Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 58

Sponsored Links

58

Tamkar wata mashahuriyar barauniya haka ta dinga bibiyar bango cikin sanɗa sanda take baro dakin da momma raihana ke ciki,hikimar ubangiji ce ta sanya ranar gidan kamar anyi shara,duhun magrib yana shigowa zirga zirga ta ragu sosai,qwalla fal idanunta,zuciyarta na mata wani irin ciwo da quna take tafiya,babu abinda ke amsa kuwwa cikin kanta illa labarin momma.

Fuskarta a lullube kanta a qasa ta giftasu,kyauro ne,ya wuce yana sababin bala’i da masifa kan barin qofar dakin da akayi a bude har kawo wannan lokaci,sai data fita wajen gate din gidan sannan ta saki qatuwar ajiyar zuciya,ta tabbatar tayi escape,saura next step kenan.

Tun lokacin data baro gidan bata sake samun nutsuwa ba sai data hada dukkan hanyoyin da take ganin xasu xama sanadiyyar fitowar umma samir zuwa duniyar ‘yanci,tana ji a jiki da zuciyarta cewa…..zata sadaukar da dukka ranta don aiwatar da wannan aikin,babu abinda ke yawo a ranya face zallar mamaki da kuma tsanar mummy jidda,tunda take a rayuwarta….bata taba katari da azzalumin mtum kuma butulu irin Mommy din ba….don haka ko bayan ta dawo gida,bata zauna ba,ta dauko dukka wani abu da take da tabbacin zai bata gudunmawar zane.

Ana kiran assalatun farko tana kammala zanen surar fuskar raihana,ta dagashi sosai tana kallo,tunda take a rayuwarta bata taba zanen da ya kama qafar wannan a kyau ba,natasan meye dalili ba,amma ta danganta hakan da wala’alla samuwar ilimi a gareta,sabanin baya da take komai bisa radin kanta da kuma iya hasashenta.

Ajjiye takardar tayi ta nufi bandaki kai tsaye ta daura alwala,ta fito ta fidda hijabi cikin kayanta,ta mulke jikinta da turare ta hada da hijabinta da abun sallar,kusan wannan al’adarta ce a duk sanda zatayi sallah,domin samun kusaci da mala’iku.

Cikin nutsuwa ta tada sallarta,ta jima tana ganawa da ubangiji cike da tarin addu’o’i da neman dafawar ubangiji,a duk wani motsi da zatayi momma raihanan ce a idanu da xuciyarta,qila a yanzun itama tana can gaban ubangijinta,tabbas lamarinta cike yake da al’ajabi,zallar qudura ta ubangiji da buwayarsa,wanda ya nuna ikonsa da kuma qinsa ga zalunci.

Gefe daya samir ya fado mata a rai,shi kansa abun tausayi ne,ya rayu tsakanin numfashi da kuma hannun azzaluma data cutar da halitta mafi muhimmanci da soyuwa a wajensa…..sai kuma taja qaramin tsaki can qasan ranta…..data tuna abinda ya faru a dazu tsakaninsa da jauhar…..sanda suke hanyar dawowa gida,duk da cewa cike suke da farincikin farkawar daddy,amma hakan bai hana jin wani abu mara dadi na yawo saman zuciyarta ba.

Sake jan tsakin tayi,batasan me takeji cikin zuciya da ruhinta ba kan abinda ya farun,ta rasa sunan da zata bashi,bata yadda kishi bane….saboda ba haka taji ba akan wasila sanda take ganinta tare da nasiru ba,wannan din ya fita daban…..sai kuma tayi qoqarin watsa lamarin gefe ta miqe ta tada sallar asuba wadda tuni kiranta ya karade masallatan kusa dana nesa.

Qarfe bakwai da wasu ‘yan mintuna ta fita daga dakinta sanye da hijabin data idar da sallar,tana son ganin bibi a yau din nan,dole saita taimaka mata da shawara,batason tayi kwaba,bibi zata fita hangen abinda ya kamata.

Ko data shiga kitchen din bata taras da kowa ba,tayi mamakin bibi da bata fito ba,amma jikinta ya bata koma yaya ne tana gab da fitowa,tunda dama tana riga duka sauran ‘yan aikin fitowar,hakan ya sanya ta jawo abubuwan da take tunanin za’a iya buqata a girkin safiyar yau,ta fara gyarawa tana daga tsaye don tafi sauri.

Yadda hijabinta ke saukowa yana hanata jin dadin aikin ya sanyata zareshi ta dora saman qofar kitchen din,hakan ya bata damar yin komai da sauri.

A nutse yake takowa kai tsaye zuwa cikin kitchen din,duk da cewa safiya ce amma jikinsa wani lallausan qamshi yake fitarwa,yayi kyau cikin fararen qananun kaya da suka haskashi ainun,qal dasu kamar ba’a tabasu.

Fita ce ta kamashi bayan kiran da daddy yayi masa direct daga Asibiti,dakinsa ne ba’a gyare ba,kuma sam bayajin dadin zama a cikinsa,samun zama da baya yi ne yasa bai tsaya gyaranshi ba.

Dan qaramin tsaki yaja,yana jin kawo yanxu ya kamata kowa ma ya daina shiga masa daki,lokaci matsayi da kuma shekarunsa yaci ace akwai wata mace by his side.

Dai dai sanda yakai qarshen tunanin idanunsa suka masa maraba da ita yana gab da qarasawa kitchen din,sai ya rage hanzarinsa ya soma takawa a hankali zuwa ciki.

Ko baa gaya masa ba koda kuma bai kalli fuskarta ba yasan tayi nisa a tunani,duk kuwa da cewa aiki take sosai cikin kuzari,bin bayanta yayi da kallo,tana sanya da wasu silk sleeping dress riga da wando milk color,wanda suka kwanta a fatarta da jikinta,hakan ya bawa mazaunanta damar fitowa sosai,ta bayan qasan dankwalinta sassalkan gashinta ya leqo,ta motsa kadan zuwa gefanta tana zuba mai cikin frying pan,abinda ya bawa jikinta damar shaking.

Tsigar jikinsa ce ta xuba,tun daga saman kansa fuskarsa har yatsan qafarsa,yadan matse idanunsa kadan,saidai kafin yakai ga budesu sautin qaramar qara ta fito daga bakin kaltum din hade da yin tsallen daya sanyata yin kyakkyawan masauki a jikinsa.

Tsam ya riqeta cikin jikin nasa,kamar wanda ke sauraron faruwar hakan,abinda ya sanyata waiwayo da sauri cikin tsoro,sai suka hada idanu,sauke kanta qas tayi da sauri saboda wani bugawa da taji zuciyarta ta fara yi,a hankali tadan soma takawa da baya don xame jikinta daga tsakanin hannayensa,sai taji ya fincikota da sauri,abinda yasa ta qarasa fadawa jikinsa gaba daya,kanta yayi masauki a faffadan qirjinsa.

Dukkansu wuta ce ta dauke musu na wasu sakanni,kafin taji heavy voice dinsa data ratsa kunnenta,ta shiga aika mata da saqo qwaqwalwarta

“Kinyi gudun fallatsin mai,zakije kuma ki daki pan din ya dawo miki jikinki gaba daya….” Har yanxu bugun zuciyarta daduwa yake,musamman da taji hannunsa saman bayanta yana shafawa daga sama zuwa qasa

“Wa yace miki ana shigowa gaban wuta da silk material?” Ya fada da wata sassanyan murya can qasa,ba zata iya amsa mishi ba,sai kanta data girgixa masa,tuni qafafunta suka fara shaking,bata sani ba ko abinda yaji kenan,saiya saketa a hankali ta zame ta koma gefe tana juyar da fuskarta daga sashen da yake tsaye.

Second kusan biyar ba wanda ya iya cewa komai

“Bani ruwa” muryarsa ta ratsa shurun,saita juya a hankali zuwa sashen da suka girke na’urar sanyaya abu,tana jin yadda qafafunta sukayi sanyi laqwas.

Binta yayi da kallo,komai na jikinta na bayyana kanshi,sai yanzun ya gasgata zancan jawahir,tana boye komai ne don kada asan tana dashi,to amma dasu tazo ko kuma a nan ta samu?.

Feeling din da yakeji ke qara yawa,gashi ita kuma tafiya take kamar ba zata kai ba,saboda ta sani a karan kanta duk sanda ta motsa din sai jikinta ya amsa,saboda yanayin kayan jikinta,don bata tsammaci xai ritsata haka ba,shi yasa ta fito haka,da babu abinda zaisa ma ta cire hijabinta.

Binta yayi a baya,duk wani daukewa da saukewar qafarta yana binsa da kallo,yana noticing canje canje da dama tattare da ita,wanda rashin nutsuwarsa kan ciwon daddy da jinyarsa,kawo yau dan daukewar idanunsa daga kanta yaga abubuwa daban daban tattare da ita.

Cikin rashin sani dukkansu suka kai hannunsu saman mabudin fridge din,hakan ya bawa hannuwansu daman haduwa waje daya,hannunta a qasa nasa saman nata,ya dan lumshe ido cikin mamakin yadda dumin hannun nata yake ratsashi,duk da sanyi sanyi safiya da yake kadawa,da kuma na hadarin daya hado a jiyan bai kai ga zub da ruwan ba ya baje ya bada iska har kawo safiyar yau din.

Ita ta zare hannun nata,kana da sauri ta miqa hannunta ta zaro hijabinta da suka kawo gab dashi ta sanya,yayin da shi kuma ya buda ruwan ya kafa kansa yana sha cike da nutsuwar nan tasa,ka kace wani abu me maiqo yaci daga tashinsa,sai da yasha da yawa sannan ya ajjiye,yana amsa gaisuwarta,wanda tuni ta koma ga dankalinta da har ya fara ja,Allah yasa bai qone ba.

Gefanta ya ajjiye keys din dakin nasa

“Zan fita,ki shiga ki sharemin dakin,after kin gama komai”

“To” ta amsa a sanyaye tana gyada kanta.

Ya juya yana niyyar fita a kitchen din jauhar ta sako kai,fuskarta cike da murmushi cikin salo nason janye hankali tace dashi

“Hi sweet baby,good morning”
“Morning babe” ya amsa mata da muryar nan tasa dake sake narkar da zuciyar mata da yawa
“Ina zaka haka da sassafen nan” agogonsa ya kalla,bayason ta tsaidashi,ita har yanzu ta kasa fahimtar cewa yana mata kara ne,amma gaba daya ita din ba tsarinsa bace,bayason mace irin jauhar kwata kwata,yaga yaran masu kudi bila adadin….yaga gidajensu na aure…..sam rayuwarsu batayi masa ba,qalilan ne a cikinsu suke iya kula da gidansu dama mijinsu,suie kuma iya sauke responsibilities dinsu

“Wani waje me muhimmanci” sai ta dan bata rai

“Har unguwa ta fini muhimmanci kenan?” Ta fada a shagwabe,sai kaltum ta ajjiye spoon din hannunta,a hankali kuma a nutse taxo ta kewayesu ta fice bayan ta kashe wutar suyar,haka kawai takejin qirjinta na mata nauyi,yanayin kuma kamar yafi qarfin zuciyar tata,ba zata iya dauka ba.

Da kallo duka suka bita,kafin samir din ya fara takawa shima yana bin hanyar da kaltum din tabi a yanzun

“Ina sauri ne…..idan na dawo ma tattauna” ya fada yana dan qara speed nashi.

Haka kawai yaji hankalinsa ya dauko ga fitarta,har ya nufi motarsa ya bude sai ya mayar ya rufe,ya dawo zuwa cikin gidan a nutse,bayan ya jefa hannayensa duka a aljihun wandonsa.

Tsaye ya hangeta gaban qaramar bishiyar ayaba dake gidan,baya ganin fuskarta amma yana iya hangen bayanta,baiyi magana ba yaci gaba da takawa,yasan ba zataji takunsa ba,saboda grass carpet ne lallausa shimfide a wajen.

Dab da bayanta ya tsaya
“Girkinki na can yana jiranki…..karki makara” ya fada cikin voice dinsa,ba shakka tayi mamakin zuwansa inda take,hakan yasa gabanta faduwa,a hankali cikin dabara ta fara qoqarin daidaita mood na fuskarta

“Ok to” ta amsa masa,sannan ta tsaya na wasu mintuna da take qiyasta cewa ya tafi daga wajen,saita juyo da confidence dinta,abinda yasa goshinta ya daki qirjinsa kenan,sai taja baya da sauri tana furta
“Otchhh…..” Tana dan mulmula wajen,bawai don taji xafi ba,a’ah,ta fada ne kawai sabo batason yaga yanayin da fuskarta ke ciki.

Maimakon yadda ta zata,zai mata sannu ne ya tafi,sai taga ya sake matsowa da dan hanzari,yana son kamo fuskarta don ganin inda ta buge din yana fadin

“Oh….sorry” qememe taqi bashi dama,sai tayi saurin cewa

“Ba wani xafi bane me yawa…..”
“Ok….let me see” kafin ta qara yunqurin yin wani abu harya dago fuskar tata,ta hanyar kamo habarta,cikin second guda qwayar idanunsu suka manne waje daya.

Kamar wani magnet ke jansu haka kowannensu yakeji,cikinsu babu wanda ya iya janye idanunsa daga cikin na dan uwansa,wasu abubuwa yake karanta masu yawa tattare da ita,duk yadda kaltum taso tayi hakan kuwa amma abun ya gagareta,har sai daya sakar mata fuskar don kansa cikin sanyin jiki ya ja da baya yana cewa

“Lokaci yana tafiya” bata iya motsawa a wajen ba har ya bacewa ganinta,saita samu kanta da murguda baki,abinda ba al’adarta bace,yadda ya kashe mata duk wata laka ta jikinta bata jin zata iya ci gaba da aikin,amma kuma ta gefe daya har yanzu idanuwanta na ganinsa tsaye tare da jauhar…..anya a yadda takeji a zuciyarta kuwa zata iya jurar ganinsu a hakan?,wai me ma yasa takejin wannan zafin ne?,bata sani ba itace amsar,sai tana matattun qafafunta ta nufi hanyar gidan.

Tana shiga ta taras tuni bibi ta kusa kammala aikin,ta dubi kaltum din cikin fara’a
“Tunda naga wannan aikin nasan ke kika fara shi” saita maida mata da murmushi,ta samu waje ta zauna suna gaisawa,don bata jin zata iya ci gaba da aikin.

Duk inda bibi ta gifta binta kaltum take da idanu,tana wassafa ta tadda zata iya sanarwa da bibin cewa hajiya raihananta tana raye?,amma kuma wannan shine dai dai lokacin daya kamata ace ta sanar mata din,don haka ta miqe a hankali tabi bayan bibi,wadda ta bude backyard na kitchen din ta shiga tsinko lemon tsami.

“Kinga lemun nan kwana biyu da ba’s tabashi sun qara kyau da yawa” bibi ta fada bayan ta waiwayo tana taga kaltum a tsaye,saita qaraso kusa da bishiyar,kamar tana taya bibin duba wadanda zata cira din

“Kinsan kuwa momin samir tana raye?” A bazata maganar ta zowa bibi,har sai da dan bowl din hannunta ya subuce daga hannun nata ya fadi qasa,sa’annan a razane ta juya tana duban kaltum

“Ke ‘yar nan?,anya kuwa hankalinki daya?,kinsan kuwa abinda kike fada?,mafarki kikayi ko kuwa?,to idanma mafarkinne kiwa Allah ki yiwa ma’aiki ki shuru da bakinki ba tare da kin gayawa kowa ba”.

Idanunta dake cike da qwarin gwiwa,tare da jin cewa zata iya tunkarar komai ta dubi bibi dasu

“Kiyi magana a hankali bibi,tunda bakison kowa ya jimu,a haka duk wanda ya taho zai dauka muna tsinkan lemo ne,zan shaida miki dukkan abunda baki sani ba,amma tabbas momin ya samir tana raye” da qyar bibi ta tattaro nutsuwarta,ta durqusa ta dauko bowl din,ta riqeshi a hannunta kamar yadda yake a dazun.

A nutse kaltum ta bayyana bibi dukkan wani abu da bata sani ba,saiga bibin taja da baya tayi zaman drishan a qasa tana ruwan hawaye,kafin ta zame bowl din daga cinyarta ta sulale goshinta zuwa qasa tayi sujjada,ta dago tana sake sakin kuka tare da kiran sunan Allah cikin girmamawa hamdala da kuma hailala,sai kuma ta taso ta rungume kaltum a jikinta gaba daya

“Tabbas alheri ce ke,ba shakka Allah ne ya jefo dake rayuwarmu gaba daya,don ki fitar damu daga duhu izuwa haske,na fiki shekaru,na fiki sanin duniya da gogewa,amma an sakamin waigin da bazan taba iya tasiri ba,sai gashi ke da qananun shekarunki sha takwas kinyi aikin da babbar mace ta kasa,tabbas ba shakka dukkan wani tsoro ya qare,tunda har muna da tabbacin hajiya raihana na raye….lokaci yayi da jidda zata kwashi kashinta a hannu,zata kuma girbi abinda ta shuka”

“Shine abinda nake tunani,ya kamata ta fito,ya kamata ta huta,ya kamata taga danta da aka rabata dashi tun bai mallaki hankalin kansa ba” kaltum ta fada cike da damuwa tana duban fuskar bibi,bibi data fada nazari……..

Bakinsa dauke da sallama ya tura qofar dakin asibitin, professor rashid ya daga kansa yana amsa sallamar gudan dan nasa,fuskarsa ta wadata sosai da murmushi da ganin samir din,abinda daga shi har samir din suka manta yaushe rabonsu da ganin hakan.

Ta wani gefan shima samir din zuciyarsa fes take,cike kuma da farincikin ganin daddyn nasa zaune sosai,mutumin da suka fara debe tsammani da samuwar rayuwarsa,sai gashi a zaune tangargar,saidai yanayi da zai nuna maka cewa lallai yayi jinya,da kuma saran ciwuka qananu dake qafarsa da hannunsa.

Kai tsaye ya isa gaban daddyn,ya fara gaidashi yana tambayarsa jikin nasa,tare da dudduba ciwukan jikinsa

“Da sauqi sosai samir…..Allah yayi maka albarka” daga kansa yayi ya dubi daddyn kafin ya amsa,tunda ya farfado yake sanya masa albarkar da baisan ainihin meye ya kawota ba,abar daya jima rabon da ya jita daga bakin mahaifin nasa

“Kana mamaki ko samir?” Daddyn ya fada da wata karyayyar murya,wadda zata jefa tausayi a zuciyar duk mutumin da ya jita,kasa amsa masa shima yayi,sai tunani da lalube da zuciyar samir din ta tafi….laluben meye haka yaketa karya qwarin gwiwa da jarumatar mahaifin nasa?,kamar yasan tunanin da yakeyi sai yace dashi

“Hadamin ruwan shayi ka kawomin,kazo ka zauna muyi magana” bai musa ba,ya qarasa inda aka kammale duk wani kayan breakfast,tamkar a gida,duk kuma aikin asibitin ne,asibiti ne babba me tsadar gaske,suna da me jinyar patient,sannan duk wani abu da mara lpy xai buqata naci da sha su suke hidimar yi,saidai duk cikin kudinka,hakan ya sanya duk wanda zaka gani cikin asibitin to ba shakka yaci ya sha ya tada kai ne.

“Na gode” daddyn ya fada bayan ya karba cup din da ya tabbatarwa samir din zai iya sha da kansa,samir din na zaune har ya kammala,ya karba cup din ya bashi ruwa

“Sai zuwa anjima,zauna Muhammad” yayi kiransa da sunan da bazai iya tuna when last da yaji ya kirashi dashi din ba

” Da farko abunda zan fara cewa shine….ka yafemin abisa mummunar fahimta dana dinga yi maka tsahon rayuwata,bahagon kallo…..da kuma kallon da nake maka a matsayin da mara biyayya,wanda yake sabawa dukkan wata magana ko qudurina……” Hankalin samir din ne yaji ya tashi,jin mahaifin nasa wai yana neman gafararsa,saiya matso sosai yankama hannun professor din

“Daddy… Meye ya kawo wannan maganar?” Wani busasen murmushi daddyn ya yayi

“Samir….na dade ina jin haushi da takaicinka cikin raina,na dade ina tuhumar kaina ya akayi na haifeka,na dade ina maka kallon bijirarre,ban taba tsaiwa nayi dogon nazari akan hakan ba…..ashe duk abinda kake yi samir baka taba saukeni daga matsayin uba daka daukeni,ashe abubuwa masu yawa da kakeyi kana yine saboda ka gyara sunana ….rayuwata…..da kuma duniyata…..abinda ya faru shine…..lokacin da muke kan hanyar zuwa azare nida baka driver….sakamakon babu wani jirgi da zan samu da zai tashi a ranar,tun kafin mu nausa tafiya na siyi jaridun da suka fita a ranar donsu tayani debe kewa idan muka shiga inda babu service…….katsam ina tsaka da duba jaridun…..saina fara cikin karo da wasu ayyuka,masallatai,makarantu,asibitoci da hanyoyi da akayi a qauyuka masu tarin yawa…..wanda kowanne dauke yake da cikakken sunana, professor rashid azare,wanda kowa yasan duk wanda aka kira da wannan sunan wa ake nufi……nayi mamaki kamar yadda na shiga doubting din waye yake aiwatar da wannana ayyukan da sunana?,daga qarshe sai naga hotunanki a matsayin wanda yake zuwa dukka wadan nan qauyuka da kwangilar aikin…..ya kuma ce daga waje na aka aiko ayi aikin…..,mamaki ya kamani,ban tsaya sanya ba na daga waya,Allah ya taimaka da sauran network bai gama daukewa ba,na kira amiru,bai boyemin komai ba ya gayamin cewa kaine kake wannan ayyukan da sunana,dukka qauyen daka tafi kaje ne saboda kayi ire iren wannan aikin,da sunana bada sunanka ba…..a take abubuwa guda biyu suka sauko suka rufeni,har bansan sanda amiru ya gaji da dakona ba ya kashe wayar.

Abu na farko shine…..kaico da nadamar irin abubuwan da suka dinga faruwa tsayin shekaru,yadda na dinga yi maka…….,kai samir ya daga yana kallon daddyn,wani farinciki yana lullubeshi.

A hankali ta rufe katafariyar cupboard din tata ta alfarma,wadda take danqare da dukiya da kuma dukkan wani abu daya zama sirrin tane,ta waiwayo tana duban najwa dake shigowa

“Ke me yasa har abada idan zaki shiga waje ba zaki koda ‘yar sallamar nan ba,na sha gaya miki ki daina min irin wannan shigowar ko?” Dariya ta saki,ta jawo pillow din gadon xata zauna a kai,ta dora saman cinyarta sannan tace

“Sorry” kai ta gyada tana takowa zuwa inda take,batasan me ya sauya najwa din ba gaba daya a ‘yan kwanakin,ta lura akwai abinda take boye mata,take kuma nuqu nuqu akai,takardun hannunta ta aje sama madubi sannan tace

“Dama takardun wajenki zaki bani,da sarqoqinki,haka kawai jikina bai bani zamansu a gida nan ba,zan kai bank a ajjiye muku,ga na jawair duka” wani kallo najwan ta yiwa mummyn

“Haba mummy,mufa yanzu ba qananun yara bane da ba zamu iya kula da kayayyakinmu ba,mun mallaki hankalin kanmu,ya kamata a sakar mana mara muyi fitsari” galala tayi tana duban najwan,ta dade da sanin hutsuwa ce ta qarsge,wasu dabi’u da batasota dasu ba ta debo,ranta yadan baci da yadda ta gasa mata magana tana diyar cikinta,saboda haka ta fara magana cikin fada

“Duk hankalin da zakuyi ai baiki na uwarki bako?,to banason shashancin banza,ki tashi kije ki kawomin,tun kafin ranki ya baci” zumbur ta miqe tana cika tana batsewa

“Nifa mummy tsahon lokacin da na dauka ina biyayya tare da bin tsarinki….banga wata riba dana samu ba,a maimakon na zama magajiyar daddy….wadda duk inda yasa qafarsa ya cire zan maidata tawa kamar yadda kike kwadaita min….abun sai ya canza,na qare da komawa aiki a company qarqashi samir,kuma a gaban idahunki,sannan baki iya tabuka komai ba…..to na kwashe dukka takaddu suna wajen fawwaz,ya fara shirya min wasu plan,duk da basu tafi a yadda muka so ba amma na fara ganin alamun nasara” kallo mummy jidda tabi najwa dashi baki bude,gabanta yana faduwa,kada dai ace alaqar soyayyar data dade da guntuleta tsakanin najwan da fawwaz tana na ta sake dinkewa ba tare da saninta ba,ta yaya zata bar fawwaz dan hajiya shuwa ya shiga nasabarta?,kwata kwata basu kai tarin dukiya da arziqin da takewa diyoyinta fatan kasance familyn masu irin wannan dukiyar ba.

Bugu da qari kar tasan kar ne,yaya za’ayi ta tura diyarta cikin mutanen da suka san sirrinta?,kai……ta yaya ma hajiya shuwa zata yarda tabar danta ya auri najwa indai ba akwai wata manufa a qasa ba?” Cikin qarfin hali da zallan bacin rai mummy tace

“Ni mahaifiyarki kike gayawa haka?,wadda ba don naso ba da bakuzo duniyar ba,ba don naso ba kuma da baki cikin daular da kike magana akanta?,fawwaz?…..ban yanke alaqar dake tsakaninku ba?”

“Mummy muna son juna,yana sona ina sonshi,banga aibunsa baiga nawa ba,mahaifiyarsa aminiyarki ce?,me yayi saura banda musha soyayarmu hankali kwance?,gaskiya mummy saidai kiyi haquri,a wancan karon kin rabani da fawwaz….amma a wannan karon…..bazan iya rabuwa dashi ba” daga haka tayi gaba abunta.

Binta da kallo mummy tayi hankalinta a tashe,tabbas dole ta yiwa tufkar hanci,saboda matsawar tana raye ba zata taba bari fawwaz ya auri najwa ba,saita dauki wayarta da hanzari ta fara kiran wayar fawwaz din,saidai kuma cikin rashin sa’a aka gaya mata a kashe wayar take.

Cikin matuqar gajiyar jiki data ruhi ya bude qofar dakin nasa,yana jin kansa bari daya yana masa wani azababben ciwo,wunin yau dukansa wani irin wuni ne me cakude da al’amura masu tsauri a gareshi,al’amura masu ban tsoro da ban mamaki,sauqinta daya akwai dafawar amini kuma dan uwa a tare dashi…..wato amiru.

Idanunsa ya lumshe yana furzar da iska daga bakinsa gami da shaqar daddadan qamshin da sasahen nasa ke fitarwa,duk da cewa ba wani cikin nutsuwarsa yake ba,amma ya kula da gyaran da sashen nasa ya samu,kamar ka sanya baki ka lashe.

Man shafawarsa ya jawo ya fara shafawa,har ya kammala ya feshe jikinsa da turare bayan deodorant da roll-on da yake amfani dasu duka saboda dare.

Jallabiya ya xura saman gajeran wandon jikinsa,yana gaban mudubi yana sanya maballi idanunsa suka tsaya can saitin fuskar dake bayansa,zuciyarsa ta buga da kyau,ya waiwaya da sauri,zanen hoton mahaifiyarsa ya mamaye wajen.

A hankali ya dinga takawa zuwa inda hoton yake,yana cike da mamakin ta ina ya shigo dakin,yakai hannu ya dauka yana qura mata idanu,saiya sanya hannu a hankali yana shafa fuskar,zuciyarsa na qara gudu,yana jin kamar kallonsa take,kamar itace tsaye a gabansa,wata kewa wadda bai taba jin irinta ba ta rugo a guje ta rufeshi,yaji cewa inda tana raye ko tana kusa da ayanz yana a zaune a gefanta yana kallonta,suna tattauna matsalolinsu da hanyoyin da zasu magancesu,yakai bakinsa a hankai yayi kissing da dai goshinta,yana dagowa takarda ta fado saman qafafunsa,saiya duqa a hankali yana riqe da hoton ya daukota,yadan juyata kadan sannan ya bude

_su iyaye koda sun rasu akwai sauran haqqinsu a wuyanmu,yi musu addu’a,samar musu da sadaqatul jariya,kamar masallaci da sauransu,wanna kyauta ce daga UMMUKULSUM….zaka iya bamu lokacinka mu da bibi zuwa wani waje da zai sama maka farincikin da ya bace maka bat a rayuwa?…..,FATAN ALKHAIRI_

UMMUKULSUM ya maimaita sunan tare da motsawar labbansa,fuskarta ta fado masa tarwai cikin kwanya da idanu,saiya daga hoton da sauri yana kallonsa,unbelievable……ashe ta iya zane har haka?,ya manta gaba daya ya santa da zane tun fil azal…..amma…..ina ta sani da zata kaishi?,amma kuma tace ita da bibi….wanne farinciki ne da ya bace masa bat a rayuwarsa?,ya kasa fahimta,saiya koma saman sofa din dake dakin ya zauna,yana son bawa kwanyarsa hutu ko zata fahimci abinda maganganun ke nufi,saidai maimakon hutun wayarsa ce tayi qara,tsaki yaja kamar bazai daga ba,saidai tunawa da yayi ya bada muhimmin aiki yasa tilas ya miqa hannunsa da kyau har ya jawo wayar.

Wanda rasa ke raya masa dinne kuwa,ya daga wayar ya kara a kunnensa bayan yayi sallama qasa qasa,sallamar dake alamta akwai gajia tattare dashi

“Sorry sir…. Kayi haquri,sai zuwa gobe bincikenka zai kammalu,daya layin wayar akwai tsaro sosai tattare dashi,amma zuwa tsakiyar dare in sha Allah zamuyi accessing komai”

“Alright” ya amsa a taqaice

“Thank you sir” mutumin ya amsa dukansu suka ajjiye wayoyinsu.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana shafa kansa,maganganun da sukayi dazu da daddy na dawo masa,wayar da yaji bala nayi kafin faruwar hadarin bayan ya rufe fuskarsa da jaridar da yake karantawa saboda nauyi da zuciyarsa tayi saboda tausayin abubuwan daya dunga aikatawa dan nasa tsayin shekaru,yayi shuru kuma na wani lokaci wanda a wannan shurun komai ya afku

“Indai abinda kunnuwana sukaji dai dai ne…..lallai ba shakka akwai gagarumar matsala,matsalar data wuce ta accident din da nayi,lallai akwai wani babban qulli a qasa da bana fatan tabbatuwarsa”

“Allahumma la sahla illa ma ja’altuhu sahla,wa’anta taj’alil hazna iza shi’ita sahla” ya fada yana miqewa gami da zama sosai,dai dai sanda amiru ya shigo dauke da ledan da ya musu takeaway na irin abincin da yasan samir din yana son ci,saboda yace baya jin cin komai,bazai yiwu kuma ya barshi ya zauna a haka ba.

Saida amiru yayi wanka sannan ya dawo ya zauna yana bude musu takeaway din,gefe daya suna dake tattauna matsalolin dake faruwa,wanda kaf duniya su uku sukasan da wannan,shi samir sa daddy.

Amiru ya jima yana kallon takardar da kuma zanen hoton baya da samir ya gabatar masa dasu

“Ba shirme bane kuwa wannan?”kai samir ya girgiza yana zama sosai tare da fuskantar amiru

“Banajin hakan a jikina,akwai wani gagarumin abu,ta ambato bibi a ciki fa?”kai amiru ya jinjina

“Of course…..bashi da amfani jan magana,inaga…gobe kawai ku shirya,sai kuje din kamar yadda ta buqata,idan kuma buqatar mijinta take ta kasa gaya maka kai tsaye ne to?” Amiru ya qarashe da zolayar samir,wani qaramin murmushi ka gefan baki samir din ya saki,wanda har ga Allah ya ratsa har ta qasan zuciyarsa,hakanan sai yaji wani kaso mai yawa na nauyin qirjinsa ya ragu,ya lumshe idanu a hankali,saiya dinga tuna lokuttan da suka kebe tare shida ita,zuwansu a zare da sauransu,tsahon lokaci yana tuna abubuwa masu yawa a kanta

“Mutumina……ya daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaqi?” Yaji amiru daya taboshi yana fada,ya bude idanunsa da suka canza kala a hankali ya zubewa amirun su

“Ina cikin wannan cakwakiyar kana min maganar soyayya?” Dariya amirun ya saki yana gyara zamansa,duk da shima ransa ba dadi,amma ya tabbatar samir ya fishi shiga cikin matsala da kuma damuwa

“Bakasan cewa shi feelings ko a wanne irin mood kake ba yana iya motsawa?,baka ga idanunka bane a yanzu, beside ma ita mata kowanne irin jarrabawa ka shiga,suna da power din sama maka nutsuwa da daidaito na hankalinka,dukkan wani tashin hankali da zaka shiga……idan kana tsakiyar qirjinsu…..kana samun wani irin peace, they are blessing from God……shi yasa in sha Allah bazan kai qarshen shekarar nan ba aure ba,na gaji da rayuwar gaurantaka” maida idanunsa yayi kawai ya rufe yana maimaita kalaman amiru cikin kwanyarsa,tabbas dukka maganganunsa haka suke,shi din shaida ne,kwana daya tak….lokaci daya tak da sukayi da ita a wanca guests house din,yayi wani bacci da bai taba jin nutsatsen bacci irinsa ba.

“Mr tunani…..jauhar na kiranka fa”

“Please switch the phone,i need a rest” ya gayawa amirun ba tare daya bude idanuwan nasa ba,amirun yasan gaskiya ya fada,don haka ya kashe wayar kamar yadda ya buqata.

*_COMMENTS DINKU NADA QAYATARWA,JAZAKUMULLAH 👏🏽👏🏽_*

*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾100

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button