Dabi’ar Zuciya 28
Wani irin miqewa tayi da hanzari,har tana hankade kaltum dake duqe a gabanta tana son tace wani abu
“Kada wanda ya sake tabamin yaro a cikinku” muryar ummanmu ta ratsa tsakanin ihun bilal da dukan da suke masa.
Tsabar mamakin da sukaji ya sanyasu tsaiwa cak daga abinda sukeyi din,kowannensu ya waiwayo cike da mamaki,mamakin jin kalma daga bakinta dangane da danta a rana ta farko a lokaci na farko,tsahon zamansu da ita,tarin kawaici dauke kai gami da haquri dake cikin dabi’unta yau dukka ta kauda,basu taba jin kalma makamanciyar wannan daga bakinta ba,sai a yau din.
Idanu dukkansu suka zuba mata sanda take takowa inda bilal ke kwance hajaran majaran,idanuwanta na tara ruwan qwallar da taketa bakin qoqarin hanata zubowa.
Hannu ta sanya zata dago bilal din,muryar babansu tayi mata waigi
“Sakeshi,kada ki kuskura ki tabashi” ya fada cikin fushi,bata fasa sanya hannu ta daga shin ba kamar yadda ya haneta,ta miqar dashi tsaye,tsaiwar daya kasa yinta da kyau,saida kaltum ta rugo ta tayata riqeshi.
“Zuwaira!,ni nake bada umarnin a hukunta min dana,gaban ‘ya’yana kike nuna musu ban isa ba?,bayan rainin da kika saka suka riga suka gama yimin shi?,ni zaki hana hukunta dana,nace kada kiyi ki aikata?” Yana fada cike da kunya da kuma mamakin yadda a yau ta saba umarninsa,abinda bazaice ga ranar data taba yinsa ba tsahon zamansu da ita
“Tabdijan,to wallahi wallahi billahillazi ba’ayi matar da zan bada umarni a gidana ta bijire ba,ba’ayi matar da zan gyatta kara ta tsallake ba…..duk zuba miki idanun da nayi kika lalata min yaro bai isheki ba?,to ki tattara ya naki ya naki ki tafi gidanku…..kai munzali…..muje”ya fada yana saba babbar rigarsa yanayin gaba kamar zai tashi sama,sai suka mara masa baya suma ba tare da sun tsaya jiran komai ba.
Kalmar ta tafi gidan nasu ta shigeta da wani irin qarfi da ba zata,kalmar da bata taba shiga tsakaninsu ba kenan tunda sukayi aure,sanoda haqurin datake hadiya a kulli yaumin,bata taba kawowa ranta amadun zai iya gaya mata haka ba,a tsayin shekarun da suka kwashe a tare,rauni ne sosai ya mamayeta,yayin da tausayin mahaifiyarta ya rufe kaltum,ta san tsoronta,tasan fargabarta,tasan dalilin daya sanya taji rauni akan kalmar taje gidansu.
“Mu tafi ummanmu,mu tafi mubar masa gidan kamar yadda ya buqata” kaltum ta fada da wani irin emotion me taba zuciya,a lokacin da suka sanya bilal a gaba,wanda har yanzu dafe yake da cikinsa.
Kai umman ta girgiza
“Babu abinda zamu kaltume,bamu da inda ya wuce nan din,koda zan tafi ku baku da gidan daya wuce nan,nan ne gidanku,a nan zaku ci gaba da zama” sai muryarta ta fara rawa,da alama kuka keson cij qarfinta,kukan da tuni kaltum ta fashe da nata,ganin irin murqususun da bilal yakeyi.
Basu gushe ba suna zaune a haka tsahon kusan awa guda suka sake jin tafiyar mahaifin nasu,kowanne yayi sak yana duban hanya.
Turus yayi daga nesa yana qare musu kallo,cikin wata hargoqa da hargagi ya fara nunata da yatsa
“Ba cewa nayi ki tattara kayanki ki tafi gida ba?,to ki hada ya naki ya naki,na baki minti goma,ki tabbatar kafin na fito daga daki babu ke a wajen nan,yau zaki gane idan ina da amfani” daga haka yayi fuuu ya wuce dakinsa ya bankada ya shige.
Tsam ta miqe daga tsakiyarsu ta nufi dakinta,kaltume ta rufa mata baya cikin kuka kai taba zuciya,tana tsaye umman tasu ta zari kayanta guda uku ta zura hijabinta sannan ta juyo ta sake fitowa,kaltum ta biyota tana cewa
“Ummanmu…..ki tsaya na dauko mana kayanmu kinji don Allah” waiwayowa tayi ta dubesu,cikin muryar dake nuna nauyin abinda take dannewa
“Ba inda zaku kaltume,nan ne gidanku,baku da inda ya wuce nan….”
“Ki tattara tsiyarki su biki,babu wanda zai zaunar min daga ita har shi,yara kamar yaran Allah bani,maza kubi uwarku” ya fada yana watsa hannu,kamar wanda ke kaɗa kaji dake son yi masa ɓarna.
A sukwane ta shiga dakinta ta figi hijabinta,ta tazo ta taimakawa bilal suka rufa mata baya duk a cikin hanzari,ganin cewa tuni har ita din tayi gaba.
Tsaiwa tayi da tafiyar da take sanda tajiyo takun sawunsu a bayanta,ta waiwayo tana kallonta tana riqe da bilal
“Me yasa zaku biyoni kaltum,ko kuma gidan mahaifinku,can ne marufar asirinku”
“Kiyi haquri ummanmu,ba zamu iya komawa ba,ba zamu iya barinki ba,koda zamu koma ma ummanmu ta yaya zamu barki a irin wannan daren ke daya ki tafi har gidan inna?,barema tunda ya koreki tare ya koremu”.
Tsaiwa tayi tana hadiye wani abu mai tauri daya riqe mata maqoshi,tana kallon yadda take riqe da bilal cikin ciwo,ko ina na jikinsa rawar sanyi yake saboda duka,da alama zazzabine ke shirin kada shi.
Itama tanajin wani wawakeken rauni na shirin kama zuciyarta tun daga wannan lokacin na rabuwa dasu,bata ce su koma saboda fushi ko qyamata ba,ta fada ne saboda nuna musu muhimmancin mahaifinsu cikin rayuwarsu,an kai gabar da bazata iya sake cewa su koma ba,don haka ga juya taci gaba da tafiya suka mara mata baya.
Kafin sukai gidan innar sun shafe lokaci mai da tsaho saboda yanayin jikin bilal,ga kuma tafiyar qasa,hakan ya qarawa dare tsaho kafin su isa,don har sunyi tsammanin ma zasu taras da gidan a garqame,saidai sun taki sa’a,gidan yana a bude ne,amma kuma an sayashi,da alama gab ake da rufeshi.
Sallama kusan hudu umman tayi amma ba’a amsa ba,saita qarasa zuwa qofar dakin mahaifiyarta ta daga labulen tana sake maimaita sallamar.
Saman gadonta na rufa ta hangeta a kashingide daga baki baki,da alama bacci ne ya kwaeheta ba tare data shirya hakan ba,saita saki labulen tana komawa da baya,ta dubi su kaltum
“Muje,inna tayi bacci” ta fada tana yin gaba,tare da duba dakunan dake cikin dakin,ta bude musu daya daga ciki,wanda babu komai ciki sai sumunti da tabarmar kaba.
Cikin kayantabta cire zani ya shimfidawa bilal saman tabarmar,kaltum ta taimaka masa ya kwanta,dukkansu idanuwansa a kansa yadda yake murqususu,zuciyar kaltum ta sake karyewa,cikin hawaye tace da ummansu
“ummanmu…..ruwan zafi ya kamata a saka masa a jikinsa fa,idan ba haka ba bazai iya barci ba” ita kanta tasan da hakan,amma batason daga shigowarsu gidan su taba wani abun na innar ba tare da saninta ba.
Saidai kafin ta qare tunaninta tuni har kaltum ta isa kitchen din innar,ta kuma fara hada wuta,babu jimawa ta dora ruwan,bai dauki lokaci ba ya tafasa,ta juyoshi ta nufo inda dakin da suke ta ajjiye a tsakaninsu,sannan ta taimaka masa ya tashi ya zauna da qyar yana nishi yana numfarfashi.
Dankwalin ummansu ta karba ta fara gasa masa jiki,tuni ya fara nishi yana kiran wayyo Allah,duk inda tasa ruwan mai zafi zafi ta danna masa sai ya saki ihu cike da radadi yana murgina kai yana cije labba.
Ihu ihun bilal din ya farkar da inna a firgice,saura kadan tayi adungure daga saman gadon nata zuwa qasa,sai data kaza kunne,ta tabbatar bil’adama me sannan ta zame ta sauko daga gadon dankwalinta a hannu tana sauri kamar zata ci da baka,tanason ganin wadanda suka shigo gidan.
Ta tur qyauren dakin dai dai sanda kaltum ta gana gasa masa jikin,ta kuma maidashi ya kwanta
“Me zan gani haka ni zainabu?,zuwaira?,meye haka?” Ta fada cikin hargagi da masifarta wadda ta riga data zame mata jinin jikinta
“Wallahi mune innah” sosai ta shigo dakin tana qare musu kallo
“Aina gani,naga kune din,yo meye haka za’amin irin wannan gangankon da tsakar dare a diro min gida ba tare da masaniyata ko izini na ba?,kamar masu fashi da makami?” Dan shuru umman tayi,tana fasalta da harshen da zata yiwa inna bayani
“Ki bude baki kiyimin magana,keda ‘ya’yanki kun yimin duru duru” tayi maganar tana rungume hannayenta a qirji,tana kuma sake zubawa inna ido
“Inna,mun samu sabani ne da baban habi,shine yace na taho gida” wani dan zakudawa innar tayi kamae wadda ta taka wani abu,kana ta daidaita tsaiwarta
“Shine sai kika tattaro qwanki da qwarqwatarki keda ahalinki kaffff kika taho gidan inna mai masaukin baqi ko?,wadan nan marasa kunyar ‘ya’yan naki,gaskiya ba’a taba rainamin hankali ba irin yau….to banda ma zuwaira ta yaya kike tunanin zan amsheki a gidana?,koda ke daya ce bare keda bataliyar wannan yaran haka saket,wato nice me wuyan dauka ko?….” Sai innar ya ranqwafo dai dai saitin umman
“To na rantse da aradu badai a gidana ba,babu masaukinki a gidana,saboda haka sahunki a likkafa kisan inda kika kama,badai nam ba,bare azo a dauramin nauyin babu gaira babu dalili”..
“Ke kuma keda wa kike ta maganganu?” Muryar jafaru dake riqe da leda ta ratso dakin
“Wacece idan ba zuwaira ba,haka kawai ta debomin bataliyar tara tayo yaji dasu,na riqeta na riqe mata ‘ya’ya,uban daya haifesu ba yaqi su bare ni karan kada miya?”
Qaraso shigowa dakin jafaru yayi,ya ajjiye ledar hannunsa a gefansa yana cewa
“Wallahi na zaci ma wasune,ashe umma ce,yanzu inna banda abunki,umma zuwaira ai dolenki ce,ko ‘ya’ya dari tazo dasu kuwa”
“A’ah,bada ni ba sa lallen karya,’ya’yana ne suke dawainiya dani,banga dalilin da za’a doramin nauyi ba,saboda haka dole ta tattara yanzu yanzu ba anjima ba tasan inda dare yayi mata”.
Tun jafaru na daukar abun da wasa har ya haqiqance da gaske inna take,duk irin mamakin da yake kanta saida mamakinsa ya ninku,qarshe ma ya fahimci cewa qoqarin sata ta barsu su zauna da yakeyi qara damal mala al’amarin kawai yake,don haka saiya sauka daga wannan bigiren,ya soma yunqurin qyalesu zuwa safiya,idan Allah ya kaimu wayewar gari,da qyar yasha kanta,ta fice tana maganganu tare da kumfar baki
“Saboda kinga akwa wadatar dakuna,to dakuna na bana zamanku bane,ba kuma gadon ubanki a ciki bare kice ban kyauta ba,ubanku bai barmin komai ba a gidansa sai wancan rugurgujajjen dakin,nan duka arziqin ubansu indo nake ci”.
Tunda ta fita dakin ya dauki shuru,tsakaninsu babu mai iya cewa komai,baka jin komai sai nishin bilal,wanda ko sau daya inna bata ma damu ta tambayi me ya sameshi ba,burinta kawai su fice mata daga gida shine abinda ya dameta.
Cikin hijabi kaltum ta shige ta dinga ruzgar kuka,gani take kwata kwata basuzo duniya a sa’a ba,kota wanne bangare qyamata ce da baqinjini yake bibiyarsu,tana iya jin yadda ummans keta sauke ajiyar zuciya akai akai,kamar qaramin yaron da aka yiwa shegen duka.
Tun bilal na nishi lokaci lokaci yana cewa
“Wayyo Allaj cikina” har wani wahalallen bacci mata dadi yayi awon gaba dashi.
Duk yadda kaltume kejin wannan daren bacci yayi kadan ya dauketa amma sai daya gwada mata qarfa qarfarsa,can tsakiyar dare sanda suke zaune ita da ummanta,kowa tunaninsa yayi nisa kan meye makomars a gobe da safe idan inna ta tsaya kan ra’ayinta na su bar mata gida?,da wannan tambaya mai nauyi da firgici baccin ya sureta.
Ƙaqqarfar bugun qofar da aka yiwa dakin ta samu nasarar ratsawa har cikin tsakiyar baccinsu,ya haifar musu da farkawa gaba dayansu a firgice daga dan gajeran barcin da ya wafci idanuwansu,duka kowanne ya miqe ya zauna daram saman mazaunansa suna duban qofar,yayin carar zakaru ke tashi daga wancan gida zuwa wannan gida,da alama a yanzu ne assalatu tayi.
Inna ce tsaye a kansu tana dubansu,kai kace daren jiya batayi barci ba,kamar ta zauna gadin daren ne tana jiran asuba tayi
“Saiku tashi ko?,kusan inda dare yayi muku” ta fada kanta tsaye,tana sake matse fuska.
Mamaki maganarta ta basu,kaltum takai dubanta ga tsakar gidan,dudum yake,duhunsa bashi da maraba da tsakiyar dare,hakan kuwa ba abun mamaki bane,saboda ko salla ba’a shiga ba a qananun masallatan dake qauyukan
“Wai da gaske kike inna?,to ina zamuje?”
“Ki tambayi uwarki!” Innan ta fada tana zazzaro idanuwa,tare da nuna ummanmu da yatsa,waiwayawa tayi kuwa ta kalli ummansu,wadda ta sad da kai
“Duk yanayin data samu kanta ita ta jama kanta,babu yadda banyi da ita kada ta haifeku a gidan nan ba,ta fito ta samu wani mai damshin arziqin ta aura amma taqi,sai data tara ku kuma sannan yanzu haka kawai saita debomin wallahi,to ba dani ba sam,duniya da girma da fadi,ai maye baya ci kansa ba” ta fada tama riqe da qugunta kamar qaramar yarinya
“Kiyi haquri inna zuwa gobe,ko anjima gari ya sake wayewa….zamu tafi” cewar umma cikin sanyin murya,a karon farko kenan tsakanin jiya da yau a aka fara dambarwar
“Me? Inji akuya?,idan kin isa shegiya nake,billahillazi kinyi kadan,ko sakan bazan qara muku ba,ku tashi ku fita?,idan kunqi kuwa saina tijara ku” ta fada cikin bambami da daga murya
“Qofar gida zan tsaya ma naga fitarku,wallahi bame qara yimin minti guda a guda” ta sanya kai tana shirin ficewa daga dakin sukayi karo da jafaru
“Wai inna maganar ce ne da farar safiya ko ince tsakar dare?,haba inna,ko gari ai kya bari ya gama wayewa ko?” Ya fada cikin jin takaicin halin innar
“Kai jafaru,kai jafaru,kai jafaru,sau nawa na kira sunanka?,ba sau uku ba?,to wallahi wallahi ka fita daga idanuna,idan ka qara magana a nan saina tsintstsinka maka mari” tafada tana huci gami da zare masa ido,ala dole yaja bakinsa yayi shuru yana kallo tana ci gaba da tijararta har zuwa qofar gida,fadi take
“Ki fito ku barmin gidana,wallahi sai kun tafi,ku fita ko nasa a fitarmin daku” cikin daga murya,wanda sautinta ya karade dukka maqotan take gefe da gefe gaba da bayan gidansu,ya kuma fara jan hankalin jama’a wadanda suka tattashi domin bada farali na sallar asuba,masu fita zuwa masallaci maza,dama mata masuyin sallar a cikin gidajensu.
Kafin kace meye mutane sun dan fara tattaruwa,dai dai sanda ummanmu dasu kaltum ke fitowa a gidan,kaltum na riqe da bilal da har yanzu jikinsa baiyi qwari ba,ummansu na riqe da ‘yan kayanta data debo.
Fitowarsu tasa jama’a suka koma kallon kallo,kowa ka kalla fuskarsa cike da alhini da kuma mamaki,anya kuwa innar kanta qalau?,wasu daga cikin jama’ar suka soma yiwa kansu tambaya,wasu kuwa sun riga da sunsan lafiya ras take,saboda sanin hali yafi sanin kama,kowa Yasan innar yasan abinda zata aikata da wanda ba zata aikata ba,a tsahon shekarun da take zaunen a nan,duk mutumin daya zauna da ita ya santa da halaye gusa biyu datayi shura dasu,zallar masifa da kuma son abun duniya,ba shakka iya wadan nan dabi’u kawai sun isa suyi mata jagora ga abinda ta aikata din a yanzu.
Suna sake nisa da ita kunnuwansu na sake kasa kama maganganu da hargowar data ke musu,idanuwan ummanmu a wannan karon sun gaza riqe ruwan hawaye da suka danno cikin idanuwanta,irin abinda innar tayi mata a yanzu yana cikin lissafin irin abubuwan da take zato tunani ko mafarkin innar zata iyayi mata a rayuwa,ta shiga matuqar rudani da mamakinta,ta zaci koda bare ne wanda innar bata sanshi ba bawai gudan jininta ba bazata aikata masa haka ba,wai dama haka qin jininta yayi nisa cikin ran inna?,laifinta kawai don babansu bashi da komai,bai mallaki abun duniya ba har ya mutu?,laifinta don taqi kashe aurenta sanda arziqi da dukiyar amadu ta durqushe?,ta gaza tantance wanne ne laifi cikin abinda ke faruwa,dabi’ar da inna ke nuna mata lailan wa naharan?,ko kuma ita abinda ta aikata da kuma yanayin rayuwa a mahaifinsu ya sami kanshi kafin rasuwarsa?.
“Ummanmu……ina zamuje yanzu?” Muryar bilal dake cike da gajiya da kuma ciwo ta fargar da ita cewa a hanya suke,sai a sanna ta daga kanta,sunyi nisa da gidan inna,zuwa sannan an shishshiga masallatai sallar asubahi
“Muje gidan umma altine” kaltum ta amsa masa maimakon umman tasu
“Ko umma?'” ta maida tambayar gareta don ta samu tabbacin abinda ta yanke din ya yiwa umman tasu.
Har cikin ranta taji bai dace sujewa altine ba,saboda ita kanta neman dauki da taimako takeyi,nauyin dake kanta itama tallafi take buqata,zuwanta wajenta a irin wannan lokacin tamkar rashin sanin abinda ya kamata ne,uwa uba ma ita din qanwarta ce bawai yaya ba,don haka saita girgizawa kaltum kai
“A’ah,ba gidanta zamu je ba,itama tana da wasu wahalhalu da dawainiya a kanta…..”
“To gidan yakumbo indo?” Bilal yayi saurin sake fada,da alama a jigace yake,so yake kawai su samu muhalli ko wanne iri ne da zai bashi damar hutu.
Nan ma kai umman ta girgiza
“Itama macace,a qarqashin wani take,ba zamuje mu dora mata jigilar mu ba har mu uku”
“To gidan kawu ado” wannan karon kaltum ce ta fadi haka,shuru umma tayi,yayin da suma dukka sukayi shurun suna dubanta,daga kai tayi,sai taga dukkaninsu ita suka zubawa ido suna jiran suji amsa
“Shikenan,muje can din” ta gada tana riqe hannun bilal da kyau,don kaltum ta samu ta huta itama,don tafiyace miqaqqiya a qafa daga nan zuwa gian kawu ado,tunda babu wani abun hawa sa zasu hau da zai rage musu wahalar tafiyar,a qalla zasu iya shafe awanni biyu kafin sukai.