Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 30

Sponsored Links

 

 

 

 

 

Episode 3️⃣0️⃣*

Gudu take kamar zata tashi sama har tsallake stari uku take ta tana na huɗu batare da ta sani ba, a dai dai tsakiyar palon kasa tayi karo da Aryan baya baya tayi zata faɗi, yayi sauri rikota yana faɗin “ai daman na san za’ayi hakan shiyasa na biyo bayan ki me ke faruwa? Bai gama rufe baki ha yaga Bgs na saukowa a guje sai wani huchi yake, a sukwane ya saki diyana yace “ki kudu sister kar ki tsaya ko ina sai bayan Abba, ai diyana bata jira taji me Aryan zai cheba dan yana sakin ta ta kwasa a ɗari tayi waje.

Azuchiye Bgs ya sauko ya nufi hanyar fita da sauri Aryan yasha gaban sa yana faɗin haba bro lfy? Hannu yasa ya hankaɗe Aryan gefe ya nufi kofar fita, A zafafe Aryan ya saƙe tare masa gaba, chikin tsawa Bgs yace “Aryan ka bani hanya tun ban illataka ba “haba Bgs pls kayi hakuri mu koma chiki, wani naushi Bgs ya kai wa, Aryan a fiska, da sauri Aryan ya tare yana faɗin “aa bro ba dai yanzu ba gaskiya, a zuchiye Bgs yasa ɗayan hannu sa ya damki wuyar Aryan ya ɗa gashi sama yayi wurgi dashi gefe guda, ya juya ya nufi hanyar fita da gudu Haidar da Umar daƙe tsaye a bakin kofar palon wadda kusan tare daman suka shigo da Aryan, suka juya suka bar part ɗin gaba ɗaya.
Tattaro dukka sauran karfin sa Aryan yayi ya miƙe ya saƙe tarewa Bgs gaba, “Aryan zan illata wlh idan baka barni na bugi yarinyar nan ba “haka na keso daman kafara illatani kafin ka illata ta, dun kule hannu Bgs yayi ya sake kai wa Aryan bugu a firji wadda sai da yasa Aryan tan gal tan gal kamar zai faɗi, amma abun ku da soja, chikin zafin nama ya kame jikinsa chikin bachin rai ya kaiwa Bgs duka a wuya da karfi, a fusache Bgs ya ɗaga sama yayi wurgi dashi a tsakiyar palon chikin zafin nama ya nufi hanyar fita..

…har ya kai bakin kofar palon zai fita sai kuma ya ja birki da sauri ya juyo, gani ko motsi Aryan ba yayine yasa Bgs kariso wa wajen daya ke kwanche da sauri,
Duƙawa yayi yasa hannun sa a dai dai sai tin kofar hanchin Aryan yana faɗin “my blood kar kamin hakan, hannu Aryan yasa ya chapko hannun Bgs tare da waro ash eyes nashi kan face ɗin Bgs ɗin, dogon tsaki Bgs yana kafin yace “me hakan ɗin? ” To ai bani da wani zaɓi na da katar da kai ne sai hakan ɗin, miƙewa Bgs yayi san man ya ɗuƙa ya ɗauki Aryan chak ya saɓasa a kafaɗar sa yanufi stair ɗin dashi
“Amma Aryan baka kyau ta min ba “me kuma na maka? ” Da ka hanani bugun yarinyar nan mana “au to kai daman so kake na barka kayita bugun yaya mutane, kuma kasan idan kache zaka bugi yarinyar nan a yadda kake chikin fushin nan, tofa zaka iya kasheta “to ta mutu mana menene amfanin ta daman? ai inaga wlh watara na idan ban kashe enamiece nawa ba kai zaka mutu a shiga faɗar da ba ruwan ka, tsaki Aryan yaza dai dai lokachin Bgs ke kwatar dashi kan katafaren gadon sa

“Wlh Bgs baka da kirki ko kaɗan yanzu gashi ga bugi yar sarki Zaria tana asibiti, jiya naje hospital ɗin dan naga ya jikin nata saboda baban ta ya ɗau zafi dayawa, kar yaga ko ɗaya daga chikin mu bai jeba ya duba taba, Allah ya rinyar nan ko motsi batayi kamar ba rai a jikinta amma a hakan kuma yau kake so na barka kasake bugun wata ko?

“au wai dan babanta har wani zafi ya ɗauka ke nan to ya baku sanar dani ba dan shima na hukuntashi, waro ido waje Aryan yayi kafin yace “zaka iya zuwa ai yanzu ma sai ka hukun tashi, ni dalla ka bani ruwa nasha hai, Aryan ya karisa maganar chikin ɓachin rai

“Wlh Aryan ba dan ina kaunar ka ba Allah da yau inaga sai dai a kwashi gawarka ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi freij, ” zaka iya ajiye kaunar a gefe ai sai ka kashe nin Aryan ya faɗa chikin fushi, Bgs ba tare daya sake chewa komai ba ya ɗauko ruwa kawai ya dawo kan gado ya ɓalle bakin robar ya ɗago kan Aryan ya kafa masa robar a baki, sosai Aryan ya sha ruwan har sai da ya kusa shanyewa, sannan Bgs ya chire roban daga bakin shi yana faɗin “ya isa haka shan ruwan, Aryan yace “to ba kai ka min wani wawan naushi a kirji ba ai dole nasha ruwa “kaɗan ma kagani ai wlh ka chigaba da shiga faɗan da ba ruwan ka watarana sai dai a kwasheka zuwa hospital.

murmushi kaɗan Aryan yayi san nan ya yunkura ya miƙe zaune, a hankali y zuro kafarsa kasa ya miƙe tsaye “ina zakaje bro? Bgs ya tambaya yana kallon face ɗin sa, “fada zanje wajen Abba mana, “why ba zaka tsaya a nan ba “no akoi maganar da zamuyi ne mai mahimmanci “ok let’s go together, ya kai karshen maganar tare da miƙewa, atare suka fito

Dai dai wajen part na Ammi sukachi karo da su Zahra sun fito daga palon Abba.
Ganin Bgs da yaya Aryan yasa diyana ta fasa ihu ta watsa a guje ta shige ɓangaren Ammi, da gudu hiyana tabi bayan ta, su Zahra ma ba’a barsu abaya ba da gudu suka wache suka bi bayan su hiyana.

“Bgs gaskiya baka kyauta wa yanzu dan Allah dubi yadda yaran nan suke ihu da suka ganka kamar sunga dodo, wani dogon tsaki Bgs yaja kafin yace “bana son haka Aryan ka daina kawomin maganan yaran nan, “ai gaskiya na faɗa maka bro menene anfanin kasa su suna jin tsoronka, shiru Bgs yayi bai sake magana ba har suka karisa chikin fada

Misalin karfe 11 :20 Aryan ya fito daga fada ya nufi part nashi dan ya je yayi wanka yazo dai dai part na Ummi sai yaji haidar da Umar suna hira tsayuwa yayi da kyau ya kasa kunne yana jin su,

“Umar ai wlh ko baka faɗaba kowa yasan Son yarinyar nan yaya Aryan yake, bakaga yadda yake kallonta ba idan mun haɗu wajen chin abinchi,

“kai haidar kai kallo kawai ka gani ka dubafa yau saboda ita yaya Aryan yayi faɗa da yaya prince, ai mugu mugun Son ta yake, wani dariya Umar yayi kafin yace “tab aiko zamuga ya, yaya prince zai yi idan yaji lbr yaya Aryan ya faɗa soyayya dariya suka kwashe a tare har da riƙe chiki,

A fusache Aryan ya juya ya fasa shiga part nashi ya nufi part ɗin Ammi sai wani huchi yake, chikin ransa yana faɗin soyayya ni wai aa never wlh har abada.

da sallama yashiga palon bb kowa kai tsaye betroom ɗi ta ya nufa, a bakin kofa ya tsaya yayi sallama, Ammi na daga chiki ta amsa masa tare da bashi izinin shigowa, shiga yayi ya zauna saman manya manya throw pillow dake tsakiyar ɗakin
“Aryan lfy kuwa naga ranka a ɓache haka, “Ammi so nake yarinyar nan ta bar gidan nan “wace yarinyar kuma? “Wan nan yarinya dake kawomin coffee “au diyana? “eh ita ban son sake ganin ta gaskiya, yana kaiwa nan ya miƙe ya fita rai a ɓace, miƙewa Ammi tayi itama ta ɗauki alkyabban ta ta sanya ta fito ta nufi fada

Da sallama ta shiga ta karisa wajen Abba ta zauna saman kujera tana masa sannu da hutawa “Aisha lfy naga kamar ranki a ɓache? Abba ya tambaya yana kallon face nata, Ammi bata ɓata lokachi ba wajen sanar da Abba abun da Aryan ya faɗi

a tunanin ta Abba zai ɓata rai sai kuma taga yana murmushi ya ɗauko wayar sa dake gefensa yafara kiran layin Aunty farida,
Bugu ɗaya Aunty farida ta ɗaga tare da faɗi “hello Abba na “my daughter ki zo fada yanzun nan ki sameni, yana gama faɗin hakan ya katse kiran,

baifi minti 5 sai ga Aunty farida ta shigo da Sallama har kasa ta duƙa chikin girmamawa ta gaida Abba da Ammi, da fara’a dukkansu suka amsa, “zauna my daughter muyi magana chewar Abba
Miƙewa Aunty farida tayi ta kowa saman kujera ta zauna ta zubawa Abba ido tana sauraron taji mai zai che “so nake yanzu ba sai anjima ba ki ɗauki diyana ku koma Maiduguri da ita, kuma karki kuskura ki sanar da wani tana wajen ki koda Aryan ne ko zai miki tambaya dubu idan ki ka kuskura ki ka sanar da shi to ban yafeba. Sai da Abba ya daka ta da magana sannan Ammi ta fara magana

Ranka yadaɗe me yasa zaka che hakan? “Aa Aisha ku kyaleni tun da har Aryan bai ji kunyar idon ki ba yazo yace baya son ganin yar ɗan uwanki to wlh sai nayi maganin sa, “tayaya zakayi maganain sa to? Ai naga shi yace bai son ganin ta to kaga idan ta tafi ai sai yafi kowa murna da hakan “Aisha ke nan yanzu kina nufin bakisan chewa Aryan na Son diyana ba, to idan ma baki sani ba yau kin sani, kuma So bana wasa yake mata ba “amma yana Son ta kuma yace baya son ganin ta a gidan nan?

“Kedai ba ruwanki kuyi abun da nache muku wlh duk wadda tasake ta faɗi inda diyana take to sai na ɓata muku, kutashi kuje, my daughter yanzun nan ku tafi kuma karki bari kowa yaga kin fita da diyana, “to kawai Aunty farida tace sannan ta miƙe tanan murna sosai dan ambata diyana atare suka fito fada da Ammi

Yola

Ihu take tana faɗin nashiga uku na ku kawo min agaji zan mutu, da gudu yaya bello ya fito daga chikin gonar sa ya nufi gonar bappan su dan daga nan yake jiyo ihun,

“Subhanallah innar buba lfy? Chikin ihu da kuka innar bubu tace “Bello mutuwa zanyi na shiga uku kumurchin machijine ya sareni a kafa, chikin sauri bello ya kai kallonsa kan kafar nata, gaba ɗaya kafar ta kunbura sundum, girgiza kai Bello yayi yana faɗin “shike nan dafin yagama shiga jikin ki wlh ko kinsha magani yanzu ba lallai ki chigaba da takawa da kafar ki ba, dan dafin ta riga ta illata namar kafar taki

“Bello ka taimake ni mutuwa zanyi wayyo Allah, da gudu yaya bello ya juya ya koma chikin gonarsa ya tsinko wasu ganye ya nufi rafi ya wanke su tas, san nan ya ɗauko wani ɗan kwarya, ya dawo wajen innar buba, murje ganyen bello ya shigayi chikin kwaryar sai da ta fitar da ruwa san san nan ya bawa innar buba, ruwan akan tasha ganyen kuma ya manna mata awajen chizon machijin.

Tana shan maganin ta fara amai, amai sosai ta amayar da dafin machijin, amma kafar ta kuma har yanzu a kunbure yake gashi yayi wani green dashi, ɗaukan kwaryar yaya Bello yayi ya koma rafin ya ɗebo mata ruwa ya dawo ya bata tasha, san nan ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗar sa ya nufi hanyar gida

Da sallama ya shiga gidan hasana na tuƙa tuwo ganin yaya Bello ɗauke da innar buba a kafaɗar sane yasa hasana miƙewa da sauri ta ɗauko ta barma mai kyau daga ɗakin ta ta shin fiɗa a tsakar gidan.

A hankali yaya Bello ya kwantar da innar buba a kan ta burman, san nan ya dubi hasana yace “kiyi sauri ki kammala abinchin ki zuba mata, to kawai hasa tace Sannan ta miƙe ta koma wajen girkin nata, innar buba kuwa sai hawaye take saboda azabar da kafarta ke mata,

*💫STAR LADY💫*

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button