Arubuce Ta Ke 36
Page 36
Yadda ta shige masan tamkar zata koma cikinsa,gaba daya ta kasa gane me yake fada,sai kawai ya buda hannayensa,ya kuma rungumeta sosai a jikinsa,yayi mata riqon tsauri ta yadda ba zataci gaba da tsalle ba.
A hankali ta fara samun nutsuwa,kukanta ya fara ja baya,sai a sannan kuma ta tuna ajikin wani take,tayi wani irin zillo ta zame daga jikinsa,cikin tashin hankali hadi da wani sabon tsoron,tunda take tsahon rayuwarta ko yatsarta ba wanda ya taba riqewa,amma yau gata a jikin wani?,ta shiga uku?,yanzu shikenan ta zama ‘yar iska?,idan ta samu ciki ta mutu fa?,bata kyautawa ummu ba,sai sabbin hawaye suka barke mata,jikinta har rawa yakeyi
“Tafiya zanyi” ta fada bakinta yana rawa,kafeta yayi da idanu yanason gane me ya tsoratata kuma dai?,kafin ya gama wannan tunanin aka fara knocking qofar,ya maida kallonsa ga qofar,kafin ya bada izini an murda handle din an shigo.
Hafsat ce dauke da jug da cup,da farki idanunta naga abbas,sai kuma sabon qamshin da taji ya baibaye falon yaja hankalinta,a hankali idanunwanta suka sauka kan widad dake tsaye tana tsuma,jikinta yana rawa,kanta babu dankwali bare mayafi,dukka suna watse a qasa,ga hawaye shabe shabe kan fuskarta,gabanta yayi wani mummunan faduwa,abubuwa biyu suka bugeta lokaci daya.
Zallar madarar kyau data gani kwance saman fuskar widad din,duk da shekarunta qananu,da kuma tunanin daya darsu a ranta a take a lokacin,abbas ya nemi tarayya da widad din,tunanin daya kusa sanyata zubar da kayan hannunta,jikinta duka ya dauki rawa.
A nutse ya amsa mata sallamar,ya dauke kansa ya maida ga widad data fara yin gaba zata fice,har yanzu tana hawaye
“Dakata” ya fada cikin salo na umarni,cak ta tsaya amma har yanzu jikinta rawa yake,tasan tata ta qare,tana shiga su anty deena zasu gane wani ya tabata.
Inda ta yasar da dankwali da mayafin ya qarasa,ya dauko mata ya tsaya gabanta ya miqa mata yana kallonta,sannan yace da ita
“Daura” jikinta na rawa ta karba din,amma ta gaza daura dankwalin,sai mayafin ta yafa kawai
“Muje na rakaki” ya fada sannan ya waiwaya ga hafsat wadda ta yiwa kanta mazaunin dole don kada ta fadi
“Ina zuwa” yace da ita suka fice shida widad din.
Kuka sosai ta fashe dashi kamar qaramar yarinya,da gaske abbas neman tarayya da yarinyar yayi?,har zuciyar abbas ta fara qawata masa ita?,duk qoqari da jajircewar da taketa yi kenan tana neman tashi a banza?,ya akayi tayi saken da har yarinyar tasan tazo sashensa?,ba shakka sanyata akayi,tunda ‘yan uwanta suna nan,tabbas ba zata ba haka ta sake faruwa ba,sai ta miqe tana barin flask din kawai ta fito ba tare data bi ta kansa ba,idanuwanta har basa gani sosai saboda tashin hankalin da takejin kanta a ciki,a daddafe ta dinga laluba hanya har takai kanta sassanta.
A gaba ya sanyata yana biye da ita har suka isa sasssan nata,ita ta fara knocking,tayi tayi shuru ba alamun za’a bude,sai yace ta matsa shima ya shiga tayata,amma shuru kakeji,saiya waiwayo yana dubanta
“I think duka sunyi bacci fa” kai ta langabe tana kallonsa,idanunta na fidda ruwan hawaye
“To a ina zan kwana kenan?,don Allah ka tashesu mana” ido yadan zuba mata na wasu sakanni kafin ya kawar da kansa,quruciyarta ta gaske ce
“Ki koma ki kwana a can,da safe saina rakoki,lokacin sun tashi ko?” Ya fada cikin sigar lallami,saboda yadda yakejin kansa yayi week,bacci ma dai a taqaice yaji yana saukar masa.
“Amm…..”
“Ba’a musu da babba right?” Ya fadi cikin sigar tambaya yana ritsata da kallonsa,karon farko taji idanunsa sun dan mata nauyi,saita sadda kanta qasa,ya sake sakata a gaba kamar dazu suka koma,jikinta duk a mace, hankalinta a tashe,anty deena ce ta jawo mata,ta yaya zata kwana daki daya dashi?.
Yayi mamaki sanda ya dawo yaga babu hafsat din ba dalilinta,sai ya tsugunna ya tattara komai waje daya ya adana,har a sannan widad na zaune a takure a waje daya,ac din dakin ya kashe gaba daya,ya rage fitilun falon,saiya kalleta
“Muje ciki ki kwanta” fuska ta tattare waje daya,tanason cewa a’ah amma kuma batason yaga kamar ummu bata koya mata cewa ba’a yiwa babba musu ba,tunda gashi dazu ya fada,haka ta miqe tana biye dashi har cikin bedroom din nasa.
Da ido take kallon komai,bedroom din nada wani irin weather mai saukar da nutsuwa,sassanyan qamshinsa ya kama dakin sosai,komai fari ne qal,kuma komai yana kan tsari a killace,saita haye kan sofa bed ta dunqule,shi kuma ya wuce bandaki.
A ciki ya shirya cikin wasu silk pyjama sky blue,yayi brush ya feshe jiki da bakinsa da turarukansu
“Zaki canza kaya ne?” Ya fada yana dan duban gefanta,cikinta ne ya bada qululu saboda tsoro,yana nufin ta cire kayan jikinta ta sauya wasu?,a dakinsa?,saita damqe jikinta waje guda kamar wadda ya taho zai rabata da suturarta,ta jijjiga kai da qarfi
“A’ah,wadan nan nakeso na jikina” dariya taso qwace masa amma ya danne,a yadda take acting yasan lallai batasan meye cikakken ma’anar aure ba,to amma me yasa take tsoro haka,sai ya rabu da ita,ya jawo wayarsa da nufin kiran hafsat din yayi mata sai da safe,duk da baisan me ya fiddata daga dakin ba,ya tsammaci zatace zata kwana kamar jiya.
Sau uku yana kiranta tana katse kiran,abun yadan daure masa kai,amma saiya tattara ya watsar,dare yayi,hutu yake buqata
“Ki koma gado ki kwanta” ya sake fadi,kamar dazun dai a firgice tace masa a’ah,sai da yayi da gaske sannan ta kuma taga ya yibi filo da bargo yana shirin bar mata dakin sannan taji ranta ya sake.
K’ofar tabi da kallo sanda ya fita,sai kuma ta fara baza idanu,dan banzan tsoron nan nata ya dawo,ji tayi kamar ta bishi,amma ba zata iya ba,curewa tayi waje daya ta lulluba har kanta,saita saki kuka,anty deena ce…..duk ita tace sai tazo,gashi nan sun rufe mata qofa,bayan sunsan ta fita,kewar ummu ta taso mata,ta dinga hawaye ita daya cikin filo,har bacci barawo ya saceta.
A hankali ya bude qofar dakin,duk da akwai qarancin haske amma yana iya hangenta a cure waje daya,sai ya kada kansa ya wuce bandaki.
Alwala ya daura ya dawo dakin,ya feshe jikinsa da turare ya sauya jallabiyyar jikinsa,ya taka a hankali zuwa gefan gadon,hannu yasa ya bubbuga saman filon a tausashe,ta motsa kadan kamar zata tashi,sai kuma ta sake qudundunewa,cikin muryar barci tace
“Don Allah ummu,ba’a idar ba,yanzu aka tayar” shuru ya danyi yana nazarinta,ta kwabe fuska gaba daya tana tura baki gaba a shagwabe,har kuma a hankali ta saki bakin nata,da alama ta koma bacci sosai.
Kai ya girgiza kawai,bai hango komai ba banda zallar quruciya a tattare da ita,shikam baisan ya al’amuran zasuci gaba da tafiya ba,bai hango sauqi ba,sai nauyi daya sake hawa kansa,sai ya juya a nutse ya nufi qofa,yana kama handle din zai.bude ta bude idanunta a hankali, saboda yadda taji cikin jikinta ba’a gida take ba,saboda duk sanda tayi irin haka ummu saita takurata akan sai ta tashi koda ba’a tayar da sallar ba.
Tana qyallara ido ta hangoshi,saita zabura ta miqe tana rarraba idanu,a nutse ya waiwayo ya kalleta,sai baice komai ba ya sanya kai ya fice.
Sai data daina jin motsinsa sannan ta miqe a hankali cike da tsoro ta tura bandakin ta shige tayo alwalar itama ta dawo ta gabatar da sallar,har Allah Allah take ta idar ta fice zuwa wajensu anty madeena,tana idarwa bata ko tsaya addu’a ba tayo waje.
Cak ta tsaya a qofar falon kamar zata saki kuka,ganin garin da duhu har yanzu,gashi dukka fitilun harabar gidan an kashesu,dan banzan tsoronta kuwa bazai barta ta wuce sashenta ba,saita koma.bakin qofa ta rabe tana maida qananun hawayen dakeson sauko mata,ba zata koma cikin dakin ba kuwa,a nan zata yita zama har sai gari yayi haske.
Baiyi zaton zai sameta zaune a bakin qofa ba,don haka cike da kuzari da kuma hanzarinsa ya buda qofar falon
“Subhanallah” ya fada da sauri yana kama murfin qofar ya riqe a hannunsa,sai kuma yadan dai daita yanayin fuskarsa yana kallonta
“Me kikeyi a nan?” Mele baki tayi fuskarta a yamutse,da alama qiris take jira ta fashe
“Ina kwana?,can zan koma,kuma wajen da duhu bazan iya fita ba” sai daya juya ya sake kallon harabar gidan,shi yasa aka kashe fitilun saboda yaron gidan yace sunata wasa da wutar kada su lalata qwayayen,qwayaye ne masu tsada da daraja
“Basu bude ba suma,ki koma ciki sai rana ta fito” kai ta maqale a kafada,sannan ta miqe kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,ta koma saman kujera ta takure waje daya,bai sani bama ko hawaye take sharewa.
Dakin ya wuce,bai jima ba ya dawo,ya haye saman doguwar kujerar daya kwana a kai,yaja bargonsa zuwa qugu ya rufe, lokaci lokaci yana dan daga idanu ya dubeta,yadda take curewa waje daya ta kwanta shine ke bashi mamaki,amma baice da ita komai ba.
Wantsalowa tayi daga saman kujerar sanda agogo ya gama buga qarfe bakwai dai dai,suna hada idanu sai kuma ta koma dai dai ta zauna,fuska a narke take dubansa,cikin salo na roqo da magiya tace
“Don Allah…..ka rakani,gari yayi haske fa?” Ido ya tsura mata na wasu sakanni yana kallonta,sai ya janye idanun nasa yana zame bargon jikinsa,daki ya sake shiga,bai jima ba ya fito yana gyara button na rigarsa
“Muje” da saurinta ta sauko muryarta tabi bayansa,don kafin yakai qofa har ta kusa cimmasa,yadan sake binta da kallo sannan ya buda qofar suke fice.
*Arewabooks:Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K’AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al’ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
[3/2, 5:28 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)