Dabi’ar Zuciya 63
63
A bakin qofa ta taras dashi a tsaye kamar wanda aka bawa gadin qofar,cikin wasu Cotton kayan bacci na maza ash colour,qamshinsa ya budade ko ina,iskar damina na baza qamshin daga hagu zuwa dama,fuskarsa tayi wani fresh,duk da qarancin hasken dake sararin samaniya,sakamakon kwantaccen hadarin dake linqaya a saman,wanda yake bada iska me sanyi,me kuma cakude da qamshin qasa.
Birki taja ta tsaya saboda yadda ya cinye qofar gaba daya babu hanyar da zata raba ta wuce,idan ta matsa kuma sai ta raba din to tabbas sai ta fara masauki a jikinsa kafin ta samu wucewar.
Idanu ya zuba mata, Adams apple dinsa na sama da qasa kamar me hadiyar wani abu,daga nan inda yake tsayen yana iya shaqar daddadan qamshinta dake sake ta’azzara yanayin da yakeji dangane da ita a jikinsa.
A tausashe ya cafkota ya kuma yi mata kyakkyawan masauki a qirjinsa,ya zagaye hannyensa gaba daya ta bayanta,da wata iriyar murya dake shaking yace
“na gode da jan aji…..amma ki sani…..bazan iya jura ba,bazan iya jurar jan ajinki ba,rauni na a kanki yawa ne dashi” ya qarashe maganar yana cusa kansa tsakanin wuyanta zuwa qirjinta,da wani irin zafin nama,wanda cikin sakanni ‘yan kadan ya birkice ya kuma birkitata itama,tsaiwa ta gagaresu gaba dayansu,saiya tallafeta ya wuce da ita kai tsaye zuwa bedroom dinsa.
Kyakkyawa masauki yayi mata kan tattausar katifarsa,cike da wani irin shauqin so da qauna,wadda ta bayyana kanta muraran har cikin idanuwansu.
Da zafi zafi ya shiga aika mata da saqonni,kamar zai cinyeta danya,zafafan kisses masu badda hankalin masoyi,daga dama ya maidata hagu,daga hagu ya maidata dama,tun yana yi da ragowar hankalinsa cikin jikinsa…..har ragamar hankalin ta qwace daga hannunsa gaba daya,yaji a ranar a wannan daren yanaso qetare shingen da yake tsayawa a baya.
Ta bangaren kaltum tun tana iya karbar saqonnin da yake aikata mata har suka qetare saninta da hankalinta,jiki da zuciyarta suka fara gaya mata lallai muhimmin al’amari ne zai faru,kafatanin jikinta ya fara rawa sanda hannunsa ya tsallake boarder,tayi caraf ta riqeshi,hawaye ya soma ambaliya saman fuskarta.
Cak ya tsaya,ya sanya hannayensa duka ya tallafo kanta,yana kallon fuskarta data cakude da hawaye,gashin kanta kuma ya barbazu saman fuskar,sai ya saka hannunsa guda daya ya yaye mata gashin gefe,abinda ya bashi damar ganin sukarta da kyau.
Da wata iriyar kwantacciyar murya me cike da nauyi da kuma taushi,cikin kuma rawar muryar kamar wanda xai saki kuka yace mata
“Dukka jiki da xuciyata sunyi amanna dake……..cikin qanqanin lokaci kuma sun cika sun tumbatsa da soyayyarki,ban taba kawowa soyayya me zafi irin wannan tana yiwa mutum kamu kamar haka ba sai a kaina……..” Sai yadan rage nauyin da ya aza mata,ya miqe a mugun kasalance ya zauna sosai bayan ya juya mata baya
“Duk yadda nakai ga dokanta na kasance tare dake…..na maishemu abu daya,bazan iya aikata komai ba saida gamsuwarki……,zan baki lokaci ki nutsu har cikin zuciyarki dani” saiya fara jan jikinsa yana saukowa daga saman gadon yana layi ya nufi bandaki,ta bishi da kallo a sace,tana jin wata soyayyarsa na tsarga mata,dama haka yake?,saita cusa kanta cikin pillow cike da kunya.
Duk da cewa haqarsa bai cimma ruwa ba,amma a ranar yayi yadda yaga dama,ta luguiguita sosai a hannunsa,wannan din ya rage masa zafi fiye da kima,saidai ita din ta rabauta da ciwon mara,wanda sai daga bisani ta samu relief,ta kuma gudu daki yana fita sallar asuba.
A abun salla ta sake samun jawahir,suna hada idanu tayi turus,sabida bata zaci a dakin zata kwana ba,ga kayan jikinta gaba daya a yamutse,wanda duk wanda ya kalla ya tabbatar akwai ayar tambaya akai.
Dauke kai jawahir din tayi,tayi kamar bata gani ba,sum sum sum ta shige bandaki,ta sakarwa kanta shower bayan ta daidaita duminsa.
Ζarfe biyu na rana dai dai motar da suke ciki ita da samir,da kuma spare wadda tayi musu rakiya ta tsaya cikin garin dinya,qofar gidan malam amadu.
A nutse ta bude qofar ta tura,sai kuma ta tsaya turus tana kallon qofar gidan nasu,maida kallonta tayi ga gidajen dae hagunsu da damansu,duk sune dai gidajen data sani,duk da su din ma kamaninsu sun jirkice da shafen suminta da kuma fenti daya haska gidajen gaba daya.
Waiwayowa tayi ga samir,sai taga ita ya zubawa idanu gaba daya,yana jingine da bayansa a owners corner,tun asubahin jiya ya zama wani me sanyi maras laka a jikinsa,duk motsin da xatayi idanuwansa na kanta
“Anya su ummanmu basu tashi ba?” Tayi maganar cikin taraddadi,saboda batasan amsar da zata samu ba.
Batasan ya iso inda take ba,sai maganarsa taji cikin kunnenta
“Ummanmu tana ciki,tana dakon isowarki…..maza ki shiga ki sameta…..amma ina nan ina jiranki kizo muyi sallama,kada a manta dani” wani qawataccen murmushi ya subuce mata,ta ritsashi da idanu tana son karantar wani abu tattare dashi,zuciyarta na gaya mata yayi halin da ya saba duk yadda akayi,sai taji gaba daya zumudi ya cikata,don haka cikin wani irin hanzari…..ko duba da high hill din dake qafarta ba ta zuro qafafunta waje.
Dai dai sanda ta doshi qofar gidan nasu wata mata dauke da qullin kaya saman kanta tazo zata gifta kaltum din,babu abinda yake tashi a jikinta illa tsami hade da wari,sai maganganu take kai kace wata zararriya ce,fuu ta wuce ta gefan kaltum din,bisa dukkan alamu bata gane wace ba.
Daukin shiga gidan ya sanya bata tsaya wani dogon tunani akan wasilan ba tayi cikin gidan,daga ciki ta tsaya tana shawarar inda zata shiga,saboda gidan ya zama kala biyu,daya sashen gini ne na musamman akayi kai bazakace a qauyen bane,daya sashen kuma an masa kwaskwarima,babu laifi…..
Yaran da suka fito daga ainihin sashensu riqe da robar man quli suka bita da kallo,ta ganesu dukansu,saidai suma da alama basu shaidata ba
“Nan ne wajen umman bilalu?” Ta tambayesu
“Eh nan ne” suka hada baki wajen bata amsa,kana suka bita da kallo sanda take wucewa sashen nasu a gaggauce.
Tana tsaye ta bawa qofa baya,sanye da atamfa ABC ja me kwalliyar korayen ganye,idan ka duba wajen qafafunta da hannayenta da kake iya ganowa ta baya lalle ne ja shar,hakanan jelar gashinta ta nuna sabintar kitso dan hannu biyu dake kanta.
Muryarta kawai taji ta tabbatar ummanta ce,magana take da wata dake daya daga cikin dakunan da aka qawata da window da qofofin zamani,batasan dawa take magana ba,amma muryarta kawai zata gaya maka cikin farinciki da walwala take.
Da sauri ta matsa ta rungumeta ta baya sannan ta saki kuka tana dora kanta saman kafadarta,qawataccen murmushi ya subuce daga fuskar umman
“Alhamdulillah” ta ambata tun kafin ta waiwayo ga diyar tata,kaltum dinta,wadda ta kwashe watanni da kwanaki masu tsaho bata bacci,ta kwashe lokaci me tsaho tana begen ganinta….tana taraddadin a wanne hali take ciki?,wacce rayuwa take?,a hannun wa ta fada?.
Juyowa tayi ta rungumeta sosai cikin jikinta itama,muryarta na bayyana tsantsar farinciki da take ciki
“Ahaf…..daga shigowa kuma sai kuka?” Tayi mata maganar itama tana qoqarin hana kanta kukan dakeson qwace mata
“Ummanmu….ummanmu” ta tsinkayi muryar habiba daga cikin daki,da hanzari kaltum ta daga kafadar umman,saidai kuma tana riqe da hannayenta da qarfi ta qwalla sunan
“Habi ta” kan kace kwabo saiga habiban tsaye a qofar daki,aka shiga kallon kallo,kafin dukkaninsu su barke da kuka suka nufi juna suka rungume.
“Wai lafiya naketa jin koke koke?” Muryar inna laure ta ratsa kunnuwansu,wanda dama kusan yanzu aikinta kenan,bata iya zama,ko yaya taji wani motsi daga sashen,tun daga sanda ta bude idanu taga sauyin rayuwa ya fara saukarwa zuwairan,shikenan bata iya wani cikakken bacci da idanu biyu,kullum cikin fargaba take,musamman da asiya ta fara haduwa da gwagwarmayar rayuwa daga gidan alhajin data aura,yau fari gobe tsumma,kullum cikin nuqu nuqu da qoqarin boye halin da suke ciki take.
“Ah….baquwa kukayi ne?……tofa….ikon Allah,wannan fuskar kamar na taba ganinta” inna lauren ta fada bayan ta zagayo saitin fuskar kaltum
“Eh,’yarku ce kaltume,tazo ganin gida gaidamu” ummanmu ta fada,dai dai sanda yara suka fara shigowa da kaya suna jibgewa a tsakar gidan daga gefe daya
“Kal wa?….kai haba zuwaira….ina kattume zata samu kyau da zatin wannan?,kigs fuska luwai luwai,jiki lukui lukui….jiki sai tahin qanhi yake…..ke bakiga kayan jikinta bama,anya kuwa zuwaira akwai Allah a ranki?” Inna laure ta fada tana kama baki,rabi da rabin hankalinta kuma akan kayan da yaran ke jibgewa,wanda sun fara cinye bakin qofar gaba daya.
Murmushin yadda hassada ta fito sosai muraran saman fuskar inna lauren ummanmu tayi
“Kayya,amma abu baiyi dadi ba da uwa ta kasa gane diyarta,matsa dai da kyau ki sake dubawa” koda inna lauren ta matsa ta tabbatar kaltum din ce,saita juya sumi sumi ta bace daga sashen,yayin da kaltum ta bita da kallon mamaki,gaba daya ta lalace,tsufa ya keto mata,idan suka jera da ummanmu sai ka dauka umma diyar inna laure ce.
Falon da aka qawata kuma aka kira da falon ummanta take bi da kallo,sanda habiba ke feshe shi da freshener samir zai shigo,qamshin freshener din ya cakude da qamshin sabon gini da kuma sabon fenti,ita har yanzu gani take idanunta nayi mata gizo ne,idan ta kalli qawataccen gidan da sunan gidan mahaifanta,kamar ba’a karkarar ba,ko ina tiles da tiles,ga ruwan famfo ga wutar solar inverter,fankoki kota ina?,fakadeden tsakar gida da yasha tiles aka qawatashi da shuke shuke,ga yalwataccen kitchen irin na zamani,ga dan qaramin gas,abun kamar a mafarki?,bayan maka makan dakuna dake tsakar gidan,duk da bata bude ba batasan meye a ciki ba,kai koda a cikin garin ba kowa zai dace da irin wannan gidan ba.
Har samir ya shigo suka gama gaisawa da ummansu tana cikin duniyar tunanin wanda ya yiwa rayuwar ummansu wannan baban aikin,umman tasu ta qara qiba tayi wani shar da ita,idan ta hada umman data bari lokacin aurenta data yanzu sai kace uwace da ‘yarta,babu wani gami ko kadan.
Bayan sun gama gaisawa umman ta qwalawa muntasir da shigowarsa gidan kenan kira,murna da mamakin ganin kaltum din ya cikashi,ta bashi key
“Ka bude masa dakin can hanyar soro,yadan huta kafin su wuce,ai baya juyawa ba daga zuwansu” ummanmu ta fada bayan ta yiwa samir magana ya dakata da zancan tafiya tun yanzu,muntasir ya karbi muqullin cikin murna ya fice.
Nannauyar ajiyar zuciya kaltum ta saki,tabi habi da kallo wadda ke ajjiye fulasan abinci masu kyau a gabanta da batasan inda suka samo fulasai masu kyau haka ba,habi din tata ta cika ta zama babbar mace,tayi qiba sosai,kamar ba ‘yqr ficikar habi din data tafi ta bari ba,tayi adonta cikin wani lace mai kyau,da alama tana samun kulawa daga wajen mijinta yadda ya kamata.
“Ina dana ko ‘yata da ban sansu ba?” Kaltum ta jefawa habi tambayar,saita dago kai,suka hada idanu,suka sakarwa juna murmushin dake cike da qauna irin ta ‘yan uwantaka
“Yaya kaltume,ki fara sallamar dan aljannar mijinki din nan tukunna,yau kwanan hira zamuyi” saita dan dubeta
“Ki baro yusufan a gida?”
“Baya nan ma,ya tafi Lagos,kuma koda ya nan shi da kansa zaice nazo na kwana din”
“Lallai yusufa,likkafa ce taci gaba haka?”
“Duk ya sanadin mijinki ne ai,arziqinku muke ci” ta amsawa kaltum,duk da maganar ta daure mata kai amma haka ta duqa ta dauki kwandon,sannan ta fice tabar su ummanmu suna binta da kallo,kowa zuciyarsa fes qal,suna mamakin yadda kaltumen ta sauya gaba daya,kai baka ce ita bace.
Zata fita taci karo da wata mata na shigowa,idanu jage jage da hawaye tana sharbar qwalla,sai taja da baya don bata hanya,saboda ganinta riqe da yaro ga kaya ga kuma tsohon ciki.
Data sake dubawa sai taga ashe asiya ce,mamaki sosai ya kasheta,asiyan ce haka?,yarkace yarkace cikin tsumma?,itama asiyan idanu ta zuba mata,amma sam zuciyarta taqi yarda cewa kaltum din ce,don haka ta gwada kiran sunanta,jin ta amsa saita zabura,sannan da sauri ta qara gaba zuwa sashensu tana waigenta tare da qoqarin boye hawayenta.
Mamaki ya cikata sanda take ajjiye kayan abincin data jiyo muryar samir a qofar gidan tare da muryoyin jama’a,ko data leqa,sai taga qofar gidan nasu cike yake da al’umma,samir na cikinsu,daga gefe daya kuma wasu kaya ne aka sauke,da alamu kuma wannan al’ummar za’a rabawa,don kowa ka kalli fuskarsa cike yake da farinciki.
Idaunta ta maida kan samir,ta zuba mishi idanu tana masa kallon qurilla,irin kallon da bata iya masa matuqar yana tsaye a waje gata gashi,yadda yake ta haba haba da mutanen kawai zai alamta maka he’s so simple man,bashi da qyamata,hakanan bai dauki duniya da fadi ba,kuma yadda suke gaisawan kadai xai gaya maka sabo sukayi,ba iya na yau ba kadai.
Ci gaba tayi da morewa kallonsa,duk inda ya matsa idanunta suna biye dashi,daga bisani ma saita zauna saman wata ‘yar kujera stool dab da window din tana bibiyar duka motsinsa da idanunta,murmushi na qwace mata lokaci zuwa lokaci,har zuwa sanda taga sun fara rabon kayan,yana miqa wani abu a envelope da tafi kyautata zaton kudi ne,ana dorawa kowa saman kayan.
Komai da yakeyi yana yinsa ne cikin nutsuwa,cikar haiba da kamala,zuciyarta ta dinga qara gudu saboda yadda yake sake burgeta da shiga ranta,ganin bai qyamaci al’ummarta ba.
Hayaniya ce ta tashi daga can baya,harta qaraso inda samir yake tsaye,da alama kuma duka akan rabon abincin ne,matar da suketa tarewa ta qaraso,data duba da kyau sai taga wasilarta ce data shige dazu,wasilar da ayanzu tafi kama da mahaukaciya tuburan.
Idanu ta zuba mata daga inda take tsaye,mamakin abinda ya samu wasilan takeyi data sauya haka gaba daya,saika dauka kakar kaltum ce bawai sa’anni suke ba,banda ma tayi mata farin sani ba zata shaidata ba,tana tsaye taga samir din ya sanya an loda mata abincin me yawa ya bada umarnin a daukar mata,sannan ya fidda envelope din guda uku ya miqa mata,tana hangen sanda ta durqusa har qasa tana godiya,yayi mata alama da hannu ta tashi,yayi taku uku ya koma cikin mutanen yana ci gaba da kula da yadda ake gabatar da rabon.
Kamar wanda aka gayawa ko kuma wanda jikinsa ya bashi,saiya waiwaya saitin window din sanda yake qoqarin jingina da itaciyar dake wajen,karaf idanunsu suka hadu,sai taja baya da wani mugun sauri cikin faduwar gaba.
Sarai ya ganta,sai ya saki wani miskilin murmushi,ya kirayi umar daga inda yake,ya danyi magana dashi na wasu mintuna sannan ya juya ya fara takawa zuwa cikin gidan.
Da sauri sauri tayi hanyar fita,saidai yana sako kai itama tana sanyo nata,abinda ya basu damar yin karo kenan da juna,sai yaci gaba da tafiya zuwa ciki,yana korata da baya a baya zuwa cikin dakin,kana ya sanya qafarsa daya ya maida qofar ta bame,bai barta ba har sai da suka dagana da bangon dakin,takai qarshe,sai ya sanya hannunsa daya ya dafe bangon dakin,idanunsa akan kyakkyawar fuskarta,bugun zuciyarta ya qaru saboda yadda take iya jin saukar numfashinsa saman fuskarta
“Meye hukuncin mutumin daka kama yana satar kallonka?” Kunya da nauyinsa suka rugo suka dabaibayeta,ta kasa magana,ganin bata tanka ba sai ya qara matsarta sosai,tayi gefe zata goce,ya tarota ta hanyar sanya daya hannun nasa ya sake dafe bangon,ya sakata a tsakiya kenan
“Babu inda zaki motsa daga nan,saikin bani amsa” a dan tsorace ta kalleshi,tana iya jiyo hayaniyar mutane har yanzu daga waje,kada wani ya shigo dakin ya samesu a haka
“Ni ba kai nake kallo ba” ya saki da qaramin murmushin gefen baki,yana tuna wasu abubuwa da suka shude,kaltum me tsiwa,kaltum mara tsoro,gata yau gaba daya ta sukurkuce tsakanin hannayensa,tun baikai ga tabata bama
“To wa kike kalla idan bani ba?”
“Yan garinmu” tayi hanzarin bashi amsa,waiko hakan zaisa ya kubuta,fuska ya bata sosai
“Wasu mazan kike kallo ma ba mijinki ba?…..lallai sai na hukuntaki” yana kaiwa nan ya tallafo kanta,ya kuma hade bakinsu waje guda.
Wani salon tsotsa yakewa lips dinta,har sai da sukaso sakwarkwacewa gaba dayansu,dama ga sauran dafin jiya da bai gama barin jikinsu ba.
Baya ya koma a hankali ya zauna dabas a qasa,banda cikin tahowar kaltum din akwai umarnin momma da baisan hikimarta na yin hakan ba,da babu shakka bazai iya tafiya ya barta ba,bazai iya nesa da itaba na wasu kwanaki.
Sai da nutsuwarsu ta daidaita sannan ya karbi zuba abincin da kansa,yace ta zauna gabansa kawai yayita kallonta ya wadatar,ya fuskanci zallar soyayyarsa ke ci mata zuciya,amma batasan ya zata sake dashi ba,don haka bai barta ba a sannan sai daya samo kanta da kaso sittin cikin dari,yana cin abincin da bata tsammaci xaici ba yana janta da hira,har tazo ta iya maida masa.
Sake kallon agogon hannunsa yayi,qarfe uku na rana,a qalla sun shafe kusan minti ashirin xaune cikin motar kawai yana kallonta,bayan ta fito ne kawai da sunan yi masa rakiya.
Numfashi ya sake ja yana dubanta,sai ya kamo hannuwanta zuwa cikin nashi yana murxa tafin hannun nata,abinda yasa ta dunqule jikinta waje guda,kwanakin nan gaba daya wani dafi yake saukarwa jikinta,wanda mutum bai isa ya kauce masa ba.
“Suna jiranka fa,kamar sun gaji” tayi jarumtar fada sanda take hango tsaiwarsu murtala ta baqin gilashin motar da suke ciki ita da sarakin
“Zan tafi…..amma,sai kinyimun abu daya” wannan karon samun kanta tayi da sanya qwayar idanunta cikin nasa,har cikin jiki da jininta itama cikin wadan nan daqiqun takejin cewa zatayi kewarsa,kamar kada ta barshi ya tafi
“Ya salam….. what a beautiful eyes….. kada ki zubamin dafin da zan kasa tafiya na barki mana” tattausan murmushi ma cakude da kunya ya sauka saman fuska da lebanta,sai ta sadda kanta,amma kafin ta gama saukarwar ya kama fuskarta ya dago zuwa gareshi
“Nooo……ki barni na kalla na mitunan da suka ragemin na tafi” fararen idanun nata ta zaro
“Mintuna kuma?”
“Yes….so kike na tafi ko?” Kasa amsa masa tayi,saita maye gurbin amsar da murmushi
“Is okay,nasan kinyi missing ummanmu…..but before na tafin, give me a kiss” ya fada yana miqa mata tausasan labbunansa sirara masu taushi da sanyi” sake fito da idanun nata tayi waje tana girgiza kai alamun a’ah,sai shima ya fitar mata da nasa idanun
“Just do it….idan ba haka ba kuwa,zamuyita zama anan”kafin ya rufe bakinsa tayi saurin dora nata bakin ta manna masa kiss din mai tsaho kuwa,wani numfashi mai nauyi yaja,ya koma da baya ya zube cikin kujerar yana shafa qirjinsa,bata ankara ba yasa hannunsa daya ya fuzgota cikin jikin nasa,tsahon wasu mintuna har sai da nutsuwarsa ta daidaita.
Hannunta ya kamo ya saka mata sabbin kudi masu kauri yana cewa
“Wannan dai kyautace daga mijinki,don naga alama fada kike da sabbin kudi…… don’t say no” dariya da kunya suka cikata,cike da girmamawa tayi masa godiya,ya fito da kansa ya bude mata qofar motar,yana tsaye yana binta da kallo har sai data shige gidan,sannan a sanyaye ya kada kai ya koma cikin motar,su umar dake tsaye gefe suna gulmar kallon da yake binta dashi,suna masa tsiya da dariyar ba sabon ba,suka shige motar
“Ku kuka da kanku akan gulmata,ku kuma dauke idanunka daga kan matata,if not, I’ll definitely deal with you” saraki ya fada fuskarsa a washe,saidai kuma akwai alamun da zai nuna maka shi dinne boss.
“Sorry sir” suka fada cike da mamakin yadda akayi ya fahimci gulmarsa suke,sai kowa ya shiga taitayinsa,suka tada motocin.
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*_DA ZAFINSU_*
*_A TSARE SUKE_*
*_SUN TANADESU_*
*_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA’AWA_*
*_ΖAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_*
*_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_*
*_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_*
_WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_
08184017082
_MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_
09134848107
*_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA…..MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_*