Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 4

Sponsored Links

๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ
*~{{MY FAMILY}}~BOOK 2*
ยฉยฎ *UZ-2023.*

*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{Ummiee Zaria}~*โœ๐Ÿผ

~~~*Page 4*

Allah yasa albishir da haihuwan Saniyata zakamin, dan satin daya wuce danaje gidan gonar na samu guda a cikin su da ciki tsoho kuma Zakariya yace min suna saran haihuwar ta cikin satin nan”
Hajiya ta fad’a tana washe baki,
“Ah ah kam wannan albishir din nawa wanda kika dade kina jira ne kedai kawai ki tanadi goron ki na albishir ni kuma idan na dawo in baki shi da zafin shi,”

Yana gama fad’in hakan ya take ma su Musty baya wadanda suka fice tuni,
Da gudu gudu ya samu ya cimmusu, kamar dama AK jiran isarshi ya ke ya wani bishi da kallo yana cin magani,

“Yusufยณ”
Ya kira sunan Yusuf din har sau uku shima kuma Yusuf din yaci gaba da amsawa ba tareda ya gajiya ba.

“Wallahi in ka fada Allah ya isa na”

“Kai dallah can ware, ai wallahi kaji dai nama Kara rantsewa yasin sai na fad’a”

‘Oh amanata zakaci bayan na yarda da kai?”
AK ya tambaya yana marairaice wa,

“Amana ta nawa kuma? Amana ta wuce wacce ka cinye tsakanin ka da zuciyar ka, malam ni mafita kawai nike nemo maka saboda ina kaunar ka da yawa bazan so inga kana wahala ba”

“Kai wai ku tsaya kunfa sani a duhu ban gane ba, meke faruwa ne anan?”
Musty ya tambaya yana shiga tsakaiyar su,

“Ni dai Allah ya isa na wallahi, kuma ma laifina ne dana fada maka damuwa ta”
Cewar AK a yayin da yayi gaba ya fice daga gidan ya barsu a baya Yusuf na mishi dariya.

“Wai Baban Affan bazaka fadamin abunda yake faruwa ba?”

“Me zai hana in shafa maka, amma dai gaskiya labarin mai tsada ne wallahi bazan fada muku ba sai naji saukar alert mai nauyi cikin asusuna,”

“Ah haba Baaba kar muyi haka mana nine fa Mustyn ka”

“Koma dai miye na dai fada maka amma ga Satan amsa zan baka, *abokin ka ya fad’a soyyaya*”

Wata irin fashewa da dariya Musty yayi kafin ya tsagaita da dariyar anan inda suke tsayen yayi ruku’u na nuna godiyar shi a wajen Allah subhanahu wata’alah,

“Ai dole kayi ruku’u wallahi”

Rungume Yusuf yayi tsamtsam bayan ya dago cike da tarin murna da farin cikin da suka sauka mishi ya sanya duka karfin shi ya d’aga Yusuf din sama yana juyawa dashi irin yanda akewa yara,
Dan koba komai dama shi Musty din yafi Yusuf din jiki kasancewar Yusuf din bafulatani sai ya zamana hatta da jikin shi irin na fulanin ne,

“Kai miye haka dallah ni saukeni ya zaka wani dunga juyi dani kamar ka dauki karamin yaro, dan allah saukeni juwa nike gani”
Ya fada yana dukan kirjin Mustyn a kokarin shi na ganin ya sauke shi,
Ajiye shin yayi yana dariya shi kuma saiya rike Mustyn sakamakon jirin da yakejin yana neman kadashi,

“Kai dan iskane wallahi musty taya zaka wani dunga juyi dani a filin Allah dan kawai kana takamar ka fini girman jiki to yasin kayi ma kanka bazan baka labarin ba”

“Kama isa ka shafa min mai abaki sannan kace bazaka fadamin ba, wacece dan Allah?, kai amma wallahi AK dan rainin wayau ne wai dama soyayyar ce duk tasa ya firgice uwa wanda ya shekara rashin lafiya? Oh Allah na gode maka ashe zanga wannan ranar da AK zaiso wata macen sab’anin matan da kullum sune suke binshi”

Dafa kafadar shi Yusuf,
“Kaga Malam muje kafin mu rasa jam’i kardai ka manta kanun labarin kawai na fad’a maka cikakken labarin sai naji alert tukun a hakan ma kuma har sai Sadeeq ya dawo zuwa gobe tukun dan yace min zai shigo gobe”

“Fad’i ko nawa kake buk’ata wallahi zan tura maka a yau din nan in dai zaka bani labarin nan, Allah Yusuf in kaki fadamin jinina yana iya hawa kafin safe”

“Oho in ka kashe kanka ai Jameela ce zatayi a Asara kaga kana mutuwa ni kuma zuwa zanyi in roki alfarma a matsayina na abokin ka a bani ita in aura basai an canza ranar auren da aka sanya ba, dan haka kama kanka Malam”

Duk yanda musty yaso Yusuf ya bashi labarin wacece yaushe kuma abokin nasu ya fara soyayyar k’iyawa yayi har sukaje sallan suka fito,

Wannan karan AK bai jira sun jera ba yayi gaba abunshi dan da gaske haushin wase yakeji,
Ya daga fada mishi sirrin shi dan wulakanci zai wani zo ya nemi baza labarin shi a faranti yana tallah dashi.

Sai da ya sake sabon wanka kafin kiran Musty ya same shi akan shifa suke jira ya shigo suci abunci suna sashen Hajiya,

“Oh dama acan sashen Hajiyar kuka saba cin abunci ba anan ba? Ko koh tsabar son ayi munafunci na a bayan idona shi yasa kuka wuce can? Wallahi nidai ban yafe ba duk wanda yayi gulma na”

“Ai sai kayi shegen mita kamar goyon mace kuma anyi gulmar naka kayi abunda zakayi, malam in zakazo muci abinci bismillah in kuma baka zuwa ma duk cikin ka tayi atoh”
Ya k’arasa fad’a tareda tsinke wayar nashi,

Hajiya, Meenal, Musty, Yusuf dukan su su hud’un zaune suke a kan dinning table din falon na Hajiya ko wanne da plate din abunci a gaban shi, sab’anin Meenal da nata plate din ke dauke da meat pie guda biyu sai lemun kunun aya mai sanyi data tsiyaya a cikin kofin tambulan tana cin meat pie din tare dashi,
Doguwar riga ce a jikinta shigar datafi ta’amali dashi a koda yaushe sai dan kwalin rigar data daura shi akan nata ba tare da ta d’aure ba,
Hira suke gudanarwa wanda kuma rabin hirar akan tsare tsaren bikin Musty ne wanda a yanzun bikin nashi ko wata biyu bai kaiba,

Da sallama ya shigo d’akin kuma yanzun din ma dai kamar d’azun ta kofar bayan ya Kara biyowa ya shigo,
Hajiya ce ta dago kai bayan sun amsa sallamar,

“Wai kai Abdul wannan kofar ta kitchen itace kake so ka mayarmin da ita kofar shiga da fitar ka ko ya yah? Karfa kaga dan d’azun ka shigo tanan bance komai ba kayi zaton kyaleka nayi,
Wannan ai salon ka nuna ma barayi hanya ne, ke tashi kije kisama kofar key ki kuma ciro key din ki kawo min nan sai inga ta inda zaibi kuma idan ya tashi fita”

Shidai bai tankata ba har sai da ya samu kujera wacce take kallon kujerar da Meenal ke zauna yaja shima ya zauna, zaman nashi kuma yayi dai dai da mikewar Meenal taje ta kulle kofar ta kuma ciro key din kamar yanda hajiya ta buk’ata,
Sai dai kuma tashin ta na zuwa da dawowa duk tayi sune idanuwan AK yana kanta dan itama dai sabon wanka tayi tadan feffesa turare kawai kuma sai zuciyar shi ke raya mishi cewa wai tayine saboda shi, kujimin wani kwala kai a faranti fa irin na jikan innan๐Ÿคจ.

“Hajiya k’ofa dukan su sunan su kofa, dan na biyo ta nan kuma ai ba laifi bane tunda naga dai ni din ba bako bane”

“Kace haka mana dama, amma ai a gaban idon ka d’azun ka firgita takwara kasa ta fara kiramin fatalwa ana zaune kalau”

“To Kiyi hak’uri zan kiyaye”

“Da dai yafi maka kam, ke kuma sai an rok’a ne kafin ki zuba mishi abuncin?”

“Toni nasan wanda yake son cine hajiya? Kuma ai baice azuba mishi bama!”

“Amma dai kin iya jin baki da neman magana inba haka ba har zaki kwana ki hantse a gidan nan sannan kice min wai baki san me zaici ba bayan kinga dukan mu anan tuwon muke ci in bake da shegen tsurfa ba da kika maida kanki wata iri bazaki zage kici abunci mai nauyi ba”

Hannun shi ya mik’a ya dauki plate,
“Kyaleta Hajiya zan zuba da kaina”

Shiru sukayi kowa yaci gaba dacin abunda ke gaban shi har suka kammala, kafin suka dunguma suka koma falon na Hajiya yayinda Hajiya taci gaba daba Wase labarin gidan gonar su Yusuf din dake samaru wanda suke tayata kiwon nata dabobin. Musty ne ya jefo ma meenal tambaya da cewa,
“Bestyn ki fa tace min ke suke jira batun cire anko wai tunda kika zo gidan nan baki zuwa ko ina daga makaranta sai gida shi yasa baku samu damar zuwa kasuwa ba”

Mai makon Meenal ta bashi amsa sai Hajiya ne ta amsa mishi da cewa,

To kai Musty ta ina macen dake iddah zan saketa sakaka ta kama yawo salon ubanta ya sani a bakin duniya,
A’ah wallahi koma miye zasuyi su jin kirta har zuwa gaba kadan in kuma ya zama dole ita Jamilan basai suje ita da Maryam su fito da ankon ba, cire anko dai ba wata tsiya ba,”

“Hajiya kasuwa kawai fa zamu awa nawa ne mun siyo mun dawo?”
Cewar Meenal.

“Eh fa kasuwar koma minti daya ne nidai nace a’a dan dole inyi kaffa kaffa dan kar kiyi mamaki ace ubanki yana nan yasa masu kula mishi da shiga da fitan ki dan kinsan dole na mishi kike zaune a gidan nan badan yana so ba kamar wani shine yama yata nakudar ki”

Cike da haushi ta tashi fuuuu kamar wata kububuwa ta haye sama tana turo baki,

“Ai sai dai Kiyi ta fushin ki amma babu abunda zai canza in fad’a miki, aini kuma shi kenan na d’auko ma kaina jangwam magana daya biyu ki wani dunga turomin baki dan kaniyar ki, da dai ina zamana abuna baki na Alaikum yanzun banda halin in zauna shiru a cikin gidan nan sai dai in kina makaranta, ai dole ma Kiyi aure da wuri wallahi tun kafin a ganmu a rana a mana gwai Allah”

Ita fa Meenal bawai saboda abunda Hajiya tace bane yasa ta wuce sama ah ah tadai tuna cewa bata da pad din da zata canza cikin dare ne dan a kayan data kwaso a gidan Sarki pad guda daya kawai ta gani,
Dan haka koda ta shiga cikin dakin kudi taso d’aukowa domin ta fita shagon dake waje ta siyo saboda gidan na hajiya dai babu yara balle ta aiki wani daga cikin su,
Sai dai kuma tana shiga dakin kira ya shigo wayar ta koda ta duba kuma sai taga malam ne ya dawo mata da kiran da tayi mishi d’azun bai dauka ba dan tunda ta dawo gidan kullum ne zai kirata dan ya tambayi ya take da fatan hajiya bata matsa mata kamar wata wacce hajiyar zata dafa ta cinye,
To anyi rashin sa’a yau din gaba daya basuyi yawa ba dan tayi sammakon zuwa makaranta wanda hakan yaja harta mance da wayarta data kashe tasa a caji,
Sun dade suna hira bayan sunyi gaisuwa kafin ya mata saida safe ya kashe wayar,
Gyalen dake kanta kwai ta gyara ta d’auko kudin ta sauko, babu kowa a falon sai Sadeeq dake waya, AK da Musty duk bata san ina sukayi ba garama hajiya taji motsin bude kofar dakin ta d’azun da alama ciki ta shige,

“Ah ah an matan Hajiya sai ina kuma?”
Sadeeq ya tambaya yana dan kauda wayar daga bakin shi,

“Kofar gida zani zan d’an siyo abu a shagone yanzun zan dawo”

“Kawo in amso miki Kiyi zaman ki dare ya farayi”

Kai๐Ÿ˜ณ” ta furta tana zaro ido, ina ita ina aiken Sadeeq siyo pad fisabilillahi,

“Ya akayi ?”ya tambaya
“Ah ah ka barshi dan Allah wallahi yanzun zan dawo kaga ai waya kakeyi”

“Kawarkice ko in baki ku gaisa ne?”

Bata tsaya ba tana ficewa daga falon take cewa “ah ah kace ina gaisheta”
Koda ta fito babu kowa a harabar gidan sai hasken wutar lantarkin daya haska ko ina ya fito fes kamar ba dare ba, daga can bakin gate kuma masu gadine zaune suna hira a tsakanin su,
Karasawan da tayi kusan sune kuma hakan yasa daya daga cikin su mai suna Isah tasowa,

“Zakiyi aike ne Hajiya?”

“Ah ah ya Isah ba bu wani abu jeka zauna kawai zan amso da kaina”

“Haba Hajiya gamu zaune ba wani abun mukeyi ba ai da nauyi mu barki kije siyan wani abu da kanki da girman kujeran ki ranki ya dade”

Da murmushi a fuskanta ta amsa mishi da cewa,
“Allah kuwa ka koma ni da kaina zanje ai ba zama zanyi ba kafin ka sani na siyo na dawo”

“To shi kenan ranki ya dade tunda kince haka a dawo lafiya”
Ya k’arasa ya bude mata kofar ita kuma ta fice a gidan,
Duk da cewa a wasu unguwan nin za’a iya cewa dare ya farayi ta yanda zirga zirgan mutane zakaga ya ragu su nan ba haka abun yake ba domin yawancin darare a cike wajen yake kasancewa da mutane sakamakon wadannan shagunan da suke raya unguwar akoda yaushe baya rabo da jama’a inba tsakiyar dare ba,
Bata tsaya bata lokaci ba taje chemist din dake nan ta siyo pad din guda d’aya kafin idan taje asibiti gobe zata dibo wasu,
Tana siya din kuma ta dawo gida, wannan karan ma Isah ne ya bude mata domin tana tsaye harta je ta dawo,

AK ta hango zaune a cikin motar shi ya kunna fitilar cikin motar sautin kid’a na tashi kadan kadan shi kuma yana zaune a mazaunin driver sai dai bai kulle kofar motar ba domin kafar duka biyun ma ata wajen motar suke yana danna waya,

Murmushi tayi, kasa kasa take cewa,
“Mutum bashi da aiki sai na cire manyan kudade yana siyan manyan motoci to muma dai baza’a mana Kuri ba atoh,”
Key din motar ta na wajen Sarki dake rike a hannun ta wanda dama ta fito dashi ne da niyyar idan zaka koma ciki ta bud’e kofar motar akwai sakon da Meelat ta bata d’azun a makaranta shi take son dauka a cikin motar,
Sai da ta jinjina mukullin da kyau sannan ta matsa luck daga inda take tayi unlucky din motar, har wani canza tafiya take a yayin da take k’arasa wa zuwa wajen motar,

Shi kuma AK dake zaune yana amsa waya ta Bluetooth din dake kunnen shi daya wayar dake hannun shi kuma yana duba sakon ni karar da motar tayi ne yaja hankalin shi zuwa gareta dan sam bai san da wanzuwar ta a wajen ba,

Kallo yake binta dashi cike da burgewa domin shi dai a yanzun kam allah ya sani babu wani abun halittan da baya gajiya da kallo wanda kullum yake fatan ya dauwama yana kallo kodan samuwar farin cikin zuciyar shi irin yarinyar nan,
Shi dai yasan bai taba jin son wata yarinya irin yanda yake jin sonta a cikin ko wani fitar numfashin shi,
Ji yakeyi kamar inbai sameta yana iya rasa numfashin shi,
Wallahi ko nawa za’a nema a wajen shi zai bada koda ko kafatanin dukiyar shine dan dai kawai ta zama mallakin shi.

Dan haka da kallo yaci gaba da binta yana jin wani yanayi mafi kololuwar dadi na lullube shi, har zuwa sanda ta isa wajen motar ta wani bude ta da still,
Murmushi yayi a bayyane ya furta cewa “da alama dai yar kauye tayi agogo shine ake mana kaud’i”
Kallon ta yaci gaba dayi yayin da ita kuma ta shiga cikin motar ta zauna, saida tayi warming motar da kyau kafin ta fito daga ciki ba tareda ta kashe motar ba ta zagaya ta bud’e bayan motar ta cire sakon da take son d’auka sannan ta maida booth din ta rufe ta Kara komawa cikin motar ta zauna itama kafafuwan duka guda biyun suna waje kamar yanda ya zauna,

“I will call you back John please excuse me”
Ya furta cikin harshen turanci bai kuma jira amsar John din ba ya yanke wayar,
Takowa yayi zuwa inda nata motar yake bayan ya tura murfin nashi kofar motar ba tareda ya kashe ba har ya iso inda take,
Tun tasowar shi idanuwan ta ke kanshi tana mishi kallon kasan ido ba tareda tayi yanda zai gane cewa kallon nashi takeyi ba, har ya iso inda take, yana karasawo kuwa kamshin turaren shi gaba d’aya ya lullube wajen, wanda dole saida ta runtse ido tana mai bude kofofin hancin ta dan taba turaren nashi damar isa cikin kwalwarta da kyau……

 

*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button