Sponsored Links
Hausa NovelsUncle Datti Hausa Novel

Uncle Datti 33-34

Sponsored Links

3️⃣3️⃣—3️⃣4️⃣

Tana cikin wannan tunanin taji an dafata kafad’an ta ta baya, ko ba’a a fad’a mata ba ta san cewa Inna ce, fuskarta tafffffff da hawaye ta juyo tana kallon ta, hanken da ke gauraye da illahirin parlourn ne ya Inna ta fahimci halin da take ciki”.
Girgiza mata kai Inna tayi alamar kar tayi kuka amma ina kuka ya kwace mata ta shige jikin Inna tana sheshek’ar kuka”. Ummana Inna, ina so na ganta na san a duk inda take hankalin ta a matuk’ar tashe yake, idan zanyi fushi da kowa bazan iya yi da ita ba”.
Bayan ta Inna ta hau bugawa cikin hikima tana zancen zuci, ita kanta zata so ace an sada yarinyar nan da mahaifan ta amma ganin yanda Ammjntacce ya fice da kuma yanayin Nana ya tabbatar mata da cewa bai ammince da bukatar Nanar ba”.
“Kiyi hakuri kici gaba da zama damu Nana Allah shi yasan nufin hakan, idan da rabo wata rana zaki koma ga iyayen ki”.
Sai da ta ci kuka son ranta kafin ta share hawaye ta dubi inna cikin kuncin zuciya tace” Don Allah a wani gari nake yanzu? “Hmmm Nana ba hurumi na bane na fad’a miki garin da kike, ni dai aikina a nan na baki dukkan kulawan da kike bukata”.
Zata kuma yin wata tambayar Inna ta ja hannun ta da sauri muje ki kwanta dare ya fara nisa”, ba dan ranta ya so ba tabi bayan ta suka shige d’akin ta.
Makeken gadon ta ta hau ta kwanta Inna ta d’auko bargo ta rufa ta dashi kasancewar hunturu ne ana sanyi sosai  yasa tayi hakan cuz bata son sanyi ya cutar da lafiyan ta”, ta koma ta zaune a gefen gadon tana mata hira can kuma  barci ya fara d’aukan ta tana gyangyad’i
Sai tausayin ta ya kama Nana ta san cewa duk dan tsaron lafiyar ta take yi, cikin hikima ta lumshe idanuwan kamar mai barci komai ne yasa ta hakan ba sai dai dan ta ba ma Inna damar da zata je ta kwanta tayi barci, bayan haka itama kanta Nanar tana bukatar kad’aici”.
Inna dai na nan a haka idan ta gyangyad’a sai ta bud’e ido, da dai taga alamar barci ya d’auke Nanar tayi mata addu’ar barci ta fita tare da rufa mata k’ofa, ta nufi d’akin ta ta kwanta ta hau sharara barci abin ta.
B’angaren Nana tana ganin Inna ta bar d’akin ta mik’e a hankali ta zira k’afarta ta a k’asa ta taso a hankali tana takawa taje jikin tagar d’akin tana lek’awa, dan k’arfin hali duk da tana jin sanyi na ratsa ta, jikin ta na  rawar sanyi  kattt katttt katttt bata yi yunk’urin kare kanta ba ko tsoron dare bata ji ba balle taji darrrrr a ziciyan ta ta fara tunanin kar tayi gamo……ance tsananin bakin ciki na cire tsoro idan mutum yaji tsoro to bai had’u da bakin ciki bane tabass hakan ya faru ga Nana a wannan lokacin.”
Hawaye ne masu uban dumi suka hau zubowa ta kasa tsaida su  zuciyan ta falllll cike take da tunanin……..tayi dana sani mai tarin yawa na ba ma Datti kanta da tayi, duk da dai ta san cewa a lokacin bata da wata cikakkiyar wayo amma duk da hakan sai da taji haushi da zafin  kanta na sakin jiki da tayi da tayi da shi sosai, ta bashi damar da zai sarrafa ta ya driving d’inta to his test”.
Tsiraren hawaye suka sake yankoma mata da ta tuna da Auntyn ta Aina, wata k’ila alhakin ta cin amanar da tayi mata ne yake binta gashi nan an killace ta a gida da bata san ko na wanene ba bata da damar fita”. Kaiiiiii ba zai yihu ba ko ta halin yaya sai ta nemo hanyar guduwa baza ta ci gaba da zama a gidan shi ba cuz bata san wani irin buri yake so ya cimma akanta ba”.
Wannan dare ko runtsawa Nana bata yi ba banda aikin kuka babu abunda take yi har sai da taji kanta ya fara yi mata ciwo kafin nan ta hak’ura ta koma ta kwanta.
Da safe bayan ta idar da sallah ta nufi d’akin Inna har kasa ta tsuguna ta gaishe ta ta amsa mata”.
Tana lura da yanda fuskar Nanar yayi luhu-luhu alamar taci kuka sosai daren jira, Inna ta d’an had’e rai tace wato baza ki hakura ki saka wa kan ki salama ba? Yanzu haka kike so ki ta zama kina kuka? Gaskiya idan kina haka baza mu shirya ba tsammm banji dad’in haka ba sai ki saka na fara zargin cewa da wani abu da nake miki wanda bakya so amma kin kasa fad’a”.
“Ganin yanda ranta ya fara baci ta hau fad’a sai ta hau bata hak’uri tare da yi mata alkawarin baza ta sake yin kukan ba”.

B’angaren Datti iya wuya hankali ya gama tashi sai baza ido suke yi a kafafen yad’a labarai amma shiru, Fu’ad ma yayi iya nashi kokarin na bada guduma dan nemo inda sahibar shi take abu amma abu yaci tura, tsakanin shi da d’an uwan shi babu wani kyakkyar alaka da ace baiyi halin b’eran ci ba da babu abunda zai saka su cikin wannan halin”. Kuka iya kuka yake yi a duk sanda tunanin ta ya fad’o mishi a rai sai yaji duk duniya babu wanda ya tsana kamar Datti.
Su Umma da Abba duk sun juya mishi baya, Alhaji ma ya fita harkan shi anyi anyi ya fad’a laifin da ya aikata amma ya ki hakan ya dad’a hasala su”. A b’angaren k’anwar shi ce kadai da Ummi da kuma baba karami yake samun sauki amma duk da halin da yake ciki kowa yayi banza dashi, ai ba yaro bane da har za’a ta tambayar shi yana raina wa mutane wayo”.
Idan ya shigo d’akin tsohuwa cewa yake su neman mishi Nana idan ba haka ba shima guduwa zaiyi ya shiga duniya, ko tausayi baya bata tayi mishi tatasss da zagi”shi yayi sanadiyar gudun shi zai nemo ta ai shi ya san sirrin da ke b’oye wanda ya kasa bayyana wa”.
Itama Aina bata ragar mishi ko kad’an babu kalar habaice-habaicen da bata yi mishi ta mata da cewa a baya dear d’inta ne wanda ta d’auki dukkan yardar ta ta d’ora mishi”.
Duk da irin mugun haushin shi da take ji ko da wasa bata fad’a wa su baba Babba cewa kashe Nana yayi ba…….., ta zuba mishi ido ne har zuwa tsawon lokacin da zai d’auka da kanshi ya fallasa komai.
Wata ranar Alhamis da rana da misalin karfe d’aya Fu’ad ne ya shigo d’akin tsohuwa za shi wajen Aina kasancewar tunda ta koma gidan a b’angaren tsohuwa take zama. Tarar da ita yayi akan kujera ta d’aga ido tana kallon ceiling hankalin ta baya jikin ta bata san ma ya shigo ba har ya nemi wuri ya zauna. Jin motsin mutum a kusa da ita ya sa ta saurin d’agowa ta dube shi tana had’a ido da shi hawayen da take kokarin mak’alewa suka samu daman gangarowa saman cute face d’inta”.
“Yanzu shikenan Fu’ad Nana ta barmu kenan har abada? Ba mu ba sake had’a ido da ita? Shikenan ya kashe mana Nanar mu? Maganar ta dake shi sosai a zuciya sai ji yayi shima hawaye ya hau zubo mishi, a yanda take maganar duk ta karye mishi zuciya”.
Cikin dishashiyar murya yace” Kin ga gawar ta ne? Ko kinji labarin wanda ya samo gawar ta? Tayi saurin girgiza mishi kai”.
“Me yasa kike zargin cewa ta mutu bayan ba ki da wata cikakkiyar shaida akan haka”.
” Share hawayen ta tayi ta ta d’au hanky a gefen kujerar ta fece majina murya na breaking tace” Baka…..ga…. ab……n da na…..ga..ni ba Fu’a….d, da ido……na naga jiki a Jikin Datti, ya shigo shi kad’ai bacin tare suka fita, wan……nan hujjar kad’ai ya tab…….batar min cewa mutu…….wa tayi ku…..ma shi ya kashe ta……..
Shiru yayi shi kad’ai tare da hard’e hannayen shi yana nazartar kalaman ta har ta gama………Tabbass akwai k’amshin gaskiya a maganar Aunty Aina dole d’an uwan shi na da hannu akan b’atan Nana………, dole ne ya zurfafa bincike ya gano gaskiya idan har Datti yana da hannu akan b’atan Nana sai yayi sanadiyar yankewar jin dad’in rayuwar shi”.
” Mik’ewa yayi yace” babu komai Aunty insha Allah sai na bi dukkan wata hanyar da zan bi na kwato mata y’ancin ta wannan alkawari ne”.
“Kana ganin zaka iya?”
Indai akan Nana ne zan iya yin komai ki kwantar da hankalin ki ba zai ci bulus ba he must pay for it”, yana gama fad’a ya sa kai ya fita”.
A main parlour suka had’u da Umma Datti ya tusa ta a gaba yana mata sambatu har taji zuciyar ta ya fara cika da tausayin shi shine ta sa kai ta fita ta bar mishi d’akin”.
“Yauwa Fu’ad dama kai nake nema”, yayi saurin karasowa ya zauna a kan kujera ya sadda kanshi kasa yana wasa da farcen yatsan kafar shi.
Zama tayi a gefen shi ta kafe shi da ido cikin tuhuma” maganganun da ka fad’a ranar sun rikita min tunani musamman da naji kana cewa bamu yi dana sani yanzu ba, sai zuwa gaba zamuyi, d’an uwan ka ma yak’i fad’a mana laifin da ya aikata har yayi sanadiyar guduwan Nana ta barmu, don Allah idan akwai wani abu da kuke b’oye mana ku fito fili ku fad’a mana”.
Idanuwan shi ne suka kad’a zuwa launin ja ya d’ago kai yana kallon mahaifiyar shi da rinannun idanuwan shi wanda babu alaman fari a ciki”.
“Ummaaaa”, kiyi hakuri nima ba zan iya fad’a miki komai ba a halin yanzu, a baya babu irin shawarwarin da ban baku ba kuka yi banza dani, idan mai laifi bai amsa laifin da yayi ba ba zaku gamsu da abubuwan da zan fad’a muku ba cuz a baya ma ba d’aukawa kuka yi ba, and kuma banda shaidar da zan tabbatar muku da ita”.
Dogon numfashi ta ja ta sauk’e a hankali” shikenan tashi ku tafi amma ka sani kai da d’an uwanka kun jefa zukatan mu cikin zullumi”.
Mik’ewa yayi za shi d’aki dai-dai lokacin Datti ya fito daga d’akin Umma cuz ya gaji da zaman jiran ta hakan yasa ya fito ko zai ganta”.
Fu’ad ya ga yanda ya zafge ya rame har ya fara kashin wuya idanuwan shi sun fito waje sosai, tsaki mai k’arfi ya ja yayi shigewan shi ko ufan bai ce mishi ba sai ma cewa yayi d’an ba k’ara ba yace abun nashi ba saiti ba ya samu yarinya yana ta danna mata ga irin ta nan, akwai  ranar kin dillacin”.
Ko ta kanshi Datti bai bi ba domin bai da lokacin da zai tsaya yana kula Fu’ad bayan da nashi matsalar da tafi komai d’aga mishi hankali.
Zai yi wajen Umma ta d’aga mishi hannu” ka kuskura ka k’araso nan sai ka had’u da fushi na, haka ya mak’ure a guri d’aya hawaye na rolling a saman fuskar shi d’aya bayan d’aya”.
Da ta gaji da ganin shi a cikin wannan halin ta tashi ta bar shi a wajen,  haka yayi ta tsayuwa da ya gaji ya fita ya bar gidan tunda basa tausayin shi bayan ya fisu jin zafin rashin babyn shi mai d’auke mishi lalurar shi, ta tafi ta bar shi da tsananin kewan ta da na dumin jikin ta sannan kuma ga garuwar da yayi kullum cikin radadin rashin ganin ta.
Cikin dare Aina ta fito main parlour she was taste a lokacin and babu ruwan sha a fridge d’in tsohuwa gashi baza ta iya hakuri har zuwa safiya kafin ta sha ba kawai ta fito ta hamma ta nufi fridge d’in, har ta d’auka zata koma taji motsin mutum a bayan ta. Datti ne da tun shigowa ta yake kwance ciwon ciki ya addabe shi ya rik’e ciki yana murd’e murd’e shi kad’ai”.
Tana had’a ido da shi ta tamke fuska kamar yana ganin ta tayi sauri zata bar wajen dai-dai lokacin cikin shi yayi wani irin murd’awa zufa ya fara sassako mishi cuz of tsabar azabar da cikin ke yi mishi, cikin sarkewar murya yace” help Aina i’m dying “.
Juyowa tayi da baya zata tafi ta ga ya rarrafo ya rik’e k’asan rigar ta da wani irin dishashshiyar murya nana jan numfashi da kyar yace” please ki taimaka min mutuwa zanyi”, ciki na ciwo wife, karki tafi ki barni cikin wannan halin”.
Jikin ta ne yayi mugun sanyi a sanyaye ta d’ago ta dube shi sai taji zuciyar ta ta karaya sosai, he really needs her help, and dole ne ta taimaka mishi even though he killed her sister but she can’t afford to loose him”, shima wani b’angare ne na jikin ta”.
Tsuguna tayi ta d’ago shi da kyar tana fidda numfashi duk ta jigata ta taimaka mishi suka bar parlourn,  D’akin Fu’ad ta shige da shi suka tarar har ya fara barci ta taimaka ma Datti ya kwanta a gefen Fu’ad d’in, kafin nan ta tapping d’in shi da hannu”. Fu’ad!!!!!! Fu’ad!!!!!!, ya bud’e ido a hankali yana kallon ta tare da mik’ewa ya zauna yana mitsik’e ido”.
Ga mamakin shi sai ganin Aina ya a gaban shi, in a surprised mood yace” lafiya Aunty kika taso ni cikin wannan dare?
“Ina fa lafiya Fu’ad, hannun shi ta kama ta manna a saman wuyan Datti yaji zafi rad’a ba shiri yayi saurin janye hannun shi ya koma zai kwanta, bai ma san da Datti a d’akin ba sai yanzu”.
Muryar Aunty Aina yaji cikin rud’ewa da magiya tace” don Fu’ad mu taimaka mishi kar shima mu rasa shi kamar yanda muka rasa Nana”.
“Had’e rai yayi sosai ya sha murrr, duk da irin duhun da ke mamaye da d’akin bai hanata gane hakan ba yace” Allah aunty ba zan taimaka ma wannan azzalumin ba, mugu marar imani mai halin akuyan ci”.
Duk da irin jin jikin da yake yi bai hana shi jin zafin kalaman k’anin nashi ba, rutse ido yayi sai ga hawaye ya biyo baya…… Me yasa Fu’ad yake neman bashi ciwon kai ne bayan ya tabbata da shine da irin kaddarar shi da sai yayi abunda yafi hakan……, amma duk da ya san komai me yasa ba zai d’auki k’addara ba? Me yasa ba zai yarda cewa ba shine ya d’ora ma kanshi son jikin baby ba?
“Haba wannan wani irin rashin imani ne Fu’ad, dan uwan ka ne fa kake gaya mishi haka? Yau ko makiyin ka ka tarar a cikin wannan halin baza ka fad’a hakan ba, ba’a gaba da ciwo ko ka manta ne?
Dogon numfashi ya ja ya sauk’e a hankali jikin shi yayi sanyi sosai” shikenan aunty bari na k’ira family doctor ya duba shi, har ya mik’e zai tafi Datti ya rik’o hannun shi da sauri cikin karfin hali ya b’alle bottle na aljihun wannan shi ya fiddo wayan shi ya mik’a mishi, yana cizon lab’a cikin pain yace” Usma…n zaka kira please”, ba tare da musu ba ya hau dailing number d’in shi four times wayar ta yi ringing daga d’aya b’angaren Usman yace” helo friend.
“Fu’ad ne bro Usman shi yace nayi k’iran ka akwai wata yar matsala ne”.
“Owk owk gani nan zuwa, ko sallama basu yi da juna ba suka katse k’iran a tare.
Jim kad’an sai gashi ya iso ya tarar da gidan a rufe ya fiddo waya ya kira mumbar Datti yace ma Fu’ad d’in gashi yan ya iso yana waje ya tarar da gidan a kulle.
” Alright gani nan tahowa yana gama fad’a ya bar wajen cikin sauri.
Har gate ya fita ya ma maigadi magana ya bud’ewa Usman gate ya shigo da motar shi ciki, yana gama parking suka shige d’akin da Dattin yake yana bin Fu’ad a baya.
Zama yayi a gefen Datti ya d’an matso gaban shi ya ga sai uban zufa ne ke ta k’aryo mishi kamar wanda yake fama da rad’ad’in dafin maciji.
Jikin shi ya tab’a yaji kamar garwashin wuta ba shiri ya d’auki kayan aikin shi ya hau mishi gwaje-gwaje, bayan ya gano matsalar ne yace ma su Aina su basu waje zasu gana, Fu’ad da ke latsa wayan shi ya d’ire ta a saman drawar bed d’in a tare suka fita su da Aina barsu su biyun suka koma parlour suka zauna”.
Bayan fitan su Usman ya dube Datti da kyau ya jefo mishi tambaya” Nayi mamakin gano lalurar da take damun ka, ba komai ne ya haddasa maka wannan ciwon ba illa sha’awa, wallahi idan ba’ayi sauring tackling issue d’in nan zai causing serious problem, sai sai kuma a inda gizo take sakar shine babu wata yarinyar da zaka iya kwantawa da ita ka samo warakar matsalar ka, mace d’aya ce kuma ni da kai bamu san inda take ba”.
Hawaye ne ya gangaro ma Datti sai ya tsinci kanshi da tsananin tausayin kanshi he knows that rayuwar shi tana cikin garari”.
“Shiru yayi for some minutes yana tunani kafin ya zuba ma Datti ido” ka sanar da su baba babba halin da kake ciki kuwa?
“Ya girgiza mishi kai yana hawaye, no Usman bana son su fahimci halin da nake ciki……bana son su gano irin rayuwar da nayi da Nana na gwammace na mutu da lalurar ta than su gano gaskiyar lamari, fad’a musu matsalata kamar tonuwan asirina ne”.
” Bai kamata ace ka zab’i ka salwantar da rayuwar ka dan baka so su san irin ta’asar da ka aikata, ka sani komai daren daddewa dole ne gaskiya tayi halin ta, so my advice here is ka daure ka bari idan baza ka iya fad’a musu ba ni da kaina zan revealing secret d’in na kuma neme su yafiya, cuz nima na bada gudumawwa mai tsoka akan b’atan Nana”.
“Na sani amma duk da haka ban yarda su sani ba…….
Shikenan tunda haka kake gani yafi maka, ba zan fad’a musu ba kamar yanda muka yi komai a sirri cikin duhu bakina ba dai furta musu komai ba.
Allura ya ciro ya danna mishi, tare da bashi pain reliever, sai da ya tabbatar ya sha kafin nan yayi mishi sallama ya tafi.
A parlour Usman ya tarar da su duk sunyi jigum suna jiran fitowan shi…….., suna ganin shi suka mik’e da sauri har suna had’a baki suka tambaye shi mai jikin”.
Amsa musu yayi yace yayi mishi allura ciki harda na barci, su barshi yayi barci sosai idan Allah ya yarda zai tashi garau”, yayi sallama da su ya fice da sauri ya fizge motar ya bar harabar gidan.
Aina kam d’akin ta ta koma she was desperate gobe yayi ta ga Datti ya samu lafiya, shima Fu’ad ya koma d’aki ya d’au wayan shi ya hau latsawa.
Libs d’in shi ya ciza da k’arfi ya d’au eye piece d’in shi ya connecting da wayar manna a kunne ya lumshe ido, bai san sanda barci b’arawo yayi awon gaba da shi.
Kamar yanda Usman ya fad’a cikin ikon Allah Datti ya koma garau kamar ba shine mai fama da ciwon jaraba ba, tun daga lokacin suka koma zaman doya da manja da Fu’ad har ita kanta Ainar ta fita harkar shi dama can tausayi ne ya bata shi yasa ma ta d’an sakar mishi fuska, duk da dai ya so ya nuna godiyar shi a gare su amma basu bashi dama ha hakan ya sa ya sha jinin jikin shi ya maida hankalin shi kan matsalar b’atan Nanar shi.
B’angaren Nana kuwa tun daga Ranar da Inna tayi mata maganar take iya bakin kokarin ta ta danne damuwar ta idan abu yayi mata yawa sai taji kukan ta bar tare da ta bada wata k’afa da zata nuna alamar Inna ta fahimci halin da take ciki”, wasa wasa har ta doshi wajen wata guda ta sati uku a gidan,
Har zuwa tsawon kwanakin da take ko da sau d’aya bata tab’a had’a ido da wannan mutumin da yayi lakabi ma kanshi da “Ammintacce” ta san wani irin ishashshe ne shi da zai killace ta a gida ya hana ta fita, abu kad’an ta tambaya sai Inna tace zata tambaye Ammintacce idan ya ammince sai taje shi yasa ma bata son tambayar abu cuz abun na matuk’ar k’ona mata rai, ba aure tayi ba sai juya ta ake yi balle ace tana karkashin ikon wani.
A lokacin ta fara jin canjin yanayi a jikin ta ga shegen ci agare ta idan ta samu abinci sai ta ga karshen shi kafin ta ture plate.
Yammacin Talata suna cin abinci a dinning ita da Inna mamaki ne ya kama Inna na ganin yanda take cin uban abinci take mishi ci ba na bisa ka’ida ba, alajabi ne ya cika ta sosai har sai ta ta k’asa hak’uri tace” wannan uban cin da kike yi na lafiya? Gaskiya abun naki ya fara bani mamaki wai ace mutum sai ci kamar gara bacin da ba haka na san ki dashi ba”.
Murmushi tayi mata ba tare da ta d’ago ta kalle ta ba sai cika bakin ta tayi da abinci dammmm sai da ta tauna ta had’iye kafin nan ta amsa” kaiiii ina ke fa kika kika ce na dinga kwantar da hankali na, ba dole ba dinga ci ba shima yana d’aya daga cikin kwanciyar hankali”.
“Hmmmmm, amma ai cin nan naki yayi yawa, bakya tsoron abincin ya shak’e miki wuya ki mutu, ko kuma yayi miki illah”.
Ta kuma murmushin maganar tsohuwa ai idan ban cika bakina da abincin ba ba k’oshi zanyi da wuri ba”.
Tab’e baki Inna tayi tace” taffffffff akwai matsala daga nan bata sake tanka komai ba har suka kammala cin abinci suka koma parlour suna hira.
D’aki ta nufa jim kad’an  sai gata ta fito da comb hannun ta ta zame d’ankwalin kanta ayalalalan gashin ta masu tsawo da taushi suka barbarzo a saman kafad’an ta wasu sun rufe mata fuska har bata gani da kyau ta hau fama dasu tana so ta tufke tace” washhhhh Inna so nake naje na wanke kai d’ina ya har tsami yake tun zuwa na ban wanke ba”.
Maimakon da taji Innar ta amsa mata sai taji shiru bata damu da hakan ba ta fad’a kan kujera tare da d’ora kanta a saman kad’an shi ta rolling hands d’inta a jikin shi zaton ta ko Inna ce, dan har ga Allah bata san cewa bata yi tunanin cewa ba ita bace, bayan ga suman da ya rufe mata fuska wuri ya fara yin duhu shi yasa tun shigowan ta bata gane cewa ba itace a parlourn ba”.
Tun da ta fito ya zuba mata ido yake ta Aikin kallon ta ya kasa d’auke idanuwan shi akan ta, yaji wani irin mutuwar jiki ya kama shi, kwanciya a jikin shi da tayi yaji tsigan jikin shi ya fara tashi a feeling d’inta ya soma shigar shi, rolling hands d’inta kuwa da tayi a jikin shi yaji wani irin shock kamar an juna lantarki, wuta na neman d’auke mishi ya zauna dirshannnn kakkawaran motsi ya kasa yi”.
Tsirisin muryar ta mai dad’in saurara yaji ya d’aki dodon kunnen shi ba shiri ya lumshe shanyayyun idanuwan shi ya bud’e a hankali yana sauraran ta” Inna nayi fushi tunda kinki kulani, sai ta mik’e da sauri zata bar wajen taji an riko hannun ta soft hand d’in shi” cakkkkk taja ta tsaya taji waji abu ya ziyarce ta, jikin ta na bata wannan rikon da aka yi mata ba na Inna bane, yunkurin juyowa tayi tana yaye suman ta ga wanda ya riko ta yayi saurin riko hannun ta ya had’a da nashi yana wasa dashi, a tare suka sauke numfashi uhmmm, sai gaban ta ya hau biting da sauri-da sauri like wacce take race d’innan”.
Matse ta yayi gammm jikin shi yana shak’ar ni’imtaccen k’amshin jikin ta, maimakon da yaji suman ta na tashi da tsami sai yaji daddad’am k’amshin ya doke hancin shi ya nutsa fuskar shi cikin suman yana shinshinawa da wani irin salo har ya fara zaucewa, hannu ya kai a birkice yana wasa da suman kanta taji wani irin salo da ya birkitata har nusuwa ta d’auke mata ta kasa katabus.
Bakin shi ya d’ora saman libs d’inta da sumar ya kamo su yayi musu mahaukacin kiss na fitan hayyaci ba shiri ta dawo hayyacin ta ta ture shi da sauri cikin masifa tace” dama burin da kake son cimma wa kenan akaina? To ka sani idan ma mafarki kake ka farka baza ka tab’a nasarar samu na ban”, ban sanka ba hasalima ko fuskar ka baka tab’a bari na kalla ba me nayi maka kake neman illata ni bayan wanda na sha a baya wanda bana fatan na sha.

Libs d’in shi ya ciza yayi murmushi, ko kad’an bai ji zafin abunda ta fad’a ba, yarinyar ta iya tsiwa hakan sai ya burge shi matuk’a.
Ganin tana hana neman had’a suman ta ta baya ta tufke yayi saurin bata baya yace ba tare da ya amsa mata ba yace” tunda kin bukaci ki wanke kai ki shirya gobe zan zo na kaiki ki wanke kan”. A goben zaki san ko wanene WANNAN *AMINTACCE* wanda ya tsare ki a gida saboda burin yake so ya cimma akan ki, yana gama fad’a ya bar ta daskare a guri d’aya, tafi minti biyu tana tsahu da kyar ta ja kafar ta ta bar wajen ta nufi d’akin ta cikin zullumi, ta kosa gari ya waye idanuwanta su gane mata wannan mutumin, ji take kamar ta jawo lokaci  gari ya waye, hakan ya saka daren ranar ta yi mata nisa sosai like longer night shorter day, daren ranar cikakkiyar runtsawa bata yi ba she was desperate gari.
Washe gari da safe Inna ta fahimci ya Nana cikin wani yanayi wanda ta kasa fahimtar ko mene ne ta taso, bini-bini ta tambaye Inna yaushe Amintacce zai zo ne? Anya kuwa mutumin nan zai zo yau Inna”.
“Nima ban sani ba amma me yasa yau kika matsu ki ganshi fiye da ko wani rana?
“Uhmmmm uhmmmm babu komai Inna”.
Tab’e baki ta yi tace kya dai ji da shi”.
Ki dai bi a hankali na lura kina rawar k’afa dashi ko dai sonshi l
kike?. Taji gaban ta ya mugun fad’uwa” me zanyi da mutumin da ko ganin shi nayi a hanya bazan shaida shi ba, baya ma cikin tsarin mazan da suke burge ni in fact ma na tsana maza duk halin su d’aya ne.”
“Ni kuwa na hango son shi a kwayan idanuwan ki, ki fito fili ki fad’a idan kina ciki ne na kad’a miki kuri’ata, nafi son nayi tuwona miyana”.
Hawaye ne ya karyo mata cikin muryar kuka tace” Inna ni dai ki daina bana so”, ta hau sharar kwalla da tafin hannun ta”.
“Ya Salam!!!!! ke dai bakya gaji da kuka, yi shiru wasa ma nake miki gida zaki koma iyayen ki su aurar da ke”.
Shiru tayi tana jin Inna bata tanka mata, babu abun da ta tsana kamar kalmar namiji talk less of ayi mata maganar aure, namiji ya gatsa ta a hannu yayi mata rik’on sakainar kashi.
At this moment ne suna cikin haka wayar Inna da ke kan TV ya hau ruri ta mik’e da sauri ta d’au wayan tana dubawa sunan da ta gani fuskar wayan ya ya saka ta saurin picking ta manna wayar a kunne, bayan sun gaisa ne ya fad’a ma cewa zasu fita da amanar shi, ina take Inna a bata wayan”.  Ga wayar nan shine ya bugo yace na baki tayi saurin karb’a ta mannan a kunne”.
” Ki same ni a waje a mota ina ina jiran ki, kuma kiyi sauri karki b’ata min lokaci”, kittttt ya kashe wayan ba tare da ya jira ya ji mai zata ce ba”.
Mik’a ma Inna wayar tayi dama a shirye take tun d’asu hakan ya saka ta shige room ta d’auko veil d’inta ta yafa.
Tafi kyau sosai kayan ma ta amshe jikin ta matuk’a ya fito mata da shape d’inta idan ka ganta zaka d’auka cewa injine cuz skin d’inta was shinning and twinning like yan duma-duman Arabs dinnan”.
Ko da ta fito ta tarar da tsohuwa sakin baki tayi galala a zuciyan ta sai cewa take” zaki iya had’a go slow Nana”, wannan kyaun haka sai ki saka Amintacce ya kasa driving d’in ku ko kuma steering mota ta kwance mishi, ashe bata sani ba maganar da tayi ya fito fili har ta juyo ta kalle ta tayi murmushin kasan zuciya  kana ta sa kai ta fita.
Tafiya take yi a hankali like sarauniya, dassss dassss footsteps d’inta yake tafiya kamar na hawainiya tana fitowa ta hango mota tinted baka, ajiyar zuciya ta sauk’e ta nufi motar sai taji gaban ta ya fara bitting ba tare da ta fasa tafiyan ba har ta iso bugun zuciyan ta na dad’a k’aruwa.
Murfin motar ta rik’e da hannun ta ta bud’e a hankali a zuciyan ta tace” finally yau dai wasan b’uya ya k’are, zata ga Ammintacce mai muryar da take zargin cewa ta san mai irin ta”, lumshe ido tayi ba tare da ta bud’e ba ta zira kanta a cikin motar ta shiga ta zauna”.
Fatt fatttt fatttttt gaban ta ke tsananta buguwa har wanda ke cikin motar yana iya jiyo sautin bugun zuciyar ta, a hankali ta hau bud’e idanuwan ta wanda tun daren jiya suke mata k’aik’aiyi suna neman agajin son ganin mutumin da take tare da shi a wannan lokacin………………

”’Please share idan da hali sharhi mai tsawo har naji kamar kaina zai fashe, idan babu kuma ko heart kuka saka zanji dad’i duk kankantar comment bana rainawa yafi a gani a wuce, lastly votes on wattpad sannan kar ku manta kuyi following d’ina a wattpad”’

*eedatou*

 

*💫SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*

”’The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.”’

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
”’JIKINA YAKE SO!”’

*WRITER OF*
*1.MAGANIN MATA(DAMUWA)*
*2.WAYE MACUCI?*
*3.RAYUWAR SUMAYYA*
*4.UNCLE DATTI(JIKINA YAKE SO)!*

©
*eedatou✍🏻*
”’Follow and ✅ote me on Wattpad”’: *eedatou*

~*Amintacce!!Amintacce!!!* kowa sai maganar ka yake a group an ma fi nanar zakewa da a ganka lol, kai jin yaro mai farin jini ne a wurin makaranta”.~💘💘

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button