Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 16

Sponsored Links

โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*PAGE 18*

Hajiya bata gama sauke maganar data d’auka ba AK ya fad’o cikin falon da d’an gudu gudu wanda alamu suka nuna cewa daga wajen gudun ya dawo, baiyi tsammanin ganin kowa zaune a falon ba dan haka ma ko sallamar da yayi k’asa sosai yayita wanda iya shi da yayi abunshi shi yasan yayin,

Turus yayi a tsakiyar falon ya tsaya yana bin su da kallo, kamar wani wanda ya mance da wanzuwar su a gida, dan shi ya fad’o ne kawai abunshi baiyi zaton zai samu wani zaune a falon ba,
ya manta shaf cewa Hajiya bata bak’unta duk inda taje sakewa takeyi ta bararraje abinta balle kuma gidan shi, ga al’adarta na yin karin kumallo sau biyu ko yanzun yasan fitowar nan nata baya rasa nasaba da neman abunda zata fara karin kumallon farkon dashi.

“Ka tsaya daga can kana k’are mana kallo kamar wasu sabbin halittun da baka saba gani ba, k’araso ciki mana sai wani bin mutane kake da kallo kamar wanda yayo makuwa, ko ka manta cewa mutane sun kwana a gidan ne tunda ka saba kwana ka tashi kai kad’ai a cikin Sashen uwa wani Dangin mayu, wato dan
haka shi yasa ka fad’o ko sallama babu to fisabilillahi mutum yana shiga waje ba sallama bama dole yayi ta rayuwa tareda shaidanun aljanu ba,
Ke kuma ki fara shiga kitchen din nan ki dubamin duk wani abun da kika san babu na kayan abincin da zamu iya buk’atar amfani dashi kafin mu tafi kizo kimin list din su yanzun nan ki bashi kafin mu fita, dan nidai bazan dunga wayar gari zuru zuru ina tunanin dame zanyi karin safe ba”

K’arasowa yayi ya samu waje daga gefen Hajiyar ya zauna,

“Barka da safe Hajiya ya bak’unta?”

“Barka ka dai, bak’unta kamar wata wacce taje wani bak’on wajen daban, gidan kafa nazo! ”

“Ina kwana Ya’ya”
Cewar Meenal daga tsayen da take tana shirin zuwa kitchen duba abinda Hajiya ta Sanya ta,

“Lafiya lau kin tashi lafiya, zoki zauna kiyi karin ki na riga nasa Mansoor yayi cefane tun jiya abubuwan da babu anjima idan na fita zan siyo”

Canza hanya tayi ta wuce d’akin da suka sauka, bakin ta kawai ta wanke sai dogon hijjabin dake jikin data cire ta fito daga d’akin,

Tare suka zauna dukan su Ukun suka gabatar da karin safen dan shima AK da wuri yake son fita daga gidan akwai inda zashi da safen,

Duk jininin da Hajiya ta dungayi akan su samu su fita da wuri hakan bai samu ba, domin shiririta Meenal ta dunga yi kawai dan dai suja lokaci kafin su fitan, karfe 8 da kusan rabi suka fito harabar gidan, Mansoor ne ya k’araso ya gaisheda Hajiya itama Meenal ta gaishe shi,

“Hajiya ai ban san fitan wuri zakuyi ba tun d’azun mai d’akina Hajara keson ta shigo ku gaisa ni kuma nace mata baku riga kun tashi bacci ba, dan Allah da kun d’an koma daga ciki bari in mata magana ta fito ku gaisa kafin ku fitan dan tun d’azun take kitchen tana had’a muku karin kumallo gashi kuma kun fito”

“To haka akayi ai nayi zaton kai kad’ai ne a gidan ashe harda iyali gareka masha Allah gaskiya kayi kyan kai, ai aure daraja ne dashi wallahi, ina dalili mutum yayi ta rayuwa shi kad’ai kwallin kwal ba mace bawai kuma dan bashi da halin auren ba,
ba damuwa kana iya mata magana sai ta fito mu gaisa tunda kaga mudai iya kwana ne kawai zai dunga maidomu gidan kuma nasan a sanda zamu shigo gidan ba mamaki tayi bacci, batun kari kuma ai da baka wahalshe taba wallahi dan yanzun muka gama karyawa a ciki dan dama tun jiyan da guzurin mu muka shigo gidan,kasan gidan da babu mace gara mutum yaje da guzuri koda ko garin kwaki ne atoh,

wucewa yayi yana amsa ma Hajiya da cewa “to Hajiya bari dai in kiratan”

Basu d’auki lokaci mai tsayi ba suka fito shida matar nashi daya kira da suna Hajara sai yaran su biyu mata Babban mai wayan duka bazata haura shekara hud’u ba sai k’aramar dake hannun uwar wacce ita ma dai batayi shekaru biyu ba, shi kuma Mansoor din hannun shi rik’e da basket mai murfi wanda cikin shi ke d’auke da wani madaidaicin jug mai had’e da kananun kofuna guda uku sai wasu madai daitan kuloli guda uku suma,
Har k’asa matar nashi ta duk’a ta gaida Hajiya kafin ta maida gaisuwar kan Mai Jama’a cike da girmama wa suma suka amsa mata a mutunce, k’aramar yarinyar dake hannun matar meenal ta amsa tana murmushi bayan sun gaisa da Maman yaran,

“Kuyi hakuri Hajiya ban san cewa da wurwuri haka zaku fita ba shi yasa ban lek’o tun d’azun mun gaisa ba dan Allah ku koma ku karya kafin ku fita tunda ga abun karin naku ya kammala”

“Kaiya bayan na riga da na fadama me gidan ki cewa mun karya kuma shine sai da ya k’ara tattago kayan abincin ya fito dashi, ya za’ayi haka daga zuwan mu kuma zaku daura ma kanku dawainiya, Meenal amsa kayan kikai mota in mun isa can d’in maci dan bazataji dad’i ba idan bamu amsa ba, angode kunji Allah dai ya muku albarkha,

Sai da suka raka su har bakin motar suka shiga sannan matar ta koma ciki ita da yaran,
AK dake gefe yana amsa waya ne ya zagayo ta gefen da Meenal ke zaune,

Key din motar dake rik’e a hannun shi ya mik’a mata ta window,
“fito ki koma wancan motar ki biyoni a baya dan bai zama lallai anjima in iya zuwa d’auko kuba dan ina da uzurori masu yawa da zanyi”

“To ni ai ba sani kan hanyoyin garin nan nayi ba”

“Eh ai saboda sanin hakan shi yasa zan miki jagora a yanzun ta yanda bazaki sha wahalar gane hanyar dawowa nan d’in ba in dare yayi,”
Bud’e mata murfin motar yayi sai ya mata alamar ta fito da hannu,

“To in ya zama haka kabar mana wannan d’in mana!”

“Ah ah waccan d’in dai zaki hau ita tafi dacewa dake koba kin fison ki hau Babbar Mota ba?,”
ya tambaya yana nuna mata motar da yatsar shi,

“To ai nidai in haka ne ai sai dai a barni in zab’a tunda ai da gangan mutum ya hanani zuwa da tawa motar”

“Oh baki gode ba kenan da na miki tayin wannan d’in?”

“Nidai bance ban gode ba kawai dai ni kayan aro ne bana so, so kake in dunga hawa wannan d’in sai na fara jin dadin hawan ta na kwana biyu sai in tafi in barta!”

“Wa yace miki kayana ba naki bane?, bari in kin dawo sai ki duba duk motar da kike so anan d’in ki d’auka ni kuma na baki ita duniya da lahira”

“Da gaske๐Ÿ˜ณ?”

“Da gaske mana!, na saba yin wasa dake ne dama ko na tab’a miki k’arya ne?”

“Ah ah amma nidai bana so mutum yamin kyautar koma d’aka kayi kukane, in kasan kana son motar ka kabar shi kawai wallahi tunda nidai ban rok’eka ba”

Dariya ma ta bashi,wai shine dan yayi kyautar mota take cema karya mata kyautar koma d’aka kayi kuka,
kai jam’a yarinyar nan ba’a tab’a iya mata wallahi Mansoor ya kira ya bashi key din motar da Hajiya ke ciki,
“Kaja motar nan ka biyoni a baya”

“To Yallabai”

Da gudu ta k’arasa wajen motar tana zagayata,

Motar fa ta had’u gaskiya dan motar kai da gani kasan ba kananan kud’ad’e aka salwantar kafin a mallaketa ba gata fara tass sab’anin wancan natan da Sarki ba bata da take bak’a wuluk ita kuma,

“Kai gaskiya ni d’in nan fa mai sa’a ce wallahi na samu kyautar motoci har biyu a cikin watanni kad’an, kuma nadai fad’a maka Allah karma kazo zuwa gaba ka wani ce in dawo maka da motar ka, allah kuwa naci halak,”

Baya ta tayi da gudu ta koma wajen Hajiya bud’e kofar gefen da hajiyar ke zaune tayi cike da jin dad’i daya ke bayyane akan fuskarta take cewa,

“Hajiya fito ki gani yauma na samu kyautar wata motar, taubashi ya bani kyautar mota shima, wuuuu ni yar gata mai yayye da yawa, oh Allah kaci gaba da lullub’e mu da arzikin da zamu amfana duniya da lahira Ameen”

Fitowa Hajiya tayi tana cewa,
“Ban gane ba wai anyi yamma da kare,
Mota dai ta hawa irin wannan itace shi Abdul din ya baki kyautar ta da sanyin safen nan?” Hajiya ta fada tana jin jina wai kyautar motar manyan kudade Ak yayi da safen nan,

Kamo hannun Hajiyar tayi tana dariyar jin dad’i tace,
“eh mana Hajiya gata ma kina gani a gaban ki kuwa, wallahi gashi nan a gaban ki ai sai ki tambaye shi idan k’arya nike miki, Taubashi ”

sai kuma ta rufe baki๐Ÿ™Š,

“Au Ya AK dan Allah ba yanzun ka bani makulin motar kace kuma ka bani motar duka kyauta ba?, itafa Hajiya bata yarda ba ka fad’a mata da kanka”

Kankance idanun ta Hajiya tayi tana kallon AK d’in dake gefe jingine da motar ya rungume hannayen shi a k’irji Meenal kawai yake bi da kallo shima yana murmushin ganin yanda take ta farin ciki dan kawai ya mata kyautar mota,

Matsawa kusa dashi Hajiya tayi, sai da takai hannunta kan goshin shi ta tab’a, jin babu zafi a wajen sai ta cire ta maida hannun kan wuyan shi,

“Kai Abdul zazzabin safe ne ke damun ka ko koh a ah iskokine suka bugeka ka kama kyautar mota da sanyin safen nan?”

Meenal ce ta amsa da cewa
“haba Hajiya iskoki kuma dan kawai ya bani kyautar mota, to shi ya Sarki daya bani wancan Motar kyauta mai yasa bakice shima iskokine suka buge shin ba? ”
Ta tambaya tana tura baki,

“Yo shi wancan tsohon mijin naki ai toshiyar bakine yayi miki, wannan kuma babu kare bin damo in kyautar ce fisabilillahi aini ya dace ya bawa ita bake ba, tun yaushe nike cewa ya siyamin tikiti inje umara daga nan in kaima iyayen shi ziyara yana k’i kawai dan baya so idan naje in ma uban shi batun auren da yak’iyi, amma tsabar son kai nida kullum nike d’awainiya dashi bai canzamin motar hawa ba sai ke da yaushe yaushe ma kuka fara shiri a tsakanin ku,rabon ma da yamin kyautar zunzurutu tsabar kud’i harna manta, kullum sai dai ya kwaso kayan abinci yazo ya jibge min uwa wata sauran yunwa,
In ma ba munafunci ba ina ce nan kullum da ke dashi d’in had’uwa goma rabuwa goma saina shiga tsakanin ku kullum sai kun raba hali kamar wasu kaji, amma daga jiya zuwa yau saboda bak’in munafurci kun wani had’e kai kun dunkule uwa wasu kashin awaki”

Dariya ma Hajiya taba Meenal,
“Hajiya kamar wasu kashin awaki fa kikace, to dan Allah wai dama kinfi so kiga muna fad’ane kullum, nidai wallahi na yafe mishi duka laifukan da yayi mun na baya harda na gaba ma, kuma dama can ai yarinta ne yasa muke fad’an yanzun kuma ni na girma, kuma tsakani da Allah ai kece kikace bana a can Saudiya din zamuyi azumi kuma ma ai bakice min kin mishi magana ya biya miki kudin jirgi yakiya ba,”

Juyawa gefen AK tayi,
“To kai yaya me yasa baka biya mata kud’in jirgi ta tafi can d’inba?”

“Oh so kike ta tafi ke kuma sai ki tsaya a gidan ke kad’ai?”

“Eh kuma fa haka ne Hajiya ki bari kawai sai lokacin da kikace sai ya biya mana mu tafi taren koh Ya’ya”

“Oh haka ka zama sai abunda tace maka shi zakayi kuma?
To ai babu
laifi mota koh Allah yasa alkhairi duniya dai Allah yasa nima na haifi yaran da suke tsaye cak wajen ganin sun sharemin hawaye na, yau idan nace motoci kaza nike so sai na zab’i wadanda za’a cikamin gida dasu, dan haka Allah ya Sanya alkhairi a kashe lafiya”

“Ameen”
meenal ta amsa dashi taja hannun Hajiyar ta maidata cikin motar AK din ta rufe mata motar sannan itama ta koma nata motar da tuni AK ya shige ciki ya zauna a gefen mai zaman banza, dan haka sai ta zaga gefen direba itama ta zauna taja motar,
ita ta fara fita daga gidan kafin shima Mansoor yabi bayan su,

sai da suka dakace shi ya rufe gate d’in gidan sannan suka kama hanya, suna tafe AK na nuna mata inda zata bi har suka isa gidan rasuwar,

Ita ko Hajiya mamaki ne yake neman sumar da ita a bayan mota ita d’aya, dai ita dai rainin wayau kawai take gani sanka sanka daga jiya zuwa yau a wajen yaran na, oh wato shi nashi salon soyayyar kenan, yafi k’arfin ya fito ya furta wato siye zuciyar ta yake son da hidimar da yake mata ko miye nufin shi,

“aiko ni nan nice maganin shi wallahi”

“Magana kikeyi Hajiya?”
Mansoor ya tambaya.

“Ah ah Malam Mansoor cigaba da tuk’inka kawai”

Yauma kamar jiya a kofar gidan dukan su suka nemi waje faka,

“Nace to batun abincin sadaqa in akwai inda zan samu wadanda zanba aikin girkawa su kawo nan ina buk’ata”
Cewar Hajiya a yayinda AK ya bude mata kofar mota ta fito

“Abincin sadaqa kuma Hajiya?”

“Kwarai kuwa ko shi kenan dan munzo gaisuwa sai mu share waje mu zauna ana dafawa ana bamu muna cinyewa?”,

“Ah ah Hajiya ba abunda nike nufi ba kenan, zan biya ta restaurant din da nike siyan abunci inyi magana dasu sai su kawo abincin ko zuwa da rana ne!”

“To hakan ma yayi Allah ya bada lada, ke kuma zaki fito daga cikin motar mu wuce ciki ko har yanzun baki gama karema motar kallo bane tukun?”

AK Bai bisu zuwa cikin gidan ba ya dai gaisa da mazan dake waje sai su Baba Adamu dake harabar gidan ya musu gaisuwa dan jiya da dare basu had’u da Baba Adamu da Baba Auta ba ya d’anyi zama na mintuna kad’an ya koma cikin motar shi Mansoor yaja suka juya.

Suma su Hajiya sai da suka tsaya suka gaisa dasu Baba Adamu dake harabar gidan dasu Farouq sannan suka wuce sashen Raheenat a can ma wani sabon gaisuwar sukayi kafin suka fito,

Mommy Hauwa ce tayi musu jagora yauma zuwa sauran sashen suma suka musu gaisuwa,

anci gaba da zaman makoki yayinda yan uwa da abokan arziki sukaci gaba da bulbulowa tako ina suna zuwa domin yin nasu gaisuwar suma,

da yawan wad’anda basu samu isowa tun jiyaba sune sukayi sammakon isowa yau d’in cikin su harda k’annen Malam biyu Mata wato Aisha da suke kira da (Momin Abuja) da kuma Fatima (Momi Zahra) wacce take aure a kano wato Maman su ya Abakar wanda yaso Raheenat a shekarun baya,
Mutanen Zaria su suka fara isowa kafin na kano su, Meelat da Maryam sai misalin 12 na rana suka samu damar isowa su kuma Musty ne ya kawo su,

Yau dai Raheenat tayi dauriya sosai wajen hana kanta kukan data wuni tanayi a jiya, ga kuma yan uwanta da suka cika sashen nata tako ina ta juya su take gani, motsi kad’an zatayi a fara tambayan ta
“Me take so? Me yake mata ciwo, ”
Gaba daya basu bar mata fagen da zata samu nasa kanta a cikin damuwa ba, dan haka ganin yanda suke mata yasa itama ta sake a cikin su duk dadai bawai hirar take taya suba tana dai zaune ne da carbinta a hannu tana ja,
Iso war mutanen Abuja ne yasa falon ya k’ara daukar harami domin kuwa duk da cewa ana cikin jimamin rashin da akayi hakan bai hana yan uwan baiyana farin cikin su na ganin juna ba,
Babbar mota mutanen Abujan suka ciko mai d’auke da Momin Abujan ita da ahalin ta yara da manya, dan duk wanda yaji batun rasuwar shima sai yace zaije dan haka duk ta kwaso su suka taho tare,

Misalin k’arfe 2 da wani mintuna ne kiran AK ya shigo cikin wayar Meenal inda yake shaida mata cewa ta fita kofar gidan abincin sadaqar da Hajiya ta buk’ata ya iso wato ta fita tayima matan iso su shiga da abincin cikin gidan,

Hijjabin ta ta saka bayan tayi magana dasu Meelat akan su rakata kofar gida daga nan ta nuna musu kyautar data samu yau da sanyin safiyar Allah, suko basu musa ba suka rufa mata baya dan dama sun gaji da zaman waje d’ayan da sukeyi a cikin d’akin tun d’azun , Hajiya ta fara nema ta fad’a mata isowar masu abincin kafin ta fice tare dasu Maryam,
da kuma wata yarinyar Momin abujan mai suna Amina itama amma suna kiranta da Sultana wacce tun isowar su ta mak’ale ma Meenal dan basu tab’a ganin juna ba domin ita Sultanan ba a hannun Momin Abujan ta tashi ba, rasuwar marik’iyar ta ce yasa ta dawo gida dan haka ba kowa ta sani a cikin mutanen Zaria ba wannan dalilin nema yasa suka kwaso suka taho dan daga nan kadunan Zaria zasu wuce suyi Zumunci kafin su koma ta yanda zasu san yan uwa sosai dan kaf a cikin ahalin yan Abuja ne kad’ai wad’anda ba kowa ya sani ba suma kuma hakance a wajen su .

Suna shirin wuce inda su Baba Auta ke zaune Baba Adamu ya kira Meenal din da cewa,

“Ke Meenal ku zonan”

Karasawa wajen sukayi ita dasu Sultanan,

“Sultana koh?”
Baba Auta ya tambaya yana nuna Sultana d’in,

“Eh Baba” ita kuma ta amsa,

“Lallai ba shakka girman d’an mutum babu wuya, kin san wadan nan?”
Ya tambaya yana mata nuni da su Ya Farouq dake zaune a wajen gefen su Baba Adamun,

Girgiza kai tayi kafin ta amsa mishi da cewa,
“Ah ah a iya hoto kawai na sansu, kuma suma ai nasan basu sanni ba”

“Gaskiya ne kam ko kun santa?”
Shima baba Adamu ya tambaya yana kallon su,
wasu daga ciki sun amsa da cewa sun Santa lokacin tana k’arama wasun su kuma suka amsa da cewa basu Santa ba,

“Ke kuma fa Uwata kin san wannan?”
Baba Adamun ya tambaya yana nuna mata wani mutum dake zaune a gefen dasu Ya Farouq ke zaune tana lura dashi tun da sukazo wajen yake amsa waya ba kajin komai sai labarcin shi dake fita a tsaftace daga bakin shi kamar wani bak’on balarabe,

Wanda shima jin ana tambaya akan ko an san shine ya sashi d’agowa, ido cikin ido suka kalli juna shida Meenal kafin ta kauda kanta ta amsa tambayar na Baba Adamu da cewa,

“Ah ah ban san shiba, ban ma tab’a ganin shiba sai yau, wane ne shi d’in? ”

“Kunga irin ta ko ana zaune cikin k’asa d’aya illah banbancin gari kawai amma ace an wayi gari d’an uwa bai san d’an uwan shiba, tun yanzun da muke raye hakan yana kasancewa, anya in muka shud’e zaku iya rik’e zumuncin ku kamar yanda mu iyayen ku mukayi kuwa?,
Koda yike ba laifin ku bane duka laifin Aisha ne da bata son turo Yayan ta in anyi hutu su zauna tare damu, su mutanen kano waye zaice bai san suba tunda lokaci zuwa lokaci ko babu sha’ani suna shigowa cikin yan uwa ayi zumunci dasu, to kin ganshi nan yayanki ne shima bayan shi akwai wasu ma Sunan shi Naseer shi kam duk da baya zama a k’asar duk yafi sauran yan uwan shi zumunci ga kanwar shi nan itama Sunan ku d’aya kinga itama sai yanzun data girma sannan ta nemo mu”

“Ayya Baba aini Wallahi dan dai bana kusa daku ne da idan na fara muku jelen zuwa hutu sai kun gaji kunce in zauna a gidan mu, kuma ko yanzun tunda har Allah yasa na dawo to wajen ku zan tare kaga koh Baba shi yasa da zamu taho fa na kwaso kaya masu yawa saboda in zauna tare daku”

Ta fad’a da sauri tana katse baba Adamu,

“Ah to in ko hakane kin kyauta gaskiya” cewar Baba Auta shima,

Su Fauxieyerh kanwar Meenal da suka shigo gidan yanzun ita da Sauran yan matan dake tasowa na gidan Malam din ne Meenal ta kira,

su taba umarnin su koma wajen su duba motar wad’anda suka kawo abincin sai su shigo dasu,
Komawar kuwa sukayi suka shigo dasu tace su musu jagora zuwa wajen Hajiya,

Su d’an bata lokaci kad’an tare dasu Baba Adamun ana hirar zumunci kafin suka fito kofar gidan,

Daya bayan daya ta bisu da kallo fuskarta cike da murmushin da yak’i daukewa a fuskar nata yau tace
“ku duba cikin jerin gwanon motocin nan ku ganomin wacce tafi kyau a cikin su, ”

“Bebs wannan ai jan raine da d’aukar alhaki dallah ni bana son wulakanci in zaki nuna mana kawai ki nuna mana atoh”
Maryam ce tace haka,

Key d’in dake hannun ta ta latsa k’arar da motar tayi ne yasa suma saka saki k’ara harda tsallen murna a tare,

“Wai Allah Qawata wane d’an aljannan ne ya baki kyautar wannan lafiyayyen motar? Kai gaskiya ko waye yaci a jinjina mishi Allah ni wannan ma har sai tafi min waccan da Sarki ya baki kyau ko Meelat?”

“Ke dallah barni ni ina zan wani iya tantancewa wannan surprise duk ya rud’ani, gaskiya nayi miki murna sosai wallahi Qawata ubangiji Allah ya tsare ya kare,amma dan Allah waye da wannan k’atoton dawainiyar haka? Ko toshi aka fara mana tun yanzun ne bani da labari dan wannan motar ai tafi k’arfin ayi kyautar ta haka nan babu wani Babban dalili kawata fad’amin wani Babban kifin ne kika kamo mana kin san wallahi ke me sa’a ce duk inda kika shiga haka nan Allah ya yiki”

Meelat ta tambaya tana dawowa da baya inda Meenal ke tsaye tana musu dariya,

“To yanzun tambayar wanda ya siya motar zakuyi ko zaku shigane mu d’an zaga gari?”
Ta tambaya tana d’age musu girarta guda d’aya ta wani kashe musu idon ta d’aya,

“Kema ai kin sani dole ne ma mu d’ana ta wallahi, amma ni zan tuk’a”

Cewar Sultana da itama ba’a barta a baya ba wajen tayasu murnar sabuwar motar,
Key din Meenal ta mik’a mata ita tajasu suka bar unguwar, Maryam dake gaban motar ita ke nuna mata inda zasubi dan ita kam tasan kan garin na Kaduna sosai sab’anin su Meelat da Meenal daba wani zuwa garin sukeyi ba in ma sunzo abunda ya kawo su kawai sukeyi su juya,

“Qawata wai bazaki fad’a mana waya miki kyautar motar nan ba?”

Meelat ta tambaya tana marairaice wa,

“Humm ki bari kawai my sister idan na fad’a miki ke kanki sai kinyi mamaki, ke Hajiya mafa sai da takai hannun ta jikin shi ta tabbatar da cewa lafiyan shi qalau yana a cikin hayyacin shi yayi kyautar sannan ta yarda,”

“Ke tsaya wai taubashin kine ya baki motar nan kyauta๐Ÿ˜ณ kowa? ”
Maryam dake gaba ta juyo tana tambaya cike da mamaki,

“Kin cinka dai dai An mata,
shi din dai yau kam naci mota halak malak dan Wallahi bai isa kuma zuwa anjima yace wasa yake min ba Allah ma yaso ni a gaban Hajiya da wanda yake zaune a gidan nashi akayi komai”

“Ke Meenal anya Yayan nan naki ba sonki yakeyi ba kuwa?๐Ÿค””
Meelat ta tambaya tana rike baki,

Ita dai Sultana tunda ba sanin wanda suke magana akan shi tayi ba shi yasa ba tasa musu baki ba,

“Umm umm baso ba aurena zaiyi, kawai shi kenan mutum bazai baka abu tsakani da Allah ba sai in akwai so a tsakanin ku, iskancin banza ina ce ni daku turaren shi muke fesawa me yasa tun da yake siyan turaren yana bani bai tab’a cewa yana sona ba, keni rabani me zai Kaini auren taubashi inba so nike hawan ruwa ya kamani ina zaman zamana ba”
Meenal ta bata amsa tana harar ta.

“Ameen ya rabbi Allah yasa ya aurekin, yo ai mu bazamu k’iba wallahi dan mu abun farin ciki ne ma a wajen mu ace yanda muke mu ukun nan muna auren Aminan juna, ba shike nan ba kuma zumunci sai illah masha Allah me yafi hakan dad’i,
Nidai zan baki shawara da zuciya d’aya wallahi Qawata ko da wasa AK ya bud’e baki yace son ki yake ki rufa mana asiri kiyi saurin Amincewa da wur wuri kai in so samu nema sai a had’e bikin mu wallahi”

“Ah ah ba biki ba suna”
Ta fad’a tana kaima Meelat dake dariya duka.

“My Sister Allah kuwa inhar abunda suka fad’a ya tabbata da gaske ki amsa kawai, dan Wallahi ina fad’a miki ba k’aramin mutum bane zai miki irin wannan kyautar”
Cewar Sultana da sai yanzun tasa musu baki.

“Rabu dasu kinji shima bazai wani fara cewa yana sona ba, dan ni mijin kaina nike so ba wanda zan dunga rabashi da yan mata ba, ai tunda kina nan zaki ganin ma idon ki ni inani ina auren mijin da idan ya fita gida zuciya ta zatayi ta hailala da salati har sai ya dawo”.

Sunyi yawo sosai gidajen kawayen su dake cikin gari basu suka koma unguwar dosa ba har sai bayan la’asar liss,

Dare nayi kuma suka tattara ita dasu Maryam din da Hajiya suka wuce gidan AK dan yanda gidan ya k’ara cika yau abun harba masaka tsinke,
D’ayan d’akin dake gefen wanda suka sauka ita da Hajiya suma su Maryam suka sauke nasu kayan, Hajiya dai da wuri tayi bacci sakamakon ciwon kan da tace yana damunta, wanda hakan ne ya basu damar shiryawa suka fice daga cikin gidan bisa jagorancin Maryam da kuma Meenal data Sanya musu kwad’ayin Ice cream din da AK ya siyo mata jiya,

Yawo suka sha abunsu sukayo siyayyar abubuwan da suke so, basu suka dawo gidan ba sai wajen 11 da wani abu,

Shiko AK yau da wuri ya dawo, sai dai ga mamakin shi Hajiya kawai ya samu a d’aki tana bacci, dan haka bai tashe taba ya fita daga sashen wajen Mansoor yaje ya tambaye shi
“tun yaushe Meenal ta fita daga gidan nan”

“Tun bayan da akayi sallan isha’i suka fita”

“Suka fita ba ita kad’ai bace kenan?”

“Eh su 4 ne ita da kawayen ta”

Komawa ciki yayi ya kunna TV din dake falon yana kallo lokaci lokaci kuma yakan daga kai ya kalli agogo,
Karfe 10 nayi ya d’auki wayar shi ya kira number d’inta,

“Kuna ina ne har yanzun baku dawo gida ba kun san kuma dare yayi?”
Ya tambaya bayan ta d’aga wayar daga can bangaren ta,

“Mun d’an fita ne amma yanzun zamu dawo insha Allah”

Daga karfe 10 zuwa 11n nan ya kirata a waya yafi k’arfin sau goma daga karshe ma tsoro ya faraji ko Sunje sun shiga wani unguwar da suka bace hanyar komowa gida ne,
Dan iskanci kuma daga baya ma sai ta dena d’aukar wayar shi, sai yayi yunkurin fita ya nemo su sai kuma yayi tunanin ai baima san ainihin inda suke ba,
Gagara zama a falon yayi ya fito tsakar gidan yana ta faman zuwa da dawowa, ba karamin salama ne ya ziyarci zuciyar shi a sa’ilin da yaji karar horn d’in motar su a kofar gate d’in gidan ba,
Mansoor ne ya bud’e musu gidan domin shima yanda yaga AK ya damu sai ya kasa sukuni shima.

*Kuyi hakuri uzurine mai k’arfi ya d’auke hankali na shi yasa bakuji niba*

#MEENAL
#MAI JAMA’A
#NASEER
#SARKI
#MOON
#TEEMAH

*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button