Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 27

Sponsored Links

Tana zaune a tsakar gidansu,yamma ne liqis tana bin gashinta layi layi tana shafa ruwan danyan karkashi data jiqa,hanya ce da take bi wajen gyaran gashinta,yana qarawa lallausan gashin nata baqi,da kuma hanashi zubewa.

Tana aikin tana tuna abubuwan da suka faru kwanakin da suka shude cikin rayuwarta,har yanxu har kuma kwanan gobe walwala da sakewarta bata dawo ba,tana jin tamkar an bude sasari ko kuma mari an sanya hannu da qafafunta,ta tuna irin nacin aiken daya ringa yi mata a jiya kan ta fito ta saurareshi,saidai gana daya lokaci guda,tunda abun ya faru taji kamar am zareshi fit daga ranta baki daya.

“Ka jirani,ina zuwa…..ai bance bazan baka ba,yanzu zan fito” ta tsinci muryar bilal yana fada,tun kafin ya qaraso sashen nasu muryarsa ta rigashi qarasowa,kasancewarsa mutum me murya.

Idanunta kan qofar har ya shigo,hannunsa dauke da wata baqar leda da baka iya ganin abinda ke ciki
“Kaida waye,me kuma zaka bashin kake fadin ya jiraka?” Tayi masa tambayar tana taje kanta da santsin karkashi ya sanya tsahonsa sake daduwa

Dan qaramin turminsu da suke amfani dashi ya janyo kusa da ita ya zauna yana amsa mata

“Dan ladi ne yake neman rancen kudi” wani kallo ta watsa masa mai kama da harara

“Kai din har yaushe kayi kudin da zaka dinga bada bashi,bana hanaka basu bama?,nawa kake binsu amma shuru babu wanda yake da niyyar biyanka?kai sun taba baka aron kudi saboda kana da buqata?,idan fa ka tambayesu kowa cewa yake bashi dashi a cikinsu”

“Kiyi haquri yaya a basu,meye a ciki?,ai na fisu lada har a wajen Allah ko?,yanxu baga irinta ba,saboda Allah yaga zuciyarmu,hijabi aka bani akace na kawo miki” ya fada yana ajjiye mata ledar,ta bita kuwa da kallo bayan ta tsaya da tazar kan da takeyi

“Waye ya baka?,ince dai ba nasuru bane?”

“Haba yaya,ni ko kallonsa yanxu banayi….mutumin nan da yace zai sakani a makaranta ne,bansan ma ya akayi yasan hijabinki ya yage ba”

“Ina fatan na roqarsa kayi ba?” Da sauri ya girgiza kai

“Haba yaya,kin manta ummanmu tace babu kyau roqo?” Hannu ta miqa ta janyo ledar bayan ta dauke idanunta daga kanshi,ta zazzage hijaban dake ciki.

Guda ukune,blue,butter colour,da purple,yadinsu mai bala’in kyau da kauri,tsoro yadan darsu a ranta,wannan ubam hijaban ko cikin lefenta aka sanyo mata shi ta taki babbar sa’a,yo ina ita ina saka wannan hijabin?,saita soma tattarawa tana maidawa ledar

“Kai maza ka maida masa,baka da hankali ne bilalu?,bakaga jikinsu yadda yake ba?” Dariya bilal ya saki har yana doka qafa

“Wallahi yaya kin cika tsoro,mutumin nan yana da mugu mugun mutunci,Allah idan aka mayar masa baxaiji dadi ba”

“Nidai nace ka mayar”

“Toki ajjiye,bari ummanmu ta dawo,duka abinda tace shikenan” ta yarda da maganarsa,don haka bata sake ce masa komai ba sai gyaran gashin dataci gaba dayi,ya miqe tsaye yana ture kujerar daya zauna baya

“A zuba maka abincin ne?”

“Me kuka dafa?” Ya fada yana leqa tukunyar dake saman murhu

“Ragowar tsaki ne akayi fate(gote)” baki ya tabe

“Tabdi,ni yau abinci me dadi ya bani,harda nama,gaskiya mutumin nan yana da kirki Allah yaaya” baki ta tabe kawai tana jinsa ba tare data tanka masa ba.

A hankali ta tuna da mutumin daya ceceta a jiya,kamar ta taba ganin fuskarsa kafin wannan lokacin,zuciyarta tana bata shine ya bada hijabin,saboda banda ita dashi bata tunanin akwai wanda yasan abinda ya faru,don ba’a zancan auwalu ma da baya cikun hayyacinsa,wanda tun lokacin bata sake jin koda motsinsa cikin gidan ba,saita yafito bilalu,ya qaraso yana goge ruwan daya gama sha daga bakinsa.

Siffanta masa samir ta shiga yi,ya tabbatar mata shine,saboda duk qauyen kusan shi kadai ne mai irin wannan siffar,data tabbatar da hakan saita sallameshi.

Ummansu ce tace ta karbi hijabin,bayan data tsare bilal da tambayoyi ta kira nasidi wada tare dashi aka basu hijabin,ta tabbatar da ingancin aiken,can qasan ranta ta dinga jin dadi da farincikin samuwar hijabin a tare da ita,duk sanda ta motsa saita juya ta daukosu ta bude ta sake gani ta maida,har ta gama tsara lokuttan da zata sanyasu,saboda yadda sukayi mata kyau suka burgeta.

********. ******. *******

Sannu a hankali lokaci ya soma murginawa,murginawar data ke murqushe al’amura iri daban daban,masu dadi da marasa dadi,wasu su bar maka tabonsu,wasu kuma lokaci ya shude dasu yayi tafyar ruwa.

A irin hakanne kaltum ke ci gaba da lissafin kwanakin da suka rage mata cikin kwanakin da baban nata ya diba mata akan ta fidda miji,duk ranar da zata fito ya fadi saiya yada mata habaici….baqar magana da kuma munanan kalamai,ya tattara dukkan wani laifi ya aza mata,yace koma meye ya faru itace sila ba wani ba.

Daya daga cikin irin wadan nan kwanakin ne,tana zaune a tsakar gidansu tana dinke wasu daga ckkin sutturunsu da suka yage,suke kuma lalabasu don suyi musu dogon zango,ummansu tana gefe zaune suna taba hira tana shafa magani a kan ciwonta.

Bilal ne ya shigo afujajan,kai kace wani ne ya biyoshi,yayi futu futu da qasa kamar kullum,alamu sun nuna daga wajen aiki yake ya tsamo yayo gida,saika rantse da Allah jikinsa bai bata ganin ruwa ba.

Sallama kawai yayi musu ya urfafi qofar dakin babansu,wanda keda rumfar da yake ajjiye ajjiyensa da basu kai kayan dake uwar dakansa muhimmanci ba,kaf cikinsu babu wanda ya isa ya doshi rumfar bare dakin,tsakaninsu da ita kallo daga nesa,to amma saiga bilal ua dufefeta sa qano irin kazar kazar

“Kai bilalu….kai lafiya.” Dakatawa yayi daga tafiyar da yakeyi yana duban ummansu

“Ummanmu…..na samu me siyan langa langar baaba,yana siya da daraja,zan dauka nakai masa ya siya”

“A’ah bilalu,na rabaka,kada ka taba masa kaya,kabar masa abinsa,da kansa idan ya samu me siyan yaga dama ya saida din”

“Allah ummanmu idan ya tafi bazai samu me siya yadda yake siya ba…..ki bari kawai a siyar masa,ko yazo zai fara fada yaga kudin bazaice komai ba” sai yayi gaba da sauri zuwa inda langa langar take

“Nidai da zaka bi ta tawa bilalu a haqura,kada aje garin neman gira……a rasa ido”

“Bazaice komai ba ummanmu,bari kiga” ya fada yana lanqwasata bayan ya daukosu daga inda suke jingine,yana jin ummanmu na qananun mitoci har ya fice daga gidan.

Bayan sallar isha’i baban ya shigo gidan,a sannan kaltum tana dakinsu tana gyara ‘yan tsummokaran kayan data mallaka.

Idanunsa ne suka qyalla masa wajen,saiya fasa bude qofar dakin nasa da ya sanyawa muqulli yake da niyyar yi,ya fara qwalawa umma kira.

Tunda taji kiran nasa gabanta ya fadi,ta miqe da hanzari ta fito ta ruskeshi

“Waye ya tabamin kaya?,wato rashin mutuncin gidan nan har yakai na ajjiye kaya wani ya saka hannu ya dauka zuwaira?”.

“Babansu ba taba maka kaya akayi ba,yaron nan ne ya samu me siya da daraja,shine yace bari ya saida maka yadda zaka fi samun riba”

“To ni na sakashi?,koni nace masa?,ko kuma nidin makaho ne?,idan inason siyarwar bansan a inda zan siyar ba,to maza a nemoshi duk inda ya shiga yazo ya gayamin yadda yayimin da kayana”.

Tsam ta miqe daga tsugunnon da tayi,dama irin hakan ta guda ta cewa bilal ya ajjiye masa kayansa,saita qarasa qofar dakin kaltum,tana jinsa yana ci gaba da bambami da fada,ta yaye labulen dakin.

Suna hada idanu,tun kafin ummanma tace wani abu ta miqe ta zura hijabinta ta janyo sudaddun slipper dinta ta soma doso qofar dakin,sai umman ta saki labulen ta juya,ita kuma ta biyo bayanta.

Tana ta yi masa sannu da zuwa amma ko saurarenta baiyi ba bare ya amsa mata,itama saita qara wuta ta fice waje,lallai saita tattalli bilalu a duk inda ta soma ganinsa,ba yadda ummansu batayi dashi ya bari ba saboda gudun irin wannan amma yaqi yarda,shi ala dole sai yayi abun arziqi.

Can ta samoshi gaban teburin abokinsu me saida rake,yasa an kankare masa guda uku,yana ganinta ya saki murmushi
“Yauwa yaya,kamar kinsan zancanki nake,ungo riqe min wannan,na ummanmu ne” karba tayi fuskarta a murtuke
“Muje ummanmu na kiranka”
“Dama ai gidan zani” ya furta yana gabtarar raken da yake hannunsa,ya juya suka jera tare,yanata zuba mata surutu,shi baima damu ko ya kula da yanayinta ba har suka isa gida.

Da fara’arshi ya shiga gidan,amma suna hada idanu da baban nasu yayi collapse

“Zo nan don ubanka” cikin hargagi yayi maganar,saiya qarasa gabansa.

Mari yakai masa yayi saurin duqawa kan qafafunsa,baban ya zaburo

“Ina kakaimin kayana?”

“Siyar maka nayi baba,sunce suna so ne,zasu siya da tsada”

“Ina kudina?”ya tambayeshi cikin muzurai,kamar zai hadiyeshi,dan jim bilalu yayi,sannan yace

“Na karbo,amma nakai kudin wajen mai magani,zan amsowa ummanmu maganin qafarta dashi.

Wani irin zagi ya maka masa

“Kayana zaka dauka ka saida kace zaka karbowa uwarka magani dashi?,nina dora mata ciwon?,a rasa da kudin da za’a nemo maganin sai nawa?,qarya ma kake munafuki,ni ban yarda sa wannan zancan ba,nafi gasgata sacemin ita kawai kayi,dama an gaya min ka fara dauke dauke,to wallahi tallahi,billahillazi la’ilaha illa huwa…..duk jaranar daka dauko kada ka tunkareni…..ka tunkari uwarka da kake samowa kana bata tana lamushewa…..kai in sha Allahu…..in sha Allahu ma saika dauko jarabar da zata sanya a daureka,naga ta tsiya,matsiyatan banza matsiyatan wofi,tashi ka bani waje dan iska shege….” Sai yakai masa shuri da qafa,yayi saurin gocewa.

Ba wanda ya iya motsawa a wajen,saishi daya bude dakin nasa ya shige yana ci gaba da bambaminsa.

A sanyaye umma ta kalli bilal
“Me yasa kayi haka bilal?,kaga irin abinda nake gaya maka ko?,gobe duk inda kakai kudin kayan nan ka karbosu ka kawo masa abinsa”

“Amma ummanmu…..”
“Dakata,banason jin komai daga bakinka,nidai na gaya maka” daga haka ta yunqura ta miqe,zuciyarta na mata wani irin ciwo,a duniya babu abinda ta tsana irin taji kalaman aibatawa daga bakin babansu akan yaran nata,ta sani cewa bakin uba shima yana da nashi dafin,tana tsoran kada yaje yayi musu illa da nashi bakin.

Bayan shigar umman daki harara kaltum tabishi da ita

“Meya kaika taba kayansa?,yanzun wa gari ya waya?,ran umma ne ya baci a banza a wofi,saika shige ka tafi,kaji dadi” ta juya zata shiga daki,saiya zabura ya bita da rake

“Ki karba yaya don Allah,fadan baba ya riga ya saba,bazai daina ba,in sha Allahu ma na kusa yin kudi mu huta” murmushin da bata shiryawa ba ya subuce mata,ta amsa raken tana dungure masa hannu

“A hakan,bayan kaqi karatu?”

“Zanyi fa yaya,idan na fara ma bazan tsaya ba,ba abokina din nan yace zai dauki nauyina ba?”

“Allah yasa”ta fada tana ji masa sha’awar yin karatun

“Bari naje na kaiwa umma nata,tana can ta damu kanta” saiya miqe ya wuce dakin ummansu,kaltum ta bishi da kallo,sau tari idan yana wani abun kamar shine gaba dasu ita da habiba,yana da qarfin gwiwa,tare da jarumtar daukar nauye nauye koda wadanda sukafi qarfinsa ne.

Bai jima ba kuwa ya fito yana dariya,da alama ya saukar da umman nasu.

*Bayan kwana goma*

Kusan qarfe takwas ne na dare,amma har a sannan tana bakin murhu tana fama da hayaqin itace,saboda dare da sukayi wajen dora abincin daren,sakamakon rashin kawo abincin da maigidan baiyi da wuri ba,don bai shigo musu da abinci ba sai magariba,sai ‘yan kame kame da sukayi,da ragowar abincin da bilal ya kawo musu wanda samir yaci ya rage mai yawa ya bashi,ya taho kuwa dashi ya kawowa ummansa da kaltume,yana ta basu labarin kirkinsa,da yadda yake sanyasu salla daga zarar lokacin sallah ya shiga,duk kuwa irin aikin da akeyi.

Daga can rumfar baban nasu kuwa yaya munzaline,wanda yaxo tun dazu suketa maganganunsu shida baban,babu kuma wanda yasan abinda suke cewa,saidai daga yadda fuskar baban take a washe zakasan cewa cikin farinciki yake.

Wannan kuwa ba baqon abu bane a wajensu,don tunda mahaifiyarsu munzalin ta fara yi musu aike,ya kuma zamana da kasin baban a ciki ya sake dinkewa da yaran nasa.

Ba jimawa saiga muzammilu ya shigo,shima yabi sahunsu ya samu waje ya zauna bayan ya gaida umma a tsaitsaye.

Hayaniya ce tafara tashi a farfajiyar gidan nasu,tun tana tashi kadan kadan har tayi qarfi,wanda hakan ya tilasta baba sanya munzali yaje ya gano meke faruwa.

Ba’a jima ba sai gashi ya shigo

“Yaron nan yaushe ya fara dauke dauke?” Duk saida maganar taja hankalinsu,baban ne ya tambaya

“Wanne yaron kenan?”

“Bilalu mana” Ai yana kaiwa qarshe baba ya saita takalmansa yana fadin

“Dan kuka,ya jawowa ubansa jifa kenan?,me yayi kuma?”

“Wai kayan aikin makarantar mai tafasa ya sace wasu daga ciki”

“Uhumm,ya kuma kenan,ai dama idan ka daurewa yaro gindi wahala ya sameka,nan ya daukarmin langa langa ya saida ya cinye kudin,uwar bata iya tabuka komai ba,to saiki taso kije kiga gingimemen aikin da danki ya janyo miki” yana kaiwa nan yayi gaba,munzali da muzammilu suka take masa baya.

A rude kaltum dake tsaye ta dubi ummansu,har yanzu bata fasa aikin tsinke zogale da takeyi ba,kai bakace da ita ake ba,kamar kaltum zata saki kuka tace

“Ummanmu….ki taso kije” bata daga kanta ba ta amsa mata

“Na taso nayi me?” Jin hakan sai kaltum din ta kasa jumurin jira,cikin hanzari ta nufi qofa.

Gidan nasu ya cika kamar wanda ake wani dan biki,bilal na tsakiya kamar an samu nama,tsakanin babansu da munzali,harma da muzammilu,suna sauraren jawaban qarya daga bakin musbahu,wanda yana kaiwa qarshe,ba tare da baban ya tsaya anji ta bakin bilalun ba yace

“Ai nasan za’a rina,tunda ka faro daga gida dama na waje sune al’umma ta gaba…..kai musbahu,kuje,gobe da safe da kaina zan tasoshi har zuwa wajen aikin naku” saiya juya ya baiwa munzali umarni sukai bilal ciki,suka tankadashi sai sashen nasu

“Don ubanka ina kayan mutane?” Baban dake tsaye bisa kansa kamar zai hadiyeshi ya fada,cikin qwalla bilal yace

“Wallahi baba ban taba daukan kayan kowa ba….”

“Qarya kake munafukin yaro…..ba daga kaina ka fara ba?,tunda ba zaka fada ba,munzali ku lallasamin dan banza” ya fada yana ja baya.

Ai kuwa tamkar suna jiransa ne suka hau dukan bilal babu ji babu gani,irin duka na rashin hankali,dukan da babu tsari a cikinsa,duka tako ina,duk inda suka samu ko hannunsu yakai nausa suke,tun yana iya jurewa har ya fara zabga ihu yana neman taimako,kaltum ta kasa daurewa,ta durfafesu cikin qaraji tana neman su bari,amma ina,babu wanda ya saurareta a cikinsu,saima duka da munzali yakai mata,wanda dama tun wancan lokacin bai huce da ita ba

“Tofa….qauna,saboda soyayya shine zaki hana a hukunta yaro,tunda ya fara dauke dauke kuma wa yasan me zai faru naj gaba?” Inna laure dake tsaye abinta daga bakin qofa tana shan kallo tavfada hankalinta kwance,kamar ba dukan daya wuce qa’ida sukema bilal ba.

Kuka ta fashe dashi ganin yadda bilal din ya zube gaba daya ya daina yunqurin qwatar kansa sanda suka kaima cikinsa suka kusan a tare munzalin da muzammilun,a gigice tayi wajen ummansu

“Ummanmu,don Allah ki hanasu…..zasu kasheshi wallahi,kinga ya fadi fa ummanmu,kice wani abu…….

 

28
D/z

*wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa*

08184017082
Ko kuma
09134848107

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button