Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 12-13

Sponsored Links

*12 – 13*

_Assalamu alaikum ƴanuwana mata dukda dai da banso inyi magana ba saidai don damu da ya isheni , Nifa kwaram baya damuna wallahi kar wacce takuma biyoni private akan wai ina labarin ɓata tarbiyya ke wayace ki karanta?,ashe bance kar wanda ya karanta mun littafiba musamman maza ko ƴanmata ? Indai adalci akebi baici a dameni ba ton inka karanta wannan kai tashafa bani ba 🤷‍♀️ garama Ni din don a faɗaka nikeyi don kowa yasan abinda ke faruwa nowaday ,kuma Ni inada madogara na amma sai a ƙwarzabi mutum da surutu bayan shikansa mai karantawan yayi surutun daɗi yikeji☹️,inba hakaba ya akayi har tasan me akeyi a cikin littafi? Ko kaji tagama surutu kijita a wani group can tana aturo muna da jarababben namiji in ba’a samuba abiyo ta pc , is it by force?🤨 to Ban saka numberna don irinkuba na sane don mutanen arziƙi masu fatan agudu tare a tsira tare…kuma ma na rigada na dasa alkalama ta harma na karɓi kuɗin mutane so no going back eheee💃. Ni tuni na saba irin littafin nan sai haƙuri don wanda zan yi ma inna gama wannan sai yafi wannan🤪 Kuma da naso ingama free page a page 10 amma yanzu wallahi saina kai 15 masu gani idonku ya tsiyaye in yaso abune ko banyi forwarding ba kina zaune zakiga an turo to ya kika iya🤣 Kinzo kina wainnan abu a social media tayaya BAZAKI zama ƴar ƙauye ba a gaban miji sai ya ƙaro aure kice ya zalunceki kindaiso zalintarsa🤐_

 

*MY FANS MU CIGABA DA GASHI SAI A PAGE 15 ZAN GAMA FREE PAGE💃💃💃💃💃💃💃💃*

 

…….Daga gidan su victory Arab garden ɗin sa yawuce

komai an gama yi guri ya tsaru ƙarshe bene hawa biyar kowanne step da kalan kayan da ake saidawa .
Hawa na ƙololuwan ƙarshe zallan gwala-gwalai ne da agoguna masu tsadar gaske,Hawa na biyu kayan mata ƴan garari ,na uku kayan maza na larabawa da turawa takalma da sauransu
Na huɗu lafayyu,alkyabbu da gyaluluwa ta alfarma zannuwan gado,barguna da sauransu
Sai hawa na ɗaya inda ake shopping na kayan cosmetics ,kayan ƙwalam da sauransu
Daga gaban wajen kuma kayan wasan yarane iri iri masu ban sha’awa daga bayan wajen kuma wajen shaƙatawa ne da aka tsara shi tamkar a Turai Amaren bana inama JULAYB talla kun huta fita honey moon. Daga gefen damane akayi wani irin siririn gini mai tsawon gaske ankewayeshi da glass da mattakala na silver a kekkewaye. tundaga farko har ƙarshe nan ne office ɗin julaybib yike daga can sama

Sai kuma na marketing manager daga ƙasa , ko’ina luf luf da grass carfet sai ƙamshin furanni ke tashi masu ban sha’awa

Wajefa ya tsaru sai shirin saka ranar buɗe wa

tuni matasa sun fara cire zafafan hotuna a wajen suna sakawa a shafinan sada zumunta na yanan Gizo kamar su IG

Don yanzu haka akwai wani yaro daya fara cire hoto a wajen ya soma sakawa a shafukan sa aikuwa ya samu followers ɗururu kowa zancen yanda yaron yasamu shiga wajen akeyi don har anbasa king of IG

hakan ba ƙaramin jawowa wajen sanuwa yayiba a kafatanin Nigeria da ma ƙetare

Don hatta JULAYB saida yakira yaran yayi masa kyautar bajinta yaronko yaroƙesa su ɗauki hoto tare.
Wow Amazing of the year ,yaro yayi suna sanadiyyar hotonsa da wannan giant Balarabe matashin mai tashen Naira kowa addu’a mace tagari yake masa .

*****
A office sai yamma liƙis sannan suka gama hadahadan lissafi da yanda za’a fara shigowa da kayan a mabanbantan ƙasashe cikin farashi mai sauƙi

Daga nan ya haɗa komatsansa ya wuto gida shaf shi yama manta da ya nemo ƴar taya kwana yau shidai hankalin sa yina nan wajen Mairo

A gida kam Mairo da babanta zafine ya isheta a ɗan ɗakinsu mai kama da akurki lolz

Don haka benci ta fito masu dashi suka aje a compoud ɗin, sannan ta shimfiɗa buhu ta zauna a ƙasa

Shikuma baban tabar masa ya zauna kan bencin suna cin gyaɗa mai gishiri ,da tsohon radion sa a gefe suna sauraran labarai

Ahaka suke ɗan taɓa firansu.

Suna cikin hakan sukaji horn ɗin su julayb tundaga farkon layin

Shidayike yasan kalan horn ɗin su . zubut ya miƙe zaije ya kware get ɗin.

“Baba menene ?”
“Mai gidan ne tafe ai “ya bata amsa da yarensu
“To Baba baka bari su ƙara so ai basu zo ba tukuna ”
Komawa yayi ya zauna “shikenan na bari ƴar albarka”

Bayan driver ya yi horn ne Baba mai gadi ya tashi da niyyar ya buɗe get.

A hanzarce Mairo ta miƙe ta sha gabansa tana kicikici da get ɗin tana dariya “Baba ba Gani ba”

Girgiza kai kurum yayi yakoma ya zauna

A haka ta samu ta kwance padlock ɗin ta fara tura get ɗin da iya ƙarfin ta

Tana turawa ko’ina na jikinta na girgiza ,tundaga cikin motar yike hangota kir yayi mata da ido bako ƙiftawa har ta tura get ɗin taje gefe ta tsaya tana faman tattare wani balabujen siket ɗinta zuwa ƙasan ɗuwawunta kaɗan yanda zata fi jin daɗin turawa tukum in sun shigo

Saida ta kauce kafin drivern ya turo kansa ciki,sai a sannan ya maida ƙwalamarsa ta hanyar tanɗe baki kamar tsohon maye😂

Suna shigowa tabi ta kulle ,saida aka ɗan jima kafin ya fito daga motar ,ita a lokacin ma tuni ta koma muhallin ta ,tana cigaba da taunar gyaɗanta ,tana gyalgyaɗa kai sakamakon waƙar barmani coge da akasa a wani tasha mai taken Akama sana’a mata

A nutsen sa ya ƙaraso inda suke fuska ba annuri kamar ba shiba

“Heey who ask You to open that get?”
Ƙuri tayi masa da ido kafin ta fara mimicking(kwaikwayen)maganar sa , kawai saita fashe da dariya

“Hhh Alhaji ba turanshi hwa” tafaɗa da Muryar dariya

Binta yayi da ido yina mata kallon taɓaɓɓa ,can kuma ya daka mata tsawa “Aina abuki ?Ala sami’ina madha a ƙulu laki?”
(Ina babanki iyeee? Ko bakijin abinda na faɗa makine?”

Taɓe baki tayi kawai ,saita mirza gyaɗa ta watsa a baki ta cigaba da harkan gabanta

Tunzura yayi yashiga ihu
“Wai wannan wani irin iskancine nayi mata magana da English tayi mun dariya seems like she’s mimicking and nayi mata da yarena ,No respond …..” Haka yadinga bala’i shi kaɗai don ita yina farawa ta miƙe ta ƙalƙala ɗakinsu da gudu don ita duk zatonta dukanta zaiyi.

A sukwane ƴan gidan suka halarta ciki ko harda baba ɗan fillo dake aikin tafa hannu
Dukda dai su yanzu ‘amarin mai gidan da Mairo dariya yike basu shi ba haƙuri itakuma ba ganewa ,hausanma da durga durga akeyi inaga turanci kuma

Haƙuri baba ta soma basa tana shaida masa “this lady that You have seen,Assume like she’s no A no ALU so dont mind her”(karka damu da wannan budurwan da ka gani kawai ka ɗauke ta ba A ba ALU”

Yamutse fuska yayi “me kike nufi ? Bata iya turanciba”

Gyaɗa masa kai tayi ,shidai baba sai tafa hannu yikeyi yina rissinawa don bayaso sanadiyyar Mairo ya bar aikinsa

“Hmm what so ever…🤷‍♂️now i wanna no there problems what do i do?”(to duk ba wannan ba inason insan damuwarsu ya zanyi ?)

“Kabar komai a hannuna zan ƙoƙarin ji daga garesu sai in gaya ma feedback”

Jinjina kai yayi ya wuce .shikam baba mai gadi faɗi yike “Alhaji warkam(welcome)” ko bi takansa baiyiba ya wuce

Aiko ya yazo daidai gurin ɗakinsu yaganta a maƙale jikin labule tana leƙowa
Suna haɗa ido ta aiko masa da saƙon gwalo

Harara ya banka mata ya juyar dakai ,haka kowa ya ƙunshe dariya suka waske.

*****

Tana ganin yawuce ta fito tana haki kamar wacce tayi tseran gudu ta fara harhaɗa kayansu tana kaiwa ɗakinsu faɗi take “baba zo mu gudu”
“Mairamuu a gidan mutnin nan muke inkikayi sanadiyyar da ya koramu to ina zamu?”

Kafin ta basa amsa suka kuma jin knocking

Dagudu ta ƙalƙala wajen
Bata tsaya tambayan wayeba kawai ta buɗe ƙofar

Tsohuwar budurwan sa da sukayi tsiya ne ya kora tashigo

Sanye take cikin crazy shiga tana tafe tana taunan cingam
Sakin baki da hanci tayi tana kallonta a bayyane tace “An gayu mai shin shingwui”😁(wai ƴan gayu masu cin cingam)

Dariya tabata amma haka ta kirne ta cigaba da tafiya ganin tayi hanyar shiga ciki

Tayi saurin shan gabanta
“Hajiya ina zakine” zare mata ido tayi

“Gyara kar in ɓarar da ke”

 

 

 

 

*Oum Aphanan✍️*
09065990265
[3/14, 06:43] Bamalli✌️: *Typing…✍️*

 

*JARABABBEN NAMIJI*

 

*Na…Oum Aphnan🌸*

________________________________

*ALHERI WRITERS ASSO.🖊️*

*A .W. A*

https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/

________________________________

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button