Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 18

Sponsored Links

Episode 18*

 

Hannu Aunty Maryam ta ɗaga, har zata kai mata mari sai kuma ta dakata ” zuba mata ido Aunty farida tayi sosai,” me ya dakatar dake kimare’ni mana, ae kin girmane shiyasa har kike tunanin ramawa, kimare’ni nace koh tayi maganar a fusache” dan Allah Aunty farida kifita a ɗakin nan “hmmmm wlh Maryam bansan baki da hankaliba sai wan ‘nan karan,to kisani idan su Abba suka dawo kinemi abun da zaki kare kanki,dan kuwa babu wanda zaiga abun da kika’wa yaran nan ya kyale’ki, naso hukun taki da kai na, amma zan bari, ƴa’ƴayn Aisha dakike ikrari su hukuntaki, dan awan nan gaɓar su kikataɓa, “tana kaiwa nan tamike tafice daga ɗakin ” ganin Aunty farida tafita, yasa Aunty Maryam, tayi kwafa tana faɗin to inaruwan’ki inba shisshigiba duk chikin ƴa’ƴan Aisha akoi wanda ya isa yamin hukunci’ne, yara kuma na buga innasake samun dama’ma bugun zanyi, dan nayi alkawarin rabasu da gidan nan tunda Aunty amarya bata san’su, juyawa tai ta gyara kwanchiyar sai surutai take

Da sallama ta dawo palon Ummi, duk datasan ba kowa, kai tsaye ɗakin’ta tawuce, tasamu diyana da amrat sunyi barchi ,”kayan jikin’ta ta chire san nan nufi toilet, after 45 mnt tafi ɗaure da towel da’alama wanka tayi, trolley ta tajawo, ta buɗe ta ɗauki kayan barchi, masu kyau da tsada farare tas masu laushin gaske, sai kamshi kayan keyi yasha turarukkan maiduguri,san nan ta ɗauko mayukan’ta masu kanshi da tsada sai dataɓi ko’ina na jikinta ta shafeshi da mai san nan,tasanya kayan barchi ta’sake feshe jikinta da turare sai kamshi take kamar anyi ɓarin turare a jikinta, “ta mai da mai da tureren chikin trolley ɗin ta rufe ta mai’dashi wajen zamansa, tadawo kan gadon ta gyarawa amrat kwan chiya, san nan ta kwanta a gefensu, tare dayin adduar barchi asuba ta gari

Yau yakama Wednesday tun safe Aunty farida ta shirya chikin tsadaddiyar lace mai Bala’i kyau baki, da ratsin ja ta zuba sarkan gold a wuya da hannunta, ta jera wasu tsadaddun zobuna uku na gold a hannunta, tayi simple make up bakaramin kyau tayiba sai kamshi take zubawa kamar anyi ɓarin turare ajikinta, tasa plat shoe ja da mayafi ja san nan tayiwa yan matan Ammi kwalliya sosai, “diyana hiyana Zahra tasasu sukasa wani haɗaɗɗen duguwar riga mai kyan gaske, da pink colour an masa kwalliya da wasu duwatsu golden colour, bakaramin kyau sukayiba amrat da lamrat kuwa sun sa wandon jeans baki da yellow t-shirt,” gaba ɗayan’su ta ɗaure musu gashin nasu a tsakiyar kai ta zuba musu jelar a baya, sai dai ita hiyana har yanzu ba a chire bandejin dake goshinta’ba “Aunty farida ina zamuje kika mana kwalliya haka diyana ta tambaya tana kokarin gyara mayafin rigar” wajen lalle da gyaranjiki zan kai ku, da naso namuku lalle da kaina to amma nayi tu nanin gara na kai’ku ae muku har da gyaran jiki ” tsalle diyana tayi ta rungume Aunty farida tana faɗin mungode sosai” to sakeni mutafi kar lokachi ya kure mana ” to diyana tafaɗi tare da sakin Aunty farida” rike hannunta Aunty farida tayi sukayi gaba, su Zahra suka rufa musu baya,
suna fita harabar gd da gudu Shahram yanufo’su ” ɗan dukar da kai yayi ya gaishe da Aunty farida chikin harchen turanci” bayan yagama gaishe da Aunty farida,su Zahra ma suka gaidashi ” bayan yagama amsa gaisuwar’su Zahra ne, ya tambayi Aunty farida ko zai iya kaisu inda zasuje da kanshi ” Aunty farida tace badamuwa ya fito da family car dan tafisan sutafi dukkan’su a mota ɗaya ” da gudu yajuya yanufi parking space na gidan,” har gabansu yazo yayi parking,”zai fito yabuɗe’musu ” Aunty farida ta ɗaga masa hannu, alamar yabari zasu ɓuɗe da kansu ” da Kanta tasa hannu ta buɗe kofar motar,” a nitse suka fara shiga sai da suka gama shiga san nan tabi bayansu ” da gudu gaske Shahram yaja motar yana zuwa bakin gate ya ɗan rage gudun motar nan’take securitys dake wajen suka wangale masa gate ɗin da’gudu ya danna hanchin motar waje, gudu sosai, Shahram ke shararawa a kan mikakkiyar titi ” ranki ya daɗe ina muka nufa yayi tambayar yana kokarin fita daga asalin babban gate ɗin gidan ” A&S muka nufa tabashi amsa ta kokarin picking call ɗin daya shigo wayarta ” miƙar hanya Shahram yayi sosai yake sharara gudu
Yana hawa kan titi dazata sadashi da gate ɗin A&S ya rage gudun motar,horn ɗaya yayi wani dattijo ya taso ya wangale masu gate ɗin da’alama shine mai gaɗin ” A nitse Shahram ya danna hanchin motar chiki, parking space na wajen yanufa yana kashe motar yafito da sauri ya buɗewa Aunty farida” a hankali ta zuro kafafunta waje ta fito “su hiyana ma sukabi bayanta hannu diyana tariƙe suka nufi chiki ” wani haɗadɗen wajen gyaran jikine da lalle da kitso, wajen ya tsaru sosai iya matane kaɗai ke shiga koka’kawo wani naka sai dai katsaya awajen zaman baki, suna da ma aikata sosai inkaje basai kabi layiba, ” hannu bibbiyu a ka tarbi su Aunty farida ” chikin ƙankanin lokachi aka fara gyara musu jiki

YOLA

Da gudu inna tafito daga ɗaki, tayi kichin, da sauri ta sauke tukunyar ɗumamen, dake kan wutar abinchin har yayi bakin’kirin, zama tayi dirshan awajen kamar zatayi kuka tafara surutai,”oh ni habiba yanzu me zanchi wayyo Allah gashi ba azumi nake ba dole naje nasake ɗaukar 1k a chikin kuɗin nan na sawo masara nazo na surfa na niƙa nayi wani tuwon, mikewa tayi ta jawo itacen wutar ta kashe san nan ta wuche ɗaki ta ɗaga katifar chiyawar’ta ta irga kuɗin taga saura 6k ta zari 1k ta mai da sauran kasan katifar ta ɗau mayafinta tafuto tanufi waje dan zuwa yin chefene

KANO

A bangaren’su Aunty farida kuwa sai gyaranjiki ake musu an gama yiwa diyana da zahra da amrat bakaramin kyau sukayiba, kamar wasu larabawa haka suka zama daman, dukkansu fararene tas jikinsu sai kyalli yake gwanin ban sha’awa,
yanzu aka fara yiwa lamrat da hiyana kuma,”Aunty farida kam already tariga da tayi nata a Maiduguri kafin tazo, ” yanzu lalle za’afara yiwa diyana da zahra ” sai zolayar’su Aunty farida keyi ” my diyana kingan’ki kuwa kamar wata sarauniyar kyau fa kinga fatar nan taki kuwa saikace na jariri gaskiya dole..bata karisaba, wayar’ta tafara ƙara alamar shigowar ƙira da sauri ta chiro wayar kiran iphone 14 daga jakarta ” laaa Aunty farida yaushe kika chanza waya chewar diyana ” last week tayi maganar tana kokarin picking call ɗin ” hello my bro ykk “lfy lau my lovely Aunty ykk y gd ” lfy lau alhamdulillah gamu nan ma awajen gyaran jiki ae ina Prince ” baya nan yayi tafiyar sirri ” murmushi tayi kafin tace kai Aryan dayayi tafiyar sirri nasan yace karka faɗawa kowa, shine kuma kafaɗamin ” murmushi kaɗan shima ma yayi san nan yace ae ke da kankima sirrinmu’ce ko bazamu faɗawa kowaba yazama dole ke kisani, ” inasu Khalid to ” suntafi kasuwa ” to yau kuma da kansu sukaje kasuwar ” eh wlh nima dai na ɗanyi mamaki ” kodai Zahra yaje yiwa tsaraba ” to waya sanin musu zaki gane kan Khalid da Yusuf ne ” to shike nan bari innakima gd mayi magana ” ok ya’jikin yaran nan ” da sauki sosai gasu nan ma ana musu lalle ” lalle kuma ya tambaya yana taɓe baki ” eh lalle mana kona baku ku gaisane ” eh to dai kibari sai kun koma gd zaifi tunda yanzu kince lalle ake musu ” ok to shike nan sai munyi waya,” ta karisa maganar tana chire wayar daga kunnen’ta ” katse kiran tayi tamaida wayar chikin jaka san nan ta ɗago tana kallan’su diyana da akewa lalle ” wow my sister’s kunganku kuwa kaman wasu amare gaskiaya idan Ammi suka dawo bazasu gane kuba wow ” diyana dai baki yaki rufuwa sai murmushi take ” Zahra kuma hannu tasa ta rufe fuska tana dariya ” bayan angama yiwa Zahra da diyana lalle ” aka fara yiwa amrat da lamrat

SAUDIA

Ammi che kwanche a kan chiyar Abba a ɗakinsu tana shafa fuskar’sa yayinda shikuma yake shafa gashin kanta ” ranka yadaɗe nayi kewar yanmata’na sosai, ” hannu Abba yasa yaɗan ja dogon hanchin nan nata yana faɗin to kwana nawa yarage mukoma, ɗazun ma munyi waya da farida take chimin zasuje wajen gyaran jiki ” Allah sarki feeda baiwar Allah, Allah yamata albarka na mata adduar samun aihuwa sosai jiya danaje masallaci ” kullun sainayiwa farida adduar bama ita kaɗaiba har da maryam da mardiya ba garama faridan tasamu ɗaya ba sauran kam aiko ɗayan basu samuba,chewar Abba ” wlh tausayi suke bani tayi maganar tana kokarin mikewa ” da sauri Abba ya rikota yana faɗin ina zakije kuma ” so nake naje nayi magana da yaron nan ” kallan chikin kwayar idonta sosai Abba yayi san nan yace wani yaro kuma, da gangan yamata tabayar, dan yanasan yau yaji takira sunan Safras da bakinta ” yaron Ummin nan mana tabashi amsa tana mai kawar da kai gefe ” to shi yaron bai da sunane ” juyo da kallan’ta tayi kansa san nan tasa hannu taja gemunsa chikin wasa take faɗin, bazadai kaji su nan a baki’naba ” murmushi yayi yana faɗin to idan inasan inji kumafa ” sai na kira maka mana ae duk abun da kakeso matikar bai saɓawa Allah da manzon’saba dole namaka ” rungumeta Abba yayi chikin farinchiki yafara magana ina kaunarki Aisha’ta nima bazan saki yin abun da baki so ba, tunda ba kyasan kiran su nan bazan saki kiraba aje a yaron kinji ” chusa kanta tayi kirjin’sa tana faɗin nima ae ina kaunarka sosaima ” nasani Aisha nasan kina kauna’na sosai nasani wlh ” to shike nan kamin izzini naje na dubo’shi dan jiya banganshi’ba kwata kwata kuma inasan magana dashi a kan yaran nan ” aa Aish ba yanzuba dan yanzu bansan ki raba jikinki danawa kibari sai anjima ” to kawai Ammi tace takara shigewa jikinsa ta lafe

Da sallama Khalid da Yusuf suka shigo palon hannun’su ɗauke da manya manyan jakun’kunar sayayya Aiman da Ahmad dake zaune saman Sofa suka amsa sallamar suna binsu da kallo ” daga ina kuke haka Aiman ya tambaya yana ɗaure fuska ” to dakake ɗaure mana fuska, saiyasa muji tsoranka mufaɗa’maka inda mukaje ne chewar Khalid ” dariya Ahmad yayi yana faɗin nidai babu ruwana ” tsaki Khalid yaja yawuce yanufi hanyar ɗakin’sa ” da sauri Yusuf ma yabi bayansa ” miƙewa Aiman yayi yana faɗin lokachi yayi da zan gano mekuke kullawa kuma sai nayi maganin’ku ” Ahmad kam binsa kawai yake da ido har yafice daga palon ,yana ganin Aiman yafita ” ya kwashe da dariya, chikin dariya yake magana wlh nidai nawa ido kawai zanga wan nan game ɗin yasake kwashewa da dariya yana mai kwanchiya a kan kujerar

NIGERIA

Sai milalin karfe 4:50 aka gama yiwasu hiyana gyaran jiki da lalle sunyi kyau sosai kamar su’sukayi kansu yaran nan gawani kitso guda biyu da aka musu a gefe da gefen kunnen’su ansa manya manyan bit an zuboshi ta gaba har kan chikinsu tsawon gashin, sauran gashin an ɗaure musu a tsakiyar kai,anzuba jelar gashin ta baya har gadan bayan’su, musammanba hiyana da diyana gashinsu yafi tsawo da baki ga tsantsi, ba karamin kyau sukayiba kamar, ƴa’ƴan larabawa ” bill akayiwa Aunty farida ta biya san nan suka nufi waje ”
Shahram dake zaune chikin mota,yana ganinsu ya fito da sauri yana faɗin wellcome ma ” da murmushi a fuskarta tace sorry Shahram for keeping U waiting ” buɗemusu kofar motar kawai yayi batare daya sake maganaba, suna shiga yarufe motar yashiga gaba yabawa motar wuta sai bakin gate mai gaɗin ya wangale masa gate ɗin ya danna hanchin motar waje da gudun gaske ya miƙi titi, gudu yake shararawa sosai, sai daya kusa isa bakin babban gate na gida tukun ya ɗan ragewa motar gudu horn ɗaya yayi nan take security suka wangale masa gate ɗin a nitse ya kutsa chikin gidan, kai tsaye parking space yanufa ,” yana kashe motar yafito da sauri ya buɗe musu ” fitowa sukayi gaba ɗayan’su suna faɗin thank U uncle ” Aunty farida ta rike hannun diyana sukayi chikin gd ” da sallama suka shigo palon ” da sauri nurse nasu dake zaune saman Sofa tamike tana faɗin ina kukaje natashi barchi ban gankuba, ” wajen gyaran jiki mukaje diyana tabata amsa ” dukawa tayi kasa ta gaida Aunty farida ” da fara’a ta amsa san nan tanufi ɗaki dan yin wanka tana faɗin sister’s kuje kuyi wanka kozo kubiya bashin sallar Azhar da la asar dake kanku ” har suna haɗa baki wajen chewa to san nan suka nufi ɗakin Aunty mardiya

yau saura kwana ɗaya sallah sai shirye shiryen tarban su Abba ake, manya manya shanu 4 aka’yanka da raguna 5 ” hayar masu soya nama Aunty farida ta ɗaukoh mata’ne masu jini ajiki masu ji da karfi da lfy, san nan tasa aka fitar da manya manyan gas daga store, aiki ake babu kama hannun yaro ,gamasu yin chin chin a gefe, gamasu donut dubula alkaki da dai sauransu, Aunty farida yau bata zauna ba sai hidima take da jama’a ” Aunty Maryam kuwa tana ɗaki kwanche abunta

Misalin karfe 1:50 diyana na zaune a ɗakin Aunty farida tadage sai make up take, wayar Aunty farida dake kan gado yafara ringing,” da sauri ta ajiye jan bakin dake hannuta tanufi wayar, ɗaukar wayar tayi zatayi waje dan takaiwa Aunty faridan, sai taga pic na Aryan ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar, sanye yake da kayan sojoji baƙaramin kyau yayiba fuskar nan tashi kamar bai taɓa sanin me dariya’ba,” da sauri tayi picking call ɗin ” daga ɗayan ɓangaren Aryan yace,”hello my lovely Aunty ” ba itabace yaya Aryan ni che ina wuni ” lfy lau y jikin naki ” nasamu sauki hiyana che kawai tarage bata samu sauki’ba ” subhanallah me ke damunta ina nurse naku ” nurse ta koma jiya wai zataje tayi shirye shirye sallah ” to meke damun hiyanar ” chiwon kai da jiri ” ok jibi zamu dawo ae sai na dubata amma duk da haka zansa a kawo mata magani ” to bari na kaiwa Aunty farida wayar ” daman kinsan zaki kai mata wayar’ne kikayi picking call ɗin ” eh ae nayine daman dan na gaisheka tun da mun daɗe bamuyi magana’ba ” to ae kece kika manta dani shiyasa ” dariya diyana ta ɗanyi kafin tace, ni ban manta da kaiba dan bani da waya’ne Allah dana kiraka ” wani ajiyar zuchiya ya sauke”to amma kina kewata kuwa ” eh mana ina kewar’ku dukkan’ku ” ok to shike nan ki ajiye wayar kawai anjima idan Aunty farida tazo ta kirani dan naji Abba na nemana ” to kawai tace tare da chire wayar a kunnen’ta ta mayar kan gadan ta ajiye,”takoma gaban mirro tachigaba da kwalliyar’ta

YOLA

Inna na ɗaki kwanche a kan yar gadon chiyawar’ta taji sallama daga kofar gd mikewa tayi daga kwanchiyar datake tana amsa sallamar,”ɗaukar mayafinta tayi tanufi waje ” ganin bello ne ke sallamar yasa inna ta ɗaure fuska sosai tafara magana to yau kuma dame kazo funafiki ” ina wuni inna ” daban wuniba zaka ganni’ne ” to Allah yabaki hakuri daman naga gobe sallane shine nache bari na sauke hakkin ma kwabtaka na kawo miki wan nan,”yayi maganar tare da ajiye wa inna gaji guda uku a gaban’ta, batare daya jira amsar’taba yayi wuce warsa gidan’su ” da mamaki inna ke kallansa har yashiga gida, duƙawa tayi ta ɗauki kajin tayi chikin gida,” a tsakar gida ta ajiyesu san nan ta ɗaukoh wuƙa tayanke igiyar da aka haɗesu aka ɗaure, ta samu wani igiya ta ɗauresu ɗai ɗai ta kaisu kichin tafito takoma ɗaki ta kwanta,” tana kwanchiya babu jimawa buba yashigo gidan da sallama yana ɗingisa kafa da sanda ” tana daga chikin ɗaki ta amsa masa san nan tace yashigo ” shiga ɗakin yayi hannunsa riƙe da buhu ” lfy buba ina zakaje da buhun nan ” bappa’ne yace na kawo miki, shin kaface wai kiyi girkin sallah ” da murna inna tamike zaune wayyo Allah kacewa bappa ngd sosai Allah yaƙara arziƙi ” amin yafaɗa tare da ajiye mata buhun ya juya yafita ” buɗe buhun tayi taga shin kaface mai kyau da murna ta tura buhun bayan kyaure ta ɓuye

KANO

Misalin karfe 7 na dare, sun haɗu a palon Abba suna buɗa baki ” kai my diyana sarkin san kwalliya chewar Aunty farida tayi magabar tana ɗan jan kumatun,diyanar ” ae kwalliyar dazanyi gobema sai yafi wan nan kyau ” Allah ko ae haka akesan mace takasan’ce mai tsabta da kwalliya ” Zahra tace Aunty farida ae muma munayi ” eh kunayi amma my diyana tafikuyi sosai, kuma kuƙara dagewa ” to shike nan zamu rinƙayi sosai ” ok to kuchi abinchin’ku dawuri muje mu kwanta dan kunga gobe sallah zamu tashi da wuri ” har suna haɗa baki wajen chewa toh ” shiru kakejin palon babu mai magana sai paran spoon kawai zakaji ” sallama sukaji anyi a bakin kofar palon ” amsa sallamar Aunty farida tayi san nan taba da izinin shigowa ” ɗaya daga chikin security bakin gate ne,har ƙatsa ya duƙa ya gaida Aunty farida ” ta amsa tare da tambayar’sa ko lfy ” eh lfy wani likitane yakawo saƙon nan wai inji oga yace abawa hiyana ” ok to ajiye a saman table ɗin gaban kan nan ” mikewa yayi ya ajiye sakon san nan yanufi waje
Bayan sun gama chin abinchine suka mike zasu tafi ɗaki, Aunty farida tasa hannu ta ɗauki sakon tana faɗin muje ɗaki kisha maganin hiyana ” toh kawai hiyana tace, san nan suka nufi waje ” sai da Aunty farida ta tabbatar hiyana tasha magani san nan takama hannun diyana da amrat suka nufi,dakinta, a gurguje sukayi wanke sukayi sallar issha suka kwanta asuba tagari

Tunda sukayi sallar asuba yau basu mai da barchiba ” diyana tun karfe 7 take gaban mirro ta goga wan nan ta fenta wan nan ba karya tayi kyau sosai tamkar zataje gasar sarauniyar kyau ” da sallama Aunty farida tashigo ɗakin tana waya da Aryan, wow my diyana kin ganki kuwa kamar wata sarauniya ” dariya diyana tayi tana faɗin ngd Aunty farida ” dawa kike magana kuma Aryan ya tambaya ” hmm nina mantama muna waya wlh, kyan my diyana ne ya rikitani ” shiru ya ɗanyi kamar mai tunani chan kuma sai yace to ɗauke’ta hoto ki turomin naga kyan daya rikitakin ” ae kuwa kai ma idan kagani sai ka rikiche ” to shike nan turomin ɗin dai kekam ” ok tace tare da chire wayar daga kunnen’ta ta katse kiran” tadubi diyana tace to tashi kisa kaya namiki hoto ” yauwa Aunty farida Allah yamiki albarka daman inasan inje in anshi wayar Aunty Zahra nazo nayi hotan, tayi maganar tana kokarin mikewa..✍️

 

 

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button