Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 29

Sponsored Links

Kafin su iso gidan kawu ado gari yayi haske tarwai,don har wasu daga cikin mutane sun fara fita zuwa sabgogin gabansu na rayuwa.

Area din da gidan kawu ado yake,area ce mai dan kyau,saboda akwai gidajen dake da ginin bulo ma,kamar yadda gidan kawu adon yake ginin bulo,da malalen siminti a tsakar gidansu,wanda hakan yasa gidan ya bambanta da sauran gidaje wansa jar qasa tayi musu qawanya har cikin tsakae gidajensu.

Da sallama suka shiga gidan,matarsa dake cikin dakin girki ta amsa tana leqo da kanta daya dan rage girma saboda hayaqin icce da take amfani dashi.

Suna hada ido da umma saita miqe tana fitowa daga dakin girkin

“Lale maraba,kune a tafe?” Ta fada fuskarta a washe tana qoqarin goge fuskarta,gefe daya qasan zuciyarta tana mamaki

“Wallahi mune tsaiba,kin ganmu da sassafe ko?” Murmushi tayi tana qoqarin karbar kayan hannun umman,don tsaiban badai kirki da daraja dangin mijinta ba

“Ah haba dai yaya?,wacce safiya?,bayan yara ma duka sun wuce makaranta?,ku shigo daga ciki mana” ta fada tana yin gaba,umma bilal da kaltum bita a baya,tana sake musu barka da zuwa.

Faffadar rumfarta dake malale da leda da kujeru ‘yan duƙui duƙui suka shiga,ta ajjiye kayan itama tana zama idanuwanta kan bilal

“Bilalu,zauna a hankali,amma dai bilalu babu lafiya ko?” Murmushin da yafi kama da yaqe umma tayi

“Baya jin dadi”

“Haba ai na gani,Allah ya sawwaqe…..ina kwana yaaya zuwaira” taqarashe zancan nata tana hadewa da gaisuwa zuwa ga yayar mijinta

“Lafiya lau tsaiba alhmdlh,ya gida ya yaran?”

“Lafiya qalau yaaya”

“Adon baya nan ko?”

“Wallahi ya fita ta’aziyya yaaya,amma ba nisa yayi ba,nan unguwar dake kusa damu ne,bazai jima na,natabbatar yana hanyar kusa da dawowa”

“To shikenan”umman ta fada,sai tsaiba ta miqe

“Kaltum,zoki karbqr muku abun kari” cewar tsaiban tana ficewa,ba tare da jinkiri ko bata lokaci na kaltum ta rufa mata baya.

Kunu ne mai zafi ta zuba musu cikin kwanon sha,sai ‘yar tsala data ji mai da quli mai dan yawa itama da duminta.

Bilal da bai wasa da cikinsa tuni ya miqe ya zauna ya fara kaiwa cikinsa,duk sai suka zuba masa ido cikin yanayin tausayawa suna kallonsa,kaltum ta janyo kofi guda biyu ta zuba kunun,ta miqawa ummansu daya,saifa girgiza kai

“Kusha kaltum,bazanci komai ba yanzu” narkewa kaltum tayi kamar zata saki kuka

“Don Allah ummanmu kisha,yana da yawa fa bare kice bazai ishemu ba” ganin yadda kaltum din tayi yasa ta miqa hannu ta karba,saidai iya kunun kawai ta iya sha,tana sha shi dinma tana ji yana tsaya mata a wuya.

Koda suka gama kaltum saita tattare kwanukan ta fice dasu,ta hada cikin wanke wanken da tsaiban bata samu yi ba ta ja ruwa mai yawa ta fara wanke mata su,tana mamakin meye amfanin su sahura da karimatu da bazasuyi mata shi ba kafin tafiyarsu koma ina ne,tanayi tsaiban na janta da hira har ta kusa gamawa,dai dai lokacin da kawu ado yayi sallama ya shigo gidan.

“A’ah’ah….batan kai kikayi ne kattume?” Kawu ado ya fada yana murmushin mamakin ganin kaltum din a gidan,saboda yasan halinta na rashin son zuwa gidan mutane,tana murmushin maganar daya fada din ta gaidashi

“Aiba ita kadai bace,ita da yaya zuwaira ne,tana ciki” tsaiba ta fada ganin yana shirin zama

“Au to….ma sha Allah,bari na samesu” saiya qara gaba zuwa dakin,ya cire takalmansa ya shiga,ganin haka yasa kaltum data gama wanke wajen ta kife mata kwanukan,sai tayi zamanta a nan tsakar gida ba tare data koma cikin dakin ba.

Kusan awa guda ya kusa shafewa a dakin,batasan me suke tattaunawa ba,taga dai daga bisani kawun ya fito ranshi a bace,ya kuma baiwa tsaiba umarnin a sake share musu dakin,zai aiko da ledar tsakar daki a shimfida musu,ta samu labule ta saka musu window da qofa ta amsa masa da to.

Ba’a kai dare ba kuwa aka shimfida musu sabuwar leda,sai labule da tsaiba ta kafa musu,ta kuma basu babban zanin gadonta saboda kwanciya.

Su zasu dinga kwana na cikin dakin,bilal kuma za dinga kwana tare da yaran kawu ado maza.

Kwanakin da sukayi cikin gidan hankalinsu a kwance yake,babu rashin ci babu rashin sha,babu kyara,babu tsangwama,tsaiba nada kirki sosai,hakanan yaranta basu da matsala,idan ka dake karima da sahura,wadanda suke jin kansu da nisa,hatta tsaiba da take a mazaunin uwarsu ba wani mutuncinta suke gani sosai ba,kowa yasan halin kaltum,bata daukan raini,don haka tunda tazo gidan taja jiki dasu,babu abinda ke hadasu,ko dakinsu ba shiga suke ba,sai idan zasu gaida ummansu.

Komai na tafiyarmusu lafiya,saidai ta lura umman nasu na cikin damuwa,ga yarinta da quruciya irinta kaltume,bataga wani abu da zai sanya umman nasu damuwa ba,bayan Allah ya musu sauyin wajen zama,zasu ci susha su qoshi ba tare da sun sha wahala ba,babu mai gaya musu baqar magana ko ya bata musu rai,ita kam bata ga wajen daya fi nan ba,addu’arta ma su dawwama a nan,suyi zamansu kawai.

*******Bayan sallar magariba ne suna cin tuwon dare ita da ummanta a kwano daya bilal ya shigo,tunda ya futa sallar magariba sai yanzu a dawo,mutum ne shi mai saurin sabo,gashi na jama’a,don kwata kwata bashi da qyuya ko son jikinsa,hakanne yasa duk inda ya shiga zaka ga nan da nan ya saba da jama’a.

Zubewa yayi saman tabarma yana yamutsa fuska,umman ta kalleshi

“Kai kuma fa?”

“Ahto,tambayeshi umma,tun shekaran jiya ya dauki wannan sarar ta yamutsa fuska da riqe ciki,a yanzu dai babu yunwa ko qishirwa bare kayi mata sharri”

“Ni tunda muka zo gidan na ban taba jin yunwa ba,kawa dai cikina ne yakemin ciwo” tsaiwa da cin abincin ummansu tayi

“Tun yaushe kenan?” Dan jim yayi kafin ya amsata

“Gaskiya tun washegarin ranar dasu yaya munxali suka dakeni” tsame hannunta umman tayi daga kwanon abincin,sai kaltum tace

“Ai dole kayi ciwon ciki,har cikinka suka nausa fa,saidai Allah ya saka maka,azzalumai…..” Kallon da umman dake qoqarin kwance habar xaninta ta watsa mata yasa ta tsuke bakinta,ta ciro naira dari biyu,cikin irin kudaden da kawu ado yake bata duk idan zai fita

“Habibu ya rakaka dan case dincan da ake baka magani,ka siya maganin ciwon cikin” sai yasa hannu ya karba yana miqewa

“Tsaya na rakaka,kada kaje ka musu shirme” kaltum ta dakatar dashi tana miqewa,saita fita waje ta wanko hannunta,sanna ta fara lalubem hijabinta.

Kallon hijabin tayi sanda take zurawa a jikinta,wanda ya bata kyautar hijabin ya fado mata arai,ba qaramin jin dadin hijabin take ba,don yana rufa asirin kodaddun suturar da take dasu,kamar bilal yasan tunanin a takeyi kuwa yace

“Oganmu na wajen aiki zaita cigiyata,sai ya jini shuru” ya fada cikin yanayin dake nuna kewa da alhini

“Nima ina saka hijabin na shi na tuna” kamar kuwa an wa bilal susa a inda yake masa qaiqayi ya shiga bada labarinsa,irin yadda yake kyautata musu,har suka fice daga gidan labarin da yake bawa kaltum kenan.

A dawowa suka samu sahura qofar gida tana zance,tana ganin dasowar kaltum din ta hade rai tayi kicin kicin,ganin haka sai kaltum din itama ta dauke kai suka shige da bilal da qwayoyin magungunan da aka bashi.

Duk da maganin daya soma sha dai ciwon sai a hankali,idan yasha maganin yana samun relief na murdawar ciwon,saidai bayan wani lokaci sai kaga yadawo,ganin haka yasa kawu ado ya daukeshi da kansa ya kaishi wani asibiti na sha katafi dake gaban qauyensu aka hada masa magunguna,kusan wuni sukayi a can din saboda babu wadatar ma’aikata,ga ubam himilin masu son a rubuta musu magani,hakan ya sanya a gaggauce suke komai,daka gaya musu abina yake damunka,babu wani dogon jira ko bincike zasu rubuta maka ganin da suke ganin shine ya dace da ciwonka ka qaro gaba.

Satinsu daya a gidan saiga habiba,tazo ta dinga kuka,wai don me zasu tafi basu gaya mata ba,sai dataje gida ta taras basa nan,yanzu haka daga gidan inna take,tace batasan inda suka nufa,sai da Allah ya kawo mata jafaru ya gaya mata,yace amma ita kanta innar batasan suna gidan ba.

A nan ta wunu ummansu tana lallabata don kada taqi komawa gida,ta cika tayi fam dasu munzali da babansu,tace inda tasan abinda ya faru kenan,ko barkar matar muzammilu ba zata je ba,suka hadu sukayita tattaunawa ita da kaltume,shidai bilalu da ciwon cikinsa ya motsa yana kwance yana jinsu,kafin daga baya bacci ma yayi awon gaba dashi.

Washe gari saiga inna ta duro,basusan a inda taji labarin suna gidan ba,ta dira da masifarta da bala’inta,da kuma maganganu masu tsauri marasa dadin ji

“Wato ke zuwaira kin zama kaska raɓi me jini?…..to nan dinma ba gurin zama kika gani ba,tunda dai ado bake kika haifamin shi ba,ki tattara kayanki ki sake sabon lale”

Maganar tayi mugun daga hankalin ummanmu,ashe dai da gaske bata da wani gata sama da gidan amadu?,duk da irin abinda yake mata?,ashe idan ta baro gidansa da gaske wajen xama ma saiya gagareta?,ashe gwara data dinga hadiye abubuwan data hadiye din shekaru masu dama?.

“Kiyi haquri inna,nan din dai gidana ne,mallakina ne,kuma dana bar yaaya zuwaira ta zauna ban sabawa Allah ba,tunda bata da wani wajen daya wuce nan,taje gidanki kin korota,kuma sannan nima kice na koreta?,bazan iya ba,a nan zata ci gaba da zama har zuwa sanda Allah zaiyi ikonsa” amsar da kawu ado ya bata kenan alokacin data umarceshi ya fatattaki umma daga gidan cikin bacin rai da takaicin halayyar innar tasu,daga haka ma saiya fice daga gidam gaba daya yadda ba zata samu damar ganinsa ba bare ta turasashi aikata abunda bazai iya ba.

Ai kuwa ta baje faifan masifa da bala’i da kuma cin mutuncinta,har tsaiba ranar ta amshi rabonta,duk da tarin kirkinta ranar ta fada komar inna.

Itadai umma tana daki tana kuka kaltume da bilal na tayata,basu samu sauqi ba har sai data taɓo ƴan rashin kunya sahura da karime shka wanketa fes,suna jinta tayi qus bata iya ce musu komai ba,saita fara tattara ya nata ya nata ta lalubi hanyar gidanta.

Kawu ado bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha’i,koda ya dawo sai daya fara shiga wajen umma ya ganta,haƙuri ya dinga bata yana kwantar mata da hankali kan babu inda zata in sha Allahu indai shine me gidan.

Murmushi tayi wanda yafi kama da yaqe,yaqen kuma da yafi kuka ciwo

“Babu komai ado,ni nasan komai me wucewa ne banda ikon Allah,amma abinda bake ganin yafi kamar yadda inna tace…..ka nema babansu habi muji ta bakinsa,idan da damar sasanci ma ayi mana” da mamaki kawu ado ya kalleta

“Amma yaya zuwaira hakan kuwa zaiyiwu?,kiga fa abinda mutumin nan yayi muku?,amma mu zamu nemeshi bama ni ba?” Sake murmusawa tayi wanda yake nuna zurfin haqurinta

“Shi aure ibada ne kamar yadda mai fura(kakarta) tasha gayamin,kuma kome zakiyi cikinsa,kisa a ranki saboda Allah zakiyi da cika umarninsa,babu gidan daya wuce gidan auren mace a wajenta,haquri kuma baya yawa,sannan duk sanda wani ya cuceka kasa a ranka sakayya na nan tahowa a kusa ko a nesa”

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke,kaf yaran innarsu babu wanda Allah ya yiwa baiwar haquri irin zuwairan,ya amince da haka dari bisa dari,inda ason ransa ne babu abinda zaisa su nemi amadu,zai riqe yaaya zuwairan ne har lokacin da zai gane kuskurensa,ya gane amfaninta ya biyo sahunta,iya tsahin shekarun zaman aurensu da amadun,kowa da kowa yasan akwai cutarwa,amma bata taba kai qararsa ba koda ga yan uwansa kuwa,har zuwa yanzu a shekaru fara turawa,to amma shi dui baiga hakan ba,sai shine ma zaice taje gida?,amma a yanzu dole ya sauke nashi shirin yayi amfani da abinda tace,tunda hakan takeso,amma yayi imanin masu juriya haquri da jajircewa,da daukar aure ibada dari bisa dari irin yayar tasa a wannan zamanin qalilanne,badan badan bama da sai yace babu su.

Kwana biyu a tsakani da yammaci,suna tsakar gida,kaltum tana yiwa inna tsaiba kitso,umma na saman tabarma sanye da hijabinta,da carbinta a hannu tana jan lazumi suna hira jifa jifa,kawu ado da bai jima da fita ba yayi sallama ya shigo

“Amadu ne shida iliya,ke karimatu” ya qwalawa diyarsa kira,wadda ke daki zaune,saita fito

“Dauko tabarma ki kawo dakin soro” ta amsa masa ta juya,ta fito da tabarmar takai musu ta dawo,sanna tace da umma taje inji kawun,bismillah tayi ta yunqura ta miqe ta fice soron.

Kaltum na yiwa inna tsaiba kitson tana saqe saqe cikin ranta,rabi da rabin hankalinta yana ga soron,saidai ba huruminta bane zuwa idan ba kiranta akayi ba.

Suna gama kitson kuwa kawu ado ya leqo ya kirayeta,ta saka nata hijabin tabi sahun ummansu.

Shida kawu iliya dinne kamar yadda kawu ado yace,sai cika yake yana batsewa,ummansu na daga gefe ita da kawu ado.

A sanyaye ta tsugunna ta gaidasu,ita dai bata kula ba baban nasu ya amsa ko bai amsa ba,ta samu waje kusa da mahaifiyarta ta rabe,sanda kawu ado yace

“To gata nan” gyara zama baban nasu yayi yana gyara zaman babbar rigarsa dake saman kafadarsa tare da cewa

“Yauwa…..to gata nan,tana daya daga cikin matsalolina na rayuwa,ta samu miji ta koreshi,kwanaki duk inda nabi sai naga ana nuna ni da baki,ana cewa diyata tayi cikin shege shi yasa aka fasa aurenta,kuma babu dama yayyensu din nan su muzammulu su saka hannu da zummar hukuntasu,sai ta haike musu tace bataso…..to yanzu dai duka ba wannan ba,na yarda zata koma dakinta,amma bisa wasu sharudda,idan ta amince falillahil.hamdi,idan bata amince ba taci gaba da zama,don ni bansan da wanne zanji ba,magana ta gaskiya ehe” ya qarashe maganar yana daga hannayensa sama.

Gyara zama kawu ado yayi yana qoqarin tausar zuciyarsa

“Sharudda kamar wanne da wanne kenan?” Ya tambayeshi yana zuba masa idanu

“Yauwa” ya ambata yana gyara zamanshi

“Na farko….duk sanda yaron nan bilalu ya sake dauko wani abun maganar,zan wanke masa hannu aka,sannan zan sallameshi daga gidana” wani kallo kawu ado ya bishi dashi,ya yunqura zaiyi magana umma ta dakatar dashi da idanunta

“Na biyu kuma….ita kattume,dama ma deba mata kwanakin fidda miji,to tun suna gidan nan kwanakinta sun cika…..zan mata adalci daya,zan qara mata sati biyu kacal ta kawo miji,idan ba haka ba,zan aura mata dan uwanta auwalu kowa ya huta”

Ba kawu ado ba kawai,wannan karon gaba dayansu suka daga kai suna duban baban,wala’alla maganarce tayi musa nauyi,sai ya waiwaya yana kallon dan uwansa

“Ko ba haka ba iliya?” Kai ya gyada

“Wannan haka yake,banda ma lalacewar zamani ai gida bata qoshi ba ba’a kaiwa dawa,sannan duk lalacewar naka ai naka ne,da a zamanin kakannu ne da saidai aji sanarwar daurin aure ma kawai,daga uwa har ‘yarta sai a sannan zasusan da batun” ya fadi kamar gaske yana wani tsume fuska.

Wani abu ne yazo ya tsayawa umma a wuya,kaltume kuwa tuni ta fara ruwan hawayem baqinciki da takaici,don ji take kamar ma an daura auren da auwalun,tunda dai a zahirin gaskiya ta sani cewa a yanzun bata da wanda zata bugi qirji tace shine maneminta,kawai sun qulla bata shi,shine za’a ce an bata sati biyu ta kawo mijia,ummanmu na ganin sanda kawu ado ya buda baki zai magana kan wannan hukuncin,tuni ta rigashi,ta bude baki da sauri tana fadin…………

 

30
D/Z

30

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button