Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 23

Sponsored Links

Ba’a dauki wani dogon lokaci ba habiba ta bayyana a tsakar gidan,zani daban riga daban,idanuwanta sunyi jazur dasu,da alama kuka tasha take kuma kanyi har yanzu.

Sai a sannan kaltum ta samu qarfin halin tunkarar habiban,hankalinta a matuqar tashe duba da yanayin data shigo dashi,riqeta kaltum tayi tana jaddada tambayar

“Lafiya?,habi lafiya?”.

Bata iya magana ba sai da suka isa gaban umma da tayi mutuwar tsaye,cikin qarfin hali itama ta sake tambayarta

“Umma…..anacan ana yamadidi da yaaya a gari wai tayi cikin shege,dalilin kenan daya sanya wai ya munzali yayi mata dukan tsiya”.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” shine abinda ummanmu ta ambata,a tunaninta cikin zuciyarta tayi,saidai tsabar rudanin data samu kanta a ciki baisa ta fahimci a fili tayi ba har sai da sautin ya fito,saita nema jikin katangar dakinta ta jingina tana kamo hannun habiba gami da zaunar da ita cike da qarfin hali,wanda kaltume ma da taji tana niyyar faduwa saita sulale ta zauna kusa da ‘yar uwarta.

Duk wani yawun bakin umma ya bushe,ta qaqalo wani da qyar sannan ta samu damar yiwa habiba bayanun yadda komai ya faru

“Na sani ummanmu,yaaya ce fa,ni nasan ba zata taba aikata wani abu mara kyau ba,bansan iblishin da yaketa yada zancan ba,har gida aka sameni tun shekaran jiya ake gayamin,baaba ce take korarsu fata fata,tace batason gulma su tashi su bamu waje,to umma daga shekaran jiya zuwa yau karo na hudu kenan ana zuwarmin da zancan,wannan wanne irin bata suna ne umma?,me muka yiwa mutane?” Sai kuka ya sake kubce mata,wanda a wannan karon ita kanta umman bata data cewa,ta rasa dukka kalama bakinta.

A daidai lokacin inna laure tayi sallama a tsakar gidan nasu cikin nuna hali na gigita,shigowarta yasa habiba saurin boye kuka ta tare da goge fuskarta,don ta sani ba alkhairi bane ya shigo da ita ba.

Diri diri ta fara yi,kafin daga bisani tace

“Zuwaira lafiya habiba ta shigo tana kuka?,ko daga gidan aurenta ne?” Idanu umma kawai ta zuba mata tana dubanta,tana kallon zallar rashin alkhairi daga laure,wadda a kullum bata fatan musu alkhairi sai sharri

“Ba komai sai alkhairi” shine amsar da umman kawai ta bata,saita juya tana cewa

“Au too…..to Allah yasa,koda yake idanma ba’a gaya mana ba idan tayi tsami zamuji,kamar yadda mukaji na dayar muna daga zaune”

Wani mugun kallo kaltum ta bita dashi,duk da cewa a yanzun takanta take da mummunan baqin sharrin da aka laqaba mata,tabbas da zata samu dama da saita maidawa inna lauren martani dai dai da maganarta.

“Saurareni habiba da kyau……” Umma ta fada tana yunqurin baiwa kata qearin gwiwa,saboda ta hangi rauni a idanun dukkaninsu,kuma ta tabbatar cewa qwarin gwiwar da zasu gani a idanunta itace zata motsa tasu jarumtar

“Kowanne bawa da kalar qaddararsa,wani tasa tafi wanna muni,dukkaninmu mun sani hatta da annabawan Allah an jarrabesu,halitta mafi soyuwa ga wanda akayi duniya da lahira saboda shi annabi Muhammadu wato nana aisha an jefeta da qazafin zina,ko kin manta?,kina tunanin indai hakane akwai wanda zai tsallake?” Kai ta girgixa a hankali,daga ita har kaltum din suna jin nutsuwa ta fara saukar musu,hakan ya bata qwarin gwiwa naci gaba da maganar da takeyi,duk da ita kadai tasan abinda takeji a zuciyarta.

“Duk wanda ya jefeku da sharri ko qazafi,ku barwa Allah komai,shi baya zalunci,kuma baya yarda a zalunci bawa,da sannu zai fitarwa da dukkan me haqqi haqqinsa komai daren dadewa” cikin hikimar iya zance,da qwarewa irin ta uwa ta gari ta sauke rudu da dimuwar da suka shiga,sannan daga qarshe ya dubi habiba

“Yanzu yusufa yasan kin fito?” Kai ta jinjina

“Ya sani ummanmu,shine ma ya rakoni,baaba tace ya rakoni saboda jikina babu dadi” sam sun mance da batun ma lalurarta saboda wannan yanayin da suka shiga

“Alla ya sawwaqe,saiki tashi ki koma gida ai ko?”narkewa habiban tayi

“Ummanmu ya barni fa,yace na zauna har dare,zaizo ya daukeni”.

Zaman nata ya yiwa kaltum dadi sosai,ya debe mata kewa fiye da kima,tayi rashin ‘yar uwa a kusa,wanda bata sake gasgata hakan ba sai yau da suka wuni tare cur da habiban,tsoro da fargaba dake ranta kaso mafi yawa ya ragu a ranta.

A nan babansu ya dawo ya taddata,ya fara zabga sababi kenan kan ta tashi ta tafi gidanta,shi ba mahaukaci bane da zatazo ta zaune masa…..saiga yusufa dan halak,harda tsabar kayan marmarinsa,lemo,kan kana da ayaba harda biredi.

Ita dai umma ta sani cewa,ubangiji kawai ya dubi irin rayuwar dasu habiba ke ciki ya bata miji na kerewa sa’a,hakanan itama ya dubeta,ya duba darajar addu’ar da take musu ya hadata da surukai na gari,fatanta ubangiji yasa ‘yar uwarta kaltum ta dace kamar yadda itama ta dace din.

Suna kewar habiban itama tana kewarsu yusufa ya tasa kayarshi a gaba suka tafi gida,saidai ba wata damuwa bace mai yawa a ransu,saboda sunsan tana samun kulawar da bata taba samun irinta ba cikin gidan mahaifanta.

 

*******WASHEGARI********

Ƙarfe goma na safiya tana duqe tana sake sharen wajen da bilalu ya gama dabdalarsa bayan sun gama karin safe,tana yi tana mitar sai tayi maganin bilal din,yayin da shi kuma yake shirin fita aiki abinsa yana dariya

“Haba yaaya kattume ta wajena,kasa kisa a ganmu a rana mana ayi mana dariya” umma dake kwance cikin daki saboda zugin da qafarta takeyi mata ta tabe baki,saman fuskarta kwance da murmushi,dramer din kaltum da bilal sai su din,ka gansu nan ka qyale kayi wucewarka abinka.

Kayan ummansu da babansu data jiqa ta nufa ta soma daurayewa,tun bayan ciwon da tayi sai yau zata fita,zata zagaya bayan katangarsu ta yiwa wata amarya da aka kawo daga qauyen kusa dasu kitso,shi yasa take aikin da hanzari hanzari,tayi ya gama taje,don tun jiya ta aiko amma bata samu zuwa ba.

Sallamar da aka rangada ce ta sata waiwayawa bayanta inda qofa take,duk da bata dago daga abinda take ba,ta amsa tana ci gaba da wankin,saidai yadda aketa koda sallamar a jejjere yasa ta saki zanin ummansu dake hannunta,ta miqe sosai tana amsa sallamar,zuwa sannan har sun iso filin tsakar gidan dake sashen nasu.

Mata ne su su uku,kowacce sanyi da hijabi,suna rarraba idanu gami da kallon kowanne lungu da saqo na gidan,hakan ya sanya kaltum sake amsa sallamar,ga zatonta ko basuji ba,ko kuma basu gan bilal ba,idanma haka ne gata ita dake tsaye tana kallonsu.

Sake amsa sallamar saiya zamana kamar kiran jan hankali kuwa a garesu,gaba daya suka waiwayo suna kallonta.

Idanunta suka haska mata fuskar daya daga cikin matan,kamar ta santa,kamar lantai babar nasuru,duk da cewa sai daya tabtaba ganinta,amma bata da saurin mance abu,tabbas ita dince,sai kunya da nauyi suka kamata,da sauri ta jawo hijabinta dake ka igiyar dake daura dasu ta zura tana fadin

“Baaba sannunku da zuwa” kafin a hankali ta nufi gabanta,ta durqusa a saman gwiwarta tana gaidasu,yayin da bilal dake gefe shima yake tayata gaisuwar.

Babu wanda suka amsa gaisuwarsa a cikinsu,sai daya daga cikinsu ce ma ta taushe gaisuwar da tambayar

“Babanki yana nan?” Kai ta girgiza cikin mamakin lafiya?

“Bai jima da fita ba”

“Babarki fa”

“Tana daki,tada kwanta ne batajin dadi”

“Ba wannan muka tambayeki ba,kira mana ita maza maza,sauri mukeyi” mamaki sosai ya sake kamata,amma duk da haka bata fasa qarasawa ta dauko musu tabarmar kaba ta shimfida musu ba,dai dai lokacin da taji daya daga cikinsu na cewa

“Lanti itace?”

“Eyi…..itace”.

A kwancen ta tadda ummansun,bacci ya fara daukarta,motsin shigowarta ya farkar da ita
“Yaya akayi?,bilalun ya tafi?” Kai ta kada,rabin hankalinta yana ga tsakar gida

“Baqi kikayi”

“Baqi…..ganinan” ta fada taba miqewa zaune,saita daura dankwalinta ta rufe gashinta da har yanzu yake da santsi sannan ta miqe cikin qarfin hali tabi bayan kaltum wadda bayan ta shaida musu gata nan,saita kasa zama tsakar gidan ta wuce dakinsu,su kuma suka rakata da kallo,kasa zama tayi,ta rakube bakin windownsu,tana jin gaba daya qafafunta sunyi sanyi da laushi,kamar ba zasu iya daukarta ba.

“Sannunku da zuwa,ya kuke tsaye ga shimfida anyi,ku zauna mana” cewar umma cikin fara’a da faram faram

“Ba zama mukazo yi ba,duk gidajenmu akwai wajen zama,hasalima saqon daga tsaye sai yafi tafiya” dan dumm umma tayi mamaki yana daureta,har ta gaza daurewa tace

“Tooo,ikon Allah”

“Ikon gaske……” Suka maida mata,sannan daya daga cikin ta matso gaba,ta yadda ta fita daga jerin matan

“Gwara na matso sosai yadda zakifi ganeni…..sunana lanti,nice nan na haifi nasuru da kaina,ba doguwar magana ko jan zance ya kawo mu ba,don haka baro baro za’a yita…..mun samu labarin cikin shegan da ‘yarku tayi,sahihin labari kuma daga majiya mai tushe,wato daga bakin mafiya kusanci da ita har mutum biyu,saboda haka mukazo mu shaida muku cewa…..mun yanke igiyar alaqar auratayya da akazo aka tambayawa dana,babu shi babu ‘yarku,kudin aure da muka kawo kuma nan da anjima manyansa zasu zo su karba a mayar masa da abinsa…..”

Duk da rudanin da umma ta shiga,amma tayi namijin qoqarin dannewa

“Shikenan saqon naki?,inason komawa daki?”

“Eh shine saqona,ni dama can bason abun nake ba,wannan baqar yarinyar me kama……” Hannu umma ta daga mata,don ba zata lamunci cin fuska ba kuma,ga mari ga tsinka jaka?

“Ya isa,tunda dai kin isar da saqonki kuje,Allah ya bamu alkhairinsa” borin kunya lanti ta soma ita da ‘yan rakiyarta,suka hau qananun maganganu,saboda basu zaci zuwan abun haka ba,suna qananun haibaice habaice da yarda maganganu suka fita a sashen,umma ta bisu da idanu.

Bisa mamakinta sai tajiyo muryar inna laure tana musu su gaida gida

“Mukusantanta mutum biyu” maganar ta dawo kan umma,su waye suka bada shaidar zurr kan abinda basuji ba basu gani ba?,basu da tabbaci?,mutum biyu makusantanta su waye kenan?,tambayar data yi mata nauyi aka,saita juya kamar kazar da qwai ya fashe mata a ciki ta nufi dakinsu kaltum inda take jiyo sautin kukanta.

Labule ta daga,tana tsaye daga vakin qofar dakin ta kalleta
“Kul…..kada na sake jin kukanki a kan namiji,Allahn daya baki nasuru shi zai sake baki wanda ya fishi da izinin ubangiji” da wannan ummanmu ta saki labulen ta wuce zuwa nata dakin,tana ta qoqarin tausar kanta da kanta,wannan babban abune da muninsa baici ta gayawa kowa shi ba,irin damuwar daya kamata isu isu su hadiyeta ne,ko kuma su tona rami su binneta.

Nan inda take ta sulale ta qoqarin tilastawa kanta ta hana kanta kuka kamar yadda ummanmu ta buqata,wani abu ya riqe mata wuya kamar zai tafi da numfashinta,da sauri da sauri tayi saurin kama

“Ya hayyu ya qayyumu,ya zuljalalu wal ikram” ta dinga maimaitawa a fili,saidai can qasa ta yadda idan ba’a kusa kake ba babu kallai ka iya jiyota.

Tsahon lokaci gidan ya dauki shuru,saika dauka babu umma bare kaltume a ciki,kowa yana kwance yana jinyar zuciyarsa,yayin da suka dinga jiyo karakainar inna laure da ‘yan waqoqinta,tanata shige da fice daga qofar sashen zuwa nata sashen,wanda hakan duka baya wuce taji ya suke ciki ne,bayin Allahn kowanne na kwance yana tufka da warwara,salla ce kawai ta azahar ta tadasu,a haka la’asar ta riskesu.

La’asar din data zo musu da wani babban tashin hankalin na daban,bayan kaltum ta idar da sallar la’asar,tana zaune saman abun sallarta tana karanta sunayen Allah.

Kamar daga sama sukaji muryar mahaifinsu,babu sallama a bakinsa,sai faman qwalawa ummansu kira da yakeyi kamar tshon makahin da ya warke daga makanta,kira ne da kana jinsa zai kada hanjin cikinka,musamman idan kasan halayyarsa.

Kaltum dake zaue batasan sanda ta miqe tsaye ta dafe qirjinta ba,tun kafin taji abinda mahaifin nata zai furta ta tabbatar tashin hankali ne ya samesu,idan ka ganta a sannan sai kayi tsammani ana cewa kyat zata zura aguje.

Ko addu’ar da takeyi din bata samu damar kaiwa qarshe ba ta yanke tana ambatar

“Hasbunallahu wa ni’imal wakil” sannan ta fito daga dakin.

Yana tsaye tsakiyar tsakar gidan,tamkar xaici babu,fushi da masifa sun bayyana muraran akan fuskarsa da kuma duk wani motsi nasa,zirga zirga yake yakai gauro yakai mari amma masifa ta hanashi shiga daki ya cimmata har sai data fito ta kawo kanta

“Ina kattume?” Ya jefawa umman tambayar

“Tana dakinsu” ta amsa tana kafeshi da idanu,gabantana faduwa,saboda batasan da wacce yazo ba

“Ba shakka zuwaira….yadda auren kattume yayi rawa,har iyayen yaron nan sukazo suka amshi kudinsu haka naki auren yake rawa……ke zan baiwa wannan saqon,duk da na tabbatar tana jina…..iyayen nasuru sun zo har wajen sana’ata sun karbi kudin aurensu….to inason ki gayawa ‘yarki…..ki gaya mata da babbar murya,ki jaddada mata cewa…..sanda tayi abun kunyarta ni ban sani ba,hakanan batayi shawara dani ba,to ki gaya mata,na bata wata daya kacal…..wata daya kacal ta fitar da mijin aure,ta kuma kawomin shi,idan kuma ba haka ba,billahillazi la’ilaha illa huwa saina bada ita sadaka ga duk meso,ga duk wanda Allah yayi rabonsa ya tsaga” daga haka ya juya fuuuu cike da fushi,iska tana cika babbar rigarsa tana qara kumbura surarsa ya fice waje abinsa.

A hankali umma ta dafa katangar dake kusa da ita,sannan ta koma ta zauna a hankali tana furta

“La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim” ta furta a hankali,tana son hana kanta kukan da taji yana son qwace mata,zuciyarta na kwabarta,idan ita tayi kuka ita kuma kaltum tace meye?,sai tayi fakare ko zataji sautin kukan kaltum din kamar yadda taso yi a daxun ta hanata,saidai shuruuuu….abinda ya dauki hankalinta kenan,ta miqe a hankali ta nufi dakin.

Koda ta yaye labulen wayam dakin babu kowa,sakin labulen tayi zulumi yana cikata,ina tayi?,tasan dai kafin shigowar mahaifin nasu tana dakin,kuma baya ya fita ita din tana zaune a nan,amma bataga fitarta ba.

Qwararawa kanta gwiwa tayi ta soma lalubenta daga bandaki zuwa qarama da babbar tsakar gidan gidan,saidai babu ita babu dalilinta,don haka ta koma ta zauna a hankali tana kiran sunan Allah,tare da addu’an ba wani abun na daban ke shirin faruwa ba bayaga wannan wanda suke ciki a yanzu…….

ZAFAFA KARO NA FARKO

SUNAYEN SU:

1_GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDULL

2_KAI MIN HALACCI
NA MISS XOXO

3_BURI DAYA
NA MAMUH GEE

4_DAURIN BOYE
NA SAFIYYAH HUGUMA

5_SAUYIN KADDARA
NA HAFSAT RANO

DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500

SAI ZAFAFA TAKU NA BIYU

1-DAURIN GORO
NA HAFSAT RANO

2-ALKAWARIN ALLAH NA
SAFIYYAH HUGUMA

3_QAUNAR MU
NA MAMH GEE

4_IGIYAR ZATO
NA MSS XOXO

5_WUTSIYAR RAKUMI
NA BILLYN ABDULL.

DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500.

SAI ZAFAFA TAKU NA 3,

1_MIN QALB
NA MAMUH GEE

2_SARAN BOYE
NA BILLYN ABDULL

3_KIBIYAR AJALI.
NA MISS XOXO

4_ABINDA KE CIKIN ZUCIYA
NA HAFSAT RANO

5_SIRADIN RAYUWAR BILKISU
NA SAFIYYAH HUGUMA

DUKA DOCUMENTS DIN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500)

SAI ZAFAFA TAKU NA HUDU.

1-ALKIBLA
NA SAFIYYAH HUGUMA

2_DALAAL
NA MISS XOXO

3_UBAYD MALEEK
NA MAMUH GEE

4_MABUDIN ZUCIYA
NA HAFSAT RANO

5_MAKAUNIYAR KADDARA
NA BILLYN ABDULL

DUKA LITTAFAN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500)

SAI ZAFAFA KARO NA BIYAR DA AKE A HALIN YANZU, (ON GOING PAID NOVS)

1-SO DA ZUCIYA
NA MSS XOXO

2-TAKUN SAAKA
NA BILLYN ABDULL

3_HALIN GIRMA NA HAFSAT RANO

4_DAB’IZAR ZUCIYA
NA SAFIYYAH HUGUMA

5-DEEN MALEEK
NA MAMUH GEE

DUKA BIYAR DIN NERA DUBU DAYA NE( 1K)IDAN AN KAMMALA SU KUMA 1500.

YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:

ACCOUNT NAME: MUSAA ABDULLAHI SAFIYYAH..

BANK NAME: KEYSTONE BANK

SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:

08184017082

IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:

09134848107

 

D/Z
24
*_MANZAN ALLAH S A W YACE: Duk wanda yaci abinci,bayan ya gama cin abincin yace:ALHAMDULILLAHIL LAZI AD’AMANI HAAZA,WA RA ZAQANEHI MIN GHAIRI HAULIN MINNI WALA QUWWA Allah zai gafarta masa abinda ya gabata na zunubinsa”_*
_______________________________

*ZUWA GA MAKARANTA DABI’AR ZUCIYA❤‍🩹❤‍🩹*

*_kuyi haquri,muci gaba da bin komai a hankali,kuci gaba da haquri da duk abinda zaku ga ya afku,kar muyi gaggawa,kowanne labari da irin salonsa,hakanan sau tari idan kace zakabi salon da masu karatu keso tabbas zaka shiga sahun marubutan dake tafka shirme da rubuta labarin da bashi da ma’ana sam,babu kuma manufa,labarin daya gaza isar da saqonshi,wanda su kansu masu karatun basa gane hakan sai an gama littafi😁😁,saboda a sanda suka qagu aje wani bigire suna tsaka da shauqi ne,basa gane idan an musu hakan ba dai dai bane sai bayan kammaluwar littafi,muna godiya a gareku da bakwa gajiya da kasancewa da ZAFAFABIYAR,Allah yayi mana jagoranci cikin dukka lamuranmu🤲🏽🤲🏽🤲🏽,muje zuwa_*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button