Dangina Book 2 Page 12
๐ฑโ๏ธ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆโ๏ธ๐ฑ
*BOOK 2*
*PAGE 12*
A hankali yaci gaba da takawa yana shiga cikin d’akin ba tareda ya warware d’aurin dayama fuskar shiba bayan ya gama k’are mata kallo,
Koda ya isa kujerar dake daura da gadon ya jawo zuwa gaban gadon ya zauna, rik’e da Boy a hannun shi wanda har lokacin bai gama bashi labaran da yakeyi ba, yanda yake binta da kallo haka itama taci gaba da binsu shida Boy din da kallo batareda ta furta komai ba dan bata jin cewa akwai ranar da zata zagayo wanda zataji cewar ta gaji da kallon nasu domin su dai halittun maza biyun nan dake a gabanta sune abu biyu da take matuk’ar so da kauna a rayuwarta tana son d’anta son daya haura soyayyar da takeyi ma yaranta uku mata, haka shima uban take mushi wani irin mahaukacin son da take jin komai ya shiga gabanta tana iya kauda shi indai wanda zai shiga tsakanin ta da Sarkine,dan haka ba tareda k’osawa ba itama taci gaba da kallon su tana jin dad’i na k’ara lullub’eta, fatan ta a kullum shine Allah yasa shima wannan cikin na jikin ta Namiji ne ba mata ba, domin kullum likitan sai ya zaulayeta da cewa ko sojoji zata haifo musu ne wannan karan shi yasa ciwon laulayin su ya bambanta dana sauran, to itama dai addu’ar da takeyi kenan Allah yasa biyun zata haifo kuma yazama na duka maza, intayi yan biyu maza mai kuma ya rage mata yanzun da bata da kishiya ai shikenan kuma bata da sauran matsala.
Can sarki ya bud’e baki cikin kakkarfan muryar shin nan da bata sarrafuwa ta dad’in rai yake tambayar ta
“Ya jikin naki?”
“Naji sauk’i Alhamdulillah yaushe kazo?”
“Isowata kenan”
“To wa ya fad’a maka banda lafiya Anty ne ta kira ka ko Daddy?”
“Bako d’aya a cikin su, keda kike ciwon baki gayamin ba, sune kike saran su Kira su fad’amin?”
“Kayi hak’uri”
Shi kuma sai ya mata banza bai amsa ba, hakan da yayi kuma shike mata nuni da cewa ranshi a bace yake dan haka sai itama tayi shiru ta kama kanta,
Bayan wani d’an lokaci sai kuma ya zaro wayar shi daga cikin aljihu sojan daya tuk’oshi ya kira sannan ya fad’a mishi inda zai shigo ya same shi, babu jimawa ko sai gashi, sai da sojan ya gaisheda uwar gidan su da mata ya jiki kafin ya rungume Boy da Sarki ya bashi dan tuni bacci ya kwashe Boy d’in,
Umarni Sarki ya bashi akan ya kai Boy din can gidan Brigadier daga can kuma shima ya wuce gida zai kira shi da safe yazo nan d’in ya d’auke shi,
“Basa bari ana kwana fa anan d’in !”
Cewar Teemah.
“Kai yi tafiyar ka sai da safe ”
Bayan sojan ya ficene ya fuskanceta da kyau, sai dai yana shirin yin magana ita kuma ta tari numfashin shi da tambayar shi,
“Kaci abinci kuwa? Idan kanajin yunwa in kira a kawo maka me zakaci?”
“Bana tareda yunwa na riga naci abinci”,
ya amsa mata a dake,
dan haka ita ma sai ta gyara kwanciyar ta hannun ta a saman cikin ta da shine abunda Sarkin ya fara gani tun shigowar shi d’akin domin ba k’arya ta rame dan ma tana da mulmulallan jiki da farko kuma cikin nunuwa da hips ya k’ara mata yanzun daya k’ara kwari shine har ya bayyana,
“Fateemah wai ke yaushe zakiyi hankalin sanin dai dai da kuma abinda yake ba dai dai bane iyeh?”
Sai da ta turo baki gaba kafin ta iya furta
“to ni mai nayi maka kuma yanzun? Kaga dai abunda ke gabana koh ka barni inji da lalurar dake jikina”
“Eh Ai dama haka zakice tunda a kullum dama ke damuwar ki ce kadai taki, yanzun fisabilillahi inba ma kin d’aukeni wani mara daraja a wajen ki ba taya ma har zaki kwanta a asibiti tsayin lokaci ace nida nike matsayin mijin ki bani da masaniya akan hakan sai iyayen kine zasuyi dawainiyar da nine ya dace inyi? Fateemah mai yasa kike son ki zubar min da kima da darajar da nike da ita a idon iyayen ki ne? Ke a ganin ki abu mai kyau kenan kika aikata, kina da ciki baki sanar dani ba baki da lafiyan ma shima bazaki iya sanar dani ba karfa ki manta cewa ni d’in nan nine mijinki uban cikin dake jikin ki kuma, amma kika wofantar dani akan wani abunda bai taka kara ya karya ba, wai me yasa kikeyin hakane ke?”
“Ai kaima tunda na dawo baka kirani ba, ai ya dace ka kira kaji kona iso lafiya ko a’ah amma da yike kana tareda wacce ta d’auke maka hankali ai bakayi hakan ba, alhalin ni kuma Allah ne yayi da sauran shan ruwana a gaba da har muka iso garin nan lafiya ban mutu a mota ko rasa d’an cikin da nima ban san cewa ina d’auke dashi ba, kuma da kake cewa ban kiraka ba nida nike ta kaina ne zan kira ka, bayan tunda na iso har yau ban k’ara samun cikakkiyar lafiyar jikina ba, kuma ai tunda ina da iyaye a raye kasan zasu kula dani”
“Kinga ni koh?
Wannan shine matsala ta dake, domin kwata kwata bakya son gaskiya ke kullum gani kikeyi cewa komai kika aikata akan dai dai kike, kuma ko mutum yaso ya miki gyara bazaki tsaya ki saurare shiba ma balle har ki gane inda ya dosa, ai nasan kina da iyayen tunda a gaban su na auroki amma ai hakkin kula dake yanzun a hannuna yake ba a wuyar suba, akan me zaki d’aura musu lalurar da kika san bazai gagareni d’auka ba, anyi magana kince ina can hankalina wajen wata saboda ita kika sa a cikin zuciyar ki yarinyar da ita sam naki damuwar baya gaban ta ita ta kanta kawai take, kuma in ban damu dake ba ai kin san bazan bar duka uzurorin dake gabana kawai dan inzo in ganki bayan kin b’ata min raiba”
“To nidai ai na baka hakuri kuma ai namaji sauk’i dan Allah kayi musu magana su barni in koma gida wallahi bana son zaman asibitin nan kullum idan nace su sallameni sai suk’i”
Tashi yayi daga kujerar da yaje zaune ya koma kan gadon sai da ya sanya hannayen shi ya dago ta daga kwancen ya zaunar bayan ya d’an jingina ta a jikin shi, wanda dama ita din abunda take buk’ata kenan wato ta rab’u da jikin nashi dan haka sai ta k’ara shigewa cikin jikin nashi da kyau,
“I miss you nayi kewar ka sosai ina ta ciwo baka nan”
“Bakiyi kewata ba da kinyi da kin nemoni da kanki”
Ya fad’i hakan a yayinda ya k’ara tallafeta a cikin jikin shi,
“Wata nawa ne cikin?”
Ya tambaya bayan ya d’aura hannun shi kan cikin ta saman riga yana shafawa,
Karo na farko data sakin mishi kayataccen murmushin ta da har saida sautin shi ya fito, hannun ta ta maida akan nashi hannun sukaci gaba da shafa cikin a tare,
“Wata biyar, kuma nima ban san da cikin bafa tunda ina ganin period wai ashe ina da ciki sai yanzun daya girma ne nike mishi laulayi”
“Sannu Allah ya rabaku lafiya”
“Ameen, ya ka baro mutanen Zaria?”
“Kowa yana lafiya”
“Harda Amaryar ka?”
“Ai kowa nace miki”
Shiru sukayi dukan su babu wanda ya k’ara cewa komai har zuwa wani d’an lokaci, can ta fara laluban shi jin tana neman taso mishi da tarzoma ne hakan yasa ya fara kokarin zameta a cikin jikin shi,
“What ๐ฆ? ”
Ta tambaya tana kwabe fuska,
“Amma kinsan cewa a gadon asibiti kike koh?”
“Amma ai nayi kewar ka”
Ta fad’a tana k’ara kwanciya a cikin jikin shi,
“Yes I know and I miss you too, amma koma miye ki bari har ki k’ara samun karfi ki koma gida tukun”
Shesheshekan kuka ta fara kasa kasa,
“Wai me nene kuma?”
“Nidai wallahi ban yarda ba wata nawa?”
“Oh bazaki hakura ba dai kenan?”
“To ai ba dagani bane Baby ne ke son gaisawa da Daddy mana tab’ama kaji” ta kamo hannun shi ta daura a k’asan marar ta, kamar d’an cikin yasan hannun waye a wajen kuwa ya motsa,
“Kaji koh?”
Ta tambaya tana mai kallon shi, a marairaice,
“Koma miye hak’uri zakiyi har zuwa gobe in aka sallame mu sai mu wuce gida kalli fa kiga dare yayi,”
Ya mata nuni da agogon dake cikin d’akin,
“Ki kwanta kiyi bacci” ya fad’a bayan ya danna abunda ake kiran nurse din da ke kula da ita,
“Zanyi fitsari tukun”
Sai da ya kamata har zuwa cikin toilet din tayi fitsarin sannan ya bata umarnin cewa ta d’auro alwallah kafin ya kamota a jikin shi suka fito daga cikin bayin,
Koda nurse din ta iso tayi mamakin ganin shi a cikin d’akin dan tunda aka kawo teemah asibitin itace ke kula da ita kuma bata tab’a ganin shi a cikin yan dubiya ba, sannan kuma tasan su yan uwan ta da wuri suke wucewa basa kai dare har haka,
Dan haka bayan ta gaishe shi wanda ganin yanda yake ta lallab’a Teemah har ya kwantar da ita kamar wasu masu tsoron kada cikin ya fad’o daga jikin teemah din ne tace dasu,
“Madam akwai abunda kike buk’ata ne?”
Tayi tambayar cikin harshen turanci,
Sarki ne ya amsa ba tareda ya kalleta ba da cewa,
“Eh muna buk’atar k’arin bargo da pillow guda d’aya”
Shima da yaren turancin ya amsa mata,
“Amma sir anan d’in ba’a barin wani ya kwana da mara lafiya mune ke kula da komai da mara lafiya zai buk’ata, ina ga da kayi hak’uri ka tafi gidan in yaso sai ka dawo da safe”
“Duk na san wannan tsarin naku sai dai kuma nima yau ina buk’atar in kula da matana da kaina kinga kema yau sai ki samu hutu tunda ni zan canje ki, kuma dai ai kamar babu wanda yasan ina cikin nan d’in sai ke kad’ai koh? Kinga in kikayi shiru har zuwa safe ma babu mai gane cewa wani ya kwana anan”
Ganin yanda yake maganar a kame babu alamun wasa ne ya sata amsawa da to ta juya taje ta kawo mishi abunda ya buk’ata d’in,
Tana fita ko ya maida kofar ya kulle ya dawo ya cire rigar jikin shi ya rage daga shi sai dogon wando da singilati wutar d’akin ya rage ya bar mara haske sannan ya k’ara komawa can gefen inda Teemah ke kwance ba wai dan tana bacci ba ya zauna, ita kuma sai ta rik’o tafukan hannuwan shi yasa a kan pillow sai ta maida kanta a kansu tayi pillow dasu,
“Sarki”
Ta kira sunan shi da k’aramar murya,
“Ai dai nace kiyi bacci dare yayi koh,”
“Kana jin sona a cikin zuciyar ka irin son da kake cewa kana min kafin muyi aure da farkon auren mu?”
Mai makon ya bata amsa sai ya zame hannun shi ya d’agota daga kwancen ya zaunar, pillows din ya gyara ma zama ya jingina su da fuskan gadon shi kuma sai ya haye saman gadon ya jingina da pillow din ya ware kafafuwan shi sai ya zamana ita ta koma tsakiyar cinyoyin shi,
Sai da ya gyara mata zama a wajen da kyau ta yanda bazata takura ba sannan ya amsa mata da cewa,
“Dama ni nace miki na fara sonki ne dan in dena son naki wata rana?, ke d’in dai Fateemah ke nike so tun kina da yarintar ki haka kuma zanci gaba da sonki har tsufan ki, a zaton ki dan kinyi haihuwa d’aya biyu hakan zai sa in canza miki ne? To ki sani ko duniyar zaki cikamin da yara indai kece uwar su zan rungume ku ke da su cike da farin ciki saboda kaunar da nike miki ba mai k’arewa bane, komai zaki min zanyi hakuri dashi inci gaba da kauda kai saboda son da nike miki ga darajar yara kuma dana iyayen mu,”
“To kana sona da yawa haka me yasa kayi min kishiya?”
“Amma koma ya akayi ai kin san komai tunda a lokacin babu abunda na b’oye miki kuma kika bani goyon baya,”
“Kuma ai an kirani ance min ka saketa amma da kazo nan ai gashi baka fad’amin ba”
Ajiyar zuciya ya sauke a bayyane, lallai ya tabbata kenan ashe komai dake faruwa a zaria akwai masu kaimata rahoto tana inda kike,
“Fad’amin dad’i kikaji da akace miki na sake ta ko me?”
“To ni na san abunda ya had’akune, kuma ai kaima kasan bazanji haushi ba”
“Shi yasa nace kina da son kanki da yawa Teemah, miye abun farin ciki dan mijinki ya rabu da macen da yake aure, cewa fa akayi ciwon ya mace na ya mace ne”
“Eh haka suke cewa amma ai kowa yasan in mutum na ciwo sai dai a tayashi zaman jinya wajen ce mishi sannu da kuma fatan samun sauk’i amma shi kad’ai yake jin azabar ciwon shi a jikin shi, ni dai bazanyi bak’in ci wai dan ka auri mata kun rabu ba, tunda ita ce ta auremin miji ba nice na aure mata miji ba”
“In ita ta tafi wata ai zata shigo ne zuwa gaba”
Ya bata amsa ba tareda ya damu da irin zaburar da tayi daga jikin shiba,
“Wani auren zaka k’arayi kuma bayan wannan?”
Ta tambaya kamar zata fashe mishi da kuka.
*UMMIEE ZARIA*โ๐ผ