Sponsored Links
Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 41-42

Sponsored Links

Page 🖤 41••42🖤

 

Sanyin harshe taji yana bin fatar jikinta,tana farkawa taga Jabeer ne yake lasar ƙafarta tamkar kare.
Zabura tayi da zauna,da sauri ya matso inda take,jikinsa har rawa yake.
“Lubnah lafiya naga kin tashi a razane,mai yasameki ki faÉ—amin koma menene.
Na haÉ—a miki ruwan wanka da kuma abinci,kayan ki ma na zabomiki wanda zai yimiki daÉ—in sakawa yanzu,bayan haka kuma mai kikeso uhm”
Wani murmushin jin daÉ—i tayi tareda jawoshi jikinta.
“Finally ka dawo gareni bayan tsawon lokaci,wannan karon kazo kenan bazan taba bari ka koma garesu ba”
“Dama ba inda naje nina nakine ke kaÉ—ai,yanzu ma idan kinaso saina sallamesu dukka”
“Ahah kabarsu su É—anayimin bauta na É—an lokaci,koya kace toh?”
“Duk yadda kikace haka za’ayi”
Cike da taƙama da farinciki lubnah tasaka Jabeer ya ɗauketa zuwa banɗaki,bayan sun fito yasaka mata kaya,yasake ɗaukarta zuwa dining.
Bayan sun gama cin abinci ma a falo suna zauna yana yimata tausa ta hakimce akan kujera.
Waya ta ɗauka taƙira Mahaifiyarta,tun kafin tace wani abu lubnah tafara magana.
“Mommyyyyy!!!! Aiki yaci fiyeda yanda kike zato,yanzu komai yana hannuna sai yanda nayi dashi mommy,wooww dama haka kikeji da kike mulkar abbah,gaskiya da daÉ—i.
“Eh da daÉ—i amma saikiyi taka tsantsan,kin tuna sharaÉ—in da kukayi da Matsafiya Zilliyyah kafin ta yarda da turomiki masuyin aikin koh.
Jinin kuliyar da kika basu shikaÉ—ai bai isa ba,lafiyar ki na hannunsu,Æ™aramin kuskure zakiyi shikenan komai zai lalace.”
“Nasani mommy i will take care,yanzu dai ya batun kuma shirin mu nagaba”
“Ahhh daga farawa,ki murji wanann lokacin da wannan damar tukunna,komai zaizo daga baya”
Ajiye wayar tayi ta kwanta Jabeer yacigaba dayimata tausa.

Kwana guda kwana biyu babu wanda yaga Jabeer ya fito daga É—akin lubnah,tun abin baya damunsu har yazo kowa abin ya dameshi.
Babu ya hajiya Zeenah da kuma su Jaleelah.
Inda babu motarsa sai a yi zaton ya yi tafiyane,amma motarsa tana nan babu abinda yasameta.
Maleekah ce tashigo sashen bombee cikeda da damuwa.
“Anty maryam kema bakiga yah Jabeer É—in ba”
“Naganshi mana,amma nima jiya na ganshi naje sashensa”
“Amma lafiyarsa kalau kuwa,mai yake a sashen anty lubnah to har yanzu,ga nan Mommah ta gagara haÆ™uri ta nufi sashennasa,yanzu ma tace na faÉ—amiki ku sameta a can É—in,dan tun É—azu take buga Æ™ofar ba’a buÉ—e ba”
“Ahh menene na abin damuwa kuma,mallakeshi akayi sannan aka hanashi fitowa,domin jiyan ma haÉ—uwa nayi dashi ya É—auki takardun Companyn sa zaikai mata”
“Whattt……kuma hankalinki yake kwance anty maryam”
“Ohh tashi zayyi nawa hankalin,yaje ina?
Mallakarsa da tayi baya cikin plan É—ina,koyana ciki?”
Takaici ne ma ya ishi maleekah tarasa mai zatace.
“To yanzu anty maryam kina ganin menene mafita,dan Allah ki saka hannunki”
“Ehh akwai mafita idan naga dama,amma kafinni ku nema a wajen Allah,domin babu abinda yagagareshi”
Fita tayi daga falonta da nufi sashen lubnah,badan kiran da akayi mata ba sai dan tanason taga mai zai faru.

Kukan Hajiyah Zeenah suke jiyowa a falon tun kafin su ƙarisa.
Jaleelah da Jawaheer suna tsaye kaman gumakai,ita kuma sarauniyar tana zaune akan kujera ta ɗaro ƙafa ɗaya kan daya,Jabeer na tsugunne a gefenta,daga shi sai gajeran wando da kuma vest,kwana biyu yayi baƙi ya rame kaman bashi ba.
“Honey kace ma wannan tsohuwar ta bani waje na sha iska mana”
TafaÉ—a tana nuna Hajiyah Zeenah,wacce take ta rubzar kuka.
“Uhm Mommah dan allah ki tashi ki tafi sashenki,na faÉ—amiki idan har na gama abinda nake zanzo na ganki in anjima,yanzu zafi takeji tana buÆ™atar iska”
“Wayyo Allah na ni Zeenatu,inda ranka zaka ga komai a wannan duniyar,mai zan gani,É—ana na cikina aka mayarmin shi kaman dabba?”
Bombee ce taja hannun maleekah wacce itama take kukan.
“Ke yanzu ba lokacin kuka bane,kija mahaifiyar ku ki fita da ita daga nan wajen ,in baso kike ku kwana yau a asibiti akan ta ba”
ÆŠaga kai maleekah tayi tareda kama kafaÉ—ar Hajiyah Zeenah, suka fita daga wajen.
“Yawwa ita waccar tsohuwar ta karbi nata lesson É—in,shima ya karbi nasa nayimin bauta saboda auroku,sauran kuma kuma naku horon na shigomin gida da kukayi..
Bazan saka yasakeku ba,zanso ku baza ido ku kalli yanda zan zuba mulkina a gidannan,ku naku aikin shine bauta,ku tashi ku bani waje.
Idan anjima zan koma sashen honey da zama,É—aya zata dunga yimin wanke wanke,É—aya abinci,É—aya kuma wanki.
Duk wacce taga bazatayi ba toga hanya nan zatayi waje a lokacin.
Ku bace ku bani waje.
Dukkansu su Jaleelah da Jawaheer barin falon sukayi,suna ganin yanda akayi da wanda suke zaune danshi,inaga kuma su karan kaÉ—a miyah.
Saidai kowaccensu da abinda yake ranta.
Bayan sun bar wajen saura bombee a tsaye kawai tana kallon Jabeer,wanda yagagara haÉ—a ido da ita,
Hannu tasaka a aljihun bujen wandonta,tareda jero feɗuwa mai ƙara.
“Weldone tun zuwana gidannan naga wani abu very interesting.
Karki damu kanki Lubnah da son taming É—ina da magani kokuma burga nayi miki abinda kikeso.
Ita kanta shugabar taku wato Zilliyyah,tun bansan kaina ba ta sakamin igiya a wuyah,saidai tana girma wuyannawa sai yayi kauri har ya É—ashe igiyar.
Kaman yanda nake faÉ—amiki har yanzu bakisan koni wacece ba,sannan mallakar shi wannan da kika baya cikin Plan É—ina.
Kicigaba da mulkinki a tsakanin matansa,ko babu magani a jikinsa ma bazai sameni ba bare yanada shi.
Inna gama aikin soon ma zan iya barin garin,dan haka kiyi harkar gabanki,batun abinci kuma da kike kallona na girka wai na girka miki,bazanyi ba,amma bansaniba komai magani kikeso na girka miki irin wanda ake yiwa beraye?”
Cigaba da feÉ—uwarta tayi zata fice,har tazo hanyar waje tasake dawowa.
“Amm lubbyyyy ki zama cikin shiri,wannan karon kinyi babban moving,wani karon Salon nawa ne,Æ™wallota ce zata zura a raga,ki sha sha’aninki zan miki talala”

*** ***

Maleekah tana kuka tashiga sashen sayyada-tateen bayan ta raka Hajiyah Zeenah É—akinta ta kwantar mata da hankali.
“Iyahh wlh wannan matar yah Jabeer É—in bazata taba ganin rahama ba inshaallah”
“Wacce ina wannan mai É—an shegen,dama menene da arziÆ™i a wajenta,matar da cimmana mutunci,nidama na fita harkarsu ne naga iya ina zasu tsaya”
“Kai iya ba wannan ba ni,waccar lubnah mana mai zubin kafirai,tun shakaranjiya ake neman Yah Jabeer ashe yana can sashenta ta maidashi kamar kare,banda aiki dare da rana babu abinda yake”
Saurin ajiye kofin kunun tsamiyar da take sha tayi,tareda zaro ido.
“Ke mekikace Æ´ar nan,mallaka tayi masa”
“Ai Æ™azama ma iya sayyada”
“Muje ki kaini naga shi jabeerun,ko tofi ai sai ayimasa”
“Hmmm tofi koh,kina zuwa zata sakashi yayi waje dake,haka zai kalli tsabar idonki yace fitah!!!!”
Maleekah taƙarisa da ƙarfi cikin bacin rai,aikuwa sayyada-tateen tana jin haka idonta yayi ƙififi.
“Haka abin yazama,maxa É—akkomin to mayafina ki rakani gidan malam Audu wali,nasan bazai rasa taimakon dazai bamu ba.
Yi sauri maza maza”
Jiki na rawa maleekah ta É—akko mata mayafin suka shiga mota driver yajasu,har sannan bata daina jan majina ba.

*** ***
“Abban haneef wlh da gaske nake,yanzu nakeji a wajen mai aikina wai Lubnah ta mallake Jabeer,sai yanda tace yakeyi,hatta Æ™ofar gida bai isa fitowa ba saida izininta.
Koda wannen malami tayi aiki mai Æ™arfin wannan oho?”
“Ohh kema kiji waye kiyimin koh?”
Alhj Abdullahi ya faÉ—a jikinsa a É—an kware.
“Haba nayi maka irin wanann asirin,baka yarda dani ba haka?”
“Uhm da yarda nayi dake,kema ai sai a hankali”
“Yaushe kikaji wanann zancen ma tukunna”
“Yanzunnan aka faÉ—amin,wai Hajiyah Zeenah ma data je sashennnasa da kuka ta dawo.
Baka ganin yanzune lokacin dazamu sake É—ana wani plan É—in?”
“Eh to hakane,amma dan yana Æ™arÆ™ashin ikonta bashi ke saka shikenan bazai Æ™ara zuwa aiki ba,dan aiki dole zaije aiki,saida abinda duk za’ayi a Company kuma sai abinda tace.
Keda kike cewa mu É—ana plan,kin manta hannun da muka haÉ—a da gen abdu manga,ni inaga shima akwai abinda yakeso,gashi Æ™arin takaicin bansan inda takarduna suke ba,idan har aka gano basa hannuna,ko meeting fah bazanje ba kinsan”
“Karka damu za’a nemosu da kadan kaÉ—an a hankali.”
Bayan bombee ta koma É—akinta runtse ido tayi tareda zama jagwab akan kujera.
Ita kadai tasan yarda zuciyarta take ganin halin da Jabeer yake ciki,waye zai hanata É—aiÉ—aita iyalan gen abdu manga ne,sun gama cutarta da kowacce hanya,lokaci take jira dazasu girbi abinda suka shuka.
Tashi tayi kaman an jabureta tayi hanyar waje,É—akin zaleeha ta nufah wacce ta dawo a daren jiyah,saida taje gidanta tayi magani kafin ta dawo..
Saida bombee ta kwanƙwasa bakin ƙofar kafin tazo ta buɗe mata,hadda fitowa da sauri kada taga mai yake ciki,murmushi bombee tayi batareda Zaleeha ta gani ba.
“Inkingama abinda kike,kizo yanzunnan ina jiranki a sashena”
“Hajiyah aiki ne?”
“Eh aikine babba ma kuwa,dan haka kiyi sauri”
“Yawwa Hajiyah nagode fah da asibitin dakika kaini”
“Karki fara min godiya tun yanzu,kizo ina jiranki a falo”
Komawa tayi tasake zama akan kujerar falon tana jiranta,dolene yau taji mai yake going gameda abinda sukayiwa Jabeer,da tace bazata shigaba amma kuma zuciyarta takasa barin abin ya wuce haka nan..
Idonta a rufe tashigo falon har ta samu waje ta tsugunna.
“Gani Hajiyah”
“Naganki,amma da farko zaifi kyau ki daina Æ™irana da wannan Hajiyan,kinsanni wacece kuma nima nasan ke wacece,dan haka babu boye boye a ciki.
Tambaya naƙiraki nayi miki akan wani abu daban,dan haka kada ki batamin lokaci ki gaya min gaskiya.
Wanne irin asiri kika bawa lubnah tayiwa Jabeer?”
Zaro ido zaleeha tayi tana muzurai,saidai a matsayinta na Æ´ar duniyarce, lokaci guda tayi fuskar rashin sanin abinda bombee take faÉ—a.
“Hajiyah bangane……”
“Matsafiyah Zilliyyah tambaya kawai nayi miki fah,bana cikin mood É—in jan magana,saidai idan hakan kike so”
Zumbur zaleeha ta tashi tsaye tareda murtuƙe fuska,girgiza tayi kayan jikinta suka sanja zuwa ainihin nata wanda take bayyana a mafarki da madubi.
“Hmmm dan kingane ni wacece shine me,kina tunanin harkinkai girman dazan faÉ—amiki duk abinda kika tambayeni ne,kema kanki a tafin hannuna kike dama sauran guda biyun,wato uwarki da Æ™anwarki”
Saidai bombee tabari ta gama surutun kafin ta É—an zaune daga kishingiÉ—en da take,idonta da suke lumshe ta buÉ—e tareda yin murmushi.
Hannunta ta ɗaga na dama tayi ƙass dashi..
Take kuwa Zilliyyah ta faɗi ƙasa tana birgima tareda riƙe ƙirjinta,saida ta galabaita kafin bombee tace.
“Turning off my robot”
Nan da nan Zilliyyah taji kaman an zare mata ƙaya a kahon zuci.
Yage rigarta tayi tana kallon inda zafin yafito,saitin zuciyarta tane wajen insa likita yace anciremata tarin jini.
“Taya haka ta faru”
“Me kike tunani Zilliyyah,banda ke daÆ™iÆ™iyace dan kawai kinsan maganin gargajiyah dana aljanu,kuma kina kashe mutane da mummunan aikin ki wasu kuma ki É—aiÉ—aita rayuwarsu,sai aka cemiki baza’a iya É—aiÉ—aita rayuwarki da fasahar zamani ba.
Na’urah nasa aka dasamin akan zuciyarki,wanda baza’a taba iyah cireta ba batareda kin mutu ba,sannan zan iya juyata yanda nakeso kaman yanda kike juya aljanu.
Idan na bada sauti na ƙass to zata hura zafi a jikin zuciyarki,idan kuma na tafah hannu to zata matse zuciyarki har sai ta maidata tamkar Fatar tsohuwa.
Karki kuma kice wai iya nan ne,duk maganar dakike inaji da ita,sannan duk inda kikaje ina gani a wayata da computer ta.
Sannan ba iya nikaÉ—ai nakeda madannan ba harda likitan daya dasamiki dakuma wasu mutane guda biyar suma.
Idan nawa yasamu matsala to duk zasu danna a tare ne,”
Cikin haki da razana Zilliyyah tafara magana daƙyar,har sannan numfashinta sama sama yake fita.
“To koda kin kashe ni kina tunanin zan barki hakane,saina É—aiÉ—ai rayuwarki ne,indan asirin dana yiwa mahaifiyar kine da kuma ke toki sani bazan taba cirewa ba,koda kuwa zaki kasheni ne”
“Ahah dakata tsohuwa,menene na yanke hukunci da wuri haka.
Ai bake zan kashe ba,kinga wanda zan kashe.
Bombee tafaÉ—a tana nuna mata hoton É—anta wanda taboye a kogo a cikin daji.
Abinci yake ci hankalin sa kwance bai sam mai ake ba,gefen fuskarsa a rufe sa farin ƙyalle.
Hannunta ta ɗaga ƙass,bayan da danna wani jan abu dayake hannunta,wanda zayyi connect ɗinta dana jikinsa.
Take kuwa yazefar da kwanon abincin yana fizge fizge kaman mai shirin fitar rai.
Hannun Zilliyyah ta haɗa biyu tana roƙon bombee akan ta dagata,saida taga dama kafin takashe abin.
Shuru yayi a ƙasa hana nishi dayaji abinda yake cinsa a zuciya ya daina.
Ajiye computer bombee tayi tareda maida kallonta ga Zilliyyah,wacce taga tashin hankali da sabon tantiranci muraran a wajen bombee.
“To Zilliyyah kinga dai yanda É—anki yake burburwa koh,idan bakyason nacigaba da gana masa wannan azabar,to dole sai kinyi abinda nakeso.
Maganar farko itace ki tabbatar daga nan zuwa gobe kin warware abinda kikayiwa innata,inada wajen daza’a kaita ayi mata magani,zuwane bazanyi ba saboda bazan asarar Æ™wandala ta ba,yanzu kike É—aura haka zaki kwance shi.
Bayan wannan kuma yanzu kiyimin bayanin komai gameda shirin da lubnah suke itada uwarta”
“Batun shirinsu zan faÉ—amiki dukka,indai zaki rabu da É—ana,saidai asirin dayake kan Innarki idan aka warwareshi to Laari bazata taba warkewa ba daga cutar Æ™urajen da takeyi,sanann kuma makantar da kurmantar dukka zasu koma kanta ne”
“To ina ruwana,idan tanaso ta mutu ma mana nina kasheta,ke nifah mutuwar wani bata dameni ba inshi yajawa kansa,nikaina nakashe ba adadi bare kuma dan wani ya kashe.
Ina saurarenki wanne irin Asiri kika danƙarawa bawan Allah can,kokuma yanzu aradu na baje zuciyar wancan mushen ɗannaki,kema na baje taki.
Abinda kike tsoro na rashin samun magaji ta tabbata yanzu nnan”
Tun kafin ta rufe baki Zilliyyah tafara bayani tiryan tiryan abinda yake faruwa.
“Karfa tayimasa,wacce bata taba karyewa har sai wanda kayiwa ya mutu ko kuma kai ka mutu,karyewarta É—aya sai idan kaika karya dokarta da kanka.
Wata uku da É—auka tana bawa aljanu jinin baÆ™ar kuliyah duk wata,kafin suka yarda sukayi mata aikin,shima kuma saida tasake bada wani abun wanda yakeda muhimmanci a rayuwarta”
“Me tabayar?”
“Lafiyarta tabayar,amma da sharaÉ—in bazamu karba ba harsai tayi wata bata kalli wanda tayiwa ba tukunna,burin mallakar mijinta ne a ranta,shiyasa bata kulada abinda ta É—orawa kanta ba.
Ita kuma mahaifiyarta hallitun haihuwar dukka Æ´aÆ´anta ta bamu,ta Æ™wammaci ta datse zuri’arta akan ta rayu da kiahiya a gidanta,wannan dalilinne yasa dukka Æ´aÆ´an ta basa haihuwa”
“No wonder biri yayi kama da mutum,to amma ina É—anta kuma matarsa tana da ciki”
“Ba dansa bane na wani ne daban,Mahaifiyar sa tayi shurune saboda kada ace batada magaji a cikin zuri’arta”
“Kutt tasanma batada magajin kuma shine take son mallakar Company?
Yanzu dai idan na raba ta dashi har na tsawon wata guda shikenan asiri ya karye”
“Ehh hakane,amma idan kika rabasu yanzu ba lallai yayi aiki ba,saboda bata daÉ—e dayin aikin ba,yanayin daÉ—ewarsa yanayin jinyar dazata gamu dashi”
“Wata biyu zayyi ina daga nan zuwa kafin na rabasu kenan koh?”
“Ehh hakane”
“To tashi kitafi na sallameki,inkina so ki dau mataki akaina kinji,ni wandon robace,da yamma ki sharemin bayan gidana,sannan inzakiyi magana ta madubinki shegantakarnan taki,saikin faÉ—amin tukunna nagaya miki abinda zaki cewa brr na’imah,idan kuwa ba haka ba saikinyi wata guda a sume a gadon asiviti.”
Tana gama maganar ta dannna yellown madannin dake hannunta,haka Zilliyyah ta riƙe kirji tana tafe a hankali harta isa ɗakinta ta kwanta,baccin wahala ne ya ɗauketa,dan ma wahalar ba kaman ta ɗazu ba.
A garin tazo tarwatsa rayuwarta ita kuma tata rayuwar na shirin tarwatsewa a hannun bombee.

 

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button