Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 64

Sponsored Links

64

Farincikin data tsinci kanta a ranar bazai misaltu ba,gata ga ummanta,ga kuma habi dinta,bata manta da bilalu ba,sai data kokawa rashinsa a dai dai wannan lokacin.

Hira iya hira,labarai rankatakaf na abubuwan da suka faru cikin gidan dana qauyen sanda bata nan sai da habiba ta sauke matashi,ko abinci saida ummansu tayi da gaske sannan ta tsaya taci.

Habiba da umman sun fara mata ne da labarin abinda ya faru cikin gidan,bayan tafiyarta ummanta ta shiga damuwa qwarai,saboda rashin sanin taqamaimen inda aka kaita,sanda kawu as ya shaida mata ya karbi address na samir ta dan samu sauqi cikin ranta na wasu lokuta,daga bisani kuma kwanciyar hankalin ta wargaje,saboda jin an debi watanni shuru babu kaltum din babu labarinta,gefe guda kuma inna laure tana murza tsiyarta,tare da baza habaici akan auren kaltum,saidai cikin hikimar Allah,data durfafi tashin dare tana kaiwa Allah kukanta,sai ya sanya mata dangana,ya fidda mata damuwa,har ma tayi mafarkin kaltum din sau biyu cikin kyakkyawan yanayi a wasu darare guda biyu bayan ta gama sallar bacci ya dauketa,abinda ya sake sanya mata kwanciyar hankali kenan.

Babu dadewa sai ga wata qungiya me suna professor rashid women aid forum,wadda tazo rabon jari ga matan karkarar,ummanmu bataje ba,amma sai gashi anzo har gida an kawo mata nata tallafin jarin me tsoka,wanda kusan yafi na kowacce mace yawa,suka dinga qara mata kudin da kadan da kadan,ta cika da mamaki da kuma tsoro,daga bisani zuwan qarshe da suka kawo.mata tace ba zata karba ba,saiga samir yazo da kanshi,ya bayyana mata kansa,bai boye mata komai ba,saboda yace yasan ita din uwace,tsayayya jajirtatta,kuma a soyayyar uwa da yarta tabbas hankalinta bazai taba kwanciya ba idan batasan inda diyarta take ba,saidai bai bayyana mata yadda zaman aurensu yake da kaltum ba.

Sosai hankalin umman ya kwanta,ta kuma samu salama mai tarin yawa,taja bakinta ta rufe kuma,bata gayawa kowa waye samir din ba,saidai kuma tun daga wannan lokacin ya dauke musu nauyin ci da sha,gefe daya ga sana’ar ummanmu nata habaka,kasancewarta dama mace mai tarin kirki tun da can,tun mijinta malam amadu nada dukiya,kasancewarsa mutum me arziqi ada,bayan aurensu ya soma tsiyacewa,mutane suka fara cewa ya auri mai farar qafa.

Tun baya dauka har ya soma yarda,abinda yasa ya tsaneta ya tsan gwameta kenan ita da yaran.

Abun mamakin da ya faru a lokacin shine,yadda hankalin malam.amadu ya fara tashi,saboda jita jita da laure ke yadawa cewar anya ba kudin diyarsu sukeci ba kuwa?,sai a sannan ya fara tada hankalinsa nason sanin inda ya miqa kaltum din,ummansu tana kallonsa bata ce masa ta tafas ba,haka zai qaraci zirgillonsa kullum rana yana zuba idanun ganin samir ya kaishi inda diyarsa take,ko sau daya ummansu bata taba tanka masa ba.

Ba jimawa kuma sai ya fara wani zabura,yana tsaka da barci sai aga ya farka a firgice ya fito da gudu yana kiran sunan bilalu,yana hirji kan bilalun ya yafe masa,gaba daya sai ya koma wani firgitacce,ko baccin rana baya samun yi bare na dare,daya fara gyangyadawa zai farka a firgice.

Da farko ance masa wai fatalwa ce,umma ta kafe kai da fata kan cewa ba ita bace ba,danta bazai taba fatalwa ba,tunda ma ai saiya kwanta bacci yake ganinsa,daga bisani da suka samu wani malami masanin addini sosai,yayi masa bayanin komai,sai ya tabbatar masa haqqin bilalun ke bibiyarsa,ya bashi shawarar ya tuba ga Allah,ya kuma yawaita sadaqa wa bilalun,da ziyartarsa duk ranar juma’a idan hakan zata yiwu.

Da taimakon wadan nan addu’o’in ya fara samun salama,sai ya jima baiyi mafarkin ba,saidai gaba daya yayi laushi ya kuma canza,bashi da buri da addu’a koda yaushe illa addu’ar Allah ya bayyana kaltum din.

Ana tsaka da wannan samir din ya dawo da plan na canza musu ginin gidan gaba daya,saidai hassada da qyashi suka sanya laure d kawo iliya cewa basuso,yarsu asiya wadda tayi aure tace zaa canza musu suma.

A sannan asiyan tayi irin auren da suke burin tayin,alhj dauda ya kashe mata kudi kamar baisan zafinsu ba,sunata murna da alfaharin sun kafa tarihi cikin qauyen,bayan ya musu romon bakan suna zuwa asiya zataci gaba da karatu,saita zama babbar likita,duk kuwa da cewa basusan kowa nasa ba,amma su murna suke yarsu tayi goshin da kaf fadin qauyen babu wanda yayi irinsa.

Baibi ta kansu ba ya gyara sashensu kaltum din,saidai bai duba halayyarsu ba yayi musu kwaskwarima kamar yadda ya yiwa maqotan.

Tun tafiya batayi nisa ba jikinsu yayi sanyi da lamarin asiya,saboda tunda taje gidan alhj dauda cikin wahala da wulaqanci take,bata da wani girma ko kima,saboda sun gama watsewarsu a waje kafin auren,don haka ko a gaban ‘ya’yansa da matansa guda uku data taras goranta mata yakeyi.

Ashe alhj dauda inuwar giginya ne shi,na nesa kasha dadinta,kowacce mace a gidansa ita kewa kanta komai,idan yaranki kuma sun tasa suyi miki,daga qarshe dai sai ya zamana laure ita ke ciyar da asiya dake aure wani gidan,sun dinke bakinsu saboda gudun dariyar jama’a,ta zauna duk da wannan wahalar da take ciki,saidai zancan duniya baya buya,kamar yadda dadi da wuya basa buya,tuni zance ya fantsama,saidai an kawo idanu an zuba musu,ana jiran ranar da zata fashe.

Babu jimawa ciki ya bayyana a jikin asiya,nan alhj dauda yayi tsalle yace ba dashi ba,ba kuma a gidansa ba,don shi bai aurota don ta haihu ba,ya aurota ne don ya huta da ita,abinda ya dagawa inna laure hankali kenan,saboda sun kama shirya plan na asiyan tayita haihuwa,kodon kwadayin abinda alhj dauda ya tara,da qyar aka ciyo kansa,bayan yarjejeniyar cewa bazaiyiwa asiya komai ba,data haihun kuwa haka akayi,laure ce tayi komai kamar ita tayi cikin,aka rufa akaci gaba da zama a haka,ba dadewa kuwa wani cikin ya sake bayyana,sai fa aka koma ‘yar gidan jiya,kullum asiyan na tafe a hanya,wadanda ake boyewa kar su san komai tuni komai ya gama bayyana,a haka ake,har zuwa jiya da hukumar NDLEA ta kawo samame gidan ta cafke alhj dauda,ashe tsohon dan safara da saida muggan qwayoyine,wannan ne abinda ya kawo asiya gida abirkice,gashi batasan wani dangi nasa ko daya ba,na kusa ko na nesa,matansa kuwa ba zaman lafiya sukayi ba bare ta tambayi wata arziqi ta gaya mata,ita sai taga ma sam cikinsu ba wanda ya damu,kowa sabgarsa yaci gaba dayi,aka tattarata aka watsar,don dama kusan kamar kowa ya tsaneta cikin gidan,kamar mujiya,babu me mu’amala da ita.

Malam amadu da yusufa mijin habiba kuwa,rumfa guda biyu cikin babbar kasuwa samir ya siya musu,ya zuba musu jari me kauri a ciki suna juyawa,idan kayansu sun qare,yusufa zai tattaki har jahar Lagos yayi musu sari,rayuwa tayi albarka,saidai har yanzu tabon mutuwar bilalu na taba amadu,da mafarkinsa da yakanyi jefi jefi,sai kuma burin ganin kaltum,wanda kunyar abinda ya aikata ya hanashi tambayar samir kaltum din.

Ita kuwa wasila,tun randa aka kaita gidan nasuru,sati daya kacal nasurun ya tsallake yabar garin nan ba’a sake jin labarinsa ba,tun lantai babarsa na ganin xai gaji ya dangana ya dawo har abun ya fara damunta,yayin da wasila kuma ta miqe qafa,tana cewa zama daram,duk inda yaje zai dawo ma,ita ba zatayi zuciya ba,hakanan ba zata gaji ba,sai ya zamana lantai ke ci da ita.

A zaton lantai zata zauna da ita kamar uwarta,sai taga ba haka bane,cangal wasila bata iya mata,saidai taci tasha ta qoshi,ta tara qawaye susha hira da shewarsu,kamar ba itace wadda mijinta ya bace ba.

Lantai bata da haquri,don haka ta yuwa wasila kaca kaca kan abinda take,nan fa wasilan ta tsiri fushu da maidawa lantai maganganu,daga bisani ma sai lantai taga ta tsira fita unguwa,tun safe sai dare,ta kuma dawo da abubuwan arziqinta taci tayi hani’an ta kwanta abinta,tama daina cin abincin lantai din,tace idan ma saboda shi take uzzura mata.

Sai zaman gidan ya koma kamar na kishiya da kishiya,idan kaga lantai da wasila ana cashewa zaka dauka kishiya da kishiya ne,haka suke zaune.

Sannu a hankali wasila ta fara mulka wata uwar qiba ta tashin hankali,tayi dimimi abinta,sai hankula suka fara dawowa kanta,zargin ciki ya tabbata akanta,koda lantai ta tuhumeta…..sai ta shaida mata eh tabbas ciki ne da ita,kuma cikin nasuru,abunda lantai ta musashi kenan,saboda tunda aka kawo wasila nasurun bai taba kwana a sashen bama,yana tsohon dakinsa,har zuwa sanda ya tsallake ya tafi ya barsu.

Sanda lantai ta musa gagarumar rigima ta barke,ita tana ba cikin danta bane,wasila na cewa dole ta musa tunda ita ke tayasu kwana a daki,daga qarshe dai aka yanke zuwa cikin gari ayo scanning,wasila batasan meye ba,tace aje din ayi,saime?,ko shi akayi zai nuna ciki na nasuru ne,su kwano za’ayi ayi.

Anayin scanning kuwa ya bayyana watannin ciki,tafiyar nasuru wata shida kenan,shi kuma ciki wata uku,tun daga nan jikin iyayen wasila yayi sanyi,ita kuma ta dage kan hakane,ana tsaka da wannan rigimar Allah ya jeho da nasuru,suka bayyana gaban mai gari,ya kafe wasila da idanu yana mamakin qarfin halinta,cikin bacin rai yake bayyana gaskiyarsa,sai wasila ta fashe da kuka tana fadin,tabbas ciki ba nasa bane,ciki na wani dan maqwafcin qauyensu ne,wata barratu cikin qawayenta ita ta bata shawarar cewa,taje kawai tasha sabgarta,tunda tana da aure yanzu babu me ganewa,koda ta samu ciki akwai na nasuru ne tunda shine mijinta,ta dnga samun ‘yan kudaden da zata kashe sabgar gabanta,basai uwar miji ta bata ba,tunda miji ya ajjiye ta ya tafi,me zata zauna yi itama.

Hankalin kowa ya tashi a wajen,iyayenta suka dinga kuka suna tsine mata,sai da me gari ya tsawata musu,a take anan nasuru ya rattaba mata saki uku,bayan wasu watanni tana gidansu da suka juya mata baya suma,nasuru ya aure lantana qawar kaltum,ya dauki matarsa suka wulla ibadan inda yake neman kudi.

Cikin naquda wasila ta hadu da jijjiga eclampsia,wannan yadan taba mata qwaqwalwa,ta haifi danta namiji,amma yazo babu rai saboda wahalar da yasha a ciki,haka iyayen wasilan suka fara nema mata magani,saidai sunyi saunyi harsun gaji sun watsar,bata warke ba saidai ta samu sauqi,wannan tabban guda biyu yasa tarasa me aurenta,bayan rasuwar mahaifiyarta taci gaba da rayuwa ita kadai cikin gidansu,ita ke dawainiya da kanta da komai nata,tausayinta ya sanya ummanmu ta dauke mata abincin rana dana dare,hakanan kuma takan aika mata dan kudin batarwa,kullum tazo gidan cikin nadama da neman yafiyar kaltum take,takan ce jifa tayi,ya kuma dawo ya sameta tsakiyar kanta.

Cikin matuqar sanyi da mutuwar jiki kaltum tace
“Allah ya kyauta,ya rufa mana asiri,ya rabamu da sbarrin zukatanmu da kawunanmu” tabbas zalunci abun tsoro ne,kuma tun a nan gidan duniya Allah ke sakayyarsa,babu daga qafa,babu jinkiri,lallai Allah baya son zalunci,kuma baya jinkiri wajen ramawa wanda aka zalunta.

A iya wunin ranar kadai kaltum ta tabbatarwa da kanta lallai sabuwar rayuwa ta zowa ummanta,mutane maqota wannan ta shiga waccar ta fita,kowa tazo ganin kaltum,tare da godiya kan kabakin arziqin da samir ya saukewa kowa,kafin kace meye wannan gida ya cika da abinci,kwano kala kala,kowacce da kalar abinda zata kawo.

Ko can dama ummansun mutum ce ta mutane,tana da kirki da kuma hannun kyauta sun suna da shi,abun hannunta bai tsone mata idanu ba,don haka ko a yanzun ma abun bai zame mata sabo ba,tana da hidima da jama’q,duk sanda wani cikinsu ita ko habi wani ya miqe sai kaltum din ta bisu da kallo,farinciki na ratsata na yadda sukayi kyau suka murje,rayuwar tayi kyau fiye da yadda tayi hasashe,kowaccensu sanye da sutura ta rufin asiri gwanin sha’awa.

Har magariba suna zaune ana abu daya,abinci kuwa har kaltum ta rasa wanne zataci a ciki,don har babar lantana sai data aiko da nata,bayan sun idar da magariba aka kawo yaron habi,sultan,yaron fes dashi sai qamshi yake,kyakkyawan bafulatanin yaro me kama da ubansa,bul bul dashi,da alama yana samun kulawa da soyayya daga mahaifinsa.

Shida uwar mijin habi din sukazo,tunda dama yana wajenta,a wajenta ya wuni,kuma dama ko suna gida ma wajenta take wunin,yadda taqe qaunar yusufa da habi haka soyayyar ta koma kan yaron.

Suka gaisa da kaltum cikin girmamawa,tayi mata godiyar abun alkhairin da samir yayi wa yaronta yusufa,kunyar baban ta kamata,macace ta gari,wadda bata qyamaci hada zuri’a dasu ba sanda kowa yake gudunsu,taso ‘yar uwarta,ta mutuntata qwarai,ta nuna mata soyayya,sun kuma riqeta da girma da mutunci

“Baba da kin bari nazo da kaina ma ai” ta fada tana murmushi,itama murmushin tayi

“A’ah kaltume…..wannan abun alkhairin yafi qarfin sai ke kinxo za’a miki godiya”.

A ranar duk sanda ta rufe idanunta muryoyin jama’a daketa mata godiya ke yawo a kanta,wai yau itace dimbun mutane ke mata godiya tare da son rabarta?,kowa yana farincikin samun wani alkhairi ta qarqashinta?.

Sultan dan habi yana jikinta,duk inda zata motsa dashi take motsawa,shidai kallonta kawai yake,saita zage tanata masa rawa sa waqa,tana cillashi tana cafewa,sai kuwa ya buda baki ya dinga bangala mata dariya,ta tsaya tana tayashi qaunar yaron na ratsata,tana jin kamar ita ta tsugunna ta haifeshi,habi na gefe tana musu tsiya.

“Wai ni kam inna?,tana nan da halin nan nata?” Baki habi ta tabe kafin dariya ya subuce mata

“Inna ai saura kadan a kaita gidan masu rangwamen hankali banda taimakon ummanmu……in gaya miki sata aka shiga akayi mata gagaruma,tun daga kudaden data mallaka har kadara,ke kaza wannan ba’a bar mata ba,hatta suturunta masu kyau sai da aka tsitsince,daga tafiyar sunan karime ta haihu,da inna ta dawo zaman ‘yan bori ta dinga yi tana kururuwa,ke daga qarshe dai abu kamar tabi tabi,amma da yake yarinyar nan karime bata da mutunci,wallahi cewa tayi zakka ce Allah ya fitarwa innan,turmin zani wannan kasa dauka tayi ta bawa inna,bakiga kudin da umma ta dinga kashewa akanta ba,don jarinta ma sai daya tabu a sannan,amma da yake Allah ya sawa sana’ar tata albarka babu dadewa ta maida komai,ta sissiya mata kaya masu yawan gaske,sannan aka fara samo kan inna,waisai ga inna ba kunya ba tsoron Allah tana shiwa ummanmu albarka,wai dama ashe har yanzun ita irin arziqi ce?,yau gashi ta maganta mata damuwarta” baki kaltum ta tabe,son abun duniya a jinin innar yake,sam bataga amfanin soyayyar da zata nuna musu a yanzu ba.

Ana gama sallar isha’i baba ya shigo gidan,fuskarsa kamar gonar auduga yana neman kaltum din,ta gaidashi cikin girmamawa a matsayinsa na ubanta,saida daga haka babu wani walwala ko sakewa ta taso daga dakin da akayi masa ciki da falo ta dawo dakin ummansu,tayi xaton umman zatayi mata fada,amma sai taga batace da ita komai ba.

Cikin awannin da suka rage kafin su kwanta ta karanci yadda baban nasu yayi matuqar yin sanyi,babu wannan fadan babu masifa,tsakaninsa da ummansu sai kulawa da kyautatawa,don kafin su kwanta din haka ya danno musu uwar fura da tsire me kyau,yace a basu ita da habiba suci.

Sai da dare ya raba sannan suka kwanta ita da habiban,sultan na gaban kaltum ba jimawa bacci ya daukesu.

Saidai tun kiran sallar farko sukaji muryar babansu a can sama,dukkaninsu suka farka,da suka kasa kunne sai suka fahimci mafarkin bilal dai yayi yadda ya saba,don haka kowacce cikinsu ta maida kanta ta kwantar.

Basu kai ga komawa baccin ba muryar muzammilu ta karade gidan da wani irin ihu da yake kwararawa,abinda ya sanyasu tashi dafa’an suka zauna,suna jin sanda ake bude qofar sashensu,don haka suma suka miqe suka tsaya daga tsakar gida,suna jin gunjin kukansa da tambayar da ummanmu da baba ke masa

“Gobara ce,ta tashi muna bacci,ta kama gidan gaba daya ta qone,salisu da jamilu da shamsu duka an fito dasu basa motsi,asibiti xamu kaisu yanzu” Allah sarki ummanmu,duka saita rude,ta koma cikin gida ita da baba wanda ke laluben babbar rigarsa da kudade ya zuba a aljihu,ummanmu ta debo wasu ya qara musu,baban yace ta zauna suje su dawo.

Daga habiba har kaltum kwanciya suka koma sukayi,duk da kowa cikinsu yaji susa cikin ransa,kodon saboda abinda ya samu yaran,saidai gaba dayansu ba abinda ke kai kawo a ransu face irin abubuwanda muzammilu ya aikatawa,wanda ya jawo mutuwar bilalunsu.

Sunajin yadda ummansu ta kasa zama,sai zirya take,babu jimawa ana idar da sallar asuba,ko addu’a ba’a kammala ba saiga baban ya dawo cikin mutuwar jiki,gaba daya yara sun rasu,biyu na muzammilu,daya da munzali,wanda wani lokaci yakan kwana a gidan,sun shaqi hayaqun gobara ne,har ya musu illa,ya toshe musu hunhunsu,fiddau kuma matarsa na can asibitin sun bata kwanciya saboda qonewa da tayi gaba daya a fuskarta.

Suna jin ummanmu na shiri tana salati,ba wadda ta bita ita da baban suka tafi,sukam sai da suka qarashe baccinsu,suka gyara mata gidan sukayi abun kari,suna aikinsu suna hira a tsakaninsu irin na ‘yan uwantaka.

Kaltum na mopping habi na kallon yadda wajen keta qyalli

“Wannan abu da kyau yake,yusufa dai yace in sha Allahu muma ya kusa yi mana gyara,kamar haka zai.mayar mana da gidan,harda tiles din xai saka mana” sai kaltum tayi murmushi,habi na dakai na karatu,inama yusufa zai barta tayi karatu,ko ita da zata dauki nauyinta,koda iya matakin secondary ne,koda kaltum ta gaya mata abinda ke ranta sai tace

“Haka baaba tace dashi,to baidai amsa ba bai kuma qi ba,kawai yace akwai nisa tsakanimu,amma idan da rabo wataran zanyi,shima yana sha’awar hakan”.

Wankansu sukayi tsaf suka shirya,sannan kaltum ta zabo flask mai kyau ta zubawa ummansu kayan breakfast din,sannan ta zuba musu ita da habiba da sultan,suka zauna a parlor suna karyawan,da nufin idan sun gama su wuce gidan mutuwar suyi musu gaisuwa.

Suna cin abincin suna hira,kaltum na tambayar habiba wai ina auwalu kuwa

“Hmmm,wa ya sanine?,ki cikin gidan sai suyi wata basusan ina yake ba,sai kuma ya kado sannan ake ganinsa”

“Allah ya gyara” kaltum ta fada tana duba agogon hannunta,data dago kai sai suka hada idanu da habiba,habiban ta saki murmushi

“Sai.nayita ganin kamar ba yaya kattume ta mai kitso ba,gaba daya kin canza,kin zama wata ‘yar gayu sosai,kalar fatarki ta canza,hanci ido dama gashinki kamar ba naki ba,irin matan da muke gani a tv” dariya kaltum tayi

“Lallai habi,ke bakiga yadda kika koma ba?,ni na zaci fa makaranta kika koma da kika waye haka?”

“Rufin asiri ne da yusufa ya sake samu…..sannan kuma ya koyamin karatun hausa,ina iya karanta hausa da rubutawa,sai yake samomin litattafan hausar nan na soyayya nake karantawa,ashe makaranta ce guda?,kinga abubuwan dana qaru dasu wanda ada bansan dasu ba?,gaskiya da ka muke rayuwar aurenmu” cikin doki da jin dadi kaltum tace

“Kai ashe kema kinbi sahu,amma naji dadi wallahi,saboda akwai qaruwa sosai a ciki,musamman zaka tsinci darussan rayuwa masu yawa,bama irin labaran da aka tsaftace alqalami,babu batsa sai soyayya mai tsuma rai,yadda zaki zauna da miji da al’umma lafiya ki samu tsira duniya da lahira…..gaskiya inajin dadin karatun novel sosai,saboda makaranta ce guda”

Suna tsaka da wannan hirar muntasir daya zama dan gidan yanzu yayi sallama

“Kaltum kizo kiyi baqo” harara habiba ta jefa masa

“Malam kaltum take yanzu…..ka daina bata mata suna” sosai ya saki dariya yana tsokanarta,kasancewarsa mutum me barkwanci da kirki kamar mahaifinsa kawu ado,kaltum na jinsu ta miqe tana sanya hijab tare da tambayar waye

“Kamar umar,yaron mijinki” jin haka ya sanya ta biya ta kitchen,ta hada kayan breakfast tace a fara kai masa,sai bayan wasu mintuna tabi bayansa,saita sameshi zaune saman motar anan ya karya din,yaji kuma dadin abincin,don ko breakfast din samir bai barshi yayi ba ya tasoshi.

“Gashi inji mai gida,yace ina kawo miki kiyi qoqari ki kunna,zakuyi magana” ya fada bayan sun gaisa cikin girmamawa yana miqa mata wani kwali,tun bata bude ba ta fahimci waya ce,tayi masa sannu da qoqari tare dayi masa sallama ta juya zuwa ciki bayan ta aiko yara su kwashe kwanukan sukai mata cikin gidan.

Yana qoqarin tayar da motar samir din ya kirashi

“Na bata yanzu yanzu”
“Ok” ya fada muryasa a qasa,sannan ya kashe wayar,umar ya saki murmushi

“So,soyayya wato bata da kirki,oga an masa mugun kamu da alama” umar din ya fada yana sakin murmushi shi kadai.

Tun a parlor din ta bude kwalin ta kunna wayar,tana gama daidaituwa kamar dama jiranta yakeyi kira ya shigo,Muhammad samir yayi saving sunanshi akan wayar,batasan murmushi ya subuce mata ba,ta saki kwalin ta shige dakin ummanmu,ta haye gadonta.

Sai data daidaita numfashinta,gab da zata katse ta daga ta kara a kunneta.

Wani nannauyan numfashi taji an saki kamar wanda ya tserewa abun tsoro

“Alhamdulillah…” Ya fada cikin tattausar muryarsa,data qara zama wani cool

“Da baki daga ba na rantse da Allah yau a garinku zanyi sallar azahar” dariya da mamaki ya kama kaltun,ta fidda idanu waje ba tare data iya cewa komai ba

“Da qyar jiya na iya bacci,banyi tsammanin zan iya kaiwa safiyar yau ba babu ke a gefena…..,abu daya ne ya ragemin damuwa da nauyin da zuciyata tayi….na kwana a dakinki,naga tarin sirrikan da aka boye ba’aso samir ya sani,naga zane kala kala na fuskar samir……ashe haka kema kike sona amma kika iya cinyewa baki furta min ba” wayyo,duk da baya kusa da ita amma ji tayi kamar qasa ta tsage ta shige ciki,saita bude baki kawai bat iya cewa komai ba,kunya na dawainiya da ita,tana tuna meye da meye ma ta boye ne a ma’adanarta,ba shakka akwai tarin abubuwa masu yawa dake nuna zallar bege da soyayyar samir din

“UMMUKULSUM” yayi kiranta da cikakken sunanta,abinda bata taba ji daga bakin kowa ba saishi,sautin da ya kashe mata duk wata gaba ta jikinta,saita sake lafewa saman gadon ummanmu,kamar zata nutse a ciki

“Idan kikaci gaba da yin shurun nan….to ki tsammaci isowata nan da awa daya,kuma bazan koma ba sai da ke…..”

“Am sorry” tayi hanzari fada da wani irin sound daya sashi sakin ajiyar zuciya mai nauyi.

Lokaci mai yawa suka bata kan waya,yana fallasa mata sirrin zuciyarsa,tare da narkar da ita cikin duniyar soyayyarsa,har ya sanyata itama ta dinga fallasa sirrikan zuciyarta ba tare data sani ba,batasan ta yiwa kanta barna ba sai da suka gam wayar ta fara tariyar kalaman data gaggaya masa,murmushi ta dunga yi tana juya wayar hannunta,wayace me shegen tsada,don irinta ce a hannunsa,saida habiba ta leao tayi mata magana sannan ta fito suka wuce.

Sun tadda gidan makokin a cikea dagule,duk kallo sai ya koma kansu,kowa sai ya tambaya
“Wai wannan kattume ce?” Habiba ke gyara musu

“Kulsum dai ko kaltum” cikin lokaci kadan suka zama wasu taurari su da uwarsu,kowa son rabarsu yakeyi,daqyar kaltum ta janye umma taje ta karya,sai gashi ana jira da rububin abinda taci ta rage din,kowa yana neman saura.

A waje suka ga munzali da muzammilu sunata share qwalla,muzammilu ma daya kasa jurewa kuka ya fashe dashi,baki habiba ta tabe

“Ashe dai kowa nason nasa” maganar data ja hankalin kaltum kenan,saita kada kai kawai,ta tabbatar zaluncin da suka yiwa bilal ne Allah ya nuna musu ishara.

Cikin kwanakin zaman makokin kusan umma ke dawainiyar abinci ita da baba,saboda muzammilun yanzu basu da komai,an daina jin duriyar mahaifiyarsu kwata kwata bare ta aiko musu da wani abu,wasu suce ta mutu,wasu suce an kamata tana sijin,to sanin gaibu dai sai Allah.

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_DA ZAFINSU_*

*_A TSARE SUKE_*

*_SUN TANADESU_*

*_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA’AWA_*

*_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_*

*_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_*

*_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_*

_WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_

08184017082

_MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_
09134848107

*_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA…..MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button