Bakar Ayah Book 2 Page 11-12
–
Page 🖤11••12🖤
“Tunda muka fito daga gidan baka sake cemin komai ba,shin zuwa gaisuwar jiki ce ko kuma dai akwai wani dalilin a ciki”
Duk maganar dayake Jabeer bai kulashi sai murmushi dayake shikadai batareda yace komai ba.
Hakan dayayine kaÉ—ai yabawa Khaleel amsar abinda yakeson sani.
“Ya dai wai ina zamujene naga baka kama hanyar zuwa office ba”
“Ohh sorry da gida zan wuce dakai ai”
Sakin baki Khaleel yayi yana kallonsa,wai dagaske yake sai ya wuce dashi bayareda ya sani ba,anyah kuwa abokinnasa baya cikin illusion.
“Kai wai serious duniyar soyayyar yarinyar can ka tsunduma da gaske?”
“To menene bata cancanta bane,ko haramunne kai”
“Kuttt yaufah amarya ta iso gareka amma kuma ka folawa wata a can nesa,kuma son aurenta kakeyi dagaske”
“Hhhhh amarya,wancan abinne amaryar,kaini fah inka dauramin waccar mai kama da aljanun zan tsinketa,kallo daya nayi mata naji bakin jininta yashiga raina,gabaÉ—aya mommah ce take rawarta take kidinta ita kadai,kai duk halin Lubnah wlh gwanda min ita sau dubu akan ta,ni bantaba ganin macen dabana Æ™aunar kallon fuskarta kamarta ba”
“Hmmmm mutumina kadaina cika baki mana haka kayi shuru kawai da bakinka,to yanzu yazakayi da wannan wacce ka Æ™ira da Jaleelah É—in,kasan fah ga Jawaheer ma a gefe”
“Ahhh ni yanzu nadaina damuwa,zuba musu ido kawai zanyi,kaman ta shawarar daka bani kan na auri wacce zuciyata ke so,ta hakane zan samu kwanciyar hankali”
“To ya batun adalci kuma inka makale a iya sashen wacce ranka keso,kana ganin su zasu amince da hakan”
“Ahhh wannan kuma yana ga mommah tunda ita ta aurosu”
Shuru Khaleel yayi da zancen,dan da alama abokinnasa yasha giyar soyayya maganganu yake kaman ba shiba,saidai yana fatan Allah hasa hakan shine sanadiyyar farincikinsa.
Nikam maidani na dau motata a office,kuma ma inada aikinyi,nasan Madeenah tana makaranta,da don ita zanje gidan”
Komawa sukayi companyn ya sauƙe Khaleel,daga nan yashige gidansa na sirri.
Hanyar kamar fita daga gari ya nufa,inda sabin anguwanni suke,wani gida ya nufah ɗan karami madaidaici kana kuma ƙayatacce.
Falor guda daya sai É—akuna biyu a gidan da banÉ—akunan su,saikuma kitchen shima karami,filin gidan kuma shine na saka mota.
Gidan a share yake fess babu datti,saidai babu alamun mutum a gidan da alama ba’azama a gidan sosai.
ÆŠaya daga cikin É—akunan gidan ya shiga ya zauna a bakin gado.
Drawer gefensa ya jawo wacce take É—auke da magunguna pills dayawa a cikin robobinsu.
Roba É—aya ya É—auka ya jajjagi kwayoyi guda biyar ya zuba su a bakinsa, gorar ruwan dake kan drawer wajen ya dauka yabi su dashi.
Ajiyewa yayi yana maida numfashi bayan ya haÉ—iye,tareda komawa ya kwanta akan gadon.
Bayan kaman mintunan dabasu fi uku ba kuwa yafara lumshe ido bacci yayi awon gaba dashi.
Misalin Æ™arfe takwas anyi sallahr isha,text É—in Hajiyah Zeenah tagani tana kan sallayah tagama yin sallah,ko addu’a batayiba ta É—auke sallayar ta ajiye gefe,kana gani ma dama kasan sallah kawai akeyi domin tazama dole.
Karanta text É—in tayi,kan tana nemanta yanzu a part É—inta akwai maganar dazasuyi.
Yar ƙaramar tsuka tayi,da bazata jeba,saidai kuma tana bukatar miƙe ƙafa,kuma Haidar yadaɗe dayin bacci a ɗakin Hilyaan,dan yanzu daya shiga wata na huɗu madarar tafara ƙarbar jikinsa,matsalarsa ma na laushin ƙashi tafara raguwa.
Doguwar rigace a jikinta,dan haka hijabin datayi sallah jundumeme har ƙasa yana jan ƙasa a mayar.
Tafiya take tana bubbuÉ—awa a cikin hijabin,kai daga nesa saikace aljana,ita kanta yanayin shigar tata yabata dariyah,wayaga da rana ayi shigar gyale da daddare kuma ayita burmemen hijabi.
Tayi ta kalle kallenta a hanya kafin ta isa sashen hajiya zeenatun..
Babu ƙowa a falon,dan haka kao tsaye dakinta ta wuce dan tasan tana can tana jiranta..
Ko sallama batayiba ta samu kujera ta zauna bayan ta naɗe hijabinta wanda yataru a ƙasa.
“Naga kin daÉ—e baki Æ™ariso ba,baki hau mota ba da darennan bakya tsoro?”
“A ina kika ganni kika bani aiki,a cikin gari kika gannin cikin gidan kaman sauran mata? Banji tsoron daji ba sai wannan cikin gidan,yanzu dai ba zancen nadaÉ—e ban iso ba,menene dalilin wannan Æ™iran”
“Amma dai yakamata ki dungayiwa manya magana da kaurin lafazi,kada ki manta fah É—ana kike aure?”
Wata dariyar shaƙiyanci Bombee tayi tareda cewa.
“Idan akwai wanda yasan wacece ni a gidannan to bayanki ne,hasalima wannan halayyar kika gani kika nemeni. Hajiya zeenah kada ki manta wacece take gabanki,ke yakamata kisan dawa kike hulÉ—a,yaushe ma kika samu dama har zakiyimin Æ™ira da daddare kuma nazo,dan kinga inayimiki laushi?.”
Cikin É—aure fuska da tsayayyun ido takarisa maganar,ba wuyah sai ranta ya baci..
Shakkarta ce tashiga Hajiya zeenah wanda sai yanzu taga hakan,wai chakwakiyah tun ba’aje ko inaba anya kuma batayi kuskure ba. Share tantama tayi a ranta tareda cewa.
“Yanzu dai ba wannan ba,dama É—azu na yi shawara,shin maizai hana ki fara dayimana maganin matarsa a cikin wata shida na farko idan babu damuwa”
“Meyasa kika ce haka,sannan wai ni meyasa bazakuyi maganin ta da kanku bane tunwuri”
“Nariga na faÉ—amiki halin da ake ciki,so nake da furta dakanta cewar ya saketa,idan ba haka ba inna tilasta shi ya saketa to zai mutu…..idan mukayi maganinta da kanmu kuma uwarta bazatayi shuru ba,wato Brr Na’ima.
“Brr Na’imah Hashim wai”
“Eh itafah kinsan ta ne?”
“Uhm amma basosai ba shikenan zanyi shawar ni barin na tafi”
“Yawwa bayan wannan kar Jabeer yasan dalilinki na zuwa gidannan,ta hakanne sirrin mu zai rufu sosai”
“Uhm bakuso yasani itakuma yarinyar dazai aura yaakayi ta sani ”
Alamar rashin sanin mai take faÉ—a Hajiya zeenah ta nuna,ta hakanne tagano cewar Hajiya rabi ce tafaÉ—awa Æ´ar ta kenan,saboda kartayi mata kallon matar masoyinta. Komai yana rufe a gidannan.
“Lahh shikenan karki damu ma bakomai ni na tafi”
Daga haka Bombee ta tashi tanufi hanyar nata side É—in.
Dariyah ta sheqe dashi tareda cewa.
“I solved some puzzle,hmmm Hajiya zeenah kenan,idan bangane mai kuke Æ™ullawa ba basunana Bombee ba wacce sunan ke zama kan harshen duk mutanen data zaga.
Kin bukaci na yimuku maganin Lubnah da farko saboda kufitarni daga shirinku a cikin wata shida nan gaba,wanda shine daidai lokacin aurawa Jabeer Jawaheer. Sannan bakuso shi yasan matsayina a gidanann saboda kada matarsa taji. Wannan duk plan É—in Hajiya rabine,amma kuma ta sanarwa da Æ´ar ta saboda ta kwantar da hankalin ta.
Ke kuma Lubnah wato ke Æ´ar barr Na’imah ce da kuma Gen Abdu manga.
Wow puzzle É—ina ya warware cikin sauÆ™i,shirina yana tare a waje É—aya batareda na saniba,am sorry Hajiya zeenah,kin kawoni cikin gidannan,amma abinda naga dama dakuma tsarina zanyi,in takanki ya biyoma saidai kiyi sorry”
Tafiyah Bombee take tana fara’ah da nishaÉ—i,da alama tasamo bakin zaren matsalolinta,tasamu fili tasamu doki,saura sukuwa kawai yarage mata.
Ba ita ta isa part É—inta ba sai wajen 9:30pm,tana shiga taji shuru tsitt,da alama su Hilyaan sunyi bacci itada Haidar kenan.
Safah da marwa take a tsakar ɗakinta,taje kana ta dawo,tarasama mai yake mata daɗi a duniyar nan ta maliki yaumiddini,ƙarfe kusan goma amma Jabeer bai dawo gidaba,kaddai ya dawo kai ya tsayah a sashen amaryarsa kaman yanda tun ɗa zu zuciyarta ke raya mata ammma taƙi bata hadin kai.
Wani irin bugawa ƙirjinta yayi,data fara gasgata hakan,mayafinta ta ɗauka ta fitah da gudu zuwa sashen Bombee.
Saidai har taje bakin ƙofar kuma sai tadawo wata zuciyar tace mata,karkuma kije kiyi mungun ganin dazai rikita miki ƙwaƙwalwa.
Turus tayi a bakin ƙofah tareda komawa cikin sanyin jiki,jidake banda tafarfasa babu abinda zuciyarta keyi,gaba ɗaya ko wata huɗu batayi ba da fita a cikin ƙangin kishi har takoma wani.
Ganin idan takoma cikin É—akinma ba bacci zatayi ba,yasa kawai ta nufi wajen motarta a daren ta nufi sashen da Bombee takeyi,ba mungun gani ba inma aljanin ganine gwanda tayi data kwana da wasiwasin kar ko mijinta yana wajen wata,watan ma wacce tayimata cin fuska a lokacin farko.
Bombee wacce bata dade da shigowa ba,tasaka kayan bacci kenan taji anan ƙwanƙwasa mata ƙofar bakin part.
Jim tayi kan wanene yake buga ƙofah haka a zuciye?
Ganin zai tayar da masu bacci yasakata nufar bakin ƙofar,ko ɗankwali bata ɗaura ba gashinta yana ɗaure ribbon.
Ta na’urar jikin Æ™ofar ta leÆ™a domin ganin wanene,Lubnah ce a tsaye ta kama kunkumi tana jijjiga tareda tsumayin a buÉ—e Æ™ofar.
Tun kafin ta buɗe ƙofar taji Lubnah tasake buga ƙofar tareda cewar.
“Ki buÉ—e Æ™ofar nan kifito min da mijina,munafukar Allah nasan daga kallon dayayi miki da safe badai kan yabiyoki dan Allah ba saidan nemarsa dakikayi”
Dan murmushi Bombee tayi tareda zare ribbon ɗin dayake kanta kana ta barvaza gashin kannata a gadon bayan da ƙafaɗunta.
Yamutsa rigar jikinta tayi tareda É—ageta ta sokata a tsakanin mamanta,ta yanda cibiyarta zata buÉ—e ana kallonta..
“Let have some fun”
Tafaɗa tareda buɗe ƙofar,hammar ƙarya tayi tareda kallon Lubnah ta lumshashshun idanuwa cikin maganar hamma.
“Baiwar Allah lafiyah,mai ya kawo ki side É—in amarya dawannan daren,wani abun kike nema?”
Sake hassala Lubnah tayi tareda ƙarema Bombee kallo,wacce take tsaye a gabanta gashi a babbaje,ga matarta a mai laushi dakkyau cikin kayan bacci masu ɗaukar hankali,kana ganinta kam babu shakka kasan sun fagen soyayyane tafitar hankali,dan jikinta ya nuna hakan da muryarta.
Cikin shaƙyaƙyƙyiyar muryar tace.
“Ina mijina yake?”
“Ohh mijinki yana cikin É—aki yana jirana,amma kuma yau a aikinsan ba mijinki bane koh,saiki bari idan mungama yabani madara na bashi mun more,in Lokacin ki ya zo saukusha naku”
“Jabeer Jabeer!!!”
Lubnah da ƙwallah masa ƙira a can ƙasan maƙoshinta tamkar mahaukaciyah.
“Shiiitt ko ya jiki bazai fito ba,domin na cemasa yayi zaman inazuwa,kinga ma ni tafiyata,inkinaso kiyi ta tsayuwa a wajen har hudowar rana”
Bombee tana gama faɗin haka maida ƙofar tarufe tana dariyar ƙasa kasa ta mugunta.
A ranar yanda Lubnah taga rana haka taga dare tana saƙe saƙe da shirye shiryen dawowar Jabeer gareta,ina kwana daya ma yayi a can amma ji take kaman an tsunduma ta a kogin ruwan zafi,taya zata iyah barinsa yayi sati a wajen wanann mai zubin karuwan,ita yanzu ma yakejin mai nene wani abu waishi kishi,da wasanta tayi kawai.
Maganin da Mahaifiyar ta bata gobe zatayi aiki dashi,itakuma a hankali zata kai sunanta wajen Boka zulumgum suyi aiki babba a gunta.
A bangaren Jabeer kuwa bashi ya tashi ba sai wajen karfe huÉ—u na dare.
Yana tashi kansa ya dafe na yan wasu mintuna kafin ya tashi daga kan gadon.
Kai tsaye banÉ—aki ya nufah ya iyo wanka haÉ—eda alwala.
Sallolin da ake binsa na ranar ya rama kafin ya fara nafilfili yana jiran shiga Sallar asuba.
Kasancewar baccin dayayi ba karami bane yasa daya gama sallar akan sallayar ya zauna yana karanta Æ™ur’ani a cikin wayar tasa.
Ƙarfe shida daidai ƙira ya shigo masa wayar na neman gaggawa da akayi a wani company dayake da share a ciki a kasar Roman,ƴar ƙaramar tsuka yayi kafin ya tashi zai shiryah.
Wardrobe ya buÉ—e inda yakeda extar kaya a shirye a ciki,É—auka kawai yayi yasaka tareda zaran keyÉ—in motarsa.
Gida ya nufah kai tsaye sashen sa dayake part É—in da Lubnah take,dan part É—insa dake side É—in Bombee bai fara amfani dashi ba tukunna,har akayi gyaransa aka gama bai saniba,shin anakai wasu kayansa can ko ahah bai saniba.
Har yazo leƙa ɗakin Lubnah sai kuma yafasa,yayi mata text kawai,dan yasan comfirm ne bata tashi tayi sallah i yanzu ba,dama yaya bare iya tazo,yana nan ma sai yayi dagaske tukunna.
Inaga bayanan,yasan sai ya Allah jaka a É—aki.
Ko Hajiya zeenah bai samu damar ganiba ya wuce,da niyyar ya ƙirata ya faɗamata,don zuwan na zayyi a ƙallah sati ɗaya ko fiyeda haka a can.
Jabeer bai tashi yiwa Lubnah text ɗin ya tafi ba sai kusan 12 na rana,iya kuluwa ta ƙulu,wato jiya yana sadi din Bombee bata ganshi ba,yanzu kuma yayi tafiya sai a waya ya faɗamata.
Hannu tasaka a kai kaman mai shirin rusa ihu,dan sannan ne sauƙowarta daga kan gado,shima dan yunwa ce ta tasheta.
Wurgi tayi da wayar ta bugu da kunnen gado,fuuuu tashiga banÉ—aki kaman zata tashi sama,tana banÉ—akin tana surutu ita kaÉ—ai kaman tababbiyah.
Sai bayan ta shirya taci abinci kafin ta É—auko wayar.
Key ɗin motar ta ɗauka ta nufi waje a zuciye,ta motsa da alama an tafi wajen zulungum👀.
A safiyar ta kama hanyar barin gari tareda nufar zulungum da tarin buƙatunta.
Gudu take a mota tana tunanin irin cin fuskar da Jabeer yayi mata.
“Inaa dole ma nayiwa tufkar hanci,duka duka jiya fah ka kawota cikin gidan,har ka fara juyamin baya kaman wata kayan wanki,zakuwa kuga aiki da cikawa daga kai har ita É—in”
A haka ta isa cikin dajin inda iya motarta zata iya shiga.
Takawa tafarayi da ƙafah tana ɗaɗɗage skirt,ita kaɗai tana tsuka kaman ansaka dole harta isa wajensa.
Tun daga nesa take gano hayaƙi yana tashi daga gefe bukkar,da alama wani abun yake dafawa.
Wata buta ce ta ƙarfe akan wuta tahaɗa ɗauda ko ganeta bakayi dakyau,kallo ɗaya tayiwa butar tashiga cikin bukkata,tun daga dosar ɗakin takejin gurnani kaman zaki. Yasake baki sama yana bacci kaman busuru,banda wari idan yasaki numfashi babu abinda yake fita daga bakin.
Wani kwano tasamu a wajen ta shamba da ƙafarta,aikuwa nan da nan yayi firgit ya tashi tareda ambaton sunan wani aljani a bakinsa(auzubillahi).
“Hmmm kai har bacci ma kake,muhimmin abune ke tafe dani wajenka tashi kayimin aiki yanzunnan”
“Ke yau ba ranar aiki bace,uwar matsafa ta bani hutun aiki yau,sanann karki damu kin kawo kukanki inda ya dace,An kawomin labarin sabuwar kishiryarki,saidai babban abin mamakin duk yanda naso samo sunanta cikin madubina ban samuba. Amma kibari zan baki wani magani wanda zakiyi amfani dashi..
Bazan faɗamiki mai maganin zayyi yanzu ba,saboda ƙa idarsa kenan.
Zaki dunga É—iga masa jinin baÆ™ar kuliyah duk bayan sati guda,har na tsawon wata uku. A wannan lokacin da maganinnan yake shan jini,ba’a yarda mijinki ya kusance ki ba sam harsai kinyi amfani da maganin tukunna. Inkuma kika kuskure toh fah zaki mutu mushe.
A sanann koh Æ™afarki kikace ya tsugunna lasha,ke ko kashinkine tofah sai ya lasa dolensa””
Karbar maganin Lubnah tayi cikeda murmushi tasaka a jaka.
“Amma a ina ka samoshi,bayan kacemin yau ba aiki”
“Kedai kije ki jarraba maganinnan tukunna,kaman na sakinnan shima kedashi mutu ka raba ne…….!!!!”
** * **
Khamees ne yashigo sashen Bombee da wani labari na uzula,wanda ya samo a daren jiyan.
A zaune yake riƙeda document a hannunsa yana duddubawa kafin tafito.
Fitowa tayi sanye da riga da skirt a jikinta Æ´an kanti,da haidar a hannunta yake gilu gilu da kai alamar bai tsayaba.
Hannu khamees yasaka ya karbeshi yana yimasa wasa,sai bangala dariya yake.
“Ahh lallai my boy ka samu sauÆ™i,gashinan idonka yana Æ™arayin irinna mommynka sak blue”
Rolling Bombee tayi da ido tareda yin ƙaramin murmushi.
“Yah Khamees ka tashi lafiya,naji Æ™iran gaggawa daga zuwa jiya,mai ka samo mana gameda su?”
Maida haidar yayi kan cinyarsa ta gefe,tareda miƙa mata file ɗin dake kan cinyarsa.
“Nasamo gidan su haidar bashi nisa daga nan,sannan shikuma uban gayyar target É—inmu na samu bayanan komai nasa,gidansa companynsa harma da labarin iyalansa dukka”
“Ehh nima nasamu wasu bayanai dan gane dashi,amma Æ´aÆ´an sa nawane?”
“Uhm ukune kacal,biyun mazane kuma basa Æ™asar,Æ™aramar cikinsu itace wacce mijinki yake aure,kinga kun haÉ—u a waje É—aya kenan,saidai kiyi taka tsantsan kada tasan koke wacece,hakan zai bada matsala babba.
A yanzu bamu gama shiri sosai ba,dan haka bamu da buÆ™atar fara komai yanzu”
“Ehh nasani,tun jiya dama nasan wacece itah,kaga kenan bazan yi aiki da tsarin Hajiya zeenah ba kenan,muna buÆ™atar lokaci sosai akan hakan,domin suna da matuÆ™ar iko. Kaifah ya yanayin zamanka a garin,baka ganin za’a samu matsala,tunda har yanzu baka cire siginal É—inka ba,deactivate É—inta mukayi,a kowanne lokaci zata dawo aiki idan tayi kusada na’urarsu,inaga kawai ka koma gembu,ni zanji da komai”
“Ahah ahhah Maryam bazaki iya ke kaÉ—aiba,sannan karki manta nima abinnnan yashafeni ba iya ke kaÉ—ai bace,dan haka yanzu ma nayi secret booking na body checiking daza’ayimin,wannan karon zanyi nasarar cirewa inshaaallah”
“Hmm idan kuma ka gano a wajen zuciyarka take fah kamar………”
Bata ƙarisa sunan ba gabaɗayah yanayin fuskarta ya sauyah,ƙokarin haɗiye hakan tayi tareda sauya alakalar zancen.
Shima khamees shuru yayi bai bata amsa ba jin Mummunan labarin data É—ago mai cikeda abubuwa marasa daÉ—inji.
“Ya batun familynsa shin suna cikin Æ™oshin lafiyah koh?”
“Lafiyansu kalau,na haÉ—u da Æ™anwarsa ma jiyah a makaranta Nu’aimah,nasaka fuska bata ganeni ba,amma dai alamu sun nuna tana cikin Æ™oshin lafiyah”
“Hmmm kenan alamu sun nuna sun Æ™yale familynsa,dan haka bazamu kusancesu ba kada musake jawomusu wata matslar,mu barsu suji da rashin dasukayi ma a baya.”
Cije bakinta Bombee tayi tareda dunƙule hannunta. Hilyaan wacce take bayan ta ne ta dafata a kafaɗa cikin sigar lallashi.
“Kiyi haÆ™uri anty Maryam,suma inshaaallah saisunga Æ™arshensu”
“Wannan yazama wajibi,indai ina numfashi saina yi daiÉ—ai da zuri’arsu ko bara sai nayi sanadiyyar data gagaresu.
A yansu basai wani lokacin ba wasan zai soma,ba gudu babu ja da baya,lokacin dazasu girbi abinda suka shuka yayi,saina saka wuÆ™a na yaga bargon mutuncin Æ™aryar dasuka yafawa kansu,saina bankaÉ—o abinda suke boyewa mutane suna zaluntarsu. Khamees kayi koÆ™arin fitar da baÆ™ar alamarsu a jikinka,idan kuma baka samu damar cireta ba ka koma kada kaima ka rasa rayuwarka,ka barni naji dasu,aradu ko ni kosune a garinnan,saina shayar dasu ruwan mamakin da suka daÉ—e basu kurba ba a rayuwarsu”
Kafin ta kaiga ƙarisa maganar idanuwanta sun kaɗa sunyi ja.
Tashi tayi kaman an cillata ta nufi É—akinta. Jijjiga kai khamees yayi shida Hilyaan,dan su kansu abin yatabasu bare kuma itah,abin kawai cin rai sosai.
_*RAYUWAR BOMBEE A BARIKIN SOJOJI*_
_*SADI-SAKHNA CEH*_
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________