Cinikin Rai Book 1
[8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: *CINIKIN RAI….*
Mai_Dambu
BOOK ONE
001
Keivroto city.
Sau dayawa mutane suna amfana ne da abin da yake, zuwa gare su ba abin da suke tsammani ba, wani lokaci abin da aka samu shi ake iya ado da shi domin lullube wata rauni. Raunin da zata durkusar da mai shi zuwa faƙiri ba ƙaramar rauni ce ba. “Xnooooooooo!” Shi ne sunan da gungun matasa marasa ji irin ta suke kiranta da shi. Bude idanu tayi tana kallon silifin dakin. “Wayyo Allah na, bakin na rayu kamar Cinderella ba, ko na rayu kamar wata Barbe Queen, amma yau na kare a sansanin jagaliyawa.”cizon lips dinta tayi tana buɗe window ɗakinta. “Wani dan iskan ne ya min kiran mafarauta? Zanci uban mutum idan na fito ku watse kafin na fito” “Allah ya huci zuciyar ki Yar kunama.” Lumshe idanunta tayi, tana me rufe window din ɗakinta, ta nufi hanyar da zai sadata da cikin gidan. Daidai ana buga kofar. “Zenobia! Please open the door!” “Ke ba jiya Babanki ya ce kar ya kuma ganin ki da ni ba?” Ta fada a tsawace. “Mtseeeeeew abinci na kawo miki ” “ko ba abinci ba, uban abinci.” Ta wuce gefen drower ɗinta, ya dauko toothpaste da brush dinta. Kasancewar gidan Babban gidan hayace kuma irin me dauke da dakuna rututu ne, har da gidan sama. Ita tana hawa na uku ne. Ta fito daure da towel a saman kanta, domin Allah ya mata baiwar gashi. A hankali idanunta ya sauka kan Kawarta. “Xno ina jiran ki” dauke kai tayi tana tafiya abin ta, ita kuma ta shige dakin ta fara gyara mata, ƙasan gidan kamar kasuwa kabilu ne mabanbanta daga kowacce kusurwa na garin ƙasar *Gista*, tun daga hawa na biyu idanun jama’a ya fara hango musu Yar kunama take suka fara watsewa, ita din kamar zakanya ce bata tab’a yarda ta haɗa kanta da sauran, wasu mata biyu dattijai ne suka shiga wanke ban dakin tare da saka garin kumfa da maganin kashe ƙwayoyin cuta. Sannan suka dauraye ban dakin, koda ta iso. Amsar bokitinta wasu matasan yan mata suka yi aka zubo mata ruwan zafi, aka surka sannan aka wuce da shi ban daki. Shiga ban dakin tayi, tana kallon shi. ” Inna ki rubuta abin da babu a gidan nan kafin nan da an jima.” “An gama yar albarka.” Ta fada tana juyawa, yau ya dace ta fara aiki amma sam bata jin aikin a kanta. Sai dai Alfarman da Mr Amjad yayi mata ya isa kome ya kuma isa ya saka ta fahimtar rayuwar ta zata juya, murmushi tayi tana kallon kanta, yo dakyar ta gama secondary school, bayan ta gama ta shiga college shima dakyar ta samu damar yin diploma a fannin Kasuwanci. Sai da Inna ta kuma karfafa mata gwiwa ta shima wai gudun kar a rena ta duk da haka bai hana ka fahimci, yadda take cin Uwar uban turanci ba. Idan.kana niman me tozarta turanci. Ba shakka Zeenobia ita ce za a fara bawa Award shi yasa ta kare mai da hankalinta kan dabancinta, jama’a dayawa na masifar tsoronta a waje, amma cikin gidan ita ke bin mutane da luma. Domin sune ita, sune rayuwarta, daidai da rana daya bata fatan ta nisance su. Ita tasan darajar su, shi yasa ko mutuwa zata yi bata fatan ya dauke ta akan idanunsu. Wanka ta fara ta fara jin ihun mutane, bata fasa ba sai da ta gama sannan ta fito. Kallon wani matashi tayi fuskar shi ya b’aci da jini alamar duka aka mishi. “Wani dan shegiyar ne ya dake ka Abbas?” Ta tambaya duk da tana can baya ne, darewa aka yi aka bata wuri. Juyawa yayi ya kuma juyawa. alamar irin dolo ne. “Abbashena waye ya dake ka?” “Wai… Wai … Wai” takowa tayi ta rike hannunsa. “Gaya min!” “Wai don na dauki madara na bawa Hibba shi ne yan uwanta suka dake ni!” Ya fada hawaye yana zubo mishi. Mahaifiyar sa kan bata iya magana ba, sai share hawayen take. “Gaskiya basu kyauta ba, ai kowa yasan yadda yake son Hibba bai dace a ci zarafinsa ba. ” Rike hannunsa tayi ta ce. “me kake so nayi musu?” “Ki gaya musu su daina duka na” rike hannun damansa tayi har dakin Mamarsa da take kuka. “Ammiy kuka kike ne? Na zata zaki daina kuka ai tunda Allah ya bashi rai da lafiya, kuma babban engeering ne, manyan kamfanonin suna niman sa amma ganin sa a haka suke tsammanin ba zai iya ba, sai dai ki sani ke ce kike karya mishi kwarin gwiwa. Daga yau Abbashena babu shegen da zai kuma dukanka” ta fada tana barin dakin. Kallon shi uwar tayi a raunane. “Mahaifinka ya ja maka wannan rayuwar, da bau cusa kansa cikin wancan rayuwar ba babu me cutar da kai.” Cak Xno ta tsaya. “Me kike nufi Ammiy?” “Ba kome Zenobia” lumshe idanu tayi ta wuce abinta. Tana jin babu dadi amma na yau yafi na kullum yawa, tana shiga dakinta ya rufe tare da sake towel din. “Ke dai baki da hali haka kawai sai kin sakawa,mutane talauci hankalinki zai kwanta.” Murmushi tayi ta cigaba da shirin ta, bata damu da Hafsah Ameen da take dakin ba. Yankar da yake kwance a gefen kafad’ar ta, take shafawa ta ce. “Hafsy? A ranar da kuka tsince ni, haka kuka same ni da wannan tabon?” “Eh da wannan oscar din muka same miki.” “Hmm!” Shiryawa tayi tsaf sanye da riga da skit na American suit, dark green, sannan ta kwaso wasu kaca na sarkoki ta zuba a wuyarta, hannun ta kuwa kai kace wani gasar nuna zobuna ake, sannan ta dauko wani mahaukaciyar takalmin me bakin tsawo ta saka. “Xno! Office din zaki fara zuwa da wannan shigar kamar kunce hauka?”. Kallon kanta tayi a madubi ta ce, “nafi tunanin daga turu nake madadin kuncen hauka.” Ba a bin ta
bashin bakar magana ko kai uban waye. Gefe guda kuwa Xno bata da damu da ado ba, ko da yake ai ba laifinta ba ne, rayuwar dabanci ya fi mata armashi sama da wani paint a fuskarta. Tozali da farar hoda ta shafa a fuskarta, sai lipglow da ta goga. A hankali ta kalli kanta. “Ina girmama namijin da zai.” Juyawa tayi ta watsawa hafsy kallon banza. “Zanci mutuncinki” ta fada ba tare da ta bari ta karasa zancen ta ba. “Allah ya huci zuciyar Yar kunama!” Murmusawa tayi, sannan ta nufi hanyar waje. Itama Hafsy ya fito tana take mata baya. “Don Allah kar a takalo rigima, kwana biyu bani da kudin biyan beli.” Juyawa tayi ta kalli aminiyarta ta ce mata. “Bani jakata” mika mata jakar tayi tana faɗin. “Allah ya bada sa’a first time in office!” Murmushin gefen baki tayi, tana faɗin. “Ba ni da lokacinki” ta nufi hanyar sauka kasa, riga da wando ne a jikinta, rigar palazzo pants grey colour sai shirt shima grey top din rigar black, sai sarkokin da ta saka a wuyarta. Asalin halittar gashin kanta, nad’e shi tayi bayan ta daure da ribom, sannan ta daura black turb akanta, wanda ya mata masifar kyau. A hankali take sauka a stairs din. “Ina kwana Aunty.” “Lafiya lau, yan makaranta.” “Barka da safiya Yar kunama” “Barka dai Mr Umar!” Har ta iso kasa, juyawa tayi tana kallon ilahirin gidan. “Yau ba wani abu ne sabo?” Da sauri kowa ya tawo in da take, suna me son duba sabon abin da take buƙatar son sani. “Babu Zenobia!” Lumshe idanunta tayi tana faɗin. “Ina Abbas?” “Yana daki” murmushi tayi ta ce mata. “Mami ki kula da shi!” Sannan ta ce musu. “Babu kome kuka ce?” “Babu kome Yarnan” “shi kenan, ku min addu’a yau zan fara aiki.” Ta fada tana nufar wurin motarta, da wasu gungun matasa suke tsaye a jikinsa. Irin motar nan ce mara koda ko murfi caterpillar, ta shiga mutane hudu uku suka shiga baya, suka tsaya. Gefen drive ne yana jan motar. “Kai ni kofar gidan su Hibba!” “An gama!” Wucewa da ita yayi kofar gidan da babu tazara da tasu. “Amma Uwardakina akwai son rai, kin san dai Abbas ba lafiya ne da shi ba.” Juyawa tayi tana kallonsa. “Sai aka yi yaya?” Shiru yayi bai ce kome ba. “Na zata kai me tausaya mishi ne? Ubansa ya gina wannan gidan ne domin saka haya, yadda zai tallafi rayuwar d’ansa daya tal, kasrshe ya mutu ba a san mene ne sanadi ba, ya kuma rabta sunan al’umma a cikin takardan gidan, kasan wahalar da muka sha kafin gidan ya zama mallakarsa? Kuma kana cikin gidan kana raye nawa kake biya a wata? Son of bitch?” Ta fada kamar zata kifa masa mari. Dai-dai isarsu kofar gidansu Hibba kenan. Ajiye jakarta tayi da yake kan cinyarta. Sannan ta nufi bayan motar ta, sauka daya daga cikin matasan yayi yana dadin. “Uwardakina me zan baki?” Kwagiri. “Mika mata driven yayi, bata amsa ba ta juya tare da nufar inda matasan suke. Mikewa matasan suka yi, tare da cewa. “Idan don wancan mahaukacin kika zo, tow maza ki juya.” Jinjina kai tayi sannan ta ce musu. “Wani dan iska ne ya dake shi?” “Ai mune muka dake shi bakidayan mu!” “Kunyi kuskuren dukansa, bani kwagirin nan Dondurus!” Ai kuwa yaci sunansa domin irin labtaceccen kato ne na bugawa a mujalla. Ya mika mata kwagirin, cire top din rigar ta tayi ta mika mishi. “Uwardakina wannan aikin na mune!” Inji daya daga cikin matasan. “Black bari naci ubansu.” Yes sunanshi ya dace da shi, idan muka yi al’akari da yadda ya kasance baki sosai, “hahhhh! Wai ita zata iya damu ne, an dake shi kiyi abin da zaki yi.” “Uwardakina ki kyale su, baki san yana yin kwarewar su ba.” Inji driven,Juyawa tayi ta watsa mishi kallon banza ta ce mishi. “Duk abin da na kasa a gabana bana jin tsoronsa, sai dai ban saka a raina ba. Paul!” Ta kira asalin sunansà0pa. Tana rike da bulalan, tana juya shi yadda zaka san ranta ya kai kololuwar b’acin, nufarsu yayi cikin zafin nama, ta shiga tsakiyar su. “Ke yar jagaliya, ki tafi idan ba haka ba zamu zane ki, mu miki tumbur.” “Na yarda idan daya kanku yayi nasarar ko kwarzanar jikina, zan bari ku min duk abin da kuke so, idan kuma kuka sake sai na bulale muku, mazauninku.” Ta fada tana kallonsu, tabbas sun san zata aikata amma abin kunya ce a gare su ana bada labarin kanwarsu tana soyayya da dolo irin Abbas. “kin ga Zeeno kin san.” Zuba mishi kwagirin tayi a cinyarsa, tsalle yayi yana fadin “Amma da kin saurare mu ko, sai mu miki bayani” bata yi magana ba ta cigaba da zane shi, ganin yadda take watsar mishi da jikimarsa. “Zenobia don Allah ki kyale mu, ki shiga ki samu megida shi ya saka mu.” Yarda bulalar tayi ta shiga cikin gidan, dattijo ne zaune, sai wasu kartin maza uku. “Yallabai barka da safiya.” D’agi kai yayi ya zuba mata ido, kafin ya ce mata. “Kece Zeenobia!” “Eh yallabai nice Zeeno, Xnoo, Yar kunama.” “Me yake tafe dake.” Ya tambaye ta, cikin sanyin murya ta ce. “Ban zo nan da wata manufa ba, sai dai nazo na gaya maka cewa. Yarka tana son Abbas kuma shima yana sonta, Yallabai ina kaunar Abbas tun daga ranar da na fara ganinsa, amma sai akayi dace Abbas baya sona kasan abin da ake nufi da son maso wani karshen wahala. Amma ita Hibba yana sonta ne da dukkan zuciyarsa. Ko Mahaifiyarsa bata san yana son Hibba ba, amma ni ya gaya min, Yallabai duk da yana da lalura wallahi zai bawa Yarka duj wani farincikin rayuwa. Kaf kudin hayar da ake biya a cikin al’umma charity House nashi ce, a ƙalla ana biyan bera miliyan goma duk shekara. Idan luxury rayuwa kake so zai saya mata expensive stuff amma abu daya nake son gaya maka, idan kace ba zaka bashi ita ba wani abu bane, amma ka da a kuma aikata kuskuren dukansa.” “Idan an dake shi me zaki yi?” Cikin fushi da dauki kofin jug din kwalba ta daki fuskarsa da ita, sai da yaji kamar yayi karo da bango ne, ta nuna mishi yatsa. “Ba da kai nake yi ba, wannan family issues ne.” Sannan ta juya ga dattijon. “yau ranar sa’ata ce zan tafi wurin aiki, Yallabai xan tafi shawara daya xan baka shi ne, ka bashi Yarka ko kuma ka shafa kaji ba tattara su, sun fecce ” sannan ta mike, ta bar falon. “Baba me yasa ka barta?” “Kasan yadda mutum yake ji idan abin da yake so ya rabu da shi? Exactly haka take ji, sannan akwai abin da na hango a kwayar idanunta, zata iya kome domin Yaron, tayi alƙawarin haka da zuciyarta. Ku kira min hibba ”
••°°••
Tana fita ta mika mata rigarta black yayi, ta saka sannan ta zauna a motar. Daukar glass tayi ta saka, tana me cuno baki tana fitto wato feduwa. Suna isa trafficking jam, aka tsayar da motarsu. “Yan majalisar dokokin Keivroto suke wucewa a guje, sai da suka gama wucewa aka sake su. “Uwardakina ga motar Mr Amjad can.” Kallon motar tayi, ta tab’e baki tana cewa. “Su suka sani” haka suka nufi Queen Elizabeth road. Kai tsaye wani katafaren Company suka nufa, sai hada hada ake kamar ana cin kasuwa a kofar Company. A hankali suka sulalle cikin compound na cikin kamfanin, suka yi parking a inda ake ajiye motoci. Sauka tayi Black ya mika mata jakarta Charles & Keith, a hankali ta maka a kafad’arta, tana tafiya ana bin ta da idanun. Saman building na kamfanin an rubuta, S….. digital art, tana isa bakin kofar aka bude mata kofar a hankali ta cusa kanta cikin building ɗin. Ware idanunta da suka sha tozali tayi tana kallon around na building. “Miss Zeenobia Nasr Hadejia!” Gyada kai tayi tana murmushi. “Kizo tare da ni ” gyada kai tayi, sannan ta bi bayan matar da take sanye da dangalallen skirt iya gwiwanta. Elevator suka shiga ita da matar tana mata murmushi. Tana ganin matar ta danna number 9, a hankali yake walking around, tsayawa yayi aka bude shi, wasu yan mata ne suma ma’aikatan kamfanin. “Good morning Mss Mary!” “Morning helima morning Faither!” “Mss Mary an kawo sabuwar employee ce?” “Yes!” Dake babu wasa a fuskar Mss Mary yasa basu fadi abin da yake ransu ba, but sun kagu da su yi gulmarta domin azabar kyan diri da cikar halittar Zeenobia Nasr Hadejia wani abu ne da dole sai kaji a ranka. Infact there never met mace irinta ba. Suna isa floor dinsu suka fita, “sai an jima Mss Mary” tab’a juna suka yi bayan fitar su. “Ke she look familiar?” Inji Helima, zaro idanu Faither tayi tana faɗin. “Really?” “Eh na santa, but na manta inda na san fuskarta but na santa.” Floor 9 suka isa, a hankali kofar ta bude, suka fito rights side suka nufa, tare da Mss Mary. A hankali suka isa wani kofa, Ciro card ɗinta tayi ta manna a jikin security door din ya bude, “waw” ta fada a kasa makoshinta, wani azazzben Office ne me masifar kyau da ɗaukar idanu. “Good morning Sir.” D’ago kai yayi, ya amsa da “morning Mss Mary! Zeeno barka da zuwa ” ya fada yana jin zuciyarsa da ransa ya biya da siffar yarinyar da take tsaye a gabansa, “moni sa” inji Zeeno, murmusawa yayi ya ce. “Mss Mary zaki iya tafiya ki turo min Mr Salim” “okay sir” mikewa mutumin yayi, yana faɗin. “Zeeno zauna, coffee ko caffeine ko tea?” “Coffee mara sugar!” Ta fada tana kallonsa. “Waw baki son kiba ko?” Murmushi tayi tana kallon office din.”muna farincikin zuwarki wannan kamfanin me albarka, wanda muka bude ta kasa da mako shida. Sai dai har yau tana nan a yadda muka bude ta.” Ya mika mata coffee ɗin, kallonsa tayi irin like how, ya ce mata.”tunda muka bude ta muna bukatar masu daukar nauyin da wasu tallace-tallace kana da masu zuba hannun jari.” Bude kofar aka yi wani kyakyawar matashi me tsawo da cikar halittar irinta maza ya shigo, ya ce musu. “Barkan ku.” “Barkar dai Salim, ga Zeenobia Nasr Hadejia, Zeeno Xnoo Yar kunama ko?” Murmushi tayi ta daura daya a kan daya. “kwarai da gaske!” “Nice to meet you!” Inji Salim yana mika mata hannu. Itama mika mishi hannu hannu tayi, sannan suka sake hannun junansu. “Zauna Salim.” Sauke numfashi MD na kamfanin yayi ya ce mata. “Mr Amjad ya bani labarinki, shi yasa muka ga dacewar mu baki matsayin me mu’amala da bakin mu da gayyato mana su, ta fuskar Kasuwancinmu.” Hàdiye yawun tayi ya ce. “Ni kuma ya gaya min cewa, zaku bani aiki ta ɓangaren security service, domin shi ya dace da ni.” “Haba Xno ba zamu dauke ki a matsayin wacce zata yi harkan tsaro ba, domin muna son kamfanin mu yayi achieve successful abubuwa Bama fatan wani abu mara dadi ya faru da mu, i hope you understand what I mean?” Tana jin abin da ya fada da turanci amma ita da ta tsani turanci taya zata iya rayuwa da abin da bata iya ba, babu boye -boye ta ce mishi. tace, “ba laifi idan kun bani shugaban security service. Hatta bera ba zan bar shi yayi shigo kamfanin nan ba, amma wend kuke ce min meka sifiki Ingilishi yu get rong idia, bikus na tsani Ingilishi ani mo!” Ta fada tana daukar jakarta. “Zeeno You can did it, zauna.” “Sa kake ko saniya nace bana jin Ingilishi, i sa i no Ingilishi meye sai ma zauna da ku dole? Dalla ku bani wuri.” “Idan baki amsa ba, zan kira Mr Amjad na gaya mishi, sannan zamu sauya miki damar haka, ko baki son rayuwar mutanen cikin al’umma charity House ya sauya ne? Zamu baku fili a gina muku makaranta da Asibitin da zai na kula da ku, sannan zamu dauki Abbas aiki a bangaren software!” Duk wanda ya zauna da Zeenobia Nasr Hadejia yasan Al’umma charity House da Abbas sune weakpoint, shi yasa suka kara tab’a inda take da yakinin aka. “zamu sauya miki rayuwa ki karbi aikin mu…”
*Barka dai Ya kuke ya kwana dayawa! Gamu nan Top-notch mun dawo i hope zaku amshe mu hannu bibbiyu*
#Zeeno
#Beauty
#Beast
#RomanceS
#Tycoon
#WeatherMan
#Top-notch
#Jelousy
#Cursed
#Mai_Dambu
[8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: *CINIKIN RAI….*
Mai_Dambu
BOOK ONE
002
Tsam tayi da ranta tana kallonsu, kafin ta mike tana faɗin. “Zanje nayi nazari amma yanzu kan ba zan yanke hukunci kai tsaye ba.” Kallon juna suka yi, ai ba haka Mr Amjad ya gaya musu ba, ya gaya musu rauninta ne al’umma da Abbas, amma bai gaya musu cewa tana da kafiya da ra’ayinkanta ba. Har ta fita a cikin office ɗin, babu wanda ya samu arzikin ce mata cikanki domin baki daya yanayinta ya sauya. Tana fita daga office ɗin, kiran Mr Amjad MD na kamfanin yayi ya ce masa. “Yarinyar nan bata yarda da matsayin da muka bata ba, asalima taki amsa fa, sannan nayi amfani da rauninta na gaya mata amma yarinyar taki amincewa sai tayi tunani.” Ajiyar zuciya ya sauke na cikin wayar ya ce. _Ka da ka damu, haka take zan ji da kome!_ gyara zama MD yayi ya ce mishi. “Kuma dole sai ita ne? Babu wasu yan matan ne?” _Itace kawai zata mana yadda muke so, ita ce zata iya daukar wasu abubuwan, kasan me? Ita din zamu yi amfani domin cimma manufar a yanzu gani muna tattaunawa da wasu kamfanoni amma babu alamar zasu amince, don haka ka lallabata domin zata mana amfani!_ “ok Sir!” Ya kashe wayar da sauri ya dauki wayar landline na kamfanin yayi kirà da shi. “ku kira min yarinyar nan!” A lokacin da kiransa ya isa office din Mss Mary da sauri ta fito ta fara niman Zeenobia. Kiran dakin tsaro tayi ta ce musu. “Ku duba min Zeenobia ta fita ne?” “Ok ma” kamar minti uku suka ce mata, “tana cikin elevator nan minti goma zata iso” “okay” ta nufi kofar elevator ɗin ta tsaya, sai kallon agogon hannunta take, tana jin kamar har lokacin zai wuce Zeenobia bata iso ba. Minti goma ciccib kofar yana budewa. Ajiyar zuciya ta sauke. “Zeenobia inji yallabai wai ki koma, tuntuni nake jiranki.” “Amma ai mun gama magana da shi me kuma yake bukata?” “Please muje.” Haka ta koma cikin elevator ɗin.
***
Daga cikin yan majalisu da suke karkashin jam’iyyar PKO, power Keivroto Own, tare da yan jam’iyyar CDL, civilian democrats labor, sai wasu manyan masu ɗauke da kamfanonin ƙasar musamman yankin Keivroto, gefe guda kuma wasu dattijai ne na musamman da suke zaune cikin shigar alfarma. Tare da wani dattijo da ya haura shekaru hamsin da wani abu a duniya. Shiru dakin ya dauka, sai kallon juna ake cikin fushi da fusata. “Dake an mai samu sakarkaru, babu wani labari daga ɓangarensu fisabilillahi a haka za a zauna lafiya? Tuntuni Khuldu Jahid Khan yake nan zaune, a ƙalla a girmama shekarunsa taron bunkasa tattalin arzikin Keivroto zai tafi amma aka dakwafar da shi a nan, anya akwai adalci cikin lamarin ku? Nace akwai adalci? Gaskiya duk wanda ya shirya wannan taron, ya shirya taron shan shayi ne domin Malik…” Bude kofar da aka yi yasa bakisaya suka mai da hankalinsu kan kofar, haka yasa shi kansa azagwaigwaidu da yake magana yayi shiru, ajiyar zuciya wasu daga cikin mutanen da suke wurin suka dauke, cikin girmamawa suka mike. Hatta masu hayaniyar da jami’iyyar adawa ta CDL su kansu mikewa suka yi, ban da Khuldu Jahid Khan da yake zaune fuskarsa bata yi na’am da zuwan mutumin ba, dauke kai yayi yana rike da sandar dogarawa. Dauke kai yayi yana kallon gefe har mutumin da ya shigo ya samu wuri ya zauna, sannan ya ce. “Ayi min afwa kusan dukkan mu, babu wanda zai so b’atawa wani lokaci. On be half of Khalquz Zaman muna bada hakuri.” “Yallabai Elbashir Jamal Arab mun yi hakuri, me yafi haka a gayawa Mayor muna jiransa an shirya mishi shagali ba musamman.” Murmusawa yayi ya ce. “Ayi hakuri Mayor ba zai samu halatta ba….” “Taya zai samu halartar taron da kowa da kafarsa zai zo? Shi kuma a keken guragu?” Inji mutumin ɗazun da yake ta b’ab’atu. Murmushi Elbashir Jamal Arab yayi sannan ya ce. “Da alamu ba karamin shan kaye kuka yi ba, da har yau baka manta rad’d’in da ya same ku, al’ummar Keivroto sun tsaya ka’in da na’in sun zabi abin da zai gina su ne, ta fuskar Kasuwancinmu, don haka abin da ya kawo mu nan shi ne, a tattauna a wuce wurin ina da trip to China!” Zuciyar Khuldu Jahid Khan ya buga, ‘ba dai wani abu Malik Menk Jordan zai kuma kullawa da gwamnatin kasar China?’ wannan wani irin mutum ne? Wani irin sa’a gare shi? Dole na ga karshen Malik Menk Jordan.
“Prime minister, ka saka baki Malik Menk Jordan ya barwa wasu daga cikin yan kasuwa damar yin kayayyakinsu a kasar nan, Malik Menk Jordan bafa dan kasa ba ne; kowa yasan cewa bakon haure ne, sannan Shugabana Khuldu Jahid Khan yana da shaidun gani da idanun da suka tabbatar Malik Menk Jordan dan ta’adda ne da yake, amfani da dukiyarsa yana kashe mutane, tare da tilasta musu karban bashin da zasu kasa biya.” Mutumin da aka kira da prime minister ya zubawa Elbashir Jamal Arab idanu ya ce. “Elbashir Jamal Arab ya haka? Abin da yake faruwa kenan?” Murmusawa mishi yayi sannan ya ce. “Mr prime minister dayawansu a nan, sun san Malik Menk Jordan, shima kuma yasan su, wasu kuma sun yarda da shi. Shima ya yarda da su. Malik yana da goyon bayan yan majalisu kusan 108, yana da sahalewan yan jam’iyyar PKO, sannan yana da hadin gwiwa da kwamishinonnin jahar nan, uwa Uba ta fuskar Kasuwancinmu muna da kyakkyawan alaka da wasu ƙasashen idan ayi dubi da yadda garin Keivroto city yake gabbatar ruwa. Mr prime idan har aka ce za a fito da abin da suke bukata, ai Malik bai yiwa mutanen da suka yi nominations dinsa izuwa matakin Mayor ba, taya zai yarda da muradunsu bayan shima yana da tasa muradun?” Mikewa Azagwaigwaidu yayi cikin fushi ya ce. “Prime minister a sake kidayan kuri’a Yallabai Khuldu Jahid Khan ya ci ba Malik Menk Jordan ba, mutumin banza kawai, dan luwadi waye bai sani ba, kaf gidansa babu Y’a Mace, wanda kowa yasan cewa Yallabai Khuldu Jahid Khan gidansa mata uku ne, Yara mata babu wanda yasan adadinsu, ka gayawa maigidanka kar yayi asarar kwayayyensa a ta baya, ya nimo ko karuwa ce, ta haifa mishi hana gori.” Gyara zaman tie dinsa Elbashir yayi ya zuba masa idanu, kafin ya ce mishi. “Na maka uzuri ni tarbiyyar Malik Menk Jordan ne, ya haramta min cin zarafin kowa.” Jin haka mutumin ya buɗe baki zai magana, Mr Khuldu Jahid Khan ya ce mishi. “kul!” Shiru yayi sannan ya cigaba da cewa. “Me yasa Malik ba zai yi show up ba?” Gyara zama Elbashir yayi ya ce mishi. “Meye matsakarka da show up dinsa, kome yana tafiya yadda yake, Kasuwancinmu da siyasar mu, tow kai me kake bukata anan?” “Wadancan mutanen!” Ya nuna mishi mutanen kusan su goma a zaune. Tabbas sun zo kwanaki uku da suka wuce, akan Mayor Malik Menk Jordan ya saka hannun jari a kamfanoninsu, sannan zasu mishi biyayya. Wato da suka ki amsar buƙatarsu shi ne, bari su dawo nan. Dariya yayi ya ce mishi. “Khuldu Jahid Khan!” Rintsa idanun yayi. “Amma Elbashir baka da kunya shugaban mu kake kira kamar, abin wasan ka?” “Kai kare bada kai nake ba, da ubangidanka nake, idan ka sake na kuma jin tashin muryanka sai na datse harshenka” juyawa Elbashir yayi ya cigaba da cewa. “Saura kiris da kunyi kuskuren amsar, dukiyar Mayor Malik Menk Jordan, da sai kun yi danasani, a yanzu ma ba kyale ku zamu yi ba, zaku biya zunubanku. Sannan shi wanda kuka daura yarda akansa bai gaya muku karon battarsa da Mayor ba ne? Ya gaya muku sanadin da yake dogarawa da sanda, Mr prime minister na gama jawabi, babu wani dan kasuwan da zai bude wani kamfani matukar Mayor Malik Menk Jordan yana numfashi ba zai lamunci haka gasa ba.” Yana mikewa, yan majalisunsa suka mike suma suna masu taka mishi baya, dayawan basu san Malik ba, kuma duk matsayin da suke da taimakon sunan Malik suka isa wurin, Idan aka ce maka Mayor Malik Menk Jordan tow, hantar sadaukan maza bari take. Domin tsaf dattijan Keivroto ba karamin tsoronsa suke ba, uwa uba ka tab’a mishi dukiyarsa sunanka shekakke.
Haka suka fito tare da raka Elbashir Jamal Arab airport, sai da ya haura jirgi sannan suka juya, wannan shi ke kira Powerful. Domin iya Elbashir yana taka muhimmiyar rawa koda Malik baya wuri.
Bayan fitar Elbashir. Jifa da kome na dakin taron Mr Khuldu Jahid Khan yayi, yana faɗin. “Sai na kashe shi, shekaru arba’in da shida kenan ina niman hanyar da zan kashe dan shegiya bakon haure, ɗan cirani!” “Yallabai wannan al’amarin, kasan cewa babu wanda ya isa karya Malik, kuma koda kuwa za a hada sama da kasa ne, babu wanda zai iya karya shi. Sannan idan kace zukatan al’umma zaka saya, ba zaka tab’a sayan tsoron da yake cikinsu ba, su ba zaban Malik suka yi ba, labarin abin da yayi kawai suke dubawa. Idan har akwai hanyar da zaka bi dole ka bi. Sannan rigimarka da Malik kar ya shafi Kasuwancin wadannan bayin Allah domin basu ji ba, basu gani ba.” Tsamo tsamo Mr Amjad yayi kutumar Uba, wato labarin Malik da yake ji, ba kome bane sai da Elbashir yazo yasan waye Malik shi baya tare su, amma anyi mishi abin da yake bukata. “kuma da ace Malik ne yazo da kansa, kana tsammanin ba wanka zai yi da jinin Daylam Yunis ba, kai ya dace ka koyawa mutanenka girmama kai, su daina zakewa. Bani manta shige asirin baya idan Malik yazo da yaron nan, baya tab’a yin tari matukar ba Malik ne ya bashi iznin yin haka ba, kai kuma saboda dalilinka kasa kowa ya zama me damar magana, kai idan har baka yi a hankali ba, sai ka ɗaure kanka. Kayi kokarin niman hanyar da zaka kadda Malik ni kuma zan tsaya maka har sai ka kadda shi. ” “Shi kenan.” Ya fada yana kurban ruwan zafi. Fita prime minister yayi, kiran wayarshi aka yi, p.a dinsa ya mika mishi. Jikinsa ne ya dauki mugun rawa, ya kasa dauka ji yake kamar zai fadi. Har suka kusan isa motarsa sai da ya shiga cikin motar ya dauki kiran. “Ranka ya dade.” _Kayi kuskure Prime minister, sauka lafiya_ kashe kiran aka yi, wasu mutane da ba asan daga ina suke ba, suna zuwa suka budewa janye p.a da driven, suka budewa motar prime minister wuta, sai da suka tabbatar da ya kama da wuta, sannan suka wuce a babur dinsu.
Lokacin dasu Mr Amjad suka fito, ganin motar prime minister duk da jami’an tsarosa bai hana a kashe shi, an tashi motar da wuta ba, take duk suka juya kowa ya cikawa bujensa iska, wannan tashin hankalin ba karamin firgita Mr Amjad yayi ba dole tasa ya koma kamfanin S digital art. Yana shiga bai tsaya parking me kyau ba, ya nufi cikin kamfanin, a firgice yana ji kamar ya tsula fitsari a jikinsa. Kai tsaye elevator ya shiga, sai da ta ganshi cikin ya tabbatarwa ya tsira, ya sake ajiyar zuciya. “Wannan wacce irin masifa ce, taron dangi akan Mayor Malik Menk Jordan ba shi ne mafita ba, tabbas.” Wayarshi ce ta yi gunji, sai da ya zabura, kamar zai gudu kafin ya tuna ai wayar shi ce take tsiwa domin da zasu shiga taron ya sakata a gunji. Dauka yayi yana faɗin. “Hello!” _Kada ka karya da abin da ya faru, ai dama ba iya nan ne shirin ba. Ka fahimta ko_ “Ni wallahi da zaka cire ni a cikin wannan lamarin da naji dad’i, Tunda aka iya kashe babban minista akan idanunmu, bamu iya me kake tunanin zai faru? Ku shafa min lafiya” ya kashe wayar, yana isa floor 9 ya bude kofar, jikinsa yana rawa ya nufi office din MD, kamar wanda aka koro shi ya isa office din, “ku bani ruwa ina jin ƙishirwa ne” mika mishi ruwan Salim yayi, sai da ya shanye ruwan tass, ya nime kari. “Sir lafiya?” Ajiye goran yayi ya ja kujera ya zauna, duk suka zuba masa idanu. “Zeeno baki tafi ba ne?” Mikewa tayi tana faɗin. “Eh Yallabai Amjad. ” Sauke numfashi yayi ya ce. “Hussain wani matsayi take bukata ma?” “Security service!” “Ya miki haka?” “Eh yallabai!” Kallonta yayi ya ce mata. “Zeeno naso na baki matsayin da zaki na, nimo mana manyan mutane suna saka hannun jira ni a kamfaninmu, na sha gaya miki ke kyanki shine jarinkie, akwai mata dayawa da suke niman matsayin da kika taka, Zeenobia idan har kika amshi security service, harajin da gwamnatin jahar Keivroto take amsa a hannunku duk wata ba zai kai ba, zaki cigaba da bangar siyasa ne? Shekarunki nawa?” Sunkuyar da kai tayi kasa ta ce mishi. “Ashirin nake!” “You see! Kiyi amfani da damarki, akwai Mss Mary zata hadaki da Dauduwa, ta kware a fannin sauya salon mutum da fasalinsa, albashinki dala dubu dari uku, kudin US. A cikinsa zaki samu dala dubu hamsin ki biya kudin haraji, me ya fi miki.” Juya idanu ta yi, ta ce mishi. “I,m satifai, idan har zaku bani dis moni, I kan do anitin!” “Yes good gurl yanzu ya yarda zaki iya, tunda kika yi magana da turanci, Hussain bani list na sunayen nan!” Ciro mishi kundin yayi ya mika mishi, a hankali ya bude yana kallon shi. “Ikon Allah kace har ka tura baki daua saura daya ne kawai ya rage?” “Yes Chairman na tura baki daya, wanda ya rage na Mayor Malik Menk Jordan ne!” Sarawa kanta yayi, ta dafe da karfi. “Lafiya!” Suka tambaye ta, “lafiya lau! Zan tafi.” Mai da kundin yayi ya ce mishi. “Ajiye akwai dayan fa na baka, bani na bata!” Bude drower din yayi ya dauko mishi wani kundin. “yawwa Dauduwa zata gayyace ki, ga wannan su zaki fara jaraba sa’arki akansu.” Juya Idanunta tayi ta ce mishi. “Wancan na farkon fa da ka mayar da shi?” A razane ya ce mata. “Wancan ai konawa zamu yi, kai Salim dauka ka je ka kona, kunna mana tv ta ji abin da yake faruwa, sunan da yake jikin wannan kundin bala’in duniya ne da tashin hankali ke yarinya ce, da babu ruwanki. Kada ki tsoma ranki da zuciyarki cikin wannan lamarin. ” Murmushi ta yi ta ce mishi. “Tow amma kada ka kona, bari na ga yadda zan ji da wadannan zan dawo kansa.” “Anya zaki iya?” Kunna tv aka yi ta juya tana jin labarin. _A yau garin Keivroto city ya tashi da mummunan al’amari da rabon a fuskanci haka tun shekaru talatin da suka wuce, lokacin kashe Mr Jahid Khan mahaifi ga Mr Khuldu Jahid Khan, me manyan kamfanonin hakkar ma’adinai, kuma Uba ga jami’iyyar adawa ta CDL civilian democrats labor, bayan nan ba a kuma samun tashin bom haka ba, sai dai shaidun gani da idanu sun ce wasu matasa hudu suka gani da babura, inda suka sauka suka idda mugun nufinsu, tare da kashe Mai girma Prime minister, a halin yanzu ana danganta mutuwar da Shahararren attajirin ɗan kasuwa, mai girma Mayor Malik Menk Jordan, wanda aka tabbatar da cewa anyi taron nan ne domin a kawo karshen mulkinsa inji wata majiya. Idan baku manta ba, Mayor Malik Menk Jordan shine mutum na farko da yake da kashi casa’in a na kamfanonin a garin Keivroto city, sannan yana da sahalewan shuwagabannin Kananan Hukumomin ɗari da shida, bayan nan dan kasuwa ne da ake zarginsa da hamdama da babakere, ga abin da wani ganau yake fada_ sako wani murya suka yi. _Gaskiya idan ka cigaba da barin Mayor Malik Menk Jordan yana abin da ya gadama, wata rana Keivroto city zata zama makabartan binne mutane amma ace babu wanda ya isa taka mishi burki sai abin da yaso, fisabilillahi taya za a rayu?”_
Kashe tv Salim yayi ya ce. “Da ina jin labarin Mayor daga nesa ne amma yau da naji ya kashe prime minister na yarda mutumin nan shaidani ne, Zeenobia Kinji ko?” Kallonsu tayi tana faɗin. “Ya naga kun razana, shi ne ya baku tsoro? Ni kuma gani nake ba kome ba ne.” “Ke ki raba kanki da masifa Mayor Malik Menk Jordan ba kanwar lasa ba ne……
Zeeno
#Beauty
#Beast
#RomanceS
#Tycoon
#WeatherMan
#Top-notch
#Rumors
#Jelousy
#Cursed
#Mai_Dambu
[8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: *CINIKIN RAI……*
Beauty and the beast♡
Mai_Dambu
BOOK ONE
003
“Mr Amjad!” “ Kiyi abin da na saka ki, babu ruwanki da Malik Menk Jordan, idan da kin ga abin da ya faru, ba zaki fara shiga wannan lamari ba. Kowani mutum yana da iyakarsa don haka ki tsaya iyakarki” kallon shi tayi na wani lokaci, kafin ta ficce daga office ɗin, lallai tana son sanin waye shi? Me ya taka har haka da kowa yake jin shakkarsa haka. Tana fita Mr Amjad ya kalli MD da Salim. “a firgice nake, ina ga zan zauna a kamfani na tsawon kwanaki, domin Malik ya manta da ni, idan ba haka ina fita qur’ani kashe ni zai yi.”
Shiru sukayi kowannen su, da abin da yake yawo a ransa, kafin Salim ya ce masa. “Yallabai me yasa ka razana haka ne? Ni fa bana tunanin Malik ya kai yadda kuke fada, kawai kashe prime minister yayi haka ne domin ya cusa muku tsoro da firgici. Kuma yayi nasarar haka” juyar da kai Mr Amjad yayi yana kallon window waje. Kafin ya mike kana ganin yadda fuskarsa ta nuna zaka fahimci yana cikin damuwa soka hannunsa yayi cikin aljuhun wandon ya ce.
“Tabbas rayuwar tana tafiya da yadda mutane suka tsarawa kansu, amma rayuwar da Malik ya tsarawa kansa, yafi kowacce rayuwa bala’i.” Kallon juna MD da Salim suka yi kafin suka mai da hankali kan Mr Amjad.
Kuma aka rasa waye zai magana, wayar Amjad ne yayi gunji. Kamar ba zai dauka ba, ya dauka.“Amjad Lamid ne?” kamar wanda aka watsa mishi ruwa haka ya amsa da cewa. “Eh ni ne, waye” “Na kira ne, na baka shawara kada ka sake shiga abin da babu ruwanka tsakanin Malik Menk Jordan da Mr Khuldu Jahid Khan”
“Amma waye kai?” Mr Amjad ya tambaye shi, murmushi me sauti na wayan yayi sannan ya ce mishi. “Sani na bai da wani amfani, amma zan baka shawara ka nisanta kanka, daga wannan hatsaniyar Malik ya fi ku hauka, a duk lokacin da ya fahimci kana cikin masu niman shi sabga shi.” ya fada mishi yana kashe wayar.
Wani azzababen tsoro ne ya mamaye zuciyar Mr Amjad, ilahirin jikinsa rawa yake, yadda zaka fahimci, yana cikin tashin hankali. “Sir akwai matsala ne?” Kallon MD yayi da ya tambaye shi, sannan ya ce mishi.
“Na jima ina Kasuwancina, ban tab’a shiga tashin hankali irin na yau ba, amma qaddara sai da ta haɗa ni hanya da Malik Menk Jordan, a da wai-wai nake shi a yau da na gani da idanuna na tabbatar shi din ba kanwar lasa ba ne.”
“Sir wai mene ne matsalar ne?” MD da shima yake razane, domin daga yadda Mr Amjad yake firgice zai tabbatar maka da cewa yana razane. “Ban san kaddaran da ta hada ni da Malik ba? Amma nasan mutuwa ta ce ta kusa bayan haka” kura mishi idanu suka yi. Sannan ya cigaba da cewa. “Idan har kuka ji labarin na mutu don Allah ku saka idanu akan iyalina.”
Su kansu a rude suke, domin kuwa labarin mutuwar Prime minister ya ratsa lungu da saƙo na cikin garin Keivroto city.
^^^^
A lokacin da Zeenobia ta bar S….. Digital art, ta nufi hanyar gida da mutanenta, a nan ne ta fahimci garin ba lafiya domin duk inda suka wuce zanga-zanga ake wanda zai nuna maka, alamar kowa a fusace yake, ko da yake ai ba kowa bane domin wannan rigimar ba don talaka aka yi ba, suna yi ne domin kare muradunsu da aljuhunsu. Duk wanda zaka gani tow ba yana yi don talaka ba ne, yanayi ne domin cikawa aljuhunsa yan canji.
Ajiyar zuciya Zeenobia tayi tana kallon yadda ake fashe-fashe, babban burinta su isa Al’umma charity House, domin kare wannan gidan hakkine da ya rataya akanta, ba iya ita ba, ga duk wanda yake numfashi a cikin gidan. Domin ganin yadda yan zanga-zanga suke barnan dukiyar gwamnati, yasa ta kalli black ta ce mishi.
“Ka taka motar, mu isa akan lokaci domin za a iya saka curfew nan da wani lokaci.”
“An gama Yar kunama!” Ya kuwa karawa mutanen gudu, cikin ikon Allah suka isa gidan cincirindon jama’ar gidan a bakin get din gidan yasa ta sauke ajiyar zuciya. “Yar kunama!” Sauka tayi daga motar tana kallonsu. “lafiya kuka yi cirko-cirko?” ta tambaye su, tana cire glass din idanunta. “ina zamu iya nutsuwa mun ji labarin gari babu lafiya, ke kuma da su Dundurosu kuna waje.” murmushi tayi ta wuce bakin get ta ja kofar tare da rufe kofar gidan bakidaya. “ina son nayi magana da murya daya, kowani lokaci za a iya saka dokar tab’aci, ban lamunci wani ya ketare gidan nan ba, idan na fahimci haka ya faru hmm.” ta fada tana haurawa sama.
“Didih wai da gaske Malik Menk Jordan, shaidani ne?” juyawa tayi ta dauki yarinyar da bata wuce shekara uku ta shiga tafiya da ita. “Sweetheart ban sani ba, Shaidani ne ko mutumin kirki ne, abin da na sani ya kashe Babban mutum me daraja.” ta fada tana shafa kanta.
“Didih Abbana ya ce wai shaidani ne, shine Iya tace kar a bari kiji labarin kome.” juyawa tayi ta kalli Iyar da ta mata yake. “Iyah sun fadi wani abu ko Sweetheart?” Gyada kai tai, sannan ta wuce kofar dakinsu yarinyar ta ajiye ta, sannan ta wuce ɗakinta, kafin ta bude ta samu Hafsy tana dakin. “Alhamdulillahi kin dawo lafiya” kallon juna suka yi, sannan ta wuce ban daki. Sai da sauya kayanta, sannan ta dawo falon dakin. Bude karamin firji tayi ta dauki abin sha, ta zauna tana me kunna TV. “Ni tsorona daya kada wani abu ya same ku, sai gashi kin dawo akan lokaci.” kurban fanta tayi tana kallon tv.
_Izuwa yanzu hukumar sun saka dokar curfew na tsawon awanin kafin a gama binciken mutuwar mai girma Prime minister._ gidan tv suka fada, rage ƙarar tayi tana faɗin. “Ban san wacce duniya muke ba, amma kuma.” saukowa daga gadon Hafsy tayi, ta rike hannunta. “Meke faruwa?” gyara zama tayi sannan ta ce mata. “Aikin da aka ba ni, wai zan na gayyatar mutane su saka hannun jari a kamfanin na zata security service zasu bani.” ta fada tana sauke ajiyar zuciya.
“Tir security service? Allah ya sauqaqe miki. Ai wuce wannan level din, matsayinki ne. Zaki kara zama yar gayu eyee!” ware idanu tayi, tana gyada kai kafin ta ce mata. “Hafsy ina son aikin amma kuma.” sai da ta sauke ajiyar zuciya me nauyi, wanda zai tabbatar maka tana cikin damuwa. Kafin ta cigaba da cewa. “ina son aikin amma kuma, gani nake kamar akwai kasada. Domin ban saba harka da mutane ba, taya zan iya bibiyar mutane don su saka hannun jarinsu. Ala misali wani abu ys faru nice a ciki fa.” rike hannunta hafsy tayi tana faɗin. “ina ji a jikina zaki yi nasara, matuƙar aka samu matsala tow dauke shi a matsayin jarabta, bayan nan kuwa labarin zai sauya.”
Kurawa Hafsy idanu tayi tana, ta kasa kiftawa. Kafin ta ce mata, “ni kuwa gani nake kamar wani abu zai tafi ya dawo. Bana son abin da zai d’aga min hankali!” Dariya Hafsy tayi tana fad’in. “Ni kuwa gani nake ba wani abin da zai faru, domin kuwa khair in sha Allah.” Ajiye tin din fanta din tayi tana cewa. “Allah yasa.” Daga nan suka bude hirarsu.
ΠΠΠ
A cikin Keivroto city kuwa, rikici ake wanda ya haifar da kona-kone, wanda yasa dole jami’an tsaro suka shiga kame mutane, don kuwa barnan tayiwa. Kuma take-taken mutane shi ne nufar manyan masana’antun Menk Jordan manufacturer’s, don haka aka zuba matakan tsaron ko ta kwana. Sannan aka bada umarnin duk wanda ya isa wurin a tashe shi.
——-
Public Officer For Legal Investigation and Criminal Emergencies stations Keivroto city (Police stations) fitowa jami’an yan sandan suke da sauri. “Ya ku jami’an tsaro, ku sani a yau garin Keivroto yana fuskantar tashin hankali da barazanar barkewar rikicin siyasa da kabilanci, sakamakon mutuwar Prime minister, Zubair Fatihu Sayyad! Don haka a cikin sanarwar da muke samu ya tabbatar da cewa manyan kamfanonin Mayor Malik Menk Jordan, yana fuskarta barazana don haka dole zamu kwantar da tarzoman da ake yi, sannan mu tabbatar mun kare takalawa da dukiyar al’umma da gwamnati.”
“Yes Sir” suka fada lokaci guda, kafin su rufe baki sai ga wasu manyan motocin Hilux 4×4 bakake wuluk har guda shida. Hankalinsu ne ya tsaya akan motar. Suna yan sanda ne suka fara fitowa a motar da bayan motar. Kafin suka budewa bakar audin da take tsakiyarsu. A hankali aka sauko kafa, sannan ta fito sanye da bakar madubi. Sara mata aka shiga yi, ta fito rike da sandarta, tana me zare glass din daga idanunta. “Barka da zuwa Asp Zulfa!” Nufar cikin Office din yan sandan tayi tana faɗin. “Ku tattaro min baki daya yan sanda office din nan, da na sauran yankuna baki daya, ina son ganawar gaggawa. ” “Yes Ma” suka fada mata, kafin minti Talatin, bakidaya sun haɗu. “Barkanku jami’an tsaronmu. Duk da a kurarren lokaci na iso, ayi kokarin rubayyan tsaro da kwantar da hankulan al’umma, sannan a tabbatar an saka shinge ga wasu wuraren kafin zuwa gobe, kafin nan a tabbatar an kama duk wani me tadda hankalin al’umma, umarni ne daga sama ba umarni na wa ba ne.” ta fada tana kallon kayan sadarwan. “Akwai dakin tsaro?” “Eh ma!” Gyada kai tayi tana faɗin.
“Ku kai ni dakin na ga yadda kulawar garin take, za a turo jami’an tsaro daga Gista nan da awa ashirin da huɗu, sannan ina
son na je inda gawar Mai girma Prime minister yake!” “Yes ma, gawar Prime minister tana, trust palace hotel. Anan suka gabatar da taron.” dakin tsaron suka kaita, kai tsaye ta umarci a fara aikin binciken wucin gadi.
Daga nan, hotel inda aka yi zaman suka wuce. Cikin gari aka kara baza jami’an tsaro, inda gawar Prime minister suka inda aka saka zaren criminal scenes. A hankali suka tsallaka wurin, leda suka bata a ta saka a cikin takalmin, sannan ta amshi handglove, kafin ta wuce. “Ma baki saka facemask ba!” “Ok officer” a hankali ta shiga zaga motar, tana gefenta wani dan sanda ne, yana rubuce rubuce. Sai da suka gama zaga motar kafin ta bude motar inda prime minister yake zaune. “ina masu binciken gawar me suke samu?”
“Gasu nan” mikawa juna hannu suka yi, sannan ta ce mata. “Khairat Hadi, nice na jagoranci binciken gawar prime minister, sai dai rashin ƙwanciyar hankali yasa ban gama ba, na koma gefe domin kuwa akwai abubuwan da ya faru. Bayan zuwanmu.” gyada kai tayi tana faɗin. “Ok gba damuwa, yanzu sauran binciken dole sai kun wuce da shi office din ku ko?”
“Eh haka nake son na gaya miki!” kallon hotel ɗin take, tana me gyada kai kafin ta ce. “Akwai Cctv a cikin hotel din nan, daga shigowa zuwa nan harabar guda shida ne, don haka a nad’e mun duk wani bayani da aka shigar na wata shida baya, har zuwa yau. Sannan a kai ni dakin da aka yi taron.” “Tow muje ma” haka ta shige har cikin hotel. Ganin yadda ma’aikatan hotel suke cikin damuwa. Murmusawa musu tayi tana faɗin. “kada ku damu, aikin mu zai yi shi ne bisa goyan bayanku. Sannan idan muka gama, zamu tafi.” Inji dan sandan da yake bin bayan. Shiru tayi tana kallon fuskar mutanen wurin. Kafin ta ce musu. “A wani daki aka yi taron?”
Fitowa Manager din hotel din yayi, yana fadin. “Sunana Nuhu Kasim, ni ne manager na hotel din, muje na muku iso cikin dakin taron.” gyada kai tayi, suka shiga cikin hotel ɗin, sannan suka fara zaga cikin dakin taron. “lokacin da aka gama taron baki daya suka fito ko daya bayan daya suka fita?” girgiza kai yayi ya ce mata.
“Mr Elbashir Jamal Arab ta fara fita, tare da yan majalisunsa, sai Prime minister.” kallon shi tayi tana kallon agogon hannunta. “an samu minti nawa a tsakaninsu?” shiru yayi yana kallon sama kafin ya ce mata. “Za a kai minti Talatin zuwa arba’in!” gyada kai tayi tana cewa. “Ok ina son zan duba dakin da Cctv din ku yake.” “Ok Ma” da ya fada, tare da yiwa ɗan sanda da suke tare jagoranci har dakin. Ita kuma ta cigaba da zaga dakin taron tana kallon wurin.
Har yamma suna zaune a wurin, kafin karfe uku garin yayi tsit, a hotel ɗin tayi salla, sannan suka koma office dinsu. Anan ta ga an kama mutane dayawa, wasu yan jagaliya ne, kallonsu tana faɗin. “waɗanan sune aka kama ko?” “Yes ma!” wucewa Office dinta, ta nufa tana me zama a kujerenta. “Ma ya zamu yi da su?”
“A rufe su, kada a ba da belinsu, a tura su ga kotu.” shiru yayi kafin ya ce mata. “ Ma akwai mutanen Xno kuma ba a kama su da laifin tadda zaune tsaye ba, kawai dai sun fito ne zasu kai Yara asibiti aka kama su” “Umarni aka ba ni, idan shima Xno din ya taka doka a karya shi, don haka kayi yadda nace.” shiru yayi sannan ya ce mata. “Mace ba namijin ba ce.” d’ago gajiyayyun idanunta tayi tana faɗin. “ Mace ce kuma yar daba?” ta tambaye shi, gyada mata kai yayi. “Ku tattaro min files na masu laifi bakidaya, don haka babu zancen sake su.”
Shiru yayi yana kallonta, bata san inda take tura kanta ba ne hala. “Hala baki san wace ce ita ba? Gaskiya ba zan iya wannan aikin ba, kawai a sallame mutanen.” sake baki tayi tana kallon shi,.kafin ta ce mishi. “Nawa take biyanka?” murmushi yayi mata sannan ya ce mata. “Ai ko daya bata biyana amma kuma ina gaya miiki gaskiya ne domin su yan jagaliyar nan sun fi mu, yanci don haka ki kyale mata Mutanenta, domin kowani lokaci zata iya zuwa kuma zata dauke su.”
Murmushi tayi sannan ta ce mishi. “Ok ina jiran zuwanta. Ina jiran abin da zata yi.”
——-
Bubuga kofar dakinta ake, domin tun bayan da tayi sallah hafsy ta fita. Ƙwanciyarta tayi abin, bata san wainar da ake toyawa ba, abun da ya faru kuwa tighgas da ake wurgawa ne ya haifarwa Chu-chu numfashinta ya fara sarkewa wanda yasa dole Black da Dundurosu suka fita da ita zuwa asibiti basu gaya mata, bayan sun kai ta asibitin ne, shi ne Black ya ce bari ya zo ya sanar halin da ake ciki, ai kuwa yana barin asibitin yan sanda suka kama shi, duk yadda ya musu bayani amma fir suka ki yarda suka saka shi cikin yan kame. A gidan kuwa kiran Dundurosu suka yi ya gaya musu, ai ya turo Black an kwantar da Chu-chu. Ai ko ba gaya musu ba, an kama Black. Jin bugub ba na kare bane, yasa ta bude kofar “Zeeno an kama Black ” barcin da bai gama wartsakewa bane ya neme shi ta rasa. “Garin yaya?” nan suka gaya mata…….
#Mmmj
#Zeeno
#Beauty
#Beast
#RomanceS
#Tycoon
#WeatherMan
#Rumors
#Jelousy
#Cursed
#Mai_Dambu
*08130269641 for more info*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: *CINIKIN RAI……*
Beauty and the beast♡
Mai_Dambu
BOOK ONE
004
“Meeeee?” ta kuma tambayarsu a hargitsassen murya. Diriricewa suka yi bakiɗaya tai musu ba wani irin kwarjinin da suka kasa samun damar bata amsa. “Nace, garin ƙaƙa hakan ya faru?” sake shiga rudani suka yi, juyawa tayi cikin dakin ta tsaya cak, tama ruɗe baki ɗaya tana me kallonta a madubi. Juyawa tayi ta kalle su. “Kuna nufin an kama Black?” “Eh Zeenobia!” suka bata amsa. Doguwar rigar da tayi sallah la’asar da shi ta saka, sannan ta dauki key din motorcircly tare da hilmet, kallon shigar jikinta tayi sannan ta koma wurin kayanta ta sauya riga da wando sai top da ta saka. Sai wasu chain da tasaka a wuyarta.
Kana ganin shigarta kasan sai a hankali kawai, domin daga sama har kasa zaka gane abin ya motsa ne. “Zeeno ko zamu raka ki ne?” da ta watsa musu harara tilas suka janye kudirinsu nason lallai sai sun bita. “Paul fito min da bike dina.” jikinsa na rawa ya fitar, ya shiga karkad’e mata. Tana isa wurin ta saka key ta tashi machine din, wangale mata kofar gidan yayi. Ta cilla kan babban titi a guje. Ta ina zata fara ma? Ta ina zata shiga? Babban asibiti ta fara nufa, inda ta shiga bin lunguna da yake cikin garin. Har ta isa asibitin, shima da kyar aka bude mata kofar, tana shiga cikin asibitin ta wuce emergency room.
Mikewa Dundurosu yayi yana faɗin. “Xnoo!” takawa tayi har wurinsa ta kalli Chu-chu da take barci. “Ya jikinta?” numfashi ya sauke sannan ya ce mata. “Sunce zuwa dare zasu sallame ta, sai dai kuma ina ga an kama Black.” cizon leɓenta na kasa tayi sannan ta ce. “Ba gani ba ne, sun yi ram da shi ne, amma ai sun san mutane na, wani shafaffe da mai ne zai kama min iyalai na?” saka hannu tayi a cikin aljuhun wandonta, ta ciro katin banki ta mika mishi. “zan tafi ka tabbatar idan an sallame ku, ka isa lafiya ko kuma ku kwana a nan, bayan nan kada ka saka rayuwarka cikin kasada.” ta dunkule hannunta, shima ya dunkule na shi, suka dan naushi juna, alamar Goodluck.
Yadda ta fita bata tsaya ba, nufar shingen yan sanda tayi, tana zuwa kafe machine din tayi, ta nufe su. “Xnoo! Da fatan lafiya dai?” murmusa musu tayi sannan ta ce musu. “Ina dan gidana da kuka kama?” shiru suka yi, kafin suka yi kasa da murya. “Xno yana can babban office din mu, nasan Ammar yana can yana ƙoƙarin ganin an sake shi, ai ba zamu iya rike miki shi.” Murmushi tayi sannan ta bar wurin. Kai tsaye babban office din yan sanda ta nufa, duk inda ta wuce babu wanda yayi yunkurin dakatar da ita, tana isa office din ta kafe machine din. Ta cire hilmet ɗinta nufi cikin office ɗin. Tana shiga ciki ta hadu da dan sanda da ya su a sake black. “Ranki shi dade, da Kanki?” “Eh ina mutumina?” shiru yayi sannan ya ce mata. “Kiyi hakuri amma.” gyara tsayuwarta tayi, sannan ta ce mishi. “baka ji me nace ba ne?”
Numfashi ya sauke, sannan ya ce mata. “ina jinki sai dai matsalar sabuwar ASP muka samu tana da zafin kai sosai.” dariya tayi sannan ta ce mishi. “Zafin kai fa? Ok ina take?” shiga cikin sosai suka yi don dama suna baƙin kofar shiga ne. Fitowar Asp Zulfa daga office ɗinta yasa suka tsaya cak. “Xno gata nan!” ƙoƙarin danne fushinta Xno tayi tana me saukar da murya. “Ranki shi dade, nazo niman belin Yarona ne.” kallonta tayi na wani lokaci. Kafin ta ce mata. “Kallonta a wulakance Asp tayi tana dandana wayarta. “Waye d’anki anan?” nuna shi Xnoo tayi.
“Ok wancan dan ta’addan masu tadda zaune tsaye? Ko ba shi ba ne?”
“Ina ga ke bakuwa ce a wannan yankin, muna tarban bakinmu da karammawa ce, sai gashi ke a rashin dace kinzo lokacin rashin sa’a. Please sake min shi, domin ya kai mara lafiya asibiti ne aka kama shi.” Zeeno ta gaya mata. “Meye shaidarku?” Ciro wayarta tayi ta mika mata, tana faɗin. “Asibitin da ya kai mara lafiyar ne suka zari kudina, sannan bayan nan idan baki gamsu ba zamu iya zuwa ki gani da idanunki!” mika mata wayar tayi tana tab’e baki ta ce. “wannan hujjar bai gamsar da ni ba, domin naji labarin kina cikin yan daban da suka yi kaurin suna?”
Cizon leɓenta tayi, tare da matse hannunta. “Yar sanda, ba bincike nazo ki min ba, belin Yarona na zo beli.” yadda Zeeno tayi magana ne ya bawa Zulfa haushi, ya Zeeno tana yar daba, mara yanci zata mata magana kamar wata me yanci, bayan ita kaki ne a jikinta. “Kai bude wancan cell din ka watsa min wannan mara kunyar a cikinsa na ga waye ya tsaya mata a faɗin garin nan.” dariya Zeeno tayi tana faɗin. “Ni ba fada nake nima ba, amma tabbas zaki yi kuskuren da zai janyo hankalin waɗanda suka tsaya min ba ni mutumina!” hannu ta kai da nufin hankad’a Zeeno. Cikin wani irin zafin nama,. Zeeno ta juyar da ita daga nufin hankad’ata, karshe ita ta fadi warwas. “Kinga yar sanda ba fada na zo ba, don Allah ki bani mutmina!”
“Kika kifar da Yar sanda a bakin aikinta? Lallai yau zaki sani!” Ciro waya Zeeno tayi ta shiga latsa wasu number, can kuwa aka dauka. “Yallabai gamu a Office din yan sanda, ta kama min Black kuma tana son lallai sai ta keta min jikimata.” Kashe wayar tayi tana kallon Zulfa da ta kallo wasu irin kwagirin domin dukkan masu laifi wasu tika-tikan dasu.
Nufar Zeeno tayi, amma kafin ta iso an kira layin. “Hello yallabai?” shiru tayi. “Yallabai yan jagaliya ne masu tadda zaune tsaye fa, idan aka sake ta ai.” shiru tayi tana kallon Zeeno da ta koma daya daga cikin kujerun cikin office din ta zauna tare da fara fyeduwa. “Ok Sir!” ta fada ranta a matukar had’e. “Ke yar sanda! Ba gaba da gaba, ko ta baya irinki goma sai sun shirya, kinga da kira daya. Me zai faru idan kika kara aikata makamancin irin wannan kuskuren.” Takawa tayi har gabanta. “Tube jami’ai irinki nake a bainar nasi na zane mazaunan su, sannan na saka su, su lashe ƙasar takalmina.” ta wani d’ago mata takalmin kafarta, ta nuna mata tana murmushi. A fusace Zulfa zata nufeta. “Madam gaskiya kibi umarnin na sama dake, idan ba haka ba.” shiru tayi, tana gani aka bude Black. Zeeno ta riko hannunshi suka bar Office. Har harabar office suka nufa, ranta na soya tabbas yar sanda nan, taci albarkacin Mr Amjad, haushin da bata sauke a kan Zulfa ba, shi ta sauke a kan Black. Domin tsinka mishi mari tayi. Sunkuyar da kai yayi, “Kasan yadda ka zubda min da mutuncina? Har ni yar sandan can zata rufe? Me yasa baka kira ni farkon al’amarin? Kasan waye na kira ya musu magana? Kada ka kuma min wannan gangancin.” Daga haka ta cilla mishi key din machine din, ta nufi wurin motarta. Daukar hilmet yayi ya saka, sannan ta shiga motar tana me tadda shi. Horn tayi me karfi da tashin hankali. Fitowa Asp Zulfa tayi ta zuba mata idanu. Sannan ta wani juya tare da d’aga musu kura. Fyaduwa sajan Barau yayi yana me dariya. Kallonshi Zulfa tayi ya daina, “Waye ya tsayawa wannan yarinyar da commissioner ya kira ni da na kyaleta?”
“Yar kunama kenan, yar karamar mace sai babbar kasada, tayi nata tayi na me karamin karfi. Yar jagaliyar da babu irinta.” juyawa tayi tana faɗin. “Akwai files ɗinta ne a Office din nan?” gyad’a kai yayi yana kallonta. “Muje ka bani.” dariya yayi yana faɗin. “Madam me zaki duba a cikin files ɗin? Ki rufe shi kamar yadda aka rufe domin babu wanda ya isa ya bude har ya kamata, kada ki manta halin da ake ciki na case din Prime minister.”
Wuce shi tai tana faɗin. “Ba ni file ɗinta.” Haka ta wuce, duk yadda ya so ya mata bayanin wacce Zeenobia amma fir taki saurarenshi. Haka ya wuce ya shiga duba tsofin kundi har ya ciro mata, ya fita ta kai mata. Office ɗinta ya kai mata, tana zaune ya ajiye mata. Tana waya, da alama da babba take wayar sannan ta ce mishi. “Ok Sir Allah ya kawo ku lafiya, amma an samu zaman lafiya domin an dakatar da zanga-zangar babu wani abu, sai case din Prime minister. Naji kace Arshad Abdul Qayyum, zai zo don haka na ajiye kome cikin kulawa, babu abin da na tab’a tunda zaku wuce da shi. Capital Crud” shiru tayi kafin ta ce. “In sha Allah sir, amma a dan bani damar wani ayyukan please Sir akwai aikin da nake bukatar farawa.” Murmushi tayi tana sosa goshinta.
“Ok Sir!” Ta fada a kunyance, domin idan na an gaya maka tana sa matukar kunya ba, ba zaka yarda ba don irin manta nan ne masu yanayi biyu kunya da mutunci, haɗe da zafi me yaji. Ajiye wayar tayi. “Sajan Barau ka kawo?” gyada kai tayi. Mika mata yayi a hankali ta amsa. Ta karkad’e shi tana kallonshi. “Jami’a na musamman zasu zo daga Capital Crud City, sune zasu amshi case din Prime minister.” “Ayya kice dama kwantar da tarzoma kika zo yi?”. Gyada kai tayi tana buɗe file ɗin. Hoton Zeenobia ne, me dauke da manyan rubutun sunanta. Zeenobia Nasr Hadejia. Kura mata idanu tayi kafin ta fara buɗe shafi na biyu.
A ranar talata ga watan march, an kama yar shekaru goma sha biyar, da laifin duka Mr Martha’s vineyard, a tsohuwar unguwar tabkin. Shiru tayi tana kallon hotonta a lokacin tana karama ne ba. Ajiyar zuciya tayi. Sake bude wani page tayi tana kallon. A hankali ta gama bude file ɗin, kusan duk laifuffukan da ta samu, laifi daya ne taga an saka babu hujja. “Sajan Barau!” ta kwala mishi kira. Shigowa yayi ya sara mata.
“Naga wani laifi amma an ce babu hujja, an rufe case din. Sannan wacce ita?” ajiyar zuciya ya sauke yana me cewa.
“shekaru goma sha uku, baya da suka wuce an tsinci gawar yan ta’addan Eagle bandit sakamakon ambaliyar da aka yi na kwacewar da Dam yayi, a cikin mutanen da suka tsira har da yarinya yar shekara bakwai a duniya, wacce ta manta da wasu abubuwan da suka shafi rayuwarta na baya. Lokacin ban jima da fara aiki ba, wannan al’amarin ya faru. Alhaji Badaru Daniyal shi yazo har Office din yan sanda tayi cike-ciken takardu, sannan ya amshe ta.
Matsalar da aka samu, shi ne tayi fama da matsanancin ciwon mantau, wanda ya sa ta koma kamar ba mutum ba, domin ba a san lokacin da ta dauka a hannun yan garkuwa da mutanen ba. Amma laifinta ba farko kamar yadda kika gani, Laifin duka tayiwa Martha’s vineyard, domin a lokacin yayi kokarin wulakanta uban rikonta ne, ita kuma ta hana faruwan haka. A lokacin da aka kawo korafin DSP Ayuba, shi ya saka aka kamota aka rufeta, tun daga lokacin da aka sake ta, ba a kuma samun kyakkyawan alaka da ita ba, domin sai ta fand’are, Madam garin nan yayi shura akan zalinci, wannan zalincin shi ya samar da Xno, domin kare mutumin da yaƙe dawainiya da ita, Madam ban san zahirin gaskiyar abin da ya faru ba. Amma sakamakon sauya-sauyan wuraren aikin da nake samu, ban san dalilin da ya mai da ita cikakkar yar daba ba, sai dai dawowa na garin nan na fahimci tana ƙare gidan al’umma charity House.” shiru tayi tana kallonshi.
“Ko tana karuwanci ne?” ta tambaye shi, kafin ya ce mata. “Subhanalillahi, idan aka ce daba da jagaliyanci, tow kuwa babu sama da ita, domin da kankantar shekarunta, take dakawa maza gunba a hannu, tunanin tana hulɗa da maza duk ban sani ba.” mikewa tayi tana faɗin. “Dole mu dawo da case din da aka ce babu hujja, sannan ina da ayar tambaya akanta, domin ban yarda da ita ba. She acting over confidence.” “Ok Madam”. “Dole nayi digging a rayuwarta single mistake na samu a rayuwarta sai na bude mata wuta ita da dabar ta.”
****
Zeeno.
Koda suka isa gidan, jama’ar gidan kamar su goya su suke, sauka tayi a motartana faɗin. “Daga yau duk abin da ya faru, kafin a aiwatar da kome, a tabbatar da an sanar da ni kafin ayi wani aiki. Wannan mutuwar Prime minister, ya sauya mana kome don haka kada wani ya sake ya fada hannun wancar yar sandar domin ba zai mana kyau ba. Idan wani abu ya faru daku rayuwata ce zata cutu, wannan alƙawari ne da na dauka muku, don Allah ku dinga nazarin kome kafin ku aiwatar!”
“Ayya Zainobia kina da naki rayuwar ki kyalesu mana, kema kiji da naki rayuwar mana.” inji Hafsy. Domin tana masifar jin haushin ganin yadda Zeenobia take bada rayuwarta akan mutanen nan.
“Hafsat ba zaki gane ba ne, su din sune ni idan babu su, tow kuwa babu ni.”
Taɓe baki tayi, tana me wucewar ta domin tasan yanzu dai sai su raba hali akan mutanen da take mutuwa akan su, basu sumarta.
Tunda ta zube a saman gadonta take, sauke ajiyar zuciya. Exactly 3 year sanyi ne da ciwon kai yake bibiyarta tun safen yau amma baki daya ba ta ce ba. Don rabonta da wannan yanayin.
****
Green House.
House of representatives. Crud City Hall.
Yan majalisar kolin ne suka hadu. Shiru hall din ya dauka, domin tattaunawa akan abin da ya faru. Fitowa Assamblywoman, Mss Lalla Salmah ta zuba musu idanu kafin ta ce. “Izuwa yau duniya da sauran ƙasashen nahiyar Afirka, sun daura idanunsu akan Mayor Malik Menk Jordan, Ni dai ban laifin shi ba, kuma har abada ban zan ga laifinsa ba, domin kare kai da dukiyarsa baya nufin ya kare kansa a matsayin lusari ba.”
“Keee Lalla Salmah, babu me sauraren wannan zancen naki. Dole majalisar koli ta sauke Mayor Malik Menk Jordan, ko kuma mu ɗauki mataki akan dan ta’adda.” Inji wani dan gajeren mutum me katon ciki. Dariya tayi tana faɗin. “Same scandalous wai suna da bakin magana, mutanen da basu gudun abin kunya.”
Kura mata idanu yayi har ga Allah, maganar ta bata mishi rai. Bai san lokacin da ya fara kokarin tsalleke wurin zamansa ya tsallako wurinta ba. “Idan ban miki shegen duka ba, Alqur’an uwata shege ta haifan!”
“Mr Abid ka kiyaye bakinka, Mayor Malik Menk Jordan ba kanwar lasa ba ne, don haka muje ga tattaunawar mu. Kowa yasan waye Malik, sannan izuwa yanzu abin da ya faru ya dace mu nazarci meke yake faru.”
“Yallabai, harkan Kasuwancin garin Keivroto city harka ce ta ban mamaki. Sai dai a bangaren ilimin rayuwa dole a fuskanci matsala, ba laifi ba ne idan Malik ya k’amk’ame kome, ai na shi ne. Kuma iyawarsa ya kai shi wannan matakin. Ko mutuwar Prime minister bana da ja tabbas bai da cikakken masaniya akan mutuwarsa.”
“Wai Lalla Salmah me kike son fada? Me kike son gaya mana? Waye bai san cewa kaf duniya Malik bai daukin ran kowa da daraja ba, har kwanan gobe Malik ubangijinsa shine kudi, matansa kuwa kartin maza ne kin isa ki kare shi da abin da ya faru, shekarun talatin da wani abu baya, tun yana daura igiya a matsayin zariyar wandonsa muka san Malik shi kare ne, wild dog ne da muka watsa mishi kashi ya bi yana haushi, duba kaina Lalla Salmah. Kin fito daga babban gida kada ki sake goyan bayan da Malik ya baki, ki tab’a nasabar gidan ku. Ka da ki zama me bawa kasungurmin dan luwaɗi goyan bayan. Ba zamu lamunci haka ba, don haka dakatar da Malik ya zama dole.”
“Shu’iba kada kayi wasa da rayuwarka,Malik ba abin wasan yara ba ne ka iya kalamanka domin duk tsohon da bai
Kunyar hawa jaki, jaki ba zai ji kunyar kadda shi ba……..”
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP for information 08130269641*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: https://chat.whatsapp.com/KZbdBOduk2c2nLpNQp7Qh3
CINIKIN RAI….!
Beauty and the Beast♡
006
_Past_
A lokacin da suka zo ganin wurin dayawan su, sun yi fatan da sune suka kawata wurin domin ai sune yan kasa ba Nasr Hadejia da Aswad Yamini ba. Taya baƙin haure zasu zo su fi yan gari kawo cigaba har haka, wani abin ya tsaya a ransu. Matukar tsaya musu. Kuma ba iya shi ba, asalin su mutane ne masu matukar Kyashi da Hassada da wannan dalilin yasa suka buɗe iyakokin duk wani tubalin bakincikinsu, inda aka fara turo musu yan jagaliya suna yiwa mutanensu daukar amarya. Koda Alhaji Nasr Hadejia ya ga haka sai ya shigar da bukatar jami’an tsaro su shiga cikin al’amarin amma abin haushi sai aka yi rashin dace. Domin yan sanda bakinsu daya. Haka yasa jikinsu yayi wani zai ce me yasa suka nace da son suyi wurin shakatawa? Abin da mutum be gane ba, shi ne fisto yana cikin garuruwan da suke buƙatar a inganta su. Na farko zai samawa birnin cigaba, na biyu matasan garin da suke sana’ar daba da jagaliyanci zasu samu aikin yi, dattawan da suke sana’ar kamun kifi, zasu samu damar baje kolin sayar sa kifinsu. Sannan gari ne masu al’adar gargajiya. Wannan dalilin yasa baki daya mutane biyun nan saka zuciyarsu, akan lallai su kawo cigaba da garin.
A hankali kome ya fara kwace musu, domin a zahirin gaskiya yan daban sun dame su. Abubuwa biyu ya dame su, ga asarar dukiyarsu ga wasu daga cikin mutanensu a hannun yan garkuwa. Akwai wata rana da Alhaji Nasr Hadejia da Aswad Yamini suka hadu a gabbar tsibirin. Kowanen su, yana da damuwa amma dan samu kwarin gwiwa a tsakaninsu yasa suka sauke ajiyar zuciya a lokaci guda. “Hadejia ina ga ya kamata mu sake budar wurin Mayor Fahad Albagwi da wannan al’amarin, idan har muka yi haka tow ba makawa zamu samu adalci, kaf garin nan kansu a haɗe yake ba zasu sake mana mutanen mu ba.” kallon shi yayi sannan ya ce mishi. “Ni ma nayi tunanin haka, amma nasan Allah yana sane da al’amarin mu, Allah zai tsaya mana.”
“Ka saka mana lokaci mu tafi wurinsa, idan yaso sai mu shirya ba.” murmushi Alhaji Nasr Hadejia yayi ya ce mishi.
“Idan Allah ya kai mu gobe, sai mu tafi. Ina son na kira iyalina ne su zo da Yarana.”
Dariya suka saka ya ce mishi.
“ai ku yan Nigeria kuna da hakuri da juriya, ina zan iya wannan hakurin? Kawai malam ja sa Madam ta dawo nan, kafin nan karatunsu da kome nasu zai dai-daita.”
“Hmmmmm! Tow ya zamu yi? Kasan idan baka yi hakuri ba, ya zaka yi da hakkin Allah, shi Allah ya sauke hakkin mu da yake kansa, saura mu mu sauke wanda yake kanmu. Ina da Yara mata biyu, ina jin kunyar na bude idanu na kalle su bayan na sabawa Allah, sannan Allah ba zai kare mu ba. Sannan ba zai kare bayan mu ba, amma idan muka ƙare kanmu da iyalinmu Allah zai kare bayanmu bayan mutuwar mu.” jinjina kai Yamini yayi yana faɗin. “Na gamsu da bayaninka. Allah ya kare zuriarmu bayan mutuwarmu” “Allahumma Amin” da wannan suka ajiye zancen zasu tafi wurin Mayor Fahad Albagwi.
Washi gari kuwa Yamini shi da kansa ya taso ya dauki Alhaji Nasr Hadejia, izuwa farfajiyar gidan gwamnati. Sun taras da mutane, musamman manyan baƙi don haka suka tsaya su jira. Bayan kamar minti Talatin sai ga sakataren Fahad ya fito dake an isar mishi da yayi baƙin. Duk da kasancewar sun same mutane a wurin bai hana sakataren isowa wurinsu ba, ya ce musu.
“Ku iso ana kiranku.” mikewa suka yi, tare da bin bayanshi, a cikin ofishin Mayor. Cikin girmamawa da mutuntawa Mayor ya mike tare da tarbansu yana faɗin.
“Malik sune mutanen da suka zo da nufin raya garin Fiston, amma Shu’iba da Dulma sun hana su, har nan suka zo suka min kashedi. Malik na kira ka ne, domin ka taimakawa bayin Allah nan, suna san cigaban jahar nan ta fuskar Kasuwancinmu.” duk da basu ga fuskarshi ba, amma baki daya basu wani gamsu da shi ba, domin kuwa ba a niman taimakon dan daba akan yan daba yan uwanshi. Hadin kai ne dasu, d’ago hannunshi me dauke da zobban ya yi musu wani alama.
“Wai ku gabatar da sunanku?”
“Aswad Yamini, wannan abokina Alhaji Muhammad Nasr Hadejia.” a hankali ya juyar da kujeran ya zuba musu idanu, mutum ne mai tsannanin kwarjini da cikar halitta. Mutane da matukar ka kalle shi sau daya sai ka sunkuyar da kanka ƙasa. Domin yanayin zubinsa kamar zubin zaki ne, rintsa idanun Yamini yayi yana jin wani irin yanayi. Domin kallo daya yayiwa Malik ya hautsina mishi tunani, banbancin shi da Nasr Hadejia da ya kuma kallonsa ido ciki ido har sau biyu. Duk da wannan yanayin bai hana shi jin kamar ya zuru da gudu ba.
“Had’ejiya ta Jigawar Nigeria?” da sauri Alhaji Nasr ya d’ago suka kara kallon juna a karo na uku. Mikewa yayi yana me fashewa da dariya, Fahad Albagwi ka had’e ni da dan uwana dan kasar kakana. Ai ni na samu aboki waye ya isa ya ce ba zasu gina wurin shakatawa ba. A shelantawa duniya na tsaya musu. Ai ko don albarkacin dan kasata na tsaya musu. Yamini kai ma ɗan uwana ne, domin Mahaifiyata yar yankin jaziratul arab ne.” lallai sun taki sa’a kuma sun dace. Sai dai basu san cewa akwai ragon azanci a amincewa Malik. Musamman yadda tambarin shahararsa tasa ya fantsama yayi wanka da munanan ayyuka ba, mutum ne ya yayi wanka da zunubai babu iyaka.
Don haka suka bada yardansu tare da yarjejeniyar habbaka Kasuwancinsu. Amma ya boye musu makasudin amsar alaƙarsu.
“Batun ma’aikatanku da suke hannunsu, zan amso su kafin rana tayi tsakiya.” ya duba agogon hannunshi. Sannan ya juya yana kallon Fahad. “Albagwi alkawari.” gyada kai yayi, sannan ya fita. Bin bayanshi suka yi da idanu. “Mayor hankalina bai kwanta da Mutumin nan ba, idan abun nan ba zai yiwu ba, mu hakura ko Yamini?” murmushi yayi sannan ya ce mishi.
“Ni kuwa naji kamar alkhairi, koda kuwa akwai matsala ba zai gaggare mu ba. Kwantar da hankalinka.” haka suka amince da Malik domin kiri-kiri Alhaji Nasr Hadejia yaki karban Malik, ba don kome ba. Sai don sanin duk inda aka samu dan daba zai yiwu ya ki taimakawa yan uwansa.
Shu’iba da Dulma.
Malik ya jima yana nimansu, ba don kome ba sai don akwai tsohuwar gaba, wanda suka jima da shi a ransu, sai dai bai samu damar ramuwa ba, domin kuwa basu tab’a zama wuri guda. Asalima wasan boya suke da shi, shi kuma yayi alƙawarin duk wanda ya gaya mishi inda suke zai mishi kome, ana haka Fahad Albagwi ya tura mishi sakon ganinsu. Ana gab da zaben kasa.
Dulma dan uwan Shu’iba ne, kaninshi cikin su daya, a duniya babu abun da Shu’iba yake so sama da Dulma, domin ta kai, hatta matar da ya aura tunda Dulma ya ganta ya ce, yana sonta. Babu musu Shu’iba ya bar mishi ita. Karshe azaba da wahala ya kashe Yarinyar, tun daga lokacin Shu’iba ya samu damar auro mata Dulma ya shiga abin da yake so da su.
Hill and Tim town.
Ana kiran wurin nan haka ne, sakamakon duwatsun da suka kewaye wurin, kuma akwai ma’adinai irinsu kuza, ana hakarsa na fitar hankali. Ba ƙaramin samu suke ba. Sannan sun kwashe maza matasa da yan matasa,. Suke musu wannan aikin cikin azaba da wahala, dalilin wannan dukiyar da yake kasa yasa suka watsar da duk wani cigaba da ya dace su samu. Musamman a fuskar garin, domin idan suka gyara garin su waye zasu musu wannan aikin? Duk matasa zasu samu abin yi. Shi yasa wurin suka kawata shi da nauyin azaba kala-kala. Babu wanda ya isa ya gudu, akwai zakuna masu gadin mutanen, domin kuwa idan mutane suka ne gudu bude zakunan ake suyi fata-fata.
Koda Malik ya bar ofishin gwamnati, bude motarshi yayi, masu kula da lafiyar shi suka fito suna me niman take mishi baya, d’aga musu hannu yayi. Ya dauki wata local gun, sannan ya shiga motar bayan ya dauki wata glass na Prado ya saka a fuskarshi, fuskar shi a kame, na zaka ɗauka yana dariya ba.
Haka ya juya ya fita, a duk lokacin da yayi irin su wannan shirin, tabbas ba ƙaramin al’amari ba ne, jinjina kai Elbashir Jamal Arab yake, yana faɗin. “Allah ka jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya, amma tabbas maza sun fita farauta.” Haka ya koma cikin motar ya zauna, tare da kunna wakar rosta.
Tafiyar kilomita bakwai ya kai shi, Hill and Tim town.
Tun kafin a bude mishi kofar shiga town din ya fara musu barna, har ya isa cikin sansanin, koda yake fushin sa ba a kan kowa yake saukewa ba, akan wadanda suka tab’a shi ne.
*present*
Koda yake kusan rabin ayyukan da tayi, bata jin akwai wanda ya kai na yau, shi yasa tayi kokarin ganin ta nime haduwa wani dan kasuwan da zai zuba jarinsa. Sai dai batayi nasarar haduwa da shi ba. A gajiye ta fito daga ginin ta fito inda Black yake jiranta, wurga jakarta tayi tana faɗin. “Wash Allah na!” Ta zauna a cikin motar tana mika. “Ina zamu?” Idanunta a lumshe ta ce. “Akwai inda yafi gida ne?” “Babu” ya bata amsa, sannan ya ja motar suka bar wurin.
“Chairman! Yarinyar nan ta kawo abin da bamu zata ba, mu kyaleta haka!” Murmushi Mr Amjad yayi ya ce mishi. “Ban gama gamsuwa ba, sai tayi min abin da3 zan barta. Amma ka sani duk kudaden da take samo mana, na hannun jari bai kai na babban kifi ba.” Shiru MD yayi ya ce mishi.
“Akwai matsala, idan har aka sake kifin ya sake ya zama me k’aya za a wahala.”
“Bana kwai na, sai da zakara don haka da ita zan amfana!”
—
A kan hanyarsu ta dawowa gida ne, suka tsaya a traffic jam. Yan sanda ne suke bincike, “Kai Xno ga mutuniyar!” Juya kanta tayi zuwa ga inda yake nuna mata, kafin ta tabe baki ta ce. “sun fito cin na goro!” Ta fada tana dauke kai, domin ta gama gajiya likis. Dama da gayya ita kanta Asp ta fito kan titin. Sake mutanen da suka tare take, kafin su Zeeno su iso ta saka an tare hanyar, dauke kai Zeeno tayi.
“Ina driving license din ku?” Banza suka mata. Ba ƙaramin kunya ta ji ba, domin ana ta wucewa da kafa, kuma ana kallonsu.
“Ina magana kin min banza!” Babu wanda ya d’ago kai ya kalleta, hannu ta kai da niyyar zata cire key din motar. Zeeno ya kai mata wani irin duka da bayan hannu, faduwa can tayi, kamar an cillata. Sauka daga motar Zeeno tayi tana me cire top din suit din jikinta, a hankali ta shiga nad’e hannun white shirt din jikinta tana faɗin.
“Kul ki ce zaki tab’a min mota ta, zan kyale ki ne domin kakin jikinki idan ba haka, kul ki kuma shiga harkata!” Mikewa Asp Zulfa tayi tana faɗin. “Kika saka hannunki a jikin Yar sanda.” Wani juyar da kai tayi tana faɗin. “Idan ta kama na zane ki zan yi ki tsaya a bakin aikin ki.”
“Da shi haka yana nufin duk wanda ya nime saita miki hanya, sai kin kashe shi dalilin da yasa kika kashe Asp Ayuba kenan?” Rintsa idanunta tayi, ta nufi Zulfa da wani irin sassarfa ta cukume ta. “Idan kika kara kiran sunan tsinannen can, sai ja tura ki idan na tura shi, ki bincike idan kin samu labarin wanda ya ga lokacin da na kashe shi, ki zo nan a gaban jama’a ki saka handcuffs.” Daga haka ta koma cikin motar ta zauna. Wani irin kallon banza Zeeno ta aikata mata, tana mata gargadi.
*Past*
“Kai ku sake mishi zakunan nan!” Haka suka sakar mishi dabobbin. Yarda bindigar yayi ya nufi zakunan da mugun gudu, kamar yadda suka nufe shi. Oho faduwar gaba asarar maza, a fusace Mayuntan zakunan nan suka nufe shi, aikuwa aka rungutsume akayi wata kazamar arangama, a duk inda aka raya fansa, tow zaka samu tsoro da fargaba bai cika samun matsuguni a wurin ba. Haka ce ta faru da Malik, domin a duk lokacin da ya dunfaru wani abun da ya shafi fansarsa. Haka suka hautsine da wani irin fada, me tashin hankali. Kafin wani lokaci,ya watsar da gawarsu, ya mike yana karkad’e jikinshi yana kallon inda Dulma yaƙe. Hannu ga saka a cikin aljuhun wandon shi ya dauko cigarette, ya kunna tare da zukar hayakin ya hura a sama…….
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI….
Beauty and the beast♡
Mai_Dambu
005
“Kai Shu’iba ka rufawa kanka asiri, ko a tashe ka da nakiya. Ko kuma a turo yan bindiga dad’i su alburushe ka.” har ga Allah maganar tayiwa Lalla Salmah zafi. “Shi yasa baku rabuwa da abin kunya a kowacce magazine ba. Ai gara Malik ya tsare kansa da dukiyarsa ce,ba mutumin banza ba ne.” Tana gama fadar haka ta mike zata bar kwaryar Majalisar. “Ya tabbata dai yan PKO party basu da abin faɗa, tunda karen farautar da suke karewa ta kusan kare mishi. Shugaban majalisa a tsige Malik Menk Jordan kawai.”
Shiru tayi sannan ta cewa shugaban majalisar koli. “Yallabai kafin ka yankep hukunci ka fara nazari, idan kace zaka biyewa yan amshin shata zasu kaika su baro ka, su basu da nasu sai na wasu. Kullum ra’ayin wasu ke yawo a kansu banbancin uban nan gidansu da Ubangidan mu kenan.” daga haka ta fita ta bar kwaryan majalisar koli da hayagaga.
Tana fita ana mika mata wayarta, amsa tayi tana faɗin. “Elbashir ina ka shiga ka bar ni sa tashin hankali? Kasan abin da ya faru kowa?” amsa maganar yayi da cewa. _Ina sane, sai dai Malik ya hana ni dawowa ne, ya ce nayi fucus din matsalar gaba na, amma please ki tuntubi Mr Shatima, a madadina ya je ofishin jam’iyyar PKO yayi magana akwai lauya malik._
“Shi kenan, zan tabbatar haka ya faru.” ta fada tana me kashe wayar. Tasan dole yau ta isa Keivroto city kome dare tunda har Malik ya iya hana Elbashir Jamal Arab dawowa tow wannan shi ne lokacin da ya dace tayi kokarin ganin ta shigar da bukatarta. Sai dai izuwa yanzu take da damar shiga ga Malik ko dan Maidah tunda an soke zancen Nadra Shatima. Dama tun can ta tsani yarinyar sai kuma aka yi rashin dace Malik yayi rejected ɗin bukatar Shatima. Domin bata mantawa a lokacin yan mata dayawa sunso shi. Haka ko Wahiba da Wahida, basu amshi Nadrah ba. Shi kuma Malik yana tafiyar da rayuwarsa ne daidai da fahimtar Yaran. Bayan abin da zai tab’a ran su, shi yasa ya dauke su a garin Keivroto ya mai da su demark su yi karatu. Da wannan damar itama take amfani idan zata taso Gista ta tura mishi Maidah. Sai dai wani lokaci bata jin wani gamsashhen bayanin sun hadu ko basu hadu ba, ba kamar duk lokacin da Nadrah taje ba, tana samun ganinsa. Ko last year kafin Mr Shatima ya mai da Maidah Demark wurin su Wahiba da Wahida, Malik da kansa ya bashi Shawaran ya mai da ita wurinsu, sannan ya dauka rashin aurensu daga Allah ne, don baya son haka ya tab’a relationship ɗinsu. Koda yake taji a bakin Mr Khamis Shatima ne da bai da sirri, bai san itama burinta ta tura yarta ga Malik din ba ne. Murmushi tayi, izuwa yanzu ta koyarwa Yarta duk abin da zata kama zuciyar namiji, imma ta koya mata yadda zata iya daukar kowanni abu daga namiji, imma ya kama da affairs ne da namiji ta yarda, amma bata son yarta tayi mu’amala da wani namijin domin tana bukatar yadda yarinyar zata kama Malik. Tow amma me yasa Malik yaki auren Nadrah Khamis Shatima? Domin tasan kuma yarinyar tafi yarta kyau, nagarta da son jama’a. Banbancin ta da Maidah koda yake ai Barewa bata gudu danta yayi rarrafe, halinta halin Yarta. Koma mene ne ohon musu kanta ta sani, ba wasu ba yarta ta samu shiga ga Malik ko nawa zata barar zata san yadda zata cusa yarta ga Malik. Koda kuwa zata kama da bin malamai da bokaye ne sai sun mallake shi.
**
A cikin abun da bai wuce sati daya ba, aka d’aga curfew inda aka bar kowa, dakin Ammyn Abbas ta nufa, tana me shiru. D’ago kai Ammyn Abbas tayi tana murmushi. “Zainaba” a hankali ta iso gabanta tare da riko hannunta. “Gaya min akwai da wani abu ne?” kansa a sunkuye ta ce mata. “Ammyn aikin da na samu, sun ce min lallai dole sai dai na zama me gayyato musu mutanen da zasu saka hannun jari a kamfaninsu. Kaina ya kunce ban saba ba, ban iya mu’amala da.” murmushi tayi tana me zaunar da ita ta ce mata. “Inji waye ya ce ba zaki iya ba? Zaki iya mana, kika iya daukar na wasu ma balle naki, Allah ya sa’a.” “Ina son tsoro ne kar a samu matsala, na ga sun addabe ni da lallai na fara aikin ne, shi yasa na fara jin kamar akwai wata manufa a kasa.”
“Ki yarda a ranki zaki iya, sannan ki saka nutsuwa a ajiye jagaliyancin nan, ki fuskanci reality dinki, da yau Alhaji Badaru Daniyal yana raye kina nufin zai barki ne a haka? Shi ya so ya inganta Miki rayuwar ne, bai da burin ki rike wuka ko gatari.”
D’ago kai tayi Idanunta sun yi jajjur, har wani kyali suke, alamar ta tuna wani abin da ya shafe ta, kasa tayi da kanta tana faɗin. “Ba laifina ba ne, ayayinda ake tunanin mika ni ga gidan Marayu, shi yayi adopt dina a matsayin second child dinsa, ya tafi ya bar min abu biyu masu daraja. Ammyn don Allah bani da wani abin da ya shafi past dina ne, ina son sani wace ce ni?”
Girgiza kai tayi, sannan ta ce mata. “Bayan takardun da na baki, babu wani abu da na sani game dake, shima Alhaji bai san kome ba, sai abin da aka baki.”
“Shi kenan na gode ma haka, ba mamaki Allah ya turo ni rayuwarku ne, shi yasa na kare nan. Amma ina ji a raina kamar ina da wata rayuwar.”
“Allah ya sa.” Ammyn Abbas ta fada, tana me dauke kanta daga Zeenobia din, har tafi daga dakin.
Bin tayi da idanu, tabbas bata yi hankali da zata gaya mata kome ba, bata samu nutsuwar da zata gaya mata daga wacce duniyar take ba, amma bari tayi digging kad’an daga cikin rayuwarta da abin da suka sani.
***
Zeenobia
_Past_
Alhaji Muhammad Nasr Hadejia, Dan asalin garin Hadeja ne na Jigawar Nigeria, bahaushe ne, da kasuwanci ta shigo da shi garin Fisto kasancewar garin da yake tsubirin lord island, kasancewar gari me dauke da manya manyan duwatsu, halo dai hade yake da ruwa me kyau. Garin Fisto yana daga cikin jahohin Gista da ake yawon shakatawa da bude idanu, sai dai wani abu daya da yake maida garin baya shine kabilanci. Kabilanci yayi tasiri da garin, musamman yadda har turawa suna zuwa yawon buɗe ido.
Kasancewar kasuwanci ya kawo Muhammad Nasr Hadejia, kuma abin burgewa yana da ilimin addini da na boko, wanda yasa shi kallon garin a matsayin garin da za a cigaba sosai. Sai dai wani abu biyu da ya dakushe garin. Kabilanci da zalunci, haka yasa shi fara binciken da bibiyar hukumomin haraji na garin Fisto, Allah ya bashi sa’a zuwan farko ya hadu da Aswad Yamini. Shima dan kasuwa ne, a’a Balarabe daga kasar Yemen. Shima mutum ne mai matukar son kasuwanci da cigaba. Don haka a tare suka yi decided yadda zasu gini bakin tsibirin. Yadda zai bada abin da ake bukata, domin ginin zai kasance a cikin ruwa ne, kamar yadda bora-bora island yake. Wannan shine kudirinsu. A lokacin Alhaji Muhammad Nasr Hadejia yana da matar shi har da Yaransa biyu mata, a garin su Hadeja. Sai dai bai yarda ya kawo su. Aswad Yamini yana da matarsa da dansa daya a garin domin a tare suka zo Fisto.
*Present*
Police headquarters.
“Har yau babu wani shaidan dan da za a iya kama Malik shi, abin da na sani mu jami’an tsaro, zamu yi tafiya kafada da kafada, da hukumar binciken farin kaya. A duk lokacin da sahihan shaidu suka samu a cikin tabbatar an kama Malik tare da gurfanar da shi a gaban kuliya. Na gama magana.”
“Ok sir!” bakidaya an sandan suka amsa, sannan kowa ya mike tare da shugaban yan sanda bakiɗaya. Suna fita yan jarida suka nufe su. “AIG wai da gaske ne kuna yiwa Malik aiki.?” inji wani dan jarida. Shiru yayi kafin ya bada amsa wani gidan jaridar ta kuma wurga mishi tambayar. “shin yau babu tabbacin Malik zai fuskanci kotu kenan? Shin Malik yana da ikon juya kowanni bangare na siyasa kenan?” duk da ba a bashi izinin yayi magana ba, amma dole ya gayawa duniya cewa hukumar yan sanda basu yiwa Malik aiki.
“Yaku yan jarida ina son na sanar muku cewa, hukumar yan sanda basu bin bayan kowanni bangare fecce aiki da gaskiya da Amana, sannan da ace yau hukuma ta kama Malik da laifin kashe Prime minister, da ba a rufe awa ashirin da hudu ba, ba tare an kama shi ba. Duk wani hujjojin da ake bukata mun tanada shi, sannan duk wani binciken da ya dace, anyi bai da masaniya a kan kashe Prime minister.”
“Sai dai har yau muna da labarin cewa, Malik Menk Jordan shi ne yaron da ya kashe Manyan yan siyasa da jami’an tsaro uku, shekaru kusan arba’in da suka gabata, shin wannan ba hujja ba ne da zai iya rufe shi har abada ba?” Kallon dan Jaridar AIG Yasir Aswad Yamini yayi, kafin ya ce mata.
“Har yau muna kan bincike.”
“Yallabai²”
Suka shiga kiranshi, amma ina yan sanda sun kare shi. Har ya isa cikin motarsa. Kallonta yayi ta zuba mishi idanu.
“Omooooo! Me yasa kika zauna a nan zafi ba zai dame ki ba?”
“Taya ba zan zauna ba? Wallahi kaji tsoro Allah, akwai cases sun kai ashirin akan Malik Menk Jordan, me yasa kake tsoron bayanan laifinsa ko kai ma kana tsoron mutuwan ne?”
“Mutane irinku, kullum tunanin su hango laifin wasu baku tab’a zama ku fahimci me yasa wane ya zama haka.” Bata bari ya kawo karshen zancen ba, ta bude motar zata fita, riko hannunta yayi ya ce mata.
“Me yasa kike fushi?” Idanunta cike da takaici ta ce mishi. “Ok ya batun binciken ki?”
“Sake ni!” Bakinsa a dai-dai kunnenta, “let me kiss you.” Ture shi tayi, tana faɗin.
“Ni ba yar iska ba ne…..” Sumbatar ba zata ya kai mata, ta wani ware idanu ta. Hura mata isa yayi. “Asp zaki iya tafiya!” A hankali ta bude kofar ta fita, kallonta yayi yana murmushi. “Ki kula min da kayan alatuna. Zan gayawa Auntynki!” Bata saurare shi ba, tayi gaba. How comes? Taya zata dauki wannan al’amarin.
Haka ya tafi ya barta da Faduwar gaba, tasan Aunty Fannah, da Bala’in kishi. Musamman akan Mijinta bata hada shi da kome ba.
—–
Kamar yadda suka bukata yau ta fara zuwa aikin, sai dai tunda ta isa bata zauna ba. A tarihin rayuwarta wannan lokacin shi yafi kome bata wahala. Sai yawo suke manyan ofisoshin gwamnati, da gidajen masu kudi,babu karya wanka iya wanka yau tayi shi. Shi yasa duk inda suka je cikin ruwan sanyi suke samun ganawa da Mutanen da ta je gani.
Past.
Daga cikin abubuwan da Nasr Hadejia da Aswad Yamini, yasa suka samu ganin Mayor na wannan lokacin, domin a basu damar Fahad Albagwi, a lokacin ya basu full attention dinsa, sannan ya basu damar gini a bakin tsubirin, tare da dauko masu gine-ginen zama daga kasar Canada.
Duk wanda ya saka gaskiya a cikin al’amarinsa, zai ga gaskiya domin a kasa da wata uku suka gama ginin, tare da fara kokarin bude shi, a lokacin manyan attajiran Fisto da Keivroto suka yi ta zuwa……
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI….!
Beauty and the Beast♡
007
_Wace ce Xno?🌚 Da za a wani dame mu da ita, yar daba da ita😏🚶🏽♀️ sai mun bindige yar tusa kanwarka tutu, yan comments section aji tsoron Allah 🙄🙄😏 ku daina abin da kuke._
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>>
_Past_
“Ni Malik!” Ya nuna kanshi, yana me kallon ilahirin mutanen da suke wurin. Sannan ya nuna su da yatsa. “Bani da had’i da ku, sannan shi bai da haɗi da ku, don haka kowa ya kama gabansa, idan ba haka ba tow kuwa zan mai da hankali wurin girbe rayuwarku.” Ganin yadda ya iya kashe dabobbin da Dulma yaƙe takama da su, babu tausayi balle imani, yasa suka fara ajiye makamansu, suna barin wurin domin kuwa suna son kansu. “kai Malik waye kai? Kana abu kamar wani mutum, bayan kowa yasan cewa uwarka ma karuwa ce.”
Wani irin b’acin rai yake ji, idan ya tuna abin da ya faru, idanunshi a rufe suke, a hankali ya buɗe su, sunyi wani irin jajjur tare da ƙwanciyar jini a cikin ƙwayar idanun. Ya juya tankar juda. Cillar da sigarin yayi ya juya kofar kegin zakunan ya ballo wani murtakakken karfe, ya nufi dulma da zazzababen gudu, yana isa wurin kafin Dulma ya ankara tuni ya zuba mishi karfen a tsakiyar kansa, zubewa yayi jini na fita ta hancinshi da baki da kunne, sannan ya juya wurin motar da ya zo da shi, ya ciro igiya, ya daure kafar Dulma ya daura da boddy motar, ya shiga jan shi. Kafin ya shiga cikin ma’aikatan, ya ciro mutanen da aka kama su, tare da sake mutanen da suke aikin bauta, sai da ya tabbatar da ya sake su, sannan ya rufe ma’aikatan ya zuba nakiya ya saka mishi lokaci, ya tattara dukiyar da ya gani, kudi da wasu abubuwan matasa da maigidanta da suke wurin ya mikawa. “Kuje da shi, duk wanda ya iya tuka mota, ya tabbatar ya ja sauran mutanen” daga haka ya shiga motarshi, sauran mutanen suka shiga motar da mutanen Dulma suke amfani da shi. Sai da yaga fitarsu, sannan ya take musu baya, yana jan Dulma. Har suka fitar daga Hill and Tim town, sannan ma’aikatan Ma’adinan ya fara fashewa da rushewa. Kome na wurin kamawa yake da wuta. Bakidaya ma’aikatan ya lalace ya kone, ya kuma rubta cikin ramin da suke hako kuzan. Yana hango rubtawan. Wani smirk yayi irin na tsantsanar mugunta da zalinci. Haka ya cigaba da gudun ganganci da Dulma, har ga shiga cikin garin Fiston ya tsaya a daidai kofar birnin. Ya sauka a motar, ya kunce dulma ya daura a kofar birnin. Sannan ya wuce zauna a saman motar. Yana kallon gawar Dulma har yau wutar da yake ci a ransa bai mutum ba, baya ji zai mutu. Kome zai yiwa mutanen ba zai tab’a wucewa ba. Domin bai ji ya huce ba.
Wasu daga cikin mutanen Shu’iba sun kai mishi labarin abinda ya faru, kamar zai yi hauka haka yake ihu, kamar ya fito daga maboyansa ya fuskanci Malik amma sun hana shi, domin babu Allah ya cikin al’amarin Malik. Yana ji yana gani Malik ya kashe mishi dan uwa, sannan ya rubuta a gefen fuskar gasar Dulma.
*Dan daudu idan ka gama gudunka, namiji yana jiranka* wannan abin da ya faru, ya sakawa Alhaji Nasr Hadejia, shakkar shigar Malik cikin lamarin, domin dai har ga Allah babu yadda za ayi su nemi taimakon dan daba, kuma makashi mara imani. Ko da yake a wani bangaren sun kammala aikin bude wurin shakatawar.
A lokacin bikin buɗewa ne, Iyalan Alhaji Nasr Hadejia suka tawo, daga nigeria. Aka yi bikin buɗewa cikin farin ciki da murna, har aka bude, dukkanin farinciki ya wanzu a fuskarsu. A lokacin ba laifi sun samu masu shigowa daga wasu ƙasashen yawon bude idanu, sai dai wasu abubuwan da suka faru kafin buɗewa wurin shakatawa. Kudin hannunsu yayi mugun sauka. Babu wanda zasu dauki ma’aikata da wasu abubuwan. Daga shi kansa Hadejian har Yamini, suna cikin wani irin matsi, sai suka yi decided amsar bashi daga banki inda suka nemi Mayor Fahad ya shiga cikin lamarin, shi kuwa ya ce musu. “Ai kuwa ba sai kun nemi na banki ba, shi mutumin da ya taimaka muku, yana badawa, kuma zai baku da Amana” duk da Nasr Hadejia bai so ba, amma haka ya amsa domin ya lura Yamini ya amince. Don haka ya saka a ransa, zai amsa amma matuƙar akwai ruwa a cikin zasu hakura. Don haka suka tsayar da lokacin da zasu je amsa,
**
*Present*
Sakarwa kanta, ruwa tayi tana tsaye a gaban shawa, baki daya kanta sarawa yake. Idan idanunta ba karya suke mata ba, tabbas taga wani abun da ya tsaya mata a kai, a lokacin da suka bar wurin yar sanda, akwai wani abu da ta san shi tsawon shekarun rayuwarta, daga baya kuma ta daina. Wani irin sarawa kanta yayi, tare da zubar da jini daga hancinta, tun shekarun baya take fama da wannan zubar jini. Sake ruwan tayi da karfi, tana me rike hancin, sai da ta d’ago kai sama, wani irin kara kamar na Harbin bindiga. Toshe kunnanta tayi, tare da zubewa akan gwiwarta. Hawaye ke zuba mata kamar an bude famfo domin dama idan ta fara irin wannan ciwon, ko a kaita asibiti. Ihu ta ta fara da karfi, wanda ya janyo hankalin mutanen gidan, har rige-rige suke na zuwa ɗakinta. Dakyar aka balle kofar ban daki, daura mata towel Ammyn Abbas tayi, suka fito da ita aka saka mata kaya, suka nufi asibiti da ita, a hanyar tafiyar ne Ammyn Abbas ta kira wata mata. “Dr Saddikah, gamu nan a hanya jikin Zeeno ya tashi fa ” “Ok ku kaita zan zo yanzu.” “Tow gamu a hanya.” Ko da suka isa, an karɓe ta. Aka shiga bata kulawa. Kafin wani lokaci har an mata alluran da ya saka ta, barci. Lallai dan adam ba a baki kome yake ba, yanzu kake takama an jima zaka zama ba kome ba. Abin da ya faru kenan.
After all Dr Saddikah tazo, ta shiga duba matsalar. Sai da suka gama ita da sauran likitocin ƙwaƙwalwa, sannan suka fito maganarsu ɗaya ce, ta takura kanta da tunani ne, akwai abin da take son lallai ta tuna.
_Past_
Sun samu ganin Malik, har sun samu kudin kamar yadda suka bukata, sannan abin da ya kara sake musu jiki, haduwa da suka yi da wani mutum da ya ce musu.
“Nawa kuka cefanar da rayuwar ku? Mutane kala uku ne a duniya.
Na farko masu rauni
Na biyu masu karfi
Na uku masu bada umarni
A ko ina na duniya suna raye.
Suna kasuwancin su ne akan haka ga duk wanda ya kawo musu tsaiko su aika shi garin da ba a dawowa…. Silarsu mutane dayawa sun rasa wasu nasu. Wasu sun yi kuka, wasu sun mutu. A duk lokacin da aka tab’a su suna fada suna karawa Kasuwancinmu ne aka tab’a. Nawa rayuwarku take da araha kuka sayar musu? Lallai kunyi kuskuren shiga tsinanniyar dukiyar da bata da albarka sai tarin tsinuwar al’umma.” Wannan maganar ya saka musu shakkar al’amarin Malik.
“Kusa ni ba karban dukiyar tsinanne bane mafita, biyan dukiyar tsinanne shaidani, ku gane rayuwarku ita ce fansar dukiyarsa ku maida mishi da kayansa. Domin baku yi magana da tsanannu ba. ” Yadda suka yi cirko-cirko suna sauraren mutumin me zubin mahaukacin, basu san Malik ya tawo ba, sai da ya ce musu.
“Ku kyale shi, ku je mahaukaci ne!” “Eheee! Ni ne mahaukacin? Bayan saboda kai na rasa duniyar da nake ciki. Saboda tsanannen dukiyarka.” Shiru yayi bai ce uffan ba, haka ya raka su Nasr Hadejia. Har suka bar garin, koda ya dawo kallon Mahaukacin yayi yana faɗin.
“Wai kai meye matsalarka da ni?” Tasowa mutumin yayi kamar zai dake Malik, ganin yadda ya taso, yasa Malik sunkutar shi, ya buga da kasa. Sai da kashin bayansa yayi kara.
Sannan ya juya zai tafi mutumin ya ce.
“Na hango iyakarka a cikin mutanen da ka yaudara,mutuwarka tana cikinsu. Kamar yadda aka haifa mana shaidani haka za a haifa mana waliyin da zai kashe ka.” Dawowa yayi ya ce mishi.
“Zan zauna na jira mutuwata, matukar bai fito daga cikin su ba, kai tsinanne ne! Kai ku min waje da Mahaukacin nan”
—–
Destiny.
Bayan sun koma, kamar ba zasu yi amfani da dukiyar ba,haka suka daure suka yi amfani da shi, A lokacin Yayan Alhaji Nasr Abubakar ya zo daga Nigeria kamar yasan halin da ake ciki, ya zo mishi da wasu kudaden, dama akan bayan wata shida zasu maida kudin,. Sai gashi ko wata biyu ba a rufa ba, sun samu kusan rabin kudin don haka bayan tafiyar Alhaji Abubakar, wanda suke kira da Baffayi, suka hada dukiyar Malik suka fara shirin maida mishi, don haka suka fara tuntubar Fahad Albagwi akan zasu maidawa Malik kudinsa. A lokacin yayi mamaki domin kudin ba kadan bane, don haka ya ce musu .
“Ku kawo na maida mishi.” Ganin yadda ya tsaya musu akan kome, so babu zancen zalunci ko damfara, suka dauki dukiyar Malik suka mikawa Fahad Albagwi. Suka tafi tare da gina rayuwarsu.
Ashe Fahada bai kaiwa Malik kudi ba, sakawa yayi a gaba ya cinye tass. Duk haka tun wata biyu saura yadda suka yi alkawarin, Malik ya fara tuntubar Yamini, shi kuma ya ce mishi ai sun turo tun wata hudu biyu ba, kasancewar tafiya ta kama shi zuwa Yemen. Bai gayawa Nasr Hadejia ba. Har ya tafi bayan tafiyar ne, Malik ya fara d’agawa Nasr Hadejia hankali. Karshe har Keivroto city yaje, amma babu wani abu me dadi, haka ya dawo. Kusan a lokacin Malik ya fahimci Fahad ya cinye mishi kudi ya gudu, sannan ya jefa mutanen da babu ruwansu cikin zancen yayi alƙawarin ba zai kuma takuwa musu ba.
Haka suka rabu, sai dai ko sati ba ayi ba, wasu mutanen suka zo aka kwace wurin shakatawar da sunan Malik ne ya turo su. Wasa wasa sai da ta kai hatta gidan da Nasr Hadejia yake an kwace kome na shi, ana cikin wannan yanayin ne,Yamini ya dawon yamini al’amarin ya kara kazamta domin a lokacin rayuwarsu ta zama mafi muni, domin barazana ake musu za a kashe su. Gashi a lokacin suna son ganin Malik abin ya ci tura. Bayin Allah nan sun ga rayuwa da iyalansu.
Wani dare me cike da tashin hankali, aka kawo musu hari, wanda yasa suka kora yaransu, amma ban da daya daga cikinsu, duk da sauran Yaransu gudu, Zeenobia bata gudu ba. Domin akwai shakuwa a tsakaninsu da iyayen. Amma sauran yaran suka gudu, ita kan bata gudu ba, koda mutanen suna zo buɗe musu wuta suka yi, a sanadin haka, harsashi ya shige mata kai. Faduwa tayi cikin jini don shekarunta basu wuce bakwai a duniya ba, abu daya ta rike *Wannan shi ne sakamakon Cinikin rai da kuka yi tsakanin ku da Malik, kunci dukiyarshi ya ci rayuwarku, Malik baya yafe dukiyarshi ko cikin uwarka ka shiga sai ka amayar da shi*
Daga wannan bata kuma sanin kome ba, daga wannan ƙwanciyar, sai da ta kwashe kwanaki ashirin a Asibitin. Kafin ta bude idanunta a wani dokan daji. A nan rayuwarta ta tabarbare, babu abin da ta tsana kamar karar bindigar. Kasancewar tana hannun yan ta’addan da suka kashe iyayen, su kansu basu damu da kansu ba. Balle ita, haka tayi ta kananun jinyar har wani rana da ruwan sama ya tsinka dam ya shigo gari, a lokacin ruwa ya korota bakin gaba, Alhaji Badaru Daniyal yana aikin aikin sayar da kifi, domin sana’ar da ya gada ne tun iyaye da kakanni. A wannan lokacin da ya same ya yi kokarin shigar da hukuma har aka mata jinya a hannun wata likitar ƙwaƙwalwa, jinyar da taci magudan kudade, tunda ta samu lafiya sai ta koma shiru-shiru. A kasancewar garin kusan rayuwar dabbobi ake wanda yafi karfin wani ya kwace abin hannunshi. Akwai wani azzalumi a bangaren garin da ya addabi Alhaji Badaru Daniyal, kullum sai ya zo ya kwace kudin sana’arshi.
Wasim sunanshi yana amfani da sunan Malik, yana.cin karen shi babu babbaka. A wannan lokacin duk inda Alhaji Badaru ya saka kafa, Zeeno da Abbas suna tare da shi. Ana haka ya tab’a zuwa ya saka Alhaji Badaru a gaba sai da ya bashi kudin. Kallon shi Zeenobia tayi, haka ya wuce shi da Yaranshi. A hankali kullum sai ta ganshi. Ranar da yazo babu kudi yasa a rufe Alhaji Badaru da duka, a gaban su Zeeno. Bayan sun gama suka tafi. Kallon su Zeeno tayi. Kafin suka nufi wurin Alhaji Badaru, d’ago shi suka. “Sannu baba, ba zasu kuma zuwa ba.” Ta fada, tana me shiga shagon ta dauko danko. Ta gyara shi sannan ta ja. Bakin Ruwa ta tafi ta tsunto duwatsu….
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI….9
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
Yau babu editing
*Past*
After few hours.
“Alhaji Badaru Daniyal, shawara daya ja nisantatta da wannan garin, ka ɗauke ta kuyi nisa idan ya cigaba da zama cikin su, dole zata rikide irinsu, amma idan tayi nisa ga nan zata tashi da dabi’u na daban, sauya muhalli yana da muhimmanci da taka rawa a rayuwarta. Don haka a nisantatta da nan.” “Shi kenan likita zan yi yadda kika ce.”
Kasancewar garin da Keivroto city tafiya ce ta kilomita talatin ba kusa bane, haka yasa Alhaji Badaru Daniyal, ya yanke shawarar barin garin ya koma cikin Keivroto city domin zai yi kokarin fara sabon rayuwa. Haka kuwa ya faru, a daren ranar suka bar garin Jista, domin rayuwar Zeenobia da Abbas da a lokacin yake fama da matsanancin rashin lafiya na kai, domin tun yana cikin ya hadu da laluran sakamakon yar bashin da Alhaji Badaru ya ci, bai biya akan lokaci ba. Shi ne garin rashin mutuncin Wasim ya ture Ammy da tsohon cikin ta fado, karshe ta haifi yaron da juyayyen ƙwaƙwalwa. Kuma mahaifarta ta samu matsala, tun daga lokacin bata kuma samun ciki ba, amma zuwan Zeenobia sai ya maye musu gurbin rashin da suka yi, domin da zasu kuma haihuwa maybe su haifi me lafiya.
Fitarsu daga garin, Yan sanda da Wasim suka nufi gidansu. Babu su babu labarinsu, kuma basu fadawa mutane, haka suka yi ta bala’i.
——-
Dawowar Keivroto suka sauka a tsohuwar garin Keivroto, wanda a kai barshi mazaunin yaku bayi, duk da ba wani nesa yake da asalin sabon garin Keivroto city ba. Amma akwai banbancin rayuwa a can, a anan kowani mutum yana kokarin kyautata alaƙarshi da na kusada shi, banbancin da sabon gari, kowa rayuwarsa yake. Matsalar tsohon gari getto area ce, anan ma matattarar yan iska da yan jagaliya take. A hankali rayuwarsu Zeeno ya sauya domin kuwa babu ruwansu da wani tsoron ko zata koma wata irin mutum.
Dake Alhaji Badaru Daniyal, mutum ne da yasan kan kasuwanci, don haka da yar kudin hannunshi ya fara gwada sayar da kifin ice, Allah ya kuwa saka mishi albarka.
Ai ganin yana samu ya saka su a makaranta, ita da Abbas duk ba wani sakewa yake da yara yan uwansa ba, amma kuma yafi Zeenobia fahimtar karatu sosai. Domin ita abu daya yake tsayawa a ranta, shi ne taga yadda yan daba suke dabancinsu, burgeta yaƙe.
Alhaji Badaru yayi yayi amma yarinyar nan taki, shekaru uku da dawowarsu garin Keivroto tsohuwa. Tana da shekara goma cif a duniya. Aka turo ispetor Ayuba, kame a unguwar sakamakon cunen da aka yi musu wai akwai yan kwaya da masu safarar kwayoyi. A ranar aka yi wani irin kame har da wani matashi me suna Fa’iz. Kakar Fa’iz suna gida daya ne dasu Zeeno.asalima babu abin da ya aikata kawai kamen ne ya fada kansu, kuma a yadda suke jin labarin kashe su za ayi, Fa’iz yana koya musu karatu ita da Abbas.
A lokacin da labarin ya fito an rigada an bada umarni, daga fadar gwamnati. A lokacin babu wanda ya isa magana. Hakan su da Inna suka yi ta yawon bin ofishin yan sanda, amma babu labarin abin tausayi. Kusan sati daya ana niman inda suke amma babu labarinsu. Sai ranar takwas ana ruwan sama, aka kawo musu gawarsu, ganin yadda gawarsu ke zubda jini yasa Zeenobia ta yanki jiki ta fadi abin da ya faru da ita three years ago ya dawo mata, dole sai da aka kaita asibiti. Sai da tai sati biyu aka sallame ta, nan ma ta manta batun Iyayenta. Sai dai kuma abu daya shine mutuwar Fa’iz. Sosai ya tsaya mata a rai.
Gashi tana da saka abu a ranta, sai ta zama ciwon yana yawan tashi a kai, sai da aka mai da ita asibiti. Ba ƙaramin kokari Alhaji Badaru Daniyal yayi ba, kafin ta koma daidai, sai dai kin karatu ya sake zama a ranta. Shekarunta goma sha uku, ya saya musu wani katon fili. Inda aka fara ginin gidan sama me hawa uku, cikin farin ciki iyalan nan suka gina gidan domin sawwaka rayuwar talakawa, a madadin kudin me yawan gaske da zaka biya a shekara sai ka biya kadan sauran ka taimakawa gidanka, idan ka biya rabi saura zaka yiwa iyalinka hidima.
Sai da aka ɗauki shakara hudu ana ginin, a lokacin da aka kammala. Ginin a ranar wani abu ya faru, wanda ya saka yarinyar nan dawowa mara jin magana sama da shekarun baya. Ranar ana ta bikin murnar bude sabon gidan bakiɗaya alumma murna suke, domin sunan gidan Al’umma Charity House. Anyi shine domin mutane, marasa galihu da gata. Sai dai ranar a madadin farinciki, bakin ciki aka yi. Don kuwa ana cikin walimar bayan budewa aka kira Alhaji Badaru. Tunda ya fita ba a kuma ganinshi ba. Sai gawarsa aka samu. Wasim da goyan bayan Asp Ayuba sun kashe shi, tare da cewa yaci bashinsu ya kashe kansa.
Don sai da suka kashe shi, sannan suka rataye shi, wannan abin ya saka Ammy cikin shock. Kafin a bude gidan ana gobe kenan. Alhaji Badaru Daniyal ya tara su, lokacin Zeenobia tana wurin yan daban unguwar, sai da ya fita ya riko kunnenta. “Ayya Abba idan ka cire min kunnena da wanne zanji nasiharka, don Allah ka bar min kunne na!” Sai da ya kawo ta falo ya ce mata. “Zauna mara jin magana.” Kallon Abbas tayi ta ce. “Tow Abba ka aura min Abbas, sai na daina rashin ji kaji.” Ware idanu Ammy tayi, ta ce mata. “Allah na tuba, Baby ai kin fi karfin Abbas, shi ba irin Mazan da zaki iya xama da shi bane, sunanki yana tafe da tarihi, iyayenki sun saka miki suna me daraja, in Greek mythology language, ke mace ce da zata yi daraja, ba kananun mutane zasu same ki ba. You’re like Queen!” Gyada kai tayi, tana kallon Alhaji Badaru Daniyal yana kallonsu idanunshi cike da kwalla ya ce mata. “Ammynku zata baki takardu, nasan idan yana hannunki ba zai samu matsala ba, har da ta jinyarki, mun samu haduwa da Dr Saddikah, tace za a miki aiki. Amma nace a bari wata shekara lokacin kin cika shatakwas, ga gidan nan na dakunan sama baki daya nashi ne, shagunan kasa Kuma naki ne, akwai shaguna a kasuwa mallakar Ammynku ne, Zeenobia don Allah kiyi karatu ki nutsu, baki daya mutanen da suke wannan gidan, naki ne a kula da rayuwarsu, na baki amanarsu. Ki rike gaskiya da amana, kar ki sake ayi amfani da ke domin ruguza rayuwar wasu, naso nayi nisan kwana na ga yadda zaki zama the great queen Zeenobia Queen of Greek”
Yadda yaƙe musu bayani sai suka zuba mishi idanu, basu san dare yayi ba, sai da suka ji munsharin Abbas,
Har washi gari haka yake kafin mutuwarsa, lokacin da Zeenobia kamar gunki ta koma, bata da wani kuzari. Har aka sauko da gawar Alhaji Badaru Daniyal, gidan farinciki ya koma gidan Bakiciki da kuka. Har aka shirya shi babu wanda ya iya magana aka kai shi gidanshi na gaskiya. Ana tafiya da shi sai ga Yan sanda da Wasim da Asp Ayuba.
A lokacin tana cikin wannan yanayin, suka iso tare da fara surutun su fita su bar gidan na Wasim ne, duk maganar da ake Zeenobia tana kallonsu. Haka suka yi ta destroy kome na gidan, sai da suka kori kowa, ta shiga cikin gidan ta rufe get din gidan. Sannan ta d’ago kai ta kalli Asp ta ce mishi.
“Kuskuren da ka aikata yasa ina ta bibiyarka,amma nasan dole nasan wata rana zaka dawo, zan rufe tarihinku. Kafin yan jana’iza su dawo. Ban san kome ba amma na san Abba.” Dauko chain na karfe tayi ta shiga nad’e hannunta, hawaye na zuba mata, wani irin pain take ji mara daɗin misaltawa, gani take idan ta bude baki zata iya hàdiye su baki daya. Don haka ta shiga dukar, gashi a lokacin da ta rutsa su, babu bindiga, haka tayi ta dukar su, domin she is out of control. Sai ya kasance baki daya ta haukace dukansu kawai take tana hango Gara ta kashe su, wanda haka yasa kawai ta shiga shake su da Chain ɗin. Har suka mutu. Hancinta da kunnenta jini yake zuba. Faruwan wannan al’amarin ya ja aka tafi da ita asibitin mahaukata. Wanda Dr Saddikah ta amshi case. Ta cigaba da kula da ita, har zuwa.
Sai da tayi jinyar wata bakwai, a lokacin da aka yi binciken mutuwar Asp, mutane dayawa da aka bincika sun ce basu san me ya kashe shi ba, kuma hakan suka saka a ransu, musamman Innah da ya kashe mata jikanta, wannan dalilin yasa aka rufe mutuwar Asp da Wasim, babu labari ita kuma Zeenobia tayi jinyar wata bakwai a asibiti, kafin ta dawo da matsin lambar Ammy da Inna ta karasa makaranta, wanda daga baya ta fara diploma, shima wasa da shiririta ya ci karfin ta, jagaliyanci kawai da tsageranci yake damunta, kashe Asp ya saka ta samu girma da daraja da aka saka mata suna yar kunama, daga nan suka shiga harka da yan siyasa, babu ruwanta ta karya na karyawa, na bar su da jinya domin rokon da Ammy take mata na don Allah kada ta kuma kisa, yasa bata kuma.kisa ba, a wannan yanayin Abbas har ya shiga jami’a, dama kuma tafiyar karatunsu ba daya ba, domin yafita kokari da mai da hankali, saboda yana gane karatu. Tunda suka girma sosai, Allah ya daurawa Zeenobia kaunar Abbas, wanda ta kasa ganewa soyayyar aure ce ko soyayyar da iyayensho suka nuna mata ne,
Wani taro da aka yi na siyasa ta hadu da Mr Amjad, sakamakon sakata da wani dan majalisa yayi tayiwa wani mutum barazana, a inda ake taron. Haka yarinyar nan ta ratsa cikin mutane, ta riko wuyar dan siyasan.nan, ta ce zata kashe shi ta kuma jin ya soki lamirin wancan mutumin, wannan abin da tayi ya saka Amjad nimanta..ya kuma fara kashe mata kudi domin kudirin dake ransa.
Tare da bata shawaran tayi karatu domin zata ci gajiyar iliminta. Dakyar da sudin goshi ta gama, domin sai da Ammy da Inna suka yi tsaye akanta, shima ta gama da uban CO, a lokacin ita kanta tayi namijin kokari, take fada amma tabbas rayuwar da take bashi ne mafarkinta ba, mafarkinta yana can wani wurin.
*Present*
After 13 back.
“Dr Saddikah ba za a iya aikin ba ne yanzu? Yarinyar nan tana wahala, idan ta cigaba da zama haka zamu iya rasata!” Inji Ammyy.
“Ba aikin bane wahala, ana yin aikin ne a garin Michigan state, sune kawai suke da alhakin tab’a kanta, anan kuma ana yi a Menk Jordan World cares, shi daya ne s faɗin ƙasar nan, idan aka ce za ayi mata aikin ana bukatar miliyoyin kuɗi ne.”
Shiru suka yi, abin da yazo ran Ammyn gidan da suke zaune, a sayar da shi kadai a mata jinya, ta kare gidan na tsawon shekaru da amana, sai ta tashi za aji ta bakinta.
—-
Amjad.
Kiran wayar shi MD yayi ya ce mishi.
“Yallabai yarinyar nan tana samun takun saka da sabuwar yar sanda da aka kawo, me zamu iya mata?” Tsaki yayi ya ce.
“Kaji shaidaniyar yarinya ba, don Allah ka saka min idanu akanta, zata lalata min shirina ni da nake son a wanke min ita.”
“An gama yallabai ” ya kashe wayar, yana wurgi da ita, kafin ya mike yana me leka waje. Ko sati biyu bai yi da fara kwana a cikin gidanshi ba, tsabagen tsoron Malik Menk Jordan.
Sake labule yayi ya rufe yana ajiyar zuciya , kafin ya nufi uwar dakinshi.
***
Lalla Salmah.
Zaune suke suna cin abinci, kallon yarta tayi a nutse kafin ta ce mata.
“Princess, yau zan tafi ganawa da Malik Menk Jordan.” Sake spoon din hannunta tai, tare da ware idanunta.
“Maama da gaske? Zan bi ki please”
Girgiza kai tayi, tana faɗin. “Zan so haka, amma haduwar mu ba zai min kyau ba, shi mutum ne da baya bukatar ba zata, yana bukatar a sanar mishi kome kafin ya iso gare shi.”
Kwabe fuska tayi tana faɗin. “But me yasa?” “Ki shirya next week zaki tafi Demark wurin su Wahiba da Wahida, tare da Nadrah, ki kame kanki bana son zubda aji, ka da ki manta Nadrah Khamis Shatima har an saka ranar baikonsu da Malik yayi rejected ɗinta, and Malik yana bukatar macen da zata kula da Wahiba da Wahida ne, so ki kula da su. Domin mu samu Malik duk abin da kika yi matukar me kyau ne, zasu gayawa Malik. Kada ki sake Nadrah Khamis Shatima ta rena ki, kin ji ai? Domin Elbashir ya gaya min saura three months su gama karatu, and na shirya miki wani course na musamman, idan kuka dawo zaku sauka a gidan Malik ne, kada ki manta Malik yana cikin jerin members na PEL, na Europe. Iya wannan kawai aka ce ya mutu ya bar miki me kike tunani? And ki san yadda zaki nemi digital dinsa. Da zafi zafi ake dukan karfe. Babban burina na auri Malik na mamaye shi, amma samunki ya rufe min mafarkina, idan kika shiga zan miki bayanin yadda zaki yi da kowa……..
#MaidaLalla
#Nadrahshatima
#Zeenobiahadejia
#Malikmenkjordan
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI….8
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
Don kar abin ya tsaya a ran yaran, ya mike tana karkad’e jikinshi ya ce musu.
“Babu abin da ya faru, kawai sun min haka ne don ban biya su kudinsu ne, amma nasan babu abin da zai kuma faruwa, In sha Allah.” Ya fada yana kokarin goge bakinsa. Domin baya so su fahimci hakan a matsayin zalunci, baya kaunar zalinci kuma ba zai yarda na kusa da shi yayi ba. Da wannan suka tattara sauran yan kudadensu, suka koma gida.
—–
Malik.
Shigowa wasu kartin maza suka yi, suka tsaya tare da ƙamewa, “Mene ne labari?” “Mun share duk wani shaida da yan sanda zasu yi Investigation akai, babu wani alama domin mun rufe tarihinsu.” Ajiye pen din yayi ya koma da baya, yana me jingina da kujeran da yake kai, yana wani irin murmushi tare da juyawa da kujeranshi.
“How dare zasu bude min wani kasuwanci? Bayan ina nan a raye? Duk wanda zai bude wani kasuwanci dole yazo ya lashe kafata. I’m the only king bana buƙatar gasa da takara. Duk wanda ya taba min dukiyata a aika min shi in da aba dawowa.”
Murmushi bakidaya wannan shine Kasuwancinsu, a kashe ko a raya su suke da ra’ayi da yadda zasu yi, shi yasa daga su har Malik din dukiyarshi yake kara habbaka. Hahawan rashin mutuncin da yake wakana a tsakaninsu da kananun yan kasuwa, ya kara kuntatta mutane. Gashi wani abin takaici duk abin da yake faruwa gwamnati bata da ikon magana, tow ai mutanen da zasu yi magana sune a jikin Malik, akwai wanda ya isa yayi magana ne? Babu kuwa.
—-
Washi gari.
Mutanen Wasim sun sake dawowa, kuma dama wannan shi ne, fatan Zeeno kenan kuma sun dawo din, saman kwanon rumfar shi ta hau idan ka yadda yarinyar nan take makale a jikin rumfar sai tsoro ya kama ka, amma kuma haka bai sakata jin ko dar ba, duwatsun da ta tara a cikin jakar fata, take cirowa a hankali taja dankon ta sake shi da ƙarfi. Sai dai mutum ya ji “Kul!” Tare da ihu me karfi suke sakawa, tsayawa tayi, ganin suna nimanta, sai bata kuma Harbin ba, incredible kawai sai da ta bari sun sake har suna yiwa mutumin farkon fada, kawai yarinyar nan tayi ta sake musu, babu kakkaunatawa. Baki daya ta hana su sakat. Sai da ta buwaye su ta zame musu alakakai kamar, daga sama suke jin al’amarin Harbin, babu shiri suka juya da gudu suka bar bakin ruwan, sai da suka tafi sannan ta sauko daga saman rumfar. “Abba basu kuma dawowa.” Ta fada tana kallon, tana kallon shi, rike da dankon. Karba yayi ya boye. “Zeeno me yasa kika yi haka? Babu kyau kar ki kuma yin haka.” Gyada kai tayi, ganin haka ya rufe shagon suka bar wurin. Ko da isa gida yana shiga suka rufe kofar. “Maman Abbas, kin ga yar nan da zuciya yau kore min mutanen Wasim tayi, yanzu ban san ya zan yi ba.”
“Mun nime Allah ya kawo mana iyakarsu, sai Allah ya bamu ita don haka babu abin da zance sai Alhamdulillahi.” Ta zaunar da Zeeno ta zuba mata abinci. Kadan taci ta tsame hannunta, tana faɗin. “Ina Abbas?” Kallon dakin tayi kafin ta ce mata. “Yana barci” gyada kai tayi. Ta mike ta kai sauran abincin dakin girki. Sannan ta wuce dakin Ammyn Abbas ta kwanta.
Washi gari da suka fito bakin ruwa, sun sami Wasim da mutanen shi. “Wani dan shegiyar ne ya jefi mutane na?” Maida Zeeno baya Alhaji Badaru yayi, zai tura ta gida. “Waye ya daki mutane na?” “Ni ce!” Ta fada da karamin murya. Bud’a mata hanyar aka yi, kanta a kasa, kafarta da babu takalmi tana wasa da ƙasa. “Ke!” Ko gizau bata yi ba, ta maida hannunta baya, tana rike da karfen rodin da ta dauka bayan Alhaji Badaru Daniyal ya maida ta baya, tana wasa da ƙafarta. “Kai dauko min wancan yar hanji!” A yadda ya ganta ya zata irin yaran nan ne masu shegen baki da tsoro, lokacin da ya iso sai da ya duka ya ce mata. “Yarinya wasa kike ko da gaske!” Kamar wacce wani abu ya shiga jikinta, ba tare da ta bude idanu ba, ta kaiwa fuskarshi wani mahaukacin duka da karfen sai da ya cilla can. Hannunta yana rike da rodin ta wani mika shi. Zaka rantse irin yaran cartoon din nan ne, na Avatar ko wonder woman, lokacin tana karama. Yadda tayi dukar hatta Wasim sai da ya sauko a samar motar shi, ya gwalalo idanu waje. “Kai ku min fata-fata da namar yar tsiyakin nan!” Murmushi tayi, tare da jan kasa baya ta ce. “Idan kuka tab’a ni, zan kyale ku salin alin ku yi fata-fata da ni, idan na kararaya kasussuwanku, babu wani shugaba sai Baba na!” Ta fada tana kallon s kou. Idan da wani zai iya bada shaida tow abun da zai fada shi ne tana cikin mutanen da ayi experiment dinta aka yi, nan kuwa babu abin da yake aiki akanta sai wannan harsashin da yake jikin ƙwaƙwalwarta kamarshi. Murmushi tayi ganinsu tika-tika kamar giwaye, hatta gudun da suke kasa tana amsawa kamar zata burma. Da’ira suka mata, yadda zaka fahimci Yarinyar nan hatsabibiya ce, domin wani irin dukar su take babu kakkautawa. Kamar mayunwaciyar xakaya haka take musu duka da karfe ga hannunta baya sab’a abin hari dake akwai karfe rodin sai da ta gama musu dukar kawo wuka, sannan ta tsaya cak, zubewa suka yi. Ta d’ago fuskarta da yayi kaca-kaca da jini da zufa. Ta nufi Wasim kafin yayi wani yunkurin guduwa ta jife shi da karfen sai da ya fadi a ƙasa.
Daukar karfen tayi tana nuna shi da karfen. “Kar na kuma ganinka a nan yankin daga yau, yankin Baba na ne tashi ka. ” Dakyar ya tashi ya ja motar shi, ya kawo yayi ta jigilar kwashe mutanenshi ya zuba su cikin motar. Sannan ya bar wurin.
Damshi da dumi taji a hancinta, a hankali ta d’ago fuskarta zata yi magana, sai zubewa tayi a wurin, da gudu mutanen kasuwar kifi suka rufa mata, tare da daukarta suka nufi asibiti da ita. A lokacin Dr Saddikah ita ta tsaya akanta. Sai bayan awa awa daya ta fito daga kanta, tana kallonsu. “Yarinyar nan rayuwarta tana cikin hatsari, me ya faru?” Shiru sukayi kafin daga baya, suka bata labarin abin da ya faru. Ai idan ranta yayi dubu ya b’aci, yadda take fada kamar zata dake su. Haka yasa suka sunkuyar da kai. “Bamu da zabi ne, ba zamu so fadawarta hatsari ba”
“Gaskiya a kula da rayuwarta!” “In sha Allah!” “Abin da yasa nake magana, a kowani motsa jiki da fushi harsashin kara nutsewa cikin kanta yake. don Allah ku kula da ita.”
Abun tausayi haka suka yi jigun-jigun, sai dare suka bar asibitin. Hmm tashin hankali wanda ba a saka masa rana domin kuwa sabon tashin hankali aka kuma haifarwa. Domin washi gari sai yan daba sun kai mota ashirin, lokacin ta farka domin har asibitin suka biyo ta. Lallai a fito musu da ita, suka fara bibiyar dakuna da aka ki fito da ita, da gudu Dr Saddikah ta nufi dakin tare da rufewa lokacin Ammyn Abbas tana bata abinci. Rufe kofar dakin tayi. “Dr lafiya?” Ammyn Abbas ta tambaye ta, “babu kome” dukar kofar aka yi da karfi, tayi maza ta fisgo hannunta suka fada ban daki.
A hankali ta cire hannun Dr Saddikah, ta ce mata. “Ammyna da Abbas kuma fa?” Fauce hannun tayi ta daki wurin key fita yayi ya cilla cikin dakin daidai shigowar su, sake dukar kofar tayi sai da ta balla. Cire piece na kofar tayi, tana faɗin. “Allah sarki me ya kawo ku?” Ta fada tana fitowa, nufar wurin Ammyn tayi ta shagwab’e ta ce mata. “Ammynay bani naci” jikinta na rawa ta shiga bata abincin tana ci. “Kee!” Yatsar hannunta ta kai baki ta ce mishi. “Dalla yi min shiru, sai na koshi waye ya gaya muku ana magana idan ana cin abinci.” Gyada mata kai suka yi, ta cigaba da cin abincin. Har suka tsaya idan aka ga basu dawo ba, wasu ma zuwa suke kafin kace me sun cika dakin. Tana gamawa ta cewa Ammyn .”Ammyna bari na share musu tantama. Waɗannan suna bukatar kulawa, kai bani abin kunnan nan” mika mata yayi har da radion ta kura karar, sannan ta cewa Ammyn. “ki rufe shi kar ya ga abin da yake faruwa ya fara jin tsoro” a hankali ta juya, “zaku taka min baya ne, ko kuma zan tara muku nauyi ne?” “Mun zo yin dagga-dagga da namarki ne!” Had’a hannun tayi tace musu. “Idan na sake ku da hannu, Ni ce zan yi jinya gara na nime bulalar da zan iya gabatar muku da kaina.” Karfen gadon ta shiga kokarin ɓallawa, sai da ta karyo shi, abin da ya basu tsoro kenan. Suna ganin kamar ba bil adam ba ce. Takowa tayi har gabansu, ta sunkuyar da kanta. Kafin ta d’ago kai sama jini yana zuba. Daga hancinta Idanunta rufe motsin takunsu kawai taji kanta yana sama, gyara rike karfe tayi koda ya iso kafin ya sauke mata,.ta daki mafitsaransa. Durkusawa yayi akan gwiwarsa ya fasa ihu tare da zubewa a gabanta. Take kansa tayi ta tsaya akan shi. “Mu cigaba ne?” Fita suka yi da baya-baya. Har suka isa wajen sai da sukayi kamar kafa goma a tsakaninsu, kafin suka tsaya, karfen wancan mutumin ta dauka hannu bibbiyu. Ta kalle jini na zuba daga hancinta, gogewa tayi tana kiran su, Dr Saddikah kamar ta fasa ihu. Ciwon yana ta’azzara ne. Abin tausayi yarinya ta koma kamar wacce aka kara mata wani abu. Da gudu suka nufeta babu tausayi ko imani balle jin kai. Haka suka rufeta da mugun nufi.
Ihun kartin maza kawai yaƙe tashi a wurin suke da yawa suke da ihu, ba mamaki na mutum ba ce, aljana ce domin a cikin minti arba’in, ta tara su a wurin. Karkarya musu cinyoyi da hakarkari. Masu nisan kwana da lafiya suka yi ta juyawa a guje. Bata kyale su ba haka tayi ta binsu tana kai musu duka. Har suka fito harabar asibitin, da gudu suka yi ta juyawa da motarsu, har suka bar asibitin. D’aga kai sama tayi tana son jinin ya tsaya. Kafin ta yanki jiki ta fadi.
<|=|><|=|>
*Present*
“Me ya faru da har ƙwaƙwalwarta ya kuma tabuwa? Kun manta halin da take ciki ne? Ya kamata a kula da lafiyarta domin kuwa rayuwarta tana cikin hatsari sosai.”
“Babu wanda ya bata mata rai, sai dai a yan kwanakin nan, uzuri ya mata yawa bata hutawa kuma Hutawa tana cikin ka’idodin kula da lafiyarta, amma zamu kula da ita don Allah ayi wani abu!” Inji Ammyn. Tausayi Zeeno ya kuma shiga ransu. “Ita domin wani yayi farinciki ita zata fadi. Ban san yadda zamu yi da Zeenobia ba, mun bar wancan garin ne domin ita, yanzu kuwa rayuwarta ta kuma fadawa matsala!”
“Idan aka ce za a mata aikin cire shi, dole za ayi rasa rayuwarta, amma kuma dole a rabata da shi domin tana kara shekaru lafiyarta zata kassara sama da yanzu, idan muka yi sake zamu rasata.”
“Dr Saddikah ya samu yi?
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI….10
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
Tsurawa Mamanta idanu tayi, sannan ta ce mata. “Maama to me yasa ba zaki nima mana shi ta wani hanya ba?” Yar ta kalleta, kura mata idanu tai, sannan ta ce mata.
“Malik baya cikin irin wadannan mazan, don haka dig your food, na gaya miki wwnda zaki yi sauran ki bar min a hannuna.” Gyada kai tayi tana cin abincin.
Ajiye spoon tayi ta ce mata. “Maama Yaran Malik ne Wahiba da Wahida?” Dauke kai tayi, kafin ta ce mata. “A’a ba Yaransho ba ne, Yaran rikonshi ne!” Tura baki tayi, “Amma Maama shi ne yake ji dasu haka?” “Ya isa haka!” Uwar ta fada, tana me dauke kai. Taya zata gaya mata abin da ya faru? Har zata wuce ta ce mata. “Princess! Kada naji ko na gani, kome yana buƙatar sirri don haka koda wasa kada na ji wannan labarin a bakin wani.
Gyada kai tayi, tana me mikewa daga table din, wayarta da yake gefenta ne yayi kara. Idanun Lalla Salmah ne ya sauka kan wayar. “ba na rabaki da Yaron nan ba?” Tsuru-tsuru Maida tayi tana kallon wayarta. “Wai sau nawa kike son na gaya miki, baki dace da shi ba? Kina da rayuwar da tafi tashi.” “Hmm! Maama dan uwana ne, ba wai yana zuwa nan da sunan soyayya ba ne, ko kira ba. Kawai yana kira na ne a matsayin kanwarsa.” Kura mata idanu tayi kafin ta ce mata. “That family basu cancanci dace dake ba, ki nutsu kina da rayuwa sama da tasu, kada na kuma jin wani abu ya hada ki da su, domin zan sab’a miki.” Gyada kai tayi Idanunta yana cika da kwalla. Har zata wuce ta ce mata. “Tun last week ya gaya min, Anyi admitting Abbana a hospital, yanzu ma ya kira ya gaya min ne.” Ta fada hawaye na zuba mata. “Pick the phone;” ta gaya mata tana dauke kai, dauka tayi a hankali ta ce mishi.
“Hello bro! Ya jikinshi.” “Maida jikinsa da sauki, amma yana da kyau kizo ki duba shi, koda ita Aunty ba zata zo ba. Please ki fahimci girman hakkinshi da yake kanki mana my sister shima yana da hakki akanki.” Kallon Lalla Salmah tayi ta ce mishi. “Ok zan zo in sha Allah, ka gaida min shi ka ji sai na zo. ” Ta kashe wayar. Kamar bata ji abin da suka ce ba, so sai tayi fuskar tare da ɗaukar jaridarta ta bar wurin abincin, dama taji ne me ya same shi, kuma taji he still alive. So bata da wani case da shi. “Maama don Allah ku bar ni na je, na ganshi.” “Tunda bai mutu ba, ai da sauki ko? Ya ce miki ya mutu ne?” Inji Lalla Salmah. “But Maama yana da hakki a kaina, Maama mi bar ni naje na ganshi, ko kuma wallahi ba zan tab’a miki yadda kike bukata ba!” Kura mata idanu tayi, wani lokaci Maida kamar Ubanta take, don wani lokaci, bata iya juya su a saukakke sai sun bayyana mata kansu na da ƙarfi. “Ok kina nufin taurin kanki zai saka nace Maida Sheikh jeki ki duba Babanki?” Hàdiye yawu tayi cikin tsananin shakkar Uwarta. Bata mantawa lokacin da ta dawo hannun Uwar, duk da taji labarin a bakin Nanny ta gaya mata sai da Malik Menk Jordan ya saka baki aka bawa Uwarta ita da sharadin zata na barinta zuwa wurin Mahaifinta, amma zata iya cewa har ta gama secondary school, ba zata kirga zuwa ganin mahaifinta ba, domin Babarta ta k’amk’ame kome, ta hanata zuwa wurin danginta da kowa nata, shima wanda Anwar din da yake kiranta, yaso ta tun tana wurin Babanta, kuma har yau shi daya yake zuwa gare ta, amma mamarta bata kaunar alakarta da danginta. Zubewa tayi a gabanta tana kuka ta ce mata. “Don Allah Maama kada ki hana ni zuwa gare shi.” “Zaki je kiyi kwana biyu, daga can zaki na zuwa makaranta. Bayan nan kuwa hmm!” Yadda tayi maganar yasa ta cigaba da abin da take. “Na gode.”. Ta fada muryanta yana rawa, “kin ji dadi?” Gyada kai tai hawaye na zuba mata, domin tasan halin Uwarta, tabbas akwai wani abu a kasan ranta.
★★★
After few days.
Zaune take, tana waya a hankali duk da ba wai ta saba da hakan ba ne, sai dai yadda kanta yake masifar ciwo ta ce.
“Mr Amjad ai na gaya maka bani da lafiya, tow me zan iya yanzu, yar sandan nan ta ishe ni.” Shiru tayi kafin ta ce mishi.
“Look na gaya maka bani da lafiya, idan baka yarda ba, kazo ka duba ni.” Shiru tayi kamar zata yi kuka ta ce mishi. “Ok zamu zo na ganki” gyada kai tayi tana faɗin.”sai kazo ” daga nan ta kashe wayar tana kallon Black. “Sai yaushe za a sallame ni?” Murmushi yayi ya ce mata. “Sai kin samu lafiya, kin ga har yau kanki bai daina ciwo ba” kallonshi tayi na wani lokaci kafin ta ce mishi. “Ban yarda da kai, gaya min me kuke shirya min.” “Yar kunama, Al’umma Charity House aka saka a kasuwa.” Wani irin shake wuyar shi yayi yana zare idanu. “Waye ya baku wannan shawarar?” Dakyar ya ce mata. “Sake min wuyata, wallahi kashi daya gare ki” sake shi tayi ya ce mishi. “Out zan sauya kaya.” Fita yayi ta cire kayan jinyar, ta sako riga da wando 3qrt. Sai farin shirt sai pink top da daura a saman rigar, gashin kanta ta daure da dankwali ta nufi kofar zata fita ta hadu da Dr Saddikah. “Mara lafiya ina zaki?” Wani kallon sama da kasa tayi mata, ta kalli black da yake gefe, cire glass din da yake sakale a aljuhun rigarsa tayi, ta dauka tare da toshe Idanunta ta ce. “na sallami kaina, tunda ba ajiyar dole” riko hannunta Dr Saddikah tayi tana faɗin. “kina jefa rayuwarki hatsari ki hakura a nima miki…” A hankali ta zame hannunta. “Tun daga haihuwata zuwa mutuwata, babu abin da Allah bai rubuta ba, so mazge babu abin da zai faru.” Ta wuce abin ta, tana murmushi tayi tana tafiya, hankalinta kwance. Girgiza kai tayi, tana tausayinta amma kwarin gwiwarta yana kara burge ta, koda yake yarinya ce har yau akwai Yaranta a kanta.
Shiga motar tayi tana faɗin. “Black babu wani abu a account ne, ina son a sauya mota nan.” “Akwai amma babu yawa, dake ance a sayar da kome za a miki aiki!” Ware idanu tayi ta ce. “Kambu! Lallai sai na zane kowa!” Kallonta yayi na wani lokaci kafin ya ce mata. “baki jin abu na zuba a hancinki ne?” Bayan hannunta ta kai ta goge hancinta. Jini ta gani tsaki tayi tana faɗin. “Habbo ne.” Dukar motarsu aka yi ta baya, ta buge kanta da karfen jini ne ya zubo daga kunnunta, ta rike kanta. Tana buɗe Idanunta dakyar. “Na mai da ki asibiti ne?” Girgiza kai tayi tana faɗin. “Mu wuce gida kawai” ta fada tana mai da kanta, saman kujeran. Har suka isa gidan tana goge hancinta. Wayarta ce tayi kara, ya duba. “Ke kin ce kina asibiti muna zuwa an ce an sallame ki.” “Eh na dawo gida ne!” Daga haka ta kashe wayar, tunda suka shiga cikin gidan, ta zubawa mutanen gidan idanun. “Me yasa zaku min haka? Ammyn!!!” Lekowa tayi ta ce. “Kai Black sai ka dawo da ita!” “Ai Hajiya ita tace na dawo da ita. ” “Tsoronta kake ji da zaka dawo da ita?” Kallonta yayi ya kalli Xnoo. A ranshi ya ce. ‘hajiya ko waye ya sha shaƙar Xnoo dan ubansa dole yayi abinda bai shirya ba.”
Fada Ammy ta mata sosai, ita kuwa ta kafe akan babu batun sayar da sayar da gidan, karshe yawan maganar da tayi yasa ta suma, sai da aka kira Dr Saddikah, tazo ta saka mata ruwa da allura, batun sayar da gida Zeeno ta rantse babu shegen da ya isa ya saya gidan matukar tana raye, da wannan suka bar zancen. Sai dare Mr Amjad yazo ya dubata, ya ajiye mata kudi sannan ya bar gidan, duk da tsoronsa kada Malik ya biyo shi ne. Babban burinshi dukiyar Malik Menk Jordan, shi yasa ya nace lallai sai Zeenobia.
Sai da tayi kusan wata guda a gida tana jinya, kafin ta koma aikinta.
Ranar Monday ta isa kamfanin da wuri, cikin nutsuwa ta nufi office din Mr Amjad, tana me gaishe shi, sanye take da white t, sai red top, da skirt black, iya gwiwarta, sai leggis da ta saka, kafarta wani hill ne black. Wuyarta ta nad’e wani dankwali multicolor, duk da bata yawan kwalliya amma yau tayi kwalliya har da lipstick red, kallonta yayi sosai, har ga Allah Yarinyar nan idan baka da imani ba zaka iya dauke kanka akanta ba, domin kuwa tana ji da kuruciya sosai. Tura mata file yayi ya ce mata. “Gashi nan!” Dauka tayi tana kallon file din, a hankali ta ce. “Na waye?” “Malik Menk Jordan!” A hankali ta bude file din Babu hoton kowa kamar yadda sauran ya kasance akwai hotunansu. Sake bude daya shafin tayi ya ce mata. “Elbashir Jamal Arab me kula da harkokin kasuwancin Malik kenan, hannun daman Malik ne, dole ki fara ganinshi kafin Malik.” Sake bude daya shafin gaba tayi ya ce mata. “Khamis Shatima, me kula da harkokin siyasar Malik ne, yana da kyau ku haɗu, idan baki samu ganin Elbashir Jamal Arab.” Shafin gaba ta kuma buɗewa. “Lalla Salmah, ita ce take control din duk wani sukar da Malik yake sha ta fuskar gwamnati, dole zaki iya haduwa da ita, kafin nan, sai kin zama daya daga cikinasu karfin arzikn, dole kiyi wani abu da zai fitar dake cikin al’umma ina bukatar bajintarki, duniya tana yin masu bajinta ne, ba tayi da lusarai ya kike tunanin ta ina za a fara?”
Shiru tayi, tana kallon shi kafin ta ce mishi. “Me zan iya yi anan?” Juya kujeranshi yayi yana faɗin. “Baki da wani hikima da basira ne, sai jagaliyancin? Zenobia wannan harkan kudi ne, kuma nayi ƙoƙarin a iso nan ne domin mu fuskanci wace ce ke? Zaki dakatar da fitowa na tsawon kwana biyu, domin ayi wani aiki. Akwai wani kamfanin mujalla na baazar zaki musu talla, a kasar Amurka.”
“Mr Amjad duk akan haduwa da Malik ne aka son nayi, duk wannan al’amarin?” D’ago kai yayi ya kalle sannan ya ce mata. “Idan ta kama ayi kisa don a hadu da Malik Menk Jordan zamu yi, amma ki saka a ranki, kamar ki zaki hadu da shi ne domin lafiyarki, don naji labarin ana bukatar miliyoyin kuɗi domin a miki aikin kanki. Idan kuma kina ganin haka ba zai yiwu ba, kiyi tunanin makomar gidan Al’umma Charity House mana zaki yi ko A’a……….?
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: CINIKIN RAI….11
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
A yadda yake maganar ya masifar bata haushi, don haka bata san da ta daki table ɗinshi ba, sai da ya razana. Takowa tayi gabanshi ta riko necktie ɗinshi ta shiga gyara mishi a hankali tana me kara zuge mishi sai da ta shake wuyarshi. Bude baki ya fara. “lalacewar bata kai wanda zaka min barazana ba, baka isa ka min barazana ba wallahi. Kasuwanci muke da kai da kai ba bauta nake maka ba, banza irinka zaka shigo da al’umma charity House!” Ta kuma tamke wuyar. D’aga hannu sama yayi yana faɗin. “Ya isa haka, kyale ni zan gaya miki yadda zaki yi, da tausassawa. ” Kara matse wuyar tayi ainun har sai da ya fara kakari ta ce mishi. “Koda wasa kada ka tab’a martabar al’umma charity House, yadda na matse wuyarka haka zan tsinke ta.” Daga haka ta wuce waje. “kayi kokarin niman wacce zata maka aikin ba dai ni ba.” Ware idanu yayi yana tari, ina ba zata sabu ba, Ita ce ta dace da aikinshi. Sosai abin ya d’aga mishi hankali, don haka ya nufi hanyar waje. Ko da ya fito ya samu har ta fito daga dakin sauya kaya. Zubewa yayi a kan gwiwarshi. “Allah ya ya huci zuciyarki, na tuba nabi Allah na bi ki.” Ganin yadda a gaban ma’aikanta kamfanin ya iya sauke girmansa ita wace ce da ba zata hakura ba?
“Shi kenan kome ya wuce.” Ta fada tana, me dauke kanta. Abin sai ya zama Gulma sosai a cikin kamfanin Chairman ya durkusa yana bawa ma’aikaciyarshi hakuri kafin kace kwabo al’amarin ya zaga ko ina har ya fada manhajar social media. Sake wasu sun yi video din abin. Haka yasa shi Mr Amjad ya dakatar da ita, kuma daman haka yana cikin shirinsu.
Kwana biyu a tsakanin, Salim ya zo ya dauke ta, suka je aka mata international passport. Saboda fitarta USA.
<<<|=|>>>
Waterfall island.
Tsibiri ne da yake kan dutse, inda ruwa yake sauka izuwa babban tekun Keivroto sabuwa. Tsuni ce da babu wanda yake da ikon ya isa wurin sai ka isa ka kai, ka kuma gawurta. Yanki ne me dauke da manyan manyan jami’an tsaro ko ta kwana. Wadanda suke aiki na tsawon awa ashirin da hudu a sati. Sannan kullum sauya su ake babu wanda zai kuma dawowa, sannan wani abin da zai kuma daure kai, shi ne masu aiki a ilahirin tsibirin maza ne va mata ba, asalima babu mace ko daya.
Fili ne fallau a saman dutse aka fasa shi, sannan aka mishi wani irin stone house, aka yi wani ƙasaitacciyar Mansion a tsakiyar dutsen, aka zagaye shi da wasu irin duwatsu wanda aka yi katangar da ya zagaye gidan, na musamman ne domin ba daga asalin duwatsun aka yi su ba, wasu irin duwatsu ne aka zo da shi, idan aka ce za ayi bayanin yadda gidan yake bata lokaci ne.
Malik Menk Jordan, Mansion kenan me dauke da abubuwan ban al’ajabi da mamaki. Gidan da babu wata mace da ta tab’a zama cikinsa, sannan ko a cikin gidan shirye yake da kayan alatu da more rayuwa, domin kome da yake cikin expensive ne daga ƙasashen waje. Babu abin da babu a gidan, daga masu kula da Flowers, bangaren abinci da sauransu babu wani ma’aikaci da yake permined dukkan su temperary ne, kullum sauya su ake.
Cikin gidan me dauke da dakuna shiga, kasa uku dama uku. Sai wani katon zanen hoto irin na da can, domin zana shi aka yi. Ba hoton aka dauka ba, wasu dattijai ne guda biyu. Mace da namiji sai wani yaro a tsakiyarsu. Gefe wani zane ne me Black and white. Bayansu babu wani abu na azo a gani, sai domin duk wani abin da yake cikin gidan ba bakon me karatu ba ne.
A saman can harabar gidan, fili ne na tashin helicopter na daidai mutane biyu zuwa uku. Sai dan gefen can da aka ajiye expensive cars, irin wanda ake yayinsu. A ilahirin mansion akwai yar karamar drum da yake tashi irin na wasan Yara, sai dai wannan an sake shi ne, saboda tsaro da kwantar da tarzoma. Sannan akwai wasu irin tsuntsaye Eagle manya da suke shawagi a gidan, dauke da Camera a cikin gidan.
Akwai wasu manyan lion dogs da aka kewaye su, sai zuwa dare aka sake su, duk da a cikin gidan inda ake kwana akwai wani daki da aka ajiye tiger, wanda girmansa yafi na irin raguna udawa, a batun gaskiya masu kula da tsaron gidan kawai, abin tsoro ne domin tun daga tsibirin har zuwa inda aka saka iyaka da tsuburin. Domin sai an ketare ruwa kafin a iso, idan ta jirgin ruwa ne. Koda yake mutum daya ne yake amfani da jirgin Elbashir Jamal Arab, saboda kusancin shi da Malik.a bakin gabbar tsibirin akwai masu kula da ruwan suma 24/7 a cikin sati. Motoci kusan guda bakwai suka iso bakin ruwan, masu ɗauke da Shatima01 har zuwa 6, a tsakiyar motoci shida nan ya fito daga cikin wata phantom. Wacce ake bude ta ta gefe daya, rike yake da wata irin sanda, yana dogarawa sanye yake da normal shigar hausawa, kanshi dauke da zanna bukar. Wacce ta kara fito da dattijuwar fuskarshi. Amma hutu da jin dadin rayuwa yasa baka iya hango dattijantaka da take tattare da shi. Lalla Salmah ta tawo a cikin motarta a tsakiya itama, sai masu tsaron lafiyarta kasancewar ta Assamblywoman. Bude mata motar aka yi, ta fito rike da yar karamar jakar Charles Keith , sanye take da turkiyya plan gown minti colour. Hade da hularsa, sai ya tafi da jakarta da takalminshi. Murmushi yayi mata sannan ya ce mata. “Yar majalisa ya kwana biyu?” Kallonshi tayi kamar ba zata yi magana ba, kafin ta ce mishi. “Lau!” Da wani irin yake, ta dauke kanta, sannan suka nufi inda jirgin da yake jiransu, shiga cikin jirgin suka yi kowa yana jin wani abu na daban akan dan uwansa, ko da jirgin ya fara tafiya, mika musu wani karamin akwati wani jami’in tsaro yayi, suka zazzage kayansu baki daya, ya ja ya rufe suka cigaba da tafiya, koda suka tsallaka ruwan. Jami’an tsaron suka karbe su, takowa suka yi aka fara screening dinsu, bakiɗaya a duk lokacin da zasu tafi ganawa da Malik sai ayi musu screening kamar masu zuwa lahira, sun san da Elbashir ne babu me mishi wannan binciken kwafkwaf din. Babu abin da ba karbe ba, domin kuwa babu yarda a cikin lamarin Malik. Karban kome da aka yi yayiwa Lalla Salmah ciwo. Haka yayi fuska sannan suma da mitarsu ba sabon abu ba ne a wurinsu. Domin ba yau aka fara bincikar su ba, shi kan Shatima bai wani ki dar ba, ai dama ba sabon abu bane a wurinshi.
Daga nan baki ruwan mota suka shiga da zai kai su, cikin Mansion ɗin. Lokacin da suka isa kamar waɗanda suka fito sansanin cutar coronavirus, domin sai da aka musu feshi da magani sannan suka wuce shingen farko. Tsaki Lalla Salmah tayi tana dauke kanta, kafin suka isa wurin aka saka su, suka cire takalmarsu. Aka basu wasu, karshe sai da aka kai su wani daki na musamman suka sauya kayansu, sannan aka mika musu wani kati.
Sannan duk wannan abin da ake musu, babu wanda ya ce uffan domin aikin kawai ake a aikace, babu magana kai kanka ka kasan cewa kome sa ake yi da ilimi ake yinsa. Sai aka gama kome sannan suka wuce wani falon da ya dace kafin su samu kira daga Malik, Elbashir ne ya fito dauke da cup na wine. “Hi! Ya kuke?” Ya isa wurinsu, waiter ne ya iso dauke da tire na ruwa da wine. Ya mika musu, dauka Shatima yayi yana faɗin. “Yaushe Malik zai daina mana haka, wallahi kunya da jin babu dad’i nake, tsawon shekaru ashirin da biyar muna tare!” Murmusawa yayi ya mika mishi kofin suka dan buge kwalbar.
“Idan baka manta ba, rashin tsaurarra tsaro yasa aka samu matsalar da har yau yake jinya, idan har Malik bai kiyayye rayuwarsa ba, me kuke so yayi?” Shiru suka yi, suna kallon juna. “Yaushe ka dawo?” Lalla Salmah ta tambayi Elbashir, tab’e baki yayi ya ce mata. “satin da ya wuce, ina Maidah?” “Tana lafiya, next up week zata tafi Demark, akwai course ɗin da zata tafi tayi akan karatunta na wata shida.” Gyada kai yayi, sannan ya cigaba da kallon jaridar da yake gabansu. Kallonta Shatima yayi ya ce mata. “Gashi kusan lokaci guda Nadrah zata gama karatu da su Wahiba da Wahida. ” Murmushi tayi ta ce. “Eh wallahi, Yaran Nuratu sun girma! Har yau ba a samu danginsu ba ko?” “Ki tambayi Malik shi yake da masaniya akan zuriarsu.” Tabe baki tayi tana faɗin. “Naga ai kafi mu kusa da Malik, kai zaka riga mu sanin kome.” “Nima bani da ikon sanin kome, sai abin da Malik ya gaya min, ba zaku gane cewa Malik Menk Jordan ba kome yake sanarwar ba, sai abin da ya zama dole Ppl dinsa ba kowa ya sani ba, sai shi kaɗan shi.”
Kallon agogon hannunshi yayi ya ce. “Oopss… Sorry ashe yau ba zaku samu ganawa da shi ba, sai nan da wata sati.” Ya mike yana murmushi, “what!!?” Lalla Salmah ta zare idanu, kamar zata fasa ihu. “Yanzu don Allah meye haka? Duk wannan wahalar ace ba zamu samu ganinshi ba?”
“Akwai matsala ne idan baki ganshi ba? Ko akwai wani abu ne rashin ganin Malik din?” Yadda ya tsare ta da idanu,yasa ta sunkuyar da kanta, ta ce. “Ko ɗaya.” Ta mike tana faɗin. “Allah ya kai mu.” Inji Shatima dama shi bai wani damu ba, harka ce ta siyasa, kuma suna fitowa yake gayawa Elbashir abin da ya kawo shi, ita kuma ba haka ba ne, kudirinta akan dole sai tayiwa Malik tallar Maidah ne.
Haka suka fito daga tsibirin ranta a bace, shi kan Shatima bai yi wani mamaki ba, domin yasan darajar Malik kafin ya yarda a ganshi tow sai kayi kamar kana yi, don haka ya sakawa ransa sallama, Indai Malik ne ko wancan watar da ake ta bala’in akan abin da ya faru suna tare a Green House. So shi bai wani damu ba.
—–
Lokacin da suka iso gida, maid dinta suka tare ta, bala’i da masifa ta tare su, sai fada kamar zata doke su, babu wanda ya kulata.
★★★
United States of America.
New York.
Anan suka sauka, a wani apartment me kyau na fita hankali, ba kowa yake zama a cikin apartment din ba, sai manyan mutane ko Celebrity da yan matan yan siyasa. Sai da aka yi sati biyu tana sauka span a kasar apartment din ana mata gyaran jiki. Kafin ranar da ta cika wata guda,aka fara kaita kamfanin Baazar ta dauki hoto tare da musu tallar wasu abubuwan, kamar kamfanin kayan kayan kwalliya, sai kamfanin sarrafa kayan sawa, D&G, sai na turaren explore. Watan ta biyu a US, suka wuce Dubai inda tayi tallar wasu abayas, tallar ya janyo aka gayyace ta bikin karrama Celebrity a London, tare da Vogur babban gidan mujallar Ingila, me cin gashin kasa, wanda yayi promote Halinta haded, Rawda Muhammad, da sauran hijabs girls, duk wannan tafiyar sun shi ne, da Salim duk inda ta saka kafarta yana biye da ita. Kayan da ta saka doguwar riga ne, shiffon material aka dinka mata, shi me shegen kyau, shara-shara me azazzben kyau da ɗaukar idanu. Kanta wani turban ne, da aka yi like net, fuskarta an yi mata normal makeup, da kayan makeup na milan, daga takalmin kafarta zuwa jakarta, abin dubawa ne domin ta nutsu tana abu gwanin ban sha’awa.
A lokacin da suka shiga hall din, hankalin kowa ya koma kanta, musamman kamfanonin da suke buƙatar sabuwar fuskar da zata musu talla, kuma abin da Mr Amjad yake bukata kenan, ta zama wacce duniya zata yayyata da zuzzutatta. Kowa ya santa duniya ta san wace ce ita, kowa ya gane ita wace ce, kuma haka ya faru. Domin a cikin wurin taren mutane dayawa sun bukaci ganin Manager ɗinta, da suke yi sponsored ɗinta, babban burinshi ne.
Kafin wani lokaci gidajen tv da na radion, Gista da Keivroto ya dauki labarin ana yayyatawa ana kara zuzzuta Zeenobia, yarinya daga getto area, ta zama shaharariyar da ba a zata ba. Dakyar ya yarda ta saka hannu a kan wasu kamfanoni guda biyu, zata yi aiki da su na wata biyar biyar, domin baki daya baya son sharararta ya wuce haka.
Haka kuwa aka yi kamfanin farko daga Gista take na sadarwa ne, ita zata na musu talla akan wasu abubuwan su. Sai na biyu kamfanin kayan kwalliyar mata ne, sai da ta kai manyan gidajen jarida masu zaman kansu, sun sayi hoton fuskartar. A wannan tafiyar sai da ta kwashe wata hudu cur kafin ta dawo gida, tsabar ta gaji, sai da ta kwana uku bata iya ko lekowa, sai ranar na hudu ta fito ta shiga cikin gari, a nan ta samu garin ya cika da poster dinta, murmushi tayi har ta. Wani shagon cin abinci, dake dare ne kuma ta saka riga me hula da facecap. Haka ta fita ta sayi abin da zata saya, a hanyar dawowarta ne, suka yi kicibis da Asp Zulfa suna patrol. Dauke kanta tayi zata wuce da motarta suka tsayar da ita. Ko a cikin dubu ta sauya shiga zata gane ta, balle a ita daya kaya kawai ta sauya. “Miss Zeenobia, ba a taba sauyawa tuwo suna ba, tun duniya na kwance balle yanzu sa take zaune da gindinta.” Cire facecap din tayi tana lashe dark red lips dinta ta ce mata. “Kina bukatar selfi ne?” Murmushi Zulfa tayi tana faɗin. “Ina selfi amma ba da watsassun mutane ba.” “Keee yar sanda!” Tayi wani karkata baki irin na samu na yan daba, ta ce mata. “Ki iya bakinki!” Ta juya zata shiga motarta, rike rigarta ta bata Zulfa tayi tana faɗin. “jagaliyarcin ya motsa ne?” “Na rantse da Sarkin da yake busa numfashi idan, kika dame ni sai na kaddamar miki, na gaya miki.” Tayi tsaki tana shiga motarta, “Na kama mutane biyu da suka lokacin da kika kashe Ayuba da Wasim.” Cak tayi ta tsaya tana kallon Zulfa in confidence ta dauka a motar tana me nufar Zulfa. “I’m glad da abin da kika yi, sai dai ki sani ni naci dubu sai ceto, idan har kina da zarra tow ki kwamushe ni, Zeenobia nake Xnoo, yar kunama karamar su Babbar su.” Ta wuce tana me barin motar, sai da ta tashi motar sannan ta bud’a musu hayaki. Tayi gaba abinsu.
★★★
2weeks.
Mika mata file yayi, ya ce mata.
“Zaki musu tallar sati daya, kamfanin abin sha, ture file din tayi tana faɗin. “Ina son kudi zan tafi Ofishin haraji ne.” Murmushi yayi ya dauki wayar shi yayi kira. “Hello bani takardar harajin nan!” Can sai ga Salim ya shigo, mika mishi takardan yayi, ya mika mata. “Zeeno gashi nan” sake bude drower dinsa. Ciro wani kwali yayi ya ce mata. “Gashi nan” murmushi yayi yana kallon yadda ta ruɗe. Kallonshi tayi na wani lokaci, kafin ta ce mishi “me zan yi da shi.” “Bude ki gani mana” a hankali ta bude kwalin tayi, zare idanu tayi kamar zata fasa ihu. “Kina tsammanin zaki yi aikin nan, babu wani abu ne sannan ki duba motarki, kina babban yarinyar babu mota na more rayuwa! Ga wannan katin ki tafi bankin golden bank a cire miki password ɗin da kike so, sai a cigaba da sharholiya.” Murmusawa tayi tana faɗin. “Dole ayi sharholiya a al’umma charity House.” Ta fada tana kallonshi. “Kinsan me yasa na zuba miki kudinki ta golden bank? Domin mutanen Malik da Yaransu a wannan bankin suke amfani da shi”, ware idanu tayi tana faɗin. “Yaushe zamu fara nufar Malik din!” “Da sauran lokaci”
Gyada kai tayi ya dauke kome ta fita, murmusawa yayi tana fita, Salim da MD suka shigo. “Me ya rage Chairman?” Murmushi yayi ya ce mishi. “Ta fada komarmu! Ita ce abin harin mu, domin Malik ba zai kamu ta dadi ba, dole sai da tsananin hawa.” “Kenan Malik kifi ne da ba za a kama shi ba, sai an watsa mishi tanna da kwari!”
D’ago idanu yayi ya ce mishi. “ita ce tannar tawa!”
Murmushi yayi ya ce ” Musu, rayuwarta wadancan mutanen ne, idan kana son ganin farincikinta, ka yiwa mutanen hidima!” Gyada kai yayi suna masu jin dadi a ransu.
——– Zeenobia kuwa motar ta dauka ta nufi bankin, yayi duk abin da zata yi, lokacin da ta shiga bankin mutanen da suka ganta, sai ta zama celeb domin kuwa kowa rubibinta suke. Bayan sun gama mata kome da girmamawa,a hanyar fitar ne suka hadu da Mr Shatima, har ga Allah kallon da yayi mata, ta tafi da imaninshi. Kara kallonta yayi yaga yadda take taku a nutse yasa shi shagala da bin ta da idanun.
Gyada kai yayi, Hadi P.A din shatima ya ce mishi. “Yallabai baka san ta bace, ita ce yar tallar nan ta Baazar da Vogur.” “Hadi ayi wani abu a kanta, tayi min sannan a tura mata kyautar ban girma a account ɗinta. Domin kuwa kaiwa Manager magana.” “An gama Yallabai!” Murmushi yayi yana imagine yadda zai sarrafa yarinyar, domin kuwa yana cikin mutanen malik masu mugun son mata, shi yasa tun rabuwarsu da uwar Nadrah bai wani kara aure ba, domin baya son damuwa, shi yasa ya bige da bin yan mata musamman yan kananun Celebrity, yana kashe musu kudi kamar yayi hauka.
Babu abin da yake tashin kanshi ya ga mazaunin mace, yana bala’in son ganin kugun mace tana juya shi, ga Kirjinta a cike, irin na yan matan da suke tashe da yan matancin su. Murmushi yayi yana ji tabbas zai more domin yasan yadda ta zama shaharariyar nan, ta goge na fitar hankali.
——
Daga fita ita kan gida ta wuce, a can aka cigaba da shagali sai saka yara take a mota. Tana nuna musu. Sarin na yan sanda yasa ta dakata, ta zubawa motar idanu. Shigowa Zulfa tayi tana kallon gidan. “Aunty Zeeno, wace ce ita?” “Aunty Yar sanda ce!” Gyada kai suka yi suna kallon su.
Takowa tayi tana shafa motar, tana faɗin. “Nawa nawa kike ka sa musu ne? Gaskiya labarin da nake ji ya bambanta da wanda idanuna yake gani,” ta fada tana shafa motar. “Zeenobia Nasr Hadejia, me kike basu suke rawan jiki akanki haka ne?” Dauke ta tayi da mari, tare da murde hannunta, ta haɗa ta da motar. “Tunda nake ban tab’a jin kwadayin bada kaina, ba kuma bana fatan na bawa wani dan iska kaina domin na burge su. Du inda na shiga ina girmama mutuncina sama da kome.”
“Zainabia!” Aka daka mata tsawa, daga sama. Inna ce, tana zuwa ta wanke ta da mari. Sai huci take. “Baki ga ta girme ki bane? Ko ance Miki sa’arki ce!” Cire hannunta tana huci ta ce mata. “Ta kuma jifar mutuncina sai na lahira yafi ta jin dadi.” Ta fada tana me barin ƙasar. “Barka dai yar sanda.” Shiru Inna tayi kafin ta ce mata. “Idan tayi laifi ba kuskure bane a hukuntatta, amma kuskure ne a ci zarafinta……
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: CINIKIN RAI….12
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
“Hmm! Dama cewa nayi ta kula da rayuwarta, wadannan yan siyasan ko yan daban ba kome zasu mata, domin daga lokacin da ta kwabe musu ba zai mata kyau ba.” Ta fada tana gyara hannunta.
Shiru suka yi, domin kamar maganar ya shige su. Juyuwa tayi zata bar gidan, kwallon yara ne yazo zai wuce ta gabanta, tayi maza tare shi, ta shiga d’aga shi a hankali tana jifa shi sama. Har tayi ta bugawa kafin ta tura musu kwallon tana murmushi ta sakar musu. Tare da barin gidan baki daya.
A can sama kuwa, tunda ta shiga ɗakinta ta rufe kofar, bata yarda ta bude kofar ba, asalima duk buga kofar da ake taki budewa, kwanciya tayi ta lumshe idanunta, tun daga tasowarta har yau babu namijin da ya tab’a nimanta da harkan banza, domin bata cikin yan matan da suke bawa maza kanta. Har zuwa yau ita bata cikin yan matan da suke da mugun kwadayi da zallama, ta iyawa kanta, bata shiga abubuwa dayawa domin kare mutuncinta, shi yasa har ta gama makaranta, babu ruwanta da kowa. Kai saurayi wannan ba tab’a yi ba.
★★★
Washi gari.
Da wuri tazo wurin aiki, tana dakin da suke sauya kaya, Mss Mary ta shigo tana kiranta. “Zeeno kina ina?” Juya tayi tana gyara zaman rigarta. “Mene ne?” “Maza kizo chairman yake kiranki!” Karamar tsaki tayi tana faɗin. “Ok gani nan zuwa!” Ta fada tana cigaba da abin da take yi, domin tasan bai wuce bita akan Malik Menk Jordan, kuma indai shine ta rigada ta hadda ce, bata bukatar wani bita domin zata iya fadar abin da abin da zai ce mata.
Sake zuwa Mss Mary tayi, “Wai kina ina ne?” “Gani nan dai” ta fada tana tura baki, har zata wuce, sai kuma Mss Mary ta ja hannunta, zuwa wuni department na cikin kamfanin kaita wani daki, bude drower tayi kaya suka bayyana, kura mata idanu tai tana faɗin. “Ki zabi kayan da ya miki bari Dauduwa yazo.” A hankali ta kai idanunta kan drower din, ba karya kayan sun hadu, wani gown ta zaro green colour, ta tsaya gaban mirror din drower din ta gwada kayan, ta kuma juyawa daidai bude kofar. “Wow wannan kayan zai miki kyau, idan kika haɗa da takalmi grey da yar karamar pose, sai yan kunne babu bukatar ki saka abin wuya, ko me kika ce Mss Mary.” Murmushi tayi tana faɗin.
“Tabbas kuwa zata yi kyau, amma ta gwada kayan baki daya mu gani, ko zata samu wanda ya fi kyau.” Ta fada tana kallon ta, aikuwa haka ta kasance tare da gwada kayan, wato yarinyar nan da tayi ta sauyawa tana kara sakawa, abin ba a magana. Binka da matsakaiciyar mace, bata da tsawo can, sannan bata cikin layin gajerun, sannan bata da auki domin dai jikin daidai ne, skin ɗinta fari ne me kyau, kasancewar mahaifiyarta Shuwa’arab daga yankin Chad.
Gashi ne da ita har baya, ba irin wanda za a kira shi har gadon baya ba, domin a cike yake, tsawon dan daidai ne, don ma yar kwalliya ce, amma duk lokacin da jagaliyarcin ya motsa takan iya wata uku bata murza kwalli a cikin Idanunta.
Zeeno tana da kyau, don fuskarta kamar ta Yara take, gashi fuskarta yana da dan tsawo, Idanunta kuwa yadda kasan yan Korea, a zahirin gaskiya idan tana jin yan gayun babu biyunta,. Amma idan abin ya motsa babu ruwanta sai tayi ta maimaita kaya, bai dame ta ba.
Sai da aka gama zaga kayan cikin drower kafin aka samu wani, Peach colour ta saka, aka yi mata makeup light, babu wani tarkace, haka suka fita tare kafatar sanye da takalmin Amina muaddi, sai yar karamar jakar Celine. A kafad’arta ta rataya jakar, suka fita tana tafiya a hankali gwanin ban sha’awa. Har suka isa office din chairman. Koda suka isa basu wani dauki lokaci ba, suka shiga da jagorancin Mss Mary. Har cikin office ɗin. Idanunta ne ya sauka akan idanun wani kyakyawar matashi. Yana zaune hannun shi rike da mujallar Fashion. Juyowa yayi ya zuba mata ido. Itama shi take kallon shi take, kafin ta janye Idanunta daga nashi, domin irin mutanen nan ne, masu kallon kurilla. “Amjad ta hadu sama da jikin jaridar, a jaridar na ganta, ashe ta wuce haka ma.!”
“Zeeno ga shi, Akram Jafar Wazir. Yaga hotonki a mujallar Fashion ya ga hotonki, daga, Nigeria yaƙe!” Dauke kai tayi daga kallon Amjad, ta nime daya daga cikin kujerun office din, ta zauna tana kallon Amjad. “Ban fahimci me kake nufi ba? Ni fa ba gwanjo bace da zaka na gayyato min mutane, Amjad wannan ya zama na karshe na gaya maka.” Daga haka ta juya zata fita. “Zeenobia! Yes na yarda da abinda aka fada, kanta yana daukar wuta sama da fuskarta.” Cak ya tsaya, sannan ta ce mishi. “Na wuce yadda kake tunani, ka tsaya a iya inda kake!” “Ni ina da mugun naci, kamar kaska nake, matukar naga abu sai na manne mishi nake samun nutsuwa, domin matukar ban ja jinin ba, bana nutsuwa. Ki tanada min abubuwa yawa, har da bayanki…..” “Tasss” ta dauke shi da mari, wani irin dariya yayi yana faɗin. “Wow! Yes dole na mallake ki koda girma….” Wayar shi ce tayi kara ya ɗauka. “Ok in sha Allah, zan biyo flight na yamma gani nan!” Ya juya ga Zeenobia. “Mark my words, babu wanda ya isa ya tsaya a gabanki sai ni, sai na lalata miki fuskar ki a gaban jama’a.” Takawa tayi gabanshi, ta kuma tsinke shi da mari, tare da cin kwalar shi. “Har gaban abada, na fi karfin jan kasar jahili irinka. Yar kunama nake” ta sake mishi kwalar shi, ta fita tun daga waje ta fara cire kayan jikinta, har ta isa dakin ta cire kayan, ta tsani kayan ban haushi.
“Amjad, yarinyar nan ta hadu.”
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: CINIKIN RAI….13
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
*Trust me, you are the one,
whom my eyes seek, whom my
heart finds, whom my destiny
wants, whom my mind reminds
me of, whom my life ill sold,
whom I really depend on,
whom I wake up for each and
every morning, whom I love
more than anything, more than
anyone, and… I will do
whatever it takes to have you
in my arms forever…..*
<<<<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>
Ware idanu Amjad yayi, yana son tayi suna ta shahara, yadda zai samu damar shigarta Kasuwancin Malik ba wai ta shahara da yan iska irinsa zasu na kawo mata farmaki ba, shi yadda zata hadu da Malik yayi koma. “And ina son ka saka idanu akanta, dole zan dawo” “Da ina ga kayi hakuri da bukatarka, ita ba a mata dole, domin.” Shako wuyar Amjad yayi yana zare masa idanu, “karya kake, yadda ta fito ta nunawa duniya ita karuwa ce, dole na tafi da ita, so nake naji ina nutsu a jikinta, don haka na gaya maka idan ba haka dole na sha jini da ruwa lokaci guda ” yana fadar haka ya ture Malik yayi tafiyarshi. Rike wuyar shi yayi yana kwashewa Akram Jafar Wazir albarka a zuciyarshi. Yana fita ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin. “Tsinanne dan iska, ba zaka bata min dagiyata ba.”
★★★
A masife ta isa gida, shi yasa baki daya ta ki kula kowa, asalima bata kaunar magana. mika mata sako Abbas yayi ta amsa ta wuce.
,Wkakaasaj Har tayi gaba, sai kuma ta ce. “Sakon me?” “Ina son ki duba, ne iyayen Hibba Yin cYuue a tura me ake bukata” ya fada yana juye-juye. Kamar zata yi kuka ta ce mishi. “kana nufin sunce ka tura manyanka?” Gyada mata kai yayi yana rike rigarshi.
“Okay Angon Hibba!” Ta fada tana barin wurin, bata ce bata ji dadi ba, amma kuma zuciyarta yaki accepting din abin yake faruwa. Baki daya ta manta da wani dan iska can.
—–
Tsohon store, Zulfa ta shiga. Haska torchlight din tayi, a hankali ta fara buɗe wasu kwalayen. A hankali tayi ta sauke kwalayen tana faman bincike, tayi karatun nan ne domin fitar da gaskiyar da Hukumarsu ta kasa fito da shi, koda kuwa ace zata cilla rayuwarta cikin kasada ce, ta shirya haka domin baki ɗaya rayuwarta akan wannan binciken zata kare shi. Buga mata kofa aka yi ta ce daga ciki. “Sajin kai ne?” “Eh Madam, wani aiki na kawo miki.” “Shigo” ta fada tana kallon kofar, a turo kofar yayi ya shigo ya sara mata, sannan ya mika mata wasu files, yana faɗin. ” Madam gashi a wani binciken da nayi, a tsohon Office din mu, don bana manta wannan case din,koda ban da cikakken tarihin faruwar abin amma lokaci zuwa lokaci ana yawan tadda case ɗin domin a tattauna a akai similar kamar kisan prime minister.” Amsa tayi tana faɗin. “Ka kyauta min, amma ba a kan case din nake ba yanzu, sai dai kuma dole zan bibiyi case ɗin. Daga baya”
“Tow Madam” ya ajiye ya fita, ta cigaba da binciken ta, har zuwa abin da take nima sai dai bata samu dukkan abinda take bukata ba, domin har lokacin sallah yayi, haka ta mike ta fita, sai bayan ta idar da sallah, ta tura aka kwaso mata binciken, ta cigaba da a cikin office ɗinta, yadda zaka fahimci tasan aikinta, tana binciken tana rubutawa, kowani single words, tana adana shi, har ta gama binciken wasu file abu daya ta samu Malik Menk Jordan.
Tattara files din yayi ta ajiye su, me yasa sai shi sunansa yake fito mata, baki daya ta kasa fahimtar kome. Koda la’asar yayi, a Office ɗinta tayi sallah tana idarwa IGP yana kiranta. Tura baki tayi faɗin ” Allah sai ya saka min sumbatar da kayi min” dauka tayi tare da daure fuskartar kamar yana gabanta. “Zulfa!” “Meye!” shiru yayi kafin ya ce mata. “Allah ya baki hakuri! Hmm ina kewarki” “Ji min gulma, ina ka bar Aunty Fannah?! Kaga idan baka da abin yi ina da shi sai an jima.” “Kinga don’t hanging my call,.” “Hmm!” Ta ce. “Ok me yasa baka tsorona?” “Saboda Idanuna yana hango min yar shekaru ashirin da bakwai a gabana, wacce ta manta yayi ta kara shekarun haihuwarta.” Dafe kai tai tana faɗin. “Allah na manta, dake!” “Dake kin sakawa kanki aikin da bana ki ba? Na gaya miki ni dake ki ajiye wannan case din ko?”
“Akhi!” Ta kira sunanshi a hankali, kafin ta ce mata. “Ni na gaya miki, ki ajiye saboda wasu dalilai, ni ma haka nayi ta wahala karshe, na hakura idan dai akan Malik ne ki ajiye domin akwai abubuwan da baki isa saninsu ba, dole sai anyi amfani da lokaci.”
Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, “amma me yasa kace na hakura, bayan akwai dubbanin al’ummar da suke zubda kwalla saboda su!” “Saboda shi ma akan daidai yake, a duk lokacin da kika fahimci waye shi, ba zaki zargi dalilin shi na kananainaye kome ba, sai ma tsoron Allah ya shige shi, Zulfa ki daina binciken nan haka, amadadin haka ki bada hadin kai, next month a daura auren sai a sha biki, kafin nan da wata hudu kina dauke da little!” “Zan kashe wayar fa!” “Tow doguwar mace me kayan marmari!” Katse wayar tayi, tun fil-azal Yasir bai da kunya inda kunya tabi bawan Allah nan bai bi ba, bata mantawa lokacin da dangin Mahaifinshi suka ce ya auri Fannah kiri kiri ya gaya musu. Fannah idan ta samu wuri kiba zata yi, kuma shi baya son macen da zata yi kiba. Shi Zulfa yake so domin ba zata yi kiba ba. Akayi ta rigima da shi kafin ya aure ta, ko bayan auren babu ruwan shi, ya ce ai sadakin shi ya biya, kuma zai more kayanshi, don haka ko da zaman yayi zama Allah bai albarkace su da haihuwa ba, amma shi yasan cewa matar da zata haihu mishi Zulfa ce, don haka yake ta bibiyarta dan rigima irinta shi. Duk wanda ya fito yana sonta koranshi yake yana fada mishi, ai matar shi ce bata tare ba ne, amm da aurensu.
Gyada kai take tana karawa, domin ta fara gajiya da halinshi. ‘ki fitar da miji kiyi aure’t tsaki tayi a fili, tana faɗin. “Mara mutunci ba barina zai yi nayi aure ba.”
★★★
Keivroto International airport.
Lalla Salmah ce tsaye da Maidah, wacce tayi sanyi, kamar ba ita ba. Baki daya bata son zuwa Demark. “Baby an gama kome, Allah ya tsare, kiyi kokarin niman number Malik. Ina bukatar shi urgent kuma saboda ke!” Gyada kai tayi har zata wuce ta dawo da baya ta ce mata. “Maama, me yasa baki da number shi?” Murmusawa mata tayi tana faɗin. “Malik yana da number mu, amma mu bamu da na shi, Malik yana tare damu amma zaku fahimta.” Gyada kai tayi tana faɗin. “Maama me yasa kike son na shiga rayuwar Malik” d’ago kai tayi tana kallon Maidah, “we need powerful! We need everything! We need Malik Menk Jordan!” Lumshe idanun yarinyar tayi sannan ta ce mata. “Zan samo miki Malik Menk Jordan!”
Sai da aka fara kiran fasinjoji, kafin ta juya ta tafi da gudu, tana d’agawa Uwarta hannu, murmushi uwar tayi tana faɗin. “Dole kiyi amfani da shekarunki da darajarki koda kuwa ta dare daya ce. Malik ya dawo hannun mu!” Daga airport din itama jiran jirgin da zai kaita *Gista* tayi har zuwa lokacin tashinsu, ta mike tare da barin wurin.
Jirginsu Maidah da ya tashi karfe tara na safe, bai isa ba sai karfe biyar na Yamma. Hajiya Jalilah ita ce ta je ta dauke ta, abokiyar harkan Lalla Salmah ce, don haka tana daukarta gidanta ta fara kaita, sai da ta huta, gidan kamar gidan Ƙaruwai da yan iska yake, domin babu Yaren da babu, kama daga bakakken fata, yan Afirka zuwa fararren fata yan Asia da birbishin turawa marasa galihu da suka fada harkan karuwanci da sauransu.
Idanun yan mata dayawa ya sauka akan Maidah, amma Hajiya Jalilah ta musu jan ido, tilas kowa ya ɗauke kanshi.
Bayan ta huta taci abinci, tana zaune Hajiya Jalilah ta shigo sanye da shigar hausawa ta ce mata. “Yar Mama zo mu tafi maza!” Gyada kai tayi tana me mikewa, sanye take da riga da wando English wear, sai kanta da ta yane da mayafin shiffon.
“Kin fahimci abin da ya kawo ki ko? Naji labarin kamar Malik yana zuwa a duk bayan wata shida, wannan karon kuma zai zo ne domin maganar wani kamfanin da zasu bude da gwamnatin kasar nan, na kera waya, ki kula sosai!” Gyada kai tai tana faɗin. “in sha Allah zan yi iya kokari na” “Good girl!”
A hankali suke tafiya har suka isa wani unguwa mara yawan mutane, da tsirarrun gidaje. Sai da aka tambaye su ina zasu, suka fadi inda zasu, sannan aka bar su, suka wuce bayan sun kira Madam Qudussiyah, ita ke kula da Yaran kusan itace dangin Mahaifin Malik da tayi saura, dattijuwa ce da ta girma ainun. Amma yadda take samun kulawa ba zaka tab’a yarda cewa takai shekaru saba’in ba, hutu da kyakkyawar cimma me kyau.
Gata tana da addini ga ilimin addinin da na boko, ba laifi sai dai tafi karfi a kan addini. Har kofar apartment din suka isa, suka fito, sai da suka danna kararrawar bakin kofar, can aka zo aka bude musu, murmushi akan fuskar yar matashiyar budurwan da ba zata wuce sha bakwai ba, ta ce mata. “Maidah Sheikh!” Murmushi tayi itama ta ce mata. “Wahiba Malik Menk Jordan!” Girgiza kai tayi tana faɗin. “Wahida Malik Menk Jordan dai! Nafi Wahiba sake fuska. Muje ki gani da idanunki.” Bude musu kofar tayi tana faɗin. “Tadaaaaaa!” Juyowa yan matan suka yi baki daya, suna kallonta, ganin ta dan girme musu, yasa baki daya suka wani dauke kai. “Ashe bana gaya miki ba, wancan me sanye da. Armenia gown ita ce.Nadrah Shatima, gefenta Wahiba Malik Menk Jordan. Ga Jadda can tana fama da Mistih, sunan magenta ne da matar shi itama….”
“Radio me jini, a bar zubata haka, uwar masu surutun Keivroto!” Tura baki tayi tana faɗin.”Jadda kin ganta ko?” ” Ai matsalarki surutu, ki bar baki su shigo, barkan ku da zuwa, sannun da zuwa Maidah.” Gyada kai tayi, tana murmushi. Hajiya Jalilah ta ce mata, “Sayyadah Qudussiyah. Ya aka ji da jama’a.” Murmusawa tayi tana faɗin.”Alhamdulillahi, muna kan fama dasu, sai godiyar Ubangiji.” Gyada kai Hajiya Jalilah taii, bata ce bata da madubi ba, kafin ta fara harkan nan da take a boye,sai da ta zauna a Diana Menk Jordan, foundation. Asalin taimako suke bawa mabukata da yan gudun hijira, tare da yan cirani.
Dare daya ta gudu, kafin daga baya taji labarin an mai da shi, Salsabilah Menk Jordan, sunan mahaifiyar Menk Jordan, bayan rasuwarsu, ita ta dawo nan suka cigaba da kula da wurin, duk da tasha bakar wahala, ko da yake ai ba ita za a ce tasha bakar wahala ba, hatta Malik sai da yayi kamar ba zai tab’a samun kome ba, kafin Allah ya nufe shi da dawowa, masu ganin ba zai tab’a dawowa da abin da aka kwace mishi, tow kuwa sai da ya shafe musu hadda.
“Ina Lalla Salmah!” Murmusawa Maidah tayi tana faɗin. “Maama tana can tana fama da majalisa.” “Allah sarki Ubangiji ya dafa musu, aikin kenan idan kana raye dole ka tashi ka nima, idan baka nima ba kare sai ya fi daraja, duk da akwai mutanen da suke da Sa’a amma kuma niman na kai yana da fa’ida! Atikah?” Ta kwalawa wata mata kira. “Yes Ma!” Ta amsa cikin girmamawa. “Ga bakuwa nan ki kaita dakin da yake kusa da na Nadrah!” “Ok Ma!” Tazo ta amshi kayan me yi mata jagora har cikin gidan, “Baby zan tafi, Sayyadah Qudussiyah zan tafi! Yan mata Wahida ko! Zan tafi” “Allah sarki na zata zai zauna sai dare” “A’a ina da abu me muhimmanci!”
“Allah sarki, sai yaushe!” Satar kallon Jadda tayi taga hankalinta yana kan mage, sai Sayyadah Qudussiyah ta bukaci haka. “duk da tserewa tarbiyyar da kika yi, har yau dai gidanku ne nan, duk lokacin da kika so zaki iya zuwa ki dauke shi kamar gidanku” gyada kai tayi tana faɗin. “In sha Allah!” Sannan ta fita a gidan tana ajiyar zuciya. Wannan shi ne zuwanta na farko bayan barin Foundation din shekaru kusan sha takwas, hawaye ne ya zubo mata.
Su uku kamar yadda suka taso, kallon fuskar Wahiba tafi kamar da Nuratu kamar me, Wahida ce dai take kokarin hango fuskar waye tabbas tasan fuskar. Amma ta manta baki daya ta manta fuskar waye, lumshe idanun tayi tana jin dariyar Nuratu. Bude idanun tayi tana kallon gefen ta. _Idan har na samu Malik dole zai hakura da kiyayyar shi, ya bani abin da nake so._ kauda kai tayi hawaye na zuba mata. “Ku zama shaida idan na kuma ganin, Jalilah sai dai a maidani gidan kaso, amma tabbas sai kashe ta.” Hawaye ne ya zubo mata da gudu da gudu. Ta zauna zaman jiranshi amma aka samu tsinannen da ya shiga rayuwarsu ya lalata kome.
“Ku fita min da ƙaruwar nan, ko na kashe ta” kuka tayi tayi tana kara kukanta, “Malik!!! Ka yarda da ni, ban san kome akan abin da ya faru ba, wallahi ba zan tab’a barin a cutar da Nuratu ba!”
Kuka take sosai har suka isa gida, rabonta da tayi kuka haka, ta manta. Tana shigowa gidanta. Kalamanshi masu zafi suka kara dawo mata. “Ke tsinanniya ce mara albarka, tsiya da lalacewa sune zasu ta bibiyar rayuwarki, kiji da kyau yadda kika bata rayuwar Nuratu Allah ya tsine Miki! Magajiyar Ƙaruwai!” Wani irin abu ne ya tsaya mata a makoshi. Tabbas Malik yayi gaskiya ita magajiyar Ƙaruwai ce, ga gidanta ta cika da karuwai, ita kanta bata taɓa tunanin maganar zai tabbata ba sai yau. Tara dukiyar take amma har yau ba zai yi albarka ba, domin da zina da wasu abubuwan aka same shi. Wucewa ɗakinta tayi abin da ake fada akan Malik gaskiya ne, yawun shi da dukiyarshi Bala’i ne.
———
Tun bayan fitar ta, Sayyadah Qudussiyah ta Sunkuyar da kai, hawaye ne ya zubo mata. “Sayyadah wallahi ban san abin da ya faru ba, a daren ranar na san mun je gidan Lalla Salmah kuma mun ci abinci mun fito, daga nan muka tsaya muka a kofar gidan Lalla Salmah muka shiga Mota. Daga nan ban san kome ba, sai farkawa nayi na ganni a asibiti. Sayyadah wallahi ban san kome ba, taya zan dauki Nuratu da bata da wadatacen lafiya, na cutar da ita, Sayyadah meye amfanin rayuwata idan na lalata rayuwar Nuratu. Don Allah sayyadah kada Malik ya ce ya fasa aurena. Ban san ya zanyi!”
Tabbas nuratu ba ta da laifi, amma waye zai yarda da ita? Bayan an gama bincike an gano biyanta aka yi ta kai Nuratu aka yi lalata da ita. Bayan ta dawo da ita Keivroto tunda Malik yace matukar ya ganta zai kashe ta, yasa ta rufawa kanta asiri ta anan ta zauna daga baya tsangwama da take fuskata yasa ya gudu babu shiri.
Zare medical glass dinta taii, domin har aka gama Nuratu ta haihu ta rasu, Jalilah bata da labari, sai bayan wani lokaci ta hadu da Sayyadah Qudussiyah ta gaya mata mutuwar Nuratu, a ranar tayi kuka tare da cewa In sha Allah wanda yayi sanadin rabata da Malik da Kawarta sai Allah ya mishi, sama da abin da ya mata. Hakika an cutar da ita. Kuma gefe daya Malik ya kara kiyayyar shi da tsinuwar shi yayi tasiri, tasan darajar rashin ahali domin iyayenta hatsarin mota jirgin ruwa suka yi, ita kuma aka sace ta, aka kawo ta Demark, ta sarafa kafin ta fada hannun Alhaji Menk Jordan……
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 2:27 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: CINIKIN RAI….14
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
Maniyyata sun fara payment! Jiran me kike?
<<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>>>>
“`Love looks not with the eyes, but with the mind, and therefore is winged cupid painted blind.“`
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>>>>>
“Jadda ya dai?” Nadrah Khamis Shatima ta tambaye ta, tana kallon yadda ta shiga damuwa. “Ba kome, kawai wasu abubuwan ne idan ka tuna bayan baka da yadda ka iya sai kaji zafi a ranka.” Gyad’a kai tayi tana faɗin. “Haka ne, amma kome yayi zafi maganin shi Allah.” ” Na yarda da haka, sai dai a wata rayuwar, Allah yana sane yake barmu da mugayen halaya. Domin ya ga yadda zamu yi, barin mu a haka shi ne babban tashin hankali.”
Ganin yadda Nadrah ta makale tana son jin me ya faru, yasa ta basar da abin ta mike tare da barin falon. Idan ka zauna da Yaran zaka fahimci kowa da halinshi. Nadrah Khamis Shatima tana da masifar son jin kome, shi yasa kullum kafin kaji labari a bakin wani a bakinta zaka fara ji. Yayinda Wahida Malik Menk Jordan, ta kasance me yawan fara’a da son mutane, da surutun tsiya kamar Radio. Wahiba Malik Menk Jordan kuma sai ta kasance miskila mara son magana, ga dan banza reni da gani-gani. Sannan idan Ubanka ba wani ba ne, bata kula ka. Gashi tana da ilimi sosai, amma magana bai dame ta ba, bayan wannan halin Nadrah yarinyar tana da kirki sosai, domin ba kowa yake iya jure zama da Wahiba Malik Menk Jordan ba, domin kusan kullum sai ta mata rashin mutunci. Amma tana like da ita, tana hakuri hakan ne domin mahaifinta ya rarrasheta da tayi hakuri ta zauna da halin Yaran. Duk da babban damuwarta, shi ne ta samu kusanci da Malik kamar yadda uban ya ce, akwai wani abu daya da suke kokarin ganin sun cusawa yaransu, shi ne dole yaran su bayyana jikinsu ga Malik ta haka sha’awa zata saka ya ga ya bukaci yaran daga Khamis Shatima da Lalla Salmah wannan shine buƙatarsu da kuma kudirinsu.
Shirin su na rikito da Malik ba karami ba ne, sannan idan har akwai abin da suke hari tow dukiyar Malik ne, shi yasa duk abin da suke har kwanan gobe babu nasara, amma zasu cigaba da fafutukar ganin sun sami hakarsu ta cimma ruwa.
★
Amjad
Sintiti yake daga Office dinsa, zuwa bakin Office ɗin. Baki daya hankalinshi a tashe yake, kai yafi ma ganin hankalin shi zaune take da gindinta, wayar shi ce tayi kara ya ɗauka tare da sakawa a kunnenshi.
“Chairman gata nan ta shigo kamfanin!” Hadiye yawu yayi, bai taɓa kawowa a ranshi zata dawo yau ba, sai gashi ta dawo ɗin. Sai da ya sauya kaya sannan ta wuce office dinshi domin Mss Mary ta gaya mata yana son ganinta.
A hankali ta tura kofar, yana zauna a kujeranshi, zuba mata ido yayi. “Ke kuma haka ake rayuwa?” Dauke kai tayi tana kallon waje, “Nasan bai kyauta ba, amma a madadin haka sai ki tsaya ki ji me zance miki, ba wai kiyi gaban kanki ba. Gashi nan zaki hadu da Elbashir, duk abinda zai faru, ya faru amma ka da ki sake baku hadi da Malik ba, shine kawai zai yarda da bukatarmu”
Gyada kai tayi tana faɗin. “Tow idan ban hadu da Malik din ba fa?” Murmushi yayi ya ce mata. “In sha Allah, zaku hadu ina jin hakan a jikina!” Gyada kai tayi a karo na biyu, sannan ta ce mishi. “A ina zan samu damar haduwa da shi?” Office dinsu yana kan titin sir Victor James black. Menk property management companies, ga wannan laptop din naki ne, mun tsara kome sannan na tura musu abin da zaki bukata, sannan sun amince da bukatar tattaunawa da ke, and ban sani ba ko zaki iya tafiyar da wasu abubuwan. Don Allah ku kula.”
“Tow!” Ta fada tana me daukar laptop din, ta fita murmusawa yayi yana hango yadda yayi nasarar kome, ya barta a cikin ruwa tsundum. Juya kujeranshi yayi yana faɗin. “Ina tausaya miki, domin kuwa nama na sakawa Zaki yadda zai fada yaci yana me shiga tarkona!”
Kamar yadda ya fada mata haka kuwa, ta isa kamfanin sai dai kuma tunda ta isa bata samu damar haduwa da kowa ba, asalima, kamar ba asan da zuwanta kamfanin ba, har yamma babu wani gamsashhen bayanin da zai bata kwarin gwiwa.
Haka ta tafi bayan an tashi gida ta nufa, tana isa wanka tayi ta kwanta domin tana hutun sallah. Don haka bata nemi abinci ba, sai dare. Washi gari da zata fita suka hadu da Abbas, nan yake tambayarta sun je gidan Hibba kuwa? Girgiza kai tayi tana faɗin. “Kawu Nura zai zo daga Kamaru, idan yazo zasu tafi da abokin Abba in sha Allah da baban Chu-chu.”
“Shi kenan. Ni dai ku tafi ku karbo min aure da Hibba!” “In sha Allah, kayi hakuri na makara.” Ta fita da sauri, tana hada step, a kasa suka hadu da Hafsy! “Xnoo!” “Babu lokaci, idan na dawo zan har ɗakinki!” Ta bude motar da sauri ta fada, tna sauke ajiyar zuciya. Da gudu ta sa kai zata fita Dundurosu ya tare mata hanya, sake glass tayi tana sako kanta. “kai mataccen nama, sai na bi ta kanka ne?” “A’a amma yau za a biya kudin wuta da na ruwa, kuma mun je har ɗakinki jiya kina barci. ” Bude jakarta tayi ta ciro katin banki ta cilla mishi. “kuyi kome kafin na dawo!”
“Har da sharholiya?” “Sai na kashe ka, idan kayi min wasa da kudi ” ta fisgi motar a guje, ya ce. “Sai mun yi wallahi!” Dukan sitiyerin motar tayi tana faɗin. “punk!” Ta kara wuta da gudun gaske, tafiyar da zai dauketa minti goma sha biyar, yar wutar ciki a cikin minti goma kacal ta isa harabar kamfanin, a hankali ta sauko kafarta wanda yake sanye da Hill na Vince brown sai jakar takalmin, sanye take da gown light brown, kanta sanye da yar dankwali ta daura shi baya, sai sunglass da ta saka shima brown. She look gorgeous and beautiful. Rufe motar tayi tana me takawa a hankali cikin nutsuwa, hannunta daya riƙe da jakarta da wayarta. Daya hannun ta soke shi a cikin aljuhun wandonta. Yau fuskar ba laifi hoda da kwali kawai ta dan goga, sai lipsglow.
Yadda take tafiya zaka iya cewa, wata macijiya ce, tsabar yauki da Yanga. Har ta shiga cikin kamfanin. Ma’aikatan kamfanin sake baki suka yi, suna kallonta domin ta share musu hadda, tana shiga ta nufi wurin matar jiya, ta tambaye ta shin Elbashir ya iso kuwa? Matar ta ce mata bai zo ba, kuma bata da sanin zai zo ko ba zai so ba. Shiru tayi tana sakawa da kuncewa.
A hankali ta d’ago idanu ta ce mata.
“Ko zan iya samun number shi!” “Kiyi hakuri Ma, tsarin aikin mu bai lamunci bawa Kowa number wani ba, domin akwai matsala idan aka fahimci haka!” Murmushi Zeenobia tayi tana faɗin. “Babu wanda zai fahimci haka, idan kin bani” “amma Ma!”
“Shi kenan na fahimta!” Ta juya a hankali, jikinta a mace, Office dinsu ta tafi, tun da ta isa ta bata tsaya a ko ina ba, sai a wurin Mr Amjad. Tana shiga ta watsa mishi files din. “Kasan baka sama min appointment na zama da shi ba, ka bar ni sai yawo nake?” “Kinga ba wani abu bane, amma don zama da shi na nima, wallahi ki duba laptop din.”
Shiru tayi kafin ta mike, “ina zaki?” “Gida!” Ta fada kai tsaye, tana me barin Office.
Wasa wasa tun daga lokacin, Zeenobia bata kuma gajiya da son ganin Malik ba, har sai da ta cika kwana talatin da bakwai, a ranar na bakwai tana isowa, Elbashir Jamal Arab, yana isowa a hankali ta bude motar dama, tana gabansu ne, dake an tura mishi sako akanta da kome da kome.
Har da number motarta, sai da tayi parking, ta fito a hankali yau sanye take da riga da skirt ta atamfar Super exclusive, wata yar karamar gyale ta rab’a a kafad’arta. Bakinta kuwa yaji lipstick alley, bakin kamar ba ita ba, gyara zaman glass dinta tayi, fari da shi. Sai da ta kwashe kome nata a motar, sannan ta wuce zuwa kamfanin duk da tasan shi ne amma duk kar a rena mata ajawali yasa baki daya ta tattara kome ta watsa a gefe, kamar bata san shi ba. Lokacin da ta isa cikin kamfanin dama sun santa suna ganinta suka tarbeta da hannu bibbiyu.
“Yau kam kin zo a sa’a, domin Oga ma ya zo!” Murmushi tayi tana faɗin. “Ayya ba damuwa!” Ta zauna tana kallon agogon hannunta, har suka shigo kamar bata ganshi ba, tana ganin yadda mutane suka mike domin girmama shi, amma ita tana zaune kamar wata sarauniya. Shi kanshi Elbashir sai da ya kalleta da wutsiyar ido, yarinya ce jagab, amma girman kan na meye? Koda ya shiga office dinsa, a hankali ya fara ganawa da bakinsa, kafin aka zo kanta. Tashi tayi ta nufi office ɗinsa. Ko da ta shiga ciki kallon juna suka yi, kafin ta ja kujera ta zauna. “Ina jinki me ke tafe dake?” Shiru tayi tana kallon office ɗin, kafin ta ce. “Malik Menk Jordan!” Kura mata ido yayi kafin ya ce mata, “Idan baki da abin yi zaki iya fita!”
Dariya tayi tana fad’in, “Ni wurin Malik Menk Jordan nazo!” “Baki da lafiya, tashi kije dama tunda na ganki na san za ayi haka fita na saka a fitar min da ke!” “Ai kuwa ba zan tab’a barin nan ba, sai na fara ganin Malik” “ke mahaukaciyar ina ce?” Murmusawa mishi tayi sannan ta ce mishi. “Mahaukaciyar garin nan”
Daukar wayar Office din yayi ya ce.
“Security kuzo ku fitar min da ita;” murmushi tayi, tana fad’in. “Ba zan fita ba, sai na samu ganin Malik Menk Jordan!” Kwankwasa kofar aka yi ya ce a shigo.
Wasu irin kartin maza, shiga suka yi sannan suka sara mishi. “Kuyi min waje da wannan yarinyar!” Mikewa tayi tana faɗin. “Zan baka nan da kwana uku, ka haɗa ni da Malik kafin na binciko waye shi! Daga lokacin da na fahimci waye shi, da zaman lafiya ko da bala’i sai ka haɗa ni da shi. Ka ajiye kalmata.” Ta juya ta fita ba tare da ta kuma cewa cikanka ba. Baki sake yake kallonta tabbas yana ganin tsagera amma ita wannan uwar tsagerancin ce.
Tun daga ta fita taa sauke ajiyar zuciya, bata tsaya ba asalin cikin gari ta nufa. Unguwar Kauraye, tasan ba zasu rasa wanda yasan Malik ba. Don haka ta nufi gidan Basiru Kaura.
Zama tayi tana kallon shi, ba zata manta Nasiru Kaura ba a rayuwarta. “Kaura! Waye Malik Menk Jordan!” Ware idanu yayi tare da rufe mata baki, “shiii!” Juyawa yayi ya riko hannunta suka shige cikin daya daga cikin dakunan gidan. “Baki da hankali ne? Kin waye kike son sanin waye shi?” Kallon shi tayi sannan ta zauna tana faɗin. “Yau nake son sanin waye Malik ? Idan baka sani ba fine!” “Ba zan iya baki labarin Dodonmu ba, amma ki tafi unguwar kudu, wurin Boss me hannu daya, ya baki labarin artabon shi da Malik!”
“Tir!” Ta fada tana me mikewa, barin dakin. “Kaji da kyau sai na nimo, Malik Menk Jordan!” Daga haka ta bar gidan, gidan su ta wuce, tana me alkawarin shigar dare zata yiwa Unguwar kudu, tasan unguwar matattarar duk wani shaidanin marajin magana ne, don koda ta koma gida, ba wani damu ba, abincinta kawai ta ci ta nufi dakin da take ajiye wasu kayan fada. Tana ganin kiran Mr Amjad taki dauka, ai yasan abin da yasa shi hadata da Malik kuma yanzu zai addabeta da kira.
Sai da ta dauki kayanta, sannan ta koma dakin ta shirya cikin kwarewa, sannan ta saka bakakken kayanta, ta saka tare da nufar unguwar kudu, da mashin din Black ta nufi unguwar, da tambaya ta isa gidan Boss me hannu daya. Yana tsaye a wani shago wanda ake sayar da duk wani nau’in makami, amma babu bindiga.
“Boss me hannu daya, Nazo sanin waye Malik Menk Jordan?!” A mamakance kowa ya juya.yana kallonta…….
Kuncanki wacce drama zata fashe next page…..
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
*Idan na samu lokaci zan karo page 1 zuwa dare! In sha Allah*
[8/28, 2:44 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: CINIKIN RAI….15
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
Maniyyata sun fara payment! Jiran me kike?
<<<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>>>>
Baki daya suka juya suna kallonta, idan ka gansu, karti ne na bugawa a mujalla, Murd’ad’an Giants. “Waye Malik Menk Jordan?” “Timmmmmm!” Aka bugata da kasa, sai da taji kamar kashin bayanta ya rugurguje. Domin buguwar irinta a kai ka lahira ne babu notice. Ganin yadda suka bugata da kasa, bata tashi ba suka juya abin su suna cigaba da aikinsu. “Boss me hannu daya,waye Malik Menk Jordan?” Sake surarta aka yi aka maka da tsohuwar motar da take wurin, “wash Allah na!” Ta furta dakyar domin ta bugu asalin buguwa, tashi tayi tana nishi dakyar.
“Last warning ka gaya min waye Malik Menk Jordan!” Da wani irin gudu, mutumin yayi kanta, kafin ya isa ta gyara tsayuwarta, kafin ya idda nufinshi akanta, ta saita shi tare da dukan wuyar shi sai, ya cilla kafin ya fadi sosai a kasa, juya wuyarta tayi ya bada wani irin sauti. Sannan ta ce. “waye Malik Menk Jordan!” Da gudu kartin mazan nan suka nufeta, karfe ta dauka a kasa kafin su isa wurinta, ta isa, gare su ta shiga musu wani irin jahilin duka, idan baka tsayar da tunaninka ba, zata zaka yi ganga ake bugawa cikin wani irin zafin na’ma. Duk abin da yake faruwa Idanunta a rufe. Sai da suka zube baki daya. Sannan ta bude idanunta hancinta yana zubda jini. D’aga kai tayi sama, sautin takunshi taji kawai ta kara rike karfen hannunta, kafin ya yi tunanin kai hannunshi jikinta tuni ta kai mishi wani irin bugu a gefen kanshi. Sannan ta kalle shi ya fadi a sume.
“Waye Malik Menk Jordan?”
“Hmmm yaushe aka haife ki? Yaushe aka reni ki da zaki gwada kwanji da Malik Menk Jordan, kin san waye shi? Shi din Mayor ne birnin nan bakidaya, a shekara sau uku ake ganin Malik Menk Jordan, sunan shi kad’a hantar fusatattun maza yake, balle kuma muryan shi firgita mace me juna biyu yake. Shi karfin da shi daya daidai yake da na kartin maza ɗari, kasuwancin sa yana sama da Ibadar shi da ki tab’a Mishi Kasuwancin sa gara ki kona garin nan ba zai tab’a kula ki ba, Yarinya Malik Menk Jordan ba kanwar lasa bane koma gida kiyi hakuri, idan wani abu ne a tsakaninku tabbas ba zaki iya ba!” Wani irin duka ta kaiwa kofar da yake tsaye, sai da kofar ta karye.
“Farautar shi na fito a daren nan babu makawa sai na sami abinda ya kawo ni, idan kuma aka ki bani, zan ta karya maka mutanenka ne!” Ta fada tana goge jinin da yake gefen bakinta.
“Zan gaya miki, amma ki sani sanin Malik ba abu me sauki ba ne, kinyi yi yarinya da son sanin wani waye shi. Zauns na baki labarin Malik Menk Jordan! Dan kazar da Uwarsa ta kasa, Allah keci da abinsa. Giwa babbar dabba, Zaki baka cin bakin wasu sai dai kaci ka rage.”
————
Kasancewar Hausawa sun yad’u ta hanyar fatauci da kasuwanci, yasa duk inda suka samu matukar wurin akwai kasuwanci basu tab’a barin wurin.
Mahaifin Malik ya taso tun daga Birnin Kano, ya sauka a garin Keivroto, mutum ne da yake da nasibi da Kasuwancin, sannan yana da matukar wadata. Domin daga yadda yake shiga ta Alfarma, gashi yana da gogewa a kasuwanci. Izuwa lokacin da ya iso garin babu wani bakin fata da yake da damar yin kasuwanci, domin turawa mulkin mallaka sun mamaye ƙasar da kasuwanci. Kuma wani abin damuwa anan yadda baki daya aka hana wasu yan kasuwan sai fararren fata da larabawa.
Masu mulkin garin babu abin da suka sani sai cin hanci, idan ka sakar musu kudi, zasu baka garin kayi yadda kake so, shi kuma kasuwanci yazo yi. Don haka ya sake musu bakin aljuhun. Suka yi yadda suke so, a lokacin akwai wani tantirin dan kasuwa Mr Jahid Khan kaf Keivroto kowa yasan halinshi.
Sonkai, son zuciya, bakinciki da keta,
mugun da zalunci, mutum ne da baya bukatar kishiya, duk abin da za a gani daga gare shi ake gani, shi yasa ya k’amk’ame sauran jahohin baki daya. Menk Jordan yana da mata da Yaronsu, baturiya ce tana Demark, asalin ƙasar ce mahaifinta babban malamin katolika ne, tunda ta ga Menk Jordan tace bata da miji sai shi, Menk Malik Jordan, Jordan ya samu asali ne daga kakanshi wanda suka yi tafiyar kasuwanci har aka haifi Menk, lokaci kakan da Uban basu nan, Malam Abdul Malik yana zuwa, ya saka mishi Menk domin mahaifinshi ya rasu a jordan. Shi yasa da ya girma yaji tarihin mahaifinshi a inda ya rasu ya kara Jordan a sunansu, domin Jordan yake kiran Kakanshi, sai ya zama mana Jordan ya fito as family din su.
Menk Malik Jordan ya fara bin kakanshi fatauci har zuwa lokacin da ya fara zuwa da kanshi. A wani tafiyar da yayi ya dawo ya samu labarin mutuwar kakanshi, haka yasa shi bazama, duniya niman kudi, sai yar Uwar.
Bayan tafiyar da yayi ya kai karo har Demark anan ya hadu da Diana, wacce tayi ruwa tayi tsaki, tace sai Menk Malik Jordan. Ubanta da yake yana sonta, ya barta ta aure shi, da cewa ba zata yi musulunci ba, baki daya sun gina rayuwarsu ne a Demark, har suka samu cikin Malik, haka suka yi ta tarerayar cikin har aka haife shi lafiya kalau. Kafin ya tafi Kano ya dauko yar uwar shi. Suka zauna da matar shi, duk wani kulawa Qudussiyah ta musu,
Wani abokinshi ya bashi shawaran su tafi, Keivroto kasuwanci, babu karya Malik da danginshi kasuwanci a jininsu take, domin duk abinda suka tab’a tana yad’o da yabanyayya.
A bangaren Keivroto kuwa, tunda Jahid Khan ya ga Menk ya fara samun jama’a sai kishi da bakin ciki ya fara kama shi, haka yasa shi fara turawa ana lalata duniyar Menk, wanda har ta kai an mishi wani irin taron dangi, amma mutumin bai yarda yayi give up ba, haka shi da matar shi suka kara hada karfi da karfe suka kara habbaka Kasuwancinsu. Abin mamaki sai gashi kasuwancin yafi nada albarka.
Bayan shekaru goma, lokacin Malik yana da shekaru goma sha bakwai, wannan iftila’in ya faru da su, shine na farko konewar Kamfanin Menk Jordan house, kamfanin yin takalmi da jaka, abin tausayi wannan itace mafi girman asarar da yayi a lokacin. Domin Diana tsabar kuka sai da ta daina gani, ana cikin wannan yanayin wasu daga cikin abokanshi suka saka shi zuwa amsar bashin duk da baya so, haka suka tilasta shi amsa, yana amso kudin barayi na biyo bayanshi, suka amshe kudin tare da mishi shegen duka.
Ko kwana ɗaya baa yi ba masu kudi, suka shiga mishi sallama, last dai abin da ya faru shine wasu sun zo gidan sun mishi kashedi. Daga haka sai tsintar gawar shi aka yi ya rataye kanshi, duk da masu binciken gawa sun tabbatar da ba kashe kai bane, kisan kai ne. Haka ya d’aga hankalin Diana wacce bata kawo haka Aranta ba, sai da ta kusan zarewa, kafin Allah ya nufeta da dawowa dai-dai, karshe bayan rasuwar shi ta musulunta, ta koma Salsabilah,. Abin haushi suna wannan rayuwar aka kwace musu kome nasu, hatta passport da zai fitar dasu kasar an kwace haka yasa Malik ya shiga tashin hankali, ga Mamanshi da bata da lafiya. Haka wata rana ana ruwan sama, ta fara rawan dari yaron nan ya rasa yadda zai da ita, dole ya shiga niman wanda zai taya shi su kai Mamar asibiti be samu ba. Dole haka ya dawo, sai a wani tsohon wheelbarrow ya dauka ya sakata suka tafi asibitin, yadda zaka san an shirya kashe su domin da ya kaita babu wanda ya damu ya duba ta, sai ya ajiye kudi haka suka barta a dandaryar kasa, ya fita yana yawo kwararo-kwararo. Kafin a hanya motar Jahid Khan ya buge shi, bai damu da buguwar ba, ya tashi…..duk da ba yawa managing…..
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[28/08, 7:47 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI….16
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
Ai dama kome a shirye yake, don haka Jihad Khan ya fito, yana faɗin. “Yarona! Ina zaka a cikin wannan daren? Ina iyayenka?” Girgiza kai Malik yayi yana faɗin. “Babana ya rasu, Ummata tana asibiti, zata mutu don Allah baba ka bani kudi a duba ta!” Ya fada yana me rike kafar Jahid Khan.
“Ai kai Yarona ne, dole a kula da mahaifiyarka, muje na ganta.” Riko hannun shi yayi suka shiga motarshi, suka nufi asibitin, kallonta yayi in pitiful kafin ya ce. “Ina Director na asibitin nan?” Baki daya asibitin aka taru musamman Drs da nurses, “ku duba lafiyarta kafin na dawo!” “Ok Sir!” Suka fada, sannan ya rika hannun Malik suka fita. “Yarona zan baka wani aiki, kafin ka dawo za a kula da ita kaji.” Gyada kai yayi. Daukar shi yayi har wani kofar gida, ya mika mishi ƙaramar bindiga. “Ka shiga gidan nan, akwai Hashim Zubair, ka harbe shi. Shine wanda ya kashe maka Babanka ya dauke maka dukiyarka. Ka tattara fushinka a zuciyarka, ka dauki fansarka!” Gyada kai yayi, sannan ya fita daga motar, ya nufi gidan ba tare da wani abu ba, ya buga ai kuwa lauyan babanshi ya bude mishi kofar, “A’a Malik kai….!” Sake mishi harbin yayi har sau uku. Faduwa Hashim Zubair yayi, a wurin bai shura ba. Shima kuma Malik ko da ya gudu, ya sami Jahid Khan yana jiranshi, don haka yana Isa wurin shi, Yan sanda suna cafke shi. “Shine ya kashe babban Lauyan nan ta fafutukar kwato hakkin talakawa, a tafi ea shi.” Sake baki yayi yana kallon Jahid Khan. Har aka saka shi a motar yan sanda. Haka suka tafi da shi, a hanya yayi ta dambe da su har suka yi hatsari. Ya fita dakyar, daga nan bai tsaya ko ina ba sai asibiti, koda ya isa ya samu Mahaifiyarshi ta rasu, tsayawa yayi akan gawar har aka zo aka tafi da shi, ba a taba kai mutum gidan yari babu shara’a ba, sai akan Malik, tunda aka kai shi, ake dukanshi da azabtar da shi, sai yayi wata shida a dakin da babu haske ko kaɗan, sannan aka fito da shi. A lokacin Jahid Khan yazo yake bashi labarin shi ya kashe iyayenshi, shima anan aka kawo shi, tow makabarta shi ce, Malik bai ce mishi kome ba, domin a zaman da yayi cikin gidan ya koya mishi shiru ko nace mutuwar Iyayenshi ya saka ya koyi hakuri da shiru, wasa wasa sai da Malik ya kwashe shekaru sama da goma sha biyar a gidan Yari, an manta da tarihinshi a lokacin muka hadu da shi, amma kafin mu haɗu Malik ya gawurta a cikin gidan Yari, domin sai da ya kwace duk wani matsayi da masu fada a ji a cikin gidan. Malik ya samu karfi tun a cikin gidan yarin, domin Yaran da yake dashi a cikin gidan suka fito tow kasuwanci suka fara mishi, misali fasa kori, sayar da kayan maye, shiga harkan siyasa, Yaranshi sun yi karfin suna..
A lokacin sai da ya kai babu wani ne tarin matasa irinsa, gashi a cikin gidan ya karasa makarantar shi na secondary, ya kuma hada da matakin diploma a cikin gidan Yarin. A lokacin da na shiga cikin tura ni aka yi na kashe shi, domin yana gidan wani dan siyasa ya bashi aiki aka yi kuma aka samu nasara, jam’iyyar adawa ta tura ni na kashe shi, amma ban kashe shi ba, an yanke min hannu.
Dawo labari.
Kallon hannun shi yayi dungulumi ya ce mata.
“Malik Menk Jordan, shi ya yanke min hannu. Yarinyar ban tab’a ganin fusataccen mutane irin Malik Menk Jordan ba, domin hatta gashin jikinshi a fusace take, a tsaye-tsaye haka suke. Lokacin da na dawo na samu an daina yayi na, dole na koma gefe da Yarana, muna tab’a Kasuwancinmu.
A lokacin da aka kafa Jam’iyyar PKO Malik da kansa ya kafa ta a gidan Yari, sannan aka samu nasara, a take aka fitar da shi ta hanyar yan majalisunsa, yana fitowa ya saye duk wani kusan gwamnatin, kafin ya shirya tsaf, ranar cika Mayor Jahid Khan, a cikin Bainar nasi, Malik ya kashe shi da duk wani me taimaka mishi sai da Malik ya ga bayanshi, sannan ya shiga bibiyar makasan Iyayenshi, a lokacin da aka ce Malik ya kashe Mayor Jahid Khan, sai da ta kai kowa rufe gidan shi yake, domin kuwa garin Keivroto ya samu tashin hankalin da rikici, yadda suke kokarin zubda jini, yasa Malik shiryawa ya nufi cikin gari, aka yi ta bata kashi sa mutanen Jahid Khan, rigimar da ta janyo dole mahukunta suka dauke kansu, domin rigimar cikin gida ce, Malik sai da yayi ta bin manyan mutane yana kashe su a cikin gari, a gaban Jama’ar gari, haka yasa mutane suke mugun tsoronshi, da kace musu ga Malik gara mutuwarsu.
Sai da ya share Keivroto tass, sannan ya amso dukiyarshi, ya shiga harkan kasuwanci da siyasa kamar me, bayan shekara biyu, Khuldu Jahid Khan ya dawo domin fansa, a gaban jama’a Malik ya mishi dukar kawo wuka.
Wannan yasa shi daina fuskartar Malin gaba da gaba, ya shiga bibiyar shi ta baya, sai dai bai sha dadi ba, domin da Malik ya fahimci haka, sai da ya mishi illar da ya bar Keivroto da kafarshi. A hankali kome ya fara typing daidai,.kafin kuma Malik yayi hatsari bayan mutuwar wasu abokan Kasuwancinsu.”
Shiru tayi kafin ta ce mishi.
“Malik bai da rauni ne?”
Kura mata idanu yayi kafin ya ce mata.
“Rauninshi Nuratu ce, ita din Marainiya ce daga gidan Marayun Demark, kamar kanwa take mishi, a lokacin yana da Yarinyar da yake so, Jalilah karshe an ce Jalilah ta sayar da nuratu ga wani Bature ya lalata mata rayuwa inda ake daurawa Malik sharrin yayiwa Marainiya ciki, kuma a haka Malik ya amshi cikin sai dai basu kasar nan, suna Demark.”
“Kenan bai da Rauni?” Shiru yayi kafin yayi kasa kasa da murya ce mata. “Ai bai da shi, sai dai akwai wani Bad side ɗinshi Dan Luwadi ne, abin da yake aikatawa kenan yasa bai yi aure ba, har yau!”
“Me yasa ba fitar da sanarwar haka ba?” Kasa yayi da murya ya ce Mata. “Babu wanda ya isa ya fada, domin mutuwa zai yi!”
“Kana nufin babu wanda isa ya fitar da zancen kashe shi za ayi?” “Eh yar nan!” Mikewa tayi tana faɗin. “Aikin Banza da ace akan wannan labarin zan bata lokaci haka da banzo ba,.” Ta saka kai ta wuce tana mita.
Karshe hudu na asuba ta isa gida, bata wani bata lokaci ba, ta wuce daki ta kwanta abinta, dakyar tayi sallah asuba. Karfe tara, ta shiga tare da nufar kamfanin Malik! Tana shiga ta wuce office din Elbashir.
Shiga tayi tana me faɗin. “Na dawo, ina son ganin Malik!” Sake baki yayi yana kallon ta.
“Ke wacce irin taurin kai ne dake? Baki ga ina waya ba ne? ” “Da sauki tunda kana raye!” Tayi kanshi da wani karamin wuka ta saka mishi a wuya. “Ina son ganawa da Malik!” Kallon wayar shi tayi taga An daka MMMJ, amsa tayi tana faɗin. “Mayor Malik Menk Jordan! Kana magana da Zeenobia Nasr Hadejia, ina son ganawa da kai na baka nan da kwana uku, ga number ta 0803032……. Idan ka shirya ka kira ni, ni kuma zan iso inda kake! Ka rike sunana Zeenobia Nasr Hadejia, ko Xnoo ko Yar kunama, Zeeno. Duk wanda ya maka kai ka sani. ” Katse wayar tayi ta cilla mishi. Tana me faɗin.
“Baka san halina ba ne, ba zaka min taurin kai ba.” Ta juya ta fita tana waka, ban da rashin mutuncin irin na Zeenobia an gaya mata waye Malik amma tayi biris tayi abin da take da niyya.
Daga nan kai tsaye kamfahinsu ta wuce, tana shiga office din Mr Amjad taja kujera ta zauna, sannan ta daura kafaffunta a saman teburin gabanshi.
“Me ke tafe dake?” Yadda ta bude kafar tana kallon shi ta ce mishi. “Daga yanzu zuwa wani lokaci, zan gana da Malik!” “What!” Ya mike tsaye, “Tantama kake?” Girgiza kai yayi yana faɗin. “Ban yi ba, amma taya haka ya faru?” “Ikon Allah, waye ya gaya maka, wayo da dabara ce?” Nan ta kwashe kome ta gaya masa, gyada kai yake yana mamakin yadda ta daki sa’a.
“Idan kuma yaƙi gayyatarki fa?” Murmushi tayi ta ce……. Me zata ce? Rigima tana gaba,
_Free pages ya kusan karewa! Saura nawa ma? Muje zuwa…._
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[29/08, 12:47 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI….17
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
Wani juya idanu tayi, ta ce mishi.
“Sai na saka shi yayi dan danasani, sai na tabbatar ya biya zunubi da ya fara dibarwa kanshi dole ma ya kira ni.”
Ta fada tana mikewa, karkad’a key din motarta tayi tana wani irin murmushin gefen baki ta ce mishi.
“Bari mu gani, zai sauke girman kai ne ya nime ni, ko sai na fitar da abin da zai saka shi nima na da kafar shi.”
Ware idanu yayi yana faɗin. “Me kike nufi? Akwai wani abu ne?” Murmusa mishi tayi tana faɗin. “Dan luwaɗi!” A firgice ya ce mata “Ke!” Ya daka mata tsawa, yana faɗin. “Kina hauka ne? Da zaki janyo mana masifa, wallahi ki rufa mana asiri!”
Dariya ta saka tana faɗin. “Cabdijan, aikin gama ya gama sai dai kuma kada a kuma !” Ta fada tare da mike zata bar Office din,
——
A can office din Elbashir kuwa, zufa me yake karyo mishi, asalima wani azazzben tsoro ne ya kama shi, muryanshi yana rawa d kira Malik. Zubewa yayi akan gwiwarshi. “Malik don Allah ka bani izini na saka a mata yankar rago.” “Hmmm!” Ya faɗa ta wayar. “Malik ka bani izini na kashe ta. Ko na saka a batar da ita, Malik ka bani izini a aikata mata kome!” “Me take bukata?” Ya tambaye shi a sanyayye, wata irin kamilalliyar murya, mara amo da hayaniya. “Wai.” Inji Elbashir. “Baka tabbatar da abin da take bukata ba kenan? Bashir?” Ya tambaye shi, sake zubewa yayi akan gwiwarshi. “A’a Malik so take ta gana da kai!” Ya fada kamar ya rushe da kuka. “Shekarunta nawa?” “Yarinya ce, bata wuce 19 zuwa 20 ba” kashe wayar yayi, sai a lokacin Elbashir ya sauke ajiyar zuciya. Sako ne ya shigo wayar Elbashir. *Ka jaraba hakurinta?* Da sauri ya tura mishi. _Kusan wata guda tana bibiyar kamfanin domin ta samu gani na_
Bai kuma turo mishi da sako ba, sai dai zuwa can ya turo mishi, *a kawo ta Waterfall island sau uku muga yadda zata yi idan bata samu gani na ba, kafin nan kasa a mata barazana sau uku muga yadda karfinta yake!*
_Done* ya tura mishi. Mikewa yayi yana share zufa da guntun hawayenshi da suka cika mishi idanu. “Shegiyar yarinya sai na saka an zakulo min ita” kiran wani number yayi ya ce mishi. “Maza ka zo kamfani akwai hoton wata yarinya, ku ci min Ubanta ” “Yes sir!”
Bayan kamar awa biyu, wasu kartin yan maza suka tawo, “Yes gamu mun ga hotonta, sannan a bisa binciken da nayi yarinyar yar hannu ce, tasan darajar kwanji!” Cike da takaici ya ce. “Ku razana min ita!” Gyada kai yayi yana faɗin. “a gaban jama’a zamu bata tsoro! Ku muje!”
Barin kamfanin suka yi, ya turawa Malik sakon. *Na bawa su Boddi aikin firgitatta.* Yana ajiye wayar ana turo mishi sakon. _Ayi min recording din kome, idan da hali a saka musu bididdigi tracking!_ gyada kai yayi kamar yana gaban Malik.
______
Da la’asar sakaliya, ita da Yara sun fita cikin kasuwa, abaya ne a saman 3qrt din jikin. Sai riga armless kanta mayafi ta yane kanta da shi, tun da ta nufi cikin kasuwan Yara nata nuna mata abin da suke so, tana cewa. “Ku ɗauka Yarana!” Suna cikin tafiya daya daga cikin Yaran Elbashir ya bangajeta, bata wani damu ba ta ce mishi. “Sannu ko” zata wuce ya janyo ta, tare da dawo da ita gabanshi. Kallon hannunshi tayi a kafad’arta. A hankali ta juya tare da cewa.
“Kayi hakuri!” Sake dukar kafad’arta yayi, yana faɗin. “Karamar karuwa, waye Ubanki?” Fashewa da dariya Yaran suka yi, suna faɗin. “Didi koya mishi yadda ake ladbatarwa.” “A’a Amir kaga Chu-chu tana jin tsoro muje na saka ku a mota!” Ta riko hannun Yaran suka juya wurin motarta, ta bude musu suka shiga, sannan ta juya tare da shiga mazauninta. Kafin su ce sun dakatar da ita ta bawa motat wani Mahaukacin wuta, a guje ta bar wurin, haka suka biyo bayanta, har zuwa Al’umma Charity House. Kafin ta isa dama ta kira Black, tana parking yana budewa Yaran kofa, suka fita da sauri. Shi kuma ya watsa mata wasu karafuna a mazaunin pasinja, da gudu ta taka motar, suka rufa mata, har zuwa filin sai da naka ko aci Ubanka..
Murmushi tayi tana kallon filin babu kowa, sannan ta sauka bayan ta dauki karafunan ta saka a hannunta. A hankali ta bude motar bayan ta cire abayar jikinta, kama gashin kanta tayi ta daure shi a baya, tare da yin gammo da shi ya zauna damar, sannan ta saka ƙafarta me dauke da canvas white and pink, kalar wandonta.
Murmushi tayi tana me kiran su, da gudun tsiya mutumin da ya bangajeta ya zo, kafin yayi wani tunani ta dake shi da hannunta me dauke da karfen, sannan ta saka kafad’arta ta kai mishi wani jahilin duka sai da ya watse a kasa, kamar yadda ake watsar da kayan wanki, yana shure -shure. Mai da kafarta baya tayi tare da yin tsayuwar dambe sosai, sai kace Kungfu girl. Ko nace jinin Mr IP. Kai zata fi dacewa da yar kabilar mandarin, Black ninja blender, wanda suka yi zamani da ibni batuta. Da mugun nufi suka nufe ta, kamar zasu yi rugu-rugu da namarta danye. Yarinyar nan, tana shiga tsakiyarsu. Ta shiga musu duka da karfen da yake yatsunta. Kafin kace kwabo, ta karkarya musu kasusuwan su, ta jibge su.
Dukar kanta Boddi yayi ta fadi can, ta kasa motsi, sake zuwa yayi ya buga mata karfen, ta hantsila ko motsin kirki bata iyawa. So take ta mike amma yadda kanta yake mata barazanar fashewa, yasa ta damke gashin kanta. Jini ne ya shiga bulbulowa daga hancinta. Kamar an bude famfo, ɗauke wuta tayi bata jin kome a duniyarta. Harbinta yayi da kafa ta cilla can gefe, baki daya bata kuma motsawa.
“Yar shegiya, har kin isa ki min wannan barnan na kyale ki.” Wayar shi ya dauko ya fara danna number, ya saka a kunne. “Yallabai Elbashir mun ga…” “Kammmmmmm!” Yayi wani irin kara daga tsakiyar kwandilarshi, zubewa yayi akan gwiwarshi shi. Kafin ya zube sumamme, wayar ta dauka tare goge jinin hancinta. “Elbashir na baka nan da awa ashirin da hudu, ka hada ni zama da Malik Menk Jordan! Ko kuma garin Keivroto city ya mana kaɗan! Nasan kuna bibiyata, don Allah zan kara maimaita maka ka haɗa ni da shi ko na nuna maka salon ukubata!” Ta taka gangan jikin Boddi ta isa gaban motar shi, da aka saka camera, a wurin zaman madubin motar. Dukar gaban motar tayi. “ku karo ashirin, ku kara su zama arba’in na baku nan da awa ashirin da hudu, sai na kakkabe su a garin nan!”
Duka ta kaiwa camera din ya dauke, sannan tayi tafiyarta.
——–
Ajiyar zuciya Elbashir yayi yana faɗin, “wannan mahaifarta ya wuce misali!” Zai kira Malik ya ga sakonshi ya ce mishi. *Darkness’s killer za a tura mata*
_Ok_
Kamar yadda ya fada, haka Elbashir ya basu umarnin su kai mata hari, cikin dare tunda an kundume Boddi,
Lokacin da ta dawo wanka tayi, sannan ta kwanta, kanta na mata azazzben ciwo. Bude kofar aka yi ta bude Idanunta.
“Ba zaki sha magani ba?”
“Ko daya, kaje ka kwanta ka kula.” Sannan ta juya ta wankata,
Sai bayan isha ta farka, kanta sayau ta farka, a hankali ta nufi banɗaki, sai da tayi wanka da alola, tazo ta gabatar da sallah magariba da isha. Sannan ta sha fresh milk, ta koma saman gadonta. Ta zauna har karfe daya na dare, tana zaune sai a kawai ta fara jin motsi me matuƙar hatsari, a hankali domin motsin da bai da hatsari da karfi ake yin shi, motsin da ake cutarwa kuwa a tsanake ake yinshi.
Dauke wutar gidan aka yi baki daya, shiru tayi tabbas ita ke nima, mayafi da dauka ta rufe fuskarta, a hankali ta bude kofar, watsa silallar da ta dauka tayi a wardrobe dinta. “tak-tak⁴!” Taji motsin kafarta, a hankali ta koma dakin, koda suka zo ganin kofar a bude, yasa suka shiga da wuƙake a hannunsu. Rufe kofar tayi bayan sun shiga dakin. Wato, baka jin kome sai karar kartin maza. Kamar zata hallaka su, sai da ta musu dukar kawo wuka, sannan bude kofar. Shiga duba gidan.
Basu nan, kafin ta nufi kofar dakin su Black, ta tashe su, dama a bisa ka’ida babu wanda ya isa ya fito kome ya faru basu fitowa sai ta basu iznin. A hankali suka bude. “Ku haura sama ku dauko min wasu yan iska a saman ɗakina.” Da sauri suka nufi dakin haka suka fita da su, aka jibga su a cikin motarsu, sannan ta shiga motar har zuwa kamfanin Menk Jordan, taje ta ajiye su. A hanyar dawowarta suka hadu da ASP Zulfa. Dauke kai tayi kamar bata ganta ba, tsayar da motar suka yi.
“Ke sauko daga motar, muje Office din mu!” Fitowa Zeeno tayi tana faɗin. “Me nayi?” “Ki bawa hukuma hadin kai, muje.” Janyo hannunta tayi, tana faɗin. “Ki bar ni na tafi, mun bar gida babu wani me iya kare su daga wata masifar.” Juyawa Zulfa tayi tana faɗin. “Kin tab’a tunanin bayanki?” Fisge hannunta tayi tana me juya bayanta. “Me ya hada ki da yan bakar daba?” Shiga motar tayi, tana faɗin. “Wannan matsalata ce” daga haka suka barta a wurin, suna isa gida suka shiga bin dakunan. Suna dubawa sai da suka tabbatar kome normal, sannan suka koma daki suka kwanta.
★★★
Baki daya wannan al’amarin Elbashir, Malik ya bari da chakwakiyya, domin bai tab’a ganin yarinya me taurin kai yana bashi, turawa Malik sakon yayi.
*Assalamu alaikum! Ina kwana Malik yarinyar nan fa bala’i ce.”
_Lafiya lau, ka kawo min ita._
*An gama*
——— Zeenobia bata nime Elbashir ba kuwa sai da ta cika wannan lokacin, kuma bai kuma turo mata wasu yan daban ba, haka tayi ta zuba idanu, karfe biyu na rana aka kira number ta, dauka tayi tana faɗin. “Malik Menk Jordan ne?” “Baki da tarbiyya ne, yau karfe tara na dare mu haɗu a bakin Waterfall, zamu isa Island”
“Hmm!” Ta fada tana lumshe idanunta, a hankali tayi ta niman wasu abubuwan ta, kashe kiran yai, zobenta me dauke da camera, sai abin wuyarta me dauke da Camera. Kafin wani lokaci ta ware kayan da zata tafi ganin shi, ta kira Amjad. Ta gaya mishi halin da ake ciki, bakiɗaya tsoro ta bashi, domin be tab’a ganin hatsabibiyar Yarinya irinta, yana da labarin abin da ya faru, domin shi ya saka mata tracking camera a motarta, a kan idanunshi fadar farko ya faru, tsabar tsoro sai da yayi fitsari a wandon shi, tabbas idan ya sake tasan abin da yake shiryawa sai ta babbake shi da ranshi domin Zeenobia ba zata yafe mishi ba.
“Hmm! Ina ga ko zaki hakura da Malik Menk Jordan din nan ne?” Ya fada mata a sanyayye. “Karya kenan! Wallahi tunda aka kai wannan matakin ai an gama kome sai na hadu da shi.”
Kamar zai yi kuka ya ce mata, “Don Allah a hakura da Malik din nan, kada ki manta mu muke nima, amma ace muke bin shi da yaki kamar akwai kasada hakan!” Murmusawa tayi tana faɗin. “Ban tab’a fail mission ba, duk abin da na saka a raina sai na cika shi don haka akan Malik Menk Jordan ba zan fara ba, kuma dole ya saka hannun jarinshi a kamfanin mu!………….._Hhhhhhh, a haduwa da Malik ya zama Jidali!_
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[30/08, 8:42 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI….18
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
Kamar ya sake zawo a wandonshi ya ce mata. “Zeenobia ayi haka a hakura da shi kawai.” “Bata lokacinka kake kawai, amma tabbas sai na ga Malik duk abin da zai faru sai ya faru!”
Tabbas yaso haka, amma bai tab’a zata haka abin yake ba, domin ta ga Malik duk ta haukace, fisabilillahi sai kace akanta aka fara samun matsala, kome sai taci da karfi, sai kace jikar iliya dan mai karfi, gaskiya ba zai yarda da wannan zancen ba.
“Chairman kayi hakuri, amma na yanke kuma haka zan aiwatar da abin da nayi niyya.” Daga haka ta kashe wayar tana me kallon wardrobe dinta, tabbas dole ta kure a daka domin zata gamu da Malik, domin bata son ta isa wurin shi yayi mata kallon bata kai wacce ta dace da ya hadu da ita ba. Kallon madubin mirror dinta tayi
Ta juya tana kallon bayanta, d’aga pillown kwanciyarta tayi tare da kwashe atm dinta, ta dauko abaya ta daura, sannan ta fita shiga motarta tayi tana faɗin. “Dole yau na gyara kaina da jikina.” Ta fada tana bawa motarta wuta.
Ita kanta tana jin wani irin d’auki na son ganin gawurtaccen zakin da ya hana kowa sakat, so take ta ga yadda ya samu damar yake bugawa kowa mulki kamar masarauta. BINTUN BATUL SALOON WORLD AND SPAN.
Gyaran jikin da saloon ake a shagon, kamarsu dilke, lalle, da Makeup. Ba karamin wuri ba ne, domin yaran masu kumbar susa ne, da matan manyan suke zuwa wurin. A hanyar titin da zai kaita wurin suka hadu da ASP Zulfa. Bin motar tayi da idanu, a hankali ta bude file din gabanta. “Sajan Barau yarinyar nan, me yasa bata da kamun kai?” “Madam bata da laifi fa, haka iyayenta suka watsar da ita, kuma ta daura rayuwarta a kan haka!”
“Allah ya kyauta” “Amin” ya fada.
★★★
Demark
Zaune suke a dinning room, kowacce da abinda take bukata. Kallon juna Wahida suka yi da Nadrah. Suka dauke kai, “Wahiba ina Maidah?” D’aga kafad’arta tayi tana faɗin. “Tana can dakinta!” “Atikah ajiye abincin ki je ki kirata” domin yau ta lura Wahiba bata jin yan surutun.
Lokacin da Atikah ta isa dakin, ta samu tana shiryawa ne, cikin girmamawa ta ce mata.
“Jaddah tana kiranki!” “Tow gani nan” ta fada tana gyara zaman yan kunnenta. “Tow!” Atikah ta ce mata, a hankali ta juya ta cigaba da abinda take, sai da ta gama sannan ta shiru tana tuna maganar da Lalla Salmah ta gaya mata jiya.
_Ni ban aiko ki, ki zama yar kallo ba ne, na aiko ki ne domin ki rabe Malik, Jalilah zata miki kome, domin itama tana da fushin Malik bana son ki gaya mata gaskiya. Kada ki sake Nadrah ta rena ki domin zan mugun sab’a miki._
Ta rasa yadda zata yi da ranta, yau kwana biyu da zuwanta, idan ta cire Wahiba da take kulata, sauran babu me kulata kowa ta kansa yake, a hankali ta fito a dakinta jikinta a sanyayye. Koda ta isa dakin cin abincin, baki daya hankalinsu na kan abincinsu. Zama tayi ta fara kokarin zuba abincin. “Ki sake jikinki, nan ma kamar gida ne. Ki daina zaman a daki kamar wata bakuwa.” “Hmm! Kin san bakon da yazo birni daga kauye dole ya koma dodon kanshi.” Juyawa Nadrah tayi tana kallonta, domin itama yau da safe Babanta ya kara mata magana, akan lallai ta samu shiga ga Malik. Domin an turo Maidah ce, domin ta samu Malik. Yadda ya tsara mata kome, da yadda zata na dragging din Maidah har ta ji ta gaji ba zata iya shiga rayuwar Malik ba.
Wahiba da Wahida, basu kai su shekaru ba. Amma kuma suna sane da cewa Dad ɗinsu anyi maganar aurenshi da Nadrah aka fasa. Amma kuma dawowarta wurinsu yasa baki daya suke shiri da ita musamman Wahida domin tafi Wahiba kirki da saukin kai, amma kuma idan ka gansu su uku, zaka dauka cewa halinsu daya ne.
“Jaddah kin gayawa Dad saura kwana biyu, Birthday dinmu?” “Kici abincin zamu yi magana idan na gama!” “Na koshi!” “Kin san dai ba zai saurare ki ba, idan baki ci abinci ba.” “Jaddah don Allah ki saka baki ni na gaji da Demark mu koma Keivroto kinji.!” Inji Wahiba. Kallonta yan matan suka yi, ta saka fuska kamar ba ita tayi magana ba, dama ba gwanar magana ba..
“Ya ce zaku koma, har da ni amma sai yayi aure domin yadda zaku ji dadin zaman gidan da mace a cikin gidan idan babu mace ai babu magana.” Cikin karambani Nadrah. “Jaddah wani auren zai yi?” Take Sayyadah Qudussiyah ta d’ago inda Nadrah ta dosa, gyada mata kai tayi, ajiyar zuciya ta sauke, tana faɗin. “Akwai wani abu ne Nadrah!” Girgiza kai tayi tana faɗin. “Babu kome ” ta fada tana mikewa. “Har kin koshi?” “Eh” ta wuce dakinta, ta dauka jakar makarantarta, ta fita daga gidan baki daya, domin tana bukatar shaƙar iska me sanyi don Allah kadai yadda take konewa ta cikinta, Malik yayi rejected ɗin aurenta. Ba tare da wani dalilin ba, kawai yayi dumping ɗinta, ba tare da tasan dalili ba, da farkon da Babanta yace zata auri Malik da kwana biyu su shigar da shi kotu, karshe a raba dukiyarshi a basu, tayi farinciki ko babu kome zata shiga sawun matan da suka shahara, amma once lokacin da aka gama kome suka yi magana da Malik sau biyu akan ta amince zata aure shi, sai da magana tayi ƙamari kowa ya sani, duniya ta dauki al’amarin bawan Allah nan ya kira Babanta ya gaya mishi ya fasa aurenta.
Kuma tsabar girman kai, mutumin naj bai gaya musu dalilin da yasa ya fasa auren ba,sai dai kawai ya ce ya fasa kuma har yau tunda ya ce ya fasa ko da wasa bai kuma nimanta ba, wani bin tana jin zai kira Yaranshi su yi ta waya, amma ba zai tab’a cewa a bata ba, wani abin tashin hankalin tun daga ranar Allah ya daura mata sonshi da kaunarshi.
Kai ko waya yake kamar ta gigice haka take ji, amma shi ko ta kanta baya bi. Wani abin burgewa ita ubanta yake kokarin shigar da ita, amma ita ta tsaya a ina nan bata son cusa kanta tunda dai baya yi da ita no way da zata ce sai yayi da ita, number wayarshi hotonshi da Yaranshi suna wayarta amma ko sau daya bata tab’a gwada kiranshi ba. Tana tsoron kada ta kira ya sake mata gwiwa.
Daki Jaddah ta koma, Maidah tana kallon kome, kamar bata san meke faruwa ba. Lokacin da Jaddah ta koma dakinta itama Maidah mikewa tayi ta koma dakin ta kira Lalla Salmah .
“Maamah! Dama Malik aure zai yi?” “Waye ya gaya miki.?”
“Yanzu naji Jaddah tana fadawa Nadrah da ta tambaye ta.”
A nan ta shiga gayawa uwar abinda yake faruwa, sosai suka yi gulmarsu, har da zagin Nadrah Khamis Shatima, bata da kamun kai tunda gashi ta iya tambayar ashe wanda ya fasa auren har aure zai yi.
—-
Jaddah kuwa kiran Malik tayi, ya kashe wayar cikin girmamawa ya kira ta.
“Babata me kike bukata?”
“Babu kome Malik, kawai ban ji dadin yadda Yarinyar nan Nadrah take ta jiran ka ba.” Shiru yayi kafin ya ce mata.
“Anne! Kin san meye? Har ga Allah na so aurenta, amma kuma maganar gaskiya ba zan aure ta ba.”
“Malik naga soyayyar gaskiya a tare da ita, idan bar kace ba za a bata damar haka ba, tow babu amfanin zamanta a nan, ka gayawa Mahaifinta ya turo ta koma domin ta haka ne kawai zata cire rai a tsammanin samunka.”
“Zan mishi magana, in sha Allah idan kuma akwai abin da take bukata a tambaye ta sai na mata, domin ba zan barta da haushina ba.”
“Duk da haka, yana da kyau ka gaya mata gaskiya ta haka zata kara ganin girmanka, ki babu soyayya kai Uba ne mata, balle kuma izuwa wannan lokacin na fahimci girman yadda take sonka. Duk da ban san me ya sauka maka ra’ayinka akanta ba, amma ina son ka sani ta hanyar rarrashi zaka iya wanke abin da ya janyo rashin aurenku, amma ka sani matukar ba wani babban dalili bane, ka juyawa auren Yarinyar nan ba, tow wallahi Allah sai ya kama ka, domin tayi matukar kokarin zaman jiranka, Malik da ace kai kake bin mutum gara shi yake binka kayi tunani sa kyau!”
“Anne, dalilina me karfi ne haka kawai ba zan ki aurenta ba, kawai zan lallabata ta fidda wani mijin tayi aure amma maganar gaskiya, bana son aurenta don Allah Anne ka da ki min dole!” Gyada kai tayi kamar tana gabanshi ta ce mishi. “Ba zan maka dole ba, kana da ikon auren abin da kake muradi, ko dan Yaran Nuratu. Sannan Jalilah mun hadu da ita!” Shiru yayi kafin ya ce mata. “Anne zan duba wasu takardun.”
“Malik idan ba zaka auri Nadrah tayi maka wani abu, tow ita Jalilah fa.” Kai tsaye ya ce mata. “Kawaliyan ce zan aura na kai gidana? Allah ya gani ba zan iya auren macen da ban isa da ita ba, sannan macen da ina ji ina gani sunanta zai taba Martaba ta da kimata!” “Malik kimar ce da kai?” Ta fada a fusace, dariya yayi ya ce mata. “Anne kima ne dani, da ba ni da kima wacece zata damu da tsoho me farin gashi. Kawai ana bina ne domin kudina da kimata, idan bani da su karen layi sai ya fini daraja. Anne matar da nake son aure wacce bata damu da abin hannuna ba, me tausayi da jin kai, wacce ta dandani irin rayuwar da nayi, ba wacce zata same ni daga sama ba, duk da..!”
“Malik a ina zaka samu irin macen da kaje bukata? A wacce duniya zata zo maka? Malik kayi hakuri da abin da yake hannunka, ka auri Jalilah tunda duk lalacewar masa tafi kashin shanu, Jalilah kaɗai zata iya tsaya maka.”
“Anne idan na auri Jalilah, shekarunta arba’in da wani abu, yaushe zata haifa min Yara? Idan na auri Nadrah burin da yake ranta sai ta idda a kaina, idan na auri wata mace daban daga wani waje, tunaninta daban nawa daban. Anne so nake na samu macen da duniya bai dame ta ba, shiru shiru wacce bata da dogon buri” gyad’a kai take fuskartar a murtuke ta ce mishi. “Shiru-shiru ka tafi makarantar Kurame, wacce bata damu da duniya ba, ka auro Aljana kawai, Malik rayuwarka ce ka da kayi auren idan kaso, shashashan wofi” ta kashe wayar dama an saba kwana biyu ba a yi ba.
★★★
A lokacin da Zeeno take wuce babban titin, South Craig. Khamis Shatima yana tsaye a bakin bankin Savanna. Suna tattaunawa da wani mutum kawai taga motar ta, ta wuce. A gurguje yayi sallama yana me bin bayan motar. Duk da tayi mishi nisa amma sai da ya bita, ganin tana shiga wurin wanke kai yasa shi rage karfin gudunshi ya bi bayanta.
Koda ta shiga shima cikin harabar SALOON WORLD din ya shiga, yayi parking, ya jima a zaune a motar kafin ya fito a nutse ba zaka tab’a yarda cewa ya ajiye kamar Nadrah ba, akan idanun Asp Zulfa da ta biyo bayan Zeeno. Tasan haka kawai K Shatima ba zai zo wurin ba, sai dai idan Zeeno wurin ko kuma akwai matar shi a wurin.
Lokacin da Zeeno ta shiga yan mata biyu ne, suka tare ta sannan suka nuna mata wuri ta zauna, suka shiga kawo mata kayan motsa baki, kafin suka ajiye mata menu, shigowar shi yasa suka d’ago kai, kasancewar wuri ne na mata zalla, kuma babu wata babbar mace balle ace matar shi ce, duk yan mata ne a wurin musamman da yake satin biki ne, akwai bukukuwa sosai a garin.
“Yallabai meke tafe da kai!” Murmushi yayi ya zubawa Zeenobia idanu kamar maye.
“Wurinta Princess Zeenobia nazo!” Juyawa tayi tana kallon Zeeno da vata san me suke ciki ba, sai da ta bashi hanya, ya wuce ya tare da zama a gabanta. Kallon shi tayi irin kai kuma daga ina? “Nazo wurinki ne!” Ganin yadda aka zuba mata idanu. “Ko zaka bani dan tazara, irin wannan zaman yayi kusanci da yawa!”
“Duk yadda kika ce Baby!” Sake baki tayi kafin ta kuma maimaita sunan Baby. Galala ta sake baki ta ce. “Baby! ”
“Yes you are my baby girl!” Kallon kanta tayi kafin ta ce mishi. “Hala Yarka da ta b’ata me kama dani ce ko?” Girgiza kai yayi ya ce mata. “Ina sonki!” Daga haka ya mike ya nufi inda ake biyan kudi, ya bada katin bankin shi aka zari kudi masu yawan gaske. Sannan ya dawo wurinta. “Ki kula min da kanki, ina bibiye da ke.” Daga haka ya juya ya fita, da farkon ganinta da yayi ya so, suyi rayuwar watsewa amma yanzi da ua ganta, ya kuma hango nutsuwar da ba kowa ya dace ya hango ba, ya shirya tsaf domin ya aure ta. Duk da yaji labarinta da kuma ƙoƙarinta, baya fatan ya rasa kuma yaji labarin dabanci ne a gabanta ba karuwanci ba. Shi yasa ya dan bata lokaci kafin ya bayyana kanshi.
Tun da ya fita take kallon kofar, “in sonki!” Dariya abin ya bata, har aka gama mata gyaran ta nufi wurin biya aka ce ya biya har da sauran canjinta, kallon matar da take wurin biyan tayi ta ce mata. “Ki dauki sauran canjin.” Ware idanu tayi tana faɗin. “Ma kudin yana dayawa kusan dubu saba’in ne” watsar da hannunta tayi tana faɗin. “Babu abin da zan yi da shi, dauka kawai.” Har gaban Zeeno ta fito kamar zata kwanta mata a kasa, ita kuwa ta wuce.
A hanyar komawa gida a ka turo mata text.
*Kina ta shirin ganin Malik bari na gaya miki, wadanda suka fiki basu samu ganin shi ba, balle ke karamar Yar iska karuwa irinki idan har kina ganin karya ce, bismillah, kamar yadda suke renawa amintattunsu hankali haka kema zasu rena miki hankali*
Wannan sakon ya fusata Zeeno, tabbas akwai renin hankali a cikin maganar amma yau, ko da muzuru ko da shawo sai ta ga Malik…. (LALLAI DUNIYA DA MUNAFUKAI! DON ALLAH WAYE YA TASHI SABON RIGIMA ANA ZAMAN LAFIYA SAURA PAGE BIYU NA GAMA FREE PAGES)
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
PLEASE IDAN KUN KARANTA KU MIN SHARE FISABILILLAHI
[31/08, 6:31 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI….19
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<|=|>>>>>>>>
Wannan shafin na kune
@Saudah Jaafar
@Aysha Dashen Allah @Maman Zara @Mom Inty @Ummu Ihsan @Z Auta
🚶🏽♀️🙄 in da ba kasa…….
<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>
Yadda take tukin yasa aka yi ta kauce mata a hanya. Har ta isa gida, wanka tayi tare da gabatar da sallah. Tana idar da Sallah hafsy ta shigo tana kallonta.
“Baby ina kika shiga ne?” Wani banzan kallo ta watsa mata, tunawa da tayi da Shatima. Ta sanshi sarai domin yana cikin files ɗin Malik, amma bata zata zai kawo kanshi cikin sauki haka ba.
Murmushi Hafsy tayi tana faɗin. “Malama kwana biyu, bamu hadu ba?” “Eh abubuwa sun sha min kai!” “Kuma shi ne babu magana!” Gyada kai tayi tana faɗin. “eh tow kuma da haka, idan ban miki magana ba, ke uwar me bakinki yake da ba zaki min magana ba?” Sake baki Hafsy tayi tana kallonta. Kafin ta juya zata fita ta ce mata. “Yawwa idan zaki fita, ki rufe min kofar domin na tsani sauro ya cije ni.” Wato ita Zeeno bata da aiki sai kunsa maka bakincikin musamman idan ka damu da ita.
“Dan Uban sauron ya kashe ki” ta fada tana me barin dakin a wangale. “Kambu! Na rantse ban yafe ba. ” Hafsy bata saurare ta ba, domin ta lura iya shege take ji, don haka bata damu da ita ba.
Sai da tayi sallah magariba da isha, sannan ta cancad’a wanka, tare da wankar kure adaka, musamman da ya kasance babban mutum ne, kuma tana son gani daya ya sara mata, ya san cewa ita ba irin kananun tsagerun nan ne ba.
Tsaki tayi kafin ta kira Hafsy a waya. “Dan Uban mutum me zan mishi?” Murmushi tayi ta ce mata.
“Ki zo ki min light make-up!” “Hala ajiye ni kika yi, ba ni zuwa.” “Mtseeeeeew, kinyiwa Kanki dama biyanki zan yi!”
“Shegiya kamar kin san bani da kudi, gani nan tawowa!”
“Mayyar kudi! Ko kunya baki ji ba.”
“Ki gaya min inda bolar kudi yake, na je na tsinta dan kaniyarki ” ta kashe wayar, Hafsy kwalliya take yi, tana zuwa har gida tayiwa mutane, duk da kusan kayan kwalliyar Zeenobia take saya mata ko ta bata kudi, duk da jagaliyarcinta, tana kwalliya kawai bata damu da saka kaya ba ne, amma yarinyar ta san darajar ado da saka sutura.
Can Hafsy ta iso bakin kofar, ta buga kofar. Bude mata tayi, kallon wata hadaddiyar doguwar riga blue-black, har sa hat dinsa. “Wow ko nace sexy!” Zama tayi ta fara Ciro kayan, tana faɗin. “Dinner zaki ne?” “Lunch za ni” d’ago kai tayi kafin ta ce mata. “Wai ke meye matsalarki da bakar magana.” Dauke kai tayi tana latsa wayarta kamar bata san me take tambayar ba. “Kutumar Uba!” Ganin hotonta an manna a wani shafin yanar gizo an rubuta.
*BA IYA DABANCIN NE SANA’ARTA BA, HATTA KARUWANCI DA MANYAN MUTANE TANA YI DOMIN SAMUN DAMAR HADUWA DA MALIK MENK JORDAN!*
aka saka hotonta a gefen wani blank pic da babu hoton kowa sai alamar tambaya. Lekawa Hafsy tayi, ta amshe wayar. “Kiyi hakuri abin da nazo gaya miki kenan, amma da nasan baki san da zancen ba da.” “Yi min kwalliyar, na rigada nayi alƙawarin sai nayi aikin nan!” “Amma Zeenobia! Ki daina shiga duk wata kazamar harka, domin da ita za..”
“Ki min kwalliyar kawai!” Haka ta shiga mata kwalliyar, har aka gama cizon bakinta take, tana gamawa ta ce mata .
“Done!” Murmushi tayi ya ce mata. “Yayi kyau, bude wancan drower din akwai abin da kike so, ki sauka kawai!”. Ta zauna tana kokarin zoge rigarta. “Zeenobia!” Bata juya ba ya cigaba da kokarin saka rigar. “Kiyi hakuri!” “Da aka yi me?” “Da abin da ya faru!” “Kai manta kawai!” Da taimakon Hafsy ta gama shirinta tsaf, sannan ta ciro Christian Dior bag and shoe, ta saka hill ne sosai. Sannan ta gyara zaman takalmin.
“Zeenobia ya baki saka turarenki ba!” Murmushi tayi ta ce . “Ban manta da shi ba, duba can akwai Tom Ford cafe rose.” Ciro mata tayi ta fesa kadan, take dakin ya dauki wani sassanyar kamshi. Kama gashinta kanta tayi, ta daure shi. Sannan ta daura hat din kanta, “Don Allah zan iya daukarki hoto zan daukar a IG na ne, zan yi magana ne!”
“Yaushe kika koyo takife?” “Zaman da Yar kunama!” Gyada kai tayi tana fad’in. “You’re welcome!” Daukarta hoto tayi sosai, a wurin ta daura a IG.
*SHI KARUWANCI IYA CE, DUK WANDA YA IYA YA KWASHE, DUK WACCE TA JI HAUSHI GOBE TA SHIRYA GANIN MAYOR MALIK MENK JORDAN…… UP-UP-UP SARAUNIYAR VOGUE MAGAZINE COVER*
Dama bata da wasu followers, amma tana sakawa ta yi amfani da Hashtag tare da gidan gwamnati dake Waterfall island, take aka fara bibiyar pagenta. A cikin abin da bai haura minti Talatin ba, sai ga Followers sama da dubu biyu sun bi ta, amsar wayar Zeenobia bata ta gyara pagen din tare da saka hotonta, ta kuma rubuta cewa.
*The dreams can be true!* Kafin ta saka yar ƙaramar hoton 🌹 kallon Zeeno tayi ta ce mata. “Yar kunama ina zaki ne ma?” “Hmmm! Ina son zan kaiwa Malik wancan takardun ya saka hannun jari ne?”
“Bura Uba! Dama haduwa da Malik ne wannan adon? A tow dole mu gayawa duniya mu haɗu da Malik!”
“A’a bana buƙatar haka, ina son sirri a rayuwata, domin sirri na da dadi, DABANCIN dai da aka sani a bar shi a haka, ban da personal life, wannan nawa ne ni daya na, koda kika ga na bude account ba yana nufin kowani shirme zan daura a kai ba, ina son rayuwata da take binne yafi armashi.”
“Kin sa jikina ya mutu, me yasa kike boye kanki?” Murmushi tayi sannan ta ce mata.
“Hafsy a gare ku, ni ba kowa bace face wacce kuke tare kuke haya gida daya. Amma a gare ni, kune duniyata idan wani abu ya same ni, ba zaku yi kuka sosai ba. Amma idan wani abu ya same ku zan mutu ina kukan abin. Rayuwar mu ta zahiri tafi dadi sama da ta social media! Ina son kowa ya za sani a zahiri ba ta media badili ba, kin ga ajiye wannan Posting din saura minti goma kacal na isa inda zamu haɗu.”
“Ok ranki shi dade, a dawo lafiya!” Daga haka ta dauki key motarta da jakarta da files din, ko da ta sauka kasa, cillawa Dundurosu key tayi yana cewa. “Kai katon banza muje ka raka ni!” Haka ya cabe, sannan ya shiga gabar motar tana baya. “Uwar ɗakina, ina zaki haka kika tashi kan gidan nan da kamshi?” “Meeting!” Ta fada tana kallon agogon chopard, tab’e baki tayi tana faɗin. “Bakin Waterfall island zaka kai ni!” “What?” “Ka kalli titi ka da ka watsar da ni a rami” daga haka bata kuma magana ba, har suka isa bakin ruwan tara saura minti biyu.
Sai dai abin mamaki, tunda tazo babu alamar akwai me jiranta, ko za azo dauke ta, tun tara saura minti biyu har tara da rabi. Idan ranta yayi dubu sai da ya ɓaci, kallon agogon hannunta tayi tana kwafa. “Muje Man” tasar da motar yayi suka bar wurin.
Da ɓacin rai ta isa gida, tana isa ko magana bata yiwu kowa ba, dama kuma haka take idan ranta ya b’aci bata magana. Har ta isa ɗakinta ta kwanta bata cire kayan ba, sai fuskarta da ta gyara ta cire makeup din ta kwanta, wurin karfe biyu na dare, tana zaune akan abin sallah, wayarta tayi kara. Bakuwar number ce don haka ta dauka tana me sakawa a kunnenta. “Me ya hanaki barci?” Shiru tayi tana son tuno muryan. “baki gane ni ba ne? Ai na yi following din ki a IG!”
“Shatima rite?” ” Yes Baby!” Murmushi tayi sannan ta ce mishi. “Ai ko a duniyar mafarki bana jin kalmar baby ta dace da bakinka. Ai kai Babana ne!”
“A’a naki wayon. Baby Ina sonki da aure!” Ajiyar zuciya tayi tana faɗin. “Don Allah kayi hakuri ni bana son wanda bai kai ka ba ma, Ni har ga Allah ka min tsofa!”
“What! Shekaru na basu wuce hamsin da takwas ba fa!”
“Allah na tuba, ai ko talatin da tara ya tsufar min balle me arba’in! Ni bana son me shekaru irin naka, kada ya wuce talatin da biyar. Yawwa muci kuruciyarmu tare ba wanda xan aura ya cinye min kuruciyata ba.”
“Zainabia kin san me kika faɗa?” Ya tambaye ta, in serious tone. “Yes na! Ni bana son namiji da ya tsufa. Ba a san waye gawan fari ba, idan ka mutu ka bar ni kafin na samu daidai dani ya aure ni, zan sha wuya so kawai hang out!” Ta kashe wayar.
Sake kiranta yayi yana faɗin. “Ni ba irin wadannan tsofin ba ne, ina da lafiyar da zan baki kulawa, ki amince da ni.” Dariya tayi sannan ya ce mishi.
“Kaga kuwa bana son tsoho, har ga Allah idan nace maka ina sonka nayi karya, kawai zan ta bata maka lokaci ne, idan na samu wani nayi aure ba ni da dogon buri. Iya abinda ba samu ya ishe ni, na fahimci maganata.”
“Young lady! Ina son na gaya miki wani abu daya, zan cigaba bibiyar lamarinki!”
“Hmmm! Ina baka shawaran ka da ka tsaya ka tafi akwai yan mata dayawa!”
“Ni ke idanuna ya gani, ki haifa kin Yara kyawawa irinki!”
“Sai da safe!” Ta kashe wayar baki daya, a wurin ta kwana, wurin karfe shida ta farka, ta shiga ban daki tayi alola ta gabatar da sallah asuba, karfe tara ta nufi wurin aikinsu, taso ta tafi ta titsye Elbashir, amma kada ya ce akwai wani abu da take nima yasa ta share shi.
Office din chairman ta shiga domin, tun a block one ta fahimci, akwai matsala musamman yadda ake kara kallonta ana kallon wayarsu. Fuska tayi tana me shiga Office din. “Wacce irin abin kunya kika aikata haka?” Ya cilla mata jaridar. Daga bangon shafin ta hango an rubuta.
*BAN SAN IYA MANYAN MUTANEN DA SUKE BINA ZAKU KWANTA DA NI BA!* bata kuma marmarin karanta sauran bayanin ba. “VOGUE MAGAZINE sun cire hotonki a jikin mujallarsu.
“Dama ai ban aike su, su saka hotona ba! Sannan da ake ihu kamar kare ni na bukace ka ko kai ne ka bukace Ni? Kamfaninka kake niman cigabanta, kai me yasa baka fuskanci Malik ba? Kasan hadarin da mutuwar da na fuskanta? Amma ka bude wawwaran bakinka kana min ihu. Kaci arzikin halaccin da kai min da sai na zane maka mazaunanka wallahi!”
Daga haka ya juya ta fita, bata tsaya ba sai a wurin motarta, tana shiga wayarta yana kara. Ɗauka tayi aka ce mata. “Ki tow daga kamfanin, akwai wata sharon ki ajiye motarki ki shiga.”
“Waye kai?”
“Kiyi yadda nace!” Da farko ta dan rude, amma kuma daga baya sai tayi kamar yadda ya ce, har inda motar take ta ajiye. Sannan ta shiga sharon ɗin, sai da aka kaita gindin gada, aka bude mata bayan an zazzage jakarta da takalminta, sannan aka nuna mata wata Audi,. Shima suka fara tafiya sai da suka bar cikin gari, sannan suna isa wurin da aka ajiye wata mota Rr, ta fita sannan aka bude mata shi, ta shiga a hankali. “Wai ina zaku kai ni?”
Wayarta tayi kara tana dauka aka ce mata. “Saurin me kike?” Aka kashe wayar, ana fara tukin, aka saka mata wani abu tare da rufe mata fuskarta.
Sannan suka fara tafiya, sai da aka yi tafiyar minti Talatin kafin aka fito da ita, tana jin lokacin da aka tadda injin kamar jirgin ruwa. Haka aka yi ta gudu da ita, ba halin ta bude fuskartar. Suna isa ana fito da ita, jin ta taka kasa sosai yasata sauke ajiyar zuciya. A hankali suka shiga mata jagora har ta shiga motar da zai katai Mansion ɗin, duk wani abin da ake sai da aaka mata bayan ya cire bakin abin da aka rufe fuskarta.
Kallon kome tayi na gidan Black and whiter. A hankali take gyara zama⁰n hular kanta, da ya zame. “Ina ne nan?” Murmushi aka yi bayanta.
“Mayor Malik Menk Jordan Mansion!” Juyawa tayi ta ga Elbashir, “zamu iya shiga!” Kallon hanyar tayi tana takawa a kasaitacce, domin shi destroy all over record na kowa ta kuma kafa nata da kanta. Har cikin gidan ya rakata, aka bude kofar shiga gidan ya shiga tana bin bayanshi.
“Me yasa jiya kayi breaking promise dinka, bayan ba haka muka yi da kai ba?”
“Shiiiiiiii! Keep quiet ba a cika surutu anan ba!”
Gyada kai tai, har suka shiga cikin gidan a ranta ta ce. “ko makabarta ana magana balle nan!” A tsakiyar Main falo suka tsaya, karar inji yasa suka juya bayansu.
“Kan bura uban can……………..
Hhhhhh kome ta gani ga Zeenobia ga Malik…..
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
*Idan na samu lokaci zan karo page 1 zuwa dare! In sha Allah*
[01/09, 1:17 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI….20
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
*Wannan shafin na ku ne, Aunty Halima da Habibay ku more!*
<<<<<<<|=|>>>>>>>>>
Wato dukkan hankalinta ta daura akan shi, har ya fito falon baki ɗaya. *Wheelchair!* Ta furta a kasar zuciyarta. Dauke kai tayi tana dariya ƙasa ƙasa, d’ago idanu yayi ya zuba mata. Sake kallonshi tayi ta kunshe dariyarta, baki daya sai yaji ya muzanta. Jikinshi ya wani irin sanyi. “Ke meye haka?” Dake bata iya boye abin da yake ranta ba ta ce mishi.
“Malik Menk Jordan! Ya kare akan keken guragu. Wai dama wannan shi ne dalilin da yasa shi nisanta kanshi da Al’umma?” Ta kuma kwashewa da dariya, sannan ta dan durkusa akan gwiwarta kamshin turaren Imperial Majesty ya daki hancinta. Sau daya ta tab’a jin kamshin nan, a rayuwarta sai yaui. “Ko a yaya nake bana kunyar haduwa da mutane, sannan maganar pmutane bata gabana. Ni mutum ce me ra’ayin kaina. Ban zo nan domin Kasuwancinmu ba, nazo na ga waye ya firgita mutane da Gwamnatin kasa baƙi daya.
Ka ji da kyau, bana tsoron tunkarar kowacce matsala, amma a karon farko na rayuwata da na ga makirkirin matsala ya koma gefe yana gudun matsala, shi yasa na mishi dariya. Da nasan cewa Malik Menk Jordan ya gudu daga cikin al’umma saboda nakasarshi da ban tako nan ba!”
A karon farko da yaga macen da ta saka shi ya ji ashe, shi in matsoraci h ne. Ashe tsoro ne ya saka shi boye kanshi. Kasa magana yayi ya kalli Elbashir. “Coffee take bukata ko Tea?” Wani dariyar takaici ne ya kamata, wato shi a haka har wani izza ce da shi. Haka kawai zuciya ta ingizata ta kai mishi naushi. Kafin ta idda nufinta, ya ja kekenshi. Sai da ta fadi can.
“Ke baki da hankali ne?” Elbashir ya fisgota zai kifa mata mari.
“Kyaleta mana, bakuwar mu ce tana buƙatar karramawa ko wacce iri ne!” Gyada kai yayi. Fita yayi kallon Malik tayi yana tafiya a keken shi har gaban wani table. Zaman shi ya gyara yana kallonta. Nuna mata kujeran da yake facing ɗinshi yayi.
Hadiye yawu tayi tana me zama dakyau ta ce mishi. “Da gurgunta kake niman maza?” D’ago kai yayi ya kalleta, kasa tayi da kanta tana wasa da file din hannunta. Kwarjini ya mata lokaci guda, yadda ya kura mata idanu, tana jin ba dadi domin tsakani da Allah idanunshi na da kaifi. “Me kake so?” Ta tambaye shi muryanta a shake. Murmushi yayi yana me juya kekenshi. Shigowa aka yi da tiren tea. Elbashir yana biye dasu, duk maza ne kuma matasa.
Ajiye a gabanta suka yi, Elbashir ya koma gefenshi ya tsaya a gefenshi. “Sha!” Ya fada a sassanyayye. “Ba na shan ruwa ko wani abu a inda ban yarda dasu ba!” Murmushi yayi ya ce mata. ” “Sugar nawa kike so.?” “Guda bakwai!” “Bakya tsoron ciwon sugar ne?”
“Waye ya damu idan na mutu? Don haka zanji dadina kafin na mutu.” Duk da tarin yarintar da ya hango a tattare da ita, amma kuma ya fahimci tana fadar duk abin da ya fito daga zuciyarta ne. Sai da ya zuba mata sugar hudu, ya juya kafin ya d’an diba a cokali ya sha kaɗan, ya tura mata. Da wutsiyar ido ta kalle shi ta ce mishi. “Duk da haka ba zai saka na sha ba “”Ok” ya kai spoon zai diba Elbashir ya ce mishi. “Malik ka manta baka shan sugar!”. Juyawa yayi ya kalli Elbashir ya ce mishi. “Kai haba dole mu karrama bakuwar mu”
Sai da ya sha sau uku kafin ya tura mata har da cookie ɗin. A hankali ta dauka tana kallon coffee ɗin. Kurba tayi a hankali, “Idan kuma da mun saka, guba fa?” “Tunda ya sha ai zamu mutu tare ne!”
Murmushi Malik yayi yana kallon ɗan bakinta yayi, yana girmama maganar da yake fitowa sam babu mara ma’ana sai dai rashin da’a. Ajiye kofin tayi tana faɗin. “Ya ishe ni” “Muje ji ga gidan!” “Tab! Ba ji ya kawo ni ba.” Ta mika shi file ɗin. “Da dai kin tashi kunje!” A fusace ta kalli Elbashir.
“Ban zuwa wani abu ne?” Ta tambaye shi, “ko daya”
“Ok Ina file ɗin!” Mika mishi tayi ya dauki medical glass ya saka sannan ta ce mata. “Su mutanen da suka baki aikin me yasa basu, bawa Yaransu ko su kansu ba?”
Shiru tayi tana kallon shi, sam bai yi kama da wanda yake dogon magana ba, amma yadda yake magana. Yana kara saka mata mamakinshi.
“A Kasuwancinmu, cinikin rai yafi kome armashi da me zaki biya asarar da aka min?”
Kallon shi tayi, sannan ta ce mishi, “Na sani rayuwa ita ce fansar, tsinannen dukiyarka”
“Ke ki iya kalamanki!” D’aga hannu yayi alamar Elbashir yayi shiru. “Hmm! Ina jinki.” Ganin babu ɓacin rai ko muzanci a kan fuskarshi yasa ta sake wani lalacin murmushi ta ce. “Ba fa ni ce ba fada ba, abin da naji mutane na fada ne, me yasa ba acin dukiyarka?”
“Saboda gumina ne, babu gumin kowa a cikinshi.”
“Kana cire hakkin Allah kuwa a cikin gumin naka?” Rintsa idanu yayi ya ce mata. “Bana cirewa ko zaki cire min ne?”. Kallon shi tayi sannan ta ce mishi. “me yasa kake jin haushi?” Nuna kanshi yayi sannan ya ce mata. “Bana jin haushin!” “Kana jin haushi mana, kokarin boye fushin zuciyarka kake, amma kafi wancan sikagon fusata!” Ta kalli Elbashir.
Matse hannunshi yayi sannan ya ce mata. “bana jin haushi, baki gani ba ne!”
“Kana jin haushi tunda gashi kamar zaka karya kashin hannunka, Malik” ta kira sunanshi a hankali, ta fuskance shi. “Kasan me? Nayi abubuwa dayawa a rayuwata, kama manyan laifuka zuwa kananu. Amma na iya saita kaina, kai kuma tunda nazo naga fushi da ɓacin rai a kan idanunka, idan baka manta ba kasan dalilin da yasa na kai maka duka? Domin na kara yarda da cewa kana cikin fushi ne, and saka hannu zan tafi”
Ya kai tsawon shekaru sha uku a wurin zaune, amma babu me zarrar gaya mishi magana ko wacce iri sai an sunkuyar da kai amma yarinyar da yasan da yayi aure da wuri da ya haifi wadanda suka haife ta , take gaya mishi magana son ranta.
“Saka min hannu?” Shiru yayi yana nazarin abun da ta fada, a fusace yake? Yes a fusace yake na tsawon shekaru arba’in yana cikin fushi da fushin wani. Amma kuma me yasa yarinyar ta zo har niman shi? Shin Ishara ce tazo ta mishi ko kuma tazo ganin sirrin shi ne ta gaywa duniya.
Kamar ta san me yake tunani ta ce mishi.
“Ka da ka damu, ban tab’a tsurku ba, sannan ban iya saran kowa ba, bana yin ka domin na fallasa asirinka, bana zama da kai domin dukiyarka, abu daya na sani idan kayi min halacci, zan maka biyayya kamar kare amma ba zan dauki cin mutunci ba, domin ina da saurin hannu. Abu daya nake son na gaya maka, a matsayinka na Mayor mai gari, ina son ka fito cikin al’umma ka, su san waye shugabansu ba ka zauna a tsibiri kamar wani namun daji ba.”
“Hmm! Kin ga?” Tab’e baki tayi tana faɗin. “Yo kwana zan yi ina surutu? Saka min hannun?”
“Zan saka hannu amma da sharadi!” Tsam tayi da ranta, kafin ta ce mishi. “Hmm! Bayan ka saka hannun kenan sharadin zai biyo baya, amma yanzu ratab’a kawai.”
“Ki tsaya ki shi sharadina!”
“Ina fa, kawai saka min sai ka faɗa min!”
“Kamfanin da zan saka miki hannu akai, basu da.”
“Wannan daga baya zan ji da shi, saka min hannu!”
“Mutanen da suka turo ki.”
“Malik Menk Jordan!” Tun daga tsakiyar kanshi ya ji sunan har sai da yaji tafin kafarshi tana kaikayi.
“”Please saka min hannun.” Kura mata idanu yayi ya ce mata.
“Me yasa ba.”
Dan mikewa tayi ta zago bayanshi, ta dan rankwafa kadan daidai kunnenshi.
“Ka saka min hannu, duk wani abin da zai faru. Zan magance shi bana son jan rai ina da wutar ciki.!”
Yadda take maganar daidai kunnen shi ya haifar mishi da mutuwar jiki.
Pen din hannun shi ne ya fara kokarin fadi, Elbashir ya fisgo ta, tare da dawo da ita kan kujeranta.
“Ke wacce irin mutum ce?” Murgud’a mishi baki tayi, ta ce mishi..
“Dan bakinciki ina ruwanka da mu? Koma meye matsalarka da mu? Yau naga hassada. Gaskiya Uncle Malik ka gaya mishi ya daina saka min idanu.”
“Elbashir!”
“Na’am Ubangidana!”
“A kiyayye!”
“An gama”
“Haka ya miki?!”
“Dama-dama, dan sarki akan jaki.”
“Kamfaninku tana da license?”
“Wai duk akan saka hannun kake wannan bididdigin?” Ta fada tana kokarin kwashe file din, tunda ya kasa saka mata hannu.
Rike file din yayi ya ce mata, “zan baki cheque, ki tafi ki kwashe duk yawan abin da kike so, amma ki sani da shar”Ka cinye sharadinka, na fasa.”
“Gashi nan ki saka iya adadin kudin da kuke so.”
“Kace na saka iya adadin kudin da ya mike?”
“Yes!”
“Ko ba Yes ba!” Ta karbi takardan cheque, sannan ya juya banki daya suke.”
“Golden bank?”
“Kin san banki ne?”
“Eh anan nake ajiye kudina!”
Yadda suke jira zaka dauka sun shekara guda da sanin juna, hiran ba wai na arzikn bane, saka iya adadin kudin da suke bukata tayi, ta mika mishi. Kallon kudin yayi sannan yayi sign.. “ka duba yayi ko?”
“Eh Malik na saka a cikin littafin amsar Cinikin rai ne?”
“A’a” ya fada yana sign a jikin file din da ta zo da shi.
“Me kike so yanzu?”
Mikewa tayi tana murmushi, “me kuwa zan bukata, bayan wanda na samu? Kawai na gama sai an fara juya kome.”
“Idan wani abu ya samu dukiyata, sai kin biya.”
“Idan ban biya ba, a rataye ni. Kuma ka gayawa Awakin da suka kawo ni ahir
dinsu, a kuma rufe min fuska idan ba haka ba, hukumar kare hakkin dan Adam zata shiga tsakanin mu.”
Karfin halinta kawai suke gani, “eyeee haka kuke barin abokin cinikayyar ku, ya tafi shi daya babu dan rakiya?” Kallon juna suka yi. “Ke dalla tafi can, tunda Malik ya dawo nan bai.”
“Muje a rakata ai bakuwar mu ce!”
“Tow Malik!” Inji Elbashir, wani gatsina fuska tayi ta ce. “Kai wallahi baka da hali, wato aikin kwarai ba zaka saka shi yayi ba, kana nan a bayan shi kamar bindi. Wallahi ka ji tsoron Allah, ka daina hana shi aikin alkhairi ba halin musulmin kwarai ba ne.”
Haka suka rakota har waje. Kallon Malik tayi ta ce mishi. “Turarenka yana min kama da kamar mun tab’a haduwa, a wani wurin but i can say ga inda muka hadu ba.” Ta fada tana kallon security na cikin gidan baki daya. “Kana kula da rayuwarka sosai.” Ta dan dukka kaɗan. “Kamar yadda kake kula da dukiyarka, da kuma.” Kasa jan numfashi yayi, domin abin da yake mugun gudu kusanci. Baya yayi da keken shi ya ce mata.”ki kula da rayuwarki da mutanen da suke zagaye dake!” Sake baki tayi sannan ta d’aga kafad’arta ta cigaba da tafiya.
“Malik me yasa ka amince ka saka hannu, bayan kasan ita kanta ba ra’ayin kanta ba ne?”
“Babu kome, domin ko na maka bayani ba zaka gane ba ne!”
“Zan gane mana, ka min bayani yadda zan fahimta. Mutanen mu suna ta bibiyar alamarinka zaku gana, kaki amma ita lokaci daya ka bata damar ku gana!”
“Hmmm! Zak fahimci dalilin sai nan da yan lokaci ƙalilan.”
Daga haka ya juya da kekenshi. *Gudu kai saboda nakasarka?*
“Elbashir yarinyar nan tayi gaskiya, a gyara min gidana na whiter town!”
“Malik tunda nake da kai, tsawon shekaru arba’in baka tab’a canza maganar ka ba, yau kai kace cewa zaka koma whiter town?”
“Na yanke shawarar haka, a maida ni whiter town!”
★★★
Kamar yadda suka daukota haka suka mai da ita, bata zame ko ina ba sai kamfanin Amjad.
“Ajiye mishi tayi a gabanshi.”
“Gashi nan na samo kome!”
Kallon cheque din yayi, ya ce mata.
“Are you sure kin ga Malik?”
“Kai baka.tab’a ganin shi ba ne?”
“Ko hoton shi kuwa ban tab’a gani ba!”. .”tow gashi nan, zan tafi gida.”
“”Da wuri haka?”
“Eh ta saka kai zata fita!”
“Zeenobia na gode sosai!”
“”Ba kome”
Ta fada tana me barin Office ɗin, ko minti biyar bata yi da barin kamfanin ba, MD da Salim suka shiga kamfanin aka shiga kwashe kome, kafin karfe shida na yamma sun kwashe kome sun sallami ma’aikata.
Karfe tara na dare, ginin kamfanin ya ruguje ya zube kamar ba a tab’a ginin shi a tsaye ba…..
*Zan kara muku page daya ya zama last free page in sha Allah idan na gama book one, book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[01/09, 9:04 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI….21
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
Last free page
BOOK ONE
<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>
Shigowar Elbashir falon yana zaune a saman sofa, ya mike kafaffun shi yana kallon network news Elbashir ya ajiye mishi tap din a gabanshi.
“Malik sun gudu daga zarrar kuɗin!” Grape ya dauka daya ya saka a bakinshi hankalin shi yana kan tv ya ce mishi.
“Ita yarinyar ta sani?”
“Da alamu bata sani ba!”
“Rigimar shekaru arba’in ne ya dawo sabo fil.” Ya fada hankalinshi yana kan tv.
“Amma kamar babu ruwan, Khuldu Jahid Khan!”
“Da hannun shi mana!”
Ya d’ago kai yana kallon Elbashir, “ko kai ne ai zaka yi abin da ya fi haka.”
“Subhanalillahi, Allah ya min tsari da cin amanarka Malik gara naga mutuwata.”
“Hmm!”
Shiru suka yi, kafin ya sake murmushi yana faɗin.
“Yanzu ya zamu yi? Domin dai kasan kudina ba zai sha ruwa ba.”
“Duk yadda kace Malik haka zamu yi, domin nasan basu bar kasar nan ba. Idan kuma sun bar kasar tow ko suna teku ko suna bakin borda.”
Murmusawa yayi ya ce mishi.
“Yarinyar nan ta ce, wai ina fusace!”
“Sharrin kuruciya ce, baka fusace!”
“Nuratu ma ta gaya min shekaru goma sha takwas baya, ta ce ina fusace amma yanayina a sanyayye yake.”
“Allah ya mata rahama, kasan saura kwana biyu Birthday din yan biyu?” “Na sani!”
“Ka gayyato min yarinyar nan!”
“An gama Malik!”
“An gama kintsa min whiter town?”
“An gama Malik domin kome na cikin gidan sabo ne, idan baka manta ba kome da muka bari babu abin da ya samar.”
“Ina son gobe Keivroto tayi sabon bakon, a gyara min gashin kaina, ina son furfuran nan su fito da kyau, fuskata ta tara kasumba a gyara min ita, ta fito shar na dan samari. Domin bayan sallah Azhar nake son na dira a cikin birnin! Domin na nuna mata ni ba matsoraci ba ne!”
“Allah ya kiya shemu aikin danasani kai ba matsoraci ba ne, tsoro da kanta gudunka take!”
“Hmmm! Me ya bawa yarinyar nan kwarin gwiwa, ta gasa min bakar magana haka?”
“Haka take Malik, bata da kunya da d’a’a.”
Jinjina kai yayi yana faɗin. “Tabbas ba ga haka, naga wannan rashin da’a a cikin Idanunta. Zainabia!”
Girgiza kai yayi sannan ya ce mishi.
“Su shatima su same ni, a whiter town!”
“An gama Malik!”
Sannan ya fita, can sai gashi tare da wani saurayi, ya zo da wani akwati ya fara fidda kayan aikin, sai da ya fara mishi gyaran fuska, sannan ya rage mishi gashin kanshi. Malik baki ne asalin bahaushe wanda jinin hausawa ko nace kanawa yake gudu a jikinshi, sai dai ya biyo siffar Mahaifiyarshi dogo ne, me matsakaicin jiki.
Fuskar shi doguwa ce, wacce ta badawa hancinshi damar bajewa. Domin bai da siririn hanci, hancin a baje take yana da kakkaura leb’a. Ƙwayar idanun shi sak take da ta zakuna, kasancewar uwarshi baturiya ce, Malik yana da fadin kirji, sannan a murde yake sosai, domin ko ba a gaya maka ba, kasan yana cin karfe.
Dan kimanin shekaru hamsin da bakwai, yana da yawan suma sannan a tsaye yake kamar Superman ko Ironman.
Idanunshi manyan ne, wani lokaci da iya su yake barazana, Malik yana da zafi wanda matukar baka kasanshi ba, zaka zata irin mutanen nan ne masu sanyin hali.
Nan kuwa babban mugu ne me shegen bakin halin tsiya. Wani abun dariya shi baya boye furfuran shi.
★★★
Tun da ta koma gida, Shatima ya addabi rayuwarta da waya. Karshe turo mata text yayi.
*Ki dauki kirana!*
“Wannan tsohon da naci yake, da talauci ne da an shiga uku da shi!”
Ɗaukr kiran tayi, ta ce mishi.
“Meye zan maka?”
“Baby gani a kofar gidanku!”
“Eyeeee! Kace?”
T
“Eh gani a bakin get din Al’umma Charity House!”
Ware jdanu tayi ta ce mishi.
“Gani nan tow”
Ta fada a sanyayye, domin bata san da gaske zai zo ba, ta shi tayi ta nufi drower ɗinta, abaya ta ciro tana sakawa akan Bom short dinta, ta fito waje yana tsaye a jikin motar.
“Wai ba na gaya maka gaskiya ba, Ni fa ba zan auri tsoho ba. Gaskiya ni ko dating tsoho ba zan yi ba.”
“Ni kuma gani a gabanki, nazo da nufin soyayyarki.”
Dauke kai tayi kamar ta sake kuka, ta ce mishi.
“Ni gaskiya ka tafi ka da mutane su dauka.”
“Muje na saya miki ice cream!”
Kallon.shi tayi sannan ta ce mishi.
“Ai ni Allah bai daura min kwadayin abin hannu maza ba, jeka na gode.”
Duk yadda yaso yarinyar nan ta bashi hadin kai, fir taki har da koranshi ma tayi, da zai tafi ne, ya riko hannunta. Ya cusa mata kudi me yawan gaske. “Ki sha ice cream!”
Sannan ya bude motar ya shiga, ya ce mata.
*Ina sonki!”
Kallon kudin tayi a ranta ta ce mishi.
“Bana sonka”
Sai da ya bar gidan, sannan ta wuce dakin Inna da kawayenta, ta mika musu kuɗin.
“Ke yar nan! Ina kika samu kudi haka?”
“Wani tsohon najadu ne wai yana sona, ya kai shekaru sittin fa!” Ta ajiye musu tana faɗin. “gashi kuci goro.”
Daga haka ta bar dakin, sai Albarka sukae saka mata.
—–
Tun karfe hudu na asuba, office din yan sanda ya cika makil da yan kai kara, kan Asp kamar zai fashe domin tun kiran sallah farko, aka kira ta haka suka yi ta shigar da korafin akan Kamfanin Digital art, abin mamaki dayawansu Zeenobia ta kirawo su.
“Yanzu me kuke so na muku?”
“So muke a kama ta, ta fitar mana da kudin mu!”
“Ok sai ku bari gari ya waye!”
——–
09:30*
Na safe, watsa mata ruwa aka yi ta ware idanun cikin gajiya da son yin barci.
“Tashi ki bamu kudin mutane?”
Tashi tayi zubur, tana kallon Sajan Barau.
“Kudi wani iri?Ba yana kamfani ba”
“Idan kin tafi Office din CID zaku musu bayani!”
Zubur ta mike hango Asp Zulfa tsaye da wasu mata yan sanda.
“Kan Uba nice za ayiwa wannan rashin mutuncin!”
“Ku fita na sauya kaya!”
Ban daki ta shiga ta wanke fuskarta, sannan ta fito waje, bata tab’a sanin al’amarin ya wuce haka ba, sai da ta m dauki abayarta ta saka.
Sannan ta bi bayansu, haka suka sakata a motar yan sanda, suka tafi da ita. Har Office dinsu. “Ita ce…. Ita ce…. Ki bamu kudin mu!”
Kai tsaye office din Zulfa aka wuce da ita. Zama tayi tana dauke kai. “Meye hadaki da mutanen can?” “Na tuna su, amma ai kudinsu yana kamfanin S….. Digital art.”
“Ya zaki ji idan aka ce miki, ba kamfani ba ne. Yan damfara ne?”
“Kai haba, haka ma ba zai yiwu ba. Domin ni nasan inda Mr Amjad ne ba zai damfare ni ba ”
“Amjad Fahad Albagwi! Damfara a jinin su take, ya zaki confront mutane akan kudinsu? ”
“Kina nufin dama Amjad dan 419 ne? Lallai ma duk inda yake sai na zakulo shi wallahi!”
Kura mata idanu Zulfa tayi ta kira Sajan Barau, ta ce mishi. “Kaita filin nan”
Haka kuwa aka yi ya tisa keyarta da tare wasu yan sanda.
Latsa wayar Zulfa tayi, tana jan hancinta ta saka a kunne tana faɗin. “Yasir tarihi ya maimaita kansa. Abun da ya faru shekaru goma sha ya kuma faruwa da Babysister.”
Ta fada tana share hawayen da yake zubo mata. “My lady, ki bar kuka ba zasu ci banza ba, In sha Allah zasu shiga hannu. Basu san wannan karon sun tab’o kusar yakin ba ne, har yanzu bata gane ki ba?”
Hawaye ne sharrrrr ya zubo mata ta ce .
“”She lose her memory.”
“God! Yanzu ki kula da ita, wasu zasu iya bibiyar rayuwarta.”
“Ok Yasir”
“Love you!” Kashe wayar tayi, tausayin Zeenobia yana kara cika zuciyarta. Mikewa tayi ta wanke fuskarta, can suka dawo.
Idanunta ya kad’ a jajjur.
Zulfa ta ce musu.
“Sajan watsa min ita cell, dama ka mara jin magana kenan!”
“Ke yar sanda, kome lalacewar gawar Giwa tafi ƙarfin Allah sarki. Kuma baki san waye ya tsaya min ba a garin nan zaku sha mamaki!”
Tura keyarta aka yi cell din, kamar ta fasa ihu.
Har karfe daya na rana, ana rikici kuma abu yaki ci yaƙi cinyewa, don haka suka fara shirin kaita kotu. Sannan da gayya Zulfa ta hana belinta.
★★★
_A yau dai jami’an tsaron yan sanda, na garin Keivroto city sun kama daya daga cikin yan damfarar da suka damfari mutane kudi masu yawan gaske. Daga cikin su akwai yar kunama, yar daban da ta addabi rayuwar al’umma. Ita ce wacce ake zargin da janyo mutane cikin al’amarin._
Labarin da ya karakad’e ko ina, kenan labarin abin da ya faru. Shatima yana gidan Malik da ya iso tun karfe biyu, shi kuma ya isa gidan tun karfe hudu.
“Ikon Allah, yarinyar nan babu ruwanta.”
“Ai har da kudin Malik aka gudu da shi. Kuma munafuka ita ta zo da kanta!”
“Elbashir ka yi belinta!”
“”Malik!”.”kayi yadda nace!”
“Kudin da suka tafi da shi fa?”
“Kwandilata idan suka tafi da ita zasu dawo min da hakkina.”
“Malik ya zamu yi da ita a kawo ta nan!” Murmushi yayi ya ce mishi.
“Yanzu tana cikin alhinin abun da ya faru, ka bari a kwana biyu muga.”
Hankalin Shatima yayi masifar tashi, da sauri ya mike yana faɗin. “Malik zan dan fita, zan dawo an jima.” “Ok!” Elbashir ya ce mishi.
Da idanu suka bishi, kafin suka cigaba da abin da suke. Bai yarda ya tafi Office din yan sanda ba, sai da ya koma gida ne yayi ta Safa da Marwa dama dalilin Malik yasa taki yarda da shi, tow yaushe suka san juna?
★
Elbashir kuwa Office din yan sanda ya tafi sa lawyer din Malik, shi yayi magana da Zulfa. Sannan suka bada belinta gida suka tawo da ita.
“Zuwa nan da jibi Malik zai so ganawa dake!”
Bata iya magana ba, ta wuce abinta.
Koda ta shiga cikin gidan ruwa ta sakarwa kanta, haka kawai take jin ɓacin rai kamar zata yi hauka.
Haka aka yi ya zuwa mata Jajje, har ta kwanta, washi gari Shatima ya zo. Kamar ba zata fita ba, ta fito tana me sunkuyar da kanta. “Ban ji dadin abin da ya faru ba?”
“Ban san damfarar mutane zasu yi ba?”
“Mene ne alaƙarki da Malik?”
Kallon rashin fahimta tayi mishi.
“Ban gane ba?”
“Wacce alaƙa ce tsakaninki da shi?”
“Babu kome, sai akan kudin da ya saka hannun jarin.” Ta mishi bayanin abin da ya faru, shiru yayi yana kallonta. Amma kuma ta wani ɓangaren ta matukar burge shi, idan har ta iya yaudarar Malik haka, tow kuwa hanya me sauki ne ya yi amfani da ita.
“Ok zan tafi! Idan da wata matsala ki gaya min kafin a san abin yi” girgiza kai tayi tana faɗin. “Babu matsalar kome ”
Daga haka suka yi sallama,
Kwana biyu Zeeno ko kofar dakinta bata taka ba, sai washi gari ranar da zata hadu da Malik..
Kamar wacce ruwa ya mata duka, haka ta tashi, ta shirya wurin karfe biyu na yamma aka zo daukarta. Ta nufi motar aka nufi gidan Malik da ita.
A tunanin ta Waterfall zai kaita, sai aka yi rashin dace. Whiter town.
A lokacin da suka shiga cikin gidan, sai da ta rena kanta. A hankali suka yi ta ratsa get zuwa get kafin suka tsaya a wani katafaren apartment, fitowa tayi a sanyayye ta nufi cikin gidan, bisa jagorancin driven da ya kawota.
Malik yana zaune a falon tare da Elbashir, sai Shatima. Zama tayi tana me dauke kanta. “Sannunki sarauniya Zeenobia.” Inji Elbashir.
Bata tanka mishi ba, mikewa suka yi tare da barin falon daga ita sai Malik, aka shiga jero mata abincin.
“Sai kuma naji abin da ya faru!” Ruwa ta kurba tana faɗin. “Eh kasan dukiyarka bata da albarka.”
“Kada ayiwa dukiyata sharri dama, ai ba yau aka fara ba!”
“Kai ma kasan su ne?”
Murmusawa yayi sannan ya ce mata.
“Kici abinci, nasan har yau baki ci abinci ba.”
Murmushi tayi tace.
“Ina azumi!”
“Ok!”
Falon yayi shiru, kafin ya ce mata.
“Tun ranar da abin ya faru naso gaya miki sharadina! Amma kika ki tsayawa!”
Kura mata ido yayi yaga yadda fuskarta yayi, murmushi yayi sannan ya ce mata.
“Kin shirya amsar sharadina, ko kina da hanyar da zaki biya Ni kudina da na mutane?”
Kura mishi idanu tayi, ido cikin ido ta ce mishi.
“”Bani da hanyar da xan biya!”
Murmushi yayi sannan ya ce mata.
“”Zan biya mutane kudinsu nan da kwana uku, nasan shine damuwarki ko?”
Lumshe idanunta tayi ya bude, sunyi jajjur.
“Mene ne sharadinka?”
“Zamu yi cantract marriage na kudina!”
Mikewa tayi zubur kamar an jona mata wuta ……. Dandan-dandan……
Kashi a nan na gama book 1 free page…
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*