Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 5

Sponsored Links

Jiki a sanyaye tabi tabayan umman nata sanda taga ta jibge himilin wankin innar ta soma jan ruwa,ta karbi gugan don taja mata,har ta qiya sai da kaltum din tayita mata magiya sannan ta sakar mata,tana ja mata ruwan tana tara mata zuciyarta na mata wani irin nauyi saboda tausayin umman nata,da dabara da wayo ta kama mata wankin suka dinga yi tare,saboda su samu su gama da wuri,tana jin innar nata jansu fatsima da hira bayan ta hanasu zuwa inda suke,suma basu sake wani jimawa ba suka yiwa innar sallama sukayi tafiyarsu gida,don duk cikin ‘ya’yan qannen umman tasu sunfi shiri dasu kaltum din akan kowa.

Bayan fitarsu saiya zaman gidan sai su yasu,innar bata sake kula kowa cikin umman da kaltum ba,sai qananun mitoci da taketa faman yi lokaci zuwa lokaci,wanda kusan fiye da rabi gugar zana ce baqar magana da habaici take yada musu,dukkansu sun fahimta,saidai babu mai ikon tankawa ko nunawa a cikinsu,duk da kaltum ta cika ta tumbatsa,amma dole ta lanqwasa zuciyarta saboda farincikin ummanta.

Basu kammala ba sai da akayi sallar la’asar,don daga nan ma alwala suka daura,suka bada faralin saman shimfidar innar,wanda zuwa sannan ta tashi.

Waiwayowa umma tayi tana duban kaltum
“Ki tafi gida hakanan kije ki samu ki yiwa matar malam kitson,don nasan yanzu haka tana can tana jiranki” sam ko kusa ko alama batason ta motsa tabar umman tata a wannan gidan,saboda haka tace da ita
“Ke kuma fa umma?”sai data shafa addu’a sannan ta bata amsa
“Zan dan qara dakatawa saboda qila inna zata buqaci a dafa mata abinci”
“Umma ma tafi tare,tunda ga kudin kawu ado a hannuna xamu iya amfani dashi koda baba bai kawo komai ba” kai umman ta girgixa
“A’ah kaltum,ita sana’a aiba sai sanda ake da matsala ake nemanta ba,ba’a wasa da sana’a kaltum,tashi kije,saina taho” batason ta koyi yin musu da mahaifiyartata,don haka kawai ta miqe,ta karkade dankwalinta data shinfida ta daura saman kanta,ta maida hijabinta jikinta,sannan ta zira takalminta,duk yadda batason ta tafi tabar umman hakan dole xata tafin.

Bata wani tsaya yiwa inna sallama ba tayi wuf ta fice don kada ma umman ta tsaidata,tana tafe ita daya iskar la’asar tana busata,tunani ne fal kwanyarta,fuskar ummanta kawai take hangowa,yadda suka wuni suna wanki amma koda wasa…..ko sau daya inna batayi musu tayin abincinta ba,duk da kalolin cimar da taketa fama da ita,kallo daya ta yiwa ummanta ta fuskanci tana jin yunwa,fade ne ba zatayi ba,saidai ita tana iya karantar haka a saman fuskarta.

Bata isa gidan matar malam ba sukayi kacibus da nasiru,ya baibayeta da murmushinsa yana kallonta
“Daga ina haka sarauniya?” Murmushi kawai itama tayi ta rausayar da kanta gefe
“Naje duba inna ne?” Fuskarsa ta nuna alhini sannan yace
“Ayyah,bata da lafiya?”
“Eh wallahi…..amma dai da sauqi”
“To Allah ya qara mata lpy….zanje na dubata idan na samu lokaci” tana son ce masa a’ah,to amma batasan da yaren da zata gaya masa ba wanda zai fahimta,bugu da qari ma batason xancan nasu yayi nisa,don tana son cika umarnin ummanta
“Har zaki wuce da sauri haka?,bari na taka miki” ya soma motsawa da niyyar binta,saita dakata tana kuma tsaidashi
“Da ka barshi ma,na gode….kawai inason shaida maka saqon umma ne” cike da bawa maganar tata muhimmanci ya fuskanceta
“To…Allah yasa lafiya,me umman tace?”
“Tace idan harda gaske kake,ka soma neman izinin baba kafin kaci gaba da tsaiwa dani” shuru ya danyi,kana ya gyada kai
“Umma tayi gaskiya,in sha Allah kuma zanyi maganar,hakan shine dai dai dama” a nan sukayi sallama dashi,ta wuce,ya bita da kallo,tana sake burgeshi tare da shiga ransa,bugu da qari kuma zuciyarsa da ruhinsa cike fal da buri da fatan mallakarta.

**********
Shuru gidan yake sakamakon dare daya shigo,bayan sallar isha’i ne,bilal baya nan ya fita,wanda dama yawanci bai shigowa gida da wuri,barci ne kawai yake maidoshi,kamar ma bayajin dadin gidan sam,fadi ne kawai da baiyi ba,habiba kuwa na zaure ita da yusufa,wanda tuni ya aiko aka nema masa izinin zuwa wajenta,cikin ikon Allah kuma sai Allah ya hada kansu da hankalinsu gaba daya,yusufa da iyayen nasa ma gaba daya ba wasu baqi ko boyayyu bane,kowa yasan gidansu halayyar mahaifansa dama na yaran gidan,dalilin da yasa baaban baiyi wani musu ko goce goce ba ya bashi izini kai tsaye,don dama shi din kamar yana neman hanyar da zai rabu dasu ne.

Tsakar gidan daga ita sai umman nata,ita ta dasa farantin dake dauke da ragowar wata guntuwar shinkafa tasu tana tsinceta,don ita ce kadai abinda ta rage musu cikin gidan,itama cikin kudin da kawu ado ya basu ce suka siyota suketa ci da kadan kadan,sam abincin da mahaifinsu yake basu baya daga cikin abinda suke lissafa ko sanya rai,saboda babu tabbas din samuwar abincin,idan yaga dama ne ya kawo,idan baiga dama ba kuma ya barsu haka,sa nema suci.

Hira suke jifa jifa da umman,tana magana ne kan bikinsu idan ya taso,ta sani bata da komai,kuma bata bawa kowa ajiya ba,juyayin da take nunawa kenan,kaltum dake tsintar shinkafa kanta a qasa tace
“Babu komai umma,kiyi addu’a,Allah zai kawo da ikonsa” tana rufe baki suka hangi inuwa daga bakin qofar shigowa sassan nasu,hakan ya sanya kowa yaja bakinsa ya tsuke suna duban inuwar,ba’a cika minti daya ba wanda ke laben ya fado,mahaifinsu ne,duk da tsakar gidan babu wadatar haske amma suna iya ganin yanayin fuskarsa
“Munafukai….zancan wa kuke?,munafurcina ko?” Waike zuwaira me yasa kullum ta Allah baki da qoqarin da ya wuce ki barar min da mutuncina a idanun yarana?….ke kuma annamimiya muna fuka,tashi ki koma daki!”ya dakawa katum tsawa,wadda batasan hawa ba batasan sauka,saita sauke farantin kawai ta miqe zuwa dakinsu kamar yadda ya buqata,batasan me yasa ya tsani yazo ya ganta tare da mahaifiyartata a zaune su biyu suna hira ba,koda yaushe yana ganin kamar idan suka zauna kamar hakan hirarsa sukeyi,abinda bai sani ba shine,umman tasu bata taba tattauna kuskurensa ko sakacinsa dasu ba,bata daga cikin irin wadan nan matan,hasalima kosu basu iya suyi qorafi a kansa ba,duk yadda suka kai ga shaqar baqiciki ko bacin ransa,tana horarsu da suci gaba da kyautata masa,ubansu ne,mahaifinsu ne,kamar jiya,datayi kitso ta samu kudi,ta siyo sabulu,ta dawo gida tana tattara kayan umman tasu da sukayi datti,amma ba’a samu damar wankewa ba saboda babu kudin sabulu,amma sai umman ta dakatar da ita
“Kibar nawan,a wanke a gaba,ki debo na babanku,naga wankakkun nasa sun kusa su qare” bata isa ta musa ba,haka taje ta debo kayan nasa,duk da cewa dama can itace mai wanke masa kayan nasa,saidai ko idan wani dalili yasa bata yin ba,bilal zai dauka ya wanke masa,haka ta debo nashin,ta kuma qarar da sabulun kaf a kansu,saidai taci alwashin da zarar tayi wani kitson koda nata ba’a wanke suke,zata fara wanke na umman nata.

Daga cikin dakin tana iya jiyo sababin da baban nasu yakeyi,wanda ita batasan dalilinsa ba,idanunta ta rufe gaba daya ta kwanta rigingine,tana jin yadda kullum kwanan duniya rayuwa ke sake musu nauyi da kuma tsanani,a zuciyarta….bilal da habiba su tafi tausayawa fiye da kan kanta,sai kuma mahaifiyarsu,tana jin da tana da iko da su zata fara tsamewa daga wannan rayuwar da suke ciki,ta kowanne fanni babu dadi,babu wata walwala babu farinciki,batasan iya tsahon lokacin daya kwashe yana sababinsa ba,sai shigowar habiba taji,hannunta riqe da baqar leda,ta aje gefan kaltum tana dubanta
“Yaaya,kada dai ace har kinyi bacci” bata amsa ba sai miqewa da tayi ta zauna kawai tana duban habiban
“Idona biyu,baba yana nan?”
“Eh…..kamar yana dakinsa”
“Umma fa?”
“Tana bakin rijiya,ruwa take ja masa” ajiyar zuciya ta sauke,bakinta ya kasa furtawa habiba dake kallonta komai,har sai da ita habiban ta magantu
“Baba ne ko?” Bata iya amsa mata ba,sai kai kawai data gyada mata,bakinta ta tabe
“Ni ai gwara mutum kawai yayi aurensa ya huta da wannan rayuwar,yaaya gwara kawai muyi aurenmu,ko itama umma ta samu sauqin wasu abubuwan,tunda kinga ko banza zamu dinga taimaka mata da wasu abubuwan,sannan yusufa ma ni yace babu matsala,koshi xaya yimun kayan daki,don shi a nan kurkusa yakeso ayi komai” daga haka ta janyo.ledar ta bude,awara ce mai zafi mai uban yawa,sai qunshin tsire,sai rake wanda aka gyarashi fes,aka yankashi qananu
“Kinga abinda ya kawomin” ta fada tana turawa kaltum ledar,kalla kawai tayi,saita saki murmushi tace
“An gode” yusufa yana da qoqari,yana kuma da hannun kyauta,hakanan yana da kirki kamar yadda ake cewa mamansa ma haka take,sosai kaltume ke yiwa habiba sha’awar aurensa,a yadda kowa ke yabon halayyarsa,tana sanya mata ran cewa zata dace da gidan aure in sha Allahu.

Matsantawa kaltum tayi,har sai data raba abun kashi hudu,nata dana umma dana kaltum din saina bilal,basuyi tunanin su raba da baban ba sam,saboda sun riga sunsan halayyarsa,yanzu akan wannan sai qilu ta jawo bau.

*******

Karfe biyu da minti talatin da uku na azahar ta dage labulen dakin ummansu,wadda suke ciki ita da habiba sunata sauke kayan kwalla na mahaifiyar tasu,da tayi shawarar gwara ta saukesu ta saidasu tun yanzu saboda bikinsu,tunda ba wani abu suke tsinana mata ba
“Umma na gama zan tafi”
“To Allah ya kiyaye,kina gama mata ki dawo gida,kada babanku ya rigaki dawowa”
“In sha Allahu umma bazan zauna ba”
“Saikin dawo yaya” habiba ta fada,ta amsa mata tana sauke labulen kana ta doshi qofar fita daga gidan.

A farfajiyar data hada sassan nasu ta samu baabar asiya da suke kira da baaba laure,a zaune saman tabarma,qaqashin inuwar bishiyar data baza rassanta a filin tsakar gidan,da alama sassan nata ya dauki zafi,da yake shi rana yake kallo,hatta da rumfar dake sashen idan rana ta take zafi take dauka,a nan kawai suke xama su samu iska da inuwa mai kyau,sabanin nasu sashen,da ya bawa rana baya,saidai dakunansu kawai su dauki zafin,amma banda tsakar gidansu,duk da cewar tun asali kowa a muhallinsa yake a zaune,amma baba laure sai data qalubalanci hakan,tace anyi ne da gayya ana sane aka bata nan din,saboda rana tayi mata lahani ita da yaranta.

“Yar baqa mayya” taji baba lauren ta ambata,ta sani sarai da ita take,ta tsani sunan iyaka,kuma ita ta sanya mata shi,duk sanda ta tashi taji ‘yan wulaqancinta a kusa haka take kiranta,tasha ce mata
“Baba laure,ba suna bane me kyau,malam na makarantar asuba yace babu kyau mu dinga kiran junanmu da laqabi mummuna fa” saita rafka salati,tace tana son kiranta da jahila,ita zata yiwa kiɗifiri da iyayin banza da wofi,suna ne tun tana tatsitsiyarta ba xata fasa kiranta dashi ba,takan qara da cewa
“Wannan inda kinyi karatun boko Allah ne kadai masanin abinda zaki dinga yi,to sai Allah yasa wadanda ba’a so din su sukayi bokon,kuma sha maka Allahu su zasu zama madubin gidan nan,ehe” baba laure wata irin macace mai.matuqar son kanta,da son ‘ya’ya,son ‘ya’yan ma har yayi mata yawa,itafa duk duniya yaranta sune kawai ‘ya’ya,na kowa ma ya mutu,nata ya rayu,tunda ta taba zuwa cikin gari,taga yadda ake karatun boko,gidan da taje gidan qanwar qawarta ne data haihu,taga yadda suke karatun boko,taga manyan yaran gidan yadda suke,akace mata kowanne ma’aikacine,kuma boko sukayi,shikenan tunda ta dawo ta tasa baba iliya a gaba,ta dinga shirya masa zance,tare da nusar dashi romo da amfanin karatun boko,babu jinkiri ya gamsu,ya kuma yarda,suka ganganda dukkanin kudadensu suka tasamma sanya yaransu a makarantar boko ta cikin gari.

Tun ba’aje ko ina ba suka ga ba zasu iya ba,basu da sauran zabi illa su dawo dasu makarantar boko ta cikin qauyen,wadda a qalla shekara ashirin da wani abu da ginata,fiye da rabin ginin makarantar ya zube,a qarqashin biyu suke karatun,nan fa manyan yaranta maza guda biyu,munzali da muxammilu suka ce sufa ba zasuyi ba,a barsu kawai suje kudu neman kudi,juyin duniya sukaqi fafur,dole ta haqura,saita karkatar da akalar burin nata zuwa kan babbar diyarta mace wato asiya,burinta shine asiyan ta zama wata tauraruwa kuma ta musamman abar kwatance akaf fadin karkarar tasu,a lokacin da suna qananunsu,idan kowa yana fadin abinda yake sha’awar yi ko xama tsakaninsu kaltum da asiyan,idan kaltum tace zane takeso,kuma fannin zane zane takeson karanta,baba laure kan karkace tayita ɓaɓɓaka dariya,babu ma sanda taji ummansu na cewa
“To Allah yasa,Allah yasa ya zame miki alkhairi”, takan ce
” ban taba ganin mutane marasa sa’a a rayuwa ba irin zuwaira da yaranta,komai.naku ku a cabe yake zuwa?,banda tohewar basira me za’ayi da wani zane?,zanen ‘yan aljanu fa?tabdi,da alama a haka zaku qare ko,ni ai asiyata babu abinda ya dace da ita sai karatun aikin banki gidan kudi,ko karatun inda za’a dinga haqo man fetur,tunda ance shima abune mai daraja”umman bata taba daga kanta dai dai da rana daya ta dubeta kota dubin maganganunta ba,ko sau daya ita wannan baya a lissafinta,addu’arta…..burinta dare da rana shine su samu mazajen aure na gari,shine tabbas!…..shine dahir!….dahir din da babu gaibu a cikinsa.

Saidai abu daya da baba laure ta kasa fahimta,ta kuma kasa yiwa tufkar hanci,asiya tun tana qaramarta yarinyace maras kunya,bata da kunya ko qanqani,fadace fadace kullum yinsa akeyi da ita,dambe da maza ba sabon abu bane a wajenta,babu wanda take kunya ko tsoro,manyance a wajenta abun ba’a magana,maganganu kuwa idan tayisu saika dauka.macen aurenta ne,a sannan ana ganin a bakin mahaifiyarta da bata da kintsi take jinsu,musamman idan tayi baqi suna hirarsu,tun ana kallon abun a matsayin quruciya da tunanin zata daina,harya zame mata jiki,ta girma ta tashi a haka,sannu sannu kuma sai dabi’ar kwadayi ta shigi asiyan,wanda buri da son rayuwar jin dadi….da kuma son ganin ta kerewa duk wata sa’arta cikin qauyen suka haifar mata da hakan,dalilin kenan da ya sanya ta duqufa karatunta,duk da cewa bata da wata basira ko qwaqwalwa,idan kaga yadda take sakewa da malamanta,har wani lokaci suna wasan jakai kamar qananun yara xakayi.mamaki,wannan sake musun da takeyi ya sanya ko yaushe ita ce ke zuwa ta daya a ajinsu,don haka ma,saiya zamana bata wani damu da karatun ba,tunda zata zo ta daya,zata nunawa babarta,ita kuwa tayita tiqar rawa tana murna tare da yada habaici,shikenan tana ganin babu wani sauran damuwa,takanje makarantar sanda ta gama yawonta da xuwa duk inda zata,wanda kusan rabi amsar kudi ne daga hannun samari,wadanda saisun gama wasan banxa kamar wani miji da mata sannan su bata.

Ko sau daya baba laure bata taba damuwa da ganin gilmawar kudi a hannun asiya ba,bayan ta sani cewa….ba ita ta bata ba,ba mahaifinta ne ya bata ba,tunda dukkaninsu basu dashi,ba wata sanaa suke ko takeyi ba,amma sam hakan ba damuwarta bane,musamman idan ta tashi buqatar kudi,asiyan zata ranta mata,kota bata kyauta.

A hankali baba lauren ta fahimta samari ne ke yiwa ‘yarta hidima,a maimakon shiga tashin hankali a matsayinta na uwa,tsaurara bincike da yanke duk wata alaqa,saita hau murna,ranar kamar zata taka kan shege,ta yiwa yarta kirari a filin tsakar gidan nasu
“Kaga diyar da ba’a haifi kamarta ba kaf fadin qauyen ƊINYA,yarinya mai farinjini tamkar daren sallah,ah….ashe nidai na haifi mai sharen min hawayena ban sani ba,daa na qwallafa raina akan wadancan sakarkarun su muxammilu,wadanda saisunga dama zasu waiwayo gida su bani abinda sukaga dama,Allah ya karemin ke,ya tsole idanun maqiya” dukka wadan nan maganganun ta yisu ne sanda asiyan ta miqa mata danƙwaleliyar gasashshiyar kaza sukutum da guda,da sassanyar fanta,dukkan maganganunta kuma da umma take,wadda ta fito tana kwashe shanyar kayansu da habiba ta manta bata kwashe ba.

Bata ce komai ba sai data gama ta kaisu sassansu sannan ta dawo inda baba laure take,ta yanke gaya mata gaskiya ne saboda girman zumunci da zaman tare,sannan ko banza JININ YARANSU DAYA,ko banza basu isa su cire jinin su asiya daga nasu bilal ba,har abada duniya ba zata daina kiransu da sunan ‘YAN UWA BA!,ba tun yau ba,tasha jin gulmammaki akan asiyan da irin abubuwan da takeyi,sai Allah ya nuna mata sau biyu itama,amma bata taba tunkarar baba lauren ba,a tunaninta na kada ta daga mata hankali,tana shawarar kiran asiyan tayi.mata fada sai kuma akayi haka.

Fara nade ledarta tayi ganin tahowar umman,duk da ta sani cewa ita din sam ba makwadaiciya bace,hasalima tana cika da mamakin yadda take da haquri da kuma wadatar zuci,duk da bata da komai,hakanan mijinta baya kula da ita,amma hakan bai sauya dabi’a ko halayyarta ba
“Laure,ni a nawa tunanin,wannan abun da kikayi bashi ya kamata kiyi ba,ke uwace mace,wanda tasan ciwon yaranta,ya kamata ki fara sanin dawa dawa asiya ke tare dasu?,meye alaqar dake tsakaninsu?,idan aurenta suke da niyyar yi…..”
“Dakata zuwaira” baba lauren ta tsaidata
“Babu alaqar dake tsakaninsu saita alkhairi,yarinyata kintsatsiya ce,kuma na yarda da tarbiyyarta,don haka kada.kizo min da wani qabli da ba’adi,farinjinin samari ne dai kawai da Allah ya bata,kuma koni ban isa na dakushe ba” saita kwashe kayanta tayi sassanta tana mita,zucuyarta baqiqqirin,kawai gani take babu wani babu wata,baqinciki zuwaira take tsagoransa,tunda ita kaltum kusan duk wanda yazo tafiya yake,habiba kuma a sannan bata tsaiwa da kowa,don tana ganin tayi quruciya,duk da cewa a qauye suke,amma ita tarbiyya idan za’a bada ita,babu alfanun duba yanayin muhalli,a bada ita kawai yadda ya dace,wannan shine abinda ke wakana a tsakaninsu da kalar halayyar asiya da.mahaifiyarta,wanda sannu a hankali abunda asiyan takeyi yake bunqasa ba tare da sanin lauren ba,tunda tun a karon farko taga goyon baya qarara daga mahaifiyartata,babu bincike ko.matsantawa cikin lamuranta,kudi takeso…..kuma tana kawo mata su,shikenan an wuce wajen 👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽.

“Ke ‘yar baqa dake nake” baba lauren ta sake fada cikin daga murya,sai kaltum ta dakata,ta waiwayo tana duban baban,ko kafin lauren ta sake samun sukunun yin magana saita jiyo sautin bilal tun daga zaurensu,hakan yaja hankalinta zuwa zauren da hanzari ba tare data sake sauraren lauren ba.

Tabbas bilal ne,ya shigo futu futu dashi kamar wanda aka turbuda a qasa,yana dingisawa yayin da hawaye ke wanke masa fuska.

A rude ta nufeshi ta kama kafadunsa tana kallonsa
“Kai bilal?,meye haka?,lafiya me ya sameka?” Muryarsa a dakushe ya soma magana da qyar
“Su musbahu ne,mun gama aiki an biyamu kudinmu,shine suka ce wai ba zasu raba dani ba,ni kuma nace saboda me,wallahi saisun bani kudina tunda haqqina ne,shine suka taru suka yimin duka,kuma don nace zan tona musu asiri ne,muna kwabin qasa suka kwashe kayan aikin suka boye,wai idan muka gama aikin zasu je su siyar su qara samun yawan kudin aikin” sosai ran kaltum ya baci,ba wanannan ne karon farko da suka fara dukan bilal ba,bama su ba,wasu mutanen da yawa cikin qauyen,saboda suna ganin kamar bashi da wani gata ko galihu,bata iya tanka masa da komai ba ta kamashi suka koma cikin gidan,tana jin baba laure tana dariya
“Oh…aikin qwadago badai wuya ba,toh…mudai namu rabon yana jikin biro da takarda in sha Allahu,daga me yawon qwadago sai me gawon kitse sumar jama’a,suma dake cike da datti da annakiya,kai….itadai zuwaira bata iya haihuwa ba….hhhhhh” ta qarashe da dariyar dake nuna cikar nishadi da farinciki.

Har tasa qafa sashensu saita tsaya cak saboda kalaman da kunnenta suka dauko mata,uwa uba dariya ta biyo baya daga bakin lauren da baquwarta abu,wadda kusan kome ke wanzuwa na samun goyon baya da asiya tayi da shawarar zainabun ce,wadda a kullum ita ke nunwa baba laure ‘yarta me sa’a ce,ta barta,kada ta toshe musu kafar samu,duk maganar da mutane zasuyi zallar baqinciki ne,abun ke dorasu akan komai.

Kaltum din zata iya jurewa komai amma banda taba qima da mutuncin mahaifiyarta,taba qimar mahaifiyarta shine abu na qarshe da mutum zai mata,koda kuwa shi waye,don haka saita saki bilal,ta dawo da baya,yayin da laure ta zuba mata idanu zuciyarta cike fal da taraddadin kada kaltum din ta yarfata,tunda tafi kowa sanin halinta kan mahaifiyarta.

Bata tsaya ba kuwa sai data isa gabansu,idanunta cikin na baba lauren ta maida mata amsar data tashi hankalin baba laure
“Ummata itace kuwa ta iya haihuwa,tunda ta haifi tsaftatattun ‘ya’ya,babu me yawon bin maza…..babu kuma wanda ta bazama duniyar qabilu da arna neman abun duniya,yaranta na killace gabanta tana qoqarin basu tarbiyya da kulawa,duk da tsananun babunta,don haka babu haihuwar datafi wannan sa’a” saita juya abinta,tana sake dannar zuciyarta,saboda tana jin amsar data bayar dinma kamar bata isa ba,kamar bata isa ta wanke mata hucin da zuciyarta ke fitarwa ba.

 

06

*Kiji tsoron Allah☝🏽,karka/karki taba haqqin wasu,saboda akwai ranar biya,randa baka da abun biyan🤌🏾*
*KI TUNTUBA WADAN NAN NUMBERS DIN DON SAMUN DAMAR KARANTA NAKI HANKALI KWANCE*

08184017082
KO KUMA
09134848107
____________________________
_ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR FAMILY💯💯🙌🏽❤️_

_MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR ZUMUNCI_

_KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR YOUTUBE CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN ALKUR’ANI MA GIRMA_

_WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA KARARRWA DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE KWARAI💯🙌🏽❤️_

_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN👇🏾_

https://youtube.com/c/sudaiskura

_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur’an at a very young age._

_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairan🙏🏻_
______________________________

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button