Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 34-35

Sponsored Links

*34 – 35*

Yafi daɗe yina barci har gari ya fara duhu .

Mairo ne cikin damuwar rashin ganin ogansu bai fito masallaci ba yasata zuwa wajen baba a ɗaki don ta shaida mata halin da ake ciki tun dadai tasan bata sani ba ,saidai wata zuciyar ne ta kwaɓeta kan ƙila ma ta sani shiru tayi ,ko kuma ma ita ta zaƙe ayi mata mugun fassara.
Da wannan tunanin ta shiga ɗakin .

“Assalamu alaikum,baba kina zaune?”
“Eh Maryamu uwar isah , akwai labarine?”
Girgiza kai tayi kafin ta koma ta zauna a gaban ta tareda lanƙwashe ƙafa haɗi da rafka uban tagumi.

“Ɗiyata me ke damunki?”
“Bakomai baba me kika gani?”
“Haba dukda ke ɗin yarinya ce mai zurfin ciki ,amma ina iya gano farin cikinki ko akasin haka, don Allah ki faɗa mun damuwarki in bahaka ba bazan iya yafewa kaina ba ,tunda ke ɗin amana ce na ɗaukar wa iyayen ki”

Hawayene ya shiga zubowa sharrrr a idanuwan ta,cikin shesheƙan kuka ta soma magana

“Baba oga bayida lafiya ,a rirriƙe aka dawo da shi yau,kuma ya kira likitan sa ya gwargwadashi ,ina kallo ya basa magunguna da allurai ,amma naji kafin ya tafi yina ta aikin basa haƙuri,kuma tunda ya tafi yake barci ,shigana ɗakin uku ina leƙensa amma har yanzu bai farka ba”

Tunda ta soma magana yawun bakin baba ya ƙafe ,haka ta hangame baki tana bin Mairo da kallo

“Baba kin jini kuwa?”
“Hmmmm(ta sauke ajiyar numfashi) Na jiki Mairo muje in dubasa”

Ɗakin suka wuce ,a falon suka taddashi yashe a gurin ko suit ɗin jikinsa bai cireba .

Da sauri baba ta nufesa “Oga? Oga meke ma ciwo?”

Shiru bai tamkata baa ,alamu ya nuna baima san tana yina

“Wohooohoo mun shiga uku,oga ka tashi kayi bayanin meke ma ciwo malaria ne?”

Nan ma shiru ba amsa ,kawai saita hau girgiza sa.
Motsi yayi ya saki jiki yararaf .

Wani gandamemen salati tasaka”Lahaula wala ƙuwwata illa billah ,oga mun bani”
Hannu Mairo tasa aka ta fasa ihu ,aguje taje ta rumfaceta “Baba ya mutu ko ,mun shigesu wazai yina bamu abinci ,ga su babana basanan ,ina zan je in kwana in oga ya mutu wayyo na shiga ukuna!”

“Ke dayalla rufe mana baki ,dama mutuwar salin alin yayi ba matsala ,amma Ni inada tarin zargi akansa ,zo mu tafi”

Ta fincike hannunta tahau janta , itakuma tana turjewa.

Tana sakinta ,ta fakaici idonta ta saɗaɗa ta koma ɗakin nasa ,socks ɗin ƙafarsa ta soma ƙoƙarin zarewa, kafin ta cire masa rigarsa na sama ,kici kici tahau yi da necktie ganin tana ƙoƙarin zarge masa wuya tace “waiii kamar ƙadduwa gwara inka tashi ka cire da kanka,kar daga taimako in kashe gawarda ba nawa ba”
Da nishi ta iya ɗaga ƙafar ta gyara masa kwanciya , bayan ta zamosa ƙasan carpet,ta ɗakko throw pillow tayi masa matashi dashi ,taje master room ɗinsa ta ɗakko bargo tazo ta rufesa dashi ,ta fesa room freshener kafin ta rage gudun acn sannan ta canza wutar falon daga me haske zuwa dimly light.

Wannan duk aikin babane ita takokoya mata , sannan ba laifi Mairo akwai ƙwalwar riƙe abu .

******
Sai wajajen asuba ya farka, sakamakon wani zafi da sukayi masa rubdugu yayi zufa kashirɓan ,numfashinsa na fita samasama

A guje ya yaye bargon ya fito yina haki ya saluɓe kayan
Tunani ya somayi mai yasashi kwana anan wajen bayan haka ko kaya bai cireba.

Jigum yayi tunowa da cin amanar da su Ahmad da Zakiyya sukayi masa
“Oh wai yau Ni julayb nine na iya kwana batare da mace ba ,lallai duniya rawar ƴan mata ,watau duk wanda yike cemaka shi ustazine ,bai samu waje bane,ji dai Ahmad ina masa kallan salihi ashe ƙwallon shegene to zai bar mun kamfani na”

Dahaka ya miƙe zuwa bathroom ya fara yin wanka kafin yaɗauro alwala ya biya bashin sallolin da suka wucesa.

Miƙewa yayi zuwa wajen hop ɗin da yike ajiye ƙur’anai don ya ɗauki carbi ko ya samu releave don shi zai iya cewa rabonda yaja carbi tun yina secondary.

Me zai gani , ƙatuwar jakar daloli da riyal ɗin da abbansa yazo masa dashi ,don ya ƙara a sabon companyn da zai buɗe ne ya ganta ayashe bako Naira 1 a ciki.

 

 

 

 

Manage
[3/14, 06:52] Bamalli✌️: *Typing…✍️*

 

*JARABABBEN NAMIJI*

 

*Na…Oum Aphnan🌸*

________________________________

*ALHERI WRITERS ASSO.🖊️*

*A .W. A*

https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/

________________________________

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button