Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 26

Sponsored Links

 

 

 

Episode 2️⃣6️⃣*

Misalin karfe 7 na safe Ammi na zaune a bakin katafaren gadon ta sanye take da wata ɗankareriyar lace baki mai zanen flower manya manya ajiki jaa, ɗinkin bubu gawn, ta sanya wani dan kareren sarkan gold a wuya ka wasu manya manyan abun hannu masu kyau da tsada a hannunta, sai kamshi take zubawa,kamar anyi ɓarin turare ajikinta

da sallama ɗauke a bakin sa BGS ya shigo, kauda kai gefe Ammi tayi tana amsa sallamar, ganin hakan yasa BGS ya kariso chikin ɗakin da sauri a gaban ta ya zauna saman lallausan karpet na alfarma dake shinfiɗe a ɗakin, chikin sanyi murya ya fara magana “ina kwana Ammi, kara ɗaure fuska sosai Ammi tayi kasa kasa ta amsa masa da lfy, kwantar da kansa yayi kan chinyar ta ya riko hannunta cikin ladabi da girmamawa yafara Magana “kiyi hakuri Ammi na, kinji nasan nayi laifi dayawa amma pls ki daina fushi dani kinji, kin fa san idan ki na fushi da ni, ina cikin fushin Ubangiji kuma kome nasa a gaba bazan yi nasara ba pls my Ammi for give me, ɗan daka tawa yayi yana sauraron yaji me zata che

….. Hannu Ammi tasa ta fara shafa lallausan gashin kansa kafin tace “ni ba fushi nake da kai ba kuma ba zan iya fushi da kai ba saboda na san idan iyaye suna fushi da ƴa’ƴansu, wache bala’i mai girma suke jawa ƴaƴan nasu, kawai dai abun da ka keyi ne baya da chewa, “zan daina Ammi na duk wani abun da baki so ki faɗa min zan dai na “kayi alkawari “na miki alkawari Ammi na keche fa farin chikina lokachin da bana kasar nan kin ta ɓa ganin nayi 2 hours ban kira ki ba, kome aikin da nake sai na daka tar na kira ki koda na 5mnt ne, saboda kawai inji ya kike, “eh hakane na sani kuma kana da gaskiya

…. yanzu dai abu biyu ne kake yi a gidan nan yake ɓatamin rai, kuma nake son ka daina yi, da sauri BGS ya ɗago kai yana kallan ta, murnushi kaɗan Ammi ta sakar masa, shima wani cool murmushi wan da bai ta ɓayi ba ya sake har sai da dimple nashi ta lotsa, chigaba da magana Ammi tayi “ina son ka rage tsawar da ka kewa su hiyana abun yana damuna kaga marayune ba uwa ba uba pls ku jasu ajiki dan ku mantar da su marai chin nasu, kannen kane kai yaka mata kafi kowa sakar musu fuska da jansu ajiki,

..ɗaure fuska BGS yayi,bai che komai ba yayi shiru yana tunani, yanzu dai sulhu nazo nema wajen Ammi bai kamata nayi wani abun da zai sake ɓata mata rai ba gaskiya bari dai na bita a yadda take so for now, in yaso daga baya na koma normal, ɗan murmushi gefen fuska ya saki a hankali ya motsa ɗan karamin bakin nan nashi ya furta “daga shi sai mai kuma Ammi, ajiyar zuchiya Ammi ta sauƙe kafin tace “sai batun kannen ka su Umar, inajin ɓachin rai idan suka gaishe ka baka amsa ba, sai kache wasu abokan gaba, ai ko bazaka amsa gaisuwar mutane a waje ba to fa ya zama dole ka rinƙa amsa na kannen ka “to shike Ammi na i will try my best kinji daɗi ” kwarai kuwa naji daɗi “Thank God, my Ammi haka nake so in ga kina chikin farin chiki, zame hannunta Ammi tayi daga gashin kan nashi tana faɗin “nima ina son naka farinchikin ai, yanzu dai katashi kaje ka shirya kuje ku raka Ahmad fada “a’a Ammi ni bazan je ba “what Ammi ta faɗa tana kara waro fararen idon ta “baka isa ba ka tashi kuma Allah idan ban ganka a fada ba.. bai bari ta karisa maganar ba yace “a’a my Ammi yanzu ma zanje na shirya yayi maganar yana miƙewa, san nan yanufi waje

Nauyayyar ajiyar zuchiya Ammi ta sauƙe, a fili ta fara magana, Alhadulillah Allah na godema da ka bani ɗa mai kauna ta mai jin tausayi na mai gudun ɓachin rai na, ya Allah ka tai makeni nima na rinƙa faran ta masa kamar yadda yake min ya Allah ka nunamin ranar da zaiyi Aure, bana son na chigaba da ta kura masa a kan batun Aure, yana min biyayya iya gorgidon iyawar sa yana son farinchiki na, bai kamata ni kuma ya dage wajen sashi abun da baya so ba zan rinƙa taya shi da addu’a har Allah ya karkato da hankalin sa kan Auren, karisa hayewa saman gadon tayi ta kwanta da kyau ya lumshe ido tana ta tunani

Misalin karfe 9:30 gaba ɗaya family sun haɗu a faɗa sun sha kwalliya sosai Abba na zaune kan kujerar mulkin su Ammi suna gefe gefensa, ga wata ha ɗaddɗiyar gujera a gefen na Abba ba kowa a kan gujerar, su Aryan suna kujerun dake jere gefe guda kujerun su Aunty farida na fuskantar nasu Aryan, ga manya manya baki kamar su sarkin zaria sarkin gombe sarkin yola da dai sauran su,

Miƙe Wa Abba yayi daga kan kujerar da yake zaune, yayi tattaki izu tsakiyar fada san nan ya fara magana “kai Ahmad tashi ka hau kujerar mulkin ka, jiki ba kwari Ahmad ya mike ya nufi kujerar, yana zama su wajiri suka miƙe suka nufoshi, nan take suka ɗauko farin kyalle suka fara naɗa masa rawani a kai, shidai kamar zai yi kuka haka aka naɗa masa rawanin sarautar,bayan su waziri sun gama na ɗawa Ahmad rawanin ne, Abba yace “salati goma ga annabi yayi maganar yana nufar gujerar kusa da Ahmad,

…zama Abba yayi san nan su kafara yiwa annabi salata bayan sun gama salati, Abba ya ɗago ido yana kallan BGS “Safras ka rufe mana da addu’a, BGS bayasan yin magana ko kaɗan amma yana gudun ya sake ɓatawa Ammi rai Allah badan Ammi na wajen nan ba da ba zanyi addu’ar nan ba, slowly ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi, da wani zazzakar Muryar sa ya fara zuba addu’oe, gaba ɗaya palon sunyi shiru suna sauraron’sa slowly hiyana ta ɗago blue eyes nata ta sauke su a kan shi chikin ranta tana faɗin “wow dama haka yake da voice mai daɗi? shi yasa baya magana dan kar murinƙa ji hmmm sosai take kalansa, har ya kai karshen Addu’ar yana kai karshe ya mike da sauri ya fice daga fada

sai sauri yake yana taku irin na jaruman maza, yazo dai dai zai shiga ɓangaren kamar daga sama yaji murya daga bayan sa tana faɗin “baka jiba, batare daya juyaba yayi shigewar sa, kai tsaye betroom nashi ya nufa yana shiga ya nufi katafaren gadon sa, ya haye ya kwanta ya lumshe ido yana jan tsaki

A hankalin ta turo kofar ɗakin ta shigo kwas, kwas, kwas, take takawa har gaban gadon nashi ta zo, kashe murya tayi tafara magana “haba mana shine ina maka magana a waje ka shareni, kasan wacece ni? nifa yar Autan sarkin zaria che pls kyakkyawa katashi mana muyi magana wlh ni bana barin abu a rai na da abu ya burgeni nake faɗe, wlh ka tafi da ni tun da kafara addu’a a fada nake kallon ka, kuma SON ka nake da dukkan zuchiyata, ko motsi BGS bai yiba bare tasa ran zai yi magana “haba mana kyakkyawa nasan ba kayi barchi… Bata kai karshen maganar ba taga BGS ya mike batayi auneba taji saukar wani gigitatchiyar ma haukachiyar mari,a kan kunchinta wani ihun azaba ta saki

.. a fusache ya zaro belt daga ma zaunin sa ya fara zuba mata ta ko ina a jikin ta, ihu take kamar ranta zai fita,shiko ko ajikinsa rai ambachi yake zabga mata belt ɗin, data ga dai BGS zai iya kashe ta ba wan da yaji ihun data ke bare yazo ya taimaka mata yasa ta miƙe da kyar tanufi hanyar fita, damko atachimen ɗin datayi chikon gashi da shi yayi ya daga ta da kai, yayi wurgi da ita gefe hakan yayi dai dai da shigowar Aryan ɗakin, a fusache BGS ya sake nufar ta, ko motsi batayi da alama ta suma chigaba da bugunta yayi

Da gudu Aryan ya karisa chikin ɗakin ya sa hannu biyu ya damko damsen BGS yana faɗin “haba blood kisa zakayi ne, chikin tsawa BGS yace “sakeni Aryan nache kasake ni “bazan sake ka ba BGS bazan sake ka ba nache, ida kuma nima zaka haɗa har dani ka bugane to Bismillah, a fusache BGS ya ya kwache hannunsa daga rikon da Aryan ya masa ya fice daga ɗakin sai huchi yake, bin yarinyar da kallon Aryan yayi a ranshi yana faɗin ko wacece wan nan kuma ko me ya haɗa su, wayar sa ya chiro daga aljihun wandon jeans dake jikin sa ya fara kiran layin Aunty farida,

….Bugu ɗaya Aunty farida ta ɗaga tare da faɗin “hello bro “Aunty farida kizo ɗakin BGS ki ɗauki wata yarinya “wata yarinya kuma? Aryan “eh nima yanzu shigowa na ka nan, na samu yana bugun wata yarinya gashi da alama ta suma “Allah dai yasa ba diyana ko hiyana bace “aa Aunty babba basu bane wan nan ma ba yar gidan nan bache “to ke nan a chikin baƙin nan ne, me tamasa zai bugi yar mutane, “to nima dai ban sani ba idan kinzo kya tambaye shi yana gama faɗin hakan ya katse kiran, ya juya ya fice daga ɗakin

Misalin karfe 2 na rana gaba ɗaya family Abba sun haɗu a babban palon Abba dan chin abinchin rana ban da ƴanma tan Ammi sune kaɗai basa nan sai BGS wadda daman ba tare suke chin abinchi da shi ba, “kin san me Safras ya aikata yau kuwa? Chewar Abba yayi maganar yana kallan Ammi “aa me kuma yayi chewar Ammi “hmmm yar sarkin zaria ya kama ya rinƙa bugu yanzu haka tana asibiti wlh bakiga yadda mahaifinta ya bata rai ba da kyar na bashi hakuri “kai wan nan yaro to me ya haɗa su Ammi ta tambaya tana kokarin ajiye spoon ɗin hannunta, da sauri Aunty Farida tace “aa baruwan DON ita taje ɗakin sa ta same sa ai, shiru sukayi dan Abba ya gane dalilin daya sa BGS ya bugi yarinyar

wai ina yan mata nane chewar Abba “suna ɗaki kasan diyana sarkin kwalliya che tana chan wai sai ta gama kwalliya, zata zo chin abinchin, su hiyana kuma suna jiranta chewar Ammi, murmushi Abba yayi kafin yace “ai tana da gaskiya gara ta rinƙa kwalliya sosai dan ta samu miji da wuri na aurar dasu, a sukwane Aryan ya ɗago ash eyes nashi karaf, idon nasa, ya sauka chikin na Abba dan kuwa shi Abba ke kallo mayar da kansa yayi ya sun kuyar ya ajiye spoon ɗin dake hannun sa ya ɗauki wayar sa ya fara latsawa,

…… Aure kuma Abba Aunty farida ta tambaya da mamaki, “eh mana my daughter yanzu su diyana basu kai Aure bane, ai da diyana hiyana Zahra sun kai Aure kuma nan ba da jimawa ba zan musu, wani dogon tsaki Aryan yaja wadda yasa gaba ɗaya mutanen palo suka ɗago suna kallon sa “Aryan lfy Ummi ta tambaya tana kallan sa daga sama har kasa, rai a ɓace yace “lfy Ummi, kau da fuska Abba yayi daga kallon Aryan ya chigaba da chewa “ita kam diyana ma ai tana da masoya ga yaya bellon ta, na Yola ga kuma malamin makarantar su duk da naji anche an karya masa kafa, baya tafi to in dai diyana na son shi zan fiddashi kasar india amasa aiki, “oh my god Aryan yafaɗa chikin tsawa yana dafe kai, wadda sai da gaba ɗaya jama’ar palon suka tsorata, “Aryan kana lfy kuwa Aunty farida ta tambaya da mamaki a fiskar ta, ban za yayi dasu ko sannu bai cheba, Abba kuwa chewa yayi “kai ku kyalesa mana tun da ba ya son magana, mikewa Aunty farida tayi daga nata kujerar tana faɗin “aa Abba wan nan irin tsawa haka ba lfy ba ta karisa maganar tana karisawa wajen da Aryan ke zaune, hannu tasa tana shafa kansa kafin tace “me nenen bro, ɗago ash eyes nashi yayi wadda suka sauya sukayi jaa ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi zai yi magana ke nan, sai sukaji yar siririyar muryan diyana tana doko sallama tun daga bakin kofar palon

Mai da kallon su gaba ɗaya mutanen palon su kayi izuwa bakin kofar palon, anko su kayi gaba ɗayan su chiki jalla biya pink colour Zahra hiyana lamrat amrat duk sun yafa mayafin rigar amma ban da diyana, ita kam ta tasaki wan nan bakin lallausan dogon gashin nan nata har gadon baya, a nitse suka kariso chikin palon kowan nan su na zauna a kujera table ɗin,

Wow my daughter kinyi kyau sosai chewar Abba yayi maganar yana kallan diyana, dan ita kaɗai che a chikin su tayi kwalliya, “laaaa Abba kasan me ranan ma yaya yusuf yace nayi kyau haka yaya Aryan ma da na kai masa coffee yace nayi kyau dana ɗan kwali, asukwane matasan gidan suka juyo da kallan su kan Aryan,

ɗaure fuska sosai Aryan yayi kamar bai taɓa dariya ba ya chigaba da latsa wayar sa, ita kuwa diyaba ko ajikin ta sai murmushi take tana bawa Abba lbr, ganin Aryan ya ɓata rai sosai ne yasa Yusuf yace “eh mana my sister ai dole kowa yace kina da kyau, to ke ba sis ɗin mu bace idan bamu yabe ki ba, waza mu yaba, wani murmushi diyana ta saki tana faɗin “Allah yaya Yusuf idan nayi kwalli ina kyau? “kai sosai ma kuwa may sis ai duk gidan nan kin fi kowa kyau kuma kin fi kowa… Bai karisa maganar ba saka makon wani mugun kallon da Aryan ya wurga masa, irin kallon nan na ina ruwan ka da ita idan ma tafi kowa kyau, shiru Yusuf yayi a chikin zuchiya yana tunani kai yaya Aryan akoi bala’e kishi to kai kaki bayyana soyayyarka san nan kuma idan wani na ya bonta ko ya raɓe ta ka hukun tashi, yanzu da kake harara’ta ni ina ruwana ai ban che ina son taba kawai yabon ta nake ni da nake da mai baby . Juyawa Aunty farida tayi ta koma wajen zaman ta ta zauna, shiru palon yayi sai karar spoon kawai zaka ji

“Yauwa yaya Aryan wan nan jakar da ka bani nan taki buɗuwa, kullun nache zan kawo ka buɗe min sai na rinƙa mantawa, chewar diyana tayi maganar tana kallon Aryan, tab aiko gaba ɗaya palon sun zuba musu ido suna jiran amsar da zai bata, ɗago ash eyes nashi yayi ya sauke su kan face nata sai murnushi take nan take kuma sai yaji wani sanyi na ratsa zu chiyar sa, calmly ya fara magana “eh nina kulle jakar zan buɗe miki amma ba yanzu ba, tirkashi Aunty amarya ji take kamar ta tashi ta shake diyana dan bakin chiki Amma tana tsoron Abba

Ayya yaya Aryan ka buɗemin kaji, kaga su Aunty Zahra duk sun sa nasu tsara bar kuma wlh kayan nasu yamin kyau nima ina son saka nawa ta karisa maganar kamar zata yi kuka, zuba mata ash eyes nashi yayi sosai, ya kasa kawar da kallon sa daga gare ta, Abba dai ajiye spoon nashi yayi ya zubawa Romeo and Juliet ido kawai yana kallan su, Khalid Yusuf Aunty farida sai murnushi suke suna murna, Aunty amarya Aunty Maryam kuwa kamar zasu mutu dan bakin chiki, Ammi da Ummi kam ko ajikin su abin chin su kawai suke chi basu ma lura da Abun da ke faruwa ba, Fahad ma abinchin sa yake chi ko ajikin sa bai ma san suna yi ba haidar Umar sai satar kallan yaya Aryan suke suna mamaki, tsoro suke kar ya kama su suna kallon sa, Aunty salma Aunty mardiya wayoyin su suke latsawa han kalin su baya kan jamar palon

Da kyar ya iya saita voice nashi kasa kasa kamar mai raɗa yace “an jima ki kawo min jakar na buɗe miki yana gama faɗin hakan ya miƙe da sauri ya bar palon, dawo da kallon ta Aunty farida tayi kan Abba, ta kashe masa ido ɗaya wani cool murmushi Abba ya sake mata a hankali ya motsa lips nashi, yayi ta alama da mun fara nasara, gyaɗa masa kai kawai Aunty farida tayi san nan ta chigaba da chin abin chinta.

Misalin karfe 3 :30 na rana gaba ɗaya ƴanmatan Ammi suna zaune a karamin palon sama na ɓangaren Ammi hiyana na riƙe da Alkur’ani mai girma tana karatu, diyana na buga game a wayar Zahra lamrat da amrat suna kallo Film a makeken Tv dake makale a bango, Zahra riƙe da littafin husnul Muslim tana karatu addu’oe, hankalin su yayi nisa a kan abubuwar da suke,

…. da sallama Yusuf ya shigo palon da sauri suka ɗago suna kallon sa, da gudu lamrat ta miƙe ta nufe’sa hannu ya buɗe mata ta faɗa kan faffaɗar kirjinsa ya mai da hannun sa ya rufe yana faɗin “my baby nayi kewar ki, cikin shogoɓa tace “nima nayi kewar ka yaya Yusuf, hannu yasa yana shafa kanta a hankali yana faɗin “my baby ina san gashin nan naki kyau yake min, lamrat zata yi magana yayi sauri raba jikinta da nashi kasan chewar yaji alamun tafiya ta bayanzu kamar mutun zai shigo palon, riko hannun ta yayi suka karisa chikin palon suka zauna saman sofa mai zaman mutun 3,

da sallama Khalid ya shigo palon shima da gudu Zahra ta miƙe tanufe sa, har zata rungume sa sai kuma ta dakata, kallanta yake itama tana kallon sa “sannu da zuwa yaya Khalid ta faɗa tana sun kuyar da kai “Auta yau kam babu oyoyo ne ya tambaya yana ɗago haɓatar da hannun’sa, chikin shagwaɓa tace “Ammi che tace wai kai zan Aura kuma na daina yi maka oyoyo sai bayan Aure, wani nauyayyar ajiyar zuchiya Khalid ya sauke tare da faɗin “da gaske Auta Ammi ta faɗa miki ni zaki Aura, gyaɗa masa kai Zahra tayi alamar eh, gyara tsayuwar sa yayi kafin yace “to kina sona, juyawa Zahra tayi zata gudu yayi sauri riko hannunta sai lokachin idon’sa ya sauka kan Yusuf dake zaune ya zuba musu ido, diyana kam bata ma san sunayi ba game nata kawai take bugawa hiyana ma kanta na kan qur’ani karatun ta kawai take

Harara Khalid ya wugawa Yusuf zai yi magana ke nan haidar ya shigo da gudu yana faɗin Ammi, Ammi ina kike yaya Ahmad ya mut….✍️

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

1 Duk Karfin Izzata
2 Gidan Aunty
3 Jini Ɗaya
4 Sarki Sameer
5 Kafita Zakka

Kar kubari abaku lbr love Story’s

*💫STAR LADY💫*27

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*
Star lady

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button