Dabi’ar Zuciya 6
“Kambu” ta furta da qarfi,wani irin zabura baba laure tayi ta durfafi kaltum dake niyyar shigewa sashensu,kafin ta ankara harta shaqo wuyanta ta fisgota baya
“Ni kike zagi don u****rki kaltume?” Ta fada cikin hargowa da daga murya
“Kibar zagarmin uwa baba”
“An zagetan….ko zaki rama mata ne ‘ya’yan kuka?” Ta sake fadi hannunta riqe da bayan hijabin kaltum,wanda tuni ya feke sanadiyyar fisgotan da tayi,dubanta take ranta na sake baci,yana kuma raya mata abubuwa da yawa akan baba lauren,batason tayi rashin kunya,kota aikata abinda zai sanya ran ummanta ya baci….kafin tayi tunani na gaba ruwan ashar ya fara fitowa daga bakin lauren,wanda ya sanya umma fitowa daga daki kusan a tare ita da habiba bayan sun saki aikin da sukeyi.
Abinda ta gani din ya bata mamaki,laure riqe da hijabin kaltum tana dura mata ashariya,abu na tsaye abinta tana kallonsu hankalinta kwance.
Cikin sanyin nan nata ta qaraso tana duban laure,bayan ta dauke kanta daga irin ruqon da lauren ta yiwa diyarta
“Lafiya laure?,me ya faru?”
“Bani zaki tambaya ba,tunda kin fini sanin komai,qila ma ke kika aikota tazo ta zageni”cikin mamaki umman tace
“Zagi kuma?,kaltum?,ban baku irin wannan tarbiyyar ba” ta fada cikin takaici tana girgiza kai,ran kaltum ya baci,qiri qiri zata mata sharri ta bata ran mahaifiyarta,bayan itace silar faruwar komai?,saita fincike hijabinta daga hannun lauren,wanda hakan yasanya yagewar da yayi ya dadu,ranta a bace tace da umman
“Don Allah umma kada ranki ya baci,ki koma ciki kawai ki zauna,ni ban zageta ba na rantse da Allah,magana ta gaya miki ni kuma na gaya mata zahirin abinda ke faruwa,wanda ita batasan dashi ba” anzo wajen umman ta fada a ranta,har kullum idan kaji fadan kaltum dama ko waye to an taba tane,bata fiya fada akan karan kanta ba,ta rasa yadda zatayi ta rabata da wannan dabi’ar,saidai wasu daga cikin mutanenta na yawan gaya mata,kaltum din haka take,haka Allah ya halicci wasu bayinsa,me kishin uwace,ba yadda zatayi da ita
“Yimin shuru!,ni nafi kowacce halitta ne a duniya da ba za’a zageni ba?,annabin Allah ma aka zageshi wanda akayi duniya da lahira saboda shi,bare ni da ba kowan kowa ba?”
“Don Allah ummanmu kizo mu wuce mu qarasa aikinmu” habiba ta fada cikin yanayin bacin rai,duk da rashin son maganarta sai data tanka,saboda ranta baqaramin baci yake ba idan har taga ana yiwa kaltum din fada alhalin ita keda gaskiya,mawuyacine kaga tana fada da wani a sanadinta,saidai a sanadin uwa ko ‘yan uwanta,ko kazo mata da rainin hankalin da ba zata iya dauka ba.
Maganar habiban saita harzuqa laure tahau zage zagen umman ta haifa marasa albarkar yara,ana fara haka habiba taja hannun kaltum don kada a sake batacciya zuwa ciki,babu jimawa umman ta biyo bayansu,bayan tayi tayi da lauren tayi haquri amma ta qiya,wanda sai data kwashi tijararta iyakar yadda ranta yayi mata sannan abu ta janyeta zuwa sashenta ta dora a can.
Kaltum din na zaune gefe tana qoqarin saisaita kanta tana kallon yadda umman ta hadawa bilal ruwan zafi yake gasa jikinsa,sannan ta sanyashi ya shiga wanka,sai daya shiga wankan sannan ta waiwayo ya dubeta
“Allah ya shirya min ke,ya kuma sawwaqe miki,shidai haquri maganin zaman duniya ne,kuma riba gareshi,ki tashi ki wuce inda zaki,bance kuma ki sake kula kowa ba,koda su musbahu kika gamu dasu bance ki musu zancan bilal ba” daga haka ta sanya kanta cikin dakin,sai kaltum din ta miqe,don itama zaman gidan ji tayi ya soma yi mata zafi,ta taka ta fice,har a sannan tanajin tashin maganganu daga sashen baba iliya,duk da baka gane ainihin me ake cewa.
Harta xarta gidansu wasila saita yanke ta biya tacan ta rakata gidan kitson,da yake wani lokaci tana rakata,kuma wasilan na yawan qorafin yadda kullum itace a tafe gidansu kaltum din,amma ita ko kara batayi ta zo mata saida dalili.
Taje kuwa a sa’a,donta isketa fes da kwalliyarta,da yake suna da yan uwa a cikin gari da suke bata kwancen kaya,ita kuma tayita gayunta da qwalisa dasu,tasha yiwa kaltum tayin wasu ma kan ta bata kyauta,amma sai tace aah,nata sun isheta,duk da cewa a kode suke,amma bata taba sha’awar karba ba,ta samo wannan qwarin gwiwar da wadatar zucin daga wajen mahaifiyarta
“Qawata irin wannan shan kyau haka?” Kaltum ta fada wasilan na bata sha’awa,irin yadda ta samu kulawa daga wajen mahaifinta,duk da cewa tana talla amma ba talauci ne yasa take tallan ba,kawai sabo ne da kuma yanayin al’adarsu ta shegen neman kudi,ji take inama itace wasilar,wadda bata da wata matsala a rayuwarta.
Murmushi wasila tayi
“Kwalliyar bakarabe ce,yanzun nan ya tafi,Allah ne yayi ba zaku gamu ba” murmushi tayi tana dosana da wani dutse da mutan gidan ke zama kansa idan zasuyi alwala,sannan ta saki murmushi
“Kullum.zancanki kenan,idan kinaso mu hadu ai takanas zaki aiko kirana duk randa yazo” wannan ba shine karon farko ba,don tunda wasila ta hadu da balaraben take baiwa kaltum labari,bata taba hadasu ba,saidai idan yazo ya tafi ta bata labari dariya wasila tayi
“To kiyi haquri,zuwa na gaba in sha maka Allahu zan aika kizo kafin ma ya qaraso”
“To Allah yasa”ta fadi cikin rashin baiwa zancan muhimmanci
“Rakani kitso zakiyi dorawa don Allah”
“To bari na gayawa babarmu” ta fada wasilan tana wucewa ciki da ledar hannunta,da alama balaraben ne y kawo mata wani abun.
Bata fi minti uku ba ta fito tana ware mayafinta ta yafa saman kanta
“Muje” tayi gaba kaltum na biye da ita a baya.
Duk da yake ranta na abace ne amma tayi qoqarin sakin fuskarta,suna tafe suna hira da wasilan,wanda hakan yadan rage damuwar dake ranta,duk da komai yana nan daram cikin zuciyarta.
Basuyi nisa ba ta hango nasiru tun daga nesa,shi dinma ya ganta,hakan ya sanya ya saki fuskarsa sosai yana jifanta da fara’a tun kafin ya riskosu.
“Kinga wancan….dan bokon garin nan,sai murmushi yake mana” wasila ta fada tana washe baki,idanunta akan kaltum,shuru kaltum din tayi ba tare data ce komai ba,don nasirun yana gab dasu.
Bai wuce minti daya ba kuwa ya riskesu,idanunsa akan kaltum din,har yanzu murmushi yake
“Gimbiyata…..sai ina haka da ranar nan,anya kuwa kina jin zafin rana?” Murmushi itama ta saki,ba laifi nasurun ya iya magana ta nutsuwa kuma a tsare
“Dole ce ta sanya hakan….,ina yini”
“Lafiya lau gimbiyata….ina fatan kin wuni lafiya”
“Lafiya qalau…..” Saita waiwaya ta dubi wasila wadda ta zuba musu idanu tana kallonsu cikin mamaki
“Ga wasila nan,qawata ce,kuma aminiyata,ku gaisa” da murmushi ya dubi wasila
“Barka da warhaka hajiya wasila” qoqari tayi ta saita yanayin fuskarta sannan ta sake muryarta sosai
“Yauwa….barka kadai,nasuru ko?” Kaiya gyada
“Haka ne,ashe kinsan sunana” murmushi ta saki
“Na sani mana,ai kusan yammatan qauyen nan dai dai kune wadanda basusan sunanka ba,saboda banbamta da kayi dasu ta fannin ilimi” fuskarsa yadan motsa a mamakance
“Amma kuma cikin yammatan banda kaltum…” Saiya waiwaya yana dubanta,kafin ya dawo da kansa ga wasila
“Sanda na santa ita bata sanni ba,har sai dana gabatar da kaina dakuma sunana” dan tabe baki wasila tayi
“Idan ana magana ba’a sanyawa da kaltume,saboda kifin rijiya ce ita,daga daki sai tsakar gida,babu inda ta sani,ba wanda ta sani” murmushin farinciki ya saki
“Ma sha Allah,haka akeson mace ta zama ai” kafin wani cikinsu ya sake cewa wani abu kaltum din ta magantu
“Inaga zamu wuce,sauri nakeyi,nabar mutane suna jirana” saiya waiwaya ya maida hankalinsa gareta
“To shikenan….amma yau zan samu ganinki?” Kaita kada
“Gaskiya bana jin….”
“To gobe fa?”
“Allah ya kaimu” ta fada tana fara yin gaba,wanda hakan ya sanya wasila biyota suna sallama da nasiru.
Shuru ne ya ratsa tafiyar tasu ya maye gurbin hirar da suka dinga yi a daxun,zuwa wani lokaci kaltum ta ankara,ta waiwaya ta dubi wasila,sai taga kamar yanayi fuskarta akwai damuwa,dama kuma ita ke qoqarin sanyo hirar tun daxu,kaltum din tayata kawai takeyi
“Lafiya dai ko wasila?” Da sauri ta dubi kaltum din,sai tayi murmushi tana kada kai
“Lafiya qalau….”
“Naga kamar damuwa a fuskarki,wadda babu ita a dazun” shuru ta danyi kafin ta sauke ajiyar zuciya,sannan ta fara magana a hankali
“Gaskiya bazan boye miki ba kaltume,banji dadin yadda kika boyemin soyayyarki da nasuru ba,a matsayina na aminiyarki,ace kun fara soyayya da nasuru amma ni ban sani ba,badon idanuna sun gani ba da sai yaushe kenan zan sani?” Hannun wasila ta kama tana murmushi
“Haba qawata,ba’a wani dade bafa sosai” hannun nata tadan zame da qarfi
“Ni ba abunda zaki gayamin,tunda ko na kwana daya ne aiya kamata na sani ko?” Dan jimm kaltum tayi tana mamaki,saita sake cewa
“Kiyi haquri wasila,bansan zakiji babu dadi ba,amma hakan ba zata sake faruwa ba”
“Shikenan,ya wuce” ta fada muryarta can qasa sosai,daga haka sukaci gaba da tafiya,saidai har a yanzun ma tafiyar kurame ce ba kamae dazun ba,hakan yasa kaltum take ganin kamar hucewa ne wasilan har yanxu batayi ba,don haka ta dinga qoqarin sanyo hira a tsakaninsu,da haka suka qaraso gidan.
Jan tunga wasila tayi tana duban kaltum
“Kaltume…kamowa zanyi gida fa” cike da mamaki kaltum ke kallonta
“Gida kamar yaya?,lafiya?” Fuskarta tadan yamutsa kadan
“Banajin dadin jikina ne”
“To…..baya bata da kadan” kaltum ta fada tana dan yin jim sannan ta dora
“Shikenan,Allah ya sawwaqe,ki koma din ki samu ki kwanta ki huta,idan na dawo zan biyo ta gidan na ganki,Allah ya sawwaqe” tana nan a tsaye har sai da wasila ta bace sannan ta saka kai gidan,zuciyarta duk babu dadi,musamman yadda suka taho tare kuma lokaci daya irin haka ta faru.
Data gama kitson sai data biya ta gidansu wasilan kamar yadda tayi alqawari,Saidai ance mata bacci take,don haka ta yiwa babarsu sallama ta wuce zuwa gida.
*_BAYAN WANNI BIYU_*
A inda suka saba zama koda yaushe cikin tsakar gidan nasu suke zaune bayan sun idar da sallar magariba,ummansu na saman tabarma ita da habiba,kowanne lazumi yake,yayin da kaltum ta shimfida sallaya tayi tata sallar,kuma tuni ta idar,rashin wani abu da zatayi ya sanyata dauko pencil ruler da farar fefa da usaina ‘yar maqotansu ta bata kyauta,ta zauna sosai saman daddumar yadda zataji dadi,saita zubawa takardar idanu tana tunani,xane takeso tayi,saidai ya rasa me zata zana,murmushi ta saki samda zuciyarta ta bata shawarar zana duk abu na farko da yazo kanta,sai ta sake sakin murmushi karo.na biyu,ta duqa a hankali ta ware takardar ta soma zanen cike da nishadi,tana kuma rayawa a ranta,daga wannan karon duk abinda ta zana din zata dinga ajjiyewa ne,tana gani itama tana tunawa,bata mantawa,cikin irin hirarrakin da sukeyi da nasuru,sanda ya taba ganin wani qaramin gida irin nasu na karkara data zanawa ‘yar maqocinsu,ya shaida mata cewa shi kansa zanen wani babban ilimi ne me zaman kansa da ake karatu a kansa,sai tayita mamaki tana jinjina abun,hakanan saita samu kanta da kwadayin inama ace zata samu wannan damar,ba shakka tana qaunar zane,kuma idan har zata samu dama,ko kuma a bata zabi,shi zata karanta kamar yadda nasuru ya shaida mata
“Inda ace ni wani ne,da bayan munyi aure,saina kaiki wannan matakin da zaki karanxi zanen” duk da ba cewa yayi ya dauki nauyi da alqawarin sanyata tayi karatun ba,to amma iya lafuzansa kawai sunyi mata dadi,harta kasa haquri sai data tanka
“A hakanma na gode qwarai da gaske,tunda ka bani labarin wani abu da bansan da wanzuwarsa ba a duniya,idan da rai da rabo,matuqar ina da rabon sai kaga wataran nayi” wannan ce amsar da ta bashi.
A hankali suka fara jiyo sautin murya,kamar fada fada kamar zage zage,dukkansu sukayi sak,kowa ya tsaya da abinda yakeyi,jin cewa muryar asiya ce,kuma sassansu take dosowa.
Ba wani jimawa ta bayyana a qofar shigowa sassan nasu,ta tsaya ta kama qugu,tana iya hangen duk wanda yake tsakar gidan,maganganu take fada na rashin kunya da rashin mutunci akan kaltum,wanda duka kan abinda ya faru ne dazu
“Munafuka algunguma,ina bacci anamin munshari,jahila kawai,wadda bata taba shiga aji ba,to wallahi duk munafurcin mutum saidai yayi ya bari,don ni na tserewa sa’a,na kuna wuce ajin mutum,hakanan aibantawar mutum b zata mana komai ba ehe,mun sha tabara mun sha yasin,mun kuma sha rigakafin Allah Ala tsine”.
Duk da kalaman asiyan sun mata zafi,duk da ranta ya baci amma bata daga kanta ta kalleta ba,sai kawai taci gaba da zanenta,hakan ya sanya taci gaba da zage zage cike da rashin mutunci.
Wannan karon habiba ce ta gaza daurewa,ta miqe tsaye tana duban asiyan daga inda take tsaye
“Ke asiya dalla ki shiga hankalinki,saboda kinga an miki shuru shi yasa zakici gaba da rashin mutunci?,ki tako har cikin gida kice zaki mana rashin mutunci,kema kinsan wallahi baki isa ba,banda darajar wasu da kike ci”
“A hayye,ai so nake na daina cin darajar wasun,idan an gaji a dauki mataki a kaina kawai,tunda tsohuwa na zaune ko?,to bari kiji,wallahi bana tsoron ta mutu balle tayi rai,ko ita ta shiga hurumina bazan raga mata ba,ni babu datajar wanda zataci a wajena….yo ina ma masu darajar suke da zataci ta?….” Ai kaltume batasan sanda ta zubda abun rubutun dake hannunta ba,tayi fatali tabi ta kansu,cikin wani irin gaggawa da sauri wanda babu wanda ya kula dashi ta isa gaban asiya,sai jin saukar wani lafiyayyen mari taji saman fuskarta,wanda ya sanyata ganin wulqawar wasu taurari gami da daukewar ji da ganinta na wani lokaci,kafin daga bisani komai ya dawo dai dao,sai sannan ta tsinci muryar kaltum cikin tsananin fushi tana bata gargadi a kausashe
“Nan gaba idan tashen iskancinki ya tashi,qwaqwalwarki ta sake gaya miki kizo ki tabamin mahaifiyata!”kiran sunan yayi dai dai da sanda umman ta qwalla ma kaltum kira,hankalinta a tashe,don ita din babu abinda tafi tsana irin tashin hankali,cikin tsawa umman tace
“bar wajen nan kafin na qaraso nayita dukanki a wajen” ta idar da abinda ta niyyata,don haka ta juya da niyar komawa mazauninta,saidai ina,tuni asiya tayi wani kukan kura takai mata cafka,cikin qaraji tana fadin
“Wallahi baki isa ba,ba zaki daki banza ba” ta danqaro ashar ta makawa umman da kaltum,wanda hakan ya sake harzuqa kaltum din,ta waiwayo ta dumfari asiya,take kokawa ta barke a tsakaninsu,soma qoqarin miqewa umma tayi cikin dabara saboda ciwon dake qafarta,tana umartar habiba kan ta rabasu,saidai habiban gefe ma taja abinta tana shan kallo,don tana da tabbacin yau dai za’a dan fiddawa asiya raini,wanda kafin umman ta samu zarafin miqewa takai dauki kaltum din ta daki asiya sosai kuwa.
Dai dai sanda take rabasun baba laure ta fito,saita soma ihu itama tana son rabasu,wanda fiye da rabin rabiyar taimakawa asiya take wajen dukan kaltum,cikin ikon Allah Allah ya jefo malam amadu mahaifinsu kaltum,wanda yana shigowa ya daka musu tsawa,take kowa ya tsaya cak,sannan ya fara neman ba’asi.
Take asiya ta sake rakwarkwabewa fiye da dukan da akayi mata,ta saki kuka mai qarfi ta fara rattabo bayanan qarya,take malam amadu ya gasgata hakan,don ko sanda ya shigo din kaltum na riqe da asiyan ne.
Baiyi wata wata ba ya kaiwa kaltum dake tsugunne a gabansa mari,ya kuma sameta sai tau a fuskarta,take shatar yatsunsa suka samu muhalli a kumatunta,inda ace fara ce ma babu abinda xai hana a gani a haske farin watan daya dallare ilahirin tsakar gidan
“Wacce irin ‘yar Allah bani ce ke na haifa?” Kalmar data fara fita a bakinsa kenan,wadda ta sanya umma rintse ido,saita juya a hankali don komawa cikin sassan,don dambe ya fito dasu ne har filin tsakar gidan nasu.
Ta zabi komawa ciki ne,don kunnuwanta ba zasu iya jure mata jin kalaman da ya fara furtawa ba,wanda tana da tabbacin cewa,tunda ya fara da haka,Allah ne kadai masanin sauran kalaman da zasu biyo baya.
“Ni na gaji dake,na kuma gaji da halayanki,nayi na Allah nayi na ma’aiki,shekarunki sunkai ki tafi gidan mijinki dama kije can ki qarata….ko.kasheki ma zasuyi ke kika so,yau din nan na bada ‘yar uwarki habiba ga yusufun malam baffa….. Saboda haka na baki nan da kwana uku rak!…ki gayawa duk wanda yake zuwa wajenki,koda bai shirya ba ya fito,ya tanadi sadaki kawai,idan ba haka ba kuwa,zan bawa duk wanda naga dama” daga haka ya juya yana baiwa asiya haquri,wadda ta saki baki taketa sharbar kuka fiye da dukan da akayi mata,itadai kaltum tunda ta dafa qasa ta miqe zuwa ciki,ta samu takai kanta dakinsu,bata sake bi takan komai ba.