassan ummu abinta,tana sallama a falon ta soma zare hijabinta daya dameta,gashinta mai santsi ya ware,don dama ita din ba ma’abociyar saka dankwali bace,tafi sanya hula,itama ba ko da yaushe ba,sai ummu tayita fama da ita.

Ummu da anty halima ne a falon

“Anty halima ina nabiha?,kikace idan zaki sake zuwa tare zaku zo?” Widad ta fada tana barewa alewan ta tura bakin yaron anty halima dake kan cinyarta.

Da kallo anty halima ta bita,tana dan jin tausayin widad din

“Oh ni sadiya?,wannan wacce irin amarya ce ummu?” Dan murmushi ummun tayi,ita kanta tausayin widad din takeji,har yanzu ma bata zauna tayi magana cikakkiya da ita ba kan auren da tasan widad din batasan meye shi ba,bata kuma da labari cikakke akan yinsa.

“Au ina yini?” Ta fada tana dariya bayan ta tuna nata gaidata ba,ba kuma tare data maida hankali ga maganarta ta farko ba

“Lafiya lau widad,nabiha zasuzo,sai satin biki in sha Allah”

“Allah ya kaimu” ta fada tana gyada kai hankalinta kwance,saita dubi ummu a shagwabe

“Yunwa wlh nakeji ummu,dazu banci abinci ba Aafiya ta matsamin na taho mu tafi”

“ki wuce latifa tana kitchen ki karba”

“Tom” ta fadi tana wurga jakarta ta zarce kitchen din,yayin da dukka su biyun suka bita da kallo.

Ummu ce ta fara dauke idanunta tana sakin ajiyar zuciya,anty halima tace tana dariya

“Wai,wa yaga widad amarya” kai ummu ta kada

“Tausayinta nakeji halima,ban taba kawo rabuwarmu a nan kusa ba” tabe baki anty haliman tayi

“Kaji ummu,to mu da aka rabu damu din tun bamu kai haka ba me ya samemu?,gamu ragal damu?,itama zata ware ne kamar kowacce mace” kai ummu ta girgiza

“Ba zaki gane ba halima,dukkanku kunfi widad wayo sanda aka muku aure,kawai don lokaci yayi ne ba yadda zanyi,amma ban shirya kaita wani uwa duniya ba”

“Tunda dai babanta ya bada ita,alhaji kuma ya goyi baya dole saidai ayi haquri,yanzu kawai yadda za’a tattarata akaita bata iya komai ba,kunbi duk kun shagwabata,bata iya komai ba,komai yi mata akeyi” anty halima ta fada tana mele baki,ta rasa wanne irin so ummun takewa widad?,tamkar ma ba mahaifin widad din ta haifa ba,ita ta haifa,ko ita diyarta ta cikinta bata jin tana mata son da takewa widad din.

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

 

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button