Sponsored Links
Hausa NovelsHausa Novels and Love StoriesZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 27

Sponsored Links

27

Kaman saukan ruwa Mai sanyi cikin maqoshin daya bushe da qishi haka dukkaninsu ganinsa ya sanyaya zuciyarsu musamman sumayyah data fara hawayen da bata shirya ba idanuwanta na Kansa.

Shima ita yake kallo idanuwansa na bayyanarda rauninsa da tsananin son da Allah ya Saka masa nata.

Benazir ma farin ganinsa takeyi a Fili idanuwanta na cika da hawaye sbd koba komai idan su Basu samu gatan rayuwa ba ‘dan da zaa Haifa musu zai samu gatan daga ubansa idan har zai aminta dashine uba Kuma magajin abinda zaa Haifa din.

Qarasowa yayi Kai tsaye gurinta ya nufa Bai tsaya Bata lokaciba ya zauna bakin gadon ya rungumota jikinsa a karo farko hawaye na ciko idanuwansa sbd tsananin karywan da zuciyarsa tayi da ganin yananinta gabaki daya ta rame sosai ga cikin Shima yafito ana ganinsa.

Saukowa hawaynsa sukai sbd yakasa riqesu,

Yayi kewanta fiyeda yanda ya tsammata zai iya daurewa,

Ga halin daya sakata yasani zuwa yanzu Ababa ya gama hukuntar da ita Harma dasu Anne ga ciki da yanxu kam dole kowa zai girbi abinda ya shuka,

Babu maganar boyo tinda ciki baa boyesa saidai babban tashin hankalinsa da baqin cikinsa tin daga ranar da aka sanar dasu wanzuwar cikin shine tarihi ya sake maimaita Kansa akanshi.,

Tayaya familynsa zasu karbi wannan girmamman zancen dazai kawo tashin hankula da damuwa.

Shigowar nurse yasa Bilal din sakin sumayyah Yana goge fuskarsa da black handkerchief din dayake aljihun kayan jikinsa.

Qarasowa tayi tana fadan har yanxu baa kawo jinin ba sai ta mutu ne zaa fara kukan ta mutu bayan sune suke son kasheta sbd ance musu da gaggawa ake buqatan jinin.

Kallan nurse yai Yana Maida kallansa kan sumayyah Yace suje Yana buqatan ganin likita.

Juyawa tai ya kalli benazir cikin kulawa da sanyin jiki Yace mata Yana zuwa.

Bin bayan nurse din yayi suka fice daga dakin.

Duka wani bayani dayake buqata yaji daga bakin likita da nurse Dan haka take Yace a duba jininsa idan zaiyi a Saka mata.

Babban Saar dataci jininsa O- ne Dan haka Babu Bata lokaci aka hau diban jininsa a Saka mata hankalinsa na rabuwa biyu sbd baisan ta inda zai fara tinkarar su Dd babba da dad Kaante da zancen kaddarar data samesa.

Benazir kuwa kwanciyar hankali da nutsuwa data samu ta lokacin ta ganin a qalla sun samu jinin da zai taimakawa yar uwarta warware.

********Karfe hudu na yamma bayan yar tafiya Mai tsayi daga gidasa zuwa kaates Ababa ya Isa qatuwar makeken gate din kaates Wanda Saida ya daga Kansa tsawon mintina ya qarewa gate din kallo Yana mamakin Wanda yake rayuwa a wannan gidan kwadayi me ze Kaisa gurin ‘yar marasa galihu.

Securities din Dake zaune a kofar gate din ya hanasa tinkarar qatuwar gate din Kai tsaye Yana Jin qarfin zuciyarsa na qaruwa Dan kuwa dole su Dd babban daya sani a jaridu da labarai su tsaya a sauraresa idan Sunki baida asara bayyanarda maganar cikin zaiyi duniya ta sani har gidan jaridu Dan kuwa tini ya tanadi makaman yaqinsa.

Ko su karba ciki ko yaja musu bacin sunan da kafin suna da mutuncinsu ya dawo daidai ba shekarun kusa ba.

Kuma ya Maka su kotu Koda sunfi karfinsa ya dai Bata musu sunan da duniya taji abinda Akai.

Tin shigowarsa anguwar securities suke kallansa Amma Babu Wanda ya kulasa tinda Basu San Ina ya nufa ba.

Gurinsu ya nufa Kai tsaye Yana Isa suka dakatar dashi daga nesa Dan basa bari ana isowa jikin doguwar katantar gidan.

Daka tawa yayi Yana kallansu kai tsaye Yace musu gurin Dd kaante yazo.

Gabaki daya securities din suka zubo masa idanuwa Jin sunan Wanda Yace yazo gurinsa.

Cikin son dakatar da koma wane irin shirme Ababan ke shirin Yi shugaban securities din fuska ba sakewa Yace

“Sir DD kaante baya qasar shekaru da dama so kabar Nan please”.

Hanya ya nunawa Ababa dayake kallansa Yana Jin takaici Amma tinda Neman ganin Ddn yake dole zai sauke Kai harya samu ganinsa tukuna.

Sanyaya murya yayi cikin Basu girma a gurin aikin nasu Yace

“Officer Alhaji Dd babba dinne baya qasar?

Dan ayimun alfarmar na gansa wlh lamari ne mai mahimmcin da idan natafi yau zaa iya rasa Rai,

Kuma ran ‘dan Nan dinne ne maana jininsu ne.

Wani kallo tsaf chief security din yake masa Yana son tabbatarda idan Ababan ba mahaukaci bane acikin kaya lullube.

Idanuwan Ababan yake kalla Yana sake katantar yanayinsa Dan kada su tsaya batawa kansu time da mahaukaci basu sani ba.

Ganin ana tantancesa yasa Ababa tsayawa da kyau idanuwansa na kan kofar gate din da aka wangale wata mahaukaciyar Lexus black ta fito baa ganin Wanda yake ciki sbd Nisan datake da Inda suke tsaye.

Ta gabansu motar ta wuce idanuwan Ababa kaman zasu zasu fado subi motar Dan son ganin Wanda yake ciki amma chief securityn ya hanasa ko motsawa daga Inda yake bare ya Isa gate din.

Sallamarsa sukai da cewan ya wuce daga layin gabaki daya basason ganinsa.

Qin tafiya yayi ya tsaya Inda yake Yana sake qudurcewa a ransa yafison su masa duka a gurin idan yaso dole a tsaya a sauraresa ya sake samun damar nunawa duniya dukan da Akai masa bayan anwa ‘yarsa fyade so uku.

Sharesa sukai a gurin tsaye suka koma bakin aikinsu iyakaci Yana kusanto babba gate din farkon dukan da zasu masa ko haukace saita sakesa.

Gyara tsayuwa Ababa yai a gurin sbd yau din a shirye yake da kwana tsaye a gurin indai zai samu dacewa da fitowan Wanda zaisa a barsa yaga Dd babba.

Rana Ce tafara gasa Kansa yafara daukan zafi Yana tsiyayar wani irin zufa Yana jiqasa kaman Wanda ya hadiye kunama da ranta.

Sanyi da gajiya qafafunsa sukai matiqa Amma Sam bayajin zai hakura ya tafi gashi hankalinsa duk ya gama tashi zuwa yanzu Kila sumayyahn ma ta mutu da rashin jinin.

Azabar ranar wunin akansa ta qare har Rana ta fadi Yana gurin Yana zare idanuwansa da wahala ta sake rinarwa.

******Acan asibiti kuwa har aka gama diban jininsa aka sakawa sumayyah ba Ababa ba labarinsa.

Daki aka sauyawa sumayyahn zuwa sama dakunan da suke ajiye masu kudi.

Komai sake siyowa akai tareda abubuwa buqatanta dasu abinci kala kala take nurses ba kunya suka hau hidima dasu.

Wanka Benazir ta taimaka mata tayo bayan angama Saka mata jakar jinin daya.

Dan qarfi ta samu a jikinta sumayyahn kafin ta zauna da Kansa ya Bata abinci tanaci a hankali itama benazir ta shiga toilet ta watso ruwan ta shirya tin a can tafito ganin sumayyah taci abinci yanda ya Dan kamata sai alokacin itama ta daure taci lafiyayyan abincin da aka kawo musu iri iri.

Har yamma Alh Bilal Yana tare dasu cikin kulawa Yana jiran Ababa sbd ganin juna da yanxu garesu ya zama dole tinda dalili Mai qarfi ya Saka.

Dayake wayoyinsa a kashe suke Babu Wanda ya Kira nemansa bayan yasan iyayensa sun San ya iso tinda daga gida driver yaje daukansa airport Kuma daga can Nan ya ajesa.

Ana kokarin Sallan magrib dole ya baro asibitin ya nufi gida da niyar zai dawo daga baya.

Driver har lokacin Yana Nan Shima Yana jiran fitowar Bilal din dan haka Yana ganin fitowarsa ya taso daga Inda yake Zaune suna fira da wani Wanda ya sani da sauri.

Motar suka shiga kusan a tare da sir Bilal din dan lokacin ya kunna wayoyinsa Kiran Dd babba ne yafara shigowa wayarsa take ya dauka jikinsa a mace.

Kicin muryarsa ta Kai tsaye Yace yazo Yana buqatan ganinsa.

To Yace cikin girmamawa sbd yasan Shima Bai kyautaba rashin Isa gidan su San da isowar tasa.

Numfashi ya sauke zuciyarsa na tsinkewa da Neman da Dd babban yake masa dan muryarsa ba sauki Kai tsaye take.

*****Ababa babbar sa’arsa daga Allah ne kaman yanda yake fada sbd ana Kiran sallar magrib a babban masallacin kaates Dake manne da qatuwar katangar gidan sai ga fitowar tsohon daya gama jiquwa a cikin arzkin Allah da tarin Hutu da dukiya Harma da boko da ilimin addini ya fito Dan shiga sallah Kuma cikin wata sabuwar sa’ar shi dayane yau sbd dad Kaante da sauran mazan dasuke dasu a gidan sunyi tafiyan kwana daya wani mahimmin daurin auren da dole kaates su halarta.

Duk kowace Rana daidai wanna lokacin Dd babba ke fitowa sallar magrib baya taba fashi matiqar Yana qasar Kuma garin.

Ababa Bai taba tinanin zai samu dama a ranar farko ba lokaci daya ta ganin Dd babba kaante Dan haka yake sake Jin Kansa me Saa.

Da gudun fanfalaki yaso zuwa gurin Ddn Amma securities sukayo Kansa Dan haka ya jujjuya baiga ruwa ko gurin alwala ba bare shima ya fada masallacin Dan haka juyawa yayi da sauri yana Neman Inda zai samu qasar taimama Amma anguwar kaman ta kafiran turawa Babu koina a tsare.

Daqyar ya samu Inda keda yar qasa yayi taimama jiki na rawa ya dawo da gudu gudu sauri sauri yana Isa ya shige masallacin kafin securities su ankare Kuma Daman baa Hana shiga masallacin Sedai bama kowa ke zuwa ya shigaba tinda anguwar akwai tsaro ba mutane.

Ba mutane sosai Dan haka ya kutsa ya shige sahun gaba Inda Dd babban yake aka tada sallah.

Ana idarwa salati da istigfar kawai Ababa yayi ya juyo Yana Satan kallan Dd babba Dake adhkar cikin nutsuwa da kwanciyar hankalin masu abin duniya.

Ahankali kowa ya fice aka bar limamin masallacin kaantes din sai Dd babba sai Kuma Ababan da bakinsa ke rawa sbd maganar Dake cinsa kada damarsa ta qwace.

Daya daga cikin securities din dazu ne ya shigo zai masa magana

Yana ganin hakan ya miqe ka tsaye ya nufa gurin Dd babba Yana miqa masa sallama da gaisuwa a tare.

Jinjina Kai kawai Dd babba yayi batareda ya amsa da Baki ba sbd Bai gama laziminsa ba Kuma Bai dago ganin kowaye ba.

#MAMUH#

#BENAZIR ABABA KAANTE

#DD KAANTE

#ZAFIN KAI

#LOVE#MARRIAGE#ROMANCE#BABY

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button